Join Our WhatsApp Group

MEEMA FAROUK PART 1 Complete Hausa Novel Document by MEEMA FAROUK PART 1


MEEMA FAROUK PART 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 76039



MEEMA FAROUK PART 1

Reading Time: 6 Hours

Added On: 05, Nov 2023

Author: Nafisat Isma'il Lawal ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 387.51 kb

File Type: txt

Views: 566+

Download: 399+

Last download: 2 hours ago

Description/Story: [08/10, 2:50 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
                   💎💎💎


*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._













             *NO_1 & 2*

             *RIYADH NORTH*
         Hannun ta riƙe da bairo tana juya wa a kan book ɗin but ta kasa rubuta komi, tunani ne sosai a ranta wanda ya hana ta saƙat, shin yaushe ne zata kasance cikin farin ciki? Har yaushe ne komi zai wuce a rayuwar ta? Komi ya koma mata kamar baya? Idan ta zauna tana irin waɗannan tunanin sai taji da ace ba'a haife ta ba...

            Faɗin da bairon nata yayi ne ya sanya ta dawo cikin hayyacin ta, idanun ta a kan bairon amma ba ta da alamun ɗauka, sai ta tsira mishi Sexy eyes ɗin ta a ɗan soconni kafin ta janye su tana jan ajiyan zuciya, lumshe idanun tayi a lokaci ɗaya tana buɗe su, ko kaɗan fuskar ta babu ɗigon fara'a wanda dama ta jima rabon da ta ganta cikin farin ciki, idan kuwa ka ga tayi murmushi sai dai tana gaban Abee ɗin ta ne, wannan kuma domin farin cikin shi take yi, ba ya ga haka babu wanda ke ganin dariyan ta bare murmushin ta a yanzu, ko yaushe a yanayi ɗaya take, walau farin ciki ko baƙin ciki, abin har ya zame mata jiki

Tashi tayi tana saka room silifers ɗin ta da ta zame su daga ƙafafun ta, sai ta taka a hankali ta nufi bakin windown ɗakin ta, hannayen ta ta sanya ta zuge cootin ɗin wanda haske ya bayyana a cikin ɗakin da ada babu, kanannaɗe hannayen ta tayi a ƙirji tana bin wajen da kallo, yayinda ta faɗa duniyar tunanin da ya zame mata jiki ko yaushe, tana tuna abubuwan dake faruwa a rayuwar ta

Daga ita sai guntun riga me ruwan Powder, dressed sleeping ne, sai gashin ta da ta ɗaure shi a ƙasan ƙeyanta ta sanya baƙin hula me kauri wanda ya fito mata da tuntun gashin nata, har kunnen ta ta rufe a cikin hulan wanda da alamu garin da akwai sanyi ne, duk da haka be sa ta sanya kayan sanyi ba, illa hulan dake kanta na sanyin, kuma ba wai don ba ta jin sanyin ba, sai dai ta saba da yanayin ne.

          Ta jima a nan a tsaye kafin ta janye idanun ta tana wuce wa cikin Toilet, wanka tayi ta fito ɗaure da Towel a jikin ta, a lokacin ne ake mata Nocking a bakin ƙofar ta

"Na'am". Tace tana me zama gaban dressing mirror

Buɗe ƙofan aka yi wata budurwa ta shigo da uniform a jikin ta, da alamun ƴar aiki ne don sai da ta duƙa ta gaishe ta kafin cikin harshen larabci tace, "ji'itu liru'uyatiki, li'annani ƙultu laki lah takruj".
( "dama na zo duba ki ne saboda naji ki shiru baki fito ba".)

Bata kalle ta ba ta bata iznin tafiya

Sai ta tashi ta fice

Ita kuma lotion ta shafa a jikin ta tare da Powder, sai ta miƙe ta nufi wardrobe ɗin ta, buɗe wa tayi ta ciro kayan da zata saka, ta shirya cikin riga da wando masu taushi brown color, sai ta ɗaura after dress baƙi sannan ta yane kanta da gyalen shi, flet shoes ta saka a ƙafafuwan ta sannan ta ɗauki handbag ɗin ta ta fito. Steps ta taka ta sauka ƙasa ta nufi ɗaya daga cikin ɗakunan

Bata kai da shiga ba wata mata ta fito tana sanye da fararen kaya, da alamu Nurse CE ita

Sai ta kalle ta tace, "Abee".

Murmushi matar tayi mata tace, "jasadahu khafifun jiddan, wal'aán huwa naà'im". ("jikin shi da sauƙi sosai, yanzu haka ya samu barci ne".)

Bata ce komi ba ta ɗago hannun ta tana duba wrist watch ɗin ta, sai kuma ta juya ta nufi kan dainning, zama tayi tana ajiye handbag ɗin ta saman dainning ɗin, sai ta saka hannu ta janyo Cup ta haɗa tea rabin Cup, ta soma sha a hankali duk da akwai zafi, sai dai hakan be dame ta ba. Cikin ƙanƙanin lokaci ta gama tana miƙe wa tsaye

A lokacin ne Nurse ɗin nan ta fito daga kichen riƙe da faɗeɗen bowl a hannun ta

Fuska ba walwala kamar ko yaushe tace da ita, "a'atani bihi jiddan min fadlik". ("ki kula dashi Please".) Bata jira cewar ta ba ta juya tayi hanyar fita, tana fita compound ɗin gidan ta shiga motan ta ta fice. Tafiyan mintuna goma ya kaita cikin school ɗin su, kai tsaye department ɗin su ta wuce, tana yin parking ta fito ta wuce class ɗin su

A lokacin babu wasu mutane a ciki sosai, sai ta samu wuri ta zauna a gaba ta ciro wani book tana duba wa

Har Malamin ya shigo ya soma musu karatu babu wasu mutane sosai

Hankalin ta na kan malamin har ya gama ya fita

Time ɗin ne waɗanda ke gefen ta suka samu damar mata magana, Esha ce tace, "Hello, my beauty, are you already here today?" Ta ƙare maganar tana murmushi

Ɗago kai tayi ta kalle su, memakon ta bata amsar sai tace, "where is Zamiya?"

"Today she will not come". Cewar Ummu Hani

"Why? But she didn't inform me?"

Ummu Hani Said, "you know the pain she is going through, today she is suffering."

"Let's go check on her before the teacher comes in."

"Ok".

Suka tashi su ukun suka fice, kai tsaye Hostel ɗin makarantan suka wuce, room ɗin da Zamiya take suka nufa, until they were Nocking before she opened it for them

Seeing them, she jumped up and hugged them happily

Esha na dariya tace, "Oh are you okay? Let's go back".

Hararan ta Zamiya tayi tana turo baki tace, "wlh I don't feel comfortable, glad to see you".

Duk dariya suka yi ban da Meema dake bin su da kallo, duk da a ranta tana jin farin ciki, amma kuma baza ta iya nuna shi a fuska ba

"Let's come in". Tace dasu tana yin gaba

Zama suka yi a kan sofa, inda Zamiya ta dubi Meema tace, "My Beauty What about Abee's Body?"

"Alhmadulillah easily".

Ummu Hani Said, "By the way, we forgot we didn't hurt him. Please I'm sorry."

"It's alright". Cewar Meema tana duba wayan ta, sai kuma ta ɗago tana kallon Zamiya tace, "what about your body?"

"Alhmadulillah, I was relieved. I wanted to go to school but I didn't get a chance."

Esha said, "Did you hear anything. You don't care about your body, do you?"

Tana dariya Zamiya tace, "Allah has made it easy for me. Let's get ready and go together."

"You are not enough wlh, you will not follow us". Esha tace hakan tana hararan ta

Ummu Hani na dariya tace, "where is your water? It's easy for her, please let her go."

"is what I see like her body". Zamiya tafaɗa tana dariyan itama

"Get up and let's go". Cewar Meema

"No there is still time for us Meema, sorry stay please?" Tayi maganar da marairaice fuska

Kallon ta Meema tayi tace, "We're going to be late for class. It's too late for us to leave, but we'll be back soon, God willing."

"Yeah then, but what can I cook for you?"

Esha tayi tsagal tace, "How are you Can you cook for us? "No, we forgive you."

"I can wlh". Zamiya Tayi maganar cikin shagwaɓa

Dariya Ummu Hani tayi tace, "The king of racism is not in front of Ummee you are".

Cike da gajiya wa Meema dake kallon su suna dariya tace, "let's go please".

Sallama suka yi mata suka bi bayan Meema da har ta fice ma, ita kuma Zamiya ta rako su har bakin ƙofan ɗakin ta sannan ta koma

Suna fita wayan Meema ta soma ringing, ɗago wa tayi tana kallo sai taja tsaki tana sauke hannun ta ƙasa suka ci gaba da tafiya

Esha da ba ta iya shiru tace, "Is that Ishaq?"

Meema bata kalle ta ba bare ta tanka ta

Sai ita kuma ta sake cewa, "but why do you want to change him? Please don't let your worries affect your love, you are suffering a lot from it, Please do peacking you see he calls again".

"Hmm". Kawai Meema tace bata kula ta ba

Ummu Hani Said, "here he is".

Duk ɗaga kai suka yi suna kallon inda Ummu Hani take kallo

Wani kyakykyawar Balaraben saurayi ne tafe zuwa wajen su, fuskar shi ɗauke da yalwataccen murmushi ya iso wajen su

Daga Ummu Hani har Esha tsaya wa suka yi wajen sa suna amsa sallaman da yayi musu

Ita kuwa Meema har ta yi gaba zata wuce, sai Esha ta janyo ta baya tana cewa, "Please O'o Meema".

Hararan ta Meema tayi bayan ta dakata daga inda take

Shi kuwa kallon ta kawai yake yi yana doka murmushi

Esha says, "we'll pass the class, when you're done find us in class".

Daga haka suka yi gaba ita da Ummu Hani

Kanta a ƙasa bata kalli inda yake ba

Hakan yasa ya ƙarisa kusa da ita ya tsaya yana faman kallon ta, sun ci mintuna biyu babu wanda ya furta komi

Sai ta ɗago kanta ta zuba masa idanun ta, ganin kallon da yake yi mata sai ta balla masa harara tana cewa, "Please I will be late for class. "

Cikin sanyin muryan sa yace, "why Beauty did you change me? Wlh I really love you! Why do you want to part with me?"

Cikin ido take kallon shi yayinda ta sake ɗaure kyakykyawar fuskar ta tamau kafin tace, "please let's stop saying that now, let's do it later".

"No, I do not agree. I cannot leave here unless you answer my questions. You know that I love you and this decision you have taken has made me very sad. How do you think I can part with you after tasting your honey love? Wlh I love you Meema, if you want I will kneel in front of you because I will apologize". Ya ƙare maganar kamar zai yi kuka

Itama fuskar ta da alamun gajiya wa in a calm voice she said, "I told you we will talk later. Please let Me go".

"Ok When?"

Dafe goshi tayi tana kallon sa tace, "Ishaq problems".

Dariya yayi yace, "on your love I am crazy".

Taɓe baki tayi kafin tace dashi, "by tomorrow insha Allah". Tana gama faɗar haka ta wuce ta bar shi nan. Kai tsaye aji ta wuce, tana zama malamin da suke dashi ya shigo class ɗin.




              Zuwa ɗaya suka sami break, sai suka wuce Hostel wajen Zamiya, a can suka yi sallah suka ci abincin da ta girka musu, sai faman hira suke yi suna dariya amma banda Meema da sai jefi-jefi take saka musu baki.

              Three O.clock suka koma class suka yi lecture ɗaya, sannan kowa ya wuce gida.

               Meema na koma wa gida tayi parcking ta fito tayi cikin gidan, gaba ɗaya a gajiye take amma hakan be sa da ta shiga ta wuce ɗakin ta ba, ɗakin Abee ta wuce ta shiga da sallama

Nurse ɗin dake kula dashi ta amsa mata sallaman tana faɗaɗa fara'an ta tare da mata maraba

Da kallo kawai ta bi su daga ita har Abee ɗin nata ta kasa amsa wa, sai dai gaba ɗaya fuskar ta ta sake haɗe wa ganin ta da poo a hannun ta, "taya ma za'a ce wata ce zata riƙa kula da mahaifin ta a irin wannan yanayin?.."

Muryan Abee ɗin ta da ya ratsa mata kunnuwa yasa ta ƙifta idanun ta da suka kawo ruwan hawaye, cike da ƙunci a zuciyar ta ta ƙarisa wajen sa

While Nurse Zara tuni ta shige Toilet don plushing kashin da yayi

A gaban gadon ta durƙusa tana kallon sa, sai ta saka hannayen ta ta kamo nashi hannun guda ɗaya, cikin rawan murya tace, "Abee.."

Murmushi ya sakar mata a hankali yace, "Ummy why are you crying?"

"Nothing Abee, I'm not crying". Ta ƙare maganar hawayen ta na silalo mata saman kunci

Girgiza mata kansa yake yi, cike da raunin murya na wanda ciwo yaci sosai yace, "Please Ummy I beg you to stop crying ok? I'm not happy to see your tears."

Tamke bakin ta tayi tana saka hannu biyu ta share hawayen tana faɗin, "ok Abee I'm stop, you see?" Sai ta ƙare maganar da sakin murmushin da ya bayyana jerin ƙananun fararen haƙoran ta, wanda har dumples ɗin ta suka samu damar fito wa

"Ok, did you go to school today?"

"Na'am Abee, I went to school, but I'm sorry I didn't come in to check on you. "

Murmushi yayi yana gyaɗa kansa yace, "don't worries, go eat and rest ok?"

Amsa mishi tayi kafin ta ɗago hannun nasa a hankali ta sumbace sa, sannan ta tashi daga durƙuson da tayi, a time ɗin ne Nurse Zara ta fito daga Toilet ɗin, kallo ɗaya Meema tayi mata ta ɗauke kai tana fice wa

Ita kuma Nurse Zara ta gyara mishi pilown da ya sauke kansa, sannan ta tambaye sa "ko da abinda yake buƙata kuma?"

Girgiza mata kai kawai yayi

Sai ta juya ta ɗauko airfreshna ta fesa a ko ina sabida warin kashin da ya ɗuma ɗakin ya fice, bayan ta gama ta fice a ɗakin.






                  ******

               Da kuka Meema ta koma ɗakin ta, tana shiga ta faɗa kan gado tana ci gaba da rera kukan nata, wanda inda da sabo ya rigada ya zame mata jiki, a kullum tausayin Mahaifin nata ƙara yawa yake yi a zuciyar ta, ta kasa saba wa da wannan ƙaddaran da Allah ya ɗaura masa, kullum gani take yi tamkar zai tashi ya koma kamar da, ya riƙa mata wasa kamar yanda ya saba yin mata, su riƙa cin abinci tare suna wasa da dariya tare, amma kuma ciwo ya yanke mata wannan ƙauna da jin daɗin, wanda tana ganin babu ranan da zata sake shiga cikin farin ciki idan har ba mahaifin ta bane ya warke ya koma kamar da ba, ba ta ganin akwai ranan da walwala da jin daɗin ta zai dawo

Hawayen ta ta saka hannu tana share wa yayinda wasu suke sake ɓullo mata, babu abinda ke sake bata haushi illa yanda mahaifiyar ta ta kasa kula da Abee ɗin ta, sai wata ce take iya cin kashin sa taci fitsarin sa, sannan kuma ta ƙetara muhallin da ba nata ba, a kullum sake jin tsanar mahaifiyar ta take yi, tana ganin kamar har da baƙin cikin ta Abee ɗin ta ya kasa samun lafiya, ko da be faɗa mata ba ta san yanda yake jin ƙuna da azaban tafiyan ta, ta zaɓi son duniya da son zuciya ta...


Read / Download MEEMA FAROUK PART 1

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album