Join Our WhatsApp Group

MAFARKIN ABDOUL Complete Hausa Novel Document by MAFARKIN ABDOUL


MAFARKIN ABDOUL

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 17892



MAFARKIN ABDOUL

Reading Time: 1 Hours

Added On: 11, Nov 2023

Author: Safiyya Ummu Abdul ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 96.17 kb

File Type: txt

Views: 441+

Download: 116+

Last download: 19 hours ago

Description/Story: MAFARKIN ABDOUL
Na safiyya ummu abdoul
Ebook creator:- Shuraih Usman 99%
Post at:- www.shuraih.waphall.com

You can download more hausa novels ebook at www.shuraih.waphall.com

MAFARKIN ABDOUL
Alkalamin Safiyyah Ummu Abdoul
WANNAN NA KU NE
Labarin nan kirkirrarre ne don kaunarku
gare ni, na sadaukar da labarinnan ga
Ɗaukacin masoyana da ke 'Kasar Nijar.
Ubangiji Allah ya Haskaka rayuwarku ya
barmu tare
2010
Zaune take gaban fannin kimiyya (Faculté
des Sciences) ta jami'ar Abdoul moumouni
(Université Abdoul Moumouni Dioffo) da ke
Niamey a jamhoriyar Nijar. Sun fito
lectures kenan kasancewarsa ɗaliba yar aji
uku a fannin tsirrai (plant biology),
Yarinya ce 'yar kimanin shekaru ashirin a
duniya, tana da matsakaici tsawo, Albarkan
mazaunen da ke gareta da kumatunta yasa
akan mata kallon mai jiki kasancewar ta ma'
aboki yar sa hijab. Kalarta mai tsada ne,
baka ce ba wuluk ba ma'abociyar fararen
idanu kalar madara.
Wasu na mata kallon mai girman kai yayin
da dayawa kan so ta saboda hakurin ta da
yalwataccen fara'an da ake samu a fuskanta.
A zahirance kallon wayarta takeyi fuskarta
ba yabo ba fallasa, amma tunaninta ya tafi
chan wani duniyar. Ko a aji yau ba zata ce
ga abinda akayi musu ba.
Kiran da ya shigo wayarta yasa ta sakin
ajiyar zuciyar da ya sa kawarta da ke zaune
gefenta kallonta.
"Sweetyna kana lafiya, duk hankalina ya
gaza kwanciya, ina ka shige" Ta faɗi a
marairaice kamar zatayi kuka.
"barci na tashi ya kike ya makaranta?"
"Alhamdulillah, ka ci abinci" Ta sake
tambaya cikin yanayin kula
"Bana jin cin abincin ne, ga de ni nan Haj
na min favorite ɗina" Ya faɗi yana dariya.
Itama dariyan tayi.
Haka suka cigaba da hira cike shaukin juna.
Har wajen mintuna ashirin sannan suka
rabu cike da kewan juna.
"Halima fisabillillahi bazakiyi ma kanki faɗa
ba, wallahi Hammad ba aurenki zeyi ba. Ki
natsu ki roki Allah ya baki nagari, kada so ya
rufe miki ido" faɗin kawarta da ke zaune a
gefenta.
"Faɗima wallahi muna son juna da
Hammad, kun kasa fahimtarmu ne, kuyi
mana fatan alkhairi kawai"
"ina guje miki halin mazan zamanin nan ne,
basu da alkawari musamman in son da
mace ke musu ya zarce misali, duk abin sa
kar ki yarda ayi gwajin takalmi da ke"
Faɗima ta ce cikin halin ko in kula.
"in ma gwajin riga zai yi ba komai bane mu
dai muna son junanmu kuma za muyi aure"
Ta faɗi a kufule duk ranta ya ɓaci. Fuuuu ta
tashi kamar mai shirin tashi sama.
***
Da kyar ta iya isa gidan baffanta da take
zama wanda ke bayan Homeland Hotel, da
ke
Off Ave du General de
Gaulle, a wahalance ta yi sallama, ta iske
matar baffanta haj Mas'uda a zaune tana
kallon tashar Sunna TV.
"Momma barka da gida" Ta faɗi tana mai
samun wajen zama a kusa da kafanta. Kallo
ɗaya tayi ma ta ta fahimci bata cikin
natsuwa.
"Halimatus sa'adiya taje makah da madina
ta sha miya mai daɗi har da kadangare
soyayye" Ta shiga rera mata tana tafi.
Dariya Halima ta farayi yayinda ranta ya
fara sanyi.
"faɗa min waya taɓa ki" Ta tambayeta tana
mai tsareta da idanu.
"Faɗima ce na rasa mai na tsare mata,
tsakani da Allah nake zaune da ita amma sai
ta yi ta min bakin ciki da hassada" Ta faɗa
ido cike da kwalla, zuciyar ta na mai jin an
ci amanar kauna.
"tohhhh fa, me ta yi miki, kwata kwata ba
tayi kalan mai wannan halin ba" Ta amsa
mata fuska cike da alhini.
"Momma a 'yan kwanakin nan sai tayi ta ce
min in rabu da Hammad ba aure na zaiyi
ba, ki duba fa ko haushin yafi mijinta kyau
da kuɗi take yi ko mai yasa ni ban sani ba"
Ta karasa tana kukan da yafi jini ciwo don a
duniya bata da kawar da take kauna sama
da Faɗima duk da kasancewarta kanwa a
wajen kishiyar uwarta.
"Na rasa me ke damun mutanen zamanin
nan. Sam bama son gyara, da ga an nuna
mana kuskurenmu maimakon mu gyara sai
mu ce ana mana bakin ciki ko hassada.
Mai sonka ke gyara maka, nasan son da
Faɗima ke miki ba za ta bari ki cutu ba.
Hammad dai iyayen ki ba sonsa suke ba,
asali ma cewa su ka yi ki rabu da shi, ina
mai shawartanki da ki roki zaɓi Allah in
Hammad ne alkhairi Allah ya tabbatar in ko
ba shi bane Allah ya kawo wanda ya fi shi a
komai"
"Momma ko ba Alkhairi bane Allah ya sa
mu mallaki juna, ina sonsa da yawa
Momma" Ta katse ta gudun yan aameen su
amsa ma addu'ar ta,.
"Halima ko dai Hammad ya sanki a ɗiya
mace ne, in ba haka ba wannan irin nacin
son da kike masa ya zarce hankali, dama
mamanki ta faɗi na karyata gashi kina
neman gaskata maganarsu". Ba ta jira
amsarta ta ba barta zaune tana gunjin kuka.
Kiran sallar la'asar da akayi ne ya tashe ta
daga barcin wahalan da ya kwashe ta a
wajen. Tashi tayi ta sallace la'asar da azahar
ɗin da ake bin ta bashi.
Tare da Momma da babbar yar momma
Amina da suke kira Amna suka kammala
girkin dare. Suka shirya, karfe shida duk
suka haɗu gaba ɗaya suka ci abincin, don
ka'ida ne a gidan cin abincin dare karfe
shida don ya zazzage kafin ayi barci, sannan
abincin safe baya wuce karfe takwas ɗin
safe duk don samun ingantacciyar lafiya.
Bayan kammala sallah isha'i ta koma ɗaki
da nufin barci. Shafin Facebook ta shiga don
duba abubuwan da ke kai, har zata sauka sai
sakon gayyata ya shigo ta buɗe sai taga
"ABDOULLAH ABOUBAKAR (ABDOUL
ABOU)" Sai da ta duba shafinsa ganin bai
bada wasu bayanansa masu mahimmanci ba
iyaka dai taga shima ɗan Zindar ne. Har
zata goge sai ta tuna da tobashinta Abdoul
Abou sai tayi tunanin Shine. Tsaki ta ja kafin
ta amince. Haka ta cigaba da shige shigenta
tana hira da kawarta da suka haɗu a
Facebook ɗin Tiddar Azzoubir.
Da ta gama ta kalli agogo ganin goma saura
na dare ta sa ma ranta tabbas Hammad ya
gama kallon kwallo. Waya ta ɗauka ta kira
shi sai da ya kusan tsinkewa sannan ya ɗaga.
Yanayin yanda ya amsa mata yasa ta
tambayeshi ko ya fara barci ne
"ke dai bari hajiyata, wallahi na ɗanyi aron
hannu ne kinsan gajiya yake sawa" Ya faɗi
cikin halin ko in kula
Bakin ciki ya cikata amma haka nan ta
ɗaure ba tare da nuna ta damu ba tace
"sweetyna yaushe zaka daina zuwa rage
ruwan nan ne, lokaci yayi da ya kamata mu
san mai muke ciki"
"anya in munyi auren nan baza'a samu
matsala ba, kishin ki na neman kaiki ga
zargi na, gaskiya da sake toh" Ya katse ta a
fusace. Nan take ta fara bashi hakuri da
kalaman soyayya da tasan yafi so. Haka suka
shirya suka cigaba da soyayya har sha ɗaya
da rabi sannan sukayi sallama suna masu
begen junansu .

2 NAMIJI KO TSIYA

Juyi ta ke yi hannunta rungume da filo
Mafarki take amma na ido biyu (day
dreaming) ga ta da Hammad ɗin ta sunyi
aure. Auno su take irin soyayyar da zasu
kwasa, kamar an mintsile ta tashi tayi ta
lalubo kananan kayan da ta siya don kaiwa
gidan aurenta. Murmushi ta saki gani take
an ɗaura aurensu da Hammad an gama.
"Toh in ya cigaba da Aron hannu fa?"
wannan sashi na zuciyar mutum da ba'a
taɓa yaudara ya tunatar da ita, bata ɓata
lokaci ba tayi fatali dashi kana ta faɗin "ai
na san zai daina da munyi aure".
Kwanciya tayi don tayi barci amma ko gezau
barcin ya gagare ta, sai ma tunani da ke
neman kar da ita, bata bari ya hargitsa ta
ba ta dauki wayarta ta hau Facebook
"Assalamu Alaikum yan mata" Ta iske na
Abdoullah Aboubakar, ita sam ta manta
wani Abdoul.
Amsa sallamar tayi , ashe yana kusa nan
yayi ta janta da hira, tun tana sharewa har
ta fara bashi amsa.
***
TUSHEN SU
Alhaji mousa uomarou ɗan asalin garin
Zindar ne, duk da tarihi ya nuna fatauci ya
kawo kakanninsa Kasar Nijar daga Kano, har
auratayya da chakuɗeɗeniya ya sa sun zama
yan kasa.
Yara biyu Allah ya mallaka masa wato
Idrisa da Abbas. Gidansa sannan nan gida
ne da a unguwar yadakwandage kasancewar
yafi sauran rufin asiri. Yayi kokari wajen
ganin yaransa sun samu yalwataccen ilimin
zamani, haka ma na addini.
A rana ɗaya sukayi aure inda Idrissa ya
auri Mas'ouda balarabiyar Kasar Aljeriya
amma mazauna Kasar Nijar shi kuma
Abbass ya auri yar gwoggonsu khadija.
Wata goma sha ɗaya bayan aurensu
khadija ta haifi yar ta mace wacce aka sa
ma suna Halima. Mas'ouda kuma sai bayan
shekaru haɗu Allah ya buɗe mata kofar
haihuwa. Lokacin Idrissa ya sami aiki a
fannin kuɗi da tattalin arzikin yammaci
Afirka wato Union Économique et
Monétaire Ouest Africaine
(UEMOA). Don har sun koma garin Niamey
da zama.
Halima ta taso cikin gata da kula, sannan
ta sami ingantaccen ilimi tun daga na addini
har zuwa na zamani. Rashin haihuwar
mahaifiyarta tun bayan haihuwanta yasa
Abbass kara aure, inda ya auro Sauda.
Tun da ya auri Sauda kuma haihuwa ta
sake buɗe wa a gidan. Sai ya zama kamar
ana gasar haihuwa ne a gidan tsakanin
khadija da Sauda.
Bayan Halima ta kammala sakandarenta
a LYCÉE AMADU KURAN DAGA (LAKD) ta
samu gurbi karatu a université Abdoul
Moumouni Dioffo, dalilin haka ta koma
gidan baffanta Iddrissa.
A shekaran Halima ta haɗu da Hammad
wata rana ta dawo daga registration dai dai
kwanar da ya raba su da homeland hotel shi
kuma ya fito daga otel ɗin. Hammad
Touareg(Buzu) ne ɗan asalin Agadez ne.
Fari ne kyakkyawa kamar shi ya kera kansa.
Ba shi da hayaniya don magana wahala
take bashi
Yana da son kyale kyalen duniya amma
mace da kuɗi sune kan gaba. Bai sha wuya
wajen zulmiyar da Halima zuwa ga sonshi
ba amma bai taɓa yunkurin taɓa ta ba
yanda bai yi yunkurin zuwa neman aurenta
wajen iyayenta ba.
A dalilin haka iyayenta suka raba ta da shi
amma fir ta ki don a tunaninta bata fara
sonsa don ta daina ba haka kuma a shirye
take da ta jira shi duk lokacin da ya shirya
suyi auren.
Babu abinda ya fi faranta ran Halima kamar
ta zauna tana MAFARKIN ido biyu.
Zaune take da Hammad suna ciyar da
junansu abinci a baki, suna yi suna jifan
juna da kallo mai cike da kauna.
Yaransu suka shigo suna kwala mata kira
cike da murnan dawowasu....
Ire-iren mafarkan nan Halima keyi sai ta
ji duk duniya babu macen da ta kai ta
dacewa da samun masoyi. A haka har ta kai
aji uku ana saura mata shekara ɗaya ta
kammala karatunta hakan ya tada hankalin
iyayenta don sun so ta kasance a ɗakinta a
wannan shekaran kasancewar ta cika
shekaru ashirin a duniya. Nan dai Halima
ta kekashe ta ce ita bata da masoyi sai
Hammad....
WANNAN KENAN
***
Washegari kamar kullum ta Shirya ta isa
makaranta, faɗi ma bata ga wani fara'anta
ba, ba yabo ba fallasa suka kasance tare
har aka tashi. A hanyar ta na komawa gida
ta shiga Faba-faba (wata yar bus da ake
motar haya dashi a Nijar) nan ta iske wasu
yan mata biyu a ciki.
"Kin san Allah Faɗima, ko da tonton
oumar ya ce an tsaida ranar auren mu da
Hammad ban yarda ba, tsoro na kar in ya
ce ya fasa" faɗin ɗaya daga cikinsu. Wacce
da gani ta fi rawan kai.
"ke ma kinsan yana sonki kawai don ya
fiye ka'idoji ne amma kawai ki kiyaye shike
nan. Allahu ya nuna mana" faɗin wacce aka
kira da faɗima.
Hankalin Halima ya kasu kashi kashi sai take
ji kamar Hammad ɗin ta ne, wani zuciyar
na faɗi mata ai Hammad ba ɗaya bane a
duniya.
Bata san sanda bakinta ya fara furta
"kar dai a ce ke ce amaryan grand frère
(yaya namiji)". Nan duk suka juyo suna
kallonta. Murmushi ta sakar musu sai ta
ɗauko littafin da ahlin ɗinsu Hammad
sukayi wai barka da sallah ta ce
"ko ba wannan bane angon naki grande
soeur (yaya mace)" Nan ma fuskarta cike
yake da murmushi yayin da ranta ke rokon
Allah kar ya kasance Hammad ɗin ta.
"kinga irinta ko Sadiya, da rashin
mutunci mukayi da kin kwan ciki, yi hakuri
kanwarmu . Ya gida ya su mama"
"Lafiya lau, gashi har na zo in da zan
sauka, zan faɗa masa mun haɗu da pretty
damsel ɗinsa" Ta faɗi tana dariyan da yafi
kuka ciwo.
Tana sauka ta hau kabu-kabu wanda shi
ya karasa da ita gida. Jinta take kamar
mahaukaciya, haukan ma sabon shiga.
Ko da ta isa ɗaki ta shiga Direct, sai da ta
tuɓe ya rage daga ita sai breziya da siket
sannan ta kira shi a waya.
"Akan me zaki je kina min bincike
Halima, ko an ce miki sadiya bata san duk
yan gidanmu bane" Ya tare ta da shi kafin
ya amsa gaisuwanta.
"Ai ban san cewa gidanku ɗaya ba sai
yanzu. Yanzu Hammad sakayar da zaka
min ke nan" Ta faɗi a raunane, idanunta na
fitar da kwalla. Zuciyarta kamar ta fitar
dashi saboda azaba kunan da yake mata.
"ki fahimce ni Halima, ban taɓa miki
Alkawarin zan aure ki ba, ina sonki mais
(but) kin san hali na, hakan yasa kike zargi
na kuma kike bincike na, bafa muyi aure
ba kenan. Kuma kinga sadiya shekarunta
goma sha shida ne kawai, zan iya zama in
tsara ta yanda nake so" Ya karasa yana
dariya.
Halima da jikinta ke karkarwa burinta ta
tashi daga muguwar MAFARKIN da take tayi
kokarin faɗin
"Amma Hammad.... " bata kai aya ba ya
katse ta da ban hakuri.
" Don Allah Halima kiyi min rai s'il vous
plaît (please) kada wannan ya taɓa
soyayyar mu kinji Don Allah " bata karasa
jinsa ba tayi hurgi da wayar ta kara rushewa
da kuka wanda ya fi jini ciwo.
Hey sweetiesssss da fatan kunyi sallah lfy.
Keep voting and commenting plssss
Mafarin Mafarki
1.1K 67 5
by Ummu-abdoul
Tsabagen kukan da tayi ya haifar mata da
matsanancin ciwon kai. Tun da ta shige ɗaki
ba ta fito ba sai faɗi ma mommansu
zazzaɓi take yi.
Washe gari ma haka ta yini sukuku,
mamaki ya cika ta rashin ganin kiran
Hammad, zuciyar ta guda na ingiza ta kan
cewa ta kira taji ko lafiya yayin da ɓangaren
zuciyarta mafi gaskiya na faɗi mata ta kyale
shi.
Waya ta ɗauka ta kira Abdoul saboda
amincin da ke tsakanin su yasa basa
kyashin faɗi ma junansu sirrin rayuwarsu.
Saurarenta yayi cikin natsuwa da fahimta.
Sannan ya ce
"ki ɗaure ki fitar da shi a ranki tun a yau,
kar ki saurare shi, zafin da zaki ji kaɗan ne
akan sai gaba ki sami ɓacin ran da yafi
wannan. Ina office yanzu za muyi magana
in na koma gida" Ta gode masa kana ta ɗan
yunkura don cire damuwa a ranta.
Haj. Mas'ouda na ankare da duk wani
take takenta amma ta basar. Cikin lokaci
kankani ta zabge ta rame, fara'anta ya
zama ragagge ga yawan tunani. A lallaɓe ta
kammala jarabawan zangonnan ta tafi
Zindar.
Abdoul kaɗai yasan matsalarta hakan ya
sa shakuwa fiye da farkon haɗuwansu.
Bakin cikinsa ɗaya sanda suka haɗu tana
tare da Hammad da babu abinda zai hana
masa aurenta. Ga shi saura wata bakwai a
ɗaura aurensu da Agaysha.
Kaifin basiranta da hankalinta yasa yake
saka ta...


Read / Download MAFARKIN ABDOUL

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album