Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da suka ganine ya sanya hankalinsu tashi lokaci guda suma.

Da sauri ta mik'e tsaye zumbur, tana mai cigaba da girgiza kai, tukun daga bisani kuma ta bud'e baki cikin rawar murya, tana mai fad'in.........✍


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*29*



"Ban amintaba, kuma bazan tab'a amintaba da wannan tatsuniyar banzar ba."
Ta k'arasa maganar tana mai juyawa a matuk'ar firgice tayi up stairs.
Da sauri Sheikh Ahmad ya fara shirin mik'ewa ya bita a matuk'ar firgice shima, amma sai Abba ya rik'o masa hannu yana mai masa alama daya zauna da kai.

Hakanne ya sanyasa komawa ya zauna, gaba ki d'ayansu su ukkun hankulansu a tashe.
Kana Abba ya gyara zama yana mai kallon Sheikh Ahmad, tuku ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Dole Umminku zata fad'i haka, domin kuwa ba ita kad'ai bama, koni da nake namiji bana san ko jin sunan garin can, saboda irin bala'in da muka fuskanta a cikinsa, amma sai dai kuma ya muka iya tunda har aikin Allah ne, kuma ku da zaku kun aminta, dan haka nima na yarjemuku kuje, in sha Allah zaku dawo tamkar yadda kuka tafi ku same mu, itama kuma yanzu zan shiga cikin in gwada lallab'arta naji ko Allah zaisa ta yaddan."

Jinjina masa kai Shekh Ahmad yayi ba tare daya iya cewa komai ba, shi kuwa Bir shiru yayi kansa durk'ushe a k'asa, yana mai fatan Allah yasa Ummin tasa ta yaddan, saboda Allah ma ya sani yana matuk'ar buk'atar ganin Iyarsa, domin kuwa ba k'aramun kewarta yayi ba.

Mik'ewa tsaye Abba yayi yana mai ce musu.
"Ku tashi ku tafi ku kwanta, in sha Allah zuwa nan da safiya zata amince."

"Tom sai da safe Abba."
Cewar Sheikh Ahmad yana mai tashi ya fuce daga cikin falon.
Hakan yasa shi kuma Bir yaje ya rufo k'ofar tamkar yadda yaga Abba nayi kullum, tukun shima ya huce d'akinsu, yayinda Abba kuma ya haye sama yana mai tafiya cikin d'akin Ummi kai tsaye.

Tsaye ya hangota tana ta kai kawo tsakanin gaban gado da wardrobe.
Yayinda idanuwanta kuma suke tsiyayar da k'walla, gaba d'ayanta a tsantsar firgice.

Sallama ya farayi, tukun yayo wurin da take kai tsaye.

Ita kuwa Ummi ko da taji sallamarsa kasa amsa masa tayi gaba d'aya, sai idanuwanta kawai data zuba masa harya k'araso wurin da take.
A hankali ya mik'a hannunsa yana mai kamo tafukan hannayenta cikin nasa, kana ya fara tafiya tana biye dashi har suka koma jikin gado.
Tukun ya saki hannuwan nata yana mai dafa kafad'arta ya zaunar da ita akan bed d'in, sannan ya samu wuri a gefenta shima ya zauna, kana ya kamo tafin hannunta cikin sanyi, da kuma tausasa kalami yana mai fad'in.

"Khadija!"

'Dago kai tayi ta kallesa ba tare data iya amsawa ba.
Hakan daya ganin kuma ya sanya sa lumshe idanuwansa, kana ya bud'esu yana mai mik'a hannu ya kamo tafukan hannayenta cikin nasa.
Sannan ya fara d'an murzasu a hankali, wanda hakan kuma yasa ta fara sauke ajiyar zuciya.
Tukun ya sake bud'e baki asanyaye yana mai fad'in.

"Hak'ik'a dolene ki firgita da jin wannan batun, amma sai dai kuma abun da nakeso ki fahimta shine.
Mutane nawa ne zasu shiga irin matsalar da kika shiga ta sanadin hanasu zuwan da zakiyi? Mutane nawane za'a rabasu da nasu 'ya'yan, tamkar yadda akai mana muma? Idan kuma har Allah yasa ta silar zuwan nasu al'ummar suka gyaru, wane irin lada kike tinanin zaki samu ke kanki? Sannan kuma kar ki manta wannan abun da zasuyi addinin Allah zasuyiwa hidima fa, kuma abune wanda ya zamana dole akansu a matsayinsu na Malamai ya zamto sun tsawatar sun kuma nuna dai-dai aduk wurin da suka san ana ba dai-dai ba. Kana kuma tafiyarsu fa ba ita take nufin bazasu dawo ba, asalima basu kad'ai zasu tafiba harda Sarki da kuma sauran jama'arsa, to yanzu ke a ganinki idan har kikace bazasuje ba kin bawa musulunci gudummawa kenan? Ko kuwa kin manta tarihin magabatan mune, yadda suka dinga tafiya suna barin 'yayansu da matansu domin suyiwa musulunci hidima? Dan haka ni na amince suje, zan dage dayi musu addu'a daga nan ma, kema kuma ina mai son ki amince musu domin Allah, Ubangiji yaga zuciyarmu yasan kuma me zasuje suyi, in sha Allah zasu dawo garemu lafiya tamkar yadda suka tafi lafiya."

Fashewa da kuka tayi jikinta na d'aukar rawa, kafin daga bisani kuma ta fad'a jikinsa tana mai fad'in.

"Nima na amice, Allah ya karemana su ya dawo mana da su lafiya."

"Amin Amin." Abba ya fad'a yana mai d'an shafa bayanta.

Washegari kuwa misalin k'arfe takwas da rabi Sheikh Ahmad ya shigo cikin gidan da shirin sa na tafiya Masarautar Fuld'e da zasuje yau.

Zaune ya tadda gaba ki d'aya jama'ar gidan a dining area suna karyawa.
Ba tare daya hayo saman floor d'in da suke ba ya samu wuri ya zauna a gefe, yana mai gaishe da iyayensa da kuma Kaka, kana suma su Bir suka gaishesa gaba d'ayansu.

Tukun Abba yayi gyaran murya yana mai kalonsa shi da Bir, yace musu Umminsu ta amince da zuwansu.

"Yeeehhh!! Wayyo Iyata na kusa in ganki."

Bir ya fad'a da k'afi yana mai tashi daga kan kujerar da yake ya doka tsalle tamkar k'aramin yaro.

Hakan shine kuwa ya sanya Kaka ta bud'e baki tana fad'in.

"Gaskiya wannan Iyar taka ba k'aramun tab'araka tayiba, haba ace yaro gardi dashi geme-geme amma kullum abun yara yakeyi."

Ta k'arashe maganar da tab'e baki.

"Anji d'in, sai ma naje wurin Iyata insha dad'in cinya."

Cewar Bir yana mai yiwa Kaka gwalo.

"Wannan ai ba sabon abu bane a wurina, tunda gashinan kullum anan d'inma sai ka hau cinya."

Shi kuwa Sheikh Ahamd murmushi yayi yana mai fad'in.

"To Alhamdulillah, ni yanzu zan huce."

"Allah ya kiyaye hanya ya dawo da kai lafiya."

Gaba d'ayansu suka had'a baki wurin fad'in haka.

Shi kuwa Bir kusa da Gimbiya Tasmir da yaga gaba d'aya yanayinta ya sauya, jkinta yayi matuk'ar yin sanyi tunda taji ance zasuje Bak'ar Masarauta.
Tukun ya lek'a fuskarta yana mai bud'e baki a hankali yace.

"Kiyi dariya zan tawo miki da Umminki fa kema."

Sharrrr!!!
Hawaye suka tsinke daga cikin idanuwanta a guje.
Hakan ya sanya Bir saurin zaro idanuwa, cikin tashin hankali yana mai fad'in.

"Subahanallahi, me akayi miki Gimbiyata? Nine? Ummice? Abbana? Autane ko kuma Kakace fad'a mun kinji."

Yayi maganar ta sigar yadda ake yiwa k'ananan yara magana a matuk'ar firgice, gaba d'aya ya manta a gaban ko suwaye yakema.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir asanyaye tace.

"Banason kaje ne, ina tsoron kar wani abu ya sameka."

"Babu abunda zai sameni Gimbiyata, kuma zan dubo miki har Umminki kinji yi shiru to."
Ya k'arasa maganar ahankali yana mai d'aukar yatsarsa ya d'ora akan fuskarta ya fara sharce mata hawaye.

Ihun da Kaka ta sanya tana mai tafa hannu tare da fad'in.

"Innalillahi wa'innailahir raji'una ni Zulai ina ganin abubuwa da yawa aduniya."
Ya sanyasu tina a wurin da suke.

Hakanne kuwa yasa Gimbiya Tasmir ta mik'e tsaye da sauri tana mai rufe fuskarta da d'an kwalin kanta cikin matsananciyar kunyarsu Ummi tayi d'akinta.

Yayinda shi kuma Bir ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Dawo Gimbiyata kar ki tafi d'aki, baza'a barni na shigo ba ance babu kyau kinji."

"Yau na shiga ukku da wa'yannan futsararrun yaran, kufa yanzu ba Kafurai bane ba amma kuke halinsu. To idan ba kuyi ku dawo ayi aurennan kowa ya huta, dan ni bazan iya cigaba da kallon wannan iskancinba!"

Cewar Kaka tana mai cigaba da tafa hannu.

Yayinda Ummi da Abba kuma harmada Auta suke ta faman gumtse dariyarsu, gudun karta futo Kaka tace sun rainata sune suka d'aure musu gindi.

Shi kuwa Bir kallonta yayi yana mai tab'e baki, kana daga bisani yace.

"Ai gwandama ayi mana auren ni dad'i zanjima."

Yayi maganar a wani irin sakalce yana mai yiwa Kaka gwalo.

"Kadallacn mara kunyar d'an dolo kawai, ai dama tunda naga Sheikh d'in kwali yana janka ajiki nasan saiya sa karainani kaima."

Ta k'arasa maganar tana mai mik'ewa ta doshi cikin d'akinta tana cigaba sa mita, su dai su Abba basuce komaiba.

A b'angaren su Sheikh Ahmad kuwa sosai akayi musu tarbar mutunci acikin Masaratar Fuld'e. Kasancewar kuma dama can ansan da zuwan nasu yau, shiyasa gaba d'aya filin da za'ayi wa'azi acikinsa yake cike dank'am da al'ummar jahar 'yan nesa da kusa.
Yayinda daga tsakiyar sa kuma aka kafa mambari gaba d'aya Malaman suka zauna asamansa kan kujeru.
Sai daga k'asa kuma aka jere kujeru da tabarmi tako ina.

Misalin k'arfe shad'aya aka fara wa'azin akan shirka, wato had'a Allah da wani da suka kasance suna yinsa tun usul.

K'arfe shabiyu da rabi aka tsaya akayi sallah, kana aka d'ora daga inda aka tsaya bayan sunci abinci.

Wa'azine sukayi mai ratsa jiki da jini, ta yadda har jama'a da dama sukaita kuka a wurin, alokacin da sukaji irin azabobin da Allah ya tanadarwa wanda ya koma garesa yana aikata irin abunda suke aikatawa.
Domin kuwa hatta da Lamid'o Sulaiman sai da ya sharce hawaye a b'oye, yayinda su Habu kuma dasu Jauron Fuld'e sukayi nasu a fili.
Tukun a k'arshe kuma aka koma jan hankalinsu akan jahilci, wato rashin ilimin addinin da basayi, wanda hakan kuma ya sanya har mutanen da suke acikin gida zubda hawaye.
Domin kuwa ita Gimbiya Haddial ma matse kanta tayi a gado wani irin tsoro na ziyartarta, saboda sanin yadda tun tana yarinya ta taso da yin tsafi kala-kala.
Hak'ik'a a yau d'in jikinta ya sakeyin sanyi, kana kuma taji tana buk'atar koyon ilimin addini, domin kuwa ta fahimci harda jahilci ya sata ta dinga hauka akan mutumin cikin mafarkinta, saboda ita ada kwata-kwata bata wani yadda da k'addara ba, shiyasa har ta dinga fad'in dolene ya zama nata, sai kuma gashi hakan bata yiwuba, asalima cikin mutane biyun da tafi tsana d'aya zai zama Mijinta.

Acan kuwa filin wa'azi Lamid'o Sulaiman da kansa ya mik'e tsaye yana tambayarsu yadda za'ayi su samu Malaman addinin da zasu dinga koyar dasu tare da jama'arsu.
Ai kuwa a wurin Malaman suka bada shawara akan dole su tura wasu daga cikin yaransu neman ilimin addini, sannan kuma su d'in acikinsu sun d'auki alk'awarin dinga zuwa duk asabar da lahadi suna koyar da jama'ar kafun Allah yasa asamu Malamai a cikinsu su fanshesu.

Hakan kuwa ba k'aramun dad'i yayiwa Lamid'o Sulaiman ba da duk sauran jama'ar garinma.
Wanda har hakan yasanya Lamid'o Sulaiman yayi musu kyautar manya-manyan shanaye ko wane Malami guda biyu.
Tukun a k'ashe da suka tashi tafiya aka yi musu shatara ta arzik'i acikin masarauatr fuld'e, suna idar da sallah la'asar kuma suka shiga motocinsu suna masu d'aukar hanya cikin tsananin farinciki.

Sosai shirye shiryen tafiya Bak'ar Masarauta ya kankama da gasken gaske acikin Masarautar Wasai, domin kuwa duka-duka kwana biyu ne suka rage kacal yanzu suyi tafiyar, yayinda ramuwar dukan shad'in da Asad zaiyi kuma suka rage kwana hud'u.

Sosai ya warke tas tamkar bashine yayi kamar bazai tashiba a lokacin da yasha zaniya, sai tabon bulalan da suke kwance akan fatarsa da yake ganinsu idan ya cire riga.

A kullum bashi da wata addu'a face ta nemna nasara a yanzu, yayinda abokantakarsu kuma da Bir tayi matuk'ar ƙarfi, ta yadda har tayi sanadin k'ulla k'awance tsakanin Ummi da Mamy.
Haka kullum suke jan Bir su tafi wuraren harkokinsu, domin kuwa tun daga ranar da akayi birthday har yau Asad bai k'ara komawa Palace ba, asalima sai tinanin rufeta da yake yi, saboda yadda yaji hukuncin mai yad'a alfasha a wurin Allah idan har ya mutu bai tubaba da Sheikh Ahmad yake fad'a musu a kullum idan suka zauna karatun bayan magariba zuwa isha, domin shi kansa yasan alfasha akeyi acikin wurin nasa, saboda maza da matane suke zuwa kuma har wanka suna shiga suyi a tare cikin swimming pool.
Gaba d'aya yanzu ya canza sosai-sosai, domin kuwa tini ya fara sabo da sanya manyan kaya, sai dai kuma har yanzu idan yasasu baiyi addu'a ba ji yake tamkar fatarsa zata d'aye dan zafi, hakan kuma shine yasa ko kad'an baya mantawa da yi yanzu.
Farinciki kuwa wurin Mai Martaba da Fulani tare da Babban Yaya harma da sauran Yayyansa mata tamkar sayi me haka sukai.
Dalilin daya sanya Mai Martaba ya had'asu su ukku har Bir yayi musu sababbin d'inkunan shaddodi da yadika masu tsananin tsada da kyau.

Ko kad'an Asad baya jin kishi akan Bir, tunda ya gane shi kwata-kwata ma babu wata Haddiyal a gabansa, asalima akoda yaushe idan suna tare labarinsa d'aya, shine Gimbiyarsa tafi kowace mace kyau.
Haka shima Asad zai dage tasa tafi kyau, shima Al'amin kuma ba abarinsa abaya dagewa yake tasa da bikinsu ya rage wata d'aya tafi kyau, sai dai kuma ana tinanin za'a had'esa ne dana Asad muddin yayi nasara akan Jauron Yamma.

_Bagan Kwana Biyu._

Tsaye suke acikin compound d'in gidan gaba mi d'ayansu.
Yayinda Ummi, Matar Sheikh Ahmad, Gimbiya da kuma Auta suketa aikin shararar k'walla.
Shi kuwa Bir jakun-kunansu ri'e a hannunsa, kasamcewar direbe aka turo ya d'aukesu zuwa masarauatr wasai.

"Allah Ubangiji ya tsareku, Rabbi ya kaiku lafiya ya kuma dawo mana daku lafiya."

Abba ya fad'a asanyaye yana mai jin tamkar ya fashe da kukan shima.
Yayinda Ummi kuma ta matso wurin da suke, tana mai kife tafukan hannayenta a tsakiyar kawunansu, bayan ta sanya su sun durk'uso.
Tukun ta bud'e baki cikin matsanacin kuka tana mai fad'in.

"Ya Ubangji, na sani kafini sanin abun da Yarannan suke da niyyar aiwatarwa, hakan yasa na kawo kukana gareka a matsayina na Mahaifiyarsu, domin ka zamto kariya a garesu. Allah na rok'eka yadda zasu tafi daga gabana lafiya ka dawomun dasu lafiya, Ubangji ka zamto gata haske a garesu, Rabbi ka karesu daga dukkan mugun abun kan hanya, da kuma wanda zasu riska a wurin da zasuje.
Allah ka jik'ansu, ka kuma tsaga rabon sake saduwa tsakaninmu dasu, Ubangji kayi musu alabrka. Kutafi Allah dawomana daku lafiya."

Ta k'arasa fad'e tana mai mayar musu da hulunansu, kana ta juya da sauri tana mai d'aga musu hannu ta shige ciki.

Haka dai su Gimbiya sukaita kuka har sai da sukaga tafiyar motarsu, tukun suka hak'ura suka koma cikin gida jiki a matuk'ar sanyaye.

Misalin k'arfe shida da minti goma shabiyar na safe suka k'arasa cikin masarautar Wasai.
Kuma lokacin da sukaje sun tadda kowa yazo, kuma kowa ya futo an gama shiryawa hatta da Mai Martaba Sarki Abdallah kuwa.

Da sauri Yarima Asad da Al'amin da suke jin mugun kewar Bir tun kafin ya tafi suka k'araso zuwa wurin da yake suna masu rungumesa.
Tukun suka bud'e baki a tare suna masu fadin.

"Allah ya dawo mana da kai lafiya, Ubangji ya sadaka da iyarka cikin aminci, ya kuma baku nasara akan abunda kuka tafi nema."

"Amin Amin, kaima Allah ya baka Gimbiyarka. Karkayi masa bulalun a hankali, ka zage iyakar k'arfinka ka dinga sauke masa Aboki, idan kaga yak'i kuka anyi kuma da yawa, to ka shimfid'a masa ita har akan fuska, nan ma idan kaga yak'i kuka to kayi masa a irin wurin da yayi maka kaim..."

"Hhhhhhh! Amma gaskiya Aboki kasan takan mugunta."

Cewar Al'amin yana mai sakinsa ya kwashe da wata shegiyar dariya.

Shi kuwa Yarima Asad murmushi yayi yana mai fad'in.
"An gama D'an uwa."

Tukun suka saki junansu saboda yadda sukaji ana cewa yazo su tafi.

Motar da Mai Martaba yake aciki ita yacewa BIr ya shigo ma.
Yayinda mota d'aya kuma suka cikata dank'am da kayan yak'i, tundaga kansu kwari da gwafa har zuwasu kibiya, mashi, tare da takkubai, sai kuma kayan guzurinsu na sawa dana abinci, saboda da niyyar yin sati d'aya dai-dai suka futo.
Yayinda motoci biyu kuma suke cike da manyan Malamn bakwai, sai kuma sauran motocin da suke cike da 'yan Silke, wato dai mayak'an masarautar da suka kai su kusan sittin.
Tukun suka fara tafiya su Babban Yaya suna d'ago musu hannu tare da sauran jama'ar masarautar da suka furfuto.

Misalin k'arfe takwas na safe suka isa bakin ruwa, saboda a jirgi suka tsara zasuyi tafiyar, kuma bawai kai tsaye cikin Bak'ar Masarauta zasu saukaba, gaba d'aya sun gama tsara yadda zasu aiwatar da komai idan sunje cikin hikima, ta yadda zasu samu jama'ar su basu had'in kai.

Cikin k'ank'anin lokaci aka gama shirya gaba ki d'aya kayansu acikin jirgin, sannan suma suka shiga, kasancewar kuma irin tafkeken nan ne shiyasa ya cinyesu su duka.
Tukun matuk'an jirgin suka d'au hanya.
Yayinda har lokacin kuma Bir yake zaune a jikin Mai Martaba, domin kuwa ba k'aramun shiga ransa yayiba, sai yake jinsa tamkar Asad d'insa ko Al'amin ako da yaushe.

Tunda suka fara tafiya sau d'aya kawai suka tsaya a wani gari sukayi alwala sukai sallah, tukun suka cigaba da tafiya, a haka har dare ya riskesu ba tare da sun isa Jahar Karfuz ba.
Kasancewar kuma jirgin yana da fitilu, shiyasa suka cigaba da tafiya har garin Allah ya waye, tukun misakin k'arfe takwas na safe suka isa Jahar Karfuz.

A lokacin da suka iso sun tadda har mutumin da suka k'ulla alak'a dashi yazo tarbarsu.
Kasancewar tun a washegarin da aka gama tsayar da shawarar yadda tafiyar zatayi, Mai Martaba Sarki Abdallah yayi amfani da dukiyarsa wurin tura wasu daga cikin jama'arsa zuwa nan Jahar Karfuz, domin su samu wani mutum daga cikin mutanen Jahar wanda zai taimaka musu da wurin zama kafun su k'arasa Bak'ar Masarauta.
Kuma kasamcewar sun tawo da mak'udan kud'i, shiyasa ko kad'an basu sha wahalaba suka had'u da wani dattijon mutum da yake a k'ark'ashin mulkin Bak'ar Masarauta.

Ada da farko nuna musu yayi bai zai tab'a cin amanar Masarautarsa ba, amma daga k'arshe da sukayi masa bayanin abunda yake tafe dasu, sannan kuma suka nuna masa ruwan dukiya sai ya amince tini.
Ta yadda haryayi musu alk'awarin samar musu wurin zama idan sun iso, tare kuma dayi musu jagoranci zuwa cikin Bak'ar Masarauta.
Kuma ya amintane harda sanin da yayi na yanzu babu Boka mai hutar kasko, ballantana asan abun da ya aikata akashesa.

Hakanne yasa suna k'arasowa suka tarar da mutumin harda d'an uwansa suna jiran isowarsu.

Gaba d'aya futowa mutanen cikin jirgin sukayi cikin tsananin jigata, suna masu sakin mik'a, yayinda sukejin gwiwoyinsu kuma duka sunyi matuk'ar sanyi.
Tukun daga k'arshe suka fara futo da kayayyakinsu.
Kasancewar kuma gidan da mutumin ya tanadar musu bashi da nisa da bakin ruwa shiyasa ko kad'an basu wahala ba wurin d'aukar kayansu suka isa.

Gine ne irin na gidajensu.
'Dakuna ne ajere har kusan guda ashirin acikin gidan.
Kuma gaba d'ayansu an tanadi shimfid'un kwanciya a cikinsu.

'Daki guda aka bawa Mai Martaba da yake d'auke da gadon k'arfe acikinsa.
Yayinda Malamai kuma aka had'a duk mutum biyu a d'aki d'aya, shi kuwa Bir da Sheikh Ahmad d'aki guda aka basu.

Yayinda sauran d'akunan guda goma shashida kuma gaba d'aya sauran jama'ar tasu suka raba kansu acikinsu, kasancewar kuma suna da girma sosai, shiyasa basuyi irin muguwar matsuwar nan ba.
Gobe ce ranar da suka tsayar a matsayin ranar da zasu fara shiga cikin Bakar Masarauta, shiyasa yanzu kuma ko wanne ya kwanta acikinsu, saboda su samu jikinsu ya ware duka.

Misalin k'afe takwas na dare bayan sunyi sallah sunci abinci Mai Martaba ya buk'aci ganinsu gaba d'aya a cikin tsakar gidan.
Cikin k'ank'anin lokaci dukansu suka furfuto suna masu zagaye Mai Martaba.

"Na buk'aci ganinku anan ne saboda mu tattauna daku akan yadda zamu shiga ciki gobe."

Girgiza kansu gaba ki d'ayansu sukayi, tukun daga bisani Sheikh Ahmad yayi gyaran murya yana mai fad'in.

"Ni ina ganin idan mukatashi zuwa ba wai zamu tafi bane mu dukanmu, saboda ganin hakan zai sanya su zargi wani abun, amma idan mutane k'alilan sukaje, shine zasufi tsayawa su saurare mu."

"To idan kuma suka farwa wa'yanda sukaje d'in a lokacin fa."
Cewar wani daga cikinsu.

Hakan da Bir yajine ya sanyasa yin gyran murya.
Kana ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Ai bazasu tab'a far musu lokaci d'ayaba, sai dai ace akai mutum d'akin Azaba ko kuma filin da ake kashe mutanen, saboda a yadda tsarinsu yake muddin za'a kashe wani to dole sai antara jama'a, akan idon kowa za'a kashesa. To kunga idan hakane kafun su gama tara mutane mu kuma da akace zamu b'uya a wurin da zan nuna mana sai mu futo."

"Tabbas na aminta da wannan batun, duk da dai ma bama fatan hakan ta faru, amma kafin nan abun da zan sanar daku shine, ko da rikici ya b'arke atsakanin mu, to kusani banda tab'a Mata, tare kuma da Yara k'anana, Manyan ma kuma muddin har mutum b'uya yayi, to kar wanda ya tab'asa, ma'ana dai sai wanda kaga yana namen ranka tukunna kaima sai kanemi nasa ran."

Mar Martaba ya fad'a musu haka, kana ya d'ora da fad'in.

"Dan haka goben sai mu had'a Malaman mu tare kuma da mutum ukku acikin ku suyi gaba, in yaso mu kuma sai mu b'uya a wurin da Abdulmajid yace zai kaimu mu b'uya duka."

Jinjina mai kai sukayi gaba d'ayansu suna masu gamsuwa da bayaninsa, kana daga k'arshe suka rufe taron da addu'a tare da fatan nasara a wurin Allah, sannan kowa ya tashi ya tafi d'akinsu.

*****
Tamkar yadda sukayi sallolin jiya a jam'i haka ma sukayi asubar yau d'in.
Tukun bayan sun idar suka fara shish-shiryawa, gaba d'ayansu suna komai ne a takure, saboda sanyin garin da yake ratsasu idan aka cire Bir kad'ai daya saba da shi.

Sai da suka gama shiryawa tsaf, tukun sukaci abincin da mutumin da suka snya ya samo musu gida ya siyo musu, alokcin kuma k'arfe kusan tara na safe.

Hakanne ya sanyasu mimmik'ewa tsaye gaba d'ayansu.

Sanye suke da kayan yak'i ajikinsu, yayinda jikin kayan kuma suka soke da mugayan makamansu, shima Bir kuwa zam irin shigar mayak'an yayi, tukun ya soke kwari da gwafa tare da mashika a jikinsa.

Su kuwa tawagar Malamai da Mai Maryaba shigar manyan kayane sukayi.
Yayinda daga k'asan manyan kayan kuma suke d'auke da abubuwan kariya a jikinsu, tare kuma da nasu makaman da suke tinanin sun wadacesu.

Shi kuwa Mai Martaba gaba d'aya cikinsu babu wanda yasan irin shirin da yayi, su dai kawai sun gansa ya futo sanye da babbar riga a jikinsa tare da rawaninsa d'aure aka.

Malamai ne suka fara fucewa, wannan mutumin ya shige musu gaba, domin ya sadasu da har cikin Fada cikin suk'i, a matsayin ya gansu ne a waje suka buk'aci ya rakosu ciki yayi dasu zaice.

Tukun Bir ya shige gaba Mai Martaba na biye dashi a baya, kana suma sauran mayak'an suka fara biyosa a layi, mana kuma da d'ai-d'ai da d'ai-d'ai, ta yadda baza'a ganesu ba.

Suna futa Bir yayi bayan wani dank'areren dutse, tukun ya fara tafiya a jikinsa cikin wani irin sand'o, saboda yadda ya hango dakaraun Bak'ar Masarauta bud'u-bud'u dasu suna ta faman kalle-kalle, da alamun dai sun dad'e a wurin ba tare da sun kauce bama.

Cikin sand'a suke bin bayan Bir da d'aya bayan d'aya, a haka har sukayi tafiya mai nisa duk ajikin dutsen, yayinda ako wane wuri kuma idan sukazo giftawar sai sunga dakarun nan, sai dai kuma cikin ikon Allah har yanzu babu wanda ya lura dasu a cikinsu.
A haka har suka yanko cikin Bak'ar Masarauta.

Da sauri Bir ya lumshe idanuwansa, yana mai jin wani irin yanayi na lullub'esa, saboda hango b'angarensu na Bayi da yayi.
Hakan yasa yaji harya k'agara ya d'ora k'wayar idanuwansa akan Iyarsa, da kuma Abokansa.
Tukun daga bisani ya bud'esu yana mai cigaba da tafiya da d'an sauri.

A haka dai har suka b'ulla cikin wurin da suke had'uwa da Gimbiya Tasmir, tukun suka rarrabu ko wanne acikin su yana mai samun bayan bishiya ya b'oye, kasancewar wurin kuma yana da wadatar bishiyun sosai, shiyasa har saura sai da sukayi.

Acan b'angaren su Sheikh Ahmad kuwa, suna zuwa bakin k'ofa samudawan Dakarun nan da suka kasance babu sutura a jikinsu sai uban zanne masarauta suka taso da sauri suna masuyo kansu
Amma ganin d'an garinsu da sukayia a tare da sune ya sanyasu dakatawa suna masu tambayarsa suwaye ne su d'in.

"Bak'in Shugaba."

Ya fad'a babu alamun tsoro a tattare da shi kwata-kwata.
Hakan da suka ganine kuma ya sanyasu kaucewa suna masu basu hanya suka huce.
Kai tsaye kuwa daga nan wurin fada ya dosa da su.

A b'angaren Sarki Barbaru kuwa ranbonsa da zaman fada tun a ranar da abun nan ya faru sai a yau, saboda ganin da yayi shiru babu wata musiba data saukar musu tamkar yadda suke zato, shiyasa yaji ya d'an fara dawowa nutsuwarsa, wannan dalilin ya sanyasa shiryawa ya tafi fadar yau.

"Kuyi sauri ku juya baya, sannan kuma idan mun shiga ciki gaba d'ayanku kuyi kome kukaga nayi, muddin mutum yana son ya tsira da rayuwarsa."

Cewar Mutuminnan adai-dai lokacin da sukazo bakin fada yana mai juya baya.

"Kamarya kuma mu juya baya, kana nufin kace da baya-da

Please Login or Register in order to submit comment