Join Our WhatsApp Group

A WANI MASARAUTA Complete Hausa Novel Document by A WANI MASARAUTA


A WANI MASARAUTA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 42307



A WANI MASARAUTA

Reading Time: 3 Hours

Added On: 01, Sep 2023

Author: Safiyya Ummu Abdul ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 243.32 kb

File Type: txt

Views: 832+

Download: 277+

Last download: 21 hours ago

Description/Story: 🏤AWANI MASARAUTA
Hausaebooks
Ummu Abduol
Creat by:- Shuraih Usman
Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so

For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading
Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata
Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521

Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu
Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya
Hakkin mallaka (m) Ummi Abdoul

Page2⃣

Haka Parveen tabar dakin mahaifinta jiki bah kwari, koda ta isa dakinta hana kowacce baiwa ta shigo mata tai. Dakanta ta hada kayanta da duk wani abu datake buqata duk da tasan chan kamar a gida take, dakyar barci barawo ya kwasheta a daran..
Washe gari wuraren karfe Shadaya jirginsu ya tashi zuwa garin gombe, Koda suka isa sun samu mutanen mai martaba na jiransu, dan haka jirginsu na sauka suka shiga motoccinda aka tanadan musu tareda yan rakiyansu zuwa gidan Sarkin Gombe..

Fulani sai shige da fice take kamar bah matar sarki bah, cikin mintina kadan aka gyara mah Parveen dakinda zata zauna Tareda haka kalolin Abinci iri iri, yau Fulani cike take da Farinciki yarta zatazo, tana daki zaune Fardeen yayi Sallama ya shigo, amsawa tai tareda dagowa ta kalleshi, yadanyi murmushi Yace "Fulani wai sarki Salman na Qasar Saudi Arabia neh zaizo ko ko Obama??" naga Sai rawar Jiki Ma'aikatan gidan nan keyi, naga Mai Martaba Sai Fara'a yake, gashi kema nazo nasameki. Murmushi tai Sannan Tace "Yarima knan, Sarki Khaleed neh Tareda Yarshi ke Tafe inaga ma yanzu suna Cikin Garin nan Qarasowa kawai ya Rage, Yadan Yatsine Fuska Sannan Yace "badai Wannan Yarinyan Tashi bah Mara kunya n I hope Bah zama Tazoyi bah" Hade rai Fulani Tai zatai Magana sukaji Horn din motoci, Dasauri Ta mike Tafito daga dakin, Bayinta dake take mata baya suka rusuna suka gaisheta Sannan suka Soma binta a baya...

Futowan Fulani daidai da Fitowan Parveen daga mota, dagudu ta Qarasa tareda Rungumeta, cikeda Farinciki Fulani Tace "Barka da zuwa Yata" Bayin dake Wajan suka zube dan diban Gaisuwa, Parveen ta Yatsine Fuska tace "Ni Fulani banaso bayi na duqamin pls kice su daina" Dan Dariya Fulanin Tai Sannan Tace "Har yanzu dai kina nan da Halinki, Wannan Shine Ikon ai" Hannunta ta Kama sukai side dinta Cikeda Farinciki..

Sarki Khaleed ya Shiga fada Cikeda Farinciki, dasauri Mai Martaba Ya mike sukai Musabaha tareda Rungume juna, Sarki Alameen Yayi Matukar Farinciki da Ganin Abokin nashi, sun Zauna a Fada, Dakatai, Masu Anguwanni, da Sauran Masu Muqamai na Sarauta nata Kawo Gaisuwa, Sai Bayan Sallan La'asar Sannan Suka Samu kebewa a Side din Mai Martaba. Suna Cikin Hiran Bayan Rabo Yarima Fardeen Yayi Sallama Ya Shigo tareda Rakiyan Abokinshi Adnan da fadawanshi, Zama Sukai Kan Carpet din Falon Sannan Suka Soma Gaida Sarki, Sarki Khaleed Ya kalli Yarima Cikeda Kulawa Yace "Yarima an Girma Ya Karatu??? Ka Kammala neh?" kai Ya gyada Sannan Yace "Angama Ranka ya Dade", Sarki Khaleed Yashafa Kanshi Yace "Allah yamaka Albarka" Yarima Ya amsa da Ameen Sannan Suka Mike Suka Bar Falon...

Side din Yarima Suka nufa shida Abokinshi, har sunkai Bakin Kofan Ya Daga Hannu Batare daya Juyoba Fadawan dake Take musu baya suka Bar wajan Dasauri, Adnan Ya bude kofan Suka Shiga. Kan Three seater Ya Fada Tareda Sakin Wani dogon Tsaki, Adnan Yakalleshi Cikeda Mamaki Yace "Deen Yadai Whts Wrong?" tsakin Yakuma Ja Sannan Yace "Wallahi Mai Martaba neh Waishi dole sai nayi aiki a Nigeria nikuma Sam Banasan Zaman Kasan nan" adnan Yadan nisa Sannan Yace "Buh Yarima Yan Kasan nan nabuqatanka matuqa, Suna neman kwararun Likitoci Kamarka, Shiyasa Zakaga Mutane na fita Qasashen Qetare Ganin likita. Kuma Bawai dan Fararen sun Fimu baneh Aa! Zakaga Yawanci mah Baqaqen Fatan neh Anan tho.... Saurin Katseshi yayi ta hanyar dagamai Hannu, Dasauri Yayi Shiru, ya Mike Sannan Yace "pls katashi kaban waje I need privacy" Mikewa Adnan Yayi dasauri dan Yasan Halin Abokin nashi Yamai Sallama Ya bar Side din...

A Dakin Fulani Suka Yada Zango itada Yar nata, Hadimai Sai Hidima suke da Parveen kamar zasu hadiyeta, Hira Suke Sosai Cikeda Farinciki, Sunci sunsha Sannan Jakadiya ta nunama Parveen Dakinta Sannan ta Nunama Altine Nata dakin..Kwanan Sarki Khaleed biyu Ya Koma..

*Bayan Kwana Biyu*

Cikin Sauri Yarima Yafito fadawanshi na takemai baya, hannunshi Riqe da Agogo yana qoqarin Daurawa, Daidai Nan Parveen Tafito daga dakinta Cikeda Farinciki Tana Waya da Ummanta, Hankalinta Sam baikai kanshibah, Shima haka. Jitai Tayi karo da mutum Ta dago Zara xaran idanunta dasauri suka hada ido, Hade Rai Tai, Hadiye Yawu tai dakyar Da Qarfin hali Tace "Haba Mallan baka Gani neh" da Mamaki Yarima Ya Kalleta Yace....

Ummy Abduol✍🏻
🏤🏤🏤👑
*A WANI MASARAUTA*
🏤🏤🏤 👑

By Ummy Abduol


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Da Sunan Allah mai rahama maijin kai

TSOKACI
Ina rokon Allah yasa yanda nafara littafin nan nagama Lapia Allahumma Ameen....
Banyi littafin nan Dan cin zarafin wani ko wata Bah. Nayi neh Dan nishadi dakuma fadakarwa...ngd..

Page1⃣

*MASARAUTAR GOMBE*

Motoci neh wajan guda biyar suka shigo cikin Airport din dai dai inda jirgin ya sauka sukai parking, fadawa neh suka dinga fitowa daga motocin, biyu daga cikinsu suka shimfida wani hadadden red carpet a daidai step din jirgin, niko ummy na gyara tsayuwa dan naga wanene zai sauko daga jirgin yanda naga fadawan sai Rawar jiki suke. Andau mintina kamar sha biyar Sannan wani hadadden saurayi fari tas ya leko tareda yatsine fuska, Ahankali ya soma saukowa daga step din jirgin, motar dake tsakiya wani bafade ya bude, wani dan dattijo ya fito cikin kayan sarauta, Tsantsar kamar da suke da saurayin neh yasa na tabbatar da mahaifinshi neh..
Dan Murmushi saurayin yayi daidai sanda ya iso inda mahaifinshi yake tsaye, dasauri ya qarasa tareda rungumeshi, cikeda kasaita mai martaba ya dan bubuga bayanshi tareda cewa "barka da dawowa my son", dan murmushi yayi sannan yace "Am vry happy to see uh dad" murmushi mai Martaba yayi aka bude musu kofar motan suka shiga..

Basu tsaya koina bah sai katafaren gidan sarauta, horn motar farko tai aka wangale gate din Gidan, dagudu motocin suka shiga cikin gidan zuwa inda yakamata su tsaya, tsakar gidan bayi neh burjik kowanne yana aikinda aka sashi, Sanin dawowan Yarima Fardeen dakuma halinsa yasa duk ma'aikatan suka aje aikinsu don zuwa kwasan gaisuwa, mai martaba da yarima na fitowa sukai cikin gidan, tareda rakiyan fadawan dake take musu baya, ganin haka yasa kowa yakoma bakin aikinshi....

Kishingide suka samu fulani a babban falonta wata baiwa tana mata tausa, da sallama mai martaba ya shigo hannunshi cikin na danshi, baiwar na ganin sun shigo ta rusuna ta gaidasu sannan tabar wajan dasauri, mikewa zaune fulani tai tana murmushi tana kallan dan nata, cikin sanyanyan murya tace "barka da zuwa dana" murmushi kwance akan fuskarshi yace "lapia lau mum nasameku lapia?" fulani daketa kallan dan nata cikeda farin ciki tace "lapia lau, ya Karatu ina fata ansamu abinda akaje nema" kai ya gyada, mikewa mai martaba yayi tareda cewa " umm ni kunga tafiyata tunda ni ba'a gani bah, mutane na jirana" dan dariya fardeen da fulani sukai ya fice daga falon yana cewa " nima lokacina na nan zuwa", mikewa fulani tai tace "zakaci abincine Yanzu ko sai kayi wanka??" Dan jim yayi sannan Yace "bari nai wankan tukun", side dinshi ya nufa, ko ina a gyare tsaf ya shiga bedroom ya chanza zuwa towel sannan ya fada toilet...

*MASARAUTAR ZARIA*

Zaune take kan wani hadaden carpet bayi zagaye da ita ko wacce qoqari take dan taga ta farantawa uwar gijiyarta rai, wata da kayan itatuwa a gabanta tana barewa, wata kuma farce take gyara mata, wata kuma gashin kanta take taje mata tareda sa sinadarai masu sa gashi laushi da kanshi akai, wacce take kusada ita koh labarai take bata na ban dariya ita kuwa sai dariya take gwanin ban sha'awa, suna cikin nishadinsu jakadiya ta iso wajan dasauri tareda rusunawa Sannan tace " Allah ya taimakeki, uwar gijiyata nasan ganinki" bata rai tai Sannan ta kalli jakadiyan cikin bacin Rai tace "jakadiya mai yasa koda yaushe kikesan batamin rai??" na fada miki ki daina durkusa min kinqi, banaso naga babba kamarki ko wanda bai kaiki tsufaba yana durkusa min, cikeda ladabi tace "Tuba nake ranki shi dade insha Allah daga yanzu na daina" Mikewa tai Altine baiwarta itama ta miqe, jakadiya na gaba tana biye da ita har side din mahaifiyar nata...

A bakin kofa jakadiya ta tsaya ita da Altine suka karasa, da Sallama suka shiga dakin zaune suka sameta hannunta riqe ta Apple tanaci, dasauri Altine ta tsugunna tareda kwasan gaisuwa, Apple dinda ke hannunta ta aje sannan ta amsa gaisuwan tace "Altine dan bamu guri", dasauri tabar dakin, ta Kalli yar nata Tace " Parveen dama bah wani abu baneh, Aisha ce ta kirani ta roqi Alfarman Tanaso kije kiyi mata hutu koda na sati daya neh" shiru Parveen tai kanta na Qasa, Ummanta ta kalleta Sannan Tace " banji Amsarki bah??" dan dagowa tai Tace " umma ban ganeh wa kike nufi bah??" umma tadanyi Murmushi Tace "Aminiyata Aisha Matar sarkin Gombe" Damm! Gaban Parveen ya fadi idonta cikeda kwalla tace "Umma kinfa san halin Yarima nidai Banaso naje"...

Haquri Umma ta soma bata dakyar ta shawo kanta ta amince badan Ranta yaso bah. Da daddare mai martaba Ya kirata dan Tambayanta Shawaranda ta yanke, Batareda bata lokaci bah Ta amsa mai, cikeda murna yace "ki shirya Gobe in Allah ya kaimu sai mu tafi nida kaina zan kaiki dan inaso dama nakai ziyara masarautar gombe"..

Tho fah! Ya zaman Parveen zai kasance da Fardeen?? Sai kun biyoni dan jin yanda zata kaya..

Ummy Abduol✍🏻
🏤🏤🏤👑
A WANI MASARAUTA
🏤🏤🏤 👑

By Ummy Abduol

Page4⃣

A hankali yake binsu Har yaga sun nufu wani Hadadden Wajan shaqatawa, A Hankali ya saki Lallausan murmushi Har saida Fararen Haqoranshi suka baiyana, Parking sukai Drivern Ya fito dasauri ya zagaya ya budemata kofan, qafan damanta ta sako a qasa Sannan ta Sauko na Hagu ta fito a hankali tafara takunta Maijan Hankali Altine na take mata baya riqe da wayoyinta da jaka, wani dan Qaramin Canopy suka Samu, Parveen ta zauna Sannan Taima Altine alaman itama ta zauna. Samarine da Yanmata a wajan dukansu cikeda farinciki, kowanne canopy ka juya zakaga masoyane zaune suna Hira cikeda nishadi, Dan Murmushi Parveen ta saki daidai nan service din wajan ya iso, Cikeda ladai ya kalli Parveen Yace "Ranki ya dade meh kikeso??" Altine tai Saurin tareda da Fadin "Ruwa zaka kawo sai fayrouz da meat pie" Amsawa yayi harya juya parveen tace Cikin lallausan muryanta batareda ta kalleshi bah "Make it 3 pls" Amsawa yayi yabar wajan dasauri..

Daidai nan Fardeen ya qaraso wajan tareda neman kujera ya zauna, Altine ta mike dasauri, Murmushin mugunta Yayi yana Kallan Parveen data hade rai Yace "No! Bah sai kin tashi bah yanzu zan bar wajan" juyawa Yayi yaga mutane burjik a wajan kowa na Harkan gabanshi, Yawanji Masoyane. Ya kara Sakin Murmushi Sannan Yace Cikin Zazzakar muryanshi kamar namai jin barci "Paveen Or What ever uh r Cal, Har keh kin isah kizo gizanmu ki gayamin Magana??. Ni Nafi Qarin a Wulaqantani, indai Jahilci neh zan nuna miki koh Hali irin na jahilai" Tabe Baki Tai Tareda Kauda kai. Bata Ankara bah Taga ya Buga Tabur din tareda mikewa, Hakan yasa kowa dake Wajan Hankalinshi ya dawo kansu, cikin Kakausan Murya Ya nunata da dan yatsa Yace "Kinyi Kadan, Bakeba kaf danginku. Soyaiya ceh nace banyi dole neh?? Meh zanyi dake Har dazaki dinga bibiyata, Oh! Dan nace bana sanki Shine Zaki rinka bibiyana Akan na Kusanceki??, Mutanen dake wajan suka zazzaro ido suna kallan juna Yace "meh kike dashi??, inaso naja miki kunni kar ki qara kiran wayana ko kice zakizo nemana Akan daqiqin qudirinki na fada miki, Banza Mazinaciya", yana Gama fadi yabar wajan dasauri tareda jan tsaki, Har Yabar wajan Mamaki neh Qarara a fuskarta, Hawayen dake Maqale a idonta ya qarasa zubowa, Mutanen Dake Wajan sai Kallanta suke Tareda Allah wadai da Halinta..

Kallan Altine tai idanunta chabe Chabe da hawaye Tace "Altine mu tafi" Altine ta kwashi Wayoyinta da jakanta, kuka sosai Parveen take a mota har Suka iso gda, Dakinta ta nufa tama Altine alama na karta biyota, Ta fada kan Gado ta fashe dawani matsanancin kuka. Fulani taji Dawowansu tanata sa ido taga Parveen anma Shiru har wajan Minti talatin, dakanta ta nufi dakin Tareda Sallama, Parveen najinta ta mike daga kwancen datake ta gogoge Hawayen Fuskanta, Fulani ta qaraso dakin Tace "Lapia Parveen naji dawowanku inata sa ido naganki yau nayi kewanki baki nan balle muyi hira" qago Murmushi tai Tace "Lapia lau fulani, Nagaji neh shiyasa dama Yanzu nake shirin zu..." Saurin Katseta Fulani tai da Fadin "Ya naga idonki yayi ja?? Parveen fadamin Gskiya meke damunki??" duqar dakai tai tace "Bkmai Fulani wani abune Ya fadamin ido" Dan Murmushin rashin Yarda fulani tai ta riqe Hannunta ta miqar da ita tsaye Tace "Muje kiga Wani abu" Tare suka fito Haraban gidan, Kamar ance ta dago suka Hada ido da Fardeen Dake chan nesa dasu Cikin Yar runfa suna Hira Shida Abokinshi, Wani Malalacin Murmushi ya Sakar Mata ta kauda kai dasauri Fulani na rike da Hannunta, Garden din Gidan Suka nufa, Sakin Baki Parveen tai Tana Kallan Garden din, A hankali ta Saki Hannun Fulani ta Qarasa Cikin Garden din, Saita nemi Bakin Cikin dake damunta ta Rasa, Ado Akaima Garden din, Fulawas neh burjik gwanin ban sha'awa, Daga gefe Guda hotunanta neh kala kala, Sai dan wanni kyalle da Aka Rubuta "Welcome to Badras Kingdom Princess parveen" Dariya tai Ta juya tana Kallan Fulani, Dagudu ta Qarasa tareda Rungumeta tana Dariyan Farinciki, Cikeda jin dadin yabawan datai Fulani Tace "Mai Martabane Yasa Akai Wannan" Sakin Fulani tai Ta karasa kan Wani hadadden Carpet dah aka zube Gifts Kala Kala, Ta...


Read / Download A WANI MASARAUTA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album