Join Our WhatsApp Group

INDO A BIRNI Complete Hausa Novel Document by INDO A BIRNI


INDO A BIRNI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 92061



INDO A BIRNI

Reading Time: 7 Hours

Added On: 28, Oct 2023

Author: Rasheedat Usman ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION

Author Phone : 08147537180

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 518.63 kb

File Type: txt

Views: 729+

Download: 604+

Last download: 2 days ago

Description/Story: [12/31/2019, 11:20 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*IཽNཽDཽOཽ Aཽ BཽIཽRཽNཽIཽ*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah)*


*(MAKAMAR KAINUWA)*👸🏻


📱
*08147537180*


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
(Baya hana gamji)
Toho


*1 / 1 / 2020*

Tsarabar sabuwar shekara domin ku masoyana.


*Deducated to*


*Aunty Fauza yar Amana*

Uwa mabada mama k'aunar ki dabanne gare ni, domin ke d'in shugaba ce, dake Adalci ga duk na k'asa dake, Allah ya barmu tare Aunty nah.



*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

Alhamdulillahi Ala kulli Halin dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah madaukakin Sarki, salati da d'aukaka da Aminci su tabbata ga cikamakin Annabawa Annabin k'arshe muhammad S'A'W da iyalan gidan sa da sahabban sa har izuwa Ranar Sakamako.

Ina godiya ga Allah daya sake dawo dani lfy, domin sake nishad'antar daku, ina rok'on Allah da yasa yanda na fara lfy ya bani ikon gamawa lfy, Allah ya bamu ikon Amfana da Abunda ke ciki. Ameen 🙏🏻



*P* 1️⃣ ➡️ 2️⃣

Yara biyu na hango suna cin Uban gudu, yayin da wacce ke gaban take gudun ceton Rai, sosai take gudun Saboda kar wacce ke bin bayan nata ta kamo ta, wani gida naga yarinyar ta fad'a, binta cikin gidan itama yarinyar dake biye da itan tayi, da Gudu ta fad'a wani madaidaicin d'aki, cikin haki.
d'akin da yarinyar ta shiga, itama wacce ta biyo tan take k'ok'arin shiga.
Cikin Sauri wata matashiyar mata ta tare ta tare da cewa.

" Lafiya *INDO* kuke wannan Uban gudu, sannan kuma zaki bita har d'aki, aiko mutuwa ma tana kunyar Idon Uwar d'a, meye *Zainabun* ta Miki?
kika biyo ta har gidan ubanta ba ko kunya.

Huci wacce aka kira da *INDO* take Cikin masifa da bala'i take cewa.

" Sai mutuwa taji kunyar Idon ki, ni kuma *INDO banji taki ba, wlh yau Babu mai hanani cin Uban Zainabu cikin gidan nan, gobe koda kud'i aka Had'a ki baxaki k'ara nema na da tsokana ba, cemin fah tayi *INDO BALA'I* a gidan uban waye aka yanka min suna da *INDO BALA'I* Kinga *Goggo Hali* ki kauce ki bani hanya, kar nayi gefe dake kiga rashin kunya ta, dan wallahi, na ture ki na shige cikin d'akin nan baxai bani tsoro ba, ehe sai dai duk abunda zai faru ya faru, ta k'arasa maganar tana murgud'a baki.

Gam sukaji An rufe k'ofar d'akin tare da dannawa k'ofar sakata, daga rufen zainabu tace

" Baxan fiton ba, kuma na fad'a *INDO BALA'I* ko k'arya nayi ke ba masifaffiyar bace.

Matsawa wacce ta kira da *Goggo Hali* tayi tare da cewa to Kinga ma ta rufe d'akin sai dai idan ni zaki Kama ki daka, tunda ke baki da mutunci, kowa ya miki shaidar tsiya a cikin garin nan.

Cewa *INDO* tayi
" Idan anga dama Amin shaidar Abunda yafi Rashin mutunci ma, kuma wlh yau sai kinga yanda ake tsiya a cikin gidan nan, badai y'ar ki ta rufe d'aki ba, d'aga murya *INDO tayi, tace zainabu kina jina ai idan ba tsoro ba ki fito, mana shegiya y'ar matsorata, kuma wallahi Yau saina huce haushi na akan *UWARKI*.

Juyawa *INDO tayi, karaf kuwa sai idon ta yayi toxali da Randar k'asar Goggo Hali, Wacce take cike fal da Ruwa, Da Gudu tayi madafin Goggo Hali ta d'auko tab'aryar ta, Randar k'asar INDO* ta nufa da Gudu tare da buga tab'aryar akan Randar, fashewa Randar tayi, take kuwa Ruwan ya zube kasa, bokiti na k'arfe dake ajiye gefen Randar k'asar *INDO* ta raruma tare da shek'awa a d'akin mahaifin Zainabu, tsayawa Goggo Hali tayi tana kallon ikon Allah a gun *INDO* domin kuwa Idon ne kawai tsakanin ta da ita, tasan Idan tayi gangancin zuwa ta tare *INDO* to Babu shakka zata iya sauk'e mata tab'aryar a kanta ba damuwar ta bane, domin kuwa tasan Halin INDO tsaf babu wanda ta gyale kaf fad'in kauyen.

Cikin Huci INDO tace.

" Kuma na watsa Ruwan a d'akin Malam Hamxa idan ya dawo shima yasan cewa y'ar sa ta tab'o *INDO* yau,
Bata jira mai Goggo Hali zata ce ba tayi ficewar ta tana rera wak'a.

" Ikon Allah cewar Goggo Hali, yarinya ta Addabi gari, kowa yake Allah wadarai da Halin ki, Yanxu fah ki duba kiga b'arnan da yarinyar tamin, Amma dai wallahi Albasa batayi Halin Ruwa ba dan dai iyayen ki kam, mutanen kirki ne, Su kuma tasu jarabawar kenan, na Samun fitinanniyar yarinya, to Allah dai ya shirye ta.
Jin motsin mutum a bayan ta ne yasa Goggo Hali juyawa, zainabu ta gani tsaye tana sauk'e Ajiyar zuciya, ai kuwa nufar ta Goggo Hali tayi, tare da sauk'e mata rankwashi a kanta, tace.
" Yanxu ke zainabu ki Rasa wa zaki tsokana sai *INDO*, sai kace wacce baki san Halin ta ba, to maxa shiga d'aki ki d'auko min mayafi na, naje wajen Uwar ta wlh sai sun biyani Randa ta, dan baxan yi Asara ba wlh.

D'akin Zainabu ta nufa tana cewa.

" Kije ki wlh Goggo a biyaki Randar ki, tunda y'ar su bata da mutunci.


Ita kuwa INDO fitar ta daga gidan su zainabu, hanyar gidan su ta nufa, tun daga nesa ta hango motar sa, cikin murna da zuwan sa, garin nasu yasa *INDO* kwasa a guje, cikin zumud'i, ta nufi motar, kasancewar Gudu baya bawa *INDO* wahala, kullum a cikin sa, take sam bata da nutsuwa, k'azanta kuma wajen *INDO* subhanallah ba'a magana, domin kuwa k'azama ce ta ajin farko, duk inda ake neman k'azama, to idan aka Samu indo ayi fatiha a tashi, domin kuwa kaf fad'in K'auyen Babu wanda yakai *INDO* k'azanta.
Wannan kenan.

A nutse ya fito daga cikin motar, tare da tsayawa jikin motar yana duba yaran da zasu shigar masa da Kaya cikin gidan, tsohuwa mai ran k'arfe *HAJIYA INNAH* da Gudu INDO ta k'araso wajen nasa tare da yin turus da k'afar ta cikin bak'ar kasa mai k'urar dake shinfid'e a wajen, take kuwa k'asar ta bulewa wannan bawan Allah k'afar sa.
Da sauri ya daga kansa ya dubi *INDO* cikin takaici kuma cikin tsawa yace.

" Wacce irin mahaukaciya ce ke, ki duba kiga yanda Kika bule ni da k'asa, wawiya marar Hankali, Zaki kauce min da gani ko sai na makeki, Useless kawai.

Tura bakin ta INDO tayi, tace

" Wlh yau Kam baxan bar nan ba sai kace kana Sona, shikenan kullum sai ni kad'ai zanta sonka, kai baxaka soni ba, wlh yau sai kace kana Sona, ko kuma kamin Irin Abunda nake gani y'an India suna yiwa y'an matan su, a tibin *Hajiya Innah*, Bari ma na tuno sunan Abun 🤔
Yawwa na tuno kuss, suke cewa, sai kamin sannan zan tafi, turo masa bakinta tayi, tace gashi kamin, kaji mustapha na.

Zaro Idon sa, mustapha Yayi tare da saurin kawar da kansa gefe, jin bugun warin bakin INDO ya bigi hancin sa, wani Irin hucin wari yaji mai tayar da zuciya, cikin k'yank'yamin ta yake cewa.

" Allah ya sauwak'a naso k'azama irin ki, k'azamar k'auye, waima tukunna uban waye zai miki kiss, da wad'annan yellown hak'waren naki, b'ace min da gani kafin na targad'a ki, mahaukaciya kawai, marar lissafi, Amma dai wlh Allah ya isa tsakanina dake, ki rasa waye zakice kina so saini, to wlh Allah ya isa kin cuceni.

Murgud'a masa Baki tayi tace.

" Niba mahaukaciya bace wlh, kuma sai kamin kuss d'in nan, rarumo rigarsa tayi, ta duk'unk'une a ciki.

kasancewar babbar riga yasa, sai buga k'afa take, tana ihu tana cewa.

" *Wayyo Allah na shiga uku wayyo jama'a kuzo ku tayani rok'ar ya mustapha ya min kuss wayyo Allah Jama'a kuxo ni kad'ai nake sonsa shi baya Sona.*

Rasa Yaya mustapha zaiyi da INDO yayi, gashi kuma yana hango wasu dattawa biyu suna, tahowa, ta inda suke,

"Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un Allahumma ajirni fil musibati, nidai wannan yarinyar ta zamo min masifa wlh, Duk Randa zanzo k'auyen nan, da tsinkewar zuciya nake Zuwa, tunda nasan zan had'u da Bala'i.

da k'arfi mustapha yasa Hanun sa cikin kyamar INDO ya b'anb'aro ta da kyar, tare da hankad'a ta, gefe.

fad'uwa tayi tare da bige kanta jikin bango, wani Irin zafi taji a kanta, Amma duk da haka Bakin *INDO* bai mutu ba, cikin Rashin Kunya, ta taso kamar wacce zata Doki Mustapha, tace.

" Ka ture Allah ya Isa wlh, mungun Azzalumi, kuma wlh Bashi ka d'auka, sai na Rama wlh.
Tana gama fad'in haka ta juya ba tare da ta k'ara Kallon mustapha ba.

Tsuka mustapha yaja, tare da tab'e bakin sa, yace.

" Wawiya kawai marar Hankali da nutsuwa, ai ko d'aura min ke Akayi a kaina, saina sinke ki da k'arfin tsiya, nayi wurgi dake gefe, *K'AZAMAR K'AUYE* kawai.
Yara biyu ya hango, Kira ya k'wala musu, bayan sunxo ne, ya umurce su, da su kwashi kayan sukai masa gidan *Hajiya Innah.*

Tsayawa yayi har suka gama shigar da kayan sannan yasawa motar sa security, yayi gidan, *Hajiya Innah*.
Sauk'ar Ruwa a jikin sa mustapha yaji' wani Irin shid'ewa Yayi, a gigice ya bud'e Idon sa, karaf suka had'a Ido da *INDO* tsaye da bokitin Ruwa a Hanun ta wanda ta juyewa Mustapha a jikin sa, takaici da haushin ta, shine ya hanasa magana, saima wani mungun kallon daya tsaya yana aika Mata.

Juyawa INDO tayi a guje tana dariyar k'eta tace.

" Na Rama tureni da kayi, daman ai na fad'a maka Bashi kaci, kuma na Rama Yanxu Babu bashi tsakanin mu, masoyina mustapha, *INA SONKA ARADU* tana gudun ne take wannan zancen.

Kad'a kansa mustapha yayi, cikin Jin haushin *INDO* da mamakin ta, yake cewa.

" Anya kuwa wannan yarinyar bata da Aljanu, don ba k'alau take ba, Kam, wai *masoyina mustapha* ko a gidan uban waye na zama masoyin nata, sai Allah, shigewa Yayi cikin gidan, tare da Sallama.

Tana Zaune gefe tana b'arar gyad'a ga kuma tarin kayan da mustapha yasa aka shigo masa dashi, a gefen ta, d'aga kanta tayi tare da cewa

" Lale maraba' da mutanen Binni, sai Kuma tayi shuru tare da tsurawa jik'ak'k'un kayan jikin sa Ido, cikin mamakin meya jik'a masa Kaya, kasa hakuri *Hajiya Innah* tayi tace.

" Muhammadu dake haka take kiran sa dashi, menene ya jik'a maka kayan ka, kodai ka biya Rafi ne kayi wanka?

Tambayar *Hajiya Innah* ta k'arshe itace ta bawa mustapha Haushi, *wai ko ka biya Rafi ne kayi wanka* sai kace ta tab'a ganin nayi hanyar rafin nasu, cikin gatse ya mayar mata amsa da cewa.

" *A'a ba Rafi Naje ba, tekun Maliya na biya nayi wankan na dawo*.

" To Uban y'an bak'ar magana da zafin Zuciya, Idan da Akwai inda yafi tekun Maliya ruwa ma kaje kayi wankan, aikin banxa kawai daga tambaya sai cibi ya zama k'ari.

Tabe bakin sa yayi tare da d'aga kafad'ar sa, Alamun wannan damuwar kine, shigewar sa Yayi d'akin daya kasance nashi idan yaxo k'auyen.
D'akin fess dashi gwanin ban sha'awa komai a tsare kamar d'akin Mace, kan dressing merron shi kuma kayan shafe shafe ne kalakala masu tsadar gaske na maxa.
Wanka ya shige yayi a ban d'akin Hajiya Inna dake tsakar gidan ta.

Itako Hajiya Inna sai mita take ita d'aya.

" Yaro ace sai shegen Bak'ar Zuciya gare sa, ga rashin hak'urin tsiya, shiyasa nake Allah Allah *Habeebu* ya dawo ya dinga ziyarta ta, sai munfi shiri dashi, fiye da wannan mai Bak'in Ran tsiyar, dan *Habeebu* yaron kirki ne d'an Albarka, na Rasa wani Irin Aiki yake a k'asar wajen Nan, da yak'i dawowa k'asar sa ta haihuwa.


Mustapha daya fito daga ban d'aki ne, yana jin duk mitar da take yi ne, yake ce Mata.

" Kamata yayi ki bisa k'asar wajen ai, ki dawo shi wannan K'auyen da Zama K'arshen K'auna, hakan ne zai tabbatar da kina sonshi, Nima banda k'addara da biyayyar iyaye mai zai kawo ni wannan, Bak'in k'auyen harma wannan jarababbiyar yarinyar ta Addabe ni.
Kuma wlh Hajiya koda wasa naga k'afar yarinyar nan *INDON* cikin gidan nan sai na b'allata.

" Kan Uba cewar Hajiya Innah, to a Bak'in k'auyen aka binne cibiyar Uban ka, kuma baka da wajen daya fi wannan K'auyen tunda shine Asalin Ubanka Haruna.
da kake maganar cewa *INDO* karta shigo cikin gidan Nan, gidan kane koko akwai kud'in ka cikin ginin gidan, to ko ubanka Haruna bai isa ya hana *AISHATU* shigowa cikin gidan Nan ba, bare kuma kai *Karan kad'a Miya* , sai dai Kuma Kai kabar min gidana, badai *INDO* ba Zan Kuma ga Uban da zai hana ta shigowa.

Hararar Hajiya Innah mustapha Yayi, tare da shigewa cikin d'akin nasa ba tare daya k'ara tankawa Hajiya Innah ba.

Itama D'akin ta ta shige tana ci gaba da zagin mustapha, wanda shine gaisuwar da sukayi daga isowar sa. 😄

" Gafaran kudai masu gida cewar Goggo Hali, dake tsaye k'ofar d'akin, Mama mahaifiyar *INDO*.

Fitowa mama tayi, tare da cewa,

"Lale marhaban da Halima, kece yau tafe a gidan nan.

" Eh Nice cewar Goggo Hali, na sameki lfy.

" Lafiya lau Halima ki zauna mana, mu gaisa, naga kin tsaya bayan ga shimfid'ar taburma.
Cewar Umma.

Kad'a kanta Goggo Hali tayi tare da cewa.

" Ba zama bane ya kawo ni Mairo, Y'arki ce tayi min D'ibar Albarka, yau a cikin gidana tare da Kuma b'arna, shine naxo a biya Ni, dan baxan iya Asara ba wlh, tunda ku y'arku tafi k'arfin ku.

Mama taji Zafin maganganun da Goggo Hali ta mata, sai dai Kuma ba laifin ta bane *d'an kuka ne mai jawa uwarsa jifa* da Indo mutum ce mai jin magana da tuni...


Read / Download INDO A BIRNI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album