Join Our WhatsApp Group

ASHE ZAMUGA JUNA Complete Hausa Novel Document by ASHE ZAMUGA JUNA


ASHE ZAMUGA JUNA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 99983



ASHE ZAMUGA JUNA

Reading Time: 8 Hours

Added On: 20, Feb 2024

Author: Mrs Isham ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 09024503194

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 519.14 kb

File Type: txt

Views: 573+

Download: 675+

Last download: 7 hours ago

Description/Story:
🌹🌹*ASHE ZAMUGA JUNA*🌹🌹




*_ story $ written _*

By

* _ MRS 🌹 ISHAM 🌹_*



*The writer of*
*NIDA PATIENT DINA*

~And now~
*🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*




*Assalamualaikum warahmatullahi wabarakatuhum masoyana, masoyan NIDA PATIENT DINA Allah yabani ikon sake rubuto sabon littafina , ya Allah ina rokonka yanda kabani damar farawa lafiya kabani damar gamawa da lafiya*


*Ina fatan kamar yanda kuka bani hadin kai a NIDA PATIENT DINA fatan zaku bani hadin kai a wannan sabon book din domin comments dinku shine babban karfin guiwa na , Allah yabar zumunci ,inayinku over 😘*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



____~THE BEGINNING~_____



Page__01

BORNO MAIDUGURI.

*Damboa road*


Babban anguwa ne acikin Maiduguri inda yatara manyan gidajen hamshaƙan masu kuɗi da kuma yan siyasa, daga kanuri,shuwa,da kuma hausa fulani , da turawa , duk suna rayuwarsu acikin anguwar, kasancewar babbar anguwa ne yasa yake da manyan gate din rufewa ga kuma masu gadi da jami'an tsaro tundaga farkon anguwar har izuwa karshe saboda tsaro banda tsoro ba, wani hadadden gidane mai matukar girman gaske wanda kaff cikin anguwar nan babu gidan da yakaishi kyau da girma hade da tsaruwa tundaga mansion din ma abin kallo balle ace mutum ya shiga cikin gidan ,awajen gidan akwai manya_manyan sojoji dakuma polisawa suna tsaron gidan da ko a kasar waje se shahararrun masu kuɗi ne da masu muƙami zasu iya mallakar gidan nan , abakin gate din akwai katon sign bod na karfe an rubuta *BISHARA's FAMILY* duk wanda yaji wannan sunan to yasan sunan shuwa arab ne

______acikin bishara's house kuwa kyawawan yara ne mata suna wasa,gabaki dayansu sunada matukar kyau kuma suna shigen kama da junansu haka yasake tabbatarwa da duk yan ahali dayane, wasan boji_boji sukeyi yara matan du ka bazasu wuce shekara biyar zuwa shidda ba , se ƴayyun su maza da suke yan matasa manyan cikinsu sukuma suna suna buga table tennis sauran kuma wa'yanda suka girmesu suna can gefe suna zaune suna kallonsu suna wasa, wasa sukeyi a babban wajan spot dake gidan sauran kuma wa'yanda suka ɗarasu girma kuma suna zaune agefe jikinsu sanye da jessi alamun ball suka gama suna zaune suna kallon yan kannen nasu suna wasa.

_____ Abbas ne ya kai kallonshi bakin kofar wajan spot din tsaye yaganta tana kallonsu hannunta rike da teddy pink color, fuskanta ashagwabe se karewa yan uwanta kallo take kamar akwai wanda take nema , farace sol skin dinta har wani glowing yakeyi tsabar hutu kanta nadauke da yalwataccen gashi baki wuluƙ an mata kitso kwalli daya se shining yakeyi ga kwantaccen sajen dake kwance agaban goshinta ya kwanta luf_luf , fuskanta na dauke da manyan idanu farare sol cikinsu kuwa tabb yake da ruwan hawaye amma fa ba hawaye bane se wanda yalura dakyau zegane hakan irinsu ne ake ce musu masu oily eyes, hancinta dogo bakinta dan karami pink dashi tanada dimple aduka kumatun nata jikinta nasanye da riga da ya tsaya mata adede guiwanta ƙafarta sanye da takalmi me matukar kyau yarinya ce karama yar shekara shidda, kyakkyawa ce kyanta yawuce misali , tana tsaye abakin wajan se wur_wurga manyan oily eyes dinta takeyi ko zata ganshi amma kaff wajan babu shi babu alamar shi.

Yar murmushi Abbas yayi yataba sauran yan uwanshi yana musu alama da ido suma maida kallonsu kanta sukayi wani kyakkyawan saurayine acikinsu wanda kansu daya da Abbas din kuma suna mugun kama ya ce " Abbas amma kai aganinka wa take nema haka" Abbas ya ce " Ahmed wa kuwa take nema da yawuce TAJUDDIN, inkaga ASRAH ta sake tana wasa da yan uwanta to TAJUDDIN yana wajen " dariya sukayi Ahmed ya ce" gaskiya ASRAH akwai rigima, ga shi wai yar karama da ita ta iya rashin kunya da neman tsokana ko dayake ba'a Nigeria aka haifeta ba kuma tunda aka haifetan basu dawo Nigeria ba se sati biyu nan da suka wuce duk yarinyar an sangartata zamansu uncle hameed da anty amarya a California yanzu yafi shekara bakwai fa tun kafin a samu cikinta " " ni kuma kunsan meyake bani mamaki kuwa ? Wallahi yanda TAJUDDIN yake matukar santa ne abin yake ban mamaki yaron da mugun miskilanci yamishi ƙatutu dashi da kurma basu da maraba ga uban zafin zuciya da girman kai tun yana karami dashi duka_duka fa TAJUDDIN baze wuce shekara sha bakwai ba amma baya kallon kowa da gashi ko mu nan bamu isheshi kallo ba balle sauran yan uwanshi mata amma duk inda ka ji muryan Taj yana magana tofa shida Asrah ne duk gidan nan ita kadai yakeyiwa magana na tsawon wasu mintuna tsabar son da yake mata " cewar Haris da shima duk sa'an su Abbas da Ahmad din ne , cire rigar jessi jikinshi Abbas yayi yana cewa " karkayi mamaki Haris karku manta fa tunda anty amarya tasamu cikin Asrah duk sanda ammi ko hajjatiye inzasu je California tare suke zuwa, Taj yana matukar son cikin anty amarya yana kula da ita, kullum maganar shi daya shine inde mace ta haifa shize aureta, shisa duk zafin kanshi da miskilanci tofa bayayiwa Asrah haka itama duk rashin kunyarta batayi mishi, Allah de yakaimu lokacin da zasuyi aure bakaramin murna zanyi ba " haka suka dinga hira kafin Haris yatashi yaje gaban Asrah ya ce" Asrah wakike nema kuma gacan su Umaisha suna wasa bakije kunyi tare ba " cuno baƙi tayi da muryanta siriri wanda Hausa be ishesa ba ta ce" ya Haris ina tajujuna? i couldn't find him " dariya Haris yasa jin yanda take kiran sunan Tajuddin din wai tajuju tsagaitawa yayi ya ce " kishigo ki zauna tajujun ki na zuwa maybe yana wani abu ne " maƙe kafada tayi ta ce " bazaje din ba se yazo tukun " lallaminta yayi yasamu ta biyoshi suka shiga ciki zama tayi akujeran kusa dasu kafin ta kalli Abbas ta ce " yaya did you perhaps saw my tajuju?" yana kunshe dariyar da yakeson kuɓuce mishi ya ce" noo i didn't " tundaga nan fuskanta yasake komawa irin na tausayi.
Sauran matan dake wasan boji_boji suna ganinta suka rugo da gudu wajan da take zaune su biyar suna haki dayar ta ce" Asrah let's go and play " " no Umaisha am not going anywhere until tajuju come " cewar Asrah, rike hannunta Iklas tayi ta ce" zezo ai to muje muyi wasa Please Asrah " dukkansu haka suka dinga roƙonta shuru Asrah tayi musu tana rungume da teddy dinta ,sude su Abbas zuba musu ido sukayi dan sunsan Asrah akwai taurin kai inta nace akan abu tofa zeyi wahala tacanza.

Saghar dake nesa dasu suna buga table tennis shida su salim da Sahil ya hangi abinda yake faruwa tsuke fuska yayi shidama rashin kunyar da Asrah takeyi agidan ya isheshi har wani tsayawa sukayi suna roƙonta suzo suyi wasa amma tana ja musu rai karasowa yayi wajen nasu afusace daka mata tsawa yayi ya ce " nikam Asrah ke wani irin shegen taurin kai ne dake har sister's dinki zasu zo suna roƙonki amma kinƙi tashi kuje kuyi wasa ! get up idiot tashi ki wuce kije kuyi wasa " yafada yana rike hannunta Abbas ne ya ce " haba saghar kadena mata shouting kabita a hankali yarinya ce fa" ko gama rufe baƙi Abbas beyi ba sukaji Asrah ta bude baki ta fashe da wani gigitaccen kuka kamar wacce akayiwa mugun duka duk tsayawa sukayi suna kallonta cike da mamaki tsabar yanda take kuka har jikinta rawa yakeyi , da karfi tana kuka tana " my tajuju kazo suna dukana " kama baƙi sukayi jin sharrin datayi musu wanda yamata tsawa daban kuma bama dukanta yayi ba he just yelled at her.

Daga bayansu sukaji daddadar muryanshi yana fadin " come here my Asrah waye ya taɓamunke?" duk juyawa sukayi suna kallonshi , dan matashin saurayi kyakyawa ajin farko fuskanshi a turnuke daga gani ranshi amatukar ɓace yake yana sanye da wandon sojaji three quarter se baƙar riga kanshi na sanye da facing cap . Asrah najin muryanshi taraba ta tsakiyarsu taje da gudu ta rungumeshi tana sheshekar kuka. gaba dayansu seda sukasha jinin jikinsu banda Abbas da Ahmad da Haris ,amma daga kan su Umaisha,Iklas, zoya ,parsa,rameesa, saghar,salim,Sahil,sudais , kallonsu yayi da rikitattun idanunshi murya adaƙile yana shafa bayan ya ce " Asrah waya taɓaki acikinsu " yayi maganar yana dagota ajikinshi kallonsu itama tayi kafin tafara nunasu da ɗan yatsanta ta ce " all of them dukansu sun zageni kuma sun dakeni" a kausashe ya ce " na rantse da Allah duk wanda ya sake sa hannunshi ajikinta da sunan duka kokuma yi mata tsawa ko faɗa ze hadu da fushi na " yana gama fadin haka yadauketa yadaurata akan wuyanshi suka bar wajan spot din, sude da kallon mamaki kawai sukabi bayansu saghar kamar zeyi kuka ya ce " Allah sena kama Asrah nayi mata ɗan banzan duka sede Tajuddin ya kasheni " ya karishe maganar hawaye Tabb a idonshi, girgiza kai Haris yayi ya ce" karufawa kanka asiri dan kasan halin Taj zakajane yamaka duka inde akan Asrah ne , sede kuyita hakuri da ita harta saba da halin nan tunda kunga ai ba anan ta tashi ba kuma karamace " kwafa saghar yayi yabar wajan sudais yabi bayanshi duk watsewa sukayi suka shiga cikin mansion din.

Yana dauke da ita akan wuyanshi tanata dariya suka shiga cikin tamtsamemen mansion ne na gani na faɗa komai na ciki anzuba dukiya kamar ba'a so , tundaga kan kayan furniture har izuwa kayan alatun dasuke falon duk yan kasar waje ne saboda irin kyaun su da tsarin su kai daga gani ma base an fada ba kasan cewa wannan babban gidan alfarma ne ganin yanda dukiya ke kuka , ga manyan kujeru masu numfashi da ɗaukan hankali. Cikin ƙatuwar haɗeɗɗiyar falon na dauke da stairs matakalar bene kusan fiye da goma inda duk wanda kahau ze sada ka da part din wani ,shi kanshi matakalar benen abin kallo ne saboda yanayin design dinshi, in har nace zan tsaya fada muku irin kyan da gidan yake dashi tofa ko one page baze dauka ba kude ku ƙiyasta kawai .

Kamar bega kowa a falon ba yanufi part dinshi shida Asrah duk maida kallonsu sukayi kansu.

Uncle Hameed ne ya ce " Taj ba magana ne ?" Kallonsu Taj yayi batare da yace komai ba yahaura upstairs yanufi part dishi kamar bega Abbu da Abbie da kuma uncle Hameed dasuke zaune afalon suna mishi magana ba.

Girgiza kai Abbie yayi ya ce " Hameed bansan yazanyi da Tajuddin ba gabaki daya shi fa rayuwarshi a murde yake yaro tun be tafasa ba haryafara konewa ? ni agaskiya nafara canza shawara akan samo mishi addimission a U.S military academy at west ,saboda Tajuddin be zama soja bama ya muka ƙare dashi balle kuma idan yazama sojan ƙasa da ƙasa bana tunanin wannan shawara ce me kyau " Abbie ya ya karishe maganarsa da damuwa akan fuskarshi.

Abbu da uncle Hameed sukansu lamarin Tajuddin na damunsu domin Taj mutum ne da inzaku zauna tsawon shekara ɗari tofa seyayi ra'ayin maka magana kafin yayi ,ba koda yaushe bane yake magana ba.

Abbu ya fuskanci ya'yan nashi wato Abbie ya ce " ya Mubarak ni aganina canza shawara akan makarantar dazeje bashida fa'ida tunda ka san wannan shine babban burinshi yanason yazama soja wannan shine mafarkinshi kuma dukkanmu munsani , to ruguza mishi mafarkinshi kuma dede yake da ruguza mishi rayuwarshi , muda muke neman hanyar da zamu dinga faranta mishi ko Allah zesa yadawo mutum kamar kowa yadinga walwala wallahi tun marigayi baba Allah yajikanshi ,nadade banga mutum irin Tajuddin ba amma gado yayi agun baba"



Yawwa muddin kunaso muci gaba da tafiya yanda Yakamata shine nadinga ganin comments dinku hakan ne ze tabbatar min da kuna biye dani 😒😒😒😒.
🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹




*_ story & written_*

By


*_MRS 🌹 ISHAM 🌹_*
(Yar lelen Jarumai)

*The writer of ✍️*
*NIDA PATIENT DINA*


~And now~
*🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*




🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️





Page 02



_______ " abinda kafada hakane kam ya Ismail saboda hanashi yin abinda yakeso zesa murɗeɗen halinshi sake ninkuwa fiye dana da,kaga garin neman gira kuma an rasa ido "cewar uncle Hameed jinjina kai Abbie ya yi dan ya gamsu da maganan ƙannen nashi , amma shi a har kullum burinshi yaga ɗan shi yadawo kamar kowa , but lamarin Taj kullum gaba_gaba yakeyi du ka nawa yake amma tun bekai haka ba shi kadai yatara zafin zuciya, miskilanci,rashin damuwa da damuwar kowa, karfi ga kuma tsastsauran ra'ayi da murdeden hali , kamar ba'a gidan yake rayuwa ba. Haka suka dinga tattaunawa akan Taj da bemasan sunayi ba yana can a part dinshi shida Asrah suna painting room domin kuwa Tajuddin da Asrah Allah ya yi musu baiwar drawing wato (zane) duk sanda suka shigo painting room shida Asrah tofa kafin su fita Asrah seta zana hotonshi fiye da goma.
__________ yanzu ma kamar yanda ta saba tana zaune agaban painting board hannunta rike da pencil ta tsurawa Tajuddin ido tana kallonshi tana zana shi , shikuwa yana drawing din ɗawisu duk kallonshi da takeyi yana sane da ita kuma yasan shi take zana wa ɗan inde yashigo da ita nan tofa shine abin zanawarta setayi fiye da goma. Gama zanen ta yi, ta dauko papper da ta yi ta nufeshi tace " tajujuna kalla kagani yayi kyau?" sa hannu yayi yakarba yaci karo da kyakkyawar fuskarshi ga facing cap din dake kanshi ya ce " ehhh not bad yayi kyau" murna tafara yi harda tsalle leƙa kanta tayi tana son ganin meyake zanawa , ganin ta zuro kanta ne yasa ya juyar da kanshi gefe da kuma paint board din yaci gaba da zanenshi zama tayi akan kujera tana kallon nata drawing din,bayan wasu mintuna yazaro papper batare da yace mata komai ba ya miƙa mata, sa hannu tayi ta karba ta kalli zanen dakyau ita ce ya zana tana zaune acikin garden ga ɗawisu zagaye...


Read / Download ASHE ZAMUGA JUNA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album