Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

JININMU DAYA Complete Hausa Novel Document by JININMU DAYA


JININMU DAYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 92472



JININMU DAYA

Reading Time: 7 Hours

Added On: 06, Jun 2024

Author: Sadiya Ibrahim Khalil ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08144665937

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 504.96 kb

File Type: txt

Views: 705+

Download: 773+

Last download: 3 days ago

Description/Story: A*JININMU DAYA*

NA

SADIYA IBRAHIM KHALI

1

Godiya
Ga Allah(SWT) tsira da aminci sukara tabbata ga Annabi Muhammad(SAW)
Godiya har kullum ga mahaifana da 'yan uwana Allah ya saka muku da mafificin Alkhairi

*SADAUKARWA*
*Sadaukarwa ga Alhaji Ibrahim Khalil family*
*Da 'Danbakane Family*

*GARGA'DI*
Ban yarda wata ko wani su yi anfani da wani shafi ko littafin gaba daya saida izinina
08144665937

*TUNATARWA*
Banyi wannan littafin don cin zarafin wani ko wata ba ta hanyar anfani da suna ko garuruwan dake cikin littafin ba duk wanda littafin yaci karo da rayuwar wata ko wani yayi hakuri arashi ne bawai da sani bane duk kuskuren da nayi a littafin ga wani ko wata bisa rashin sani ya femin domin dan Adam ajizine ina rokon Allah ya femin duk kuskeren da zansamu a rubutun nan

*SHINFI'DA*
*Kaddara bata taba sauyawa da mizanin rubutun ta saidai addu'a takan jawo zuwanta da sauki 'dan uwa komai yadda abubuwa suka ta'azzara ga juna ba'a canzashi zaka iya canza komai amma banda 'dan uwa karka zamo mai rabon kawunansu 'yan uwa komai tsanani domin shi dan uwa tamkar kashin baya yake duk sanda ka rasa sa to tambar wannan kashin bayannaka ya karye kayi afuwa da rangwame da kyautatawa ga duk yan uwanka ka nufesu da alkhairi domin shi dan kone baya faduwa kasa banza babu riba ga duk wanda yakasa hakuri da dan uwanshi domin karshe danasani zaiyi mara yankewa hakama iyaye sa babu wani mai canza wannan sunan gareku ga 'ya'yanku karkai tsinuwa karka la'ancesa domin dai sunan dai bazai canzama ka haifeshi karkayi fushin da zai jawo rusa kaunar dake tsakaninka da ya'yayennaka domin uwa da uba sune bangon da muma muyi kokarin gyara biyayya ga iyayenmu komai tsanani muddin ba akan sabon Allah sukesan muyi biyayya garesu ba domin sudai iyaye koda daga haifarmu suka yardamu ba abin wulakantawa bane kuma shi kanshi lokacin sakaraine munaji muna gani zaizo yawucemu batareda mun aikata dai-daiba a cikin lokacinmu Kaddara kuma ba abinda bata sauyawa*

*TAURARI*

*ABDUL-RA'UF*
*RUFAIDA*

*FARKON LABARI*

A nutse ta iso falon ta tsaya bayan kujerar da matashin da zai haura shekaru 33 da yake zaune wani yaro a cinyarsa yana shafa kanshi matashiyar bazata haura shekaru 22 zuwa da 23 ba sai da yaji numfashi a bayansa yasa ya maida dubensa kacokam ga bayan kujerar a tsaye ya sameta ta harde hannayenta tana murmushi ya dan sauke ajiyar zuciya yace Rufaida na lura dai sam yau tsokanata kike ji Rufaida tace bahaka bane Yaya Wahid ya dan juyar dakai yace to ya akai tace dama naga yau kurum ta Yasir kake ni ko kulani ma bakayi Wahid yace to meye damuwar Yasir dai dan kine banasan rigima dawo nan kizauna ya nunamata kujerar da suke ta zauna kusa da yasir tana mai ambatar Bismillah Yasir Ya dan dubi fuskar Rufaida yace Mami kinji Dad sai je Zaria kuma ba zashi daniba Rufaida ta Kalli Ahad tace kaji Dad kurum ka bari wani satin sai mutafi mu duka ya dan marairaice yace Mami kinsan kiran Umma ne gwara na naje wani satin saina kaiku tunda ba kwana zanyi ba tace haba Yaya yaza'ai ka tafi yau ka dawo yau yaushema harkabar Abujar yace ai bawai a motar haya zaniba zan iya kaiwa har na juyo ni narasa Kiranma Umma takemin Rufaida tace ni fatana ma dai har kullum Allah yasa lafiya kalau nima kiran na kasa gano dalilinshi yace to Allah yasa lafiya Rufaida sam bazata iya furtawa mijinta tasan dalilin kiranba da mahaifiyarshi ke masaba don batun yau ba tasan komai tunma kafin aurensu shima Wahid bayajin zai iya furtawa Rufaida dalilin kiran dukda ya tabbatar Rufaida mai hakuri ce sai dai bayasan wani abu yasa zuciyar kuncin da bazata iya furta komai akaiba amma shi bayasan ace daga aurensu ya kara wani auren dukda suna da daya amma duka Yasir nawa yake baikai uku ba har yau to kuma suna zaune lafiya da matarshi meye dalilin kara auren Ruqayya da Umma takeso tayi don baya tunanin zasu zauna lafiya yaji ma da matsalolin aiki kuma yadawo gida ya tarar da wani shiyasa bai fadawa Abba zuwan ba dan yasan ba zai amincemasa yazoba shikuma yanason mahaifiyarsa yaje gareta ya mata magana yadda zata fahimcesa kota samu ta barsa da wannan zancen shi dai har ga Allah baya yiwa Rukayya irin son aure ta kasance abokiyar rayuwarsa sai dai sona zumunci tunda yasan Rufaida tasan komai shiyasa bayason jagwalgwala maganar danshi mutum ne da bayason a dinga tada abin bacin rai,Jin shirun da Wahid yayi yasa Rufaida cewa Yaya koka FASA tafiyar ne lokaci fa baya jira cikin sauri ya dawo daga tunaninsa,yace ai kema kinsan sai an amsa kiran Umma yau Insha Allah,fitowa sukayi shida Rufaida da Yasir har bakin motarsa suka kaishi yace har zai tadane Rufaida tace Yaya Wahid namanta fa zuwanmu gidan Luba yace au nashafa'a jeki ki shirya tace ai Yaya na shirya bara na rufo ciki murmushi yayi yace to suna tsaye da Yasir ta karaso ta shige gidan gaba Yasir yana baya Wahid yana zolayar Rufaida da cewa da ya tafi sai dai tahau taxi murmushi tayi tace ai kudinka ne zai kuka a bakin gate ya tsaya masu gadin Barrack din ya tsaida motar suka gaisa suna yallabai sai ina yace Zariya zanje amma su a gidan abokina Kabir zan saukesu addu'ah suka yimusu kana ya fice daga barrack din 'yan sandan na cikin garin abuja Area1 a Gwarinfa ya saukesu Rufaida har gidan Kabir ya shiga suka gaggaisa da Luba tana baya shigowa sai dai taji firarsu a sitroom yace kusan bana zuwan banzane kinsan shine dalili Rufaida tace ayimasa hakuri zai gyara Yusuf dan Luba yana ganin Yasir suka fice harabar gidan sunata fara wasa,Yace Luba ina abokin nawane yace wallahi ya fita shida Nazir amma bazasu jima ba yace ai ki kyalesa kawai ni tafiya zanyi zanje Zariya zamuyi waya idan naje,bai jira komai ba ya mike Luba tamasa addu'a Allah ya kiyaye hanya yace Amin ya fice daga Falon Rufaida ce tabisa tana masa addu'a sannan tace ya gaida kowa da kowa harda su Gwaggo da Malam da Abba yace aiko da wuya naje gidansu Gwaggo cikin bata fuska tace maiyasa yace saboda kinsan ba kwana zanyi ba tace shikenan amma dai ka daure kaje yace to ranki ya Dade abinda kikace shi za'ayi murmushi tayi tace ko kaifa Yasir ya karaso gurin Babannasa shida Yusuf suna cewa Dad Allah ya tsare Rufaida ma cewa tayi Allah ya tsare Allah ya dawo dakai lafiya a gaida kowa da kowa Wahid ya amsa da amin yana murmushi yaja motar ya fice daga gidan sai da yafita da motar Yasir ya dawo gun Rufaida yana kuka babansa ya ki tafiya dashi Rufaida ce ta shiga lallashin yasir din tana cewa idan baka daina ba Yusuf zai yima dariya ka ganshi can yana kallonka Yusuf can gurin wasa Yasir din ne ya tafi gurin Yusuf din Rufaida murmushi tayi tace kawai ta shige ciki

Luba ta kalli Rufaida tace sai yanzu kika barshi ya tafi kenan,Rufaida murmushi tayi tace kai Luba banda sharri yaushe ma muka fita,ni cikina ya fara kiran ciroma goma ta wuce na safe bikinsan mai zaki dafa ba kin daka ta wannan chat din gaskiya Yaya Kabir yana hakuri ace mace bazata gama girki ba sai wajen 4 na yamma Luba tace to hadasu kasa rabasu duka sau nawa kika zo gidan nawa kika tarar bangama abinci ba da wuri wannan chat dinma saikisa a hana mutane Rufaida tace dama yafi Luba tace da kema nasa an hanaki baki Rufaida ta ta'be tace ni kinsan baidame ni ba,Luba tacanza zancen da cewa mutumin kifa yau zanyi Rufaida tace alala gaskiya ki tashi mu dora tun yanzu haka suka mike suka shiga kitchen

Bugun Zuciyar Rufaida ne ya karu dole ta bar kitchen din taje falo ta kwanta hakanan yanzu take jin bugun zuciyar batasan daliliba anbatan Allah ta fara yi a cikin zuciyarta,wayarta ta lalubo ta danna tasa a kunne,a daya bangaren murmushi Ahad yayi ganin sunan mai kiran My wife ya daga ya gabatar da sallama ta amsa tana cewa Yaya Ya hanya yace Alhamdulillah nakusa zuwa Kaduna wayar ta ka tse tana masa addu'ar Allah ykiyaye hanya yayi murmushi yana kara jin kaunar matarsa a ransa da haka ya cigaba da tukinsa
Wahid bayan barinsa cikin Kaduna yana gaf da shiga Zariya,duk yadda yaso kaucewa motar sai da tazo ta bugi da motarsa nan motar tasa ta dinga mirginawa yanata salati motar man da tayi gefe ta kama da wuta abinka da cikin jama'a yasa dan dan nan gurin ya cika AbdulWahid ake kokarin ceto aka tsaida motar da ta fara shigewa rami kuma mai zurfi dakyar aka fiddoshi
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download JININMU DAYA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album