Join Our WhatsApp Group

TANA TARE DA NI Complete Hausa Novel Document by TANA TARE DA NI


TANA TARE DA NI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 244141



TANA TARE DA NI

Reading Time: 20 Hours

Added On: 21, Oct 2023

Author: Miemiebee ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 1.35 mb

File Type: txt

Views: 645+

Download: 1297+

Last download: 13 hours ago

Description/Story: [16:09, 12/19/2016] Swtbaby: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫

❣🎀❣🎀❣

*_written by miemiebee👄_*

In dedication to *Aunty Sis💕*
0⃣1⃣



*ANAS*
     K’auyen Bama dake jihar Maiduguri, Borno.

            Da yammacin ranan Asabar misalin k’arfe biyar da mintuna aka. Ruwan sama akeyi me ni’iman gaske, ga wani iskan dake hurawa me kad’a bishiyoyi da flawoyi, ko ina ya d’au sanyi. Tsit kukeji a garin, yara da manya, maza da mata kowa na cikin gdajensu, masu tafiya akan hanya kuwa sun faka gu d'aya, motoci dabasu fi a k’irga ba ke wucewa time-to-time. Can k’ark’ashin wata bishiyar ’yim na hango wasu samaruka guda hud’u wanda barasu gaza kuma barasu fi shekaru 17-18 ba.

        Daga nesa nake, amman hakan be hana ni tantance kyakkyawan cikin wad’annan samarukan ba. Wani kyansan ma sanda na gama k’arisowa, fari ne yellow shar da gashi kwance a duk sassan jikin d'an Adam da akasan na tsirar da gashi. Gashin kansa nada yawa saidai bawai afro tayi ba saboda tsantsin gashin bai tsayuwa, luf-luf yake kwance a kansa, bak’i k’irin yana yalk’i wane yasha mai.

      Saje ne kwance akan farar fatar fuskarsa wanda da ace yanada gemu da sun had’e. Gashin girarsa ba a cike take erin thick dinnan ba, silky yake a kwance d’an siriri wane yayi carving nasu. Dogayen eyelashes nasa wanda suke kallon k’asa santsi ne dasu. Bashida dara-daran idanunu, idanun nasa suna nan madaidaci da k’wayoyin idan nasa light blue wane na bature.

          Nasha jin ana cewa a Africans akoi masu blue eyes ban tab’a yarda ba sanda naga wannan saurayi. Hancinsa ma ba dogo har bakan nan bane, daidai yake cikin 'yar fuskarsa wanda yakasance shi ba dogo ba bakuma gajere ba. Bakinsa light red yake d’an madaidaici cikin fuskar tasa. Dukda cewar ya d’aure fuska hakan be hana dimple na kumatun damarsa lotsewa ba wanda babu hakan a na hagun.

   A zaune yake amman hakan be hanani tantace tsawonsa ba, dogon na miji ne, yanada faffad’ar k’irji duk da cewar siriri ne. Ofcourse ana cewa d’an Adam bai cika goma but za’a iya kiran wannan saurayi hallitar data cike goma bansani ba halan ya gaza ta hali amman inde ta hallita ne kam masha Allah, Allah yabasa, ban tsammanin akoi macen da zata ga wannan saurayi bata kuma kallonsa ba. I mean ba mace kad’ai bama kowa in all.

      Sanye yake da mint blue T shirt wanda ya mugun amsar farar fatarsa, jeans na jikinsa kuwa tad’an kod’e alaman tasha ruwa. Rik’e yake da kara a hannunsa yana wasa dashi da siraran yatsunsa wanda suke nan kan ba na miji ba.

      Gefensa saurayi ne me kama da shi sak, saidai komi na wannan kyakkyawan yafi nasa, kuma shid’in be kai kyakkywan fari da k’war jini ba, duk yadda akayi wansa ne na jini saidai na kasa tantance wane babba cikinsu. Sauran biyun k’arshen kuwa chocolate skinned suke, saidai still d’aya yafi d’aya haske.

     “ANAS na mata kenan!” Cewar d’an bak’i na k’arshen tare da kewayo da kallonsa kan kyakkyawan cikin nasun wanda nake da tabbacin shine ANAS d’in yana mai murmushi wanda hakan ya bayyano da brown teeth nasa, tabbacin kanuri ne shi kenan. “Uhm uhm fa BAANA!” cewar me haske na gefen d’an bak’in da yayi magana yanzun kenan. BAANA yace, “ah’ah barni in tsokanosa de.” Shide kyakkywan nasu da ake kira da ANAS be tanka saba, hasali, yi ma yayi kamar besan ana magana a gefensa ba se b’antare karan dake hannunsa yakeyi yana kallon yadda ruwan saman ke sauk’owa.

        Wanda nake kyautata zaton wan Anas d’in ne yace da d’an bak’in gefen nasa “barsa de KASHIM, neman magana yake yau gun ANAS.” KASHIM ya karkato da kallonsa kan BAANA “aikam naga alama rad’au a fuskarka, kuma wallahi kasan inya shak’ure ka bame k’wato ka, kasan halin mazan namu. Ko mata ma bai ragar masu ba bale kai,” ya d’an yi shiru sannan ya k’arisa “gardi” Yafad'a cike da gatsine.

     BAANA yace, “hummm zagen dai, naga kap nan gardawa ne har Shettima k’anin mun ma(k’anin Anas knan)” Duk suka k’yalk’yale da dariya illa shi wannan kyakkywa da suke kira da Anas wanda yayi burning face sekace besan me kalmar dariya ba.

        Niko miemie na matsu injiyo muryan wannan kyakkyawan da suke kira da Anas. Yawancin anacewa wanda yafiye kyan fuska bai fiye zaqin murya ba kuma hakan ne sanda na jiyo muryan Anas na k’aryata wannan batu.

        “You see, ruwan nan na tsayawa barama kuganni anan ba to talk more of kumin tsiya mtschww.” Cewar Anas tare da watso musu harara sekace mace.

      Lallai! Allah yayi murya anan, muryar Anas sautin na miji ne da anji amman saidai ba tattausar murya bace, zaqi ce ga me sauroro, bakuma zaqi erin ta mata ba saboda yadda muryar ke cracking a hankali in yana magana.

       “Toh Anas meyayi zafi daga fad’in gaskiya? Ai gaskiya ce wallahi kap ‘yan matan garin nan basu san wani na miji sekai, narasa menene kake dashi bamuda, ni da bansanka bama se ince asircesu kayi.” Cewar Baana yana nuna yadda abin ke damunsa.

      “Ahhh lallai Baana ka soma zarewa” cewar Kashim cike da mamaki. “Yanzu har seka tambayi ko mesa matan garin nan basu kula kowa se Anas? Bakada ido ne?” Shettima ya karb’esa “gaskia da alama.” Kashim ya cigaba, “k’warank’wasa ace yau ni mace ce nima sena so Anas wanga blue eyes sekace bature, ko ka manta teacher'n English namu da ke sansa.” Suka sake sheqewa da dariya at once kuma sukayi shiru suna jiran tsiwar Anas to thier suprise be ce masu ko uffan ba miqewa yayi da niyar tafiya dukda cewar ruwa akeyi fuskarsa a tamqe kwata kwata abin be basa dariya ba.

        “Haba maza yi hak’uri mana karka fad’a min cikin ruwan nan zaka tafi!” Cewar Shettima wansa tare da rik’o shirt na Anas. Harara Anas ya galla masa da nufin ya sake masa kaya, kafin ace me k’arfin ruwan saman ya dad’a k’aruwa ba yadda ya iya dole ya koma ya zauna. “Wai zanso inga Anas yayi aure wataran, muga ya zena controlling wannan uban temper'n nasa da matarsa.” Cewar Baana. Take Shettima ya juya ya kallesa tare da zaro masa ido yana me masa warning.

         Dukda cewar Anas be tanka sa ba amman fuakarsa takoma ja alokaci d’aya ya had’e girarsa gu d’aya kallo d’aya za’a masa asan ransa ya b’aci ko dan meh oho? Kodan kiran kalmar ‘aure’ da abokin nasa yayi ne?

      Cikin tsiwa yake maganar ba alamar walwala a tattare dashi. “Baana don't push it, nasha fad’a maka time without number bana san kana min maganan aure ko kuma ‘yan mata in muna tare, that goes to both of you” ya nuna Kashim da Shettima. “Banaso! Banaso! Inhar kuna sona yaci ace kundena for goodness sake!” Shettima ya dafe kafad’arsa “toh maza we are sorry.” kallonsa yayi ba tare da yace masa komi ba sannan ya kau da kai. Baana ya numfasa sannan yace, “toh ka fad’a mana why mana, kullum se kace bakasan kalmar aure ko budurwa amman baka tab’a gaya mana mesa ba, as friends we have to know ko bahaka ba Kashim?”

      Kashim ya giad’a kai “sosai mah kayi gaskiya.” Shettima kuwa dayasan mesa wan nasa bayasan wannan kalmomi guda biyu kawai ya kad’a kansa cike da nadama, yayi yayi ya ganar da d’an uwansa gaskia yakuma sa ya yafe wa mahaifiyar su amman ina abin ya gagara sam saboda abinda tayi ta sa Anas ya kariya, zuciyarsa a toshe take da bak'ar kiyayya is hardly aga Anas yana dariya, murmushin ma se in abu yakai ya kawo ne yakeyi.

      “I can't tell you guys, I'm sorry saboda talking about it makes me sick kawai ni kudena tareraya ta da wannan magana banaso give me a break please.” Baana ze sake magana Shettima ya dakatar dashi ta aza yatsa kan lips nasa. In akoi abinda yafi damun wannan abokai guda biyu, (Baana da Kashim) befi wannan halin abokin nasu ba, ace da an kira kalmar aure se mutum ya b'ata rai, aure da ta kasance sunnah me k’arfi wanda kowani d’an Adam keda burin cikata. Gaskiya da abun duba.

     Kashim yakasa hakura shikam sanda ya kuma tambaya “Anas munsan baka san maganan nan amman ka dage ka fad’a mana, who knows! we might be of help.”

     Juyowa Anas yayi ya kalle sa tare da wata murmushin takaici ta gefen lips nasa wanda a sakamakon hakan ya bayyano da fararan hak’waransa da suke kamar an daidaita tsawonsu “help? Hmmm, k’arshen k’ok’arin da zaku iyayi shine ku dawo da ita kuma koda kunyi hakan ma barinyi appreciating ba saboda tafita a raina, bana san sake sata cikin idanu na, ta cuceni ta cuci two siblings d’ina Shettima da Amal, and most of all ta cuci Abuu (mahaifinsu). I don't want her ever in my life.”

      Cike da mamaki Baana yace, “subhanallah wa kenan?” “Bade mahaifiyarku ba?” Kashim ya tambaya. Anas bece dasu komai ba Shettima ne ya giad’a masu kai da nufin eh mahaifiyar su Anas ke nufi. “Subhanallah! Subhanallah! Anas be kamata kana maganar mahaifiyar ka da ta kawo ka duniya haka ba, uwa uwa ce. Kome tayi maka ka tuna ita ta kawo ka duniyah.”

   “Thats my point!” Anas ya fad’a a masifanche. “Ita ta haifeni, ita ta kawo ni duniyah abin dayafi ban haushi fiye da komai kenan. Taya matar da ta kawo ni duniyah zata tafi ta bi wani na mijin daban ta bar family’nta a baya, How? Why? Mesa mata basuda tausayi? Mesa Allah yayi su mugaye masu san kai da abin duniyah mesa? Mesa basuda Imani? Mesa tayi breaking heart na Abuu haka? Har yau yakasa trusting wata ‘ya mace a duniya. Why does it have to be this way? Why? Mstchww!” yaja tsaki cike da haushi.

       “We are sorry” Kashim yafad'a cike da tausayi, so wannan grudge d’in Anas ke holding a zuciyarsa har yanzu saboda abinda mahaifiyarsa da Shettima tayi musu. Yau shekaru kusan bakwai kenan da sanin junansu amman be tab’a sanin mesa Anas ke cikin k’unci ba, kullum ba walwala a tattare dashi se yau. Tun ba yau ba yakeson jin me tarihin Anas amman Anas ko kad’an baisan maganar haka zalika ya hana wansa Shettima fad’a ma kowa. Yau d’inma halan saboda sun tak’ura masa ne yasa ya fad’a.

         Tun da suke a secondary school haka Anas yake, ko erin secondary school dating da akeyi d’innan Anas be tab’ayi ba hasali betab’a showing koda slightest interest akai ba ma. Unlike his brother Shettima daya d’au komi as k’addara yake living life nasa peacefully cikin walwala da dariya.

       Tunanin ya zeyi ya karkato da hankalin friend nasan kan gaskiya yake. Gyaran murya yayi sannan a hankalche yace “Anas we are all here for you, we are like brothers yanzu. Nasan how hard this must be for you amman dole kayi haquri ka rungumi qaddara kamar yadda Shettima yayi.”

       “No Kashim, I can’t baran iya ba. Karka had’ani da Shettima, Shettima was a small kid back then time da abin yafaru, definately ya manta komai bare iya tuna koda abu ba, but me? Da wayona da komai na wannan matar ta tattara kayakinta, we were all begging on our knees muna roqarta karta tafi... Mschww I don't want to talk about it banasan ciwon kai, you two have heard enough.” Anas ya fad’a tare da miqewa daga mazauninsa. “Finally ruwan ya tsaya” yayi qoqari canza topic d’in, yana miqa wanda a sakamakon haka joints na jikinsa suke sakar k’ara. “Shettima lets get going, yakamata mud’an taya Ummee da aiki kafin Maghrib yayi” (Ummee; k’anwar mahaifinsu wacce takasance tamkar uwa a garesu tunda mahaifiyarsu ta tafi ta barsu take kula dasu).

        Shettima ya mik'e shima suka d’anyi manly shake da juna, “alright! Se mun had’u a masjid” Anas yace da Baana da Kashim da suke zaune har yanzu sannan ya juya shida Shettima suka soma tafiya.

     “Huh!” Kashim ya numfasa, “ina tausaya wa abokin nan namu, like sosai. Zuciyarsa ta riga ta toshe da tsantsan k’iyayya.”  “Sosai fa Kashim, but tsaya kaga wani abu yanzun nan ze dawo” cewar Baana yana murmushin jin dad’i. “Bade ya manta blessing d’inba?” (Yaren da masu shaye shaye ke amfani dashi wajen kiran ‘wiwi’). Baana yace, “Yup!” Tare da d’aga girarsa sama yana murmushi.

*© miemiebee*
   beeenovels.mywapblog.com
[16:09, 12/19/2016] Swtbaby: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫

❣🎀❣🎀❣

*_written by miemiebee👄_*


0⃣2⃣




Tafiya suke a sahu d’aya, tsayin nan nasu na nan d'ai da kad’an Anas ya d’ara Shettima inba wai ance ya da k’ani bane za’a zata agemates ne. Daidai lokacin da suka yanko wata corner kenan Anas yasa hannu a aljihu yaji wayam ba komai, cak ya tsaya hakan yasa Shettima tsayawa...


Read / Download TANA TARE DA NI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album