Join Our WhatsApp Group

LAUNIN FATA Complete Hausa Novel Document by LAUNIN FATA


LAUNIN FATA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 52946



LAUNIN FATA

Reading Time: 4 Hours

Added On: 07, Sep 2023

Author: Rabi'atu Abubakar Nasidi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 267.48 kb

File Type: txt

Views: 684+

Download: 410+

Last download: 19 hours ago

Description/Story: LAUNIN FATA
Littafi na daya 1
Rabi'atu Abubakar Nasidi
Ebook creator:- Shuraih Usman
@http://fb.com/hausaebooks


Showing posts filed under Launin Fata
Launin Fata 1-01
Posted by ANaM Dorayi on 10:04 AM, 03-Oct-15
Tare da Alkalim
Rabi'at Abubakar Nasidi
Fatan zaku karance da Dan
Uwaku ANaM Dorayi
Falon ya yi tsit gaba daya iyalan gidan na ciki
kowanne kansa a kasa suna sauraron abinda zai
ci gaba da biyo bayan bambamin da dattijo sir
Abdulkareem baba ke zazzagawa diyarsa
Rabi'atul Badawiyya wadda ke durkushe a
gabansa rungume da yarinyar goye da bata
wuce watanni goma ba a duniya. Ya ci gaba da
fadin na taraku ne a nan don ku zama shaida
kamar yadda na taraku a baya kuka zama
shaida a kan abinda na gayawa Rabi ko ba ayi
haka ba? Sai da ya maimaita tambayar babban
cikinsu Rufa'i ya ce an yi haka Abba, duk da
haka muna baka hakuri..... Ya daka mai tsawa
tunda ka tabbatar mini an yi haka bani bukatar
a bani wani hakuri dole a yi abinda na ce. Kar bi
wannan bakar 'yar da ta zo mana da ita ta
rakaka har inda ta yi auran ta mayar musu da
'yarsu. In ba haka ba wannan bata zama min
gida. Ya juya har ya kai bakin kofa ya dawo ya
ce kar in dawo in samu yar nan a gidan nan ran
kowa zai iya baci idan ba a yi abin da na ce ba
a kiyaye. Yana fita Rabi ta dora hannu aka ta
fashe da kuka ta ce ni na shiga uku, yaushe
zanji dadi ne a duniya. Yarinya yar watanni
goma za a kai gidan daba a kaunata ni kaina
ake ba? Gidan da wahalarsa ta sa na fito ba dan
bana son mijina ba. Wacce irin rayuwa za ta yi a
gidan wannan yar. Ko shakka babu ba zan bada
yata ba a kai ta gara in hakura da zaman gidan
nan. Mahaifiyarta ta taso cikin tausayawa ta ce
Rabi rayuwa fa Allah ce duk wanda Allah ya
nufa zai rayu babu wanda ya isa ya hanashi
rayuwa. Ke ko duk duniyar nan zata hadu a kan
bata son rayuwar wani idan Allah ya nufa
rayayye ne zai rayu. Ci gaba da kafiya ga
mahaifinki abu ne da zai ci gaba da kawo illa ga
rayuwarki ba zai bari ki samu nutsuwa da
walwala ba. Idan kika yi hakuri Allah ya ji kanta
ya kaita hannu na gari ki tuna rayuwarki ba
itace rayuwar wannan yarinya ba, idan kin dage
sai kin rayu da ita sai Allah ya karbi rayuwar taki
ta kuma ta na raye tunda rayuwar ta Allah ce
rai da yake jikin mutum kayan aro ne, duk
wanda wa'adi ya cika mai shi zai karbi abinsa
ne kiyi yaya.Rabi ta kalli diyar ta nono na
bakinta, baiwar Allah bata san abin da ake yi ba
tana barci ta dagata ta rungume kam kam tana
kukan da ya baiwa kowa tausayi ta ce nabila zan
bada ke ba dan raina ya so ba sai dan babu
yanda zanyi ina fatan Allah ya kaiki hannu
nagari wanda zai tausaya miki dangin babanki
basa kaunata na san kema ba zasu kaunaceki
ba amma na san rayuwa ta Allah ce.wannan
jarrabawa ce wata rana lbr zata zama, domin
babu wani abu da ya taba dawwama dadi ko
wahala.
A hankali ta maida ita cikin zanin goyonta ta
mikawa yayanta Rufa'i ya karba ya rungumeta a
jikinsa a sanyaye.
Ya ce ki yi hakuri Rabi dole ne komai girman da
uwa bata son rabuwa ballantana yarjaririya
kamar wannan.
Allah yana sane da halin da kike ciki shi ne mai
magani zai miki magani kin sani babu yadda za
mu yi da maganar Abba in banda haka ba mai
rabaki da yarki a yanzu.
Ta zaro yan kayan nabila daga cikin nata ta kulle
a leda ta dauko wata yar sarka ta azurfa siririya
ta rataya mata a wuya ta mike ta shigo daki ta
kwanta.
A wannan lokaci fatanta mutuwa kawai ta zo,
nono na zuba hawaye na zuba dan tsanani sai
ta kama karanta adu'ar.
Allahumma la sahla illa ma ja'altahu salha
wa'anta taj alul hazna iza shi'ata sahla.
A hankali sai barci ya dauketa zuciyarta dauke
da tunanin baya
ASALIN ALHAJI ABDULKAREEN BABA LABARAN
Dan kasar yamen ne, ya zo Nigeria dalilin
kasuwanci, tun yana zuwa ya koma har ya dawo
da iyalansa gaba daya ya gina gidan shi a kano
suke zaune a wanan lokaci yayansu uku.
Hajiya maryam itace matar tasa muhammad
Rufa'i shine na farko sai nafisa sai muhammad
narardin, wadanda ta hafa a can na nan wadda
ta fara haifa itace Asiya sai muhammad Bashir
sai Rabi sannan fatima zahra sai idris dan auta
da suke cewa khalifa.
Duk inda mace mai saukin kai da hakuri ta kai
hajiya maryam ta kai, ko kusa bata dauki duniya
da zafi ba, tana tafiyar da rayuwarta cikin sauki,
yayin da mijinta Alhaji Abdulkareem yake
mafadacin gaske, babu hakuri a harkarsa, duk
wanda yake tare da shi ya san wannan.
Tun daga kan makota da abokan huldarsa a
kasuwa ballantana iyalinsa.
Ya shigo Nigeria da kafar dama bai jima ba ya
shiga sahun masu kudin da ake fadarsu a duk
fadin jihar kano.
Alhaji abdul mutum, ko abokan harkarsa a kasu
sai larabawa yan uwansa.
Saboda yadda ya tsani bakar fata ko mi son da
yake wa abu in har a gun bakin mutum zai saya
to ya hakura. Zirga zirgarsa tsakanin Ngr da
kashashen lrbw irin su Sudan, saudi arabiya,
egypt da malaysia da can kasarsa yemen da
sauransu.
Duk karshen sati ya kan tara iyalinsa kaf a gana
hirar tuna baya a yi raha ayi addu'o'i ga
wadanda suka mutu a ci a sha, kafin a tashi
gargadin da yake musu shi ne baya son hulda
da talaka.
Baya son hulda da bakin mutun idan sun
kaucewa wanan za su zauna lafiya da shi. Idan
ba haka ba zasu gamu da hushinsa wanan
huduba bata yiwa hajiya maryam dadi tana
ganin kuskure ne babba yake dorasu a kai.
Talaka da bakin mutum duk Allah ne ya halicce
su bata isa tayi mai musu ba saboda masifarsa
gaban yayanta sai ya iya rufe ido ya ci mata
mutunci ba damuwarsa bane.
Dan haka duk lokacin da ya gama nashi
hudubar ya tashi in gari ya waye zata tarasu in
bai nan ta ce da su Yanda nake matsayin
mahaifiyarku a gunku nake da hakki kuyi mun
biyaya akan duk wata hanya da nake son kubi
matukar ba ta kaucewa hanyar Allah ba haka
mahaifinku yana da hakkin kuyi mai biyayya. Sai
dai bana jin dadin muguwar da bi'ar da yake
doraku a kai. Ko wannenku a anan yasan Allah
ne ya halacci mai kudi ya halacci farin mutum
ya halacci baki, duk mai hankali da tunani ba
zaiki wani dan bai da dukiya ba, ba zaiki wani
don bai da farar fata ba. Watarana rufa'i ya
kada baki ya ce da ita ummi idan bamu bishi ba
yaya zamuyi? Sanin kankine gaba dayan mu
karkashin sa muke da zarar mun kaucewa
abinda yake so sai ya wulakantamu ya kore mu.
Itama Rabi ta sami bakin magana ta ce ummi
wlh nima raina ba karamin baci yake yi ba in
naji abba yana fadar haka sai in dinga ganin
kamar ba magana bace irin ta dattijo mai ilimi
wanda yasan abun da yake yi ba. Nafisa ta ce
to wai me akeyi da talauci, annabawa ma da
sukafi kowa daraja agun Allah naiman tsari
sukeyi da shi balantana mu? Ni banga laifin
baba ba dan ya ce mugujewa talaka. Ai nufinsa
mu diyansa ne mata kada mu dauko mai talaka.
Haka ku maza kada ku dauko mai aure gidan
talakawa, yanda yake mai kudi yafison harka da
daidai shi, kwarya tabi kwarya. Idris ya tabe
baki yace nima haka dai naganiNura ya ce to
ma in banda abinsu gida kamar namu yadda
abbanmu ke kashe mana kudi gun cin abinci
mai kyau mu sha mai kyau suturu da kayan ado
masu kyau, amma sai mu lalace a auren talaka?
Haba in anyi haka ai anci baya, ina amfanin
shuka idan ba a yi girba ba?
Abba ya sha gaya mana cewa yana kashe
kudinsa a kanmu ne dan mu zame masa riba,
idan mun tashi aure mu na da tagomashin da
zamuyi tsadar da zamu auro mata masu tsada a
gida mai tsada.
Ku kuma mata duk wanda zai zo auranku ko
kallon fatarku yayi ya san an kashe muku kudi
dole sai yana da kudin da zai iya daukarku idan
wanan bai samu ba ina amfanin kudin da yake
narkarwa a kan mu?
Rabi a ta ce kai ni a ganina wannan ba tunani
ne mai kyau ba yaya nura, ni dai a guna talaka
da mai kudi duk daya ne, don a Alkur'ani mai
girma Allah ya ce babu wanda yafi wani a
cikinku a gun Allah sai wanda ya fi tsoron Allah.
Duba da wanan ayar za ku ga cewa fifiko gun
Allah shi ne abin nema a rayuwar mutum ba zai
samu wannan fifikon ba kuwa sai ya kasance
mai tsoron Allah.
Fifikon jinsi ko yare ko dukiya ba sa amfanarwa
mutum komai a ranar lahira matukar bai bi
Allah ba. Nafisa ta zabga mata harara ta ce to
sarkin wa'azi sai ki dauko duro ki hau ki yi ta yi.
Muhamma Bashir ya ce kyaleta ta fadi ra'ayinta
kowa ba ra'ayinsa yake fada ba.
Fatima ta ce ni dai ba ruwana duk wanda Allah
ya bani ina so in mai kudin in talakan mi dai
nafi son in yi auran soyayya ba auran kudi ba.
Babu wani kudi da zai tsolewa gidan nan ido mu
da abbanmu ke buf mana dakin kudi mu debi
yadda muke so mu yi abin da muke so.
To wane kudi zamu je kwa dayi a gidan wasu?
Rufa'i ya ce daga randa abba ya ji kina cewa in
mai kudi in talaka kin daina cin kudinsa dan ba
a banza yake buf muku dakin kudinsa ba yana
son ya fanshe ne a gaba. Ummi duk ta gama
sauraransu ta gyara zama tayi murmushi ta ce a
takaice dai nafisa da nura da Rufa'i ra'ayinku
daya in har zan gaya muku kuji ku sauka daga
ra'ayin mahaifinku dan ku zauna lafiya.
Gidan kyawawa ake kiran gidan tun daga titi ka
tambaya inkiyarsu kenan, kowanne na takama
da kyau na a gayawa duniyar farare ne kai kai
kamar a taba jikinsu jini ya fito, duk wanda ka
gani sai ka zata yafi duk yan gidan kyau sai kaga
wani sai kaga yafi shi kyau.
Babu abin da ya damu umminsu da cin buri a
kansu, rigimar tana gun abbansu wanda ya dau
burin duniya ya dora musu kamar shi ne ya
fara haihuwar yaya masu kyau.
Mutanan unguwarsu kaf sun san dabi'arsa ta
girman kai da daukan dan adam ba a bakin
komai ba shi yasa basa ma shiga harkarsa
gaisuwa ma sai sama sama.
Duk abinda aka gaya mai ba zasu je baba zai
bar matarsa ta je ba haka diyansa .
Hajiya maryam na son hulda da mutaner yaki
yarda duk randa yaga wani bakuwar fuska a
gidannsa sai ya kare mata cin fuska tas a gaban
bakon dole ta hakura c mai shiga gidanta ita c
ta zuwa gidan kowa a matkotan sai gidajan
abokanan sa masu kudi dai dai da su.
Abin yana mata ciwo sai dai da yake babu
yadda ta iya, fadan da yafi karfinka sai ka mai
da shi wasa dan ka zauna lafiya.
Rufa'i na da sassaucin ra'ayi akan ra'ayin
mahaifinsa a boye yana hulda da ckaken
talakawa a makaranta har yanata bakake yana
yi saboda ra'ayinsa na kashin kansa yafi
sha'awar mace chaculate colour ba fara kal ba.
Nura shi ne mai ra'ayin rikau irin na mahaifinsu
shi yasa suka fi daidaitawa yafi sakar masa kudi
nura dan duniya ne dan fafa na gani kasheni a
dinka sutura a hau mota ana zaga gari idonsa
ya bude sosai da bariki duk wannan bai damu
mahaifinsu ba tunda dai bai jajibo mai talaka da
bakin fata ba an gama haka nafisa yar lelen
abbansu ce tafi kowa iya jin kai da yanga a
gidan dukansu suna da kyaun ta ya hadu da
gayu idan ta dau ado ta shiga mota tana tukawa
kai kace tauraruwa zahra cikin taurari haka take
zama cikin sauran mata karya ne nafisa ta wuce
guri ba ta ja hankalin mutane an maida hankali
ga kallonta ba.
Fatima ke take mata baya a nan inda halinsu ya
bambanta shi ne fatima bata tsani talaka da
bakar fata ba jin kansu dayanga ne iri
daya.Masu halayyar mahaifiyarsu a gidan Rabi
da Asiya suna adawa karara da Nafisa Bashir da
irdis ra'ayin ba ruwanmu ne .. ..
Rufaida da nura sun gama karatun su ne a
malaisia sna aiki a nan kano duk karkashin
kamfanin abbansu a baya musu rowar kudi duk
abinda iyalan sa ke so an gama, matsalarsa
daya fada shima sai ka saba masa.
Kai tsaye a iya cewa basu da matsala a rayuwa
ta fannin kudi dai kam.
Sai a wannaan shekarar akayi auran Rufa'i da
irin diyar da abba yake so, diyar kakadan a
karasu ta yemen a nan Nigeria, gata farar fata
ga uwa uba dukiya. Sunanta zainab suna mugun
sö juna ita da rufa'i haka iyayansu na son hajiya
maryam ce kadai yarinyar bata kwanta mata a
rai sosai ba.
Saboda lokacin da aka fara maganar auran sai
rufa'i ya dauko ya kawota dan ta gaida
iyayensa.
Hajiya maryam na zaune a kan kujera a falonta
suka shigo suna manne da hannun juna shi da
ita har shi rufa'in na dan jajjanyewa saboda
kunyar umminsa ita kuwa zainab ko a jikinta sai
dada mannewa take a jikinsa tana shagwaba.
Rufa'i ya zauna kan kujerar zaman mutum 2 sai
ta zauna a jikinsa ta lankwashe a kafadarsa a
haka ta gaida ummi.
Haushi ya kama ummi ta mike ta bar musu
falon, har zainab ta nunawa Rufa'i rashin jin
dadinta da haka ya ce kar ta damu kunya ce da
umminsa saboda shi dan fari ne.
Suka bar maganar a haka bayan ya kai zainab
gida ya dawo ummi ta dube shi ta ce wannan
yarinyar itace irin yayan da abcnku ko yaushe
yake burin ku auro saboda farar fata ce
kyakyawa, kana iyayanta na da kudi kuma
sanannu mutane ne bai damu da cewa tana da
tarbiyya ko babu ba. Yaya tarbiyar gidansu da
iyayanta suke?
Shi fari da dukiya kadai ya dame shi wannan
kuskure ne da ba za ka fahimce shi ba sai nan
gaba.
Rufa'i bai faìmci abinda ummi take son ya
fahimta ba saboda son da yakewa zainab, dan
haka ya share batun ummi ya ci gaba da
harkokin gabansa.Lokacin da aka yi daurin aure
da biki abbansu ya gina mai gida na kece raini a
tsadadiyar unguwar nan Nasarawa GRA da sai
masu kudin gaske ke iya zama a cikinta. Ya ce
kuma kada a kawo zainab da ko allura sun
gama shirya gidansu.
Amma ina sai mahaifin zainb ya ce tuni ya gama
shiryawa yarsa gida da komai ango ne zai biyota
gidanta dake sultan road duk a kano.
Su yi hakuri haka tsarinsu yake gida ne na bada
labarin kyansa da tsaruwarsa ba zai taba
yiwuwa ba an kashe kudi iyaka.
Duk saboda buri da son duniya wannan bai
damu Abba da rufa'i ba suka bi a haka, ga
gidansu ga komi ya bi zainab gidanta bayan an
gama biki an kaita.
Wannan ma ya bata ran ummi amma ba ta ce
komai ba ta sa musu ido.
Matsalar zainab ta farko da rufa'i ya fara
fuskanta bata iya komi ba sai soyayya.
Yar gata ce yar shagwaba da ma tun ran da za
a kawota har gida ubanta ya kirashi ya ce to fa
shi yarsa ba ta saba da wahala ba, kuma
tattalin farinciki ta ake a gidansu dole ya dora a
inda suka tsaya. Ita kadai ce diyarsu mace suna
sonta fiye da zatonsu.
Sun bashi i ta ne don ta nuna shi take so fiye
da kowane namiji su kuma ra'ayinta shi suke bi.
Basu son diyarsu ta shiga wata matsala dole ne
ya kiyaye da wannan tun daga wannan lokaci
jikin rufa'i yayi sanyi ya jiyo kamshin gaskiya a
maganganun mahaifiyarsa da tace aure a gidan
tarbiyya ya fi aure a gidan dukiya tarbiyya ita ce
zata dore dukiya fararriya ce kararriya.
Bai gaya mata yadda suka yi da iyayen zainb sai
abbansu ya gaya mawa, shi abban ya rufe shi
da fada ya ce ni bani son irin wannan korafin
menene a ciki don sun ce...


Read / Download LAUNIN FATA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album