Join Our WhatsApp Group

YAR KURMA Complete Hausa Novel Document by YAR KURMA


YAR KURMA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 34679



YAR KURMA

Reading Time: 2 Hours

Added On: 13, Sep 2023

Author: HausaEbook ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 192.44 kb

File Type: txt

Views: 744+

Download: 225+

Last download: 3 days ago

Description/Story: YAR KURMA

GODIYA

Dukkan godiya ta ga ubangijin talikai, daya hallice ni cikin ni'mar musulunci. Ya kuma bani ikon d'aukar alk'alami dan yin karambani a kan wani tak'aitacen lamari bisa san sanin makamar aiki. Har gobe nid'in me neman gyara ce daga na sama dani harma na k'asa nà kasantuwata k'ank'anuwa cikin harkar adabi.

Cikin takaici ta nuna Marwanatu da hannu, zuciyarta na yi mata k'una saboda dariyar da take yi mata. A zafaffe ta kai mata bahagon duka, amma kash! Bata same ta ba ta saki wata giggitaciyar k'ara, ji kake kauuuuuuu! A kunnuwan Marwanatu. Benaziratu ta k'yalk'yale da dariya ta buga k'afa irin na Bebaye ta murd'a yatsu, take suka bada sauti d'as! 'Das!! Das!!! Alamun gargad'i tuni Marwa ta ranta ana kare.
Bata jinkirta ba ta rufa mata baya, ai kuwa suka kasa a guje. In baka yi bani waje, basu samu matsaya ba sai a d'akin Hajja Yakura, bisa tsatsauyi suka zubar mata da biskin geron da ta ajiye. Ai kuwa cikin hargowa ta yo kansu, Marwanatu ta falle caraf ta kama Benaziratu."Wato ke 'yar kurma bakya jin magana ko?". Benaziratu ta turo baki, bata ji abinda ta furta ba amma bakinta da ta kala ta gane me furucinta yake nufi. Tuni ta hau tirje-tirje Allah ya bata sa'a ta k'wace a guje ta bar sashin. Kafar! Sukai karo da shi, a razane ta d'ago sukai ido hud'u dashi Baana. Cikin razana ta so kaucewa kamunsa amma ina ta makaro. Yana rik'e da ita ya shiga gidan, da salama Yakura ta d'ago tana amsa masa mamakin ganinsa a wannan lokaci yasa ta kasa magana cikin yaransu take kiran mai gidanta tana sanar masa. Bakura ya taso da saurinsa yana nuna farin cikinsa da ganin Baana. Da wannan damar Benaziratu ta kufce ta fyala da gudu, yabi bayanta da kallo yana murmushi karaf suka hada ido da Yakura ya sune kai yana shafa k'eya.
Gimtse fuska tayi ta shimfid'a masa tabarma karauni, ya zauna yana gaishe su tare da tambayar yadda ya same su. Cikin murmushi suke amsawa, shigowar Marwanatu tana kuka ne ya katse su. Cikin masifa Yakura tace"kin tsaya ta dake ki ko?" Marwanahtu tai ajiyar zuciya tana lab'e-lab'e saboda ta san mudin Yakura ta kamata duka zata sha. Saboda kullum gargad'inta ta daina bari Benaziratu na dukanta ne. Cikin mamaki Baana yace" wace ce ?" Cikin jin haushi ta numfasa.
"Wacce ce kuwa banda Benaziratu?" Ta fad'a da gurb'ataciyyar hausar ta.
Mumushi yayi a ransa yana fad'in "yaushe Hajja zata sauya?". Shiru na tsayin lokaci, ya yunk'ura zai mik'e " ina zaka"? Cewar Yakura. Kansa a k'asa ya furta "zan je in huta an jima in shiga in gaishe da Abbagana". Murmushi mahaifinsa yayi yace "Allah ya kaimu" k'wafa tayi taja hannun Marwanatu suka bar wajan. Daga shi har mahaifinsa murmushi sukai_.





Washegari da misalin k'arfe bakwai na safe Baana yana zaune a dakalin k'ofar gidansu, ya hango tahowar Benaziratu tunda ta taho ya zuba mata ido. Shi dai rayuwarsa yarinyar tana birgeshi, komai nata cikin nutsuwa take yi duk da cewar tana da son barkwanci. Bai ankara ba harta k'araso ta zo giftawa ta d'aga masa hannu tana murmushi gab da zata shiga gidansu ya d'aga murya da k'arfin gaske, ya k'wala mata kira *"Benah"*. Juyowa tayi ta murgud'a d'an k'aramin bakinta, ta murd'a yatsu suka bada sauti ta shige gidan. Yai murmushi a ransa yana fad'in "hallayar Benah tana nan". Cikin gidan ta shiga da fuskarta d'aure tai salama, duk haushin Baana ya tuk'eta nan duniya ta tsani a kirata da Benah, ganinta kawai iyayine irin na Baana dan yaje birni karatu.

_"Ke! 'Yar kurma" aka fad'a da k'arfi daga gefanta, juyowa tayi tamkar mayunwacin zaki tana huci. Ganin Hajja Yakura sai ta sadda kanta k'asa tana gaisheta cikin gwarancinta irin na Bebaye. Matsowa tayi ta kama kunnanta ta murd'e ai kuwa ta saki k'ara saboda azabar wahala, shar k'wala ta zubo mata. "Dan ubanki me Marwanatu tayi miki jiya, da zaki sata Ku........?" Maganar ta katse sakammakon k'watarta da Bakura yayi yana bambamin fad'a.

"Ke dai Yakura kinji kunya, me yarinyar nan tai miki? Tsabar k'in Allah kin takura mata idan da kara itama 'yar ki ce"._

_"Kai! Kai!! Kai!!! Bakura dai na fad'in wannan, Allah suturi buk'wui ina amfanin sai da rai a nemo suna? Wai kai kana tunani zanso wannan abar? Hmmmm! Allah ya kiyayye had'a iri da kishiya". Wata muguwar harara ta makawa Marwanahtu, tuni ta ja hannun Benaziratu wadda take razgar kuka, kasancewar duk da k'arfi Yakura take maganar tana jinta. Kad'a kai Bakura yayi ya shige d'akinsa.

Suna fita sukai kici6us da Baana, hannun Benahziratu ya kamo yana tambayarta. Ta k'wace hannunta dan tuna abinda yai mata d'azu. Bata kula kowa cikin su ba ta warce hannunta tana kuka, kai tsaye gida ta nufa. Cikin raunin murya ya dubi k'anwarsa"Marwah me ya samu Benah"? Murmushi tayi dan taji dad'in yadda ya kira sunan. Tiryan-tiryan tai masa bayanin abinda Yakura tayi, kansa ya ri'ke yana jinjina hallayar mahaifiyarsa a ransa yana fadar" wai shin yaushe Hajja zata sauya?"............

_Kai tsaye gida ya shiga, alamu da yawa sun nuna tsantsar damuwarsa. Yana shiga da salama ta amsa masa babu yabo ba fallasa, ya samu guri ya zauna. Minti biyar babu wanda yace uffan cikin su, ganin babu fuska ya yunk'ura ya bar gidan. Zuciyarsa na zafi.

Kai tsaye gidansu Benahziratu ya nufa, cikin murmushi yai salama. Mamaki ne ya kamashi ganin Benazirahtu normal (lafiya) tana aikin ta. Mahaifin Benazirahtu ne ya fito da murmushi ya ce "a'a Baana barka da zuwa, saukar yaushe?" Ya shafa k'eya d'abi'ar da ta zamo masa jiki da murmushi yace. "Abbagana jiya da yamma nazo hala Benah bata gaya muku ba? Ta gani a jiyan". Cikin murmushi yace "kasan halin kayar ka", zama sukai suka k'ara gaisawa. Can sai ga Hajja Faanah ta fito, suka gaisa da nuni da hannu. Ruwa mai sanyi Benazirahtu ta ajiye masa cikin a kofin kushi, ta sake dawowa d'auke da babban a kushi ta sunkuya ta ajiye. Murmushi ya yi ya bud'e k'amshin manshanu ya yi masa salama, ya lumshe ido ganin biskin gero da miyar kub'ewa ga manshanu. Ai ba jinkirtawa ya sab'a hannun riga ya soma kwasar loma.
_Can ya d'aga murya yace "Abbagana ina ce Hajja ce tayi girkin nan ba wannan ba?". Tsaf ta kalle bakinsa, ta gane furucinsa ai kuwa ta turo baki ta hau buga k'afaffu alamun shagwab'a. Gaba d'aya suka saki dariya, cikun gurbataciyyar maganarta tace "nafi matarka iyawa". Dariya suka sake yi, Hajja Faanah na tambayar abinda Benazirahtu tace. Mahaifinta yai mata bayani da hannu._

_Bayan ya gama ta d'auke kwanukan, ya dubeta "Benah d'auko jakarki ta school (makaranta) in gani kinji", babu musu ta mik'e sai ga ta ta dawo d'auke da'ita, karb'a yayi yana duddubawa a hankali yake mata tambayoyi tana amsawa . Sossai yaji dadin yadda ta maida hankali tana karatu fiye da Marwah.Bai bar gidan ba sai gefun sallahr azahar, a ransa ya k'udiri kyautar da zai mata.
************
_Washegari kuwa sai gashi da dogayan riguna, dai-dai ita guda uku bayan sun gaisa da Hajja Faanah ya bata. Godiya sossai sukai masa, Banazirahtu baki yak'i rufuwa ya gonar audiga. Da gudu ta suri kayan ta nufi gidan wan mahaifinta, tun a soro take kwad'awa Marwanahtu kira. Tana fitowa ta hau nuna mata kayan, cikin murna tace "waya baki?" Babu komai ranta tace "Baana"........... Kafin ta k'arasa magana taji an warce kayan kai tsaye cikin murhun girki Hajja Yakura ta watsa su, wata giggitaciyar k'ara Benazirahtu tayi ta shid'e ji ka ke yif! Ta fad'i. Hakan yai dai-dai da shigowar Baana cikin kad'uwa ya furta.
"Benah!




Cikin kad'uwa yake girgizata yana kiran sunanta *Banah! Benah!! Benah!!!* amma kash! Shiru Malam yaci shirwa. Hankalinsa ya yi matuk'ar tashi da wani rikitacan kallo yake duban mahaifiyars. Sai dai kawaici irin na d'a da uwa ya kasa tankawa. Surarta yai bai zame ko'ina ba sai d'akinsa, sossai yake zuba mata ruwa ta k'i motsawa. Ya kasa kunne amma bata motsi, k'irjinsa ya dinga bugawa fat! Fat!! Fat!!. "Kadai ace *Benah* ta rasu"?. Ya fad'i hakan a ransa. Can ya tuno wani bayani da akai musu a wata lecture, yayin da mutum yai dogon suma. Hamdala yayi ga ubangiji, ya toshe hancinta ya bud' e bakinta ya had'a da nasa. Ya soma musayar numfashi kafin minti uku ta soma motsi, cikin sauri ya watsa mata ruwa.

_A hankali ta zuba masa ido, can ta fashe da matsanancin kuka saboda tunawa da kayanta."Baana kayana" , ta fad'a cikin gwaranci. Janta yayi jikinsa yana shafa kanta a hankali tai shiru sai ajiyar zuciya take. Sai da ya tabbatar da ta yi shiru ya d'auko chaculate ya bata, tare da alk'awarin kawo mata wasu sababbun kayan. Da murna tai masa salama ta nufi gida. Tana zuwa ta zauna ta bawa mahaifinta labari, murmushi yayi tare da bata hak'uri ya gargad'eta da kada ta gayawa Hajja Faanah komai, saboda gudun matsala. Koda ta tambayeta cewa tayi "kayan ne sukai yawa canzowa za'ayi".

_Cikin rashin walwala ya shiga gida, Hajja Yakura ta dubeshi "wai kai dan an k'ona kayan waccan nakasshashiyar *'YAR KURMAR* kake ciwa mutane kunu? Meye abun damuwa da lamarin mutanan da suke da nakasa a rayuwar su? Mtssss!" Ta ja tsaki tana gunguni. Cikin taushin murya ya dubeta._

_"Hajja ki fahimce ni koba komai *Benah* 'yar uwata ce, kuma k'abilarmu d'aya nakasa ba zaisa in nuna mata k'yama ba. Bafa laifi sukaiwa ubangiji ya hallice su haka ba, suma mutane ne kamar kowa kuma ubangiji yana kishin su yana sonsu. Haba Hajja". Ya fad'a da sanyin murya, ai kuwa yana direwa ta hau sababi, kai kace zaginta ya yi jikinsa yai sanyi zuciyarsa na radad'i yana takaicin hallayar mahaifiyarsa.

TUSHAN LABARIN*_

_Baana d'a ne ga Alairam Modu kalmar Modu na nufin Muhammad kenan, Modu wanda akafi kira da sunan Bakura,saboda kasantuwarsa babba a gidansu. Kalmar Alairam na d'aukar Alhaji ne a yaran Kanuri ko kuma Aisami wato Alhaji. Hajiya kuma sukan kirata Aisaram, yayin da . Bakura dai haifaffan garin Mai duguri ne, su biyu iyayyansu suka haifa da k'aninsa mai suna Hamza. Sun taso cikin so da k'aunar juna, mahaifinsu fittacan Malamine wanda yake koyar da d'alibai sama da hamsin.Sunansa Aisami Muktar Bunu, wanda da yawan muta ne ke kiransa Malam Bunu. Mahaifiyar su kyakkyawar mace ce mai suna Falmata a salinta shuwa ce._

_Sun taso cikin ingantaciyyar tarbiyar da mahaifinsu ya basu, mahaifinsu mutum ne mai neman na kansa. Saboda sana'a maganin wulak'anci ce, shi kuma Kanurin mutum nan duniya ya tsani raini da wulak'anci. Haka kuma Kanuri ya tsani 'kazanta baya son rashin gaskiya da girman kai uwa uba d'aukar al'adar da ba tasa ba._


_Idan kuwa so kake ka burge Kanuri, to kayi masa kyautar gwal ko hula ko turare mazan su da matansu akwai son k'amshi. Kanuri akwai iya kula da tattalin mace tamkar k'wai, sun tsani rashin iya girki da yawan dariya. Matansu kuwa in kana son burgesu kyautar gwal da mindil. Mindil wani gyala ne na bare-bare, shigar su kuwa mata sunfi yin shigar lafayya, ko riga mai dogon hannu da mindil. Tsofaffun cikin su dama wasu cikin matasa, da yawa suna cin goro.Suna amfani da wani abu mai suna; ingwargo abun yana nan green ne(kore) in suna cin goro suna goge bakin su dashi don hak'orin su ya yi ja.Idan na tsaya yi muku bayanin Kanur sai mu kwana, saboda suna da al'adu daban-daban ababban sha'awa._

_Malam Bunu yana sa'ar d'inkin hula, sai kuma d'an hasafi da yake samu daga masu zuwa ayi musu adu'a. Hakan baisa zuciyarsa ta mutu ba kullum burinsa yaransu sui karatu domin gobansu._

_Yaransu na samun kulawa dai-dai gwargwado, sun tsaya kan tarbiyar su. Kaf d'insu sai da suka hadda ce alk'ur ani mai girma sannan suka saka su a makarantar boko. Lokacin Bakura nada shekaru goma cif, Hamza kuwa nada bakwai, sai dai mahaifinsu na yi musu lesson a gida wata rana kuma Falmata tayi musu, wadda suke kira Hajja.Fanin ilmin boko ma babu dama, sun tsaya tsayin daka da karatun su. Bakura na primary four Hamza na primary two wani muhimmin al'ammari ya tasowa Alairam wanda hakan ya tilasta masa tashi daga Maiduguri zuwa garin biu d'aya daga k'aramar hukumar jahar Maiduguri._


_Al'amarin ya samo asali ne na wata makaranta
da aka bud'e ta islamiyya a garin biu dan
bunk'asa harkar ilmin addini. Aka d'auki Malam
Bunu zuwa wannan sashi, da farko ya soma
zuwa ya dawowa iyalansa duk mako d'aya wato
kwana bakwai. Daga baya yaga rashin dacewar
hakan, saboda yadda sukai sabo da iyalansa
shawarar Falmata ya nema ya samu k'aramin
gida ya sai musu suka koma can da zama gaba
d'aya. Dama ba wani dangi ne da shi sossai ba
duk sun mutu sai k'anin mahaifinsa guda d'aya
shima ya tsufa sossai. Haka suka tattara suka
koma._
************
_*GARIN BIU*_
_Garin Biu na d'aya daga cikin k'anannan
hukumomin jahar Maiduguri.Shi dai k'auyen Biu
k'auye ne babba, wanda Allah ya a zurta su da
noma da kuma karatu.Sun d'auki karatu da
muhimmanci fiye da yadda mai karatu yake
zato.Shiya sa suka samu cigaba a cikin
Maiduguri, dama wasu garuruwan a cikin
Maidugurin. Idan kika cire ma'aikaci d'aya na
biyu zaki ga babur ne wato yaransu. Ilahirin
mutanan biu babur ne.Haka kuma ta b'angaran
noma, Mata suna yi Maza suna yi. Amma duk da
wannan noma, dole yaro sai ya bawa karatu
lokacinsa. Suna noman gyad'a masara da
barkono da kuma gauta._
_Mutanan garin sun iya zaman duniya da kissa,
da kuma wayo sai dai suna da rowa. Sanan kuma
hanyar zuwa biu bata da kyau akwai gargada a
hanyar. Allah ya horewa mutanan Biu iya
soyyaya, sun iya soyayya 'yan garin. Matan garin
kuwa suna da had'in kai tsakanin su.Mai karatu
kar kayi mamaki in nace maka, zaka ga mace ba
abinda take b'oyewa mijinta komai tare
suke.Suna tanadi da tattalin junan su._
_Idan kuwa ka shiga jami'ar Maiduguri zaka riski,
gungun d'alibai 'yan garin har taron su suke duk
k'arshen wata. Sukan yi had'in guiwa wanda ba
shi da kud'i su tara masa.Kishi da jinsin Kanuri
akwai wahala, ballantana kishi da matan garin
Biu.Kishi da su yana da wahala saboda suna da
bala'in kissa da iya kula da Miji uwa uba
biyayya._
_Wannan shi ne bayanin garin Biu a tak'ai ce,
kuma mudin akai hutun makaranta lokacin
damuna to zaki ga d'alibai mazauna Biu na
turruruwar zuwa yin noma garin su._
_Komawar su garin Biu bai kawo nak'asu a
rayuwar su ba, hasalima cigaba suka samu ta
fannoni da dama. Makaranta mai zaman kanta
mahaifinsu ya saka su, sab'anin da da suke zuwa
makarantar gwamnati.Zama suke cike da
walwala da jin dad'i, a jikin gidan su akwai
mak'ota guda biyu d'aya 'yan garin Gwaza ce
yaranta biyu d'aya sunan sa Alangubro d'ayar
kuma Aysa. Aysa na nufin Aysha, Alangubro
kuma ranka ya dad'e.Akwai kyakkyawar alak'a
tsakanin wannan mak'ota. A hanun daman su
akwai wata dattijuwa mai suna Hajja Faanah.
Hajja Faanah...


Read / Download YAR KURMA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album