Join Our WhatsApp Group

SHU'UMAR MASARAUTA Complete Hausa Novel Document by SHU'UMAR MASARAUTA


SHU'UMAR MASARAUTA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 44078



SHU'UMAR MASARAUTA

Reading Time: 3 Hours

Added On: 20, Oct 2023

Author: Ameera Adam ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION

Author Phone : 07062062624

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 226.16 kb

File Type: txt

Views: 6036+

Download: 2651+

Last download: 1 day ago

Description/Story: [10/4, 11:13 AM] Ameera Adam🌚: *SHU'UMAR MASARAUTA*


©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba. Ban yi shi don cin zarafin kowacce ƙabila da Masarautunsu ba.

SHAFI NA ÆŠAYA

Masarautar Huddam

Shekara Saba'in Baya (1953)

Wani irin zafi take ji yana ratsa ta tun daga tafin ƙafarta har zuwa tsakiyar kwanyarta, dalilin haka ya sabbaba mata karkarwar jiki tamkar wacce ta ji kiɗan gangi. Wanda hakan ne ya haifar mata gumin da ke tsatssafowa daga kowacce kafar da ke cikin ilahirin jikinta. Ba yau ne karo na farko da haka ya taɓa faruwa da ita ba, sai dai a wannan ranar ji take tamkar an saka ta a tukunya ana dafa naman jikinta da ruwan zafi. A hankali ta cije baki tana yarfe hannu haɗe da lumshe idanu. Baiwa Maimuna da ke bayanta tana mata fifita cikin ƙwarewa a makirci ta fakaice ta, ta yanki ƙasan jelar gashin kanta ɗan ƙanƙani ta yadda ba za ta fahimci hakan ba. Da sauri ta soke shi a jikinta haɗe da sauke ajiyar zuciya don ko babu komai ta san ta tsira daga siraɗin Fulani Umaima. Ta ɗan numfasa a hankali.

"Ki gafarce ni uwar ɗakina zan ƙarasa sashen Takawa na ce Jakadiya ta karɓo miki magani kamar yadda na ji kin ambata a baya, ranki shi daɗe lamarin ciwon nan na ki ƙara ƙamari yake yi amma tuba nake idan da kuskure a kalamaina uwar ɗakina."

Ta so musa mata kamar yadda ta yi kafin zafin jikin ya fara galabaitar da ita, dalilinta na yin haka bai wuce yadda take gudun kada Bayin cikin masarautar su fuskanci zaman doya da manjar da ke tsakaninta da Mai martaba ba. Gyaɗa mata kai ta yi haɗe da ruƙo hannunta ta furta, "Idan kin fita Maimuna ki turo mini Baiwa Zainaba." Cike da girmamawa ta russana, "Allah ya ƙara wa Fulani lafiya, Ubangiji ya buɗi ido lafiya ya kawo mana Yarima mai jiran gado cikin yalwar ariziƙi da ƙoshin lafiya." Da hanzari ta fice a gaggauce don ko kaɗan ba ta son wargaza shirin ɓoyayyar uwar ɗakinta. Sai da ta turo wa Fulani babba Zainaba sannan ta wuce sashen Fulani Umaima cike da firgici, tana tafe tana waige kamar sabuwar munafukar da ta yi gulma a fada. Da yake Fulani Umaima ta kwana da sanin shirinsu, tun da doshin magriba ta sallami bayinta suka wuce sashensu na bayi. Tamkar wacce aka jefo daga sama haka ta faɗa ɗakin Fulani Umaima da ke tsaye tana kai kawo don gudun samun matsala a shirinsu, duk da tana da yaƙinin Baiwa Maimuna ba za ta iya shallake wa umarninta ba.

A ƙasa ta zube tana sauke numfashi ta furta, "Hutawarki lafiya Fulani mai magajin masarauta, zinariyar Mai martana haskenki bai tsaya iya shi kaɗai ba kin haske lungu da saƙon cikin Masarauta. Ina gwanar wani ga tawa? Kin yi taki kin yi ta kowa, garnaƙaƙin dutse kike kowa ya ja da ke shi zai faɗi..." Fulani Umaima ta katse ta da cewar, "Ina fatan komai ya tafi yadda ya kamata?" Baiwa Maimauna ta saki murmushi, dalilin haka ya sa Fulani Umaima ta sauke ajiyar zuciya duk da ba ta kai ga jin amsar Maimuna ba amma ta fahimci sun yi nasara domin kuwa labarin zuciya a tambayi fuska. "Ranki shi daɗe an gama aiwatar da komai, ga wannan." Maimuna ta ƙarasa maganar tana kunto gashin kan Fulani Babba ta miƙa wa Fulani Umaima. Wani yalwataccen murmushi Fulani ta saki, Baiwa Maimuna ta ci gaba. "Yanzu haka tana can magashiyan har ta umarce ni da na aika Jakadiya ta karɓo mata ragowar maganinta a wurin Mai martaba." Wata irin dariya ce ta suɓuce wa Fulani Umaima wacce ba ta tsammace ta ba, tuna wacce take gabanta ya sa ta tsuke fuska haɗe da furta. "Ki jira ni." Uwar ɗakinta ta shiga can ƙarƙashin gado ta zura hannunta, ta ɗauko wani ƙoƙon kan ƙwarangwal. Wani garin magani ta ɗebo a ciki ta kulle a cikin wata 'yar busasshiyar ƙaramar fata. Ta fito zuciyarta fes cike da takun isa da ƙasaita. Sai da ta koma kan ƙasaitacciyar kujerarta ta zauna sannan ta miƙa wa Maimuna.

"Ki fara zuwa ki karɓo maganin wurin Mai martaba, amma ki tabbata wannan kika ba ta ta yi amfani da shi, za ki zuba mata a ruwa ko abinci kuma ki tabbatar da ta shafe jikinta da shi. Duk dare ina buƙatar ganinki domin akwai fitar sirrin da nake so mu yi." Cike da girmamawa Maimuna ta russuna. "An gama ranki shi daɗe, fansar kaina gare ki ya shugabata domin kai da kaya duka mallakar wuyane. Ki sa a ranki na aiwatar da duk abin kika buƙata na gama, Allah ya taimaki giwar Takawa ɗawusu mai yawan ado." Fulani Umaima ta gyaɗa kai sannan Baiwa Maimuna ta miƙe, har ta je bakin ƙofa Fulani ta furta. "Ki tabbata ba a samu matsala ba, idan aka samu matsala ki kuka da kanki." Baiwa Maimuna ta russuna. "Godiya nake uwar gijiyata." Sai da Maimuna ta ɗaure maganin wurin Fulani Umaima sannan ta nufi sashen Mai martaba, Jakadiya ta samu ta sanar da ita saƙon Fulani Babba. Kai tsaye Jakadiya ta tunkari turakar Takawa. Sai da rangaɗa sallama haɗe da kirarin girmamawa sannan ta isar da saƙon Fulani Babba. Kamar ba zai amsa mata sai kuma ya miƙe ya nufi wata jakar fata da ke saƙale a jikin bango ya zura hannunsa, wasu ƙullin magunguna biyu ya ciro ya miƙa wa Jakadiya, ta karɓa tana godiya. Har ta fara tafiya ya furta. "Daga yau a sanar da ita ta riƙa karɓar magani kafin almuru, ba a koyaushe muke da buƙatar hakan ba." Jakadiya ta amsa sannan ta fice ta damƙa wa Baiwa Maimuna tana jaddada mata saƙon Mai martaba.

Maimuna na shiga sashen Fulani Babba ta same ta kamar yadda ta bar ta, Baiwa Zainaba na gefe tana matsa mata ƙafafuwanta da suka ɗan kumbura. Cike da girmamawa ta miƙa mata maganin da Fulani Umaima ta bata sannan ta furta, "Allah ya ƙara wa Fulani lafiya, Ubangiji ya shiga lamuranki uwar ɗakina. Mai martaba ya ce a jiƙa rabi, rabi kuma a shafe miki jiki da shi." Idanun Fulani jawur kamar sabon barkono ta buɗe su a hankali ta furta. "A yi yadda ya da ce Maimuna." Zuciyar Maimuna ƙal ta tashi jiki na rawa ta jiƙa maganin kamar yadda Fulani Umaima ta gaya mata, ta taimaka wa Fulani Babba ta tashi zaune haɗe da kai mata ƙoƙon bakinta. Tas ta shanye shi sannan Maimuna ta shiga shafe mata a jiki gabaɗaya, sannu a hankali ta ji wata sassanyar iska na ratsata. Ta koma ta kwanta sakamakon jin daɗin jikinta da ta fara yi. Ta dubi su Baiwa Maimuna. "Maimuna za ku iya tafiya, Zainaba a tabbata an gyara makwanci su Khadija." Cikin girmamawa suka zube ƙasa, "An gama ranki shi daɗe, Allah ya ƙara lafiya ya kawo mana Yarima lafiya." Ba ta iya amsa musu ba sai ma runtse ido da ta yi sakamakon jin wata irin hayaniya da ta yi a tsakar kanta, ga wani irin jiri da ke ɗaukanta. A ɓangare ɗaya kuma wani abu mai tsini ya fara fusgar can cikin ƙasanta. A gurguje Maimuna ta fice haɗe da sake ba wa Zainaba umarnin gyaran ɗakin su Khadija da yake ita ce gaba da ita, ta juya ta fice daga ɓangaren 'yayan Fulani Babba. A sanyaye Baiwa Zainaba ta bi Maimuna da kallo don haka kawai take jin zuciyarta na wasuwasi a kan Baiwa Maimuna tun da ta taɓa ganinta ta shiga sashen Fulani Umaima sau biyu.

Kai tsaye sashen Fulani Umaima ta faɗa, kuma a wurin da ta tafi a nan ta koma ta same ta. Fulani Umaima na ganin Baiwa Maimuna ta faɗa uwar ɗaki, wani sirrintaccen akwatinta ta ɗauko ta buɗe cikinsa. Kamar kullin idan za ta ziyarce shi haka take saka wannan sihirtacciyar rigar da Boka Bamagujen dutse ya bata, a lokacin ma sai da ta tube kayanta gabaɗaya sannan ta zura rigar mai ɗauke da launin ja, baƙi, ruwan ɗorawa da launin ruwan ƙasa. Rigar ɗinke take da waɗansu ƙananan layu sai kuma wasu ƙananun rubutu da aka yi da larabci, wani ɗan ƙaho ta riƙe a hannunta sannan ta fito wurin da ta bar Baiwa Maimuna. Hannu ta miƙa wa Maimuna babu musu da yake ta san kwanan zancen ta ɗora tafin hannunta a saman na Fulani Umaima, wanda ta tabbata ba don wannan sirrintacciyar tafiyar da suke yi ba babu dalilin da zai kai hannunta jikin Fulani Umaima, musamman yadda take nuna ƙyamar bayi da talakawa ƙarara a fili. Saka hannun Maimuna cikin na Fulani babu jimawa, ta runtse idanunta ta ɗaga hannunta da ta ke riƙe da ƙahon ta busa sau uku sannan ta kira sunan Bamagujen dutse sau uku. Wata irin guguwa ce ta karaɗe cikin ɗakin kamar ƙiftawar ido sai ga su a bakin wani ƙaton farin dutse mai ɗaukar ido, wurin kamar rana tarwai babu abin da ba ka iya gani. Kamar yadda yake bisa al'ada a duk lokacin da suka ziyarce shi, sai da suka saka ƙafarsu ta hagu a tare a kan wani jini da ke malale a gabansu. Sun ɗan ɗauki kamar minti biyu a haka sannan suka ji an bushe da wata irin dariya wacce take alamta musu aikin da ya da ce su yi a gaba. Ƙafarsu suka sake ɗagawa suka ɗora a kan wani kabari da ke gaban wannan jinin sannan suka fara takawa suka haye can sama dutse. Zaune suka hango shi babu ko ɗigon sutura a jikinsa, Maimuna ta kawar da kanta gefe don har cikin zuciyarta ba ta son ziyartar wannan shu'umin bokon don dai ba ta da yadda za ta yi ne. Suna ƙarasawa wurin wata ƙaramar bishiyar kuka Maimuna ta russuna tana faɗin, "Fatan nasara a kodayaushe ya shugabata." Fulani Umaima ta ci gaba da tafiya don Maimuna ta san ko karen hauka ne ya cije ta ba ta isa ta ƙara koda taku ɗaya ba.

Fulani na zuwa sai da ta fara ɗiban wani jan ruwa a cikin wani ƙoƙon kan ƙwarangwal ta wanke fuskarta, sannan ta nemi wuri ta zauna tana fuskantar Boka Bamagujen dutse.

"Barka da aiki uban gidana."

Jinjina kai ya yi ya furta. "Barkanki Fulanin Sarki Abdul'aziz." Shiru ne ya ratsa Fulani Umaima ta kawo ido ta sa wa Bamaguje, ya saki murmushi don ya san wace ce Umaima. Ga tsananin buƙata fal ƙirjinta ga kuma taƙama da izzar mulki, kallo ɗaya ya yi mata ya fahimci halin da take ciki. "Umaima kin yi ƙoƙari."

"Sanin haka ya sa na kawo ziyara a ranar da ka buƙata." Ta amsa masa a taƙaice.

"Kin aiwatar da komai yadda ya kamata, don haka kishiyarki ita da Sarki Abdul'aziz sai kallo sai hange daga nesa. Matuƙar ba asirin nan ne ya karye ba, ba na jin kishiyarki za ta sake ɗaukan ciki a doron ƙasar nan. Ke ba ma ciki ba ina mai tabbatar miki ita da sake yin wata mu'amala da Sarki Abdul'aziz sai dai a lahira idan ana yi. Ina ragowar kayan aikin?" Ya wurga mata tambaya. Jin haka ya sa Umaima ta saki malalacin murmushi ta ɗebo gashin Fulani babba da gashin Sarki Abdul-aziz, haɗe da ƙasar maƙabarta da ta gidan tururuwa ta miƙa masa ba tare da ta tanka masa ba. "Mun sakar mata lalurar fitsarin kwance, kuma mun saka mata lalurar mantuwa da warin jiki." Bamaguje ya faɗa yana jefa tarkacen da Fulani Umaima ta bashi a cikin wata tunkunya da ke cike da jini tana tafasa. Kusan duk abin da suke tattaunawa Maimuna tana jin su, haka kawai ta ji tausayin uwar ɗakinta ya ɗarsar mata. Musamman da ta tuna zallar cin amanar da take yi mata mai haɗe da zagon ƙasa.

"Ina maganar cikin jikinta ya kwana?" Fulani ta tambaya cike da izza.

Bamaguje ta ɗebi wani jini mai yauƙi ya watsa a jikin wani allon farin ƙarfe. Take waɗansu inuwoyi suka bayyana, yana fara nazartarsu sai gani ya yi ɗuff komai ya ɗauke. Cikin da damuna ya sake ɗiban jinin ya watsa har sai da ya yi haka sau uku sannan ya dubi Umaima cikin damuwa. "Kishiyarki a daren yau za ta haihu!" Dum! Fulani ta ji tsakiyar kanta ya sara kamar wacce aka buga wa guduma. Rai a ɓace ta dube shi. "Wanne irin mugun labari nake ji haka, zancen banza kenan ƙafa ta mutu ta bar takalmi. Cikin jikinta ya fi komai ɗaga mini hankali..." Da sauri ya katse ta.

"Tun fil azal kundunsa rubuce yake da zanen ƙaddararsa, cikin kishiyarki shu'umin ciki ne lulluɓe yake da almara tamkar yadda masarautarku ta kasance SHU'UMAR MASARAUTA. Kamar yadda na gaya miki a yau za ta haihu..." Duk dakiya da ƙarfin zuciya irin ta Fulani Umaima sai da hawaye ya suɓuto mata, Bamaguje ya tsaya yana kallonta haɗe da jinjina kai. "Yau shekarata biyar kenan a cikin masarautar nan ko ɓatan wata ban taɓa yi ba, tun Fulani babba na da goyon fari Takawa ya auro ni. Bamaguje kana son na ƙare rayuwata cikin ƙasƙanci da rashin mamora?" Girgiza kai ya yi, ya sauke ajiyar zuciya.

"Wa ya ce miki ba za ki haihu ba?" Fulani ta zuba masa idanu zuciyarta na bugawa. "Yanzu haka kina ɗauke da juna biyu na tsawon makwanni uku." Kamar a mafarki haka ta ji kalaman Bamaguje na ratsa majiyar sautinta. "Ki yi imani da ni Umaima matuƙar ina numfashi ba za ki tozarta ba." Sanyi ta ji har cikin ranta.

"Da kai na dogara Bamaguje na yi imani da kai tun da ba ka kunyata mahaifiyata ba na tabbata ba za ka tozarta ni ba." Ta yi maganar a raunane.

Wata ƙatuwar kunama ya ɗauko da hannunsa ya ce, "Ba ni hannunki." A firgice ta wurga masa kallon baka da hankali, ya saki murmushi don ya fahimce ta. "Umaima kenan kura kike ga tsoro ga ban tsoro." Umaima ta haɗe fuska kamar ba ita ba. "An ya kuwa? Kar fa ka manta ko kura ta rame ta fi ƙarfin gawurtattun karnuka, dalilin haka ya sa masallacin kura ba a ba wa kare limanci." Murmushi Bamaguje ya yi. "Kwantar da hankalinki kamar kin faɗa rijiya. Matso kusa ki ji." Bamaguje ya furta. Tun bai rufe baki ba Umaima ta matsa kusa da shi, raɗa ya yi mata a cikin kunne lokaci ɗaya ta bushe da wata iriyar dariya cike da farinciki. Ta koma mazauninta na farko tana sauraronsa. "Ki tabbatar da kin aiwatar da abin da na umarce ki, don kuwa kowa rai ya yi wa daɗi ba ya mai shi ba."

"Bamaguje kenan! Ai ranar biyan buƙata rai...


Read / Download SHU'UMAR MASARAUTA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

4 Comments On SHU'UMAR MASARAUTA
avatar
zainab-8-2

6 months ago

Reply

Tnx

avatar
asiya-mashi

6 months ago

Reply

Allah ya kara basira

avatar
taskar

6 months ago

Reply

Replying to asiya-mashi

Ameen

avatar
taskar

6 months ago

Reply

Ameen

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album