Join Our WhatsApp Group

BAKAR GUGUWA book 2 Complete Hausa Novel Document by BAKAR GUGUWA book 2


BAKAR GUGUWA book 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 15526



BAKAR GUGUWA book 2

Reading Time: 1 Hours

Added On: 17, Sep 2023

Author: Shehu Usman ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 83.05 kb

File Type: txt

Views: 719+

Download: 185+

Last download: 20 hours ago

Description/Story: An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__
BAKAR GUGUWA
littafi na biyu 2
Na Shehu Usman Muhd
typing by Shuraih Usman
post by Shuraih 99%
Part A
.
.
Kafin Matsafi Bahalu ya bar wajen Buniyatu ta
tasar masa da nufin karbe kurtun sihirinta daga
hannunsa, ta kai masa sura za ta fizge kurtun sihirin shi
Kuma ya sanya sandar tsafin dake hannunsa ya maketa.
Buniyatu ta yi karaji ta tafi ta bugu da jikin wata itaciya
dake tsakiyar lambun nan take ta zube kasa sumammiya,
Jini na zuba ta hanci da bakinta.
zuhairu ya fusata da ganin wannan al'amari ya zare
takobinsa cikin kabbara ya tasarma matsafi Bahalu da
nufin kai dauki gareshi ya ketashi gida biyu ya halaka,
shima Bahalu ya juyo gareshi a fusace, ya tasar wa
zuhairu cikin karaji da gunji mai tsananin karfi dake
tattare da aikin sihiri gaba daya dukkanin wajen ya yi
amsa kuwwa da amo mai hauhawa da ya gauraye ko ina,
suka hadu a tsakanin fusatuwar su suka kaiwa juna sara
da bugu da makaman da yake hannunsu, kaifin takobin
Zuhairu ya hadu da sandar sihiri dake hannun matsafi
Bahalu wani farin hayaki ya tashi sama tare da tartsatsin
wuta tamkar haduwar karfe da karfe. Zuhairu ya sake kai
masa sara a fusace kafin matsafi Bahalu ya kare kaifin
takobin ya sauka a jikinsa amma abin ka da shu'umin
matsafi sai Bahalu ya zama hayaki saran ya wuce ta
jikinsa ba tare da ya ji masa rauni ko wata illa ba, ya sake
bayyana a gabansa dasaran ya wuce
Zuhairu ya sake maida kaifin takobin a tsakiyar
kansa Bahalu ya kare saran da sandar sihirin dake
hannunsa, suka kaiwa juna sara rin ta neman makasar
abokin karawa kaifin takobin Zuhairu ya wuce ta gefen
an matsafi Bahalu da karti kadan ya rage ya sare kansa daga gangar jikinsa, suka yi tirjiya irin ta arangama
sannan suka sake zaburowa suka yi wata bahaguwar
haduwa irin ta zaratan sadaukai dake sanya halaka da
matukar tsoratarwa ga kananan jarumai masu raunin
zuciya. Makaman dake hannunsu suka hadu da karfi har
sai da dukkaninsu suka yi baya taga-taga kamar zasu fadi
sannan suka tirje suka tsaya.
Suka sake zaburowa suka kai dauki ga juna,
Zuhairu ya suri matsafi Bahalu ya cirashi sama da
dukkanin karfinsa ya makashi da kasa, ya bi shi da sara
cikin azama da zafin nama, kafin kaifin takobin ya sauka
a kansa Bahalu ya bace, takobin ta sari kasa, ya sake
bayyana a gefe Zuhairu ya sake yin kansa da sara cikin
fusatuwa ya rika kai masa saran cikin jarumta da kwarewa
irin ta sadaukantaka, shi kuma matsafi Bahalu ya rika
karewa da sandar sihirin dake hannunsa ko kuma ya goce,
wani lokacin ya kan tsage kashi biyu saran ya wuce, ta
jikinsa ko kuma ya bace ya zama iska.
Haka suka yi ta fafatawa da arangama a tsakaninsu
har sai da kaifin takobin Zuhairu ya dakushe haskenta ya
dusashe, saboda yawan kai sara da haduwar da take yi da
sandar sihirin da take hannun matsafi Bahalu.
Da Bahalu ya ga lamarin ya ta'azzara a gareshi
Zuhairu ya tsanan ta masa da kai sara yana shirin
halakashi, sai ya yi wani irin karaji da kururuwa mai ban
firgici dake tattare da aikin sihiri, wata bakar guguwa ta
turnuke a tsakaninsu, sannan ya nunashi da sandar sihirin
da take hannunsa yana ambaton wasu dalasunmai na aikin
sihiri, wata irin iska mai tsananin karfi ta yi sama da
Zuhairu ta makashi da kasa, Zuhairu ya yunkura ya tashi
matsafi Bahalu ya sake nunashi da sandar sihirin iska ta
sake yin sama dashi ta makashi da jikin bishiyar dake tsakiyar lambun ya bugu da buguwa mai tsanani har
takobin da take hannunsa ta subuce ta fadi kasa.
Haka matsafi Bahalu ya ci gaba da nuna Zuhairu da
sandar sihirinsa iska mai karti tana wujijjigashi ta maka
da jikin itatuwan da ke cikin lambun har sai da Zuhairu
ya yi matukar jigata, ya fadi kasa jini na zuba ta hanci da
bakinsa, matsafi Bahalu ya dubeshi ya bushe da dariya
sannan ya ce da shi.
"Ahir din ka, da yin jayayya da hamshakin matsafi
da ya buwaya cikin lamarinsa kamata, Bahalu na ke bin
Kauwas cikamakin ma'abota sani na ilimin bokanci da
sihiri da ke raye a doron kasa, ka sani cewa na yi yanka
ga ababen bautata don neman nasara a kanka kuma ina
da tabbacin samun nasara akan hakan. Babu shakka ka
cika namiji ma'abocin jarumta da sadaukantaka don duk
a cikin masoyan Gimbiya Hasima da na halaka babu
wanda ya kai ka jarumta da karfin zuciya. Sai dai
wannan rana ita ce sa' arka ta karshe a rayuwar duniya
da zan halakaka kamar yadda na dauki alkawarin halaka
duk wanda ya ambata yana kaunar Gimbiya Hasima
Ya daga sandar sihirin dake hannunsa zai daki
Zuhairu da ita a tsakiyar kansa ya halakashi Gimbiya
Hasima da ke tsaye a gefe tana gani abin da yake faruwa
ta yi karaji da kururuwa irin na firgita da ganin matsafi
Bahalu zai halaka Zuhairu a sannan Buniyatu ta farfado
daga suman da ta yi ta hangi abin da yake shigin faruwa
yayanta matsafi Bahalu ya daga sandar sihirinsa zai daki
Zuhairu da ita, ya halaka Nan take ta mike cikin sauri ta
shiga tsakaninsu ta kare Zuhairu kafin ya dakeshi da
sandar tana mai fadin cewa.
"Kada ka halaka abin begena dan kuwa ba zan iya
rayuwa a duniya ba batare da shi ba, idan kuma ka ce sai ka halakashi to kuwa sai dai ka halakamu gaba daya ni da
shi."
Matsafi Bahalu ya fasa dukan Zuhairu da sandar
Sihirin ya dubı "yar uwarsa Buniyatu ya ce da ita.
"Tunda kin zabi kare abin begenki akan zama da nj
dan uwanki to kuwa zan barki tare da shi ba zan
halakashi ba, duk da na yi rantsuwa da ababen bautata
akan aikata hakan, sai dai ki sani daga yau babu ke babu
sake aikata wani aikin sihiri tunda na kwace kurtun
sihirin dake hannunki, kuma ba zan sake maidashi a
gareki ba har abada. Za ki ci gaba da zama a wannan
birni tare da wanda ki ka zabi zama dashi fiye da ni dan
uwanki na jini, ni kuma zan dauki Gimbiya Hasima na
tafi da ita Darul Sabar fadar da mahaifinmu ya gina kafin
ya tare a cikinta ya rasu, mu zauna a can tare da ita.
Kuma har abadan ba za ki iya riskar inda wannan fadata ke
ba, bare ki dawo gareni har karshen rayuwarki, saboda ba
kya tare da duk wasu dalasumai na aikin sihiri da za ki
yi amfani da su don zuwa wannan fada."
Yana gama fadar maganar ya juya ga Zuhairu ya
nunashi da sandar sihiri da take hannunsa ya soma
karanta wadansu dalasumai na aikin sihiri wani farin
haske ya fito daga jikin sandar ya shiga jikinsa. Nan take
Zuhairu ya soma tsuma da makyarkyata irin ta rawar
sanyi har sai da ya durkushe a kasa, sannan sai
kamanninsa suka soma sauyawa daga siffarsa ta saurayi
maji karfi ya zuwa siffar dattijo mai tarin shekaru
ma'abocin rauni, gaba daya gashin jikinsa ya koma fari
fat irin na furfura tamkar dattijo da ya haura shekaru
tamanin a duniya, daga nan ya fadi kasa a sume.
Buniyatu da Gimbiya Hasima suka kwala wata
razananniyar kara saboda ganin abinda ya faru akan zuhairu, matsafi Bahalu ya bushe da dariya irin ta
mugunta da zalunci sannan ya dubi Buniyatu ya ce da ita
"Wannan shi ne yadda abin begen naki zai kasance
har karshen rayuwarsa kuma haka za ki kasance da shi
cikin wannan siffa ta dattijantaka, har abadan ba zai dawo
siffarsa ta asali ba, ko matukar bani ne na karya wannan
aikin sihirin ba kuma aka bashi ruwan da ke cikin rijiyar
BASRA dake tsakiyar fadar Darul Sabar da zan tafi da
Gimbiya Hasima, kuma babu wani mahaluki da ya isa ya
shiga cikinta komai karfin tsafi da sihirinsa idan bani da
na mallaketa ba ko kuma wanda na yiwa izinin ya
shigeta.
Ya sake kyakyacewa da dariya sannan ya daki kasa
da sandar sihirinsa, iska mai karfi ta keto daga bayansa
tare da bakar guguwa suka hadu suka turnuke wajen
suka yi tsiri a sama, matsafi Bahalu ya bi ta cikin bakar
guguwar ya bace, sannan ya biyo ta inda Gimbiya
Hasima take a tsaye cikin kuyanginta ya sureta ya yi
sama da ita
Gimbiya Hasima ta yi karaji da kururuwa mai
tsananin karfi sanda matsafi Bahalu ya sureta ta cikin
bakar guguwar nan ya tashi sama da ita. Buniyatu da
sauran kuyanginta suna ganin sanda guguwar ta yi sama
da Gimbiya Hasıma tana karaji da kururuwar neman
taimako amma duk cikinsu babu wanda za ta iya taimaka
mata. Tun suna hangenta da jin karajinta har ta bace
Cikin bakar guguwar nan matsafi Bahalu ya tafi da ita.
Bayan tafiyar matsafi Bahalu sai wajen ya washe
duhun da ya lullube sararin samaniya ya yaye suka daina
Jin karaji da rugugın da suke ji tun da farko. Buniyatu ta
dubi Zuhairu ta ganshi cikin halin suma ta tafi gareshi
cikin sauri ta dago kansa tana girgizashi taga babu alamar motsi a tare da, shi, hankalinta ya kara tashi. Ta
tashi cikin sauri ta tafi bakin kogin dake gudanarwa ta
tsakiyar lambun ta debo ruwa ta dawo ta zauna ta rika
shafa masa ruwan tana girgizashi cikin kuka. Sai da ta
dauki lokaci mai tsawo Zuhairu yana cikin wannan hali
sannan ya farfado daga suman da ya yi.
Da farfadowar Zuhairu ya tashi zaune a firgice, ya
duba bai ga matsafi Bahalu da suka fafatawa a kusa da
shi ba, ya dubi jikinsa ya ga yadda kamanninsa suka
koma irin na tsoho tamkar dattijon da ya shafe shekaru
casa'in a duniya, ya sake duban inda kuyangin Gimbiya
Hasima suke tsaye bai ganta a cikinsu ba, hankalinsa yai
matukar tashi, duk da irin halin da yake ciki na
komawar kamanninsa irin na tsufa, babu abin da ya fara
tambaya sai ina Gimbiya Hasima.
Daya daga cikin kuyangin nan ta amsa masa da
cewa wannan shu'umin matsafin ya dauketa, ya tafi da
ita.
Zuhairu ya mike tsaye cikin karaji duk da siffa irin
ta tsufa da kamanninsa suka koma yana jin karfin jikinsa
kamar yadda ya ke ji tun da farko. Kafin matsafi Bahalu
ya yi masa wannan aikin sihiri a jikinsa, ya dauki
takobinsa ya tasarwa Buniyatu cikin fushi daharzuka
yana mai fadin cewa "Sanar dani inda yayanki matsafi
Bahalu ya tafi da Gimbiya Hasima. Idan kuma ki ka
bijirewa ambatona na rantse da sarkin da raina yake
hannunsa sai na halakaki da kisa mafi muni da kaskanci,
kafin na kai ga gano inda yayan naki yake na tafi gareshi
shima na halakashi akan daukar Gimbiya Hasima da ya
yi.
Buniyatu ta amsa masa da cewa "Ya abin begena
Zuhairu ka yarda dani da abinda zan ambata gareka, da


BAKAR GUGUWA
littafi na biyu 2
Na Shehu Usman Muhd
typing by Shuraih Usman
post by Shuraih 99%
Part B
.
.
nake yi maka ya zarce yadda nake son komai a duniya.
Zuhairu ya ce da ita "Ba zan amince da maganarki
ba, har sai kin yarda za ki yi imani da Allah ki karbi
addinin Musulunci, ki daina bautar gumaka da tsafi ki
rabu da duk wata shirka da sihiri da ki ke aikatawa."
Buniyatu ta ce da shi "Na amince zan karbi addinin
Musulunci idan har za ka yarda dani na zama abar
gasgatawa a gareka, maganar aikin sihiri kuwa a yanzu
bani da ikon aikatawa tun da dan uwana ya kwace kurtun
sihirin da yake hannuna wanda a cikinsa ne alkaluman
sihirin da zan iya amfani da su don yin wani aikin sihiri
suke ciki, kuma a yanzu ya yi fushi dani saboda ina
kokarin baka kariya daga abinda yake son aikatawa a
gareka, ya kuma yi alkawarin ba zai sake maidashi a
gareni ba har abada."
Da ta gama yi masa wannan bayani Zuhairu ya sata
ta yi kalmar shahada ta shiga addinin Musulunci tare da
sanar da ita abinda ya wajjaba akan kowane Musulmi,
daga nan ya tambaye ta cewa yanzu ta wacce hanya zamu
iya riskar inda matsafi Bahalu ya tafi da Gimbiya Hasima
dan na kubutar da ita daga hannunsa.
Buniyatu ta amsa masa da cewa "Ban san inda
fadar take ba, a fadin duniya amma na yi sani da wani
rubutaccen sako na sirri da mahaifinmu ya bari, wanda
ke kunshe da tarihin yadda aka gina fadar da dukkanin
Siminta, sai dai a yanzu rubutaccen sakon baya tare da ni
yana cikin kogon dutsen da muke zaune tare da dan
uwana da mahaifinmu kafin ya rasu.
Zuhairu ya sake tambayarta "A ina wannan kogon
dutsen ya ke."
Buniyatu ta ce da shi "Yana can kusa da birnin
Kisira tsakanin wasu manyan tsaunuka a gabar kogin bahar Sugaira, tafiyar kwanaki biyu muke yi cikin
alkaluman sihiri na rage nisan tafiya. Kafin mu iso
wannan kogon dutse amma a yanzu sai D
mun yi tafiyar
kwanaki arba'in saboda bada alkaluma sihiri zamu yi taiyar ba."
Zuhairu ya ce "Na dauki alkawarin sai na kubutar
da Gimbiya Hasima daga hannun matsafi Bahalu da ya
tafi da ita ta kowane irin hali matukar zan yi sani da inda
wannan fada take a fadin duniya, don haka mu tafi ya
zuwa birnin Bahazum fadar sarki Shaiban mahaifin
Gimbiya Hasima, na sanar da shi abin da ya faru gare ta,
sannan mu wuce alkaryarmu na sanar da kakana abin da
ya faru gareni daga nan na yi shiri don tafiya wannan
fada."
da ya
Da nan ya juya ga kuyangin Gimbiya Hasima ya
umarcesu da su kama dawakansu su hau don komawa
gida su sanar da Sarki abin da ya faru, kuyangin suka
kama dawakansu suka hau ita kuma Buniyatu ta hau
dokin Gimbiya Hasima, Zuhairu ya hau nasa dokin suka
kama hanyar komawa birnin Bahazum
Da isar su Birnin Bahazum...


Read / Download BAKAR GUGUWA book 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

2 Comments On BAKAR GUGUWA book 2
avatar
auwal-6-7

4 months ago

Reply

Littafine hadadde wanda Na dade ina nema

avatar
abasu-kala

4 months ago

Reply

Replying to auwal-6-7

Ga shi kuwa yanzu ka sameshi

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album