Join Our WhatsApp Group

SIRRINA Complete Hausa Novel Document by SIRRINA


SIRRINA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 7745



SIRRINA

Reading Time: 0 Hours

Added On: 24, Jun 2023

Author: Khadija Muhammad Shitu ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : +234 911 744 0993

Author Phone : +234 911 744 0993

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 41.62 kb

File Type: txt

Views: 981+

Download: 217+

Last download: 5 days ago

Description/Story: *SIRRINA*


*_Khadmah K_shitu🦋_*

_FREE BOOK_

*[2023]*

_Wannan littafin sadaukarwa ne gare ki lishat oum neehal, ina miki fatan Alkhairi._
Ina miƙo gaisuwa ta gare ku Lailat Abdullahi, Gimbiyar AMB, Princess Khadija,Sarauniyar _Jarumai,Nanakhadii duk ina muku fatan Alkhairi._

*_ƊANƊANO_*


*BISMILLAHIR RAHMANUR RAHIM*


Kallo ɗaya Zaka Mata kasan ba chikakkiyar mutum bace! Tsaye take riƙe da madubin tsafin ta, tana hango Yanda Sahash Ke kokarin ƙona Mata fuska duk ta Hada zufa, Wani nurmushi ne ya subuce Mata ta shafo gefen fuskar ta, tare da zama Bisa makeken Gadon ta, Madubin Nata ta ajiye ta nufi ban daki, wanka ta shiga Bata jima ba ta fito sanye da wata Riga Mai Fadi da Alama rigar wanka Ce, gashin ta ta Fara tsanewa, kafin ta shafa Wani Mai Baƙi sai ga gashin ya bushe tana kammala shafa Mayuka kala-kala a gashin, ta Saka wata doguwar Riga milk Kamar gown ta sha adon zinarai, sannan ta ɗauko alkyabba maroon ta Saka Daga Bayan doguwar rigar Na Ja ƙasa.

Tun da ta nufi hanyar fada bayi Ke zubewa cikin tsananin girmamawa Suna gaishe ta, Daga hannu take yi tare da sakar musu murmushi Har ta karasa fadar ba tare da Wani yayi yunkurin yi Mata iso ba ta shige kai tsaye, zaune ta Samu mahaifin Nata Bisa kujera ya hakimce Yana sakar Mata tsadadden murmushi, risinawa tayi ta gaishe sa ya amsa cikin tsatsar kulawa kafin yace “Yake wannan wannan kyakykyawar gimbiyar, Ko akwai abun da kike bukata gurin mahaifin ki?” Dago bulalen idanuwan ta tayi, cikin shagwa‘ba tace "Mai martaba Ina so in fita yawo Kuma nida Risha Kawai Bana son Wani ya buyo mu." Ƴar dariya yayi cike da ƙaunar Yar tasa yace "Toh shike nan Amma Ku Kula." cikin murna ta sumbaci goshin sa, ta fice da sauri sashen ta ta koma ta Kira Sunan Risha Sai gata ta bayyana cikin ladabi ta durkusa, tare da Fadin “Ranki ya Dade umarnin ki nake Kira.” "Ki shirya ina so zamu fita zaga gari yanzu". Cikin girmamawa ta Kuma Faɗin "Ai ranki ya Dade Yanzu ma a shirya nake zamu Iya tafiya, in Har kina bukatar Hakan." Tana Gama Fadin haka Aliya ta fito, Ita Kuma ta biyo ta a Baya Wani Farin doki ne ajiye dai-dai bakin sashen Nata, Sai Wani Farin Shima Dan Dai Bai kai Na gimbiyar ba Aliya ta Hau Nata sannan Risha ma ta Hau, cikin sauri fadawan ta suka taso ta Daga musu hannu, Risha tace "Gimbiya Bata buk’atar rakiyar Kowa". Da sauri suka Bata hanya cikin girmamawa, Daga haka suka Fara tafiya.

_ƘASAR YALAZ_
Ƙasar yalaz ƙasa ce da ta kasance ƙasar mayu, sannnan ƙasar tana da masarautu guda ukku Masarautar Manaaj itace babbar masarauta mai ɗauke da ɗunbin tarihi, sun kasan ce suna da yalwar arziƙi, babu ruwan wani da wani kowa na rayuwa cikin salama mafi akasarin mayun masarautar suna da ƙarfin sihiri sosai, uwa uba kyawu ko wane maye yana chanza suffa, zuwa kyakykyawar suffa saidai yawancin su ƙwayar idanun su blue ce ko yellow sannnan yanayin tafiyar su a lanƙwashe zai tabbatar maka da ba chikakkun mutane bane, sun kasance suna bautawa wani gunki da suke kira da Abin bauta Mihar sannan ga baki ɗaya mayun ɗai-ɗaikun su ne, ke shan jini domin kaso tamanin cikin ɗari basa sha, suna da adalin sarki kuma jarumi jajirtacce, sarki Zahir yana gudanar da mulki cikin adalci da kuma izzar sarauta matan sa biyu Sarauniya sarah ita ce uwar gida sai Sarauniya Kunjam ,kunjam tana da yara mata biyu Sahash sai Sanam sanam nada shekara huɗu aka haifi Aliyaa, tun asali sarki zahir yana zaune da sarah ne, mace mai kirki ga tsananin kyawu Sarah tana da wani matsanancim kyau mai natsuwa tana da manyan idanuwa masu ɗauke da ƙwaya blue, idanuwan ta na matuƙar tafiya da zuciyar mutane.
Sarki zahir ya aure ta ne a dalilin Aminin mahaifin sa Tsoho Arar tun da suka yi aure bata taɓa haihuwa ba hakan yasan ya bayan shekara bakwai aminin sa yayi masa tayin ɗiyar sa kunjam babu ɓata lokaci ya auri kunjam, duk da auren kunjam da yayi bai daina nuna wa Sarauniya Sarah tsananin ƙaunar sa gare ta ba, hakan yasa kunjam ta kasance cikin matsananciyar tsanar Sarah, kullum a koda yaushe burin ta taga bayan sarah sannan taci buri ta samu haihuwar ɗa namiji da zai gaji sarki sai dai abun baƙin cikin ta haifi mace, sai dai tun yarinyar ta sahash nada shekaru biyu ta samu wani cikin farin ciki gun ta ba'a magana, sai dai anyi rashin sa'a a wannan karon ma mace ce ta haifa, jin daɗin ta ɗaya mai martaba na nuna ƙaunar sa gare su, hakan yasa ta rage damuwa sai dai fargabar ta ɗaya sarah ta haifi namiji, ana cikin haka sanam ƴar ta takai shekara biyu, kwatsam sai ga ciki ya bayyanar ma sarah baƙin ciki da tashin hankali kamar kunjam tayi hauka, gashi sarki ya ɗauki soyayyar duniya ya ɗaura kan sarah da cikin ta kuma ƙarara yake nuna hakan daga lokacin wutar ƙiyayyar sarah ta ƙara kunnuwa zuciyar kunjam har ta yaran ta ta hana su koda shiga sashen sarah, tun lokacin da Sarah ta haifi yarinyar ta Mai martaba ya ɗauki ƙauna da soyayyar duniya ya ɗaura kan aliyaa.
A wannan lokacin kunjam tana fitowa ƙarara ta nuna ƙiyayyar ta gare su, tsoron ta ɗaya sarki dan tasan shi ɗin ba kanwar lasa bane,hakan yasa take shakkar ƙuntatawa Sarah, tun tasowar Aliyaa ƴan uwan ta ke nuna mata tsananin ƙiyayya hakan yasa ta ja jikin ta da su dan kwata-kwata bata zuwa koda inda suke, ita Allah ya yita tun tasowar ta tana ƙaunar rawa dan ta iya sosai, gefe ɗaya mahaifin ta na koyar da ita faɗa a kuma samun ƙarfin ikoh duk da dama tana da wani irin ikoh mai ban mamaki, gashi ta zarce mahaifiyar a kyau an abun ya haɗe mata, ga uwa ga uba hakan yasa su sahash da kunjam kulkum suke ƙoƙarin kai farmaki ga kyakykyawar fuskar ta, kuma basa ita ɓoye matsananciyar ƙiyayyar su gare ta da mahaifiyar ta a koda yaushe tana zuwa gun kakan ta tsoho arar yana ƙara mas sihiri da kuma kariya, shi yasa aka gaza cin galaba kanta.
Sannan Aliyaa na da wani irin ƙarfin iko na wucin gaban misali, kowa na alaƙanta hakan ne sanadin Kakan ta tsoho ARAR, sannan kowa ya san da cewa babu mayu daban-daban masu sheɗanci da tsananin ƙarfin iko kamar na masarautar manaaj, wannan dalilin ya sanya kowa ke burin mallakar masarautar.

Masarauta ta biyu ita ce masarautar Nahaar, masaraurtar nahaar masarauta ce mai ɗauke da mayu kala-kala sannan suna da yalwar arziƙi da ƙarfin iko, sai dai mayun ƙasar suna shan jini suna da wani azzalumin sarki wato sarki Gobrar ga baki ɗaya bashi da burin da ya wuce ya mallaki ga baki ɗaya masarautun da masarautar manaaj da ta Hizaar ya haɗe ya chigaba da mulkar su baki ɗaya gashi kuma yana da ƙarfin iko sai dai bai ma ko kama ƙafar, sarki zahir ba.
Hakan yasa a koda yaushe ya cikin tada fitin-tinu, sai dai duk makircin sa yana shakkar sarki zahir yaran sa biyu, Karan Sai Arman su kan su yaran basa ji a koda yaushe suna zaluntar mayun dake ƙar-ƙarshin su.

Masarauta ta ukku ita ce masarautar Hizaar, masarautar hizaar masarauta mai ɗauke da tarihi, mayun sun kasance masu ƙarfin ikoh, sannan suna da ƙarfin iko da arziki suma, saidai masarautar bata kai sauran ba , suna da sarki Ahal kwata-kwata bashi da maƙiyi kamar sarki zahir bashi da lokacin yin wani mulki, a koda yaushe yana ƙoƙarin kaiwa sarki zahir farmaki kwata-kwata baya ƙaunar sa, sabo da a da yaso sarauniya sarah amma ƙememe tsoho Arar ya hanashi auren ta, ya bawa sarki zahir.
Yana da makirar mata da yara biyu duka maza Razan sai Tazaan yaran sa azzalumai ne sosai sannan mahaifiyar su kullum cikin makirci take wa kishiyar ta dan bata taɓa haihuwa ba.

Duk masarautun ukku ko wace masarauta nada tambarin ta, MANAAJ suna da tambari a hannun su kafin a kai wuyan hannu An rubuta manaaj, kowa dake masarautar yana da shi. NAHAAR suna da tambarin su a tafin hannu, kowa dake cikin masarautar yana ɗauke da tambarin. HIZAAR Suna ɗauke da tambarin su ne a bayan wuya, kuma kowa dake masarautar yana da tambarin.



K_shitu🦋



*SIRRINA*


*_K_SHITU🦋_*


*_SHAFI NA ƊAYA DA NA BIYU._*
*P 1-2*


Gudu suke yi na fitar hankali cikin baƙin dajin, babu abun da kake ji sai kukan tsun-tsaye da na namun dawa. ja sukai suka tsaya dan babu hanya, ruwan dake gaban su tsayin shi yafi ƙarfin suce zasu zagayo, saukowa gimbiya Aliyaa tayi daga bisa dokinta, hakan yasa itama Risha ta sauko. wata bukka suka nufa daga chan gefen dama sai dai a mamakin su bukkar a buɗe take, bayan sun san ko da tsoho Arar yazo a koda yaushe rufe take, babu alamun wani a ciki, hakan ya suka ƙarasa sai dai da alama kamar yana ciki.
Tsayawa Risha tayi ita kuma ta shige ciki, zaune ta tarar dashi yana ta faman bincike-bincike, cikin sauri ta ƙaraso tare da faɗin "Ranka ya daɗe! lafiya kazo a wannan lokacin. bayan nasan sai zamu haɗu ko wani abu ya taso a masarauta kake zuwa, shin ko da akwai wani muhimmin abu dake faruwa ne?"
Cikin damuwa ya dube ta sannan ya furzar da iska yace "Ina kike ƙoƙarin zuwa baki sanar dani ba, ko akwai wani abu dake faruwa dake ne?" da mamaki take ƙare masa kallo cikin nuna Ƴar damuwa tace;
"Babu Abun da yake Faruwa ina so naje nayi wani bincike ne shi yasa".
"Bincike kuma Aliya! akan me?"
"Babu komai ina so na samu wani ƙarfin iko ne nagani ta yadda ake samun sa a wani littafi ko akwai wani abu da ba dai-dai ba." Numfashi yaja yace,
"A safiyar yau wani yayi yunƙurin cutar dake! ko akwai wani baƙon abu da kika gani?" jim tayi kafin tace gaskiya babu kowa sai dai Sahash! ita kaɗai ce tayi yunƙurin ƙona mun fuska". "Aliya! kuma shine baki sanar dani ba?"
"Kayi haƙuri gani nayi ba sabon al'amari bane a garemu."

Jin-jina kai kurum yayi, cikin sigar gargaɗi ya fara mata magana "Ki sani a yau da ban zo nan na dakatar dake ba, da kin rasa dukkanin ƙarfin ikon da kike dashi! wannan littafin baki yi tunani a ina aka same shi ba, baki yi mamakin ganin shi kwatsam a ɗakin ki ba. baki tsoron abun da zai je ya dawo. A cikin y'an kwanakin nan kina wasu abubuwa na gaza gane kanki, ki sani akwai manya-manyan matsalolin dake shirin kunno kai a lokacin da ba ayi zato ba! Mahaifiyar ki Tana cikin matsala sai dai a iya bincike na ban fahimci komai ba, ya kamata kiyi taka tsan-tsan zan saka miki hodar iko a madubin tsafin ki. dan a lokuta da dama idan kina kallon sahash tana ganewa, ya zame miki dole ki kiyaye dan akwai mafarkin da nake yawaita yi akan Naz... masarautar Nahaar akwai wani ɓoyayyen tuggu da suke shiryawa Ki sani kece kece! Aliya kece mgajiyar masarautar manaaj sarki zahir mahaifin ki ya faɗi hakan a gaban kowa, hakan yasa maƙiya suka taso ki gaba ana burin ganin bayan ki". Numfashi ta sauke a hankali jin ya ambaci mahaifiyar ta, sannan tace "Ranka ya daɗe ka ce Naz baka ƙarasa ba" "ina so nace nahaar ne." gyaɗa kai kawai tayi, alamar gamsuwa Sun jima suna tattaunawa kafin daga bisani ya saka mata farar hodar ikon. har zasu rabu ya kira sunan ta "Aliya! ki kiyaye kisani a koda yaushe ba sahash kaɗai ke ƙoƙarin ƙona miki fuska ba, sa'a kawi suke neme kuma jin san cewa babu magajin da zai iya gadon ko wace masarauta in har yan da wata tawaya, ki kiyaye a koda yaushe ana burin ganin bayan ki."
jin-jina kai kawai tayi sanan suka rabu...

Cikin tsananin ɓacin rai take farfasa duk abun da ta gani a ɗakinta, lokaci ɗaya ta fita a hayyacin ta hannuwan ta duk ta tsattsage ga jini na zuba wata kwalba ta ɗauka, ta buga da ƙasa nan take ta tarwatse. jin ana buga ƙofar ya sata nufar ƙofar cikin wani ɓacin ran, sai dai kafin ta ƙarasa ta taka kwalbar da ta fasa, zubewa tayi ƙasa jin wani raɗaɗi na ratsa ta.
Kifewa tayi fasassun kwalaben suka soki jikinta, wani irin ihu tayi hakan yasa Sarauniya kunjam da ke bakin ƙofar ta faɗo ɗakin jikinta har tsuma yake, a gigice ta ɗaga duka hannayenta sama ta ɗauke ta sama, sannan fa jefar da ita kan gado. cikin gigita take faɗin "Sanam! mai kike son mayar da kanki? me ya sameki ko Karan ne?" lokaci ɗaya ta jero mata waɗan nan tambayoyin waɗan da suke barazanar fasa zuciyar Sanam ɗin. cikin ƙaraji da mugun kishi ta fara magana "Na rantse da wannan duniyar tamu! bazan taɓa ƙyale Karan da Sahash ba dole na ɗauki mummunar fansa akan cin amanar da suka aikata min. ya zama dole su biya abin da suka aikata! Ni sanam in har na barsu haka ni ba jinin Masarautar zahir bace!"..... Da wani irin mamaki take duban ta wanda ya kasa ɓoyuwa kwata-kwata sai duban sanam ɗin take wacce ita kuma, wani matsanancin ɓacin rai ne kwanche a kan fuskar ta wanda ya bayyana zata iya aikata komai a halin yanzu dan tana da muguwar zuciya! Ajiyar zuciya sarauniya kunjam ta sauke dan tasan bata da kalmomin da zata faɗawa sanam zuciyar ta tayi sanyi, dan a halin yanzu ta fara karaya da al’amarin su daga sahash ɗin har Sanam ko waccen su idon ta ya rufe mulki take buƙata da ƙarfin ikoh. Sahash idon ta yafi na kowa rufewa tsabar kwaɗayin mulki da ƙarfin iko, jiya sun tattauna sosai da sahash tayi mata bayani akan yanda take ƙoƙarin mallakar karan, dan samu wani ƙarfin iko a tattare dashi saidai bata yi tunanin sheɗancin ya kai haka, sai yanzu zuciyar ta ke hararo mata abubuwan da suka shuɗe a shekarun baya, da waɗan da take a raye abubuwan suka faru da waɗan da mahaifin ta ya sanar da ita tasan itace ta ɗaura su akan wannan turbar amma yanzu ta fara sarewa, tashi tayi ta fice daga ɗakin tana girgiza kai dole ta dakatar da wannan wutar ƙiyayyar da ta hango tana ruruwa a...


Read / Download SIRRINA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album