Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

KUN MAKARO Complete Hausa Novel Document by KUN MAKARO


KUN MAKARO

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 69758



KUN MAKARO

Reading Time: 5 Hours

Added On: 23, Jun 2024

Author: HAERMEEBRAERH ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 360.39 kb

File Type: txt

Views: 448+

Download: 822+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: ๐Ÿ’…๐Ÿผ *KUN MAKARO* ๐Ÿ’…๐Ÿผ








*BY HAERMEEBRAERH*







*Ina farawa d sunan Allah,mai rahama mai jin qan bayin shi, tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad sallahu alaihi wa sallam, bayan lokaci mai tsaho yau inshaa Allah zan kawo maku sabon labari, wanda nake fatan ya sauya rayuwar mutane da dama, ta fuska kala2, labari ne mai qunshe da darrusa mabayyana, ina fatan zaku bude zuqatan ku masu albarka, kamar yanda kuka saba, domin fahimta da daukan darussan dake ciki.*


*Kamar koda yaushe ina roqon makaranta novels dina,ku na adanawa koda bakuyi sha'awar bi ba a yanxu, kar sai gaba ku zo kuna nema lokacin an wuce kuuu, wannan rubutun ina son nayi d sauri fiye da da, saboda kunsan na koma makaranta, ina roqon addu'ar ku akan samun nasara akan wannan karatun nawa, na gode maku*



Page 1:




Aeeshaa ke zaune a kan kujerar zaman mutum daya, dauke da wuqa da kwano, tare da kubewa tana yankawa, tana yi tana kallon lokaci, aiki take kamar wata inji, ba hutu, abinda ke tsaida ita wannan aiki, sallah.

Cikin sauri ta tashi ta koma kitchen ta dau turmi da tabarya, ta saba wannan kubewar da ta yanka, tana gamawa ta je ta zuba a tukunyar miyar data ji nama da kifi, ta kada ta rufe kadan, sannan ta koma kan tuwon semo da ta tuqa tin minti biyar da ya wuce, tuqawa tayi taga yayi,maza ta dakko leda da mazubi ta fara zubawa tana murde ledar tana sawa a inda ya dace, da sauri ta juya kan miyar dataji ta fara alamar zubewa, ta kashe gas din, ta qarasa rufe tukunyar, sannan ta qarasa kwashe tuwon ta.


Tana kammalawa ta diba fridge taga zobon data hada ya dau sanyi, murmushi ne ya kwace mata, da sauri ta koma ta wanke dik abinda ya dace, ta fara jera abincin akan dinning, sai da ta kammala komai, ta juya da sauri dan wucewa dakin ta tai wanka ta shirya islamiyya, kar ta makara kamar yanda tai da safe, zuwa makarantar boko, taji kiran Umman su, zuciyar ta ce ta buga da qarfi.


"Na'am Umma gani nan zuwa"


Cikin azama ta nufi dakin Umman nasu, inda ta tsaya a bakin qofa, tai sallama tare da qwanqwasa qofar, shiru kafin daga bisani ta amsa mata cikin tsawa,



"Dan ubanki sai yaushe zaki riqe akan ki inna kira ki kina shigowa? Sai ki tsaya dan gulma kina wani jira sai na baki izinin shiga,kina abu sai kace wata uwar mata, da ban son ganin ki zan kira ki ne?"



Shiga Aeeshaa tayi, ta samu gefe ta tsaya tace,


"Umma kiyi hakuri,gani,"


"Yauwa nace kin gama abincin ne?"


"Eh na gama,na hada komai kan dinning, yanzu shirin islamiyya zan, kar na makara kinsan yau banje boko ba saboda makara da nai, na kammala komai har dare nai abincin ma tinda naga tiwo ne"



"Waya saka ki yi har dare? Ni nace ki dafa har dare ko iyayi? Ko kin fini sanin me ya fi dacewa da ayi ne?"


"Umma dan Allah kiyi hakuri bana son ranki na baci, bari inna dawo islamiyya kome kk so zan dafa, dan Allah ko zan fashin boko bana son nai fashin islamiyya,"


"Alhuda huda kenan sarkin karatu, wuce ki tafi,kina dawowa kizo akwai wankin da zaki hada dana qannen ki kimin, kinga sai kisa uniform dinki ma dika ki wanke ko?"


"Eh hakan ma yayi Umma na tafi sai na dawo,"



"To"



Aeeshaa da sauri ta shirya ta fito, dan ko wankan bata samu yi ba gudun makara, in ta dawo tayi.


"Aunty Aeeshaa muma mun shirya,"


"To Ameena maza muje kar mu amshi bulalan latti ko? Ina Abdul hakeem?"


"Gani meye?"


"Kai dai Allah ya shirye ka baka da kunya ko kadan har yanzu,girma kk amma kana shiga daji,"


"An shiga din, ni na tafi kar ku taho ku tsaya surutu,"


"Aunty Abdul baida kunya, amma karki fada masa nace haka,"


Murmushi Aeeshaa tayi, ta shafa kan qaramar qanwar ta, sannann suka fita daga gate din gidan nasu, sannan tace.


"Kar ki damu, ba zan fada masa ba,ai dama baida kunya ko baki fada ba, muyi sauri,kinga ga yara can sai gudu suke suma,"



Qara sauri sukai, dankar su makara, suna zuwa suka shige ajujuwan su, Abdul Hakeem ajin su daya da Aeeshaa,Ameena na ajin dake qasa danasu, domin itace qaramar su.


Karatu ake amma hankalin ta yau sam baya jikin ta,yana can wajen tinanin rayuwar gidan su, gaba daya basu tausaya mata, basu san tayi abu a gode mata ba dik da qoqarin da take yi, tana baut masu kamar bata son jikin ta,amma ko a jikin su, burin su kawai ta masu aiki, su amfana da ita kuma su zage ta, sai kace ba Umman tasu ce ta haife ta ba, tinawa da mahaifin ta da ya rasu ne yasa wata kwalla me zafi ta saukar mata,to ko dai ba Umman ce mahaifiyar ta ba ne? Tinda mahaifin ta ya rasu tin tana shekara bakwai, sabida cancer, .......




"Aeeshaa tinanin me kk haka? Har da kuka?"



A firgice ta miqe tsaye ta fara rera karatun da ta haddace jiya,a zaton ta an tashe ta ne dan tai karatu, nan da nan kuwa ajin ya dau dariya,banda Abdul,wanda ya bata rai, ya juya ido, ya kalli waje.



Shiru tayi,dan ta kula da abinda ta yi, nan ta sunkunyar da kan ta, tana son taji me malamar tasu ta fada da farko.


"Aeeshaa tambayar ki nake me ya same ki?"




"Kaiii kaiinaaa ke ciwoo"


"Wayyoo sannu maza jeki gida,tinda ba nisa, sai kisha magani, ki zauna, gobe kin bada haddar ki,"


Da sauri ta fara karatun ta,dan bata son abinda zai sa ace ta koma gida ba a tashi ba aiki na can na jiran ta, bata huta da aikin da tagama tiqa ba tin safe.


Kyale ta malamar tayi, ta kammala, sannan suka dora sabon karatu.


Qarfe 5:30pm suke tashi,dan haka suna tashi gida ta nufa,ita da qannen ta.



Suna shiga taga kan dinning kaca2,ga qawayen Umman ta a parlour suna ta hira, ana shewa, an barbaza kayan sayarwa a qasa,ga cups nan da plates anci snaks, sai ciniki sike ma Umman nata,suna yi suna hirar batsa, lura da dawowar yaran yasa suka nutsu,




"Ah Aeeshaan Umman ta,kun dawo kenan, yanzu nake cin wani daddadan abinci, Umman ki tace ke kk dafa, ina matuqar mamakin ki Aeesha, dika dika shekarar ki sha shida amma kin iya abinci kala2, kamar wata babba,"



Wani irin dadi ne ya kama Aeeshaa,yau a rayuwar ta gaba daya an yabe ta, ji tai kamar ta kama Aunty Safnaa ta rungume dan murna, ta bude baki zatai magana kenan Umman ta ta amshe.



"Wannan me shegen son zaman dakin? In ba dan nayi qoqari na tsaya tsayin daka ba da ko ruwan zafi bazata iya dafawa ba,sai shegen son karatu, kamar wata babbar mace, kullum ina nuna mata hanyar kasuwancin nan tana kauda kai, bata san ko kayi karatu ba wani aiki zaka samu ba, maza ma wahala suke sha bare ke mace da zaki qare a dakin miji,"



Aeesha bata ji dadin kalaman Umman ta ba amma cikin murmushi tace,



"Umma me za a dafa? Ko kawai naje na dora abinda ya dace?"



"Kije ki yi dik abinda kk ga ya dace, ga wankin nan karki manta"

"To Ummana"



miqewa tayi ta shiga ciki, ta sauya kayan jikin ta, ta koma Office din nata wato kitchen, taliya ta dafa da miya, dan ta samu sauqi, da sauri cikin kazar2 ta wuce dakin Umman nata ta hada kayan wankin su, ta koma ta dauki na qannen nata ta fita qofar baya ta kama wanki,ba ita ta gama ba sai ana kiran magrib.


Bayan tayi sallar magrib, tayi azkar,tayi karatun ta na qur'ani, sannan ta yi isha'i, ta nadr abun sallah, ta leqa wajen umman ta ta tambaye ta ko akwai abinda zata mata?



"Ba abinda za ki min yanzu, ki tabbatar dai kin gyara kan dinning kan ki kwanta,"


"To Ummana sai fa safe,"


"Allah ya tashe mu lfy,"


Tana mamakin Umman ta, wai ace magana mai dadi bazata hada su ba, komai a cikin fada yake da kushewa, ga qannen ta nan suma sun dauka, musamman Abdul,gwanda2 Ameena, wataqila itan ma dan yarinya ce,ba zata wuce shekara 5 ba.


Daga komai tayi takai kitchen, ta kashe fitulu ta kulle masu qofa ta tofa ayatul kursiyyu sannan ta yi dakin ta.


Tana Assignment din ta bacci ya dauke ta ko kammalawa batai ba tsabar gajiya.

********************




"Wai makaranta nan da can ki taka kije sai na kai ki na dawo dake, ga su Ameena dake nesa, suma saina kaisu, na aje su, ke ko tausaya min bakiyi,"



Hawaye ne ya gangaro ma Aeeshaa, tai saurin saka hannu ta share, ita dik wahalhalun da take ba'a gani sai kaita makarantar da ake shine zai zama abin magana, lallai bin iyaye yana da wahala, Allah ya bata ikon cin wannan jarabawa, yanzu in ta amsa ta tace ta barta tana zuwa ta jama kan ta aiki, taje
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download KUN MAKARO

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album