Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

BAƘAR MASARUTA Book 2 Complete Hausa Novel Document by BAƘAR MASARUTA Book 2


BAƘAR MASARUTA Book 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 179298



BAƘAR MASARUTA Book 2

Reading Time: 14 Hours

Added On: 20, Jun 2024

Author: Umar Faruq D ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08038135929

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 989.86 kb

File Type: txt

Views: 790+

Download: 1903+

Last download: 17 hours ago

Description/Story: 
*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*01*



Duk wani mai imani idan yaga halin da Bir yake ciki sai ya tausaya masa, sabo da yadda waƴannan dakarun suka yagal-gala sa tamkar sun riƙe tsumma a hannun su.

Wani badakare ne guda ɗaya ya damƙo sumar kansa yana mai ɗago sa daga kwancen da yake zuwa zaune a haka.

Da ƙarfi Bir ya rumtse idanuwansa, yana mai sakin wata irin ƙarar azaba.
Sai dai kuma tun kafin ya gama dawowa dai-dai ya sake jin wacce tafi ta farkon raɗaɗi a cikin ƙwaƙwalwarsa, saboda yadda wannan badakaran ya ƙara funcikar gashin kan nasa yana mai gwara sa da jikin shirgegiyar Bishiyar da take manne a gefen ruwannan.

Lokaci ɗaya kuwa komai nasa ya tsaya cak, gaba ɗaya ya zamto tamkar gawa, domin ko hatta da numfashin sa ma ɗaukewa yayi.
Yayin da idanuwan sa kuma suka kakkafe suna masu kallon sama.


*ƘASAR HAUSA, JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULƊE.*

Tun da suka tafi Yarima Asad baice komai ba, sai Al'amin da Habu ne kawai suke ta zuba labarai yadda kasan sun daɗe da sanin juna, a haka har suka ƙarasa cikin ɗakin Habu da ya gaji da haɗuwa da wasu haɗaɗɗun kayan funitures, tare da docoretion ɗin kayan ado irin na fulani da aka ƙawata bangwayen ɗakin da su.

"Bismillah mu shiga daga ciki ko?"

Cewar Habu yana mai nuna musu ƙofar bedroom ɗin sa.
Ba tare da sunce komai ba suka rufa masa baya zuwa ciki.

Sosai aka ƙawata bedroom ɗin yayi matuƙar kyau, babu abun da yake tashi a cikin sa sai daddaɗan ƙamshin turaren da aka sanya a ciki.

Kan doguwar kujerar da suka gani kafe a jikin bango suka zauna.
Yayinda shi kuma Habu ya huce zuwa cikin bathroom domin ya haɗawa Yarima Asad ruwan wanka.

Lumshe ido Yarima Asad yayi yana mai ɗan sakin wani ɗan gajeran numfashi.
Har yanzu babu abun da yake gani face kyakkyawar fuskar ta a cikin idanuwansa.
Sosai yake son ta ɓace masa daga zuciya amma abun ya citira.
Zai iya cewa tun da yake a rayuwar sa wannan ne karo na farko da ya taɓa ganin mace har ta bar wurin sa tana cikin ransa ba tare da ya manta da babinta ba.

"To mene yakawo hakan? Me yasa sai akanta kawai zanji haka?"

Ya wastowa kansa tambaya a cikin ransa, yana mai ɗan tura lowar lips ɗin sa cikin bakin sa.

"Saboda ita kaɗai ce macen da ta taɓa yi maka laifi ta tafi ba tare da ta baka haƙuri ba, sannan kuma ita kaɗai ce bagidajiya a cikin matan da kake haɗuwa da su, kana kuma ko kallon mahaukaciyar suturar da take sanye a jikin ta da kayi ai zata saka ka kasa mantawa da ita."

Zuciyar sa ta basa amsar tambayar sa, amma sai kuma ya girgiza kai,yana mai faɗin.
"Inaa, to amma ai ita kuma kayan sun mata kyau, duk da kasancewar su na mahaukatan kuwa."

"Lafiya dai Asad? Wacece hakan, kuma mene yayi mata kyau?"

Muryar Al'amin ta daki dodon kunnensa yana mai wasto masa tambayoyi.
Hakanne yasa sa fahimtar cewa zancen zucin da yake ya futo fili ba tare da ya sani ba.

A hankali ya ɗan buɗe idanuwansa da suke a lumshe, tukun ya ɗan juyo da fuskar sa ɓarin da Al'amin yake, yana mai zuba masa lumsassun idanuwansa da gaba ɗaya suka canza launi akan fuskar sa, ba tare da ya iya ce masa komai ba, domin kuwa bai san abun da zai ce masan ba.

"Ya dai Aboki, shin meke faruwa ne wai?"
Al'amin ya faɗa yana mai sake fuskantarsa, tare kuma da gasgata abun da yake tinani a cikin ransa tun ɗazu.

"Babu."
Yarima Asad ya faɗa ataƙaice yana mai janye idanuwansa daga cikin na Al'amin.

A kuma lokacin sukaji muryar Habu yana cewa.
"To Aboki bismillah komai yayi ready, wankan kawai ya rage maka."
Ya faɗa yana mai ƙarasowa bakin kujerar da suke zaune a akai.

"Thank you."
Yarima Asad ya faɗa a taƙaice, yana mai tinanin yadda za'ayi ya iya wanka a wani wurin da bana sa ba, domin kuwa shi dai yana da matuƙar ƙyanƙyami.
Kana kuma ko abubuwan da suka zamto mallakin sa muddin yayi amfani da su sau ɗaya to ya gama baya mai-maici, gashi kuma bashi da tabbacin zai samu komai sabo anan cikin, hakan yasa yaji tamkar kawai yacewa Habu ya fasa yin wankan idan yaje gida yayi.
Sai dai kuma da ya sake kallon jikin sa yaga yadda gaba ɗaya yake a ɓace, ga ɗan ƙarnin da yake ta taso masa yana dukan hancin sa, sai yaga ai gwanda yayi wankan koma a ina ne da tafiya a haka, kuma yana tsammanin ƙila ya samu wurin da tsafta ma, tunda ko a cikin ɗakin ma babu wani abun wanda ya dan ganci ƙazanta da suka gani a cikin sa, asalima ko nashi na gidan bazai nuna masa tsafta ba a yadda suka gansa, sai dai kawai ya fishi da kayan ado.

"Tabbas Yarinyar nan kin cuceni, kai anya ma ba mahaukaciya bace ba kuwa?
Haƙiƙa mahaukaciya ce yarinyar nan, domin kuwa babu wata mai hankalin da zata ai'kata abun da ta aikata kuma ta juya ta ƙara gaba ba tare da ta bawa wanda tayiwa hakan haƙuri ba, asalima sai kallon banza.
Lallaikuwa mahaukaciya ce babba ma a cikin mahaukatan yarinyar nan, Allah ne ya rufamun asiri ma da bata shaƙo mun wuya ba."

Ya faɗi haka a fili cikin muryar sa da har dai ba kana kusa da shi yayi maganar ba baka isa kaji mai yace ba, yana mai tura kansa zuwa cikin bathroom ɗin.

Tsaye yayi a jikin ƙofar bathroom ɗin, yana mai lumshe idanuwan sa, saboda wani irin daddaɗan ƙamshin da ya bugi hancinsa.
Kana daga bisani ya wara su yana mai bin ko ina na cikin sa da kallo.

Komai neat yake babu wani alamun datti a cikin sa.
Kana akwai komai na buƙata anan ɗin ma, domin ko hatta da mirrow akwai sa manne a jikin bango.

Akan wata sabuwar baƙar bathrobe fidigil ya dire ƙwayoyin idanuwan sa.
Kana a gefen ta kuma sabon boxer da singilet ne a jiye suma.
Hakan ne yasa ya ɗan girgiza kai yana mai sauke wani ɗan gajeran numfashi.
Kana ya fara zame kayan jikin sa tun daga nan bakin ƙofar yana mai dosar gaban shower da ya hango.

Tsaye yayi a tsakiyar ruwan bayan ya kunna sa, yana mai lumshe idanuwansa.

Lokaci ɗaya ya fara sauke wasu irin tagwayen ajiyar zuciya, yana mai jin tsigar jikin sa na wani irin mimmiƙewa, sabo da yadda idanuwansa suka sake hasko masa kyakkyawar budurwar da yayi arba da ita tsaye a gaban sa.
Take a wurin kuwa yaji gaba ɗaya yanayin sa na sauyawa, ga zuciyar sa da take ta bada wani irin dip-dip-dip.

Da sauri ya buɗe idanuwansa, saboda sautin ƙarar nociking ɗin da ya daki kunnuwansa, da har yayi sanadin tsinkewar tinanin nasa, kasancewar zuwa yanzu ya ɗauki kusan mintina talatin da shiga, amma gaba ɗaya shi kansa ba zaice ga abun da yayi ba.

A hankali ya juyar da kansa yana mai kai idanuwansa kan ƙofar nan.
Yasan ba kowa bane zai aikata masa hakan sai Al'amin, hakan ne yasa sa janye idanuwansa daga kan ƙofar yana mai ɗan sakin tsaki.
Kana ya janyo sabon sponge and soap ɗin da Habu ya ajiye masa, yana mai haɗa kumfa ya fara saɓe jikin sa da shi cikin sauri, domin kuwa sai yanzu ya tina da basu kaɗai bane sukazo wurin ba hadda babban yaya, kuma at any time zai iya kiran su su futo su tafi, sai dai kuma har kawo yanzu tinanin Gimbiya Haddiyal yaƙi ɓacewa daga cikin ransa.

"Mtseewww! Shin anya ma kuwa mutum ce wannan yarinyar?
Haba, tsabar jaraba kawai kizo ki tsayawa mufum a cikin rai daga kalo ɗaya."

Ya faɗi haka a lokacin da yake ɗaura bathrobe ɗin da take saƙale a jikin sa, bayan ya sanya sabon boxer ɗin da ya gani a ajiye, sannan ya juyo yana mai kamo hanyar waje yana yi yana sakin tsaki.

"Wai kai me yasa ako ina ma sai ka nuna halinka ne banza kawai, ace ɗan watsa ruwan da zakayi ka futo kawai shine har sai ka ɗauki almost one hour baka gama ba."
Al'amin ya faɗa yana mai buga masa harara.

Shi kuwa Habu kwashewa da dariya yayi yana mai faɗin.
"Gashi kuma shi ba kalar ka ba ballan tana ace ko so yake ya dawo ɗan ja."

"Kuttt, wato har da kai kaima ko?"
Al'amin ya faɗa yana bugawa Habu harara.

"A a fa ni bance komai ba."
Cewar Habu yana mai tashi yayi gaban wardrobe ɗin sa.

Shi kuwa Yarima Asad inda suke bai ɗago ya kalla ba, ballantana har
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download BAƘAR MASARUTA Book 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album