Join Our WhatsApp Group

YA ZA A YI BOOK 1 Complete Hausa Novel Document by YA ZA A YI BOOK 1


YA ZA A YI BOOK 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 27573



YA ZA A YI BOOK 1

Reading Time: 2 Hours

Added On: 03, Jan 2024

Author: Binta Umar Abbale ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08089965176, 07084653262

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 142.96 kb

File Type: txt

Views: 736+

Download: 329+

Last download: 2 days ago

Description/Story:  YA ZA A YI?
BOOK1
NA KUDI NE LITTAFIN
MASU BUKATAR COMPLETED GA NUNBAR WAYA TA
WhatsApp kawai ban da kiran waya
08089965176
07084653262
BINTA UMAR ABBALE

KUSKURE NE MAI GIRMA A DORA MINI LITTAFINA A WATA TASHAR, KO KUMA A KAI FCEBOK KO WATA MANHAJAR BA TARE DA IZININA BA, WANDA YA AIKATA HAKAN NA BAR SHI DA ALLAH MUTUKAR INA DA HAKKI SAI ALLAH YA SAKA MINI.

1
Tunda na ji Tokar na maganar dawowarsa gida nayi saranda! na riga na san kuma shikkenan ni da samun walwala da farinciki har sai ya tafi ban san me yasa ya tsane ni ba, shiyasa nima kwata-kwata bana 'kaunarsa duk da kasancewar mu 'yan uwan juna na jini, amma tsakanin mu, kamar Annabi da kafiri! bama jituwa kuma duk lokacin da za mu had'u wani guri sai mun yi rikici! kamar masu ya'ki! Ya zage ni Ya ci mutuncina watarana ya kai hannu ya dake ni duk da karfin ba daya bane amma ina kokarin ramawa domin ba na iya hakuri da cizo da yakushi nake kwatar kaina na yi ta kuka ina zaginsa, aikuwa ya sha zubar mini da jinin bakina domin har ha'kora biyu ya fitar mini inda Allah yasa na gefe da gefe ne wannan dalilin yasa na ke bala'in jin haushinsa kuma har yanzu ina kan bakana sai na salwantar masa da wani sashi na jikinsa kamar yanda yasa nayi asarar ha'kora na biyu.

Zaune kawai nake ina tufka da warwara! ta rarrafo tsakar gidan ta fito tana surutai kamar koda yaushe bakinta baya shiru ita kad'ai magana take, idan ba haka ba kuma za ka same ta tana taune-taune! koda kuwa babu komai a bakinta.

Kallonta nayi na sha kunu! domin na riga na san irin soyayyar da take tsakaninta dashi, na san yanzu za ta zo mini da son zuciya to ba zan lamunta ba.

Tasa hannu ta shafa yamulallan gashinta da gabad'aya yake dabaibaye da furfura! ya cukurkud'e! kamar audiga kuma iya tsakiyar kan ne kawai ke da gashi amma gefe da gefe da k'eyar duk sumul kamar ba a ta'ba tsirar gashi a gurin ba, amma saboda fitina irin tata duk sati sai ta sanya ni nayi mata tsifa na wanke mata kan sa'an nan nayi mata sabon kitso.

Ta kalle ni da cewa" Ma'kiyin ki zai dawo shine ki ka fito tsakar gida ki ka zauna kina k'unci! wai ke Jamila yaushe za ki daina nunawa d'an uwanki kiyy.....Katse ta nayi ta hanyar daga mata hannu da cewa; Kin ga Tokar don Allah ki rabu da ni da maganar wannan d'andaban! ni ina ruwana da dawowarsa, abinda na sani shine yana shiga harkata zan keta masa rashin mutunci, domin wallahi na daina raga masa."

Ta ja tsaki tare da sa tsinke tana sakace ramuka da kugunan ha'koranta! aikinta kenan sakace! ta ce" To ai ga ki gashi nan ai, tunda kina ganin za ki iya gwada kwanji dashi."

Zuciyata tayi zafi ruwan hawaye ya ciko idona! na ce" Tokar ban san me yasa ki ke fifita Bahago a kaina ba, alhalin duk ke ki ka haifi iyayenmu! a gabanki fa ya zubar mini da hak'ora har biyu, amma baku d'auki mataki ba, babarsa ma har yanzu ba tace komai ba, kodan
mahaifina yana da kawaici da hakuri ya yi muku shiru shiyasa kuke nuna mana wariyar launan fata! Tokar na jima fa da gane ba kya kaunata saboda ba kya son mahaifiyata duk da irin dawainiya da kaunar Babana yake nuna miki."
Ina maganar hawaye na gararanba a saman fuskata! na cigaba da cewa" Idan na yi magana ko na nemi k'watar ha'kkina a ce bani da kunya! bani da tarbiya wai shin ya kuke so na yi da rayuwata ne? Tokar ina k'ara fad'a miki wallahi ku ja masa kunne babu ruwansa da ni, ba zan shiga harkasa ba to nima kada ya shiga tawa, idan ya yi mini akuyanci! nima zan nuna masa zara! domin nima na iya ta'addacin sai dai ayi mutuwar kasko tsakanina dashi!

Hankalinta a kwance take kallona tare da cigaba da tsokane! dadashinta da tsinke dake hannunta alhalin duka ha'koran dake bakinta sun zube bai fi biyar suka rage ba, amma kullum cikin sakace! su take! duk sun yi jajawur! da ti'kar! goro!

Ganin ta tsira mini ido tana kallona yasa na yun'kura domin barin gurin zuciyata kamar ta tsage! saboda 'bacin rai! kafin na kai ga shiga d'akin Kawu Sammani ya shigo gidan dawowarsa kenan daga kasuwa da hannunsa rike da leda mai zane! kawai sai ji nayi ta fashe! da kuka! da cewa" Jamila na gaji da wannan rashin arzikin naki kawai kin tasa ni a gaba kina zazzaga mini rashin mutunci! kina so ki kashe ni to ta Allah ba taki ba ehe! ba zan mutu ba sai kwana na ya 'kare." Ta kai k'arshen maganar tana goge majinar da ta ziraro mata da hannunta.

Ban damu da maganarta ba domin na san za tayi abinda ya fi haka saboda ganin d'anta ya shigo gidan ta ke wannan maganganun shiyasa kullum gidan yake a rikice! domin ita da kanta take haddasa rigimar ta haifi iyayenmu su uku amma ta ware wad'anda take so a cikinsu kuma tana fifita 'ya'yansu ciki kuwa har da Bahago wanda take ji dashi kamar ta d'auke shi ta goya.

Kawu Sammani ya san halin mahaifiyarsa sai kawai ya girgiza kansa ya kalle ni a lokacin da nake tsaye a jikin bango ina jiran hukuncin da zai yanke, Cikin lumana ya ce." Me ki ka yi mata?"
A sanyaye na ce." Ban yi mata komai ba."
Ta ce." Don Ubanki 'karya nayi miki kenan?"

Shiru nai domin bana so maganar ta yi tsayi!
Ya kalleta a lokacin da take kumfar baki da balolo'ko! duk akan Bahago! Ya ce." Tokar ya isa haka kiyi hakuri ki bar maganar haka, in sha Allah idan ya dawo zan zaunar dasu nayi musu sulhu."

Ta ce." Ai ko ka zaunar dasu wannan mai 'kirar samudawan ba zata saurareka ba domin bakar zuciya ce da ita kamar kafira! idan ba mugun hali ba, ina ita ina yin gaba da wanda ke fita ruwa! da iska! ya nemo mata abinda zata ci, amma har tana kiransa da d'andaba! wannan kalamar ta yi mini ciwo mutuk'a." Ta kai k'arshen maganar tana sake goge majinar da take tsiyaya dakalin hancinta, tafi sati biyu tana mura amma ta'ki shan magani! kuma ta'ki daina kwanciya a farin wata. haka 'ya'yanta suke fama da ita domin muguwar rikitacciya ce, to dukkaninsu lallabata suke domin su rabu lafiya.

Shi dai Kawu Sammani bai ce komai ba ya ajiye mata ledar lemo da ayaba wanda ya siyo mata ya nufi 'bangaransa yana mamakin rikici irin na mahaifiyarsu, haka suke fama da ita kullum ta Allah, burinsu dai suga sun rabu lafiya.

Kallonta nayi tana ta sosa hancinta nan ta janyo wani tasono mai had'e da majina ta lakace! a jikin bango! sannan ta janyo ledar lemon ta d'auko d'aya da ayaba ta bani. Girgiza kaina nayi tare da yatsine fuskata! can 'kasan ma'koshi na ce" Tokar ai ni tuntuni nayi sallama da cin abincin hannunki ko wani naga zakiyi wa kyauta mutukar ina gurin sai na hana shi kar'ba! ace mutum kullum hannunsa a cikin hanci! bayan haka kuma idan tayi bayan gida (kashi) sai tace sai tayi tsarki! da kanta gashi ba wani iyawa tayi ba hannunta duk yayi jirwaye! idan nazo zanyi mata tace bata so Allah ya suturta ban isa naga tsaraicinta ba. haka surukanta suke fama da ita da 'kyar take bari suyi mata wanka! amma kafin hakan akan d'auki sati biyu zuwa uku. sai dai kuma tana da k'ok'arin ibadah! lokacin sallah yanayi zata ja jikinta ta dauro alwala! amma bata bambace! gabas ko'ina kallo take, idan anyi mata magana sai tace ai ko'ina da Allah!
Kallona tayi da fadin." Me ki ka ce?" Da sauri na girgiza kaina " Ban ce komai ba kisha kayanki na gode."
Bakinta ta ta'be da fad'in."Kinyi wa kanki mai ba'kar zuciyar tsiy." Ba tare da nace mata komai ba na dauki buta na shiga band'aki domin gabatar da uzurin da yake damuna.

Koda na fito daga band'akin sai na riski Baba Iyami ta kawo mana abinci a cikin langa mai murfi, dama ita ke bamu na dare Baba Hama matar Kawu Sammani ta bamu na rana. da safe kuma babana ke bamu kudin kunu da kosai, ko kuma idan ya fita gurin sana'arsa ya aiko mana da shayi da biredi har da wainar 'kwai! tunda sana'arsa kenan!

"Ke kuwa Iyami wace irin mugunta ce wannan da zaki bamu dambu! da daddare! gashi babu wani wadataccen ganye da mangyad'a! an baki kudin cefane kinyi abinda ki ka saba."
Tana maganar tana jujjuya dambun kamar zata zubar dashi.

Baba Iyami ranta ya 'baci amma sai ta danne! ba tace komai ba ta kama hanyar gurinta. sai ta d'aga muryarta da cewa" D'anjuma yana samun kudi aure zai yi domin dai ke ba matar rufin asiri bace."
Ni kaina sai da maganar ta bani haushi kawai na bar alwalar da nake na tsaya ina kallonta raina a 'bace!

Iyami ta ce." Tokar idan Danjuma ya yi aure sai me? don Allah ki aura masa mata dubu bai dame ni ba, nifa saboda 'ya'ya nake zaune a gidan nan amma da ban ajiye kowa ba wallahi da tuni nasan inda dare ya yi mini me za a yi da irin wannan auran."

Baki idan yasan abinda zai fada bai san abinda za a mayar masa ba. Tokar ta ji zafin maganganun Iyami! kuka take wurjajan! tana tsitstsine mata wai ta tozartata!

Na ce" Baba Iyami don Allah kiyi hakuri ki tafi gurinki kin dai san halinta zaku iya kwana kuna mayar da magana hakan bai dame ta ba, duk ta watsa zuriarta bata sani ba.

Cikin rawar murya ta ce." Jamila gajiya nayi da cin mutunci wallahi! haba ai ba Danjuma ne autan maza ba, zan iya karkad'e yara na tafi gidanmu tunda nima ba daga sama na fad'o ba." Na ce." Ki dai yi hakuri kada ki sake tanka mata"

Ba ta sake magana ba ta nufi sashenta. ni kuma na d'auki butar domin d'aura alwala kamar yanda nayi niyya. sai na ji tana fadin" Jamila yanzu kina jin Iyami na zagi na tana watsa mini zuria shine ki ke bata ha'kuri! dake za a had'a baki a ci mutuncina ko? dama ai na jima ina kokwanto a kanki domin wannan uwar taki sai da ta gama tallace-tallacen ta sannan 'Danlami ya auro ta, in banda masifa da 'kaddara ina fillo da hada jinsi da wani yare irin bayerabe! ai tunda ki kayi haka na tabbatar da cewa; ke din ba jinina bace."
Ban ce mata komai ba har ta 'karaci! ci mini mutunci tayi shiru! nazo na wuce ta na shiga d'aki na d'auko dadduma da hijab na fito, gefe guda na shimfid'a a nutse na gabatar da sallah ta.

2
Cikin sujjadar 'karshe kuka ya k'wace! mini domin tunda na tayar da sallar nake kokarin danne kukan amma hakan bai samu ba, ganin ina ganawa da mahallici na yasa na kasa daurewa kuka nake sosai ina rokon Allah ya magance mini matsalar da nake fuskanta tare kuma da kyakykyawan zabi nagari. cikin raina naji ina sha'awar aure ko don na samu sauki da salama a rayuwata! domin kwata-kwata bana jin dadin zaman gidan, dalilin cin zarafin da Bahago yake mini uwa uba kuma Tokar a duk lokacin da ta bushi iska sai ta ci mini mutunci da ni da mahaifiyata da tuntuni ta fita ta bar mata gidan saboda tsabar tashin hankali da rashin kwanciyar hankali. gyara
Kwanciya nayi kan daddumar ina nazarin rayuwa! tunda na taso har na zama cikakkiyar budurwa babu wani namiji da ya ta'ba furta kalmar so a gare ni, ni dai nafi tunanin abu daya yasa maza suke guduna rashin kyau! domin zahirin gaskiya ni kaina nasan bana daga cikin mata masu kyawun fuska. 'baka ce ni sosai babu wani abu da yake da haske a jikina sai idona da ha'korana sai kuma faratana su kadai ke da haske a jikina, ni din gabjejiya ce sosai doguwa! mai garin jiki kuma ko'ina na jikina a cike yake mussaman kirjina da kuma kasa ina da hips mai fad'in gaske ga d'uwawu! masu tudun tsiya shiyasa bana sanya mayafi idan zan fita sai da hijabi amma duk da hakan kirar jikina a bayyane take.
Kwata-kwata ban d'auko kammanin mahaifina ba, domin dai gaba da bayansu fulani ne usul shiyasa duk suka kasance farare! domin Tokar tsabar haskenta har d'aukar ido take koda ta tsufa din nan haskenta yana nan. abinda na san na d'auko gashi, domin kaina sunkuf! yake da gashi mai yawa ba'ki'kirin ga santsi da kyalli! mahaifiyata tana da karfin jini sosai shiyasa kaf na kwashe kammaninta kamar tayi kaki ta tofar! wannan dalilin yasa Tokar take gwa'ba mini magana a duk lokacin da tayi ra'ayi sai ta ce tana kokwanto a kaina, wannan kalmar na tayar mini da hankali mutuka!
Kiran sunana na ji tana yi nayi saurin goge hawayen fuskata na amsa tare da daga labulan dakin. ta kalle ni da cewa" Yau ba zakiyi mini shimfidar bane ko mulkin ne ya motsa."
Cike da jin haushinta na ce." Mura fa ki ke yi tun dazu ki ke goge majina kuma ba komai ne ya janyo miki hakan ba sai kwanciya a hasken farin wata don Allah kiyi hakuri ki kwanta a daki tunda dai ba a zafi a garin."
"A'a ba zan zauna na kashe kaina ba a wannan sunkurun! ke da bakya jin zafin sai ki shigo dakin ki kwanta ni dai ba zan kwanta a ciki ba.''

Tunda na ji haka sai kawai na tashi naje na janyo katifar na shimfid'a mata a tsakar gidan kamar yanda ta bu'kata! ta rarrafo ta fito tana surutai! maganar Iyami take yi har yanzu abin yana damunta. cikin raina nace'' Duk abinda Iyami tayi miki ke kika jawo.
Hijab nasa a jikina na kama hanyar fita! da saurin gaske ta ce." Ina kuma zakije yanzu?" Ba tare dana kalleta ba na ce" Shayi zanje na kar'bo gurin Baba."
Shiru tayi ta mayar da kanta kan fillo.
Lokacin dana fita unguwar cike da matasa rukuni-rukuni! kowa yana harkokin gabansa! naji dadin hakan sosai don haka da sauri nake tafiya domin isa can k'arshen layi gurin da tiredar mahaifin nawa take.

Zuwa na gurin ke da wuya shima taxi tana sauke shi gabana ya yanke ya fad'i! "Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! itace adduar da nayi. lokacin na dan...


Read / Download YA ZA A YI BOOK 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album