Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*01*



Duk wani mai imani idan yaga halin da Bir yake ciki sai ya tausaya masa, sabo da yadda waƴannan dakarun suka yagal-gala sa tamkar sun riƙe tsumma a hannun su.

Wani badakare ne guda ɗaya ya damƙo sumar kansa yana mai ɗago sa daga kwancen da yake zuwa zaune a haka.

Da ƙarfi Bir ya rumtse idanuwansa, yana mai sakin wata irin ƙarar azaba.
Sai dai kuma tun kafin ya gama dawowa dai-dai ya sake jin wacce tafi ta farkon raɗaɗi a cikin ƙwaƙwalwarsa, saboda yadda wannan badakaran ya ƙara funcikar gashin kan nasa yana mai gwara sa da jikin shirgegiyar Bishiyar da take manne a gefen ruwannan.

Lokaci ɗaya kuwa komai nasa ya tsaya cak, gaba ɗaya ya zamto tamkar gawa, domin ko hatta da numfashin sa ma ɗaukewa yayi.
Yayin da idanuwan sa kuma suka kakkafe suna masu kallon sama.


*ƘASAR HAUSA, JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULƊE.*

Tun da suka tafi Yarima Asad baice komai ba, sai Al'amin da Habu ne kawai suke ta zuba labarai yadda kasan sun daɗe da sanin juna, a haka har suka ƙarasa cikin ɗakin Habu da ya gaji da haɗuwa da wasu haɗaɗɗun kayan funitures, tare da docoretion ɗin kayan ado irin na fulani da aka ƙawata bangwayen ɗakin da su.

"Bismillah mu shiga daga ciki ko?"

Cewar Habu yana mai nuna musu ƙofar bedroom ɗin sa.
Ba tare da sunce komai ba suka rufa masa baya zuwa ciki.

Sosai aka ƙawata bedroom ɗin yayi matuƙar kyau, babu abun da yake tashi a cikin sa sai daddaɗan ƙamshin turaren da aka sanya a ciki.

Kan doguwar kujerar da suka gani kafe a jikin bango suka zauna.
Yayinda shi kuma Habu ya huce zuwa cikin bathroom domin ya haɗawa Yarima Asad ruwan wanka.

Lumshe ido Yarima Asad yayi yana mai ɗan sakin wani ɗan gajeran numfashi.
Har yanzu babu abun da yake gani face kyakkyawar fuskar ta a cikin idanuwansa.
Sosai yake son ta ɓace masa daga zuciya amma abun ya citira.
Zai iya cewa tun da yake a rayuwar sa wannan ne karo na farko da ya taɓa ganin mace har ta bar wurin sa tana cikin ransa ba tare da ya manta da babinta ba.

"To mene yakawo hakan? Me yasa sai akanta kawai zanji haka?"

Ya wastowa kansa tambaya a cikin ransa, yana mai ɗan tura lowar lips ɗin sa cikin bakin sa.

"Saboda ita kaɗai ce macen da ta taɓa yi maka laifi ta tafi ba tare da ta baka haƙuri ba, sannan kuma ita kaɗai ce bagidajiya a cikin matan da kake haɗuwa da su, kana kuma ko kallon mahaukaciyar suturar da take sanye a jikin ta da kayi ai zata saka ka kasa mantawa da ita."

Zuciyar sa ta basa amsar tambayar sa, amma sai kuma ya girgiza kai,yana mai faɗin.
"Inaa, to amma ai ita kuma kayan sun mata kyau, duk da kasancewar su na mahaukatan kuwa."

"Lafiya dai Asad? Wacece hakan, kuma mene yayi mata kyau?"

Muryar Al'amin ta daki dodon kunnensa yana mai wasto masa tambayoyi.
Hakanne yasa sa fahimtar cewa zancen zucin da yake ya futo fili ba tare da ya sani ba.

A hankali ya ɗan buɗe idanuwansa da suke a lumshe, tukun ya ɗan juyo da fuskar sa ɓarin da Al'amin yake, yana mai zuba masa lumsassun idanuwansa da gaba ɗaya suka canza launi akan fuskar sa, ba tare da ya iya ce masa komai ba, domin kuwa bai san abun da zai ce masan ba.

"Ya dai Aboki, shin meke faruwa ne wai?"
Al'amin ya faɗa yana mai sake fuskantarsa, tare kuma da gasgata abun da yake tinani a cikin ransa tun ɗazu.

"Babu."
Yarima Asad ya faɗa ataƙaice yana mai janye idanuwansa daga cikin na Al'amin.

A kuma lokacin sukaji muryar Habu yana cewa.
"To Aboki bismillah komai yayi ready, wankan kawai ya rage maka."
Ya faɗa yana mai ƙarasowa bakin kujerar da suke zaune a akai.

"Thank you."
Yarima Asad ya faɗa a taƙaice, yana mai tinanin yadda za'ayi ya iya wanka a wani wurin da bana sa ba, domin kuwa shi dai yana da matuƙar ƙyanƙyami.
Kana kuma ko abubuwan da suka zamto mallakin sa muddin yayi amfani da su sau ɗaya to ya gama baya mai-maici, gashi kuma bashi da tabbacin zai samu komai sabo anan cikin, hakan yasa yaji tamkar kawai yacewa Habu ya fasa yin wankan idan yaje gida yayi.
Sai dai kuma da ya sake kallon jikin sa yaga yadda gaba ɗaya yake a ɓace, ga ɗan ƙarnin da yake ta taso masa yana dukan hancin sa, sai yaga ai gwanda yayi wankan koma a ina ne da tafiya a haka, kuma yana tsammanin ƙila ya samu wurin da tsafta ma, tunda ko a cikin ɗakin ma babu wani abun wanda ya dan ganci ƙazanta da suka gani a cikin sa, asalima ko nashi na gidan bazai nuna masa tsafta ba a yadda suka gansa, sai dai kawai ya fishi da kayan ado.

"Tabbas Yarinyar nan kin cuceni, kai anya ma ba mahaukaciya bace ba kuwa?
Haƙiƙa mahaukaciya ce yarinyar nan, domin kuwa babu wata mai hankalin da zata ai'kata abun da ta aikata kuma ta juya ta ƙara gaba ba tare da ta bawa wanda tayiwa hakan haƙuri ba, asalima sai kallon banza.
Lallaikuwa mahaukaciya ce babba ma a cikin mahaukatan yarinyar nan, Allah ne ya rufamun asiri ma da bata shaƙo mun wuya ba."

Ya faɗi haka a fili cikin muryar sa da har dai ba kana kusa da shi yayi maganar ba baka isa kaji mai yace ba, yana mai tura kansa zuwa cikin bathroom ɗin.

Tsaye yayi a jikin ƙofar bathroom ɗin, yana mai lumshe idanuwan sa, saboda wani irin daddaɗan ƙamshin da ya bugi hancinsa.
Kana daga bisani ya wara su yana mai bin ko ina na cikin sa da kallo.

Komai neat yake babu wani alamun datti a cikin sa.
Kana akwai komai na buƙata anan ɗin ma, domin ko hatta da mirrow akwai sa manne a jikin bango.

Akan wata sabuwar baƙar bathrobe fidigil ya dire ƙwayoyin idanuwan sa.
Kana a gefen ta kuma sabon boxer da singilet ne a jiye suma.
Hakan ne yasa ya ɗan girgiza kai yana mai sauke wani ɗan gajeran numfashi.
Kana ya fara zame kayan jikin sa tun daga nan bakin ƙofar yana mai dosar gaban shower da ya hango.

Tsaye yayi a tsakiyar ruwan bayan ya kunna sa, yana mai lumshe idanuwansa.

Lokaci ɗaya ya fara sauke wasu irin tagwayen ajiyar zuciya, yana mai jin tsigar jikin sa na wani irin mimmiƙewa, sabo da yadda idanuwansa suka sake hasko masa kyakkyawar budurwar da yayi arba da ita tsaye a gaban sa.
Take a wurin kuwa yaji gaba ɗaya yanayin sa na sauyawa, ga zuciyar sa da take ta bada wani irin dip-dip-dip.

Da sauri ya buɗe idanuwansa, saboda sautin ƙarar nociking ɗin da ya daki kunnuwansa, da har yayi sanadin tsinkewar tinanin nasa, kasancewar zuwa yanzu ya ɗauki kusan mintina talatin da shiga, amma gaba ɗaya shi kansa ba zaice ga abun da yayi ba.

A hankali ya juyar da kansa yana mai kai idanuwansa kan ƙofar nan.
Yasan ba kowa bane zai aikata masa hakan sai Al'amin, hakan ne yasa sa janye idanuwansa daga kan ƙofar yana mai ɗan sakin tsaki.
Kana ya janyo sabon sponge and soap ɗin da Habu ya ajiye masa, yana mai haɗa kumfa ya fara saɓe jikin sa da shi cikin sauri, domin kuwa sai yanzu ya tina da basu kaɗai bane sukazo wurin ba hadda babban yaya, kuma at any time zai iya kiran su su futo su tafi, sai dai kuma har kawo yanzu tinanin Gimbiya Haddiyal yaƙi ɓacewa daga cikin ransa.

"Mtseewww! Shin anya ma kuwa mutum ce wannan yarinyar?
Haba, tsabar jaraba kawai kizo ki tsayawa mufum a cikin rai daga kalo ɗaya."

Ya faɗi haka a lokacin da yake ɗaura bathrobe ɗin da take saƙale a jikin sa, bayan ya sanya sabon boxer ɗin da ya gani a ajiye, sannan ya juyo yana mai kamo hanyar waje yana yi yana sakin tsaki.

"Wai kai me yasa ako ina ma sai ka nuna halinka ne banza kawai, ace ɗan watsa ruwan da zakayi ka futo kawai shine har sai ka ɗauki almost one hour baka gama ba."
Al'amin ya faɗa yana mai buga masa harara.

Shi kuwa Habu kwashewa da dariya yayi yana mai faɗin.
"Gashi kuma shi ba kalar ka ba ballan tana ace ko so yake ya dawo ɗan ja."

"Kuttt, wato har da kai kaima ko?"
Al'amin ya faɗa yana bugawa Habu harara.

"A a fa ni bance komai ba."
Cewar Habu yana mai tashi yayi gaban wardrobe ɗin sa.

Shi kuwa Yarima Asad inda suke bai ɗago ya kalla ba, ballantana har ya tanka musu, sai wucewar sa da yayi gaban dressing mirrow yana mai fara kallon mayukan da suke a jiye akan sa.
Kafin daga bisani kuma ya buɗe wani mai mai kama da vasline, yana mai fara shafa sa a jikin sa.

Cikin ƙanƙanin lokaci ya gama shiryawa tsaf, tukun ya juyo ɓarin da su Al'amin suke.

"Yawwa ga kayan nan sai ka matso kasa idan ka gama."
Habu ya faɗa yana mai dire kayan da ya zaro a cikin wardrobe ɗin tasa a gefen gadon sa, tukun ya koma kusa da Al'amin yana mai zama shima.

Yayinda Yarima Asad kuma ya fara ɗaga ƙafafuwansa yana mai nufar wurin da kayan suke, idanuwan sa ƙur akan su.

Lumshe idanuwansa yayi a dai-dai lokacin da ya ƙaraso gaban kayan, sabo da ganin su da yayi sak irin suturar da yake sanyawa, gasu kuma sababbi fidigil suma, alamun bama a taɓa sasu ba.
Kafin daga bisani kuma ya buɗe su yana mai sa hannu ya ware kayan.

"Blue jiens ne tare da shirt mai haske masu matuƙar kyau.
Hakan yasa cikin kwanciyar hankali ya ƙarasa ware kayan yana mai fara sanya su a jikin sa.

Sosai sukayi matuƙar yin kyau a jikin sa, kana sukayi masa cip-cip yadda kasan an gwada sa, kasancewar babu ta inda zaifi Habu daga tsayi har ƙiba.

"Yawwa ku tashi mu tafi ko."

Yarima Asad ya faɗa, yana mai ɗaukar wayar sa tare da walet ɗin sa ya zura a cikin aljihun sa.

"Kamar ya kutashi ku tafi kuma tun yanzu, bayan kunsan ko madara bakusha ba?"
Habu ya faɗa yana mai wurgawa Asad hararar wasa.
Yayin da shi kuma Yarima Asad yayi murmushi daga tsayen da yake, domin kuwa aɗan zaman da sukayi da Habu sosai ya fahimci ba ƙaramun kirki gare sa ba, hakan yasa yaji yayi matuƙar birge sa.
Kana ya sake buɗe baki yana mai faɗin.

"To amma dai ai kasan jiran mu ake a waje, kuma ma bayan haka nifa a ƙoshe nake wallahi."
Ya ƙarasa maganar yana mai ɗan yamutsa fuska.

Shi kuwa Habu sake taɓe fuska yayi yana cewa.
"Amma dai kun riga da kun san har na aika a kawo muku wata ko, sannan ma kuma taya ya za'ace ku shigo har cikin masarautar fulɗe ace kun fita ba tare da kunsha fura da nono ba, haba dai, kuma kun san hakan ba abu bane mai yuwuwa."

Habu ya faɗa yana mai miƙewa tsaye da niyyar futa dan ya anso musu da kanshi.
Hakan da Al'amin ya gani ne gashi kuma shima yasan yanzu Babban yaya zai iya kiran su, kana idan yaji basu gama ba zai iyayin faɗa, yasa sa miƙewa tsaye da sauri shima.
Kana ya buɗe baki yana mai faɗin.

"A'a Aboki, dan Allah kawai ka barta dan ni kaina a ƙoshe nake, in yaso duk randa muka dawo sai ka kawo mana har ta yau ɗin mu haɗa mu shanye duka, kaga kenan munyi biyan bashi ko."
Al'amin ya faɗa yana ƴar dariya.

Hakan da Habu yaji ne yasa sa tsayawa yana mai juyowa ya kalle su, kana ya buɗe baki yana mai faɗin.

"Kaji sa, sai kace da gaske dawowar zasuyi."

"Caɓ, me zai hanamu dawowa, ai karka cire tsamannin sake ganin mu a cikin satin nan ma mun dawo, domin kuwa mu dai munga wuri, sabo da naga alamar brother ɗin naw...."
Hararar da yaga Yarima Asad ya kwaɗa masa ce ta sanya sa dakatawa daga faɗar abun da yake faɗe, yana mai kwashewa da dariya.

Yayin da shi kuma Habu yace.
"To Allah yasa da gaske kake."

Shi kuwa Yarima Asad shigewa yayi gaba yana mai rigasu fucewa daga cikin ɗakin.

Zuwan su ƙofar Fada yayi dai-dai da lokacin da su Babban yaya suka futo daga cikin ta, kasancewar sun riga da sun gama cinikin, dan hatta da shanun ma an jera musu su a cikin mota.
Hakan yasa gaba ɗayan su suka rankaya sukayi wurin motocin su.

"To Abokai ya da tafiya ba tare da munyi ko exchange ɗin contact ba, ko kuwa dai bakwa son abotar ta ɗore ne?"
Cewar Habu a lokacin da su Yarima Asad suke shirin shiga mota, yana mai marairaicewa, domin kuwa haka nan kawai yaji baya son tafiyar tasu ko kaɗan, tamkar dama can sun san juna.
Sosai suka shiga ransa tun kallon farko da yayi musu, hakan yasa yaji bayan son alaƙar su ta tsaya a iyakar yau, barin ma Al'amin da yake uban surutu irin sa.

"Sorry ɗan uwa, mu mun isa muce alaƙa taƙare iya yau, bayan kana ji nace maka munga iri."
Al'amin ya faɗa yana gumtse dariya abakin sa.

Shi kuwa Yarima Asad yi yayi tamkar baiji abun da yake cewa ba, sai hannunsa ma da ya miƙa yana mai karɓar wayar habu ƙirar Iphone 12 pro max.
Kana yace.
"Sorry friend mun manta ne."

Ya ƙarasa maganar fuskar sa ɗauke da murmushi, yana mai fara jera nombobinsa a cikin wayar Habu, abun da bai taɓa yi ba kenan, wato rubutawa wani mutum number sa, sai dai ya baka katin sa idan kaso ka kira shi, amma haka nan kawai yaga Habu ya girmi wannan babin a wurin sa, sabo da yadda yake ganin wata irin ƙimar sa a cikin idanuwan sa, bai sani ba ko dan yadda ya tarbe su ne da hannu bibbiyu ya muntata su shiyasa yake jin hakan.
Yayinda a ƙasan zuciyar sa kuma har yanzu tinanin wannan ƴar fulanin yaƙi wucewa daga cikin ta, kamar yadda idanuwansa suka gaza manta hoton fuskar ta.

"Yawwa to gashi nan nima, sai ka kirani in yaso sai in saver ta ko."
Yarima Asad ya faɗa yana mai miƙawa Habu wayar.

Hakan kuwa akayi, gaba ɗayan su suka sanya masa numbobin, shi kuma ya kira su sukayi saving ɗin tasa number, kana suka shige cikin motar su kamar yadda gaba ɗaya jama'ar tasu suka shige cikin mota.

"To sai naji kun ko, idan kuma baku dawo ba sai nace ni sai nazo to."
Habu ya faɗa yana mai ɗaga musu hannu a lokacin da suka fara tafiya.
Suma ɗago masa hannun sukayi gaba ɗayan su fuskar su ɗauke da murmushi.

Suna zuwa bakin get ɗin futa daga cikin Masarautar Yarima Asad ya lumshe idanuwansa, yana mai jingina da kujera.
Saboda yadda yaji gaba ɗaya jikin sa yayi wani irin sanyi, ga zuciyar sa da take masa ba daɗi, ta yadda har yake jin tamkar yayi mantuwa a cikin Masarautar.
Shi kuwa Al'amin cikin farin ciki ya juyo inda Yarima Asad yake yana mai faɗin.
"Amma gaskiya Fulani akwai kirki da iya karrama baƙo, domin kuwa zan iya cewa tun da nake a rayuwa ta ban taɓa zuwa wurin da akayi matuƙar karramani a kaji tamkar kar in tafi irin yadda aka mana anan.
Kai gaskiya ni dai sun birgeni kamar yadda garin nasu ya birgeni sosai."

Ya fada yana mai sakin murmushi, kana ya ɗora da cewar.
"Yawwa kai wai dan uwarka ma mene yasa kace ba wannan yarinyar bace ta kifo maka madara, bayan naga ko kallon mutunci batayi maka ba ballantana har ta iya buɗe baki ta baka haƙuri ta juya ta tafi?"
Al'amin ya watsowa yarima Asad tambaya, bayan ya gama jero surutan sa na farko bai kulasa ba.

Inda yake bai ɗago ya kalla ba ballantana har yasa ran zai amsa masa, asalima shi ko jin abun da yace duka baiyi ba, sabo da yadda yayi nisa a wurin tinanin wannan kyakkyawar hallitar da yayi arba da ita yau.
Sosai yake jin bugun zuciyar sa na ƙaruwa aduk lokacin da zai tuna ta.
Bashi da wani buri a yanzu wanda ya huce yaji ya manta da ita a cikin zuciyar gaba ɗaya, kana kammanin ta su ɓace daga cikin idanuwansa, amma sai dai kuma abun yaƙi yiwuwa, asalima ji yake tamkar har yanzu tana tsaye a gaban sane, gashi kuma abun takaicin har kawo yanzu zuciyar sa ta gaza jin haushin ta akan hulaƙancin da tayi masa.

Jin da Al'amin yayi Yarima Asad yaƙi kulasa kwata-kwata ne ya sanya sa kama bakin sa yayi shiru, yana mai janyo wayar sa ya fara shafata, sai dai kuma shi kansa cike yake da tinanin abun da ya canza ɗan uwan nasa alokaci guda a cikin zuciyar sa.


*MASARAUTAR YAMMA*

Zaune Jauro'n Yamma yake a gaban Lamidon su yana kora masa bayanin yadda sukayi da Gimbiya Haddiyal kansa durƙushe a ƙasa.
Yayinda shi kuma Lamiɗon Yamna yake zaune akan wata haɗaɗɗiyar kujera fuskar nan tasa babu alamun annuri, sabo da jin irin tarbar da akayiwa ɗan nasa mafi soyuwa a ransa.

Girgiza kai yayi adai dai lokacin da Jauron Yamma ya tsaya da bayanin sa.
Kana ya ɗan juyar da kan sa gefe, yana mai fesar da wata zazzafar iska daga cikin bakin sa, sannan ya buɗe baki idanuwansa akan fuskar ɗan nasa, yana mai faɗin.

"To shi Lamiɗo Sulaiman ɗin yaji labarin yadda kukayi da ita ne?"

"A'a Baffah, kawai na tawo ne bayan nayi masa sallama."
Jauron Yamma ya faɗa har lokacin kansa durƙushe a ƙasa.
Yayinda shi kuma Lamiɗo ya girgiza kansa.
Kana daga bisani ya buɗe bakin sa yana mai faɗin.
"Tom shikenan, gwanda da baka fada masan ba, domin kuwa babu amfanin ya sani ɗin, tunda ba dakatar da waccan zaiyi ba, saboda dama ana neman abokin takara ne, sai dai kuma ina son ka kwantar da hankalin ka, karka kuskura ka bari maganganun ta su sanya ya maka guiwa, har kayi tinanin bazata zamto mallakin ka ba, domin kuwa tun farkon kafuwar a halin mu a cikin masarautar nan har kawo yau babu wanda tarihi ya nuna cewa ya taɓa bugun shaɗi baiyi nasaraba.
Dan haka kuwa baza'a taɓa farawa a kanka ba, domin kuwa bulalan mu ba irin sauran bulalan bane, saboda haka tun yau ma zansa anemo su a fara tsuma su, ta yadda muddin suka hau jikin mutum ko waye shi sai ya koka, sai yasan yayi gamo da maza.
Dan haka tashi kaje ka kwantar da hankalin ka nasara na tattare da kai."

Ya ƙarasa maganar yana mai ɗan bubbuga kafaɗar sa.

"Godiya nake baffah na."
Jauron Yamma ya faɗa yana mai miƙewa ya sanya takalman sa, tukun ya juya yana mai tafiya ransa cike da farin ciki da annashuwa.


*ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.*

Ko da ganin Bir ya sume hakan bai sanya jikin dakarun nan yin sanyi ba, saima ɗaya daga cikin su da ya sake matsawa zuwa wurin da yake yana mai sa hannunsa ɗaya ya dago sa, kana ya tsundumasa a cikin ruwan nan.

Yana faɗawa cikin ruwan kuwa yaja wata irin doguwar a jiyar zuciya, yana mai ɗagowa sama, kana ya fara wani irin huri-huri, gaba ɗaya babu ƙarfi ko kaɗan a jikin sa.
Yayinda shi kuma ruwan nan ya fara shirin tafiya da shi.

Ganin da dakarun nan sukayi yana shirin nutsewa cikin ruwan ne, ya sanya ɗaya daga cikin su buga tsalle yana mai faɗawa ciki, kana ya damƙo gashin Bir suna masu ɗagowa a tare, sannan ya futo daga cikin ruwan yana mai sake sakin Bir daga sama zuwa ƙasa.

Zuwa yanzu tini Bir ya dena ihun da yake ma, sabo da yadda gaba ɗaya ƙarfin sa ya ƙare, domin kuwa babu abun da yake iyawa sai faman lumshe idanuwansa tare da buɗe su, dan ko a yadda yake jin kansa ko hannunsa ba zai iya ɗagawa ba, amma kuma duk da haka kyakkyawar fuskar Gimbiya bata ɓace daga cikin idanuwansa ba, kamar yadda har yanzu kuma baiji ko ɗigon haushinta ba, ballantana kuma tsanar ta a cikin ransa, sabo da azabar da tasa ana gana masa.

Cikin rashin imani ɗaya daga cikin dakarun nan ya fara saro taɓon da yake manne a jikin ruwan nan, sai da har ya tarasa da yawa a wuri ɗaya, kana ya juya wurin da Bir yake yana mai zuwa ya funciko sa da hannu ɗaya.

Danna kansa yayi a cikin taɓon nan yana mai murza sa, tukun daga bisani ya ɗago sa yana mai sake yin cilli da shi a gefe.
Yayin da na kusa da shi ma ya sake tafiya yana mai ƙara cakumo Bir tamkar ya riƙo tsumma, kana ya sake damƙar gashin kansa yana mai ƙara dulmiya kansa a cikin ruwan nan.
Haka sukai tayi masa har kimanin sau biyar, sannan suka futo da shi suna masu zare mahaukatan bulalan su daga cikin jikin su suka fara zane sa tako ina.

Sosai sukayi masa mahaukacin duka yadda kasan sun samu dutse, domin kuwa ko dabba bai kamata ace anyi mata irin wannan abun ba, asalaima bazata taɓa jurar sa ba.

Basu suka bar dukan nasa ba har sai da sukaga baya iya ɗaga ko yatsar hannun sa, duk da dai har lokacin da rai a gangar jikin sa, sai dai kuma da shi da gawar basu da bambanci kwata kwata, sabo da yadda bazata iya ɗagawa ba ko motsi haka shima gaba ɗaya ya kasa yin sa, dan ko hatta da idanunsa ƙin buɗuwa sukayi gaba ɗaya, sai wani irin numfashi da yake futarwa a fuzge.
Yayin da jijiyoyin kansa kuma suka futo sukai raɗa-ɗara akan goshin sa.

Jansa suka farayi akan hanyar nan, suna

Please Login or Register in order to submit comment