Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

UWAR MIJI Complete Hausa Novel Document by UWAR MIJI


UWAR MIJI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 8277



UWAR MIJI

Reading Time: 0 Hours

Added On: 10, Aug 2024

Author: Aisha Yahaya Tanko ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : KING AND QUEEN WRITING CHAMBER

Author Phone : +234 817 384 6034

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 43.88 kb

File Type: txt

Views: 404+

Download: 230+

Last download: 15 hours ago

Description/Story: UWAR MIJI


Da sunan Allah ne rahama me jikai

Gargadi

Banyar da wani ko wata yayi amfani
Wani shashi na littafina ba batare da
Izina naba ko mai da shi document
Ko masi YouTube channel su mai
Da shi audio

In kunne yaji......jiki ya tsira
Wannan labarin ƙirƙirar rene duk
Yaga yayi dai-dai da rayuwar sa
Ya dauka armashi ne......



Bisimillahir rahamanir rahim


*🍁🍁UWAR MIJI🍁🍁*






PAGE 1





*BY AISHA YAHAYA TANKO✍️*





~Wannan labari ba wai na rubuta shi dan cin mutuncin wata ba, kawai nayi shi ne saboda nishadanarwa da kuma ɗaukar darussa akan abinda ya kunsa~

*Ina neman addu'arku masoyana akan FATIMA IBRAHIM MUHAMMAD Allah ya yaye mata lallurai da take damunta😭 ga dukkan wanda ya karanta pls ya taimaka sadaka ce Allah ya bata lafiya da dukkan musulmin duniya baki daya* 🙏🏻🙏🏻


Hajja Sarai ce zaune a ɗaya daga cikin kujerun dake katafaren falonta cikin kasaita take magana tana kurbar lemon gwangwani tana ajiyewa ta ajiye lemon tana bin ko waccen su da kallo,yayin da suke zube akan kafet ɗin falon magana tayi da cewa.


"nasan baku san dalilin da yasa na taru ba koh, to inaso Ku bani hankalinku Ku buɗe kunnuwanku ku ji abinda zan faɗa muku,da farko dai kunsan zaman aure shi ya kawo Ku gidan nan kuma kun san koni wace a wajenku ni dai UWAR MIJI ce ba uwar Ku ba ina da sharadan wanda zan kafa muku game da zama da ƴaƴan na duk wadda tabi su zata sha romo kuma haka duk wadda ta ki binsu zata fada cikin rijiyar me zurfi bani da farin cikin daya wuce farin cikin su nasan kun auresu ne dan so da kauna kuma nasan ko waccen Ku bazata rasa buri ba na ganin ta mallaki wani abu daga wajen mijinta to inaso ku kiyaye ku san zaman aure bauta ne ba wai hutu bane kar kuga kun shigo daular da ko wace ƴa mace take mafarkin samo sannan ku dage da yiwa mazajenku biyayya da kuma yi musu fatan alkairi sannan kunsan dole ku dinga yiwa kanwarsu zahra biyayya itama tare da faranta mata rai da kuma gujewa bacin ranta nazo gareki Khadijah karki dauka dan mahaifiyarki aminiyata ce shi zaisa na raga miki to ba wannan maganar a wanna lokacin ki manta da wannan alakar ki yi amfani da aure kika zo".


Ta kara kurbar lemon sannan ta kara gyara zama tace.

" ke kuma Salma karki duba dan gantakata dake na ƴar kanwata ki cireta acikin ranki na dawo gareki Amina kema zaman aure kika zo ba wai ki nuna gidan wan mahaifinki bane dukkan ku cire alakar sanayya kuyi amfani da ni UWAR MIJIN ku ce fatan kun gamsu da bayanai na daga karshe inai muku fatan alkairi sannan ku zauna lafiya ko akwai wadda bata gamsu da bayani na ba to tayi magana tun kafin na shiga daki naga dare ya fara.

Gaba daya suka amsa da Aa ko wacce ta mike ta nufin sashenta.

Salim da Adam da Aminu suka shigo a tare suka rusuna agaban Hajiya suna gaisheta ta amsa cike da nuna jin dadinta ta sawa auren nasu albarka sannan ta musu kashedi akan su kiyaye dan yanzu bata shirya karbar jikoki ba.


Gabaa ɗaya suka zaro ido lokaci guda Aminu ya yi gyaran murya ya soma magana.

"Amma Hajja karki manta mutum baya shiryawa kansa rayuwa kuma duk wanda yai aure burinsa ya tara zur'ia tunda ya raya sunnar ma'aiki".

Baka da kunya ne Hajjan kake fadawa irin wadannan kalaman to wallahi idan baka bata hakuri ba yanzu zaka fuskanci hukunci .

Aa ku rabu dashi ya fada min abinda yake bakinsa ai yau yayi aure dole yaga kamar kanmu daya amma inaso ya sani duk abinda zai fada baze sa na janye kudirina ba.


Dan Allah Hajja ki gafarce bawai na fada dan na saba miki ba sai dan na tunasar dake amma ki yafemin kimin afuwa na tuba yana gama fada be jira yaji abinda zata ce ba ya shiga sashensa cikin sauri.

Nan ya iske Salma tayi tagumi hannu biyu hawaye na zuba ta kuncinta cikin sauri ya karasa inda take hannu yasa ya fara goge mata sannan ya ajiye mata ledar a gabanta..



```Ya kukaji wannan page ɗin, comment ɗinku shine ze bani ƙarfin gwiwar da zan ƙara sa muku```




🍁🍁UWAR MIJI🍁🍁




PAGE 2 ✍️




*BY AISHA YAHAYA TANKO🥰*






Salma kiyi hakuri nasan rabuwarki da umma akwai damuwa amma ki sani dama wannan ranar zata zo ko ba dade ko ba jima tunda dole za kiyi aure aike gida kika dawo tunda Hajja uwace a gareki ko da ban aureki ba.

Nifa ba wai rabuwa da Ummata ne yake damuna ba kawai dai ina tuna wani na daban da kuma irin rayuwar da zan fuskanta ta zaman aure.


Duk ki bar wannan maganar ki tashi muje muyi alwala muyi sallah muci abinci dan ni rabon dana sa wani abu a cikina tun a wajen dinner shima ke kika bani 2 spon ɗin nan,nan ya fara kici kicin cire babbar rigarsa yai wurgi da ita gefe guda suka mike a tsaye a tare suka nufi Toilet.

Tun bayan tafiyar Aminu Hajja ta kasa zaune da tsaye a cikin falon ta dubi su Salim da Adam tace kar kuyiwa Aminu komai Ku kyaleshi zan zauna da shi na fahimtar dashi dalilina na yin haka nasan ze gane manufata

Ta tsaya a tsakiyar falon hannu tasa tai musu nuni da su tafi wajen amarensu,suka mike cikin sanyin jiki kowannesu zuciyarsa cike da sake-sake ya doshi wajen amaryarsa.

Shigar Adam dakin ke da wuya ya tarar da khadija ta manne da bangon dakin tana faman sharbar kuku tamkar wadda akai mata auren dole turus yayi abakin kofar yana mamakin ganinta cikin wannan halin ya soma kiranta.

"Khadija! Khadija!!khadija!!! ko ba kece wadda muka shiryawa kanmu rayuwa ba kina tuna kin min alkawari adaren da muka tare zaki shayar dani zumar soyayya amma sai gashi tun kan aje ko ina kina zubar da hawaye pls ki dakata haka kin wannan ranar tana cike da daraja da kuma dumbin alkairai".

Ya karaso inda take hannu yasa ya yaye mata mayafin dake jikinta yana dubanta haba kanwata saboda kin rabu da Abbanki shine zaki sa kanki cikin wani hali ko dan ke shalelansa ce kin san dai nan ma gida ne tunda Hajja uwace garemu yanzu ki bar wannan kukan haka zan kira miki shi Ku yi magana kinji.


Ta dago Kai cikin sauri ta dakatar dashi karka kirawo shi bana bukata ka kyaleni da radadin da zuciyata takeyi na....

Ya saurin rufe bakinta me kike shirin fada ne ki tashi mu shiga ciki ki samo kici kazar nan ki huta nasan kina tare da gajia ya kama hannu suka shige cikin daki.

A can bangaren su Salim kuwa tun bayan shigarsa wajen amarya yaci karo da kwandon masifa duba daya yai mata yace inaso kiyi hakuri be kamata a irin wannan ranar mu sami matsala ba kin san dai Hajja sarai mahaifiyata ce dan haka ya zama dole kibi dukkan sharadin data kafa muku idan har da gaske kina min soyayyar da baki taba yiwa kowa ita ba koda ban aureki ba nan gidan wan mahaifinki ne inaso ki kwantar da hankalinki mu zauna lafiya ya zamana munfi kowa jin dadi kinga yanzu idon kowa yana kan gidan nan tun bayan rasuwar Baban mu mutane suka zuba ido suka yadda zamu kasance da ke kin fi kowa sanin wace Hajja sarai ba sai na fada miki ba kiyi hakuri kisha koda ruwana ne dan zuciyarki ta sami sauki.



Washe gari ne Amare suka sha ado suka nufi sashen Hajja Sarai anan ne zasu dimga cin abinci an shirya musu abinci iri daban daban Hajja Sarai ta dubesu tace.


"Ko wace zan sa mata ranar da zata dinga girki a gidan nan da kuma lokacin yinsa sannan bazan sallami su karime ba, zansa su dinga taimakon kon wajen gabatar da girki sannan zasu dinga nuna muku abinda baku gane ba zaku su sanar daku irin abincin dana fi so fatana anan ku bani hadi Kai mu gudu tare mu tsira tare".


A yanzu Amina ce zata zubawa kowa abincin da zaici amma inaso ko wacce ta fadi irin wanda take sanci .

Nan da nan Amina ta fara kokarin buɗe katafaren plas da aka shakareshi da zabi ta fara zuba Hajja Sarai ita dai kawai tana binta da kallo bayan an gama cin abinci ne Hajja Sarai tace.


"Inaso nan falon ya zama wajen da ku dinga zama kuna hira bana san ku yawaita zaman daki kuna shirman banza
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download UWAR MIJI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album