Join Our WhatsApp Group

ZUMUNCINMU A YAU Complete Hausa Novel Document by ZUMUNCINMU A YAU


ZUMUNCINMU A YAU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 201561



ZUMUNCINMU A YAU

Reading Time: 16 Hours

Added On: 04, Nov 2023

Author: Aisha Ya'u Kura ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 1.11 mb

File Type: txt

Views: 1431+

Download: 2140+

Last download: 9 hours ago

Description/Story: [04/12 09:41] Meela Adeel: 1⃣
° *ZUMUNCINMU A YAU* °
By Aysha Ya'u Kurah

*FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*

'''BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM'''

Sadaukarwa ga mahaifi na kwarai *LATE ALHAJI YA'U KURAH* Allah SWT ya jikanka ya kai rahama kabarinka..

*SHIMFIDA*

"Assalamu alaikum" Ta faďi karo na uku cikin siririyar muryarta,
cikin ďaga murya taji ance,
"Wai wacece ta ke ta kwaďa mana sallama ne haka?!"
A hankali jikinta na rawa ta amsa.
" Ni ce."
"Tooo!! Sannu NI CE, me ya kawoki?"
Cikin rawar murya ta ce "Mamma ce ta aikoni in kawo muku abinci."

Daga cikin ďakin ta jiyo muryar dattijon wanda ya bata tabbacin shima yana ciki. "Toh ki ce an gode, je ki ďauki naira ashirin a saman tagar ďakina kiyi gaba."
A hankali ta sauke ďankwalin da aka ďaure kayan a ciki ta kwance ta fito da sababbin samirun tuwo da miya ta cire ďankwalinta tace "Nagode BAFFA, Allah ya saka da alkhairi." Ta ďauki ashirin ďin ta fita cikin k'unan rai.

A hanyar da zata sada ta da kofar gida taci karo da su Husna rik'e da manyan kuloli suna tafe suna nishi da kyar, rab'ewa tayi ta basu guri dan su wuce, suna karasowa dab da ita suka kwashe da dariya haďe da faďin "Nadiya roba-roba."
Badariyya ta ajiye kular hannunta ta shafi kayan jikin Nadiya tace
"Kaiii!! Wannan ba roba bace rai fess ce."
Suka sake tintsirawa cikin shakiyanci suka ce "Su Nadiya bana an samu canji, daga atamfar roba zuwa shaddar roba."

Cikin sanyin jiki tayi gaba tana jiyo ihunsu har suka shige cikin gidan.

Tana fita tayi tafiyar minti biyar sannan ta isa titin da zata roki masu mota su ďauketa da naira ashirin ďin da aka bata, dan in tace zata tafi gida a kafa sai ta kai yamma saboda nisa,
zuciyarta cike take da mamakin yadda zumuncin zamani ya koma,
tun tana karama ta ga mahaifiyarta na fuskantar irin waďannan wulakancin saboda kasantuwarsu talakawa, sau tari takan tambayi mahaifiyarta anya Baffa ne ya haifeta kuwa?

Acikin gidan kuwa, su Husna na shiga babu ko sallama suka faďa ďakin,
zabura Baffa yayi ya sakko daga kan gado yana faďin. "Lale da matana, lale-lale."
Badariyya ta faďa jikinshi tana faďin "Kakus, ina barka da Sallah na?"
Cikin rawar jiki yasa hannu a aljihu ya ciro yan ďari biyar-biyar sababbi ya k'irga goma ya bata,
yatsina fuska ta yi tace "Haba kakus, dubu biyar fa ka bani, ni gaskiya sunyi min kaďan Pizza kaďai zanci da su." Washe baki ya yi yace "To yar lele, an gama." Ya karo mata wasu biyar ďin ta mike a jikinshi babu ko godiya sai ma faďin "Ko kaifa, ai da na sake ka yanzun nan,,,
Husna ta matsa kusa dashi tace " Saura ni kakus."
Dubu goman itama ya bata saboda yasan sakon barka da sallan shi na tafe don tun safe y'arshi mafi soyuwa a gareshi ta kirashi tace zata aiko MUSADDIQ da sak'o, yasan sakon bai wuce na kuďi.
"Ina yayanku? Ko ba tare kuka zo ba?" Baffa ya tambaya yana gyara aljihu.
Badariyya tace "Ka ji kakus a kofar gidannan fa muka sameshi, yana fita muna shigowa dan ya riga Nadiya fita ma." Kallon mamaki yayi musu yace "Aiko bai shigo ba."
Goggo ta rufe kular da ta bude ta ce "Kasani ko ya manta da wani abu ne?"
"Hakane kuma." Ya faďi tare da basar da maganar.
Nan suka hau hira da ciye ciye, sun ma manta da samirun tuwon da Nadiya ta kawo saboda sunsan babu wani abun arziki a ciki.

Zaune take tayi tagumi tana jiran shigowar Nadiya dan tasan in Allah Ya yarda zata samu ko ďari biyar ce a gurin su Baffa na barka da sallah,
Zainab ce ta taso rike da robar abinci tace "Mamma zan kara abinci." Janyota ta yi jikinta tace "Yi hakuri auta, yanzu Anti zata dawo har madara ma sai kisha in kinaso kinji?"
Gyaďa kanta tayi cikin murna ta kurawa kofar gidan ido tana jiran b'ullowar yayarta.

A gajiye ta shigo gidan ta nemi guri ta zauna tana maida numfashi,
da sauri Zainab ta mike ta ďauko mata ruwa, karb'ar ruwan tayi haďe da janyota jikinta tace " Kin ci abinci?"
D'aga mata kai tayi, "Eh naci amma ban koshi ba. Mamma ta ce zaki kawo kuďi a siyo min madara."
A hankali ta ďago jajayen idanuwanta ta sauke kan mahaifiyarta, kallon tausawa juna sukayi sannan suka kau da kawunansu, cikin sark'ak'ak'k'iyar murya Nadiya tace "Mamma na kai musu, Baffa ya bani naira ashirin, ki tayani yi mishi godiya dan ya taimakamin, da a kafa zan dawo gida."
Cikin b'oye b'acin rai Mamma tace "Kai madallah!! Allah ya biyashi da aljanna, gaskiya naji daďi, tashi maza kije kiyi sallah."
Tana kokarin mikewa taji anyi sallama, juyowa tayi haďe da amsa sallamar, suna haďa ido tayi saurin kau da kanta,
Mamma ta mike cike da murna tace "Maraba da Musaddiq, yanzu kake tafe?"
"Eh Mamma ina wuni."
"Haba dai daga tsaye?" Ta faďi haďe da shimfiďa dadduma.
Zama yayi yana sosa k'eya suka gaisa sosai,
kuďi ya zaro a aljihunshi kusan dubu dari biyu yace;

"gashi inji mummy tace a kawo muku" bai jira jin me zata ce ba ya ajiye kuďin ya fice daga gidan da sauri dan yasan in ya daďe a gidan to asirinshi zai tonu..

Kasa tab'a kuďin tayi saboda firgici Kai anya Musaddiq yaji inda aka aikeshi da kyau kuwa?
Wannan kyautar tayi yawa dan tsakanin ta da yar uwarta bai wuce kyautar dubu biyar,

"Nadiya mik'o min wayar can" tace tana mai nuna ma nadiya wayar,
da sauri ta ďauko ta mik'a mata. Hannu na rawa ta fara neman lambar yar uwarta, sai da ta kusa tsinkewa sannan ta ďaga cikin isa da tak'ama,
murya na rawa Mamma tace "ina yini Hajiya"

"lafiya" kadai tace murya can k'asa, bata damu da amsawar ba dan in da sabo ta Saba, sai ta cigaba "yanzu Musaddiq Ya kawo min sak'o shine nace bar..."

Dakatar da ita tayi ta hanyar cewa "ina da abin yi Suwaiba nasan godiya kika kira kiyi, bakomai yiwa kai ne" tayi saurin kashe wayar, cikin mamaki ta ajiye wayar tana duban kuďin zuciyarta cike da farin cikin yar uwarta ta fara sanin muhimmancin zumunci....

Musaddiq na fita ya nufi motarshi ya kashe wayoyinshi ya ta da motar yayi gaba yana nazarin yadda zaiyi ya fahimtar da mahaifiyarshi da kakanninshi muhimmancin zumunci,

A kullum yana mamakin yadda zumuncin zamanin yanzu ya zama sai in kana da kuďi,
yana takaici matuka saboda irin wulak'ancin da Mamma suwaiba da ya'yanta ke fuskanta saboda kawai basu dashi, bashi da wani burin da ya wuce yaga kan zuri'arsu ya haďu, Mai shi ya taimaki mara shi, amma kullum abun k'ara lalacewa yakeyi saboda masu shi ďin basa taimakawa na jikinsu saidai na neman suna..

Mrs Tijjani Shattima...
[04/12 09:42] Meela Adeel: 2⃣
°ZUMUNCINMU A YAU °
BY Aysha Ya'u Kurah               

"Nadiya amshi maza kira min yayanku,
cike da murna ta karbi wayar ta latso number,

Yana zaune ya kifa kanshi a wheel barrow yana tunanin ta inda zai fara,
'Dan kudin dakon da ya samu na Sallah shi ya had'a yayi ma kannenshi kayan sallah, ragowar ya ba mahaifiyarshi tayi abincin sallah,
karar da wayarshi keyi ne ya dawo dashi cikin duniyar tunanin da ya tafi,
hannu ya zira cikin aljihunshi ba tare da ya d'ago ba ya danna ya Kara a kunnenshi,
Assalamu alai-- "hello Ya Hafiz ta katse shi cikin kaguwa,
dago kanshi yayi  cikin firgici yace "Nadiya Lafiya,?
fizge wayar mamma tayi tace "Hafizu kana Ina ne, duk abunda kakeyi ka barshi ka dawo gida, mikewa yayi da sauri ya Sanya silifas dinshi, ya kalli abokin aikinshi yace "Haladu dan Allah ka Mik'a min baron nan gidan oga lukman in har ban dawo da wuri ba,  Haladu yace "lafiya dai ko, "walhy ban sani ba mamma ke kira na, ya karasa fadi yana tafiya da sauri ,
"Allah yasa lafiya haladu ya fadi da karfi dan Hafiz ya kusa karya kwana,
zuciyarshi cike take da fargabar abinda zai je ya tarar a gida...

Hello Baffah, an yini lafiya,
baki har kunne baffah "yace lafiya lau ya sallar,
"sallah alhamdulillah,
"Dan Allah Baffa kace ma su Husnah su biyo MUSADDIQ na aiki Haruna driver,
to bakomai daga ya karaso zansa su taho saboda dare,
"kana nufin har yanzu bai zo ba baffah,
baffah yace "eh to sunce min sun ganshi d'azu amma ni har yanzu bansa shi a idona ba,
ikon Allah ta fadi hade da gyara zama,
ya rigasu fita gida fa, kuma saida na mishi kashedi akan yawo, Yanzu haka yana can gurin abokan banza, amma dai ya basu sak'onka ko? ,

"ko kusa bai basu ba, baffah ya fadi had'e da yak'e wanda yafi kuka ciwo dan ya kosa yaji makwafin kudin da ya ba jikokinshi da Karin wasu a aljihunshi,
"karka damu baffah bari in kirashi inji inda ya tsaya,
"too bakomai Kar dai ki matsa mishi kin San yaran yanzu saida lallami,
haka ne baffah nagode a gaida Goggo,"to zata ji Nima na gode,....

Kiran Musaddiq ta shiga yi, abin ya d'aure mata kai da taji wayoyin shi a kashe, lallai yau zan bala'in sab'a ma Yaron nan, duk fadan da na mishi akan shirman partyn nan baiji ba ko, Allah ya kawo shi gida wallhy Mai rabani dashi sai Allah ta wurga wayar cikin jaka ta d'auki gyale da mukullin mota ta fita...

"ji nake kamar a mafarki mamma, shafar kudin ya sake yi yace
"ban taba tunanin zan rike irin wadannan kudin ba a rayuwata,
Mamma da farin ciki ya mantar da ita damuwa da yunwa tace
"kaidai bari, Allah kenan maji rokon bawa, duk yadda mutum ya kasance cikin kunci da bakin ciki to in ya dogara da Allah sai ya samar mishi mafita,,
Hafiz yace "haka ne mamma, to yanzu ya zamuyi da kudinnan,
"shi nake tunani hafizu,
mu jira babanku ya dawo sai musan abin yi dashi,
  dubu biyu ta ciro cikin kudin tace je kayo mana cefane da wannan muyi abinci kafin ya dawo,

Zainab da ke kwance Kan cinyar Nadiya tace "anty Madara ta, Nadiya tayi dariya tace "kiyi hakuri yanzu za'ayi abinci muci,
mamma na jinsu tayi kamar bata ji ba tace,
"au Hafizu na manta ka siyo ma auta Madara kaji, Nadiya tayi murmushi tace kamar kinsan maganar da takeyi kenan, Mamma tace au haba, taho auta ta kinsan ni namiki alkawari kuma bazan manta ba,,                    haka suka kasance cikin farin ciki a ranar, ji sukeyi kamar babu kamar su a doron duniyar Allah SWT,                     Allah sarki, kud'in da bai wuce kudin naman wani gida ba shi ya Sanya bayin Allahn nan murna har suke Jin babu kamarsu......

Mrs Tijjani Shattima...
[04/12 09:42] Meela Adeel: 3⃣
°ZUMUNCINMU A YAU °
BY Aysha Ya'u Kurah

*******10:56pm******

Zaune yake cikin motarshi kafafunshi duk biyun na waje yana latsa wayarshi da ko minti uku baiyi da kunnata ba,
text din mummy ya karanta yayi d'an murmushi had'e da shafa kwantaccen sajenshi,
rufe wayar yayi ya sake duba agogo,…
gyara zamanshi yayi ya rufe motar yace
"na tabbata yanzu mummy ta isa k'asar Singapore ita da k'awanta cikin mafarki,
tada motar yayi ya karaso kofar gida,
kiran mai gadin su yayi a waya dan ya bud'e mishi gate,  yana tsoron latsa hon ya dawo da mummy cikin kasar Nigeria,
da sauri Mai gadin ya bud'e mishi,  ya shiga yayi parking a gurin da aka tanada dan ajiye Motoci,

Kiran waya ya shiga yi kafin ya karasa kofar parlon..

Badariyya na zaune tana buga game taji land line din dakinsu na Kara,
pause ta danna ta Mik'e tana tsaki,
"hello.. ta fadi cikin muryarta Mai cike da izza da isgili,
"hey Badar zo ki bude min kofa kuma kiyi a hankali Kar mummy ta jiki kin gane ko,
katse wayar tayi ba tare da ta amsa shi ba ta juya ta fita daga d'akin, 

d'akin mummy ta nufa, bud'e kofar tayi ta shiga ba tare da tayi sallama ba, dan a ganin Badariyya sallama ta talakawa ce,,
hasken da ya gauraye d'akin ne ya farkar da mummy daga bacci,
Mikewa tayi hade da mik'a tace "BADAR lafiya,
yaya Musaddiq ne ya kira ni wai in bud'e mishi kofa....

Bawan Allah yana waje yana jiran Badariyya ta bud'e mishi kofa,
ganin da yayi har minti 5 ta wuce bata bude ba ya fara mita cikin zuciyarshi, d'aga wayar yayi da niyyar sake kira yaji ana tab'a kofar,
tura wayar yayi cikin aljihu ya k'arasa kusa da kofar fuskarshi d'auke da murmushi,
"ina kika tsaya ne haka, har hakuri na ya fa---- maganar ta makale mishi a mak'oshi sakamakon ido hud'u da sukayi da mummy,
zaro ido yayi ya had'iye wani mugun miyau,
dariya ya fara yi yana fad'in mummy baki kwanta ba,
tun d'azu Ina nan k'ofar gida a zaune ni da Tinau Mai gadi yana bani Labarin k'auye,
sannan malam--- juyawa tayi ta barshi a tsaye,

shigowa yayi ya rufe kofar ya bi bayanta da gudu,
can gefe ya hango Badariyya tsaye tana mishi kallon raini,
harara ya jefe ta dashi yace "tun kina yar ficiciya kin iya munafurci da makirci Ina ga in kin girma, wallhy kinji haushin rayuwar ki idiot,,

tsaki taja ta wuce d'akinsu,,

Kofar dakin mummy ya karasa,
a hankali ya murd'a kofar ya shiga had'e da sallama,
kusa da ita yaje yayi kneel down ya kamo hannunta yace
"kiyi hakuri mummy, wallahi ba party na je ba, ina gidan su Mahmud tun da na fita daga gida,
sai dare na bar gidansu na dawo kofar gida na zauna,
Dan Allah kiyi hakuri banason wannan fushin please ya karashe a shagwabe,,

bata tanka mishi ba ta zame hannunta cikin nashi tace "bani,,

zuciyarshi na dukan uku uku yace "me zan baki?,

K'ara tamke fuskarta tayi tace kud'in Baffa da na aike ka dashi,

dakewa yayi yace "ni gidan mama suwaiba kika aikeni saidai ko driver kika aika gidan Baffa,

"karka raina min hankali Musaddiq,
kalleni da kyau banyi girman da zan fara mantuwa ba,

dubu biyar na baka ka kaima "SUWAIBA"

dubu d'ari biyu na Baffa, sai dubu Hamsin na k'anwar k'awata "Hajiya Nafeesa dake layin su suwaiba,

bud'e baki yayi yace "Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun,
mummy ai banji duk lissafin da kika min ba, ni dai sunan mama suwaiba kad'ai naji, na bata dubu dari biyu da biyar,
ga dubu hamsin nan a aljihuna na manta inda kika aikeni dashi,
karki damu gobe in shaa Allah da wuri zan kai mata, kika ce gidanta na kusa da gidan mama suwaiba ko?

Wani mugun kallo ta bishi dashi had'e da taune leb'enta,
matsawa baya ya fara yi dan yasan in mummy ta fara taune leb'e to abin da zai biyo baya bazaiyi kyau ba,

dai dai kofa ya tsaya kamar zaiyi kuka "yace mummy kiyi hakuri dan Allah,

cike da takaici tace "Musaddiq Anya rayuwar da ka daukarwa kanka Mai b'illewa ce,
ka zama almubazzari Wanda baisan darajar kudi ba,
in ba iskanci ba me suwaiba zatayi da dubu dari biyu harda d'oriya, wallhy tun muna mu biyu da kai gobe kafin goma na safe kaje...


Read / Download ZUMUNCINMU A YAU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album