Join Our WhatsApp Group

MIJINA SIRRINA Complete Hausa Novel Document by MIJINA SIRRINA


MIJINA SIRRINA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 89027



MIJINA SIRRINA

Reading Time: 7 Hours

Added On: 26, Oct 2023

Author: Ummi Aisha ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : HASKE WRITERS ASSOCIATION

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 512.8 kb

File Type: txt

Views: 1243+

Download: 672+

Last download: 11 hours ago

Description/Story: MIJINA SIRRINA


[7/4, 5:13 AM]

El-hajj

_©HASKE
WRITERS ASSOCIATION (HWA)_
*​MIJINA SIRRINA​.....!*🌹
_(Labarin K'auna)_
**Based on a true life story**
_*NA​​*_
*_​​UMMI A'ISHA​​_*
_​Dedicated to Alh .I. Uba family​_
*_DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN
K'AI,Rabbishrahli sadri, wa yassirli amri, yafqahu
qauli.._*
_Shafin farko nakine pherty b~b.._
*​1​*
~~~ "Oyoyo yaya kabeer...,oyoyo yaya kabeer.."
Wannan shine ihun da yaran dake zaune cikin
tsakar gida suna wasa suketa faman yi daidai
lokacin da suka ga shigowar matashin saurayin
wanda ke sanye cikin farar shadda kansa babu
hula sai yar kyakkyawar suma da ya dan ajiye,
Fuskarshi dauke da murmushi ya rungume yaran
wadanda akalla zasu kai su kimanin guda hudu,
Daga inda take acikin kitchen ta sake lab'ewa
saboda bata son ya ganta duk da sanin cewar
dominta yazo gidan, sadadawa tayi ta buya a
bayan fridge gamida leka kanta ta window ta
yadda tasan bazai iya hangota ba,
Ganinshi tayi rike da hannun Amira da waleeda
kannenta sannan ga amir da husna atsaye sai
faman jajja masa riga suke suna tsalle,manyan
chocolate samfarin coconut chocolate ya debo
daga cikin aljihunsa ya mimmikawa yaran,
Sunkuyawa yayi wurin Amira saboda itace babba
tafi su husna wayo,
"Amira ina mama?"
"Tana falon abba?"
"Yaya NADIYA fa?"
"Tana kitchen mama tasata aiki.."
Murmushi yayi ya mike saboda yasan aduk inda
take taji shigowarsa shiyasa ta gudu ta buya,
Yana rikeda hannun su Amira ya bi hanyar da
zata sadashi da falon Abba,
Sai da ya tsaya yayi sallama mama ta amsa ta
bashi izini sannan yasaka kai ya shiga cikin
falon,
Mama yasamu zaune kusa da abba suna yin
hira gefe daya kuma kwanukan abincine da
abban yaci kasancewar bai jima da dawowa
daga wurin aiki ba,
Su walida da amira na biye dashi har cikin falon
sai da suka rakashi ciki sannan suka ruga da
gudu suka fita,wuri yasamu ya zauna kanshi a
kasa saboda kunya da kuma girmamawa,
Ganinsa yasa abba sakin fara,a tareda mikewa
daga kishingiden da yake ya gyara zamansa
yana murmushi,
"Kabeeru yanzu kake tafe? Barka da zuwa.."
Cikin jin kunya da sose sosen keya kabeer ya
daga ido ya kalli Abba,
"Ehh wallahi abba, shigowata kenan dama nazo
ne in gaisheku saboda kwana biyu ban samu
damar shigowa ba.."
Murmushi Abba yasake yi ya kalli kabeer din,
"Haba kabeer har yaushene rabonka da gidan,
nazaci ai jiyane kawai baka zoba amma ai
shekaran jiya ma kazo kodai ka manta ne?"
Maganar da abba ya fadice tasa mama tsoma
bakinta tana dan murmushi amma fuskarta babu
yabo babu fallasa,
"To ai Alhaji tunda yasaba zuwa kullum jiya
kuma baizo ba ai dole yaji kamar yafi sati daya
rabonsa damu"
Dariya abba yayi yakoma ya kishingida yana
kallon kabeer wanda ya gyara zama yafara
gaisar da mama,
Shiru falon ya danyi nawani lokaci saboda shi
kabeer nauyin mama da abba yakeji yanzu sam
baya iya sakewa yayi hira dasu yanzu kamar da,
Ganin yanata zaune shiru sai dai dan lokaci
zuwa lokaci abba yana sakoshi cikin zancen da
suke yi da mama yasashi mikewa,
"Abba bari naje waje.."
"To kabeer tafiya zakayi?" Abba yafada yana
gyara zamanshi,
"A'a ba tafiya zanyi ba waje zanje"
Fita yayi daga cikin falon cikeda kunya, yana fita
abba ya dubi mama yana fara,a,
"Nasan dama ba tafiya zaiyi ba wurin mutuniyar
tasa zaije.."
Shiru mama tayi batace komai ba saboda ita
kwata kwata bata son wannan maganar saboda
wani dalili wanda ta barwa zuciyarta ita daya
amma idan hali yayi zata bayyanar dashi ga
abban shima yaji, ganin taki zancen yasa abba
barin maganar ta hanyar shigo da wani zancen
daban domin ya fahimci duk lokacin da zaiyi
magana makamanciyar wannan wadda ta shafi
kabeer da nadiya mama bata bada goyon baya.
Yana fitowa daga falon abba cikin kitchen
yawuce, a bakin kofar kitchen din ya tsaya
saboda ganinta da yayi tsaye tana mopping
bayan ta kammala share cikin kitchen din,
Yarinyace yar budurwa wacce bazata wuce
shekaru goma sha biyar aduniya ba, tanada
hasken fata amma ba farace can ba, tana sanye
da atamfa kalar koriya dinkin riga da zani, daga
inda yake yana iya hango gashinta dake
nannade cikin dan kwalin dake daure akanta,
"Sannu da aiki.." Yafadi yana murmushi har
lokacin yana tsaye akofar kitchen din,
"Sannu da zuwa yaya kabeer" tafada ahankali
sannan maganar ma tayi tane cike da kunya,
"Yawwa sannu sarki aiki.."
Tunowa da tayi cewar bata gaidashi ba yasata
saurin dan rissinawa,
"Yaya kabeer ina wuni?"
"Bazan amsa ba har sai kin jiyo kin kalleni ido
da ido.."
Murmushi yasaki bayan ya furta mata hakan
saboda yasan ba karamin aiki ya hadata dashi
ba domin kunyarshi da takeji bazai taba barinta
ta iya hada ido dashi ba...
_*Ummi Shatu*_
[7/4, 5:13 AM] Humaira Khaleel: _©HWA_
*MIJINA SIRRINA.....!*🌹
_(Labarin k'auna)_
**Based on a true life story**
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Dedicated to Alh .I. Uba family_
_Fatan alkhairi ga k'awata maryam qaumi,
kina raina akoda yaushe yan matan shaddad.._
_*2*_
aishaummi.blogspot.com
~~~Jin abinda ya fada ya sata sake sinne kanta
kasa tana kallon tiles din dake malale a kitchen
din,
"Bazaki gaida ni ba kenan in tafi ko?" Kabeer ya
fada har lokacin fuskarshi tana dauke da
murmushi,
"To ba na gaisheka ba kaki amsawa" nadiya
tabashi amsa tana mai sake juya masa baya
dan kar yaga fuskarta,
"Nadiya kenan wai wannan kunyar yaushe zaki
dainata ne? Kullum idan nazo sai ki gudu ki
buya alhalin nikuma saboda ke nake son zuwa
gidan nan, duk ranar da ban gankiba idanuwana
radadi da zugi suke yimin, kuma nazo sai ki
hanawa idanuwa tozali da kyakkyawar fuskarki?
Uhm nadiya? Dan jiyo mana.."
Badan taso ba ta dan jiyo dakyar tana kallon
kasa,
"Kinga kyankyaso nan a bayanki.."
Tun kafin ya karasa maganar ta dako tsalle
tabar wurin sai gata a bakin kofar kitchen din
kusa dashi, dariya ya fara yimata domin dama
yasan tana mutukar jin tsoron kyankyaso
shiyasa lokuta da dama yake tsoratata dashi,
Ganin yanata dariya yasata gane cewar ba
dagaske yake ba,
Fuska ta bata, "yaya kabeer ashe dama
tsokanata kake?"
Dariya ya sakeyi ya daga mata gira,
"Wasane matar yaya kabeer.."
Hannuwa tasa ta rufe fuskarta cikeda kunya
domin kowa adangi da haka yake kiranta tun
tana yar jaririya har ta girma, kowa matar
kabeer yake cemata,
"Yau ina ka bar hular taka ka taho haka?"
Sai da ya dan matsa kusa da ita sannan
ahankali yace,
"Wai duk zumudin zuwa ganinki ne yasani
manto wayata da hulata adaki har sai da nazo
nnpc sannan na ankara.."
Dariya itama tafara yi masa, yayinda shikuma
ya tsaya yana kallon yanda kumatunta ke
lobawa, hakan ba karamin burgeshi yakeyi ba,
"Kici gaba da dariyar bana son ki daina"
Tsagaitawa tayi daga dariyar da takeyi,
"Yaya kabeer na kawo kayi min assignment din
biology? Skeleton teacher dinmu yace mu zana
nikuma ban iya drawing ba"
Makale kafada yayi,"nima ban iya drawing ba.."
"Please yaya KB"
Jin abinda tace yasashi kallonta tareda sakin
wani tattausan murmushi,
"Dauko nayi miki"
"Yawwa yaya kabeer thanks.."
Rabawa tayi ta gefenshi ta wuce fuskarta dauke
da murmushi, juyawa yayi ya bita da kallo,
yanzu SS 2 take a secondary school alla alla
yake ta kammala domin so yake ya zama
mijinta sirrinta,
Yana nan a tsaye har ta fito hannunta rikeda
pencil, cleaner da note book dinta sai kuma
modern biology, tsayawa tayi ta bayanshi tana
kallonshi domin a zahirin gaskiya yayi mutukar
tsaruwa sam bashida makusa ko kadan.
Babu zato ya jiyo nan tayi gaggawar dauke
idonta daga gareshi,
"Yaya KB gashi.." Tafada cikeda jin kunyarsa
domin tasan yagane kallonsa ta tsaya yi,
Hannu ya mika ya karbi books din hannunta
sannan ya sakar mata wani murmushi, ahankali
ya furta,
"Ki ware idanuwanki ki kalleni son ranki kidaina
kunya saboda nidin nakine...."
Fuskarta ta rufe da hannayenta ta juya ta nufi
cikin kitchen tana cewa "kai yaya kabeer.."
Murmushi yayi kawai ya nemi wuri ya zauna kan
wani dan dakali dake zagaye da wasu flowers
wanda yake opposite da kitchen din,
Zana mata skeleton din yafara yi yayinda ita
kuma ta kafeshi da ido tana daga cikin kitchen
din bayan ta kammala mopping din da take yi,
Kallonshi ta tsaya take tayi ko kiftawa
batayi,dago kanshi yayi da niyyar yi mata
magana nan ya kamata tana aikin kallonshi,
Saurin kawar da kanta tayi ta juya zata koma
cikin kitchen nan yayi gaggawar dakatar da ita,
"Nadiya zo nan.."
Tana rufe da fuskarta ta karasa gabanshi ta
tsugunna,
"Meye kike satar kallona?? Ba nace miki idan
kina son kallona kawai ki kalleni kanki tsaye
batare da kunya ba..?"
"Nifa ba kai nake kalloba yaya kabeer" tafada
muryarta na rawa dan jin kunyarsa,
"To naji, idan nazana miki skeleton din ai basai
nayi miki labelling ba ko?"
Kai ta daga masa batare da tayi magana ba,
Murmushi yayi yaci gaba da zanen, "to bani
labari inji.."
"Yaya kabeer nikuma wanne labari na iya bare in
baka?"
"Ko na makarantarku ma idan kika bani ina so.."
"Ai makarantarmu babu wani labari acikinta"
"Kedai kawai bakya son ki fada min labarin
makarantarku..."
Kafin ta bashi amsa mama ta zo daf dasu zata
shiga kitchen domin dora tuwon dare, batare da
mama tayi magana ba tasaka kai ta shige cikin
kitchen,
Ganin mama yasa hirar tasu takare sai aikin
murmushi da suke aikawa junansu,
Littattafanta ya mika mata ya tashi tsaye yana
yimata wani murmushi wanda ita kadai ce ta
fahimci sakon da yake son isar mata,
Kitchen yabi mama yayi mata sallama ya wuce
batare da yayiwa nadiya magana ba amma
kuma yana ta kokarin aika mata da sakon
bankwana ta cikin idanuwansa sai dai ita ta
kasa kallonshi, tana tsaye tana satar kallonsa
har ya fice daga gidan,wucewa tayi ta nufi
dakinsu itada su amira,
Akan gadonsu ta zube tana mai tuno yaya
kabeer acikin zuciyarta duk da cewar har yanzu
bai bude baki ya furta mata kalmar so ba amma
tasan soyayya suke yi a boye ita dashi batare
da sun bayyanawa junansu sirrin dake cikin
zuciyoyinsu ba.
*_Ummi Shatu_*
[7/5, 3:35 PM] Ummi A'isha🏻: *MIJINA
SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
*HASKE WRITERS ASSO.*
**True life story**
*3*
aishaummi.blogspot.com
~~~Note book dinta ta bude tafara kallon zanen
skeleton din da yaya kabeer yayi mata, gefe
daya kuma kamshin turarenshi ne yake tashi
daga cikin littafin,
Bin zanen kawai take yi da kallo tana murmushi
wanda ita kanta bata san ko na menene ba
amma kuma zuciyarta tafi aminta da cewar
kawai na tsantsar farin cikine,
"I love you yaya kabeer.."
Tafadi ahankali tareda lumshe idonta,waleeda ce
ta shigo cikin dakin da gudu,
"Yaya nadiya kizo inji abba.."
Ajiye littafin tayi ta dauki hijabinta ta fita
saboda al'adar abbansu ce haka duk lokacin da
ya dawo daga office ko kasuwa to tattara
yaranshi yake yi a falonsa suyi hira masu wasa
suyi wasansu yana zaune yana kallonsu masu
karatu kuma suyi har lokacin sallar magrib yayi
a lokacin ne kowa zai dauro alwala yajasu jam'i,
haka sallar isha ma, wannan dalilin ne yasa su
nadiya basa fita ko ina idan ba makarantar
islamiyya ko boko ba sannan hakan ya haifar da
shakuwa mai karfi a tsakaninsu dashi,
Ahankali ta tura kofar falon abbansu ta shiga,
kishingide ta sameshi yana kallon labaran
yamma a tashar AIT, can gefe daya kuma Amira
ce da amir suke rubuce rubuce ajikin littafinsu
na makaranta da alama home work suke yi, sai
husna da walida daketa aikin mammatsa game
wanda duk karar game din ta cika cikin falon,
"Sannu da hutawa abba.." Nadiya tafada tana
kokarin zama kusa da abban nasu,
"Yawwa nadiya, kabirun har ya tafi ne?"
"Ehh abba ya tafi yanzu bai jima da tafiya ba.."
Shiru abban yayi ya maida hankalinsa ga kallon
labaran da yake yi, ita kuma nadiya wurinsu
Amira taje tasa ido tana ganin yanda suke yin
home work din har mama ta shigo ta iskesu.
K'arfe 9 nadare bayan su nadiya sun kammala
cin abincin dare mama tace suje su kwanta
domin har waleeda da husna sunyi bacci su
amir ne kawai idonsu biyu,
D'aukar husna nadiya tayi zuwa dakinsu ta
kwantar da ita akan katifarsu sannan ta sake
zuwa ta dauki waleeda taje ta kwantar da ita su
Amira suna biye da ita, gyarawa amir wurin
kwanciyarsa tayi ya kwanta sannan itada Amira
suka haye gadon dake cikin dakin suka kwanta,
Wayar mama dake ajiye a karkashin pillow dinta
ta zaro ta yiwa yaya kabeer plashing, kusan
kullum haka suke raba dare suna hira a wayar
mama amma ita maman sam bata taba sani ba
ita dai kawai tasan nadiya bata taba barin
wayarta ta huta mutukar tana gida sai dai idan
makaranta ta tafi to lokacin ne wayarta zata
samu lafiya.
Ko minti biyu da yi masa plashing din bata yiba
ya kirata,da murmushi akan fuskarta ta daga
wayar,
"Yaya kabeer kaje gida lafiya?"
"Lafiya lau nadiya, yasu mama?"
"Suna nan lafiya"
"Ya kunya?"
Dariya tasa saboda jin abinda ya fada,
"Yaya kabeer kenan kaima ai ya kamata ka rinka
jin kunyata.."
"Saboda me?.. "
"Saboda na cancanci hakan.."
Murmushi ya saki kafin ya bata amsa,
"See you, idan a wayane kibi ki isheni da surutu
amma idan nazo sai kiyi shiru ki kasa magana
kamar wanda zan kamaki"
Itama dariyar tayi, "to ba kaine ba"
"Nine me?"
"Kaine idan naganka sai naji nakasa yin
maganar.."
Dariya ya sake yi, "nadiya kenan.."
"Meya faru yaya kabeeru?"
Murmushi yayi saboda jin ta kirashi da kabeeru,
"Kin ganki ko? Bakinki ya iya fadin kabeeru sake
fada naji"
"Yaya KB.."
Dariya suka yi dukkaninsu musamman ma shi
kabeer din wanda yake cike da nishadi cikin
wannan dare,
"Yaushe zaka zo? Zaka zo gobe?"
"Yaushe kike son kara ganina? Duk lokacin da
kike son sake ganina zanzo.."
"Koda kuwa yanzu ne?" Ta tambayeshi tana
murmushi,
"Yes even now i shall come if you wish..."
"To ina jiranka idan har dagaske kake zaka zo
din"
"Dagaske kike kina son ganina yanzun..?"
"Kaji yaya kabeer da dawasa nake? Dagaske
nake mana"
K'arar bude kofa ta jiyo hakan yasata saurin
dakatar dashi,
"Ina zaka zo da tsohon daren nan?"
"Sabon dare dai ba tsohon dareba,wurinki zanzo
ki ganni"
"To yi zamanka na hakura da wasa nake yi.."
"Inama kiyi dagaske kigani idan zanzo ko bazan
zoba"
"Yaya kabeer kenan ai nasan zaka zo"
Murmushi yayi, "to yaushe zan kawo miki
budurwata ne ku gaisa?"
Jin abinda yafada yasata mikewa da sauri bayan
zuciyarta ta harba, nan taji wani shiru ya ziyarci
cikin kunnenta duhu ya mamaye ganinta yayinda
bacin rai ya lullube zuciyarta gaba daya.
*_Ummi Shatu_[7/8, 6:42 AM] Humaira Khaleel:
*MIJINA SIRRINA...!*🌹
_(Labarin k'auna)_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
® *HASKE WRITERS ASSO.*
*_4_*
aishaummi.blogspot.com
~~~Hannu tasa ta danne zuciyarta gudun kada
ta faso ta fito waje,
"Nadiya... Yanaji kinyi shiru ko bazaki gaisa da
budurwar tawaba?"
Ajiyar zuciya ta ajiye ahankali, dakyar ta iya
sassaita tunaninta tayi magana ahankali,
"Yaya kabeer me zai hana ingaisa da ita idan
har ka kawo min ita?"
Dan murmushi yayi mai kayatarwa kamar yana
gabanta tana kallonshi,
"Ina fata dai har zuciyarki kika fada ma'ana da
zuciya daya.."
"Yaya kabeer kenan.."
"Nadiya kenan, nadiya yanmata"
Murmushin dole tayi kafin tayi magana,
"Yaya kabeer nafara jin bacci gashi kaga gobe
zanje school"
"Nadiya nifa da wasa nake yimiki banida wata
budurwa so karki dauka dagaske ne.."
Duk da cewar taji dadin maganarshi amma sai
ta basar,
"Kaji yaya kabeer da wani zance, to idanma
dagaske ne ni ba abin in tayaka murna bane??
Sanyayyen murmushi ya saki,
"Hakane to balle ma ba dagaske bane da
wasane"
Itama murmushin jin dadi da farin ciki tayi,
"Shikenan tunda kaji tsoro ka sauya magana.."
Yar dariya yayi wadda har tana iya jiyo sautinta,
"Nayarda naji tsoron..."
Juyi nadiya tayi taja bargo ta dan rufe rabin
jikinta,
"Yaya kabeer zan barka haka yanzu saboda
kasan gobe zan je makaranta"
"To ya nadiya babu komai, Allah ya kaimu goben
sai kin jini" yafada cikeda tsokana,
"Ok tom bye bye" tabashi amsa bayan ta lumshe
idanuwanta, katse wayar tayi lokacin da taji
yace "bye bye good night and have a nice sweet
dream"
Addu'ar kwanciya bacci tayi ta shafe jikinta, da
tunanin kabeer bacci yayi awon gaba da ita.
Washe gari da misalin karfe biyu nadiya ta
dawo daga makaranta dama ba makarantarsu
daya dasu amir ba su akusa da gida suke ita
kuma nadiya makarantarsu da dan tazara da
unguwarsu, a gaggauce ta shiga gida tana shiga
tasan cewar yaya kabeer yana gidan saboda taji
kamshin turarensa sannan ta hango takalmanshi
a kofar falon mama dan haka bata bari kowa
yaji dawowarta ba ta wuce dakinsu ta ajiye
school bag dinta ta fito ta shiga kitchen,
Abinci ta zuba ta zauna tana ci kamar ance kalli
window tana kallon wurin tayi ido biyu dashi
tsaye yana kallonta yana yi mata murmushi,
Sunkuyar da kanta tayi tadaina cin abincin,
murmushi kabeer yayi ya saki karfen dake jikin
window din,
"Kici abincinki dama kawai nazo ganinki ne, bari
natafi inyaso sai nadawo da yamma lokacin kin
gama laumar.."
Bai jira abinda zatace ba ya juya yawuce,
murmushi tayi ta tashi ta leka sai da ta
tabbatar da cewar yatafi baya gidan sannan ta
koma ta dauki abincinta ta nufi dakin mama
tana tafe tana cin abincin,
A falo tasamu mama tana shirya husna da
alama wanka tayi mata,
"A'a kekuma yaushe kika shigo? Jibeki kina
tafiya kina cin abinci, keda zaki yiwa wani fada
amma kece meyi"
Zama nadiya tayi saboda mama kamar yayarta
take sam...


Read / Download MIJINA SIRRINA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album