Join Our WhatsApp Group

MIWASMITI Complete Hausa Novel Document by MIWASMITI


MIWASMITI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 106894MIWASMITI

Reading Time: 8 Hours

Added On: 15, Sep 2023

Author: Aisha Ali Garkuwa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : ‪+234 909 785 3276

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 583.2 kb

File Type: txt

Views: 1186+

Download: 754+

Last download: 1 day ago

Description/Story: [4/9, 1:47 PM] ‪+234 909 785 3276‬: 🕌🕋🐄🐄🐄🐄
📝💫Bismillahirahamanirahim***🌳🐄
Mi'wasmiti. Page 1⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
🕌🐄🐄🐄🐄🐄

Tafiya take cikin sauri sauri da Dan sassarfa tana tafe tana Dan mita da holo irin Na tsofaffi da sauri Na dan qarisa gunta Na Dan kalleta a nitse a take Na gano tsohur ba fillatace cikin hikima Na gaidata da yaren fillanci cikin Dan sakin fuska ta amsamin ba tare da ta tsayaba a hankali Na bita gami da cemata kakata ina zakije haka da sanyin safiya gashi sai sauri kike kamar wacce jirgi ke shirin tashi ya barta ..
Ta Dan juyo ta kalleni tare da ci gaba da tafiyarta tana mai cemin ba doleba nai sauri ai ko faduwa zanyi Na fasa bakina Na zubda haqaran robar sai Na hamzarta .ai shi yafi jirgi shi sama da jirgi yake in ya shirya baya jiran kowa kuma shi jirgi ai yana bada lkci. toshi bai bada lkci shi tamkar hadari yake inya fito tofa ba jira kuma shi kamar guguwane sarkin birkita taro....
Cikin mmk nace keko kakata waye wannan ? kuma a ina yake? Cikin surutunta da mita tace gidan kamannin zani zanyi aikene Dan yau zasu gembu cikin mambila ..da Dan sauri na bita nace gidan kamanni kuma ?su haka sunan gidan yake ? Wannan wacce irin kamace dasu ? Na jera mata tabbayoyin aiko ta fara bani lbri tiryan tiryan🐄🐄🐄

Zuriyar Alhj Muhammad babayo Wanda akafi sani da Mlm babayo kuma sarkin shanu Dan asalin jihar tarabane can cikin mambila. Matansa 2 yayansa 5 maza 4 mace 1 uwar gidan innayi tana da Yaya 3 maza 2 sai mece 1 babban dansu barrister Muhammad Bello Muhammad sai mai binshi doctor Aliyu Muhammad sai qanwarsu Aysha.Muhammad

Sai amariyar yayanta 2 duk maza Amadu shine babban danta sai hamisu
Duk da kasan cewar mlm babayo ba fillatanine baiyi qasa a guiwaba wajen ilmantar da yayansa ilimin zamaniba sunyi karatu mai zurfi

Barrister M.B.M Wanda suke kira baba bello yana da matarsa daya Nenne Aihuwarta 12 Amman yanxu haka yayanta 3 ne kadai sabida aihuwar wabi take Sadiya itace babba bayan aihuwar sadiya sai da tayi aihuwa 5 duk suna komawa sai Na 7 in ta sami da namiji mai suna Ahmad tokoran qaninshi Amadu bayan Ahmad ta kuma aihuwa 4 duk suna rasuwa sai ana 12 ta samu Allah ya barmata shi sunanshi Rabi,u...

Sai doctor Aliyu Wanda suke kira Abba da matarsa Ummi yayansu 4 Yusuf shine babban dansu sai Abubakar da Usman sai Autarta Aysha .

Sai Goggo Aysha wacce take Aure a Yola tana auren doctor Umar babban Abokin yayanta doctur Aliyu Abba kenan yayanta 3 Adam sai hydar sai Maryam

Sai Amadu Wanda suke kira baba matarsa 1 yayansu 2 Abdul sai Amira.

Sai baba Hamisu matarsa 1 dansa 1 Sadiq .

Kamanni Family zuriyace da ta samu wadata da rahamar ubangiji Allah ya musu baiwa tako ina ga ilimi ga kyau ga arziqi ga zaman lfy da qaunar juna da tsantsar shaquwa da tausayawa

Su yayan inna basu karatu sosaiba sai suka Koma makarantar Dan gote baba bello da Abba su suka budemusu wani katafaren filin seye da sayarwa mai suna kamanni family kuma su Amadu da Hamisu suna zaunnene da iyayensu acikin garin mambilan yayinda
bb bello da Abba suke cikin taraba da zugar iyalensu sai dai alqawarinsu ne duk weekend suke zuwa gaida iyayensu da qannensu

Years en Adam da Yusuf da Ahmad dai daine Sa.annine su randa akayi 40 en Adam a ranan aka aifi Yusuf ran sunan Yusuf kuma aka aifi Ahmad rayuwarsu Ahmad Abin Sha.awane da burgewa rayuwace mai tsafta sun kasance masu qaunar juna ga wani irin kamanni da suke fiye da tunanin mai karatu mutane da dama sukan dauka yan 3 ne sabida zallan kama fararene tas irin farinnan mai daukar hankali gasu kyawawa tamkar larabawa ga tsantsar cikar haiba gashin kansu tamkar indiyawa kamanin su kuma ya samo asaline sabida dukkansu da iyayensu suke kama sukuma iyayen kamane Na haiqan a tsakaninsu

Sabanin abinda ke sakaninsu sai hali haqiqa halinsu ya banbanta dana juna kamar yadda wasu al.amura suka banbanta a tsakanin su Adam irin mutanenane da zan iya cemusu fadi garas mgn dai da zaran tazo ransu toh fa zata fito yana da yawan surutu da abin dry gashi da raha

Ahmad bawan Allah damo sarkin haquri haka Allah yayishi shi mutumne mai haquri da tawakkali ga sauqin kai ga iya zama da jama,a gashi da fara.a ko yaushe fuskarsa Na dauke da murmushi Sam bai iya fushiba shi....

Ayagi sarkin fada mishkili kafi mahaukaci ban haushi muqu baya dry sai Abu ya baci Yusuf yadda wasu Al,amura Na rayuwarsa yasabawa sauran jama,a hakama halinshi shi Yusuf irin jarirenane da ake aifarsu da kaciya a jikinsu shi da kaciyarsa ya fito duniya tun tashinshi bai da yawan mgn haka kuma baison yawan surutu gashi da ra.ayin riqau ba,a juyashi yana da zuciya ga iya horon yara baison shishshigi da Sa ido ko Kadan madafacine sosai zakayi zaman shekara dashi bazakaga dryarsa ba haka kuma ko shekara 4 zakayi dashi da wuya kaga qwoyar idonshi kuma kab wanan halin bb bello ya gado yayinda shikuma Ahmad ya dauki haqurin Abba danshi Abba tamkar ba mai suna Aliyu bane. Amman duk da fadan Yusuf bayayi da su Adam sun shagu shaguwar da ba adadi tare suka tashi gida 1 daki 1 don dole mahaifin Adam ya haqura ya barshi a taraba tare sukayi marantarsu tun daga primary har xuwa university innada sukayi digiru ensu Na firko a qasar India Yusuf da Adam sun karanci medicine shi kuma Ahmad Abba ya sashi ya karanci business Amnan shi Yusuf yanxu haka yana karatu a jami.atul Madina enda yake qara karantar likitanci a musulunci Sai in sun Dan samu Hutu yake zuwa kamar yanzu tun cikin Ramadan yazo duk ya buwayi qannenshi mu samman Aysha da basa hada inuwa daya tamkar wuta da audiga haka kuma su Usman da Abdul d Rabi,u suma duk ya fara gungurarsu Amira ko dama cewa take suna zuwa bikin sallah bazata dawoba sai ya Koma Dan ita Amira a gaban bb bello take haqiqa kowa najin takaicin yadda Yusuf da Aysha basa shiri qiyeyyace sosai Yusuf yake mata wasu lukutan ji yake kamar ya karyata Ahmad kuma wata soyeyyace mai qarfin gske ke tsakaninsu hakama Adam da Amira

Kumuje zuwa dai Ku biyoni a hankali lbr Na can gaba 🐄🐄🐄

By garkuwan fulani
[4/9, 1:47 PM] ‪+234 909 785 3276‬: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
MI,WASMITI.....page 2⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Taci gaba da bani lbr su Usman da Rabi,u da Abdul ma Sa,annine hakama Aysha da Amira da Maryam ...
Yusuf ya kasance mai zuciya tun yana dan yaronshi sanadin zuciyarshi yanzu haka yana da matsalar ciwon zuciya💔 tun suna primary school yana dan shekara 6 makarantar su da aka shigar dasu yinifom en makarnar dan gajeren wondone da yar riga Amman tunda aka dinka musu kayan Yusuf yake ta faman cin rai shi ala tilas bazai Sa gajeren wondo ba dan shi ya kasance mai kunyar bayyana jikinshi tako wanne bangare ne ba yadda ba,ayi da shiba yaqi Abba yace sai a shigar dashi wata makaratar nanma yaqi yace shi dai inda su Ahmad suke nan zaije dole akayiwa shugaban makarantar bayani da yake abokin bb bello basu samu matsala ba
Yusuf ya kasance mai kwarjini agun abokan kara tunshi kowa so yake yarabesa ko dan ilimin da Allah ya bashi

Wata rana a makarantar yayi fada da wani yaro Mujaheed aiko suka rinqa gudu dan ya samu ya yarama Amman ya kasa kamo Mujaheed ga mlmansu da suka shiga tsakaninsu shi kuma yace dole sai ya rama da aka hanashi ramawarne ya rinqa kuka cikin xuciya da takaici kuka yake har numfashinshi Na yankewa basuyi auneba ya fadi sumemme

Kai tsaye gida suka kawoshi Abba ya dugufa coto rayuwarsa da qyar aka samu ya farfado yana tasowa da kuka ya farka yana wlh ni sai Na rama bazan yardaba abi dai yaci tura dole aka nemo yaro yazo da iyayenshi yana zuwa Yusuf sai cewa yayi yazo gabansa ya duqa zai rama Abban mujaheed ya tura masa shi yana jeka ya rama aiko ya samu tsakiyar bayan shi ya rinqa dakamar duka gami da cemai wlh in baka ban haquriba bazan bar kaba yaro ya juya ya bashi haquri
To daga nan suka zama abokai

Ta dan zagaita surutun nata ta kalleni anitse tace to abinda yasa kikaga ina saurin Yusuf yazo nasan zai azalzalamusu su tafi ba tare da nakai aikenaba.""""
Na danyi dariya a raina nace hajia Zubaida ikon rabbi daga tabbaya daya taban bayanin da ya zarce zatona
Tacemin jikata ban sankiba gashi har mun saba daga ina kike haka nadan kalleta a nitse nace ni bakuwace daga jihar Adamawa nake sunana Aysha Ali Garkuwan Fulani kuma dama nazone gun Fulani yan uwana saiko nai Sa,ar cin karo da zuriyar sarkin shanu nima zasu barni Na kaimishi gaisuwar sallah ko? a madadin babana
tace sosaima kuwa ai suna son baki

⭐⭐⭐⭐⭐⭐

Babban gidane Na gani Na fada acikin babban birnin taraba gate en gidan ma kawai abin kallone ga ma aikata tako ina jamin sarone masu tsaron barrister M B M cikin gidan muka nufa kai tsaye wani babban parlor mai kama da dakin taro cike yake da mutanen gidan cikin hikima Na zuba musu ido 👀 dan naga wani abin al,ajabi kamace ta gsky a fuskokinsu gaba dayansu shiga iri daya sukayi galilace mai kyau da tsada bb bello da Abba suna zaune kan kujera daya tamkar tagwaye sai dai Abba ya dan fishi tsawo sai Nenne da Ummi suma suna zaune wuri daya cikin shiga ta alfarma da ka gansu kaga jin dadi da kwanciyar hankili haqiqa Nenne macece mai mutunci da kawaici da tsantsar qawaunar dan wani ga alkunya bata iya gwada son yayanta sama da sauran yaran Ummi Na mutunta ta matuqa
Daga can gefe kuma su Usman ne suna dan hiransi.

Ahmad kuma da Adam suna tsakiyar porlon kan wani tattausan carpet Sai Amira da take ta zirga zirgan zuwa tadda Aysha wannan zuwanta Na 3 kenan sai ta tashi ta zauna da zaran Amira ta fita sai ta sake nadewa a borgo

Muna shigowa ba jimawa

Naji wani irin qamshi mai ratsa zuciyar dan Adam nan take parlon ya hargitse da qamshin mai dadin shaqa gaba daya Na maida hankalina kan qofar danafi zaton tanan qamshin ke shigowa

Cikin nitsuwa yake tfy da cikar kamala taku yake da salon girma hasken fuskarsa kamar tauraro⭐ komai najikinshi tamkar shi ya tsarawa kanshi kai tsaye gaban bb bello ya dan duqa ya gaidashi ya gaida su Nenne ya dan miqe yana gyara riqon da yayiwa briefcase enshi da woyoyinshi ya miqawa Ahmad hannu suka gaisa Adam ya dan harareshi cikin tsokana yace kai yaro ninefa babba ka fara gaida kanina ya qarishe mgnar yana dry
Ya dan kalleshi cikin salon ka isheni da shegen son girma

Abdul dake gefe yace good morning Hamma Yusuf a hankali yace morning Usman dake zaune gefen Abdul yace da kyau ba gaisuwaba ai yayi mgninka shi ko gaisuwar baiso dan haka ni bazan wahal da bakinaba Rabi,u ya danyi dry yace ni bari in gwada ya dan kalleshi da kyau yce Hamma Yusuf..... da sauri ya daga mai hannu ya yimai nuni da su taso su tf ya dan kalli bb bello yace baba mu tafiko

Sagal kaka ta amshe mgnar tana mai cewa kai Yusufa ni ban kai ka gaisheni bane komeye kana tafe kana yamutsa fuska kai dai har Abadan baza,aga fara Arkaba
Rabi,u ya ce toh ma ai Aysha muke jira tun dazu bata fitoba ya dan juya ya qarewa parlon kallo bata gun Amira dake manne jikin Ummi sai yanxu tace Hamma Yusuf ina da sauri ya dakatar da ita gami da cewa cikin mishkilanci da Alamun bacin rai yana mgn da dan fada fada ke tashi kije ki kirata in kuma ba hakaba wlh zan shigo Na babbalata muna fukar yarinya sai baccin tsiya ta iya da sauri ta nufi dakin
Kaka kuma taci gaba dacewa Amira kije kicemata jirgin✈ ya iso kuma har ya fara dirin tashi ta dan juyo ta kalleshi kanshi a qasa tace mutum baida aiki sai sababi ni wlh ai wannan turaren daka zubbuda zai sani mura Abu kamar anyi barin motar turaren ta kuma shaqar qamshi tai ajiyar zuciya tace gsky ka tsammin turaren dan wlh yamin dadi ya kalleta cikin murtuqe fuska ya dan tabe baki
Adam ya kwashe da dry yace kai kaka sharrinki yafi ta tsohuwar mota yanxufa kikace zai kasheki da turaren zai saki mura sai kuma kice ya baki duk sukayi dry yace Allah biyaye karka bata ta dan harari Adam tace toh dan hassada kada Allah yasa ya banin mana ga mai gidana zai sayamin ta fada tana kallon Ahmad ya danyi murmushi yace zanma dauko miki nashin matar
Tai dry cikin jin dadi Usman yace toh yaukuma menene saqon naki?
tce kai da Allah tafi daga can mai muryan mata kai sai shegen made Amman dai duk da hakan kafimin yusufa kam ta maida hankalinta kan Ahmad tece Ahmadu in kaje kace innayi ta baka naman raqumi nakeso..... aiko su
Rabi,u sun sami abin dry Yusuf ya kalleta yana cewa Aku kawai baki da aiki sai surutu sai shegen kwadayi ke dai nama nama kowa ya gaji da nama Amman banda ke
Edin tace nayi surutun so kake naita baqin hali irin naka baki kamar dinkekke andai ji jiki wlh kuma sai kaban turarenan ehe
⭐⭐⭐⭐
Kwance take ko a jikinta kamar ba ita ake jiraba cikin sauri Amira ta daka mata duka ke Aysha toh wlh ga hamma yusuf ya fito
Da sauri ta bude ido gami da zazzarosu 😳 ta diro daga kan gadon tana qoqarin cire kayan jikinta gaba daya jikinta bari yake tana shiga toilet tana Na Shiga uku 🙉 dan Allah Amira fitomin da kayana da mayafina da takalmi yau kam Na kade mugu ya samu dan dalilin jibgata

By garkuwan Fulani

Ku biyoni masu karatu wannan goron sallarkune daga gareni
[4/9, 1:47 PM] ‪+234 909 785 3276‬: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 MI,WASMITI.....page 3⃣ Na Aysha Ali Garkuwa 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

9:55 PM*12-09-2016

Bayan ta gama yan gyare gyarenta ta fito sab da ita gonin sha,wa Doquwar rigace ajikinta tayi kib da ita cikin sauri ta dauki ribbon enta da dan kwalinta a hannu ta fito parlon tfy take cikin sauri sauri hankalinta gaba daya nagun Ahmad shiyasa bata lura da shi a gunba tana isa ta miqawa Ahmad en ribbon en gami da dan juya bayanta tce ya Ahmad gashi tufkemin gashina ga yan kunnena ma ka samin da sauri kasan yanzu za,aitamin masifa...


Read / Download MIWASMITI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album