Join Our WhatsApp Group

BARIKI IYAWA Complete Hausa Novel Document by BARIKI IYAWA


BARIKI IYAWA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 53643



BARIKI IYAWA

Reading Time: 4 Hours

Added On: 02, Sep 2023

Author: Hauwa Damari ,Feenart Jafar ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 275.64 kb

File Type: txt

Views: 761+

Download: 261+

Last download: 12 hours ago

Description/Story: BARIKI IYAWA
Complet
Hauwa Damari & feenat ja'afar
Ebook creator: Shuraih Usman
Daga:- http://fb.com/hausaebooks

[9/12, 8:25 PM] ๐Ÿ’๐Ÿ›๐ŸฌSalma๐Ÿฌ๐Ÿ›๐Ÿ’: [6/2, 5:38 PM] Feenat Ja'afar: Feenat Ja'afarSalma๐ŸฌSalma๐Ÿฌ๐Ÿ›๐Ÿ’: [6/2, 5:38 PM] Feenat Ja'afar: Feenat Ja'afar๐Ÿ›๐Ÿ’: [6/2, 5:38 PM] Feenat Ja'afar: Feenat Ja'afar
BARIKI...IYAWA
1_Tafe take cikin tukun ta na masu isa,da
takama,tamkar mai gudun taka kasa,,hasken
solar,kadai ke haskata da walwalin net din jikin
ta..duk wanda yaci karo da ita,,toh koh ya tsaya
kallon ta,, ko kuma ya wuce yana waiwayen
ta,,wata iriya ce ita.. Allah ya bata abu 3...
Kwarjini...
Kyau,dan akwai zubii.
Sannan uwa uba Aji..
Duk ustazan cinka akaf unguwa da kewayen nan
kasan da zaman ta., sanye take cikin Riga da
skirt na wani rantsatsan farin net,da head blue, ta
zuba wata uwar sarka ta Daham kirar Dubai,,ga
wane shegen takalmi mai tsinin tsiya blue,.rike da
karamar jakar ta blue,, sai katon net data rufa
blue a matsayin gyale,,in ka ganta,zaka rantse da
Allah ko wata yar shugaban kasar ce.. Ba yar Haj
Ladi da Malam Abdu ba..."BARIKI"kenan..wanda
take wa kanta kirari da "IYAWA.
kai da ganin ta zaka gani wani take jira,domin
tana kallon agogon hannun ta tana dan
tsuka,,fuskar nan sai sheki take tasha make up
tamkar wacce zata zaben sarauniyar kyau..harara
ta kwada mishi,lokacin da yai parking din motar a
gaban ta,, sanin hali yasa daga nesa ya fara bata
hakuri "Hajiya amini afuwa, wlh go slow na samu,
gashi mai goge motar ne aka kai Matar shi asibiti
kuma ya hana baya nan a bada...tsaki taja kanta

warce mukullin motar ta,," kai kana rasa karyar
kare kanka ne..ji shi a gun,,wlh na kusa sauya
ka...kasan kwa yau ranar nan yadda take a waje
na??ya dukar da kai"Hajjaju ai hakuri..ta bude
pose din ta da bashi dubu1 "kaban waje..tuni ya
kauce ta shiga motar... Tana zama ta duba
mudubin gaban motar, ta Wai waiga cikin
motar,kan ta bude ta dakko air freshener ta
feffesa.." Dan iska,duk ya loda min garadan banxa
a mota tana wari.. Tai tsaki,kan ta daura belt ta
bata key.. Motar ma kamar bata so take Jan
ta..wayan ta ne yai kara..ta dauka,ita kanta
wayan kasan ta manya ce..
"Haba "BARIKI"... wulakancin da zaki min
kenan??8 da kwata fa yanxun... Da sauri ta katse
ta" ee eehm...yi min a hankali.. Gani nan bisa
hanya..tace"Dan ke muka maida abun nan fa
8,kowa yazo amma kujerar ki empty..sannan har
yanxun.. Kit ta kashe wayan"jaraba..mutum sai
mita ya tsohuwa.. Ta sanya CD na wakar Ashique
ta taka totur mota ta kara gudu... 15 mint ya
kaita harabar hotel din da zasuyi program din,,tai
parking kan ta fara takun nata na isa..waje ya
hargitse..tamkar wanda ake gidan bikin mata,don
baa gama zama ba,,da Zee ta fara karo da
Royal... Tuni suka hau mata kirarin da ita kadai
suke wa a duk qawaye.. "Yeee...kaga manya a
Baku naku daban... Kaga mai sai maza caroling
mai sa mata su watse...kaga farar
mace..Alkyabba ta mata..wai sukari bakai farin
banza ba..tuni kanta ya fara fashe wa..dan mudin
suka gamu da da qawayen ta yan qarya.. Mai
kirari ta cigaba..ita kwa sai wani juyi take tana
yatsina halamar mai tai lacking.."Dawusu ce
ke..ta kowa dole a kalle ki..in dake a waje dukkan
mata su kauce..Allah ja mana ran suka Sara
mata tare da cewa"BARIKI... Tuni tai wani fari
tare da rausayar da kai ta na kada keys..kan a
hankali ta furta"IYAWA ba..ta barsu nan tai chan
ciki ta zauna kujerar kusa da amarya..suka bita
da kallo...tana kula da Yadda mutum 2 ke Binta
da harara .. amarya da abokin ango..ta kalle shi
ta tabe baki kan ta zauna..
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[12/22, 4:59 PM] Feenat Ja'afar
BARIKI...IYAWA
2_Tamkar ita ake jira kuwa aka fara sanar da
kowa ya zauna a mazaunin shi..
Suka danyi bayanan su..tana ta kula da har
yanxun Harar da Hafeez yake mata.. Ta kada
kai.. Lalle ya kamata tai gaggawar saita mutumin
nan.. Tunda take babu wanda ya taba kokarin
shiga hancin ta sai Hafeez,da kudundune ma ya
shiga shi..tai kwafa dai dai lokacin da aka tashi
amarya da ango zasu yanka cake, chan baya yai
yadda shi kadai ne karshe,, a hankali itama ta
tako,tare da daukar kwalin 5alive tai wajen da
yake..da wannan takun nata, yana ganin ta ya
kara hade rai,, tai murmushin mugun ta, a dai dai
shi ta tsaya kamar zata gogi jikin shi,, yai
tsaki,Yarinyar nan ba karamin tsanar halin ta yai

ba..tunda ya gano ita wacece... Yasan duk macen
kwarai bazata so a kirata da sunan BARIKI
ba..yai tsaki tare da kara matsawa.. Bude kwalin
tai,ta dai daita shi dai dai kafadar shi da gan gan
ta kar kata shi a kafadar, tuni ya fara bulbula
mishi cikin jiki..take yaja baya dan ya tsorata, ga
lemon da sanyi..ya kalle ta ya kalli taron, ba
wanda ke kallon su, an dukufa kallon yankan
cake.. Baisan lokacin da ya sau mata mari ba.,ji
kake"Tasssss,hall ya dauka..abun ka da Babban
waje,tuni ya dauka,,zata dafe kunci da sauri lbrn
wata ya fado mata.. Ana juyo wa ta nuna shi da
hannu.."Wallahi in ka kara sai na maka Marin da
yafi haka... Taja tsaki kan ta juya tai waje tana
dagowa amarya hannu..da mamaki kowa yake
binsu,musamman ango da amarya.. Shi kwa
Hafeez dan tsabar takaici kasa ko motsi yai,..lalle
ya yarda, yarinyar nan "BARIKIN ce da gaske.. Da
sauri yai waje..motar ta yaga ta fita..da sauri ya
shiga tashi,,Ita kwa tana fita data shiga mota ta
sau kuka..tunda take ba mahalukin da ya taba
Marin ta sai Hafeez,, duk da ta maida mishi Marin
kanshi,,kuka take tamkar ranta zai fice..ita rasa
mey zatai ta huce ne yasa tai mai haka... Waje
ta samu tai parking a gefen hotel din ta daura
kanta a stirring motar ta cigaba da kuka..mai ta
tsare wa Hafeez a rayuwa ne?? Jiyan nan ya
gama dizgata gaban mutane..sannan yau ya
sakar mata mari a bainar jama a..
Jin an tsaya da mota a kanta yasa ta dago..shine
kwa,da sauri ta fara kokarin tada mota taki tashi,,
ganin yana kokarin bude mata kofa da sauri ta
danna lock tana kallon shi,, ta tsorata matuka,
tasan yau kam ya ritsata sai wata ba ita ba..
Glass din ya fara buga mata..tuni ta gigice,ganin
yana kokarin fasawa..sai kokarin tada motar
take,.Allah yaso ta ta tashi,,.
Kallon motar yake da tsabar takaici..yau kam da
ya far mata sai taga karyar BARIKI..
Ango da Amarya ne suka fito..suma a mota,suka
karaso wajen,," Mey zakai Hafeez?Yasha gaban
shi sai huci yake yana kallon motar harta
kule..."Dan Allah yaushe ne zaku hadu Baku bar
abin fada a waje ba?yanxu fa shikenan kun bata
mana taro,,amaryar ta kallo Hafeez "kayi hakuri
Hafeez, akan ido na komai ya wakana,da sauri
suka kallo ta,tace" BARIKI fa ta wuce inda kake
tsammanin ta wlh Hafeez,, kuma kai yadda ka
dauke ta wlh ba haka take ba,,da sauri Hafeez ya
tsayar su"kina nufin kinga lokacin da na mare ta
ta dawo dashi kaina? Ta kada kai "tun zuwan ta
wajen ka nake hankalce daku.. "Itama fa ramawa
tayi,, in anbi ta Allah abinda kai mata jiya yafi
haka.. Yai tsaki," kuban waje na wuce..kauce
mishi sukai,,suka bishi da kallo har Shima motar
shi ta kule.
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[12/22, 5:00 PM] Feenat Ja'afar
BARIKI...IYAWA
3_Tana zuwa gida Maman su na waje suna fira
da Abban su a kan taburma,,da sauri ta wuce

daki ko magana bata musu ba tana hawaye.. Baki
sake suka bita da kallo..dan ko su da suke iyayen
ta rabon da suga hawayen ta tun tana
karama..tashi sukai suka bita..lalle yau kam ba
kanta..duk abinda yasa Sa'adatu toh mai girma
ne..
A gefen gadon ta suka zauna.,in kaga dakin,
tamkar irin na yar gatan nan..yasha kayan
alatu,duk da rufin asiri ne dasu dai dai
gwargwado.. "Sa'a lfy?mey ya same ki haka?ta
kallo su.." Ba komai,,Abba mayi maganar
gobe..suka kalli juna.."Toh toh shikenan.. Sai da
safen,,ta daga musu kai,,kan suka fita..nan ta
cigaba da kwance wa tana daura wa.
Asalin lbrn..Sa'adatu yan asalin jahar Yobe ne,a
karamar hukumar Nguru,, baban ta malamin
makaranta ne na primary,,yana da rufin asiri dai
dai gwargwado..duk da bai da ko gidan kansa a
garin guru,,yana da mata 2,haj Ladi da
Mairamu,,yaran shi 2 rak,Fadeela sai
Sa'adatu..tun suna yara mairamu tasa maman su
a gaba da kissa da kisisina sai da ta fidda
Maman su gidan..dake mace ce ita mai
hakuri,tunda ta kyalla taga ita haihuwa..ga
amaryar ta harda yara 2,,tai mugun halin taga
baci,sai ta koma kissa da BARIKI..inta fahimci
mai gidan zai shigo saita fito tsakar gida ta fara
kukan kissa,,"Nima ai Allah bai manta dani ba,da
har zaki min gurin haihuwa Ladi,,koda yake laifin
malam ne.. Tuni zai karaso yana "Subhanallah,,
mairamu mai ne?mey ladin ta miki?sai ta cigaba
da kukan ta,, Wai na aiki Sa'adatu yarinyar nan
tace bazata ba,daga magana Ladi ta hau zagina,,
dan ban Haifa kaza da kaza..tuni ya fara huci,,ya
ban kada dakin Ladi.." Ke na fahimci kin fara
sauya hali tun ba yau ba,, infa naga dama saina
Debi ya'yan duka na bata,, a wannan lokacin
Maman su Sa'adatu takan ji haushi,ganin gashi
an fada mishi abu.,amma bai bincike ba ya hauta
da masifa,,"toh ka bata su, sai kwa ya sake
tunxuro wa..dan ita fa zaman gidan har ya
ishe,lokacin bata fi yar shekara 22 ba,,amma ba
bakin cikin da bata dauka na mairamu in ba idon
mai gidan, sannan mairamu tasan ta kan Miji,shi
yasa a kullum tafi Ladi Power a gun mai gidan,,ga
tsabar iya barikanci,,agaban kowa sai tace zata
rungumi malam.,ita ta matse ta zauna a tsakar
gida bai zame mata komai ba,,duk abunda ya
dace ladi tayi ita da take amarya kuma
karama,amma mairamu ta amshe,kuma ita sam
bai damun ta bare tai koyi da ita..akwai lokacin
da malam ya kawo kifi,,yana rawar jiki yau girkin
mairamu,,gaba daya tai farfesu ta watso musu
kayuka a kwano..haka take ta hakuri da ladi,dan
datai magana,malam zaice ta fiya kawo kara,,shi
wlh ya gaji,ita kullum cikin korafi take??inkwa
ranar yan muguntar suna kanta haka zata kama
su Yaran tai ta nadar su.,uffan ladi bazata ce
ba..sai dai in ta gama zakaji Sa'a na zuba mata
Allah ya isa.. Sa'adatu ba kyal bace,,shekarar
ta3,amma Allah ya bata bakar wayo,,ga baki na
fitsara,,tuni ta fara karantar kishiyar uwar tata
tun kan ta tafasa.. Ana haka ranar aikin mairamu
ne,,sai tace wa fadeela taje ta kawo kwano a

zuba musu,,fadeela tana bala'in tsoron mairamu
kamar mey,lokacin shekarar ta 5.,ta zuba musu
ta kai daki..chan saiga Ladi ta fito da abinci tazo
kan mairamu..
A gaskiya mairamu kina jin tsoron Allah,, yanxu
abincin nan ne zai ishe ni,har na bawa yara
suci??kullum kina zuba haka bana magana, indai
yara sun koshi sai dai ranar Girki na,,wane irin
mugun ta ne wannan? Tuni dama da gaiya
tayi,,jiya ta samo Sa'a,. Kiris take jira Ladi ta
tanka,,"Haka naga damar zuba muku,,sai dai kar
kici..tuni ta tunxuro.. Ba tasan sanda ta watsa
mata abincin a jiki ba.. Yai dai dai da shigo war
malam..tana ganin haka ta sau kuka.. "Nikam
naga ta kaina a gidan nan,,Ladi ni zaki zubawa
abinci a jiki daga abin kirki?? Bayan kin gama
zage ni ban kula ki ba,,yau dole na bar gidan nan
dan naga haka kike nema..tuni tai hanyar daki
tana kuka,ta saci kallon malam din da yai kan
Ladi..mari ya kifa mata,sai a idon su
Sa'adatu,,tana kallo tai wa Maman tasu gwalo
sannan ta cigaba da kukan karya..malam yace"
Ashe rashin mutuncin naki yakai haka Ladi?tuni
ta fara hawaye rike da kunci.. Toh kije gidan Ku
saina neme ki..ta kada kai.,kan ta kallo
mairamu..."In Allah ya yarda sharrin ki sai ya
sauka a kanki..ta juyo kan malam din,,Ka dinga
tsananta bincike a lamarin ka,,sannan ka zamo
mai adalci a...hannu ya daga zai zuba mata wani
mari yaran suka kan kame shi,,kuka suke suna
bashi hakuri.. Duk tsiya,yana ji da yaran shi,
musamman Sa'a.. Ya sauke hannu,,tuni taje ta
fara hada kaya tana kuka..
Tunda ta bar gidan take gasa yaran,,wanka da
ruwan sanyi,duka,,barin Sa'a, dan ta bala'in
tsanar yarinyar.. Tana jibgar ta tana mata Allah
ya isa..kuma in ta tashi saita fanshe., inta dai
daici ta daura abinci taje ta zuba kasa ta
gudu..ko ta zuba ruwa a murhun,yadda har
baban su ya dawo bata gama Girki ba.. Nan zai
hau fada..tuni Sa'a zata hau dariyar keta.
Zancen Ladi kuwa,sai da yai wata 3 tukun ya Wai
waye ta,,fir tace bazata dawo ba, ita saki take
so..a lokacin mairamu ke gaban shi, ba musu ya
mata 1,, baa jima ba tai auren ta.
By
FeenaJa'afar
&
Hauwa Damary
[6/2, 5:48 PM] Feenat Ja'afar: ยฉ Feenat Ja'afar.
BARIKI...IYAWA
4_Yau shekara 5 da rabuwar Ladi da
malam..Iyanxu babu wata kissar da Sa'adatu
bata koya ba wajen Matar uban ta.. Dan tsaf ta
zame mata tamkar makaranta.. Sharrin yau
daban na gobe daban..ga Baban yana masifar son
Sa'ar..
Yau da yamma ta zaunar da fadeela.. "Yau komai
nace kicewa Baba haka ne,, ta harare ta." Saura
ki tsaya tsoron ta..bulala ta dakko..tace ta da kar
kare Iya karfin ta ta shauda mata a singalalin
hannun ta.. Ido fadeela ta zaro,, "kina da kai
kuwa..Sa'a tai tsaki.." Dallah ni ki daken
nace,,fadeelan ta kada kai.,kan tai baya,,ta Dakar

kare ta zula mata bulala,,da sauri ta hular
ta,,harda hawayen ta Sa'an amma ta kara miko
mata, ta daga kafar ta,, saura kafa,,tace"ke ni
bazan Iya ba,, ta juyo da harara"ni nace kimin
dallah.. A haka banxa ma wata katuwar duka na
take, bare yau da zan ci uwar ta nima..tuni ta
kara zaro ido "Sa'a wlh ba ruwana..haka kurin
bazaki jamin masifa ba,,ta juyo kan ta kalli
hannun ta, tuni har ya fara tashi.." Kar ki Iya
din.,amma wlh Allah komai nace ba ruwan ki da
karya tani, ke ko kishin uwar ki bakya yi..nan
kishiyoyi sun hana ta zaman gidan aure..auren
mama 2 harda na baba 3..kina nufin zuba ido
zanyi wasu wanda basu isa komai ba suna maida
ta bazawara??ta girgiza kai "wlh Allah zaman
mairo a satin nan zai kare a gidan nan..kin ganni
nan..shekara ta 7 ina Neman ta takwas.. Na koyi
halin mairamu kaf harda kari..duk wata BARIKI na
koya a wajen ta.. Kede naki ido..ta dau bulalar ta
leka waje,,lokacin mairamu tana daki,,ta ajiye
bulalar a kofar dakin nata kan tai waje..chan
kwanar su ta nufa.. Tasan duk inda baban su
yake yanxu yana hanya..dan su yan primary tun
dazu suka dawo..shi kuma ya koma secondary..
Ta labe tana leken shi, in ka ganta taci uwar
damara da hijab din islamiyar ta..ko minti 5 batai
da tsayuwa ba ta hango shi yana ta howa shida
malam kallah,, da gudu tai gida..dai dai mairamu
ta fito zata duba abincin ta.. Ta dan leka.tana
kallo lokacin da take dokawa dakin su harara..tai
kwafa,da gudu ta shigo da gan gan ta mangaje
ta,sai kwa tai taga taga ta dafe rumfar da take
Girki a gun,,ta Dakar kare ta mako ashar,,ita kwa
ta kama kugu tana murguda baki.. Dube ta fara
sai kwa ta dau bulalar target din Sa'a,, tana
ganin haka tai baya.." Wlh nifa ba jakar uban ki
bace da zaki ta nadar mu kullum.. Tuni ta kara
tunxuro ta"ni kika zaga saude?lalle yau zaki yaba
wa aya zakin ta., tai kanta"shegu gadon tsiya..tai
charaf"kece dai gadon tsiya wlh,, Tsohuwar yar
BARIKI.. Ni wlh na fiki Iya ta..da gudu fadeela ta
fito.. Ganin yadda ake danbe da Sa'a da
mairamu,, ta rike bulalar tamau ita kwa kira take
ta sake,,tana jin kilin kilin din besfar Baban ta sau
wani uban ihu..."Wayyo Allah.. Wayyo Baba kazo
ka taimake ni... Na shiga uku zata kashe ni.. Tuni
ta hau burburwa a gaban Mairo..ita kwa da
tsabar mamaki ta sau baki tana kallon ta..
Da gudu ya shigo.,ganin katuwar bulalar dake
hannun mairamu yasa da sauri yai kan
Sa'a.,"Badai da bulalar nan ta dake ki ba..tuni ta
kan kame shi tana razgar kuka"Baba ta kusa awa
1 tana duka na da ita.,kawai dan nace yunwa
nake ji,, Wai ta fara zagi na,fadi take Wai,dama
da bin malamai ta kori uwar mu..mu kuma da
duka zata kashe mu.. Da hanxari ya kallo
mairamu.,wacce ta yar da bulalar ta daura hannu
a ka,,ta yi mata gwalo tana dariya, da taga baban
zai kallo ta sai ta hau matso hawaye...a fusace
ya tashi yayo kanta., "wlh karya kike,,yanxu
dama in bana nan haka kike cimin zalin ya'ya??
Tuni ya kwada mata mari,,kira take wlh karya
take mata..yace" wannan yarinyar har tasan wani
karya,ai ganau ne ni ba jiyau ba..saboda haka

yau zaki dan Dana kudar ki..ganin ya juya zai
dakko bulala da gudu tai dakin ta ta rufo da
sakata tana"wlh Baja isa tsawan zaman mu yau
kace zaka daken ba...ke kuma inna fito wlh saina
ci uwar ki a gidan nan..gadon jaraba..tana kukan
tace"mudai ba gadon jaraba bane ehe.. Baban ya
juyo kanta,, "yi hakuri uwata..dama haka take
muku?ta hararo fadeela,,...


Read / Download BARIKI IYAWA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album