Join Our WhatsApp Group

JALALA Complete Hausa Novel Document by JALALA


JALALA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 77544



JALALA

Reading Time: 6 Hours

Added On: 18, Sep 2023

Author: Rashidat Usman ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION

Author Phone : 08147537180

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 440.52 kb

File Type: txt

Views: 620+

Download: 464+

Last download: 6 days ago

Description/Story: [5/10, 8:41 PM] Oum Nasmah 🌹: 💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


✨ *_JALALA_* ✨


💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫




*_New story from Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)_*



*_The writer of_*


-Sauyin Rayuwa.
-Nasmah ko Nasirah.
-Sara da Sassaqa.
-Indo a Birni.
-So Bai San Jini Ba.
-Ruɗanin Zuciya Biyu.
-Akan Ƴar Uwata.
-Doctor Hassan.
-Gelle Ɓingel.
-Ƙauyenmu.
-Hatsabibiya Saude.
-Aminaina ko Ita?.
-Ƙullalliya.





*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association


*____________________________________*



*_ALHAMDULILLAH TSARKI YA TABBATA GA UBANGIJIN DA YA HALICCI SAMMAI DA ƘASSAI, YA HALICCI MUTUM DA ALJAN YA YI WUTA DA ALJANNA, SARKI MABUWAYI WANDA BASHI DA KISHIYA BAI HAIFA BA BA'A HAIFESA BA, YANDA NA FARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA INA ROƘON UBANGIJI DA YASA NA GAMA LAFIYA_*



*_Special tnx to my people, masoya masu ƙaunata a ko yaushe yauma dai gani da sabon salo mai tafiya da zamani, labarin daya ƙunshi abubuwan ban al'ajabi da dama, ku kasance dani a cikin wannan labarin._*





*_WRITING ON 01/03/2022_* ✍🏻




*_Pg 1 to 2_*





*KWARA STATE.*
*_IFELODUN local Government_*



*_IYABO QUARTER'S NEAR OMUPO WORD_*




"Sauyin rayuwa kan nuna maka alamun ka hankalta, amma ina mamakin mutane da basa gane azancin duniya, duniya tamkar waina ce dake bisa kasko takan iya juya mutum a duk sanda taso, shiyasa ko yaushe nake fatan Duniya ta muku juyin alkairi, domin bana fatan abinda zai shiga tsakanin ku har ya samu damar rabaku tamkar jinina haka nake jinka *_NAMEER_* so nake ku kasance tsintsiya maɗauri ɗaya har ƙarshen numfashinku,
*_HISHAM NAMEER_* ba iya Amini yake a wajen ka ba tamkar ɗan uwa na jini haka yake tunda a hannuna ya tashi tun bayan mutuwar mahaifansa, Soyayyar ku da abotarku tun ta yarinta ne, duk da a zuciyata bana jin akwai abinda zai iya rabaku saboda tsantsar ƙaunar dake tsakanin ku, amma wasiyya da nasiha ta dole ce a gareku, abotarku tana da ƙarfin da tafi jini tasiri, nasan dole ne kuyi nasara akan maƙiyanku ina matuƙar alfahari daku ina muku wannan nasihar ce saboda ita mutuwa bata da notice haka kuma bata ƙwanƙwasawa bawa ƙofa, zan iya komawa ga mahallicina a ko wani lokaci."
Kallon Nameer Hisham yayi tare da sakin numfashi yace.
"Abba Ina mantawa da cewa Nameer Abokina ne, kallon jinana kawai nake masa, yana kyautata min Abba, yakan yaƙi da duk wata damuwar da yaga ta tunkaro ne, karka manta Abba, Ammi ta kasance ta bamu tarbiyya iri ɗaya, ta bamu abinci a baki tare, ta share mana hawaye tare, to ta yaya zan ɗauke sa iya Aboki kawai? ya wuce wannan matsayin Abba, domin ƙaunar da nake masa ta kai ga zan iya mallaka masa komai a rayuwata domin kuwa yafi min komai mahimmanci ina matukar alfahari da Nameer Abba shine jigon rayuwata na basa duk wata yardata."
"Abba Hisham fa ɗan uwana ne ka daina shakku akanmu domin kuwa zamuyi ƙargo har abada, igiyar Amintar mu tana da ƙarfin da bazata taɓa tsinkewa ba ni da Ɗan uwana Hisham mutu ka raba Abba, zamu bawa maƙiya kunya ka kwantar da hankalinka a kanmu Abba."
"Hmmm! Ni ma shaida ce Abban Hisham domin kuwa yarana basu taɓa ko da cacar baki bane bare faɗa, lokacin Office na ƙurewa kuyi maza kar ƙananan ma'aikata su gaji da jiranku Allah ya muku albarka ya tsare min gabanku da bayan ku."
Murmushi Hisham yayi tare da cewa.
"Ameen Ammin mu, mun gode sosai sai mun dawo."
"Sai mun dawo Ammi."
Shima Nameer yayi Maganar cikin fara'a, da adawo lafiya Ammi da Abba suka amsa, kafin ko wannensu ya ɗauki jakar aikinsa suka fita tare, Murmushi Ammi tayi kafin ta mayar da kallonta ga Abba tace.
"Abban Hisham, shaƙuwa da ƙaunar junan da suke yiwa junansu har yayi yawa, ina jin Nameer a jikina tamkar ni na haifesa, Abban Hisham, mutane sai saka maka albarka suke bisa ɗaura Nameer a matsayin shugaban Companyn ka *_ HISHAM RICE MILL LIMITED_* madadin ka bawa Ɗanka Hisham ka kyauta sosai na tabbata kuma zai tsare maka dukiyar ka da mutuncin Companynka, Allah ya jiƙan iyayen Nameer mutane ne na ƙwarai da suka san haƙƙin makwabtaka."
Numfashi Abba ya saki yace.
"Na lura yafi Hisham nutsuwa da sanin abinda yake zaifi mai da hankali ga cigaban Company shiyasa na basa dan haka ki daina gode min abinda ya kamata nayi, Nameer shima ɗana ne."
"Hakane to Allah yayi jagora, bara naje na bawa TUTU key ɗin store ta ɗauko coffee na kitchen ya ƙare."
"Okay kina iya tafiya."
Abba yayi Maganar yana maida glass ɗinsa idanunsa tare da ɗaukar jarida ya cigaba da karantawa itama Ammi bedroom ɗin su Nihal ta nufa.



Tafe suke a ƙas sun fito daga ofishin Jaridar Aminci, suka hango cincirindon mutane, a gefen hanya, duban Basmah tayi tace.
"Basmah meke faruwa a can.?"
"Kaji wata tambayar rainin wayo, mu fito tare sannan ki tambayeni aljana ce ni ko boka da zansan abinda ke faruwa a wajen."
"To sarkin ɓakar magana, ni bara na ƙarasa wajen naga abinda ke faruwa."
Kanta Basmah ta girgiza tare da cewa.
"Kina da matsala *JIDDA* baki san meke faruwa a waje ba ki kai kanki saboda kawai kina ƴar jarida mai tarar kasada ko ke gaki mai son ɗauko rahoto."
"Bani da lokacin ki idan zaki iya zuwa ki biyoni idan bazaki iya ba, mu haɗu a gida."
Tayi Maganar tana saka kai tabar wajen, bakinta Basmah ta taɓe tare da bin bayanta, ko da Jidda ta isa wajen a cike yake babu masika tsinke jama'ar wajen ta dinga ketawa har ta samu ta shiga tsakiyar wajen da ƙyar, wata ƴar matashiyar budurwa ce baje ƙasa, da alamu bata motsi, yayin da jama'ar dake Wajen suka zuba mata idanu babu wanda yayi yunkurin taimakon ta, jikinta duk ya kuje da alamun yaguni da sauri Jidda ta sunkuya a kanta tana furta.
"Subahanallah! Meya faru da ita, kun zuba mata idanu bazaku kaita asibiti ba idan ta mutu a wajen nan fa.?"
Wani daga cikin wadanda ke tsaye a wajen ne yace.
"Ta yaya zamu sanya hannu a jikinta bayan muna kallo aka wurgota daga mota, mun sanya hannun mu a cikin masifa kike so, idan taimakon ta kike son kiyi to ki fara kiran Police tukunna."
Ɗago idanunta Jidda tayi a zuciye tace.
"Amma dai Allah wadarai wallahi kuna kallon mace wurge gefen titi ku gagara taimaka mata, idan ƙanwarku ce zaku zuba mata idanu haka ba tare da taimako ba, mtsss! Wai kuma har kana da bakin bani shawara, ku kauce ku bani ni zan rungumi kasadar idan yaso masifar da kuke gudu ni ta kasheni."
Tayi Maganar tana miƙewa tare da kwaɗawa Basmah kira, duk kaucewa gefe sukayi suka bata hanya babu wanda ya ce komai a cikin taron, Basmah ƙarasowa tayi ta tsaya a gabanta tare da cewa.
"Gani kiran me kike min.?"
"Taimakon ta zamuyi Basmah domin kuwa tana buƙatar taimako ta zubar da jini da yawa Sannan bata motsi zata iya rasa rayuwarta muddun muka tafi muka barta a hannun wadannan marassa imanin."
"Hmmm! Jidda ba rashin imani yasa basu taimaketa ba, karki musu mummunar fahimta domin kuwa rayuwa ta lalace, a sanadin taimako sai ka shiga cikin wata masifar banga laifin su ba, ko da ma suna da laifi to laifin ɗaya ne na rashin kiran jami'an tsaro da wuri, karmu taɓa wannan yarinyar idan har taimakonta zamuyi to police ya kamata mu kira kamar yadda wannan bawan Allah ya faɗa miki."
"Kinga Basmah bazan tsaya har sai an kira Police sunzo ba! Kafin a kaita asibiti rayuwarta zamu ceta bama bukatar jira idan zaki taimaka to idan bazaki taimaka ba kija baya zan iya ba tare da taimakon ki ba."
Tayi Maganar cikin masifa tana fita sarari da kallo Basmah ta bita domin kuwa ko yaushe bata gajiya da mamakin taurin kai da kafiya irin na Jidda ba, sam ba'a juyata inda ta sanya kanta nan kawai takeyi tana kollonta ta taro adaidaita, da ita da mai adaidaitan suka kama yarinyar suka sanya ciki kafin Jidda ta shiga ta tallafota jikinta, Basmah kanta ta kaɗa tare da shiga cikin adaidaitan, harara Jidda ta watsa mata tare da cewa.
"Nayi zaton ai imaninki ya gushe ashe har yanzu da saura."
Tayi Maganar dai-dai mai adaidaitan yana ja.
"Bazaki fahimce ni bane, yanzu da kika ɗauketa kina zaton asibiti zasu amsheta ba tare da Police bane.?"
"Bazasu amsheta ba na sani, shiyasa ma na turawa Ahmad text cewa kinyi accident muna IBUNKU OLU CLINIC wataƙil ya rigamu isa kinga police ɗin ma aishi zai jiramu."
"What! Jidda meye kikayi haka."
"Ceton rayuwar mace ƴar Uwar mu shi nayi ko akwai laifine ayin hakan."
"Ƙwarai kuwa akwai babban laifi ma, akan me zakiyi ƙarya dani ki faɗa masa gaskiya mana zaki wani ɗaura min mungun abu."
"Koma dai mai zaki faɗa kiyi haƙuri ni ne na miki laifi amma kin sani muddun na sanar dashi gaskiyar abinda ke faruwa ba zuwa zaiyi ba."
Tsuka Basmah taja cikin ɓacin rai tace.
"Dole ki bani haƙuri ai tunda kin cuceni."
Tayi Maganar dai-dai suna shigowa asibitin, shima Ahmad dai-dai yayi parking ɗin motarsa ya fito a gigice turus ya tsaya ganin Basmah sun rungumo wata, wajen su ya ƙarisa da sauri yace.
"Jidda ya haka kince Basmah tayi accident kuma naga kin rungumo wata ga Basmah tsaye lafiya.?"
"Ahmad bamu lokacin Doguwar magana dan Allah ka sanya hannu a duba wannan baiwar Allah, kafin mu maka bayani, a gefen titi muka tsinceta cikin wannan halin."
Ahmad zaiyi Magana Basmah ta katsesa da cewa.
"Kar ka mata gardama domin kuwa kasan mayya ce ita, ka sanya hannun."
Numfashi Ahmad ya saki kafin likitoci suka taho da keken marassa lafiya aka turata, ganin Ahmad da kayan Police a jikinsa, bayansu yabi ya cike dukkan wata takadda rashin sanin sunanta yasa ba'a rubuta sunanta ba kafin sukayi emargency da ita.
Bayan an shiga da ita ne Ahmad yayi kan Jidda da faɗa na ɗaukar wannan kasadar, ita dai bata kulasa ba, suna nan tsaye har doctor ya fito duban Ahmad yayi yace su samesa a Office bayansa sukabi tare da zama doctor ya dubi Ahmad yace.
"Wannan marar lafiya da kuka kawo, gaskiya ta zubar da jini da yawa, muna da jinin da yayi dai-dai da nata kasancewar tana neman jini cikin gaggawa yasa bamu muku magana ba muka sanya mata da alamu faɗowa tayi daga sama ko dai something haka ta kuje sosai amma dai Alhamdulillah! Babu matsalar buguwar kai, mun mata allurar bacci sannan akwai zazzaɓi a jikinta zata iya farkawa ko wani lokaci zakuje receiption ku biya kuɗin jini, ga kuma takaddar magani zaku saya."
Hannu Ahmad ya sanya tare da amsa yace.
"Thank Doctor."
Tashi yayi ya fita bayansa suka biyo, Jidda ce tace.
"Akwai kudi a account ɗina ni zan biya wannan taimakon da kayi da jikinka ma kaɗai ya wadatar na gode sosai."
"Hmmm! Jidda kece zaki biya kudin kika ce, Karki manta ɗawainiyar mahaifiyarki da ta ƙaninki kuɗin hayar gidan ku duk a kanki suke, dan haka idan ba'a ƙara miki ba baza'a rageki ba, ni zanje na biya da aljihu na."
Numfashi Jidda ta saki tana ganin darajar Ahmad sosai musamman yacce yake tausayawa rayuwarta.
"Hakane Ahmad na gode sosai, yanzu yaya za'ayi da kwana a wajen yarinyar kaga fa Ummana ba lallai ta amince na kwana ba infact ma bazata yarda ba."?
"Karki damu Jidda, zan kira A'isha sai tazo su kwana zuwa gobe ta dawo hayyacinta sai musan ahalinta, kuna iya tafiya zanje na gama komai kafin Aisha tazo ni sai na wuce."
Murmushi Jidda ta yi tace.
"Na gode Ahmad Allah ya maka abinda kayiwa wannan yarinyar sai goben."
Tayi Maganar tana yin gaba, Basmah duban Ahmad tayi tare da sakin murmushi tace.
"My Dear ina matukar girmama Soyayyar mu, kai Mutum ne na Musamman a rayuwata, ina sonka matukar Soyayya."
"Hmmm! Basmah idan ban kyautata miki ba waye zan kyautatawa, kinfi ƙarfin komai a gareni Basmah dan haka ki tafi kuje huta zan shigo anjuma."
"Shikenan farin ciki na bye."
Tayi Maganar cike da soyayya tana bin bayan Jidda.



💫💫💫💫💫💫



"Na rantse da Allah sai naga bayan zuri'ar Iyabo bazan taɓa gushewa ba sai naga ƙasƙantarsa da tozarta sa, koda kuwa zanyi yawo tsirara, nasan zuwa yanzu saƙona ya fara ƙwanƙwasa musu ƙofa, sai na sanya su a cikin *_JALALAR_* da sai sun roƙi mutuwa da kansu, *TUNDE* muddun kai jinina ne to tabbas bazaka gushe ba har sai ka ɗauki bashin gabar da ke tsakanin mahaifinka *Babawale* da *Iyabo*, kadda ka saurara musu nima kuma bazan saurara musu ba, na sanya mutanena a cikin Companyn su suna sanya min ido akan dukkan abinda zaije ya dawo acikin Companyn to yana tafin hannuna dan haka karka saurara."
*Mama Bisola* tayi Maganar cike da tsantsar wutar fansar dake ruruwa a cikin zuciyarta da tsanar familyn Iyabo.
"Mamabisola karki manta cewa babu mutanen dana tsana a wannan duniyar sama da su Iyabo ba kuma zan gushe ba har sai naga bayansu, daga ƴaƴansa zan fara da wannan tsintaccen yaron da ya ijiye ya basa yardarsa fiye da matar sa da ɗansa, wallahi Mamabisola sai na sanya su kuka a tsakiyar titi."
"Haka nake so Tunde kaje kana tare da Sa'a."
"Na gode Mamabisola, zan wuce wajen Bola."
"Ka dawo lafiya."
Mamabisola tayi Maganar cike da ƙaunar Tunde, yana...


Read / Download JALALA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album