Join Our WhatsApp Group

HIKAYAR JANSHAHU DAN SARKIN KABUL Complete Hausa Novel Document by HIKAYAR JANSHAHU DAN SARKIN KABUL


HIKAYAR JANSHAHU DAN SARKIN KABUL

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 25721



HIKAYAR JANSHAHU DAN SARKIN KABUL

Reading Time: 2 Hours

Added On: 10, Oct 2023

Author: Danladi Z Haruna ,Prof Ibrahim Malumfashi ,Bukar Mada ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08071051138, 08032767547, +1248032767547

Book License : Free

Category: Tales

File Size: 135.76 kb

File Type: txt

Views: 567+

Download: 271+

Last download: 2 days ago

Description/Story: This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng

1. HIKAYAR JANSHAHU DAN SARKIN KABUL

Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA

Sabuwar Fassarar:

Ibrahim Malumfashi,
Danladi Z. Haruna,
Bukar Mada.

... Bulukiya ya shiga cikin tsibiri yana yawo, sai ya tarar da wani saurayi kyakkyawa, fuskarsa tana sheki, hawaye na tarara daga idanunsa. Yana zaune tsakanin wasu kaburbura guda biyu, yana kuka yana gunji. Bulukiya ya yi masa sallama, saurayi ya dakata da kuka ya mayar masa da sallama. Bulukiya ya tambaye shi, "Wanene kai? Wadannan kaburburan fa? Su waye a cikinsu?"

Saurayi ya dube shi ya kara fashewa da kuka. Ya yi kuka har sai da hawaye suka jike masa gaban riga. Sa'annan ya ce, "Ka sani ya kai dan uwana, labarina abin mamaki ne da ban tausayi. Amma ba zan gaya maka shi ba har sai ka zauna tare da ni ka gaya mini labarinka da kuma inda ka nufa."

Bulukiya ya sami wuri kusa ga saurayi ya zauna. Ya kwashe labarinsa duka, tun daga mutuwar mahaifinsa da yadda ya fito gida da dalilin fitowarsa da abubuwan mamaki da ya gamu da su, ya gaya wa saurayi. Ya kara da cewa, "Yanzu Allah kadai ya san abin da zai faru gare ni bayan wannan."

Saurayi ya yi ajiyar zuciya, bayan ya ji labarin Bulukiya. Ya ce, "Ya dan uwana, Wallahi ba ka ga kome na mamaki ba a kan abin da na gani. Ka sani ya kai Bulukiya, ni na gamu da wakilan Shugabanmu Annabi Sulaimanu a wadanda ya dora kan wakilci tun a lokacin rayuwarsa. Na gamu da abubuwan mamaki barkatai. Hakika labarina bako ne, ina so ka zauna nan wurina har in gaya maka dukkan labarina. Za ka ji sababin zamana a wannan wuri, da labarin wadannan kaburbura da kake gani."

Lokacin da Sarauniyar Macizai ta kawo nan da labarinta sai Hasibu ya katse ta ya ce, "Allah ya ba ki nasara ya Sarauniya, ki bar ni in tafi gida. Ki hada ni da bayinki su fitar da ni daga wannan rami su kai ni bisa ga bayan kasa. Na rantse miki da Allah idan na koma gida ba zan kara yin wanka a gidan wanka ba sai a gidana duk tsawon rayuwata."

Ta ce, "Ba zan bari ka fita daga wannan rami ba, domin ban yarda da rantsuwarka ba." Da ya ji haka sai ya fashe da kuka, macizai suka yi kuka don tausayinsa. Suka shiga ba Sarauniya hakuri suna cewa, "Muna rokonki ki hada shi da daya daga cikinmu ya fitar da shi daga wannan rami. Ya ranste miki ba zai kara shiga gidan wanka ba tsawon rayuwarsa."

Yayin da Sauraniyar Macizai, mai suna Yamlaika, ta ji macizai sun matsa mata da roko, sai ta juya wurin Hasib ta sa ya rantse har cikin zuciyarsa cewa bayan ya fita daga wurinta ba zai kara shiga gidan wanka ba. Bayan ya rantse sai ta umurci wani katon maciji, wanda ya fi jaki girma, ya dauke shi ya fitar da shi waje. Maciji ya duka zai dauke shi, sai ya juya wurin Sarauniya Yamlaika ya ce, "Ba zan tafi ba sai na ji labarin saurayin nan da Bulukiya ya iske yana kuka a cikin tsibiri da kaburbura a gabansa."

Sarauniya ta ce, "Ka sani ya Hasibu, yayin da Bulukiya ya gaya wa saurayi labarinsa tun daga farko har karshe, ya kuma zauna domin jin labarin saurayin da dalilin zamansa a wannan wuri yana kuka da kaburbura biyu a gabansa. Sai saurayi ya ce masa, "Ya dan uwana, me ka gani na mamaki? Ai ba ka ga kome ba akan abin da na gani. Ni na ga wakilan Shugaba Sulaimanu wadanda ya nada da kansa a lokacin rayuwarsa. Na hadu da abubuwan mamaki iri-iri wadanda wanina bai taba gani ba. Sai ya fara labarinsa kamar haka:

LABARIN JANSHAHU DAN SARKIN KABILA

Ka sani cewa ya kai Bulukiya, mahaifina Sarki ne, sunansa Daigamusu. Yana mulkin daular Kabila (Kabul) da ta Banu Shahalan. A karkashin mulkinsa akwai daulolin sarakuna dubu goma, kowane sarki yana mulki da birane dari, kowane birni yana da kauyuka dari a karkashinsa. A cikin kowane kauye akwai akalla gidaje dari. Duka wadannan dauloli sukan kawo masa haraji a kowace shekara. Saboda haka a tsaya kwatanta yawan arzikinsa da yawan askarawansa bata lokaci ne kawai. Ya kasance Sarki mai adalci, yana kuma mulkin jama'arsa da gaskiya. Sai dai duk da wannan ni'ima da yake ciki, Allah bai nufe shi da samun da ba, wanda zai gaje shi bayan ransa.

Kullum da wannan tunani mahaifina ke kwana, da shi yake tashi. Ran nan dai sai ya sa aka tara masa dukan Malaman kasar, da masu bugun taurari da masu hisabi. Ya ce musu, "Ina so ku duba mini taurari ku gani, shin zan sami dan da zai gaje ni kafin mutuwata?"

Kowanensu ya dukufa ga aikinsa. Masu bugun taurari suka shiga zane bisa kasa suna sharewa, masu hisabi suka shiga lissafi, Malamai suka dauko takardu suka shiga nazari. Zuwa can suka ce masa, "Ya Sarki, hakika Allah zai arzuta ka da haihuwar da namiji. Amma ba za ka sami wannan da ba sai tare da 'yar Sarkin Hurassana."

Sarki ya yi farin ciki da wannan albishir na Malamai. Ya yi musu kyauta mai tarin yawa, ya sallame su. Ya kira babban Wazirinsa mai suna Ainazari, shi kuma wani shahararren jarumi ne wanda shi kadai yakan fatattaki rundunar mutum dubu. Duk fadin daular Kabila da kewayenta sun san shi, sun san tsananin jaruntaka tasa. Da ya zo Sarki ya gaya masa abin da Malamai suka gani a cikin taurari. Ya kara da cewa, "Yanzu sai ka shirya maza ka tafi zuwa Hurassana, ka nemo mini auren 'yar Sarki Baharwanu."

Waziri Ainazari ya tafi ya hada tawagar da zai tafi da ita, suka kafa tantuna bayan gari suna jira Sarki ya sallame su. Sarki Daigamusu ya kawo dukiya mai yawa ciki har da kyankyandi na alharini alfan da dari biyar, da zinariya da azurfa da yakutu da sauran duwatsu masu daraja, ya ce a kai wa Sarki Baharwanu. Ya kuma kawo kaya irin wadanda amarya za ta bukata wajen yin ado ya bayar. Aka labta wa rakuma da alfadarai kaya. Kafin su tafi Sarki ya dauko takarda da alkalami ya rubuta wa Sarki Baharwanu wasika. A cikin takardar ya rubuta:

Bayan gaisuwa da fatar alheri, daga Sarki Daigamusu zuwa ga Sarki Baharwanu. Ka sani cewa mun tara masana ilimin taurari da hisabi sun gaya mana cewa za mu samu haihuwar da namiji, amma wannan da ba zai samu ba face tare da 'yarka. Saboda haka ne na turo Wazirina Ainazari tare da gaisuwa zuwa gare ka da kuma dukiyar neman aure. Na umurce shi, idan ka yarda, ya zama wakilina a wurin auren da duk wata hidima da za a yi. Idan an kammala kome ya zo mini da amarya. Kamar yadda na sanka mutum mai saukin kai da saurin fahimtar al'amurra, na san ba za ka juya wa wannan muhimmiyar bukata tawa baya ba. Kada ka manta ya Sarki Baharwanu, ni ke mulki da daular Kabila da ta Banu Shahalan, a karkashina ina da dauloli masu karfi. Idan na auri 'yarka za mu yi tarayya a cikin mulkin wadannan dauloli, na kuma yi alkawari zan rika turo maka da wani yanki na harajin da nake karba duk shekara. Ko ba kome ma, ai dan da za mu haifa shi zai gaje ni, kuma jikanka ne. Wannan ita ce bukatata zuwa gare ka.

Sarki ya like bakin takarda, ya manna mata wata alama shaidar daga gare shi take, ya ba Wazirinsa. Waziri ya tafi tare da tawagarsa zuwa birnin Hurassana. Kwanci tashi har suka isa bayan birni, suka kafa tantunansu. Yayin da labarin zuwansu ya iske Sarki Baharwanu sai ya ta da manyan fadawansa domin su tarye su. Aka aza wa dabbobi abinci da abin sha da kuma harawa saboda dabbobi, suka nufi wurin tawagar Waziri Ainazari da ke bayan gari. Da suka isa suka sauka daga kan dabbobinsu, suka gaggaisa da juna, aka shirya abinci da abin sha. Suka zauna suka ci suka sha har suka tumbatsa, daga nan sai suka shiga hira. Haka suka kasance a bayan gari tsawon kwana goma, sa'annan suka shirya kayansu duka, suka hau dabbobi suka dunguma sai cikin gari. Sarki Baharwanu ya taryi Waziri Ainazari a bakin fadarsa cikin murna da farin ciki, suka rungumi juna, Sarki ya ja shi zuwa cikin fadarsa.

Ainazari ya kawo dukan dukiyar da ya zo da ita daga Sarki Daigamusu ya ba Sarki Baharwanu, ya zaro wasika ya ba shi. Bayan Sarki ya karanta wasika ya fahimci sakon da ke cikinta, sai murna ta kashe shi. Ya juya wurin Waziri fuskarsa cike da fara'a ya ce, "Ka yi murna ya kai Waziri, Wallahi da Sarki Daigamusu zai bukaci rayuwata da sai in ba shi balle 'yata." Ya tashi ya shiga cikin gida, ya tarar da diyarsa da mahaifiyarta, ya kwashe labarin abin da ke tafe da Wazirin Sarki Daigamusu ya shaida musu. Ya tambayi ra'ayinsu, suka ce ya yi abin da duka ya ga ya dace. Ya kuma tara fadawansa ya gaya musu dalilin zuwan Ainazari, ya nemi shawararsu. Su ma suka ce masa ya yi abin da duk ya ga ya dace.

Za mu ci gaba gobe, da karfe tara na dare (9:00PM), in sha Allah.

Allah ya kai mu!2. HIKAYAR JANSHAHU DAN SARKIN KABUL

Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA

Sabuwar Fassarar:

Ibrahim Malumfashi,
Danladi Z. Haruna,
Bukar Mada.

Sarki Baharwanu ya nemi shawarar iyalinsa da fadawansa, suka ce masa ka aikata abin da ka ga ya dace. Sai ya tafi wurin Waziri Ainazari ya shaida masa cewa ya amince da bukatar Sarki Daigamusu ta auren 'yarsa. Waziri ya zauna a wannan birni tsawon wata biyu, daga nan sai ya ce wa Sarki, ya kamata a yi haramar daurin aure domin yana so ya koma kasarsu. Sarki ya ce, wannan shi ne zancen hankali.

Aka shirya dukan abin da ake bukata na daurin aure. Sarki ya tara waziransa da hakimai da fadawa da malamai, kai har da talakawan gari sai da aka gayyato. Aka taru tinjim a kofar fada. Sarki ya umurci malamai su kulla auren Sarki Daigamusu da 'yarsa karkashin wakilcin Waziri Ainazari. Bayan an daura aure, Sarki ya sa aka kawata birni da kwalliya, aka shimfide dukkan hanyoyi da shimfidu na alfarma. Aka shirya amarya da kayan ado iri-iri ta fito kamar 'yar tsana.

Da ranar tafiya ta zo Sarki ya kawo dukiya mai yawan gaske, tare da duwatsu masu daraja, ya ba 'yarsa. Aka shirya mata darbuka ta musamman bisa wata rakuma wadda za ta hau. Amarya da tawagar Waziri Ainazari suka dunguma zuwa birnin Kabila. Yayin da labari ya riski Sarki Daigamusu, sai ya yi kamar ya kashe kansa don murna, ya sa aka yi ta buga tambura a cikin birni. Da ya kwatanci Waziri da amarya sun kusa isowa, ya yi umurni aka kawata birni aka shiga shagalin tarye. n amarya.

Da amarya ta iso bayan gari, Sarki da duka jama'ar gari suka fita suka taro ta. Aka dawo cikin gari aka ci gaba da goce ganguna babu kama hannun yaro. Aka yi kamar kwana bakwai ana sabga, sa'annan kowa ya kama gabansa. Tun a daren farko Sarki ya shiga dakin amarya ya kawar mata da budurci, ya mayar da ita mace cikakkiya. Tun daga wannan rana wata ya bace mata.

Bayan wata uku ciki ya fara bayyana, murna a wurin Sarki ba sai an fada ba. Da watanni haihuwa suka cika, ta haifi danta namiji wanda don tsananin kyawonsa har mata suka fara gulmar ko ba mutum ba ne. Yayin da Sarki ya sami labarin matarsa ta sauka lafiya kuma an sami yaro kyakkyawa, son kowa kin wanda ya rasa, nan da nan ya sa aka tara masa masana ilimin taurari da hisabi. Ya ce musu, "Ina so ku buga kasa ku duba mini taurari. Ku gaya mini abin da zai faru ga wannan yaro tun daga yanzu har zuwa lokacin mutuwarsa."

Suka share kasa suka yi zane, bayan sun yi nazarin zanen sai suka ga cewa wannan da na Sarki zai girma har ya zama saurayi ba tare da wani mummunan abu ya same shi ba. Amma idan ya shekara goma sha biyar zai auka cikin kunci da wahalar rayuwa. Idan ya tsallake wannan wahalar zai zama babban Sarki wanda har sai ya fi mahaifinsa shahara. Suka gaya wa Sarki abin da suka gani, ya yi murna da farin ciki. Ya rada wa yaro suna Janshahu.

Sarki ya danka yaro ga hannun mai shayarwa da reno, ta shayar da shi tsawon shekara biyu sa'annan ta yaye shi. Ta ci gaba da renonsa har ya kai shekara biyar. Yayin nan mahaifinsa ya ci gaba da koyar da shi karatu da rubutu. Ya koyar da shi addini da koyarwar littafin Linjila. Sarki ya koya masa fada da takobi da harba baka da suka da mashi. Kafin shekara bakwai Janshahu ya zama jarumin gaske. Ya kware ga hawan doki, ya iya sara da takobi, ya iya harba baka, ya iya suka da mashi, ya zama gwanin zamuwa. Sai ya kasance babu abin da ke kayatar da shi irin farauta.

Wata rana sai kaddara ta sa Sarki Daigamusu ya fita farauta tare da dansa da askarawa masu yawa. Suka kutsa kai cikin daji suka yi ta kisan namun daji, tsawon kwana uku. Ran nan da rana tsaka, sun tsaya suna hutawa a cikin inuwa, sai dan Sarki ya ga wata barewa, launin jikinta gwanin ban sha'awa, ta gifta ta gabansa da gudu. Nan take ya zaburi dokinsa ya tasar ma ta, askarawa bakwai suka sakar wa dawaki linzami suka bi bayansa.

Da barewa ta ji kofatan dawaki bayanta sai ta kara mai, su kuma suka ci gaba da bin ta har ta kawo su bakin teku. Tana isowa bakin ruwa sai ta tirje domin ba hanya. Suna zuwa sai suka yi kukan kura da nufin yi mata kofar rago. Ita kuwa tana ganin haka sai ta yi kulin kubura cikin teku, rakuman ruwa suka ja ta suka tafi da ita, sai ta fada cikin ragar wani masunci. Ta yi, ta yi ta fita, ta kasa. Janshahu ya sauka tare da askarawa suka kwance wani kwale-kwale da ke daure a bakin gabar tekun, suka shiga suka nufi wurin da raga ta kama barewa, suka bar mutum guda a bakin gaba yana tsare musu dawaki.

Suka kama barewa suka sa a cikin kwale-kwale, sun yi niyyar juyowa sai dan Sarki ya hangi wani tsibiri a gabansu. Ya ce wa askarawa ina so in dan yawata cikin wancan tsibirin. Suka tuka jirgi suka nufi tsibiri. Da suka isa sai suka daure jirgi a gaci, suka shiga cikin tsibiri suka yi ta yawo suna kashe kwarkwatar ido. Can da yamma ta yi, sai suka hawo jirgi tare da barewa suka yi nufin juyowa zuwa ga dawakinsu. Allah da ikonsa sai wata...


Read / Download HIKAYAR JANSHAHU DAN SARKIN KABUL

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album