Join Our WhatsApp Group

BAKIN KISHI Complete Hausa Novel Document by BAKIN KISHI


BAKIN KISHI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 38618



BAKIN KISHI

Reading Time: 3 Hours

Added On: 02, Sep 2023

Author: Muhammad Lawal Barrister ,

Ebook Compiler : Anam Dorayi

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 189.59 kb

File Type: txt

Views: 794+

Download: 241+

Last download: 8 hours ago

Description/Story: BAKIN KISHI
NA MUHAMMAD LAWAN BARRISTER
Ebook created by Shuraih Usman
Published at www.hausaebooks.com.ng



Bakin Kishi 1 Posted by ANaM Dorayi on 08:16 AM, 29-May-15 Farko Ta



sunkuyar da kanta da sauri kana ta sa tafukan hannunta ta rufe idanunta, "Allah da gaske ka ke Alhaji?". Ta bukata da muryar kunya. "Allah da gaske na ke Zainab...Ni fa mallakar ki ce kawai hutu da kwanciyar hankalina a yanzu. Wai ki na tunanin idan ban mallake ki ba, zan iya ci gaba da kyakkyawar rayuwa? Kin ko yarda da son da nake miki?" Ta yi gaggawar girgiza kai, "Wallahi ba haka ba ne Alhaji." Ta fada da saurin baki, a lokaci guda kuma ta na mai ci gaba da girgiza kan. "Wallahi Alhaji na san ka na so na, kuma na yarda da sonka gare ni, kamar yadda na ke fada maka kullum ne, abu guda kawai na ke jin tsoro a tattare da aurenka...". "Dakata Zainab". Ya katse ta ya na mai daga ma ta hannu, "Ni fa sam-sam ba na kaunar ki rika dawo da hannun agogo baya. Ya kamata zuwa yanzu a ce kin gamsu da abubuwan da na jima da fada miki. Don Allah ki saki ranki, ki manta da wannan...shin wai akwai wanda ya isa ya hana ikon Allah yiwu wa? Ko kuma idan Allah ya tabbatar da ke a matsayin matata duk dunutar nan akwai wanda ya isa ya hana? Wannan abu da ba kanta farau ba." Ya yi kasa-kasa da murya, "Don Allah ki sa tsintsiya ki share wannan daga ranki...komai na Allah ne". "Haka ne". Zainab ta ce da nisawa, "To Allah ya taimake mu, Ya zaba mana abin da ya fi alkhairi gare mu." "Amin". Alhaji ya amsa a takaice, kana ya ce, "Amma fa addu'arki ba ta cika ba." Ta daga kai ta dube shi fuskarta kunshe da alamar tambaya. "Mene ne saura a cikin addu'ata?" Ta bukata. "Sai kin biya zan fada miki." Cewar Alhaji. "Nawa ka ke so a ba ka?" Ta ce da dariya. Ya nuna ta dan yatsa, "Zainab na ke so a ba ni". Ta yi dariya bayan ta sunkuyar da kai, "Ai dama Zainab taka ce, tunda babu wani a zuciyarta sai Alhaji Basiru. Nemi wani abin daban, wannan ka samu." ya yi dariya, "To ai shi kenan...dama ni Zainab ce burina, tunda kuwa tawa ce ai shi kenan an biya ni. A cikin addu'arki kin manta ba ki ce Allah ya kara mana dankon soyayya da kaunar juna ba." Ta kasa dago kai ta dube shi don kunya, "Ai wannan addu'a ita ce a ruhina Zainab kowace rana, a kwance, a zaune, a tsaye ko a tafiye, babu abin da Zainab ke yi sama da wannan addu'ar". Ya ji dadin abin da ta ce don haka sai da ya yi wata yar takaitacciyar dariya kafin ya ce, "Na gode kwarai zainab, kuma ina yi wa Zuciyarki albishir da cewa, ni ma haka na ke, kowace rana, ko yaushe, a cikin kowane lokaci da ke na ke motsi a cikin zuciyata. Babbam fata nashi ne, Allah ya tabbatar da kyakkyawan kudirinmu, a wayi gari a zahiri kin zama mallakata, ba a bafini ba." "Amin". Ta amsa a zuci. A zahiri kuma murmushin jin dadi kawai ta yi. "Ya na ji kin yi shiru ba ki ce komai ba?" Ya ce ya na yi ma ta wani irin kallo. "Na fada fa a zuciyata." Ta ce har lokacin kanta a duke. "To ai ni ban ji ba". "Yanzu ya ya ka ke so a yi?" Ta bukata. "Ina so Zainab ta dago kanta, ta kalle ni ta kuma amsa mini da, amin". Ya ce idanunsa a kanta. Ta dago ta kalle shi. Da sauri sai ta kuma mayar da kanta ta dukar, "Ni ba zan iya kallon ka na fada ba." "To ya ki ke so a yi?" Ya bukata. "A yafe mini na fada a haka." Ta ce da muryar kunya. Ya yi murmushi, "An yafe, fada a hakan". "Amin". Ta fada da wata irin tattausar murya. "Amin me?" Ya dawo da hannun agogo baya. "Amin, Allah ya kara mana kaunar junanmu ko?" Ta ce da karfin hali. "Au tambaya ma ki ke?" Ta girgiza kai da sauri. Su ka fashe da dariya lokaci guda. *** Alhaji Basiru ya yi murmushi a karo na farko tun tsawon kusan mintuna talatin da su ka shafe su na musayar yawu da maidakinsa Hajiya Rukayya. "Ba ki fahimce ni ba Hajiya... Wallahi a cikin wannan al'amari ba na nufin tozarci ko cin zarafi a gare ki, kuma ko da wasa ba..." Dole ka ce haka." ta katse shi murya na rawa, "Dole ka ce ban fahimce ka ba Alhaji...ya za a yi ka fahimta na fahimta, ai abin sai ya yi yawa?" Ta tsahirta ta na kokarin daidaita numfashinta da ke ynkurin dauke wa. Hakan shi ya haifar da shirun wucin gadi a tangamemen falon. Yau kusan watanni biyu kenan da Alhaji Basiru ya fara fuskantar wannan matsala a wajen uwargidan tasa. Koda ya ke ba ya raba daya biyu ya san dalilin da ya jawo hakan, bai wuce shawartar ta da ya yi ba akan zai kara aure. A kalla shekarunsu uku su na zaune, zama na lafiya da kwanciyar hankali, har da arzikin yaya biyu mata (yan tagwaye), amma tun da ya shawarce ta kan karin auren, kwanciyar hankali ta karanta a gare su. Alhaji Basiru ya numfasa bayan dan gajeren tunani da ya yi. Kamar koda yaushe kokarinsa daya ne, duk lokacin da su ka yi irin wannan sa'insa, ya gamsar da ita ta amince da halaccin kara auren nasa. Da sanyin murya ya soma da kiran sunanta. Ba ta ko daga kai ta kalle shi ba balle ta amsa. Hakan bai dame shi ba. Ya ci gaba, "Gaskiya ban taba tsammanin za ki bijire wa wannan abu da na zo miki da shi ba, musamman ma da na yi la'akari da cewa, addinin musulunci ne ya ba ni damar yin wannan abu, kin kuwa san shi kadai ne addini a wajen mahaliccinmu. Kada fa ki manta Allah madaukakin sarki, a cikin Alkur'ni mai girma cewa ya yi, "Ku auri bibbiyu, uku-uku, hurhudu, idan ba za ku iya adalci ba ku auri daya..." To kin ga anan ina da kwakkwarar hujja ta kara aure, tunda kuwa insha Allahu zan iya yin adalci a tsakanin..." "Ka ga saurara Alhaji". Ta kuma katse shi a karo na biyu, sai dai wannan lokacin cikin karaji ta yi maganar, kuma muryarta na kunshe da alamun tsiwa sabanin maganganun da ta yi a baya. Lokaci guda kuma ta mike daga kan tattausar kujerar alfarmar da ke cikin jerin kujerun da su ka gewaye falon. Da muryar tsiwa ta ci gaba da cewa, "Dole ka yi min wa'azi yanzu tunda ka na bukatar aure, Na- mamajo! Ai a lokacin da ka ke matsiyacinka tsumma gaba tsumma baya ba ka tarka ba, sai yanzu da mu ka gama shan wahalarmu, ka ga ka yi arziki za ka je ka auro wata banzar-bazara wadda ba ta san halin da mu ka shiga ba, ta zo ta ci bulus! To, ba zai yiwu ba, wallahi ba zai taba yiwu wa ba, ka ma sake tunani tun dare bai yi ma ka ba...domin kuwa na sha alwashin matukar ina motsi a doron kasa kuma ina cikin gidan nan, babu yadda za a yi wata shashasha ta zo ta samu gindin zama balle har ta mike kafa". Ta tsahirta ta na duban sa, duba mai cike da raini. Na-mamajo. Ita ce kalmar da ta fi sauran bata wa Alhaji Basiru rai a duk tarin masifar da ta yi masa, domin ya san mayen mata, shi ne abin da kalmar ke nufi. Sai dai kuma duk da hakan, ko kusa ko alama ba zai iya yi ma ta komai ba koda ran nasa zai tafasa ya kone ne saboda abin da ta yi masa, don kuwa shi dai Allah ya jarrabe shi da tsananin son ta, ga shi ya ki jinin rabuwa da ita. Aure dai zai kara ne saboda umarnin Mahalicci da kuma son da ya ji ya na yi wa wadda zai auro. Amma a nata bangaren ba ta la'akari da hakan, shi ya sa duk kalmar da ta fado bakinta ba ruwanta da ta tauna kawai za ta yaba ma sa ita, ita kuma a tunanin ta hakan ne kadai zai sa ta yi nasarar dakushe yunkurinsa na kara auren. Sai dai abin da ba ta sani ba shi ne, duk da irin son da ya ke ma ta, ya kuduri aniyar babu abin da zai hana shi kara auren ko ana ha-maza-ha- mata. Ya numfasa da karfi bayan tsawon lokaci da ya dauka ya na tunanin irin soyayyar da su ka tafka da matar tasa kafin wannan lokacin. Ita kuwa ta na tsaye a kansa kerere kamar falwaya. "Ki kwantar da hankalinki Hajiya". Ya ce bayan ya daga kai ya dube ta, "Zauna, na ga har zuwa yanzu ba ki gamsu da..." sauran maganar ta makale a fatar bakinsa ganin ta juya ta nufi kofar da za ta fitar da ita daga falon. Ya bi ta da kallo cikin damuwa kamar mai kirga takun sahunta har ta fice daga falon. *** Kamar kowace safiya, yau ma ita kadai ce zaune cikin dakin nata, ta yi tagumi ta na sake-saken hanyar da za ta bi don ganin bayan kishiyar tata, abin da ya zame ma ta wajibi a kowace safiya tsawon shekaru ukun da amaryar mijin nata ta tare. Fadi-tashi, kujiba-kujiba da buge-buge babu irin wanda ba ta yi ba don hana auren amma abin ya faskara, aka zo aka yi auren, yanzu kuma ga amaryar kullum kara samun gindin zama ta ke yi a gidan. Sau da yawa takaici da bakin ciki su kan lullubeta ta idan ta tuna da rashin goyon bayan da mahaifinta ya nuna tun farkon al'amarin, sa'ar da ta je ma sa da batun za a yi ma ta kishiya. "Kada ki kuskura na sake ganin kafarki a gidan nan matukar akan wannan maganar ce, mutuniyar banza. Idan kuwa ki ka ki zan saba miki". Maganar da mahaifinta ya gaya mata akan lamarin ta bijiro ma ta a zuciya, ta ji kamar an harbo wani mashin bakin ciki ne ya soki zuciyar. Duk da dai a wancan lokacin mahaifiyarta ta yi wa mahaifin nata martani da cewa, "Haba Malam, gaskiya bai kamata ka ki goyon bayan yarka ba akan wata can". A fage guda kuma, alwashi da alkawarin da ta sha dauka na ba wadda za ta shigo gidan muddin ta na raye, shi ya ke dada daga mata hankali. "Lallai ya dace na dauki matakin gaggawa akan yar iskar nan". Ta tsinci kanta tana mai fada a fili, wanda kuma shi ne abin da ta saba duk lokacin da ta yi irin wannan tunani. "Tabbas lokaci ya yi da ya kamata na san duk yadda zan yi na ga babu ita a gidan nan, ko don na cika alkawa..." Sallamar da aka yi a bakin kofar dakin ta katse furucin nata. "A'a, ah! Baraka...yaushe a gari in ji maki bako. Saukar yaushe? Ta ce cikin fara'a bayan ta kawar da alamun tunani da damuwar da ke kan fuskarta, sannan da gaggawa ta mike ta tari yar siriyar matar da ke kokarin shigo wa dakin. "Oh! Hajiya Rukayya ashe rai zai ga rai". Siririyar matar da ke amsa sunan Baraka ta ce ta na duban tsarin dakin cikin mamaki. Hakika ta san cewa shekaru da dama da su ka wuce dakin ba haka ya ke ba, duk abubuwan da ta sani na daga cikin abin da aka kawo wa kawar tata a sa'ar da ta na amarya babu a ciki yanzu. Kai idan banda ta na tsoron kada ta yi karya ma da sai ta ce hatta kusoshin da aka kafe labulen dakin ba wandada su ka kawo Hajiya Rukayya da su ba ne. Koda ya ke tunanin nata bai zurfafa ba, da ta tuna da labarin shaharar da aka ce mijin nata ya yi.Yau rabonta da su hadu da Hajiya Rukayya tun ranar da ta tare a gidan mijin nata lokacin ya na talakansa. Tun daga wannan rana ba su sake haduwa ba, sai a yanzu saboda tashin da su Barakar su ka yi su ka koma jihar jigawa. "Wayyo Allah makashin kakana". Baraka ta ce daidai lokacin da ta zauna a daya daga cikin manya-manyan kujerun laushin da ke cikin dakin. Hajiya Rukayya da Baraka su ka gaisa cikin fara'a da murnar haduwa da juna. "Cewa na yi bari na zo na gaida ke tunda ke Allah ya yi miki arziki kin manta da mu". Baraka ta ce ta nayatsine fuska. "Uhm! Ke dai bari". Hajiya Rukayya ta ce ta naduban Baraka ido cikin ido. "Ba wani batun arziki, gari ne kawai ya dagule mana...ke dai bari na kawo miki ruwa ki tsotsa". Ta mike ta nufi wata karamar na'urar sanyaya ruwa da ke durkushe can gefe guda. Baraka ta bi ta da harara. "Ban gane gari ya dagule mu ku ba? Mutumin da ke cikin daula irin wannan ya ce gari ya dagule masa? To, mu kuma mu ce me?" Ta daga kanta zuwa saman dakin ta naduban kyakkyawar fanka ruwan zuma da ke makale ta nata faman aiki abin ta. Hajiya Rukayya ta yi wani motsattsen murmushi lokacin da ta dawo gare ta dauke da kwalin tataccen lemon zaki hade da karamin kofi, "Fara jika makogoron..." "Ina fa zan iya jika makogorona ban ji cikakken abin da ke damun aminiyar ba." Baraka ta katse ta bayan ta dawo da dubanta gare ta, "Hajiya wanda ke cikin daula irin ku jin irin wadannan kalamai ai ba karamin tashin hankali ba ne..." "Uhm! Ke dai bari Baraka." Hajiya Rukayya ta shiga cewa bayan ta koma wajenta ta zauna, "Wadannan kyale-kyalen ba su ne ba, al'amarin ya fi karfin su Ni yanzu duk a banza na ke ganin su...ke ni Wallahi da zaman su cikin halin da na ke ciki, gwanda zamana cikin halin da mu ke ciki farkon aurena da Alhaji". Baraka ta yi tagumi hannu bibbiyu bayan ta mayar da hankalinta sosai ga Hajiya Rukayya, "To, ni ban gane abin da ki ke nufi ba. Yanzu ki na nufin ki ce mijinki ba ya iya gamsar da ke ne ko ya ya?" Ta yi shiru cikin saurare da mamaki. "Duk ba haka zancen ya ke ba Baraka, na ga har zuwa yanzu ba ki fahimta ba. Ba ki da labarin an yi mini kishiya?" "Laa....ila...ha...illallahu".Baraka ta yi doguwar hailala ta natafa hannu, "Kishiya? Kishiya fa ki ka ce? A garin ya ya haka ta faru?" "Ke dai bari Baraka, Kishiya na gaya...


Read / Download BAKIN KISHI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album