Join Our WhatsApp Group

RAYUWAR MARYAMU Complete Hausa Novel Document by RAYUWAR MARYAMU


RAYUWAR MARYAMU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 196550RAYUWAR MARYAMU

Reading Time: 16 Hours

Added On: 14, May 2024

Author: Aisha Muhammad Maman Shakur ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 572.5 kb

File Type: doc

Views: 220+

Download: 132+

Last download: 16 hours ago

Description/Story: kin idar da sallar ?" sai tayi shiru tana kallonsa kamar tana nazarin wani abu a tattare dashi,sai ya sunkuyar da kansa kasa.
Inna sarai tace cikin fulatanci "wai nikam babangida me yake damunka"ina lura dakai jiyama da kazo gidan nan,duk jikin ka sanyi Kalau.kodai kulun ce ba lafiya" matarsa kenan sunanta hauwa ake kiranta da kulu.duk da tasi,u ya kasance bafulatani,kuma ansan fulani akwaisu da kunya=H amma hakan bai hana inna sarai sakewa da danta ba.saboda shi kadai gareta, duk da ya kasance da na uku a wurinta amma duk sauran sun rasu baban namiji ne sunanshi sale ya rasu bayan an haifeshi da kwana uku daman bezo da lafiya ba.sai ta kuma haifar zainabu itama tana yar shekara biyar ta rasu.
Sai kuma ta haifi tasi,u wanda har ta cire rai da kara haihuwa, domin kwa bayan rasuwar zainabu sai da ta kwashe kusan shekaru goma sha 18 sannan ta samu cikin tasi,u sunsha farinciki ita da mijinta malam buba makama wanda a wancen lokacin yana da rufin asiri.kafin Allah ya karbi ransa a lokacin tasi,u yana da shekaru goma,malam din kamar yadda kowa ke kiranshi.domin malami yana koyar da karatu ne anan rugar marayo da kuma sauran rugar dake makotaka da rugar marayo din.
Malam buba ya rasu sanadiyar ciwon cikin da yayi na kwanaki biyu, inna sarai taji mutuwar mijinta sosai saboda soyayyar dake tsakaninsu, sannan shi kadai take dashi a duniya. domin marainiya ce ba uwa ba uba,sannan ba yan uwa ita kadai mahaifiyarta ta haifeta,sai wacce suke uba daya sunanta iya tsahare tana aure a wani kyauye mai suna rakumi.iya tsahare ta tsani inna sarai


Story & writing by

MOM MASHKUR.


page 5_6

Tsana ce wadda tun tasowar su,take nuna mata,haka babarta ta nuna mata.wanda hakan ba hali ne mai kyau ba. sai dai ita inna sarai bata nuna damuwa akan hakan domin ba irin tarbiyar da mahaifiyarta ta mata ba.wannan kenan

Bayan rasuwar malam buba,su inna sarai sun shiga damuwa sosai ,saboda babu abinda ya bari sai wata gonarsa da yake nomawa, itama gonar ya siyar da rabi rabin ce tashi.

Sai gidan da suke ciki wanda gida ne na kasa daki daya sai kuma bukka,da kuma rumbu wanda suke ajje kayan amfanin gona a ciki.

Inna sarai tana dorawa tasi,u tallar kayan miya,ita kuma tana saidawa a gida da manja,da yan kulle kulle na gida.ta hakane suke dan samu abinda zasu rufawa kansu asiri.har tasi,u yakai shekaru goma sha bakwai a lokacin ne ya fara bin dan makotansu hashimu zuwa legos neman kudi.

Yana aykin karfi sannan yana dako, da dai sauran aiyuka wanda yake ganin zai iya hi.kuma alhamdulillah yana samun alheri,tunda ko gida ya tashi zuwa yakan siyo klin me yar dama da sabulun wanki,da gishiri dan leda ya kawo a rabawa makota da abokan arxiki.A haka har ya shafe shekara guda, yana zuwa birnin na legos neman kudi.daga nan sai aka fara gulma ana cewa mahaifiyar tasi,u ta fifita neman kudi akan aure sunnar ma,aiki. kunsan su kauye da rugage akwai auren wuri=.

domin shi hashimun da matarsa, har da dansa. daga lokacin ne da tasi,u ya dawo daga legos ganin gida inna sarai ta hanashi komawa.tace ya bari sai anyi bikinsa ya koma sannan babu mai cewa bashi aure yana tafiya neman kudi,tace "yanzu zakaji ana cewa fasikanci kake idan kaje can"sai aka hada dan abinda ya samu da wanda inna sarai take dan tarawa aka fara shirye shiryen auren tasi,u da budurwarsa sadiya wacce suke soyayya.

sorry=O=O=Oayi hakuri da wannanStory & writing by


MOM MASHKUR

Page 7_8

Ansha biki sosai,biki irin na fulani ansha fura da nono =. amma bikin daga Jama,ar gari sai yan unguwa wato babu wani dan uwa na inna sarai, sai makociyarta salamatu babar hashimu wacce ita ce ta zame wa inna sarai kamar yar uwa.

saboda zaman na amana da sukeyi,da kuma mutunta juna.har akayi biki aka watse amma iya tsahare babu ita babu dalilinta kuma inna saratu har kauyen rakumi tasa dan mashine ya kai ta, ta fada mata bikin na tasi,u.
amma bata zo ba,itama inna sarai bata tofawa kowa ba,koda an tambayeta ita sai tace bata da lpy.shima malam buba dangin nasa sun kasance dangin takanda, sai dai muce Allah jikan rai.
an kawo amarya sadiya gidan angonta,nan cikin gidan inna sarai,inda tasi u (babangida) ya gyara dakin kasar nan, sai ya kewaye musu da kara, ya musu bandakin na iccen ridi.an kawo amarya sadiya dakinta,sai fatan allah basu zaman lpy.

Zama tsakanin inna sarai da sadiya zamane akeyinsa mai tsafta,domin inna sarai bata da fada ta dauki sadiya da tasi,u duk daya ne a wurinta. itama sadiya yarinya ce mai biyayya ta dauki inna sarai tamkar mahaifiyarta,tunda daman mahaifiyarta ta rasu wajen haihuwar autansu inusaa, sai mahaifinsu kawai ne a raye.na (sanya sunan matar tasi u hauwa kulu to na canja na sanya sadiya ina ftn mai karatu ya fahimta).

Cigaba da Labari

inna sarai tace"to idan ba sadiyar ce ba lpy ba,to ko kaine ba lpy babangida"
tasi,u yayi shiru sai kuma yace"wlh inna nima bansan me yake damuna ba, kawai dai inajin jikina ba dadi" inna sarai tace"toh allah sawaqe,amma banajin dadin ganinka a haka" "lah ba komai fa inna" cewar tasi,u.

"kona zuba maka tuwon burabusko,gashinan har daman shanu"inna ta tambayeshi.yace "kai a koshe nake yanzu inna" inna sarai tace "to ai shikenan,nima salamatu ta aiko mini dashi" shi dai tasi,u baiyi magana ba sai ta sake cewa" to ko sadiya zaka kaiwa ko zataci ita"tace "gaskia inna ba lallai taci ba,saboda fitowar nan tawa na siyo mata dambu na kai mata.kuma kinsan ita ba gwanar cin tuwon burabusko bace, sai dae ki ajje min da safe nazo inci dumame"

Inna sarai tace "kaji ja,iri dumaman matar taka fa="shima dariya yayi yace "sai ta cinye kayanta"yana mai tashi ya dau wayarsa akan tabarma,yace bari inje inyi sallah naga lokaci yayi" tace "to babangida" har ya fara tafiya tace masa" in kayi sallar gida zaka wuce"yace eh gida zan wuce"(yanzu ba anan gidan inna sarai suke da zama ba,a gidan abokinsa hashimu suke tare da hashim).Story & writing by

MOM MASHKUR

page 9_10

"idan naje gida zamu fita kallon shadi (wani wasa ne da fulani keyi da sanduna kamar fada ko ince gasa ce) nida hashimu" inna sarai tace" shadi kuma babangida a ina za,ayi shadi yau"yace a rugar baduku "tace to Allah kiyaye amma kar kuyi dare dan allah" " yace insha allahu inna"

bayan yaje gida, ya tadda sadiya har ta kwanta,yace "sadiyayye har an kwanta" tace wlh kasan sanyi wajen itama abokiyar hirar tawa ta shiga daki "(aisha matar hashimu)shima dazu ya dawo yana tambayarka"yace " yace ai gani na dawo daman shadi zamuje kallo" ku ko sanyin nan bakwaji"duk cikin fulatanci suke maganar nice ke fassarawa >* "ina kika sakamin rigar sanyina" yace yana mai dubawa cikin lokar kayanshi. "tana kan igiya dana wanketa dazu, dana kwaso kayan wankin naji bata karasa bushewa ba"yace toh nagode matar aljanna, Allah dai ya saukeki lafiya inga abinda za,a haifa min"ummmm ta fada tana rufe fuskarta da tafukan hannayenta. alamar kunya shi kuma yake mata dariya.ya fita ya dauko rigar sanyin yasa,ya dauki takalmin roba sau ciki ya sanya, ya dauki sandarsa ya fito kofar daki.

Sadiya ta yunkura ta mike faker,saboda tsufa da cikin nata yayi ta biyo bayan tasi,u ta tsaya daga bayanshi, tana kallon bayanshi.kamar ance juya daman a jikinsa yaji kamar ana kallonsa,"ko kema zaki kallon shadin sadiyaye"ya fada yana dariya itama dariyar tayi " yoni yanzu ina zan iya zuwa Banda gidan inna" ta fada tana mai jingina da bango "baka ganin yanda nake "ta kuma fada tana kallon jikinta zuwa cikinta "sai in goyaki" ya fada kamar mai rada "kai malam in zaka ka taho mu tafi kar a fara muna hanya"sukaji muryar hashimu yana magana "da ita zan tafi" cewar tasi,u "to na tafi sai kun karaso, dan nasan nan da shekarama bakwa karasa ba"hashimu ya fada da zolaya yana kama hanyar fita daga gidan."zan kamaka" tasi,u ya fada cikin wasa.
"Sai kun dawo,a dawo lafiya" ta fada kamar batason yin maganar "amin sadiyayye"yace yana tafiya har zai fita daga gidan sai ya juyo aikwa ya ganta tsaye, yadda ya barta sai ya daga mata hannu,alamar bye bye=K.itama ta daga masa,ya juya ya fita daga gidan yanajin jikinsa ba dadi.

Can yaga hashimu yana tsaye m,yana jiransa ya tsayar da sandarsa ya dafeta da tafin hannu yana zuwa yace masa "toh muje mana"hashimu beyi magana ba ya bishi suka fara tafiya.maimakon subi hanya sai hashimu yaga tasi,u ya kama hanyar gidan innarsa,wato inna sarai "kai wa ina muka dosa ne" hashimu ya tambayeshi "inna zanwa sallama"ya fada ba tare daya kalli koda inda hashimun yake ba "jeka ka dawo ina jiranka" ya fada yana mai zama akan tayar kofar gidan.be masa magana ba,ya shige cikin gidan.

"Salamu alaikum" "wa alaikumus salam"inna ta amsa sallamar daga cikin dakinta "babangida"cewar inna tana me tashi daga gadon karfe "kai amma dakin nan naki inna akwai dumi" "gaskia akwai dumi babangida ai saboda wutar nan da nake kawowa daki" "kamar in fasa zuwa wurin shadin nan in zauna muyi hira"inna dariya tayi kawai tace"babangida kenan " "ga matar ka nan da tsohon ciki, in har firar ce kaje kuyi da ita mana yar amana"inna ai wannan amanar taki ce"tayi dariya tace "amma ka fini karfin rikon"murmushi yayi kawai.sai kuma yace "inna ko bana raye ai kece zaki kula da sadiya" "me ya kawo maganar mutuwa" duk da Allah ne yasan gawar fari dan nan.muma zaman jiranta muke=" sai yace "allah jikan baffana ya hadamu a gdn ajannah"amin"inna tace daker saboda ya tada mata mikin mutuwar mijinta.

"to innata sai mun dawo " "adawo lpy ta fada tana kallonsa" Har ya fita daga dakin ya dawo "zan dawo da safe ki ajjemin burabuskon nan.


Story & writing by


MOM MASHKUR


Page 11_12


MUNA JAJANTAWA KATSINAWA ABINDA YA FARU A JAHAR SU,WATO JAHAR KATSINA.UBANGIJI YA KUBUTO DASU YA ALLAH KADA KA BASU IKON KASHE SU,KO CUTAR DASU.=O=O=O


ina mika dinbin godiya ga QUEEN MEEMI BASHIR marubuciyar RAI DA SO,LABARIN HUSNA,RAHEENA.da dai sauran littattafanta ngd sosai da gudunmuwarki gareni, Allah kara daukaki ya daukakaki ya raya Zuri,a=OInna sarai tace "Toh Allah kaimu goben da abin aro" yace "ameen" ya fita daga gidan da sauri dan tunowa da yayi da hashimu na jiransa,a
kofar gida.
Aikwa yana fitowa ya fara fada "malam kasan dadewa zakayi ka barni ina jira,da nasan zaka jima dana yi tafiyata" tasi,u yace "yi hakuri abokina" hashimu dae tafiya ya farayi ba tare da ya kara mishi magana ba.sai ya kara cewa " wai kodae me machine zamu samu ya kaimu tunda bamu fito da wuri ba" sai a sannan hashimu yayi dariya yace "yawwa ko kaifa na sadiya"

sun shawo kwana kenan sukaga me machine suka tsayar ya musu goyon biyu,suka kama hanya suna tafiya suna haduwa da mutane,wasu a kafa wasu a machine.sun isa suka tadda an fara wasan,nan sukayi kallo har aka gama.bayan an tashi suka kamo hanya a kafa dake basu kadai bane akwai yan rugarsu, akwai yan wata rugar dake kusa da tasu suna cikin tafiya a daji sai ake tada zancen yadda shadin ya kasance aikwa sai aka fara musu,wasu suce "ga wanda yayi nasara "wasu suce " anyi galaba akan wane"duk musun nan da ake tasi,u beyi magana ba da hashimu akeyi.

Abu kamar wasa sai ya zama fada,aka fara cacar baki sosai,wasu daga ciki suna rabawa tasi,u yana janye hashimu amma hashimu yana komawa har takai sun fara doke doke da sanduna (kunsan bafulatani baya rabuwa da sanda) lol tsakanin hashimu da wasu su biyu daga cikin ayarin da suka taho dasu.tun ana rabiya har tasi,u yaga sun rufarwa hashimu,su biyu shi daya.sai tasi,u ya shiga fadan,shigarshi da wuya dayan ya daga sandar kafin tasi,u ya kare dukan da sandarsa ,ya sakar masa duka a tsakiyar kansa da karfi,nan take jiri ya daukeshi ya fadi a wurin


Story & writing by

MOM MASHKUR


Page 13_14


A nan take hashimu yayi kanshi ,yana kiran sunan shi,su kuma wanda ake fadan dasu suka fara tafiya.ko a jikinsu Wanda ya kwala masa sandar ne ke cewa " da kasan kai ragone baka da karfi kake tarewa wani fada" suka tafi abinsu,sai sauran mutanen da suka tsaya suka kewaye tasi,u suna masa sannu.

shi kuma tasi,u murmushi yayi yana kokarin tashi zaune,sai hashimu ya kama hannunsa ya taimaka masa ya tashi zaune."hashimu inason insha ruwa" tasi u ya fada sai wani cikin mutanen nan ya miko ruwa a cikin jarka,wanda ke rataye da tsumma a wuyanshi.

Aikwa yasha ruwan nan sosai,bayan ya gama sha ya mika musu jarkar,aikuwa nan take ya fara gumi sosai gumi yake zubowa daga jikinsa " ya kamata mu tafi gida " inji tasi,u " ka bari ka dan huta " cewar hashimu " A ah mu tafi kawai "tasi,u ya fada yana kokarin tashi tsaye,aikwa jiri yake dibansa.

sai daya cikin mutanan da suka tsaya yace " kunji karan machine yana tahowa ku bari, ya karaso sai ya rage masa hanya "hashimu yace to idan da mutum a bayanfa " sai tasi,u yace " kawai kazo mu tafi "ya fara tafiya taku daya biyu ana ukun sai ya jiri ya daukeshi ya tafi zai fadi,hashimu yayi saurin tareshi shida daya cikin mutanen nan.dai dai nan machine din nan ya karaso,mutum biyu. ne aka mai tukawa da kuma wani a bayanshi .suna zuwa suka tsaya ganin mutane a wurin da kuma hasken fitulu,sai direban yace" lpy dai ko "sai yaga mutum a zaune ya jingina da wani a kusa dashi.anan wani ke labarta musuw abinda ya faru sai na bayan machine dn ya sauka yace " ka hau ya kaika gida bazaka iya tafiya ba ni sai in tafi a kasa "sai direban yace "ya yau sai dan uwan nasa ya hau bayanshi in kaisu " suka hau dan tasi,u sai da hashimu ya tallafeshi sannan ya iya hawa machine din.

Sun fara tafiya me machine din yace " wace ruga zan kai ku " "rugar marayo " hashimu yace yana mai sauke ajiyar zuciya. " "kai amma basu kyauta ba gskia " me machine din ya fada yana me jajantawa "wlh ni bansan...


Read / Download RAYUWAR MARYAMU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album