Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka.
Shin a ina ka tab'a jin anyi aure tsakanin d'iyar Sarki da Bawa.
Hak'ik'a auren ka da Gimbiya Bazai tab'a yuwuwa ba Jarumi, duk da irin soyayyar da kuke yiwa junanku kuwa, asalima abu d'aya ne nake ganin zai sa har abarka da rai idan wannan abun ya bayyana ba tare da ankashe ka ba, wato matsayin da kake da shi a wurin su.
Dan haka ina ganin ka koma wurin ta ku sake tattaunawa akan yadda zaukuyi ku manta da junan ku dukan ku, domin kuwa ina da tabbacin ko zata mutu ita kanta ba zasu tab'a aura mata Bawa ba, duk da irin son da suke mata kuwa.
Kaga kuwa tayaya zanyi farinciki, bayan duk wa'yan nan abubuwan dana sani Jarumi?"

Ta k'arasa maganar a sanyaye tana mai zuba masa idanu, tare da jin da ace tana da yadda zatayi ya samu damar mallakar Gimbiya, da babu abun da zai hanata yi, domin kuwa ita kanta ta fahinci ba k'aramun so Bir yake yiwa Gimbiya ba yanzu, ta yadda har ta gane koda zai iya cireta a ransa to bata cikin sauk'i ba, wanda ita kuma ko kad'an bazata so faruwar hakan ba.

Shi kuwa Bir da k'arfi ya rumtse idanuwansa, yana mai aminta da bayanan Iya d'ari bisa d'ari.
Hak'i'k'a shi kansa ya sani, babu ta yadda za'ayi wannan batun yaje kunnen su Sarki Barbaru ba tare da ya fuskanci wata matsala ba.
Hakanne yasa sa yin shiru jikin sa na yin wani irin mugun sanyi.
Yayinda fargaba da tsoron halin da zai shiga idan akace sai ya bar Gimbiya suka lullub'e zuciya da ruhinsa.

Ganin hakan da Iya tayi ne ya sanya ta d'ago tafin hannunta, tana mai kife sa akan lalausar sumar kansa.
Tukun ta shafata tana mai bud'e baki tace.

"Ba naso ka sanya damuwa acikin ranka Bir, ni kaina zanso yuwuwar al'amarin domin farincikin ka, sai dai kuma tayaya? Ta wace hanyar hakan zai faru? Shine bamu sani ba.
Dan haka yanzu ka tashi ka tafi d'akinka ka d'auki abincinka kaci, idan gobe kun had'u sai ku tattauna akan al'amarin da ita kaji ta bakinta."

Ta k'arasa maganar tana mai janye hannunta daga kansa.
Hakan da Bir yaji ne ya sanya sa jinjina kansa ba tare da yace komai ba, yana mai mik'ewa tsaye.
Har ya fara tafiya sai kuma ya juyo b'arin da Iya take yana mai fad'in.

"Yawwa Iyata akwai nama a leda gashi nan na ajiye sa a k'ofar d'aki."

"Tom shikenan Jarumina bara na futo na gyara sa."
Cewar Iya tana mai mik'ewa tsaye.
Yayinda shima Bir ya cigaba da tafiyarsa yana mai fucewa daga cikin d'akin.

A can b'angaren Gimbiya Tasmir kuwa, cikin tsantsar farinciki da annashuwa mara misaltuwa ta k'arasa d'akin ta.
Tana shiga ciki ta fad'a kan tamfatsetsen gadonta tana mai lumshe idanuwanta.
Yayinda fuskarta kuma take d'auke da murmushi, sabo da tuna yadda had'uwarsu ta yau ta kasance gaba d'aya.
Ta jima kwance akan gadon tana juyi ranta farik'al.
Kafin daga k'arshe kuma ta mik'e tsaye tana mai cire kayanta ta doshi hanyar Bayi.
Ko da tana wankan ma babu abun da take gani face fuskarsa a cikin idanuwanta alokacin daya sumbuci lips d'in ta.
Hakanne ya sanya har tayi wankan ta gama bata bar sakin murmushi ba.

Cikin sauri ta shirya kanta cikin wata doguwar rigar bacci mai tsananin taushi da kyau.
Tukun ta fuce daga cikin d'akin nata ta tafi wurin mahaifiyar ta domin suci abinci a tare, abun da rabonta tayi tun lokacin da suka fara had'uwa da Bir.
Hak'ik'a a yau ta tabbatar da babu abun da yakai soyayya sanya farinciki, muddin ma'abocin yin ta ana yin sa.
Tamkar yadda kuma ta shaida babu abun da yakai ta sanya k'uncin zuciya da k'unar rai, idan mutum bai samu yadda yake so ba, kamar yadda ya faru da ita a baya.
Hak'ik'a dolene ma tayiwa Hadima Fulaika jin-jinar kyauta, irin wacce bazata tab'a mantawa da ita ba har abada a rayuwa, wato dai zata sanya mahaifin ta ya 'yanta ta, wannan shine tukuicin da zata yi mata na bak'in cikin da tayi sanaddiyar yayewar sa daga cikin zuciyar ta.

Sosai Iyayenta sukayi mamakin yadda yau take ta sakin murmushi da far'a, abun da kwata-kwata basu saba gani a tattare da ita ba tun tana k'arama.
Hakanne ya sanya su sukai ta tambayarta abun da ke faruwa, da har ya sanya ta farinciki amma tak'i sanar da su.
A k'arshe dole dai suka hak'ura kowa ya huce d'akin sa ya kwanta.

*WASHEGARI*
Rabon da Gimbiya Tasmir tayi irin baccin da tayi a daren jiya har ta manta.
Baccine tayi mai tsantsar dad'i, wanda yake cike da mafarkan masoyinta tamkar yadda ya buk'aci tayi hakan.
Hakan ko ya sanya yau ta tashi cikin tsantsar nishad'i, annashuwa tare da farinciiki.
Kana kuma da mararin sake ganinta gata gashi tamkar yadda suka kasance jiya.

Yayinda acan b'angaren Bir kuma ya kwana da tinanin magan-ganun Iya a ransa.
Wanda hakan ya sanya yau ko da ya tashi gaba d'aya yaji sa ba shi da wani kuzari atare da shi.
Hakanne yasa koda iya takawo masa farfesun naman daya kawo musu jiya gaba d'aya ya kasa cinsa sosai kamar yadda ya saba.
Sannan kuma bayan ya gama ma ya kasa tafiya ko ina, sai d'akin sa daya koma ya zauna yana mai tinanin yadda abun zai kaya, tare da jiran zuwan yamma domin yaji abun da ita zata fad'a, kasancewar da yamman sukayi da ita zasu had'u a wurin da suka had'u jiyan.

Misalin k'arfe Biyar da rabi na yamma dai-dai Gimbiya Tasmir ta shirya cikin wata jar doguwar riga mai tsananin kyau da tsada.
Sosai tayi matuk'ar kyau cikin shigartata tamkar a sace.
Ga wani irin sassanyan k'amshi dake tashi daga cikin jikin ta.
Yayinda fuskarta kuma take d'auke da wata irin had'ad'd'iyar kwalliya mara hayani da tayi ta da kanta yau.
Tukun tabi ta hanyar data futa jiya tana mai tafiya wurin da zasu had'un, gudun kar wani ya ganta ya tambaye ta wurin da zataje, ko kuma idan taje futa wa'yan nan dakarun nata su tawo da niyyar yi mata rakiya, sabo da sanin da tayi na muddin bata futa da su ako da yaushe dole ne Babanta ya tambayeta dalilin da ya sanya hakan, wanda ita kuma bata san abun da zatace masa ba idan hakan ta faru.

Tsaye ta hangesa jingine a jikin wata k'atuwar bishiya ya lumshe idanuwansa.

Kallo d'aya tayiwa fuskarsa ta gane cewar yana d'auke da damuwa a zuciyar, sabo da ko abaya da fad'a ke had'asu ba bata tab'a ganin yanayinsa a haka ba, ballantana kuma yanzu da komai ya dai-dai ta.
Hakanne ya sanya ta jin wata irin fargaba da tsoro sun lullub'eta, domin kuwa duk a tinaninta ko basa da lafiya ne yau d'in.

Cikin sauri kuwa ta d'aga k'afarta tana mai dosar wurin bishiyar.
Yayinda idanuwanta kuma har lokacin suke kafe akan fuskarsa, a haka har ta k'arasa gaban sa ta tsaya.

Tunda ta kusa k'arasowa kusa da shi ya fahimci ita d'in ke tawowa, ta sanadin bugun zuciyarsa da yaji ya k'aru.
Amma sai dai kuma bai iya bud'e idanuwansa ba, har sai da yaji alamun tsayuwarta a kusa da shi, tare da saukar idanuwanta akan fuskar sa.
Tukun a hankali ya bud'e idanuwan nasa a cikin nata.

Wani irin bala'in kyau Bir yaga tayi masa fiye da koda yaushe.
A hankali ya mayar da idanuwansa yana mai lumshe su.

Ganin hakan da Gimbiya Tasmir tayi ne, ya sanya ta jin jikin ta ya sake yin bala'in sanyi, domin kuwa sosai ta fahimci damuwar da take kwance akan fuskarsa, harma da cikin idanuwansa.
Hakanne ya sanya ta bud'e baki cikin wata irin murya mai matuk'ar sanyi da rauni, tana mai fad'in.

"Hak'ik'a ba haka na saba ganin fuskar bangon zuciyata ba ko abaya balle kuma a yanzu.
Shin meke damun kane masoyina?
Gani a gabanka ka fad'amun ko macece damuwarka, ni kuma na maka alk'awarin zamtowa silar tafiyar ta muddin abun baifi k'arfi na ba."

Jin hakan da Bir yayi ne, ya sanya sa bud'e dara-daran idanuwansa da gaba d'aya launin su ya fara sauyawa akan fuskarta, tukun ya d'anja numfashi tare da fesar da shi.
Kana ya bud'e hannuwansa biyu yana mai mata alamar data tawo gare sa, ba tare daya iya furta mata komai ba, domin kuwa sosai ya sake jin jikin sa na k'ara mutuwa ta silar sauraran muryarta da yayi.

Tsaye Gimbiya Tasmir tayi a wurin da take, tana mai kallon sa ba tare data iya k'arasawa ba, sabo da yadda taji wata irin muguwar kasala na lullub'eta, ga kuma yadda tsigar jikinta ke tashi yar-yar, ta sanadin kalon san da take a haka ba riga a jikin sa.

Ganin hakan da Bir yayi ne ya sanya sa lumshe idanuwansa yana mai sake bud'e su akan fuskarta, tukun yayi mata alamar ta tawo da idanuwan nasa, still ba tare daya bud'e baki yayi magana ba.
Hakanne ya sanya Gimbiya Tasmir ta fara d'aga k'afafuwanta a hankali, tana mai nufar wurin da yaken kanta durk'uske a k'asa.

A hankali, kana kuma cikin sanyi ta shige cikin jikin nasa.
Hakanne ya sanya Bir mayar da hannuwansa wuri d'aya ya had'e su, yana mai rungumeta tsam-tsam tamkar zai mayar da ita cikin cikin sa.
Yayinda ita kuma ta kwantar da kanta akan faffad'an k'irjin sa mai cike da yalwatacciyar lallausar bak'ar gargasa akan sa.

Take kuwa suka sauke wasu irin tagwayen a jiyar zuciya a jere.
Tukun daga bisani kuma Bir ya fara rank'wafo da kansa a hankali, har ya kawo fuskarsa saitin tata fuska.
Kana ya d'an had'e tsinin hancinsa da nata a wuri d'aya yana mai d'an jujjuya fuskarsa.
Wanda hakan kuma ya sanya su shiga cikin wani irin yanayi gaba d'ayansu su biyun.
Tukun a k'arshe ya bud'e bakinsa yana mai busa mata iskar sa mai matuk'ar d'umi akan fuskarta.

Hakan da Gimbiya Tasmir taji ne ya sanya ta bud'e idanuwanta a hankali, tana mai d'an sakin numfarfashi.
Take kuwa k'wayar idanuwansa da nata suka sark'e a wuri d'aya.
Cigaba da goga hancinsa Bir yayi akan nata suna masu kallon cikin idanuwan juna.
Tukun a k'arshe ya bud'e baki cikin wata irin murya da take acan k'asan mak'oshinsa, yana mai fad'in.

"Kece damuwata 'yammata na, domin ko jiya ko cikakken bacci Bir d'in ki baiyi ba ta silar ki."

Ya k'arasa furucin da busa mata iskar bakinsa.
Yayinda ita kuma tayi wata irin zabura, tana mai zaro idanuwanta cikin tsantsar firgici, rud'u da tashin hankalin da furucin sa ya saukar mata, tana mai f...............✍



IDAN NAGA RUWAN COMMENT ZAKU JINI GOBE IN SHA ALLAH, IDAN KUMA KUKAI DIP NIMA ZAKU JINI DIP.







UMAR FARUQ*


BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*15*



Fara k'ok'arin b'anb'are jikin ta daga cikin nasa, gaba d'ayanta ta rud'e ta firgice lokaci guda.
Ganin hakan da Bir yayi ne, ya sanya sa k'ara matseta a cikin jikinsa sosai, ta yadda gaba d'aya takasa cigaba da motse-motsen da takeyi, sai dai kuma har lokacin hankalinta a tsantsar tashe yake.
Shi kuwa Bir sake durk'uso da k'ansa yayi zuwa saitin fuskarta.
Kana ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Ya akai ne? Ki nutsu mana kinji ko."

Yayi maganar a wani irin sakalce, kana acan k'asan mak'oshi, yana mai d'an hura mata iskar bakinsa a hankali.
Hakan ya sata lumshe idanuwanta, tana mai sauke 'yar gajerar ajiyar zuciya.
Kana ta sake bud'esu a cikin nasa, har yanzu dai kwata-kwata babu nutsuwa a tattare da ita.
Kafin daga bisani kuma ta bud'e baki cikin rawar murya tamkar zata fashe da kuka, tana mai cewa.

"Taya zan iya nutsuwa, bayan na zamto silar rashin nutsuwar Masoyina."
Tayi maganar a hankali, muryarta na rawa, yayinda idanuwanta kuma suka tara ruwan k'walla.
Tukun ta d'ora da fad'in.
"Shin wane laifine na aikata maka da harya hanaka runtsawa?
Hak'ik'a ina son jinsa yanzu, domin nasan irin hukuncin daya kamata nayiwa kaina."

Tayi maganar har lokacin idanunta a cikin nasa.

Hakan da Bir yaji ne, ya sanya sa bud'e hannuwansa daya nad'eta a cikin k'irjin sa dasu a hankali.
Kana ya zame jikinsa daga nata yana mai fesar da iska, tare da lumshe idanuwa.
Kana daga bisani ya bud'esu yana mai juya mata baya.
Yayinda ita kuma har lokacin idanuwanta suka kasance akan fuskarsa, tana mai son jin abun da tayi masan.

Cikin wata irin murya mai sanyi had'e da shagab'a taji sautinsa na futowa, yana mai fad'in.

"Bakiyi mun lafin komai ba Gimbiya, na kasa bacci ne ta dalilin tinanin goben mu, na kasa bacci ne sabo da tsoron halin da zamu tsinci akan mu aduk ranar da alak'armu ta bayyana a idon al'ummar cikin Bak'ar Masarauta"

Ya k'arasa maganar cikin wata irin murya mai matuk'ar sanyi, tukun ya juyo b'arin da take, yana mai sake zuba idanuwansa akan fuskarta .
Yayinda ita kuma tuni ruwan hawayen da suka taru a cikin idanuwan nata suka fara dira akan kuncinta.
Ba tare da ya tsaya jiran cewar taba ya d'ora da fad'in.

"Munyi kuskure babba, munyi kuskuren barin zucuyoyinmu suka kamu da son junan mu, bayan kuma daga ni harke mun riga da mun san bamu dace da juna ba.
Zaren ba kalar yadin bane, gaba d'aya idanuwana sun rufe, ta yadda har na k'asa yin tinanin makomata a gaba, sai jiya da Iya ta tunatar dani.
Tabbas dole ne mu hak'ura da junan mu Gimbiya, sabo da sanin kanki ne kema babu ta yadda za'ayi d'iyar Sarki da Bawa su zauna a k'ark'ashin inuwa d'aya."

Da sauri Gimbiya Tasmir ta fara ja da baya, tana mai girgiza masa kai, gaba d'ayanta ta rud'e ta firgice, sabo da jin furucin da yayi, yadda kasan wa'yan da suka shekara d'ari a tare.
Sosai hawaye ke tsiyaya daga cikin idanuwanta yadda kasan an bud'e famfo.
Ko kusa ko kad'an bata tab'a tinanin faruwar wannan al'amarin ba.
Kafin daga bisani kuma ta zube a wurin da take tana mai cake gwiwoyinta a k'asa, ta fashe da wani irin gigitaccen kuka mai sosa zuciya.

Sosai hankalin Bir shima ya tashi da ganin yadda take kukan.
Hakanne ya sanyasa fara d'aga k'afafuwansa cikin matsanancin firgici, yana mai nufar inda take, yayinda bakin sa kuma ke rawa yana son bud'esa yayi magana, amma gaba d'aya ya kasa.

Lura da hakan da Gimbiya tayi ne, ya sanyata d'aga masa tafin hannunta da sauri.
Kana ta bud'e baki cikin matsanancin kukan da take tana mai fad'in.

"Me yasa kasan tun farko ba sona kake ba ka barni na kamu da sonka? Me yasa sai da kabari na aminta da kai, zuciya ta zab'eka amatsayin abokin rayuwa zaka juya mun baya? Akan me zakana fad'in dole ne mu rabu da juna?
Shin kasan ko irin adadin son da zuciyata take maka Jarumi? Shin kasan kuwa da cewar kaine bugun numfashina a yanzu Jarumi?
Shin me yasa zakiyi mun haka zuciya? Me yasa zaki kamu da son wanda bai damu dake ba?
Hak'ik'a idan ka barni a yanzu dana fara sabo da kai zuciyata zata buga Jarumi!"

Ta k'arasa furucin cikin matsanancin kuka, muryarta na sark'ewa, yayinda tafin hannunta d'aya kuma yake dafe da k'irjinta.

Dasauri Bir ya sake matsawa gabanta hankalinsa abala'in tashe, yana mai cake gwiwoyinsa a k'asa.
Yayinda idanuwansa shima suka tara ruwa tini.
Gaba d'aya hankalinsa ya tashi, sabo da yadda yaga duk Gimbiya ta rikice, gashi kuma tana wasu irin furuci marasa dad'in ji.
Hak'ik'a ko shi baiyi tinanin girman san da take masa ya kai harta iya yin kuka akan ya fad'i wannan kalamin sai yanzu.
Hakanne ya sanya sa rumtse idanuwansa da k'arfi.
Tukun daga bisani ya bud'e su akan fuskarta, yana mai jefasu cikin nata da suke zubar da ruwan hawaye, hawayen da yake jinsu suna ta farfasa zuciyarsa.
Sannan ya bud'e baki cikin wata irin raunatacciyar murya, yana mai fad'in.

"Ni bance bana sanki ba, asalima sanki shine ya sanya har nayi furucin da nayi, amma bawai nayi sa bane domin ya sanyaki zubda hawaye, nayi sa ne domin mu had'u musamarwa kanmu mafuta.
Sabo da sanin kanki ne ba zasu tab'a barinmu ba a tare, ni bani da mtsalar komai Gimbiya, gaba d'aya matsalar daga gareki take, kuma idan da akwai wanda ya kamata yayi danasanin afkawa cikin soyayyar nine bake ba, domin kuwa nine rayuwata zata shiga cikin matsala ta sanadin haka, amma sabo da irin girman son da nake miki, shi ya sanya har banyi hakan ba.
Shin tayaya kike ganin wannan abun zai yuwu?"

Ya k'arasa furucin yana mai kafeta da idanuwansa.

Rumtse idanuwa itama tayi da matuk'ar k'arfi, kalamanta na ratsa zuciya da b'argon ta.
Hak'ik'a cikin duka abubuwan daya lissafo babu guda d'aya da yake ba haka ba.
Ita kanta sai yanzu ta hango abun da yake hange, tabbas ta sani babu ta yadda za'ayi iyayenta su aura mata Bawa, ko da kuwa ace duka 'ya'ya mata garesu, ballantana kuma ita kad'aice ta kasance d'iya mace a wurin su.
Duk wasu burikansu akanta suka k'are.
Tabbas aurensa ba k'aramun k'ask'anci bane a wurin su.
Sai dai kuma ya zatayi da son da take masa.
Hak'ik'a bata jin akawai wani abu da zai iyayi mata katanga a tsakanin ta dashi.
Tabbas bazata iya rabuwa da shiba, sabo da a yanzu hakama da suke zaune a wurin, wani irin mugun sansa take jin yana k'ara shigarta, ta yadda har take jinsa dai-dai da adadin futar numfashinta.
Hakanne ya sanyata rumtse idanuwanta da matuk'ar k'arfi.
Sabo da fahimtar abun da yake son ta fahimta d'in da yaji tayi yanzu.
Shi kuwa Bir sake zuba mata tsumammun idanuwansa yayi, yana mai cigaba da kallonta, yayinda hawayenta kuma da suke zuba har yanzu suke tafasa zuciyarsa.

Ta jima rumtse da idanuwan nata tana mai tinanin abun da ya kamata tayi, amma gaba d'aya babu wani abu da yazo mata cikin ranta.
Hakanne yasa ta sake bud'e idanuwan nata tana mai girgiza masa kai, tare da fad'in.

"Bazan iya rabuwa da kai ba Jarumi.
Hak'ik'a bazan iya rabuwa da kai ba, sabo da soyayyarka tini tayi mun ramin da ban san iyakar inda zurfinsa ya tsaya ba a cikin zuciyata."

Ta k'arasa maganar wasu sababbin hawayen na sake b'alle mata.
Hakan da Bir ya ganine ya sanya sa rumtse nasa jajayen idanun da matuk'ar k'arfi.
Gaba d'ayan sa shima ya canza, fuskar sa tayi jajajir tamkar wanda yay kukan.
Yayinda jijiyoyin kansa kuma suka futo sukai rad'a-rad'a akan goshinsa.
Tukun daga bisani kuma ya bud'e idanun nasa a hankali akan fuskarta.
Kana ya d'an taune leb'ensa na k'asa, yana mai d'ago zara-zaran yatsun hannunsa ya d'ora su akan fuskarta.
Tukun ya fare d'auke mata hawayen da suke kwance akan fuskarta da yatsunsa, yana mai girgiza mata kai alamun tayi shirun haka.
Amma gaba d'aya ta kasa, sai wasu irin hawayen da suka sake b'allewa da tsananin gudu ma, tamkar wacce ake tunzurawa.

Ganin hakan da Bir yayine, ya sanya sa matsawa jikinta, tukun a hankali yakai fuskarsa kan tata fuskar, yana mai had'esu wuri d'aya.

Kallon k'wayar idanuwansu suka cigaba dayi a haka, tare da busawa junansu numfashi.
Kafin daga bisani kuma Bir ya zaro harshensa a hankali, yana mai d'orasa akan fuskarta, yana mai fara zagaye da shi aduk wurin da ruwan hawayen ya zuba yana d'auke su.
Ganin da yayi har lokacin tak'i tabar kukan da yake jin zafinsa a cikin zuciyarsa ne, ya sanya sa d'ago tafin hannunsa yana mai tallabo k'eyarta dashi, tukun a hankali ya mayar da tongue d'in sa cikin bakinsa, yana mai dawo da lips d'in sa dai-dai kan nata, tare da sanya tsinin hancinsa ya danne nata hancin da shi.

Aiko take taji numfashinta na shirin tsayawa, hakanne ya sanya ta bud'e baki da sauri domin ta futar da shi tanan d'in.
Wanda hakan kuma yabawa Bir damar hulla tongue d'insa cikin bakin nata, yana mai fara yawo da harshen nasa a ciki.

Take kuwa Gimbiya Tasmir ta sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya, tana mai lumshe idanuwanta, tare da yin shiru da kukan da takeyi.
Sabo da yadda taji gaba d'aya tsigar jikinta tayi wani irin mik'ewa yarrr, ga kuma wata irin mutuwa da jikin nata yayi lokaci guda.

Shi kuwa Bir ahankali ya sanya uper and lower lips d'in sa yana mai damk'ar nata lower lips d'in da su, tukun ya farayi musu wata irin tsotsa tamkar ya samu sweet.

Sosai kuwa Gimbiya Tasmir ta k'arayin lak'wam a jikinsa, tana mai futar da numfarfashi.
Lokaci d'aya gaba d'ayanta tayi wani irin laushi.
Yayinda take jin tamkar karya dena abun da yake yin, duk da dai ba tayasa tayi ba, shi kad'ai ta bari yana bidirinsa, ga kuma wata irin matsananciyar soyayyarsa da taji na k'ara dabai-baiye ilahirin jiki da zuciyarta.

Ganin da Bir yayi tayi lak'wam ta dena kukan da takeyi gad'aya, ya sanyasa zame bakinsa daga cikin nata a hankali.
Domin kuwa dama yayi mata hakanne sabo da ta dena kukan da takeyin, kuma yayi nasara tunda gashi nan tayi d'ip.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir tanajin ya zame bakinsa daga cikin nata ta saki wata irin nannauayr ajiyar zuciya, tana mai sake lumshe idanuwanta.
Tukun daga bisani ta bud'e idanuwan nata da suka canza launi, tare da d'an k'ank'ancewa akan fuskarsa.

Shi kuwa Bir numfashi kaiwa yake fesarwa yana kallon fuskarta.
Tukun a k'arshe da yaga ta bud'e idanuwanta shima ya d'aga lab'b'ansa cikin wata irin sassanyar murya mai matuk'ar taushi.
Yana mai fad'in.
"To yanzu ya zamuyi? Wata mafuta zaki samar mana?"
Ya fad'a idanuwansa a cikin nata.

Shiru tayi tana mai cigaba da kallon idanuwansa ba tare da tace komai ba.
Kana daga bisani kuma ta fesar da numfashi, tana mai lumshe idanuwanta, sannan ta sake bud'e su tana mai cewa.
"Hak'ik'a bazan iya rabuwa da kai ba Jarumi.
Zanyi duk abun da zanyi domin naga mun rayu tare.
Dan haka ina son kabani daga yau zuwa gobe da safe, zan sanar maka da irin mafutar da zan samar mana acikin daren yau.
Fatana kawai ka aminta da koma mene ne, muddin kasan zai bamu damar rayuwa a wuri d'aya."

Ta k'arasa maganar tana mai mik'ewa tsaye ahankali.

Shiko Bir mik'ewa tsaye yayi yana mai kallon yadda gari yayi duhu sosai.
Tukun ya bud'e baki yana mai fad'in.
"Ina maraba da zuwan gobe, ta yadda har nake jin tamkar na janyota da hannuna, fatana Ubangiji yasa mafutar mai b'ullewace."

Jinjina masa kai Gimbiya Tayi ba tare da tace komai ba.
Tukun daga bisani ya rik'o tsintsiyar hannunta yana mai fad'in.
"Muje in rakaki ko, naga dare yayi."

Jim ta d'anyi ba tare da tace komai ba, tukun daga bisani kuma ta sauke kanta k'asa tana me fesar da iska.
Sannan ta d'aga k'afafuwanta suka fara takawa a tare ba dan ranta yaso rabuwa da shi a yanzu ba, asalima ji take tamkar su dawwama a tsaye a wannan hurin daga shi sai ita.

Shiru suke tafiyar babu maicewa wani k'ala, sai k'arar sark'ok'in gwal d'in k'afar Gimbiyane kawai suke d'an tashi aduk d'aga k'afar da zatayi ta dire.
Yayinda a cikin zuciyoyinsu kuma suke cike da tinanin hanyar da zasubi su rayu a tare.
A haka har suka k'araso dai-dai wurin da suka rabu jiya.
Tukun Bir yaja ya tsaya cak a wurin, yana mai kallon fuskarta.
A hankali itama ta d'ago kanta tana mai sanya k'wayoyin idanwanta da suka k'ara tara ruwa yanzu a cikin nasa.

Ganin hakan da Bir yayi ne, ya sanya sa d'an karkatar da kai gefe, kana ya bud'e baki cikin wata irin sakalyar murya, yana mai fad'in.

"To mene kuma akayi na wani kukan yanzu?"

Tamkar kuwa jira take yayi maganar, saiga hawayen nan sharrr sun b'alle suna dira da tsananin gudu.
"Kashh!"
Bir ya fad'a yana mai yamutsa fuskarsa tamkar zai fashe da kukan shima.
Kana daga bisani ya rank'wafo da kansa zuwa kan tata fuskar.
Tukun ya zaro harshensa yana mai fare wiping d'in hawayen nata da shi.
Kana a k'arshe bayan ya gama d'auke hawayen nata, ya watsa k'wayoyin idanuwansa a cikin nata.
Sannan ya bud'e baki, cikin wani irin sautin da ya sanya ta jin tsigar jikinta na bada yarrrr.
Yana mai fad'in.
"Bana son ganin tsadaddun hawayen Gimbiyata suna zuba a k'asa, domin kuwa ina jinsu tamkar saukar ruwan dalma a zuciyata, dan haka idan har bakyason ki jigatar da masoyinki, ya kamata kiyi k'ok'arin tsayar dasu daga yanzu."

Ajiyar zuciyata saki tana mai lumshe idanuwanta da sauri.
Yayinda shi kuma ya d'ora da fad'in.
"Ni zan tafi yanzu.
Banda kuka, banda tinanin da zai wahar mun da zuciya.
Ki kwanta kiyi bacci cikin aminci da salama.
Ina sonki fiye da yadda nake son kaina da rayuwata."

Ya k'arasa maganar da sakar mata kyakkyawar sumba akan goshinta.
Tukun ya janye kansa daga kan tata fuskar, yana mai mik'ewa, tare da yi mata bye-bye ya juya ya tafi.

Tamkar ansa igiyoyi an d'aure jijiyoyin jikinta haka Gimbiya Tasmir taji.
Domin kuwa kwak'k'waran motsi kasayi tayi daga wurin, sai idanuwanta da tabi bayansa da su, tana mai jin sonsa na k'ara huda zuciyarta.
Hak'ik'a muddin ta samu Bir a

Please Login or Register in order to submit comment