Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

ZAFIN RANA Complete Hausa Novel Document by ZAFIN RANA


ZAFIN RANA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 79376



ZAFIN RANA

Reading Time: 6 Hours

Added On: 24, Feb 2025

Author: Ayusher Muhammad ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : HASKE WRITERS ASSOCIATION

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 457.72 kb

File Type: txt

Views: 2+

Download: 4+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: *ZAFIN RANA*

*_Shafi na Daya_*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*



*Masarautar Biram*



Ta ko ina ya rurufe kofa da window din dake cikin dakin, kallan juna sukai hankalinsa a tashe yace "Yaya!"

Kusa dashi ya zauna tare da rike hannunsa, wanda ya kira da yaya ya kalleshi cikin matsanancin jin jiki, hannunsa ya matse yace "Abdul-Salam!"

Da sauri yace "yaya."

Yaya ya kalleshi yana magana dakyar, yace "Abdul-Salam ga Amanar Junaid nan, ka kula dashi, in da dama ka fitar dashi daga masarautar nan, dan sam
Bana sanshi da mulki."

Cikin mamaki Abdulsalam ya kalli yayansa yace "yaya? Wani irin magana kakeyi bayan Junaid shi kadai ne dan da ya cancanci ya gajeka? Shikadai ne danka namiji, babu wanda ya dace da mulki sai shi."

Kai ya kadamai da sauri yana magana a hankali yace "A'a kai kayi mulkin, dan Allah ka barshi yayi rayuwar da ya dace dashi, kasanshi yaro ne mai ilimi, da san kwanciyar hankali, banaso ya taso cikin wannan yanayin wanda rayuwarsa ma take cikin garari."

AbdulSalam yace "yaya to ya kakeso ayi?"

Idanunsa ne suka shiga lumshewa, rigarsa ya riko yace “ka kula da Junaid dan Allah Abdul-Salam, na barma mulkin nidai ka barshi da rayuwa.............”

Yanda yanayin jikinsa ke rawa ne ya hanashi karasa magana, zuciyarsa ce ta daina bugawa, numfashinsa ya tsaya, wanda hakan ya nuna rai yayi halinsa.

Hankali a tashe AbdulSalam ya dinga jijiga yayan nasa wato Sarki Zubair.

Fitowa yai jikinsa duk a mace, bayi da kuyangun dake tsaye a gun ne suka kalleshi.

Matar da ta taho tana kokarin shiga gun mai gidan nata ne tai turus tana kallan sa.

Idanu ya runtse sannan ya girgiza mata kai alamar babu.

Nan bayi suka fara kukan rashin Sarki da akai, ja da baya da baya ta fara yi, tana girgiza kai, da sauri ta matso tana neman shiga gun mijin nata? Matsa mata yai ta shiga, a kwance ta ganshi wanda hankalinta ya tashi da sauri ta sa hannu ta jijigashi, sai dai ganin jikinsa ya koma ya kwanta yasata ta saki wani irin kuka.

Kan kace me zance ya shiga lungu da sako na cikin masarautar, harma cikin gari inda mutane suke, ta ko ina tururuwa ake ana zuwa ana mika gaisuwa, gidan ya cika makil.

Washe gari....
Matansa da yaransa wadanda duk mata ne kowa ya hallara, yaro ne dan shekara 8 zaune kusa da mahaifiyarsa, kuwa kallan tausayi suke mai, wasu kuwa kallan soko suke masa, shikam yana makale da mahaifiyarsa har ganin ana neman yima mai martaba sallah yasa ta kalleshi tace “Junaid aje za’ayima Mai Martaba sallah.”

Kuyangar dake kula dashi ta kalla tace “kuje.”

Nan ya mike yai waje.

Yana fita wata tace “yanzu ya za’ai da Junaid?”

Sarauniya wacce itace mahaifiyarsa ta kalleta, yanda ta mata kallan ne yasa taja bakinta tai shiru.

Anyima mai martaba sallah kowa sai gaisuwa yake yima Abdulsalam, a wannan lokaci babu wanda yabi takan Junaid, duk mutanen da ke zuwa gunsa da kula dashi yau suna can gun Abdulsalam ba wanda yabi ta kansa.

Shikam da yake yaro ne, mikewa yai yace “zan koma gun Mamana.”

Bawan daya rako shi gun ya bude mai hanya suka juya.

Yana zuwa bakin kofar bangaren Mahaifiyar tasa, yaji ana kwalla mai kira “Yarima Yarima.”

Waigawa yai ya kalli mai maganar, da sauri ya karaso inda yake cikin gudu, yana haki, sai daya dan huta sannan yace “Hakimi AbdulSalam yana nemanka.”

Juyawa yai suka koma, mutumin daya gani cikin mutane sosai dazu yayi mamakin ganinshi a cikin bangaren Sarki mahaifinsa shi kadai a wannan lokacin.


Yana shiga Abdulsalam ya kalleshi, Junaid wanda ya shiga kif kif da ido kawai yasa kuka, da sauri ya matso ya rungumeshi, Junaid ya shiga yin kuka yana cewa “Kawu wai Baffana ya rasu?shine wanda akama Sallah dazu?”

Abdulsalam ya rungumeshi cikin tausayawa yace “Junaid.”

Kuka sosai Junaid yakeyi kafin ya tsagaita.

Abdulsalam ne ya kalleshi yace “yanzu zamuje a kaishi makwancinsa, nazo ne da sauri dan na sanar ma wani abu.”

Junaid sam bai fahimta ba sai dai kallansa kawai da yakeyi.

Abdulsalam yace “yanzu zaka bi wannan, ya fada yana nuna saurayin daya kirashi dazu, tare zamu tafi dakai sai dai kai zakabi wannan zakuje wani guri, wanda ba dadewa zakuyi ba zanzo na daukeka.”

Kai ya jinjina alamar to, sannan yace “kar kuma ka fadawa Mamanka, kadai ce mata zakaje inda za’akai Mai martaba.”

Kallansa yai ba tare da wani zargi ba ya daga kai, nan ya juya ya fita, wannan saurayin yabi bayansa.


Shiru Abdulsalam yai, indai yanaso yai yanda Sarki yace to lalai dole ne ya fita da yaran nan ana cikin hargitsin nan, dan inhar ya bari sai an lafa to ko za’a mutu mahaifiyarsa bazata taba yarda da wannan lamari ba, shiyasa tun a daren jiya shi da yaran nan wanda yake jarumi ne shi sannan mutumin ne wanda ya yarda dashi, suka fita cikin dare dan neman inda ya dace yaran ya zauna, ya debi kuyangu ya kaisu, da sassafe da bayin da zasu kula dashi.


Junaid ya je gun Mahaifiyarsa, sai dai yawan mutanen dake shigowa yi mata gaisuwa ya hanashi karasawa kusa da ita, sai dai hangoshi datai daga nesa, saurayin ne ya kalleshi yace “Yarima lokaci yayi.”

Junaid ya kalleshi yace “muje in na dawo na fada mata.”

Nan ya juya ya fita, sam yayinsa ma da suke mata ba wanda ya damu dashi, kowa najin haushin shi kadaine namiji dole ne kuma ya gaji mai Martaba.


Sun fito suka shiga cikin jerin masu kai Mai Martaba gidansa na gaskiya.

Ana kokarin shiga inda za’a birneshi, saurayin yaja hannu Junaid suka bar gun, Junaid ne ya kalleshi sannan ya kwace hannunsa suka fara tafiya yana cemai “ina zamu?”

“Ba dadewa zamuyi ba can kauyen ne, yarima ai kanasan hawa doki ko?”

Da sauri Junaid yace “eh sosai ma.”

Saurayin yai murmushi, dan wani kauye suka nufa, wani gida ya shiga sai gashi ya fito da doki.

Junaid cikin murna ya kalleshi yace “aikuwa da gaske kake.”

Nan ya hau da Junaid gaba shi kuma ya hau suka harba doki sukai gaba.......

Sundanyi tafiya mai nisa kafin su isa wani kauye, Junaid cikin sha’awa yake kallan mutanen kauyen, ta ko ina kowa hada hadar sa yakeyi, kallan saurayin yai yace “sai yau na taba shigowa cikin mutane haka, zanci wancan..”
Ya fada yana nuna mai wani abu da suke saidawa, kamar mazarkwaila.

Saurayin yace “Yarima kayi hakuri in munje zansa a zo a duba maka mai kyau ba irin wannan ba.”

Junaid yai dariya yace “ina binka bashi kenan.”

Sauka sukai akan dokin suka karasa dan karshen kauyen kadan.

Gini ne wanda kana ganinshi kaga gini na sarauta, mamaki ya kama Junaid ya kalleshi yace “gidan waye?”

Saurayin yace “gidan Sarki Zubair ne.”

“Babana?”
Ya fada cikin mamaki, saurayin ya daga kai, yana murmushi dan shi kansa bai taba ma sanin kauyen nan ba sai a daren jiya da sukazo da Abdulsalam, wanda Sarki zubair ya sanar dashi inda kauyen yake da gidan dayasa aka ginama Junaid tun sanda ciwo ya fara kamashi, wato shekara biyu da suka gabata.


Masarautar Biram.....
Nasan duk wanda yaji sunan Biram zai fara tunanin ina ne? Sai dai nasan wasu daga cikin mu su san sunan.

Biram shine asalin sunan garin Hadejia wanda mutane suka fi sani a wannan lokaci, gari ne wanda aka gima shi tun asalin hausa bakwai da banza bawai, gari ne wanda ya kafu tun Alif Dubu daya da dari takwas da takwas (1808)

Yana daga cikin kasashen da Bayajidda ya kafa, gari ne na hausa da fulani, gari ne wanda suka taso suna shuke shuke, kiwo da sauransu.





*Ayusher Muhd*



*ZAFIN RANA*

Haske Writers Association 💡

Na Ayusher Muhd🏹


Shafi na biyu



Junaid suna shiga ya shiga kallan gida cikin tsananin jin dadi, dan abin ya birgeshi, yaje zai shiga cikin falo ne ya hango kuyangun gidansu.

Mamaki ne ya kamsashi ya nufo gun yana cewa "Hari kece?"

Juyowa tai da sauri jin muryarsa, ta nufo inda yake tace "Yarima!"

Kallanta yai yace "me kike anan?"

"Da sassafe aka kawomu nan akace mu zauna zaka zo."
Ba tare da yai tunanin komai ba yace " ke dawa?"

Nan ta shiga kiran ragowar kunyangun, yana ta dariya, cikin gidan ya shiga yana tattaba abubuwa, mamaki sosai yakeyi ta yanda duk wani abu dayake fadawa Mahaifinsa yanaso akwaishi a wannan gidan, kallan saurayin nan yace "kai ya sunanka?"

"Azi sunana Yarima."

Junaid ya kalleshi yace "Ali ko Azi?"

Yace "Azi."

Dan dariya yai sannan yace " kace zaka sa a siyomin wannan abin?"

Azi yace "eh yarima amma sai ka zauna anan ka kwana baka kuka ba."

Ba tare da damuwa ba yace "to, amma in mun tashi zamu gun Mamana
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download ZAFIN RANA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album