Join Our WhatsApp Group

ME YA FI KUDI Complete Hausa Novel Document by ME YA FI KUDI


ME YA FI KUDI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 30561



ME YA FI KUDI

Reading Time: 2 Hours

Added On: 28, Sep 2023

Author: Nazir Adam Salih ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 171.14 kb

File Type: txt

Views: 509+

Download: 220+

Last download: 2 days ago

Description/Story: ME YAFI KUDI ? - 01
.
(c) Nazir Adam Salih
.
Copy Right (c)
Nazir Adam Salih 1996
.
Hakkin Mallaka (M)
Nazir Adam Salih 1996.
.
An Fara Bugawa A 1996
.
An Sake Bugawa A 2009
.
GARGADI
Wannan Littafi Kagagge Ne Anyi Shine Kuma Badon Cin Zarafin Kowa Ba Musamman Ma Masu Hannu Da Shuni Sai Don Nuni Cikin Nishadi Dakuma Fadakarwa. Ba'a Kuma Yarda Ajuye Shi Ta Kowace Hanya Ba Saida Izinin Marubucin.
.
Adireshin Marubucin
Abubakar Saddik Islamiyya Dakata
Akwatin Gidan Waya 4792.
NAZIR ADAM SALIH.
.
ME YAFI KUDI
.
BABI NA DAYA 1
.
LAILA na zaune atsakiyar furanni da fulawowin bishiyoyin da sukayiwa farfajiyar gidan kawanya akan wata kujerar karfe fara mai launin azurfa agabanta akwai teburin dake dauke da manyan takardu guda biyu farare ne irin wanda masu zane ke amfani dasu.
Agefen takardun daga hannun dama akwai farin akwatin kala wanda ke dauke da kaloli goma sha biyu da kuma burusan zane guda uku. Dan karamin teburin dake gefen lallai daga hannun hagu yana dauke da goran zuba shayi FLASK adab dashi kuma akwai kofuna biyu daya daga cikin kofunan na dauke da ruwan madara dayan kuma kusan rabinsa acike yake da ruwan shayi nata tururin zafi wani bangare kuma na teburin farantin kayan marmari ne dakuma wata katuwar salula mai kamar dankali.
Lallai ta dauki daya daga cikin manyan fararen takardun nan ta kurawa zanen data fara idanu sannan ta gyada kai cikin gamsuwa da abinda ta gani ta kurbi shayina ahankali ta mayar da kofin shayin wurinz amansa sannan ta dauko daya daga cikin burusan zanenta ta tsoma shi cikin ruwa ta shafi shudiyar kala ta fara shafawa a zanenta bayan tayi kamar minti daya tana shafa kaloli iri daban daban saita ajiye burushin sannan ta sake nazarin abinda take zanawa.
Adaidai lokacin ne taji salularta ta dauki dan kara. Nan da nan ta mika hannun tsakiyar teburin ta dauko salularta ta kara a kunne tafara magana da zazzakar muryarta.
Na'am ta amsa sannan ta bata fuska tace ina zuwa
cikin muryar da zaka iya cewa raini cikin fushi saitayi jifa da salular dake hannunta izuwa tsakiyar dan karamin teburin nan hakan ne ma ya janyo har kofin madarar dake kai ya bare bata ko kula abinda yafaru ba saita mike tsaye.
Shi baba sai ya dami mutum da kira kamar tsohon makaho. Ko kadan baya barin mutum ya more rayuwarsa shi ya dauka kowa ma irinsa ne da zaiyi ta neman kudi ta kowane hali babu hutu babu godiyar Allah ga ya takurawa talakawa shi baiji dadin kudin ba kuma bai bar wasu sunji dadin kudin ba.
Laila taci gaba da tafiya tana zancen zuci cikin kunan rai.
Bari naje naji abinda zaice min kuma nasan dai tatsuniyar gizo bata wuce ta koki ni dai wallahi nagaji da bada muguwar shawara haba wannan wane irin Ubane ?
Laila tayi tsaki sannan cikin fushi saita kara sauri ta ratsa ta cikin korayen ciyayi da furannin alfarma dake farfajiyar gidan ta nufi wata kofar gilas da sauri tun kafin ta karasa sai kofar ta bude a kanta sannan saita kutsa kai tashiga batareda ta damu datayi sallama ba.
*** *** *** ***
Karfe tara da minti bakwai agogon dake manne ajikin bangon dakin ya nuna ALHAJI BALARABE fari dogo kakkaura mai manyan kumatu na zaune akan daya daga cikin manya manyan kujeren alfarmar dake dakin. Alhaji Balarabe zaiyi kimanin shekaru arba'in da biyar aduniya amma idan ka dube shi saika dauka baifi shekara talatin da biyu ba. Yana da tarin dukiya kamar dan karuwa domin wasu makaryata ma sun dade suna jita jitar cewa wai zai iya yin kasafin kudin Najeriya na shekara guda batareda ya girgiza ba.
Abinda kawai ke ba mutane mamaki shine babu wanda yasan takamaiman hanyar da Alhaji balarabe yabi ya sami kudinsa shi mutum ne wanda bai cika kula talakawa ba domin wai aganinsa hakan yakan kawo raini. Bai kuma cika mu'amala da kananan masu kudi ba domin shi aganinsa zasu rika tunanin matsayinsu daya idan kuwa maganar manyan kudi ne to akullum kalmar alhaji balarabe daya ce akansu Gara a banbance tsakanin miloniya da biloniya yawancin lokuta alhaji balarabe kan fadi hakane idan suna da Laila 'ya daya daya mallaka aduniya kuma yake matukar sonta kamar ya hadiyeta. Tun da uwar laila ta mutu har yau Alhaji balarabe bai sake aure ba saidai kuma anki cin biri an ci dila domin awannan lokacin ne ya shiga harka da matan banza duk da yake dai daman can yana tabawa a boye amma bashida sukuni saboda yana matukar tsoron mahaifiyar laila.
Tun daga talakawa da manyan yan sa ido har zuwa kan kananan masu kudi da manyansu babu wanda zai iya rantse ma dacewa yasan daga inda dubban miliyoyin kudi ke kwararowa zuwa asusun Alhaji balarabe ba kowa yasan cewa idan harkar masana'antu akwai wadanda masana'antunsu sunyi biyun na alhaji balarabe to amma idan akazo kan maganar ya'yan baki fa? Shine biloniya uban masu kudi babu wanda ya yarda ma kansa cewa alhaji balarabe ya dogare ne kawai da masana'antunsa lallai kam akwai wata hanya amma wacce hanya ce?
Amsar itace babu wanda yasani.
Agaskiyar lamari alhaji balarabe na daya daga cikin manyan masu safarar hodar ibilis daga najeriya zuwa kasashen afirka dake makwabtaka da ita
.
Yaki halak yaki haram shine aikin Alhaji balarabe duk wani babban barawo daya shahara awajen satar motoci alhaji balarabe ne bangon buyansa yan fashi da makami bata garin yan sanda da yan daukeni na kashe. Duk suna samun albashinsu ne daga wajen alhaji balarabe.
Idan kuma muka duba bangaren sauran masu kudi alhaji balarabe ya zame musu kadangaren bakin tulu akwai jita jita dake cewa akwai masu hannu da shunin da suke tsoron alhaji balarabe fiyeda ubangijinsu ya zama kamar ubansu sai abinda yace. Idan ka saba masa kuwa tun kafin wani abu yafaru akanka zakaga masu kudi sun fara yi ma jaje domin sun san kai taka ta kare idan ya bukaci wani abu daga wajenka bai samu ba tabbas zai yi amfani da karfin dukiyarsa wajen cimma bukatarsa koda kuwa ta hanyar kisan kai ne.
.
Shekaru shida da suka shude tun lokacin da mahaifiyar laila ta mutu sai ya fara tunanin koyawa laila mugayen halayensa domin yace ai kyan 'da yagaji ubansa wajen neman abin duniya.
Lokacinda laila zata tafi makarantar gaba da sakandire sai alhaji balarave ya turata kasar ingila acan ne tayi digirinta na farko fannin zane yau shekarunta biyu kenan da dawowa wani abin mamaki shine alhaji balarabe na matukar tsoronta kamar yadda yake tsoron mahaifiyarta domin duk zaluncin da zaiyi sai ya nemi shawararta idan tace ayi ayi to an gama amma idan tace a'a to an bari kenan.
Yau kimanin watanninsu hudu kenan suna haka da ita hakanan akullum kwanan duniya nuna mata yakeyi cewa ita fa duniya bata rago bace kuma saida wuru wuru.
Sau da yawa alhaji balarabe na son ya zauna yayi hira da yarsa laila tun ma kafin tayi wayo yakan zaunar da ita akan kujera shi kuma sai ya zauna akusa da ita yayita bata labarin dukiyar daya samu ta hanyar zalunci. Da kuma irin dabarun da yake amfani dasu wajen aikata zalunci wani lokacin sai ya dubi laila cikin murmushi yakira sunanta idan ta juyo ta kalle shi sai yace inason ki hadda wasu ayoyi guda uku wanda zasu miki amfani idan kin girma
sai ta dube shi tace To Baba a tsammaninta ayoyin da zai fada mata irin ayoyin da ake karanta musu ne a islamiyya.
Shi kuma saiya dubeta yace
Inason ki san cewa zama da talaka na kawo raini sannan mu'amala da kanan masu kudi ita ke zubar da darajar biloniya har takawo raini tsakaninsa da kanan masu kudi harma su fara tunanin matsayinku daya kina jina ko ya ta? Alhaji balarabe zai tambaya.
Ita kuma saitace ina sauraro baba.
Amma cikin zuciyarta ba haka bane domin aduk lokacin daya fadi haka saitaji girmansa ya zube agurinta.
Shi kuma sai yaci da cewa Idan kin girma yata inason ki gaji dukiyata domin kema ki bambance
Na banbance me baba? Tambayar da laila keyi masa kenan a kullum idan ya soma karanta mata ayoyinsa na shedan.
Shi kuma yakan amsa mata da cewa ki banbance tsakanin talaka almajirin masu kudi sannan kuma miloniya da biloniya.
Ita kuma laila saitayi murmushi tace nagane banbance tsakanin talaka da almajirin masu kudi saidai kuma ni baba ban gane banbance tsakanin miloniya da biloniya ba.
Shi kuma saiyaci gaba da cewa ki dauki misali dani laila idan kika lura zakiga duk masu kudin garin nan tsorona sukeji fiyeda yadda suke tsoron ubangijinsu ba kuma don wani abu ba sai don karfin kudina da kuma karfin kungiyata da kuma irin rashin imanin da nake nunawa akan duk wanda ya shiga hanyata.
Kamar wanne irin rashin imani kake nuna musu baba? Laila takan tambaya.
Shi kuma sai yace Misali yanzu ina bukatar wani abu daga hannun wani hamshakin mai kudi idan na tambaye shi ta hanyar lumana yaki sai nasa a tsorata shi idan yayi taurin kai yaki sai nasa a kashe shi in kwashe dukiyarsa ta zama tawa. Kuma kinga wanda zansa yayi kisan kan bazaiyi ba saina biya shi kudi masu yawan gaske kinga ashe kenan da banida karfin kudi abayana da yanzu zaman garin nan yayi min wuya don haka kullum 'yata nake so ki rika amfani da abinda nake karanta miki domin kinsan harka da talaka kan kawo karayar zuciya da kuma rage kwarin gwiwar samun kudi ta kowace irin hanya don shi talaka kullum shi zai nuna ma shi mai tsoron Allah ne shiyafi kowa tawakkali bazai tashi ya nemi duniya ba idan ka biye masa saiku taru ku mutu cikin talauci.
Aduk lokacin da alhaji balarabe ya fadi haka ita kuma laila saita tambaye shi dacewa KAI BAKA TSORON ALLAH NE BABA? Shikuma saiyace kudi basu cika samuwa agurin matsoraci ba awannan zamanin namu don haka idan kina so ki banbance yadda kike so to ki fitar da harkar tsoron komai azuciyarki Alhaji balarabe kanyi shiru aduk sa'ar dayazo nan ita kuwa laila saita kalle shi cikin dariya sannan tace Lallai baba kayi nisa.
Kin fadi gaskiya yata itace amsar alhaji balarabe sannan saiyaci gaba da cewa kudi sune rayuwar mutum idan ba kudi to kai da dabba duk daya kuke a samu kudi ta kowace hanya 'yata abanbance tsakanin biloniya da miloniya aduk lokacin daya fadi haka sai yacika da nishadi yayi dariyar mugunta...ME YA FI KUDI ? - 02
.
Duk lokacin daya fadi haka sai yacika da nishadi yayi dariyar mugunta ya buga kafa a kasa sannan saiya dauki Laila ya dora ta akan cinyarsa itakuma tana dariyar yarinta shikuma idan yaga tana dariya sai yace Gaskiya ce 'yata a bambance.
Ita kuma saita amsa da cewa
TSAKANIN BILONIYA DA MILONIYA.
.
Da kyau 'yata. Alhaji balarabe zaice cikin dariya sannan sai ya kalleta yace idan kuma karya ne to afada mana
ME YA FI KUDI?
To a wannan safiyar kuma Alhaji balarabe na karatun jarida sai yayi kicibis da inda aka rubuta wani abu kamar haka. Alhaji Abubakar tsohon ministan sufuri na kasa ya saye kasaitaccen kamfanin nan na takalma dake Ikko
Alhaji balarabe yayi shiru sannan ya sake karanta rubutun ya girgiza kai cikin fushi sannan yace a bayyane.
Wato kamfanin da nake kokarin saya ma shine wannan marar kunyar ya saye? To shikenan ya tari aradu da ka zakuma ta rugurguza shi nan da nan ya dauki salularsa ya buga cikin dakiku uku saiga shi yana magana da laila.
Menene? Laila ta tambaya sannan alhaji balarabe yace da ita kiyi sauri kizo nan inason ganinki sannan ya ajje salular ya sake nazarin jaridar dake hannunsa sai ya ga har da hoton kamfanin ashafin farko na jarida haushi ya kamashi sai ya yi jifa da jaridar zuwa kofar falon.
Adaidai lokacin ne kofar ta bude laila ta shigo dakin ta kalli alhaji balarabe sannan ta kalli jaridar dake kasa kana ta matsa kusa da daya daga cikin kujeren falon ta nutse aciki
Shiru na dan lokaci babu wanda yace da wani kala sannan sai alhaji balarabe yace da laila dauki jaridar can ki duba.
Laila ta taso daga kan kujerar da take zaune ta dauki jaridar ta koma wajen zamanta tafara karanta abinda ke ciki.
Dakin ya sakeyin shiru bayan dan lokaci da fara karanta jaridar saita ajje ta akan kujera sannan ta dago kai ta kalleshi a yatsine.
Nagani menene kuma?
Me kika fahimta? Alhaji balarabe ya tambaya cikin fushi.
Laila ta kalleshi a fusace tace abinda na fahimta shine alhaji abubakar ya sayi kamfani kuma an sallama masa amma kai baka so ya saya ko ba haka bane baba?
Ganin ran laila ita ma ya baci sai alhaji balarabe yayi murmushi sannan ya sassauta murya yace ashe kin gane 'yata ya danyi shiru yana juya kalmar da zai fada ta gaba cikin zuciyarsa.
Menene shawararki akai kinsan dai yadda kamfanin yake duk fadin najeriya babu kamfanin daya fishi wajen yin takalma masu inganci kuma babu wanda ya kamata ya mallake shi sai ni domin ni nasan dadin kudi nasan wahalarsu sannan kuma ni na iya juya su.
Laila tayi masa wani irin kallo irin kallon da zakayiwa mutumin da kake tsammanin ya tabu sannan laila ta lumshe fararen idanunta tana fadi a zuciya Allah kayi mana tsari da shedanin uba. Allah ka tsareni bin hanyarsa.
Bakiji abinda nake fada bane? Maganarsa ta katsewa laila addu'arta ta dago kai ta dubeshi sannan tace dashi batareda ta dubi fuskarsa ba.
Ni babu shawarar da zan baka baba kayi duk abinda kaga ya dace tafara kokarin mikewa tsaye.
Dakata dakata mahaifinta ya katse ta wato rashin kunya zaki min ko? To bari kiji ko uwarki bata isa tayi min rashin kunya ba lokacin da take raye kinfi ni sanin abinda yadace nayi ne? Malamai ma sunyi sun barni duk huduba ko wani wa'azi in bana kudi bane banza ne agurina ke yanzu in banda haukanki ina ke ina biye shirman talakawa wai Allah zai kawo to shi Allah akwance zai baka?
Dole ne awannan zamani in har mutum yanaso yakai labari ya nemi ta kowace hanya.
Amma ba hanyar haram ba laila ta katse shi.
To naji Alhaji balarabe yace wato duk abinda nake gargadinki dashi tun kina karama aikin banza nake yanzu ke in banda shashanci wa kika taba ganin yayi kudi ta hanyar halak azamanin nan? Ai abinda akeyi kawai shine a nemi kudin ta kowace hanya koda haramce idan sun taru sai a debi kashi biyu daga cikin dari na kudin a ginawa talakawa masallaci rijiyoyi da kuma asibitoci kinga ladan da Allah zai baka awannan ya isa ya share dan alhakin daka dauka na waccan haram din dakaci.
Alhaji balarabe ya danyi shiru sannan sai bakinsa ya fadada zuwa murmushin mugunta Laila ke haryanzu yarinya ce ana nuna miki hanyar da zakibi ki samu kudi nan da nan kina ki.
In banda abinki Me Yafi Kudi? Ai babu ke inaso kiyi gadona amma kullum sai fama kike da tawakkalin talakawa wai Allah zai kawo.
Yaushe zai kawo in kana kwance kamar tabarma?
Allah ka tsare mu da sharrin shaidanun iyaye ka kuma tsare mu da sharrin jahilci allah ka shirye shi dain...


Read / Download ME YA FI KUDI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album