Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idanuwanta akan fuskar Yayan nata.

Shi kuwa Habu da sauri ya bud'e baki irin bai san komai ba, yana mai fad'in.

"Me yayi miki ne? Wani abunne ya faru da kika kai masan?"

Rumtse idanuwa Gimbiya Haddiyal tayi da matuk'ar k'arfi.
Kana daga bisani ta bud'e su akan fuskar Habu tana mai fad'in.

"Wai..wai haka yace yana s.o..na!"

Ta fad'i maganar a wani rarrabe, saboda yadda zuciyarta ke sake yi mata nauyi da tuna kalmar da take.

"Shin dama so yana zama laifi ne?
Hak'ik'a da na tsorata da yanayin ki, domin kuwa nayi tinanin wani abun yayi miki daban da kike kuka haka, amma ni a wurina ai sai nake ganin masoyi baya tab'a zama mak'iy..."

"Ya isa haka, ya isa dan Allah Hamma."

Ta katsesa da fad'in haka cikin sauri da zafin rai, da alamun dai ta manta matsayinsa a wurinta ne yau.
Hakan da Habu yaji ne ya sanyasa yin shiru yana mai binta da idanuwa, domin ko talallami yake son ya bita ko Allah zaisa su dace.
Yayinda ita kuma ta d'ora da fad'in.

"Akan me zaka furta hakan, bayan kuma kai da kanka kasan nid'in ta wanice tun tuni.
Gid'ad'o am shine kad'ai nawa, shi kad'ai ne mutumin da nake buk'atar jin wannan kalamin daga bakinsa, bayan shi kuma babu wani mahaluk'i da zai furtan shi d'in ban tsanesa ba a duniya, domin ko ina rik'e mutuncin masoyina ne."

Ta k'arasa maganar idanuwanta akan fuskar Habu.
Ganin hakan da Habu yayine ya sanya sa mik'ewa daga kan gadon nata yana mai fad'in.

"Allah ya baki hak'uri k'anwata na manta ne nima.
Amma kuma abun da nake son ki sani shi ne, har abada akwai bam-banci tsakanin soyayya da k'iyayya, dan haka babu tayadda za'ayi masoyi ya zamto mak'iyi."

Ya k'arasa maganar yana mai juyawa ya fuce daga cikin d'akin nata.

_BAYAN SATI BIYU_

*K'ASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAK'AR MASARAUTA...........✍



_I'M TIRED WALLAHI 😫_


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*12*



Tun daga waccan ranar har kawo yau Gimbiya Tasmir ba ta sake yin murmushi ba.
Gaba d'ayanta ta canza, damuwa tayi mata yawa, duka duniyar tai mata zafi, ba komai ba ne kuma ya kawo mata hakan sai kalaman Bir da suka zauna sukai daram acikin k'wak'walwarta.
Babu yadda ba tayi ba domin taga ta manta da duk abubuwan da suka faru a tsakaninta da shi, amma gaba d'aya abun ya citura.
Asalima sai zamtowa yay ko rufe idanuwanta tayi babu abun da take gani face kyakkyawar fuskar sa, yana jifan ta da murmushinsa mai tsananin kyau, da zarar kuma ta kwanta bacci shikenan ta fara mafarkinsa, har zuwa lokacin da zata tashi.
Idan wanka take shi take gani acikin idanuwanta, haka kuma idan tana magana da yayyinta sai tai ta jin muryar su na zamtowa tamkar tasa.
Idan kuma tayi tinanin hukuncin da ta d'auki alwashin yi masa na abun da yayi mata, sai taji gaba d'aya tsoro ya lullub'eta, tausayinsa yayiwa zuciyarta k'awanya, atak'aice dai gaba d'ayan ta tarasa sukuni, domin kuwa kome take tinaninsa take yi.
K'arin abun takaicin kuma bai wuce yadda a kullum take jin idanuwanta na mararin ganinsa ba, yayinda kunnuwanta kuma suke tsumayen jin muryar sa, wanda hakan kuma shine ya sa gaba d'ayan ta tak'ara canzawa, shiru-shirun ta ya k'aru fiye da da.
Babu juyin duniyar da mahaifiyarta ba tayi ba akan ta fad'a mata abun da ke damunta, saboda ganin ta da tayi tana ramewa amma tak'iya, wanda hakan kuma ya sanya dole ta hak'ura ta barta.

Hakan da take ji ne ya sanya zuciyarta ta fara rayamata cewar ko dai gaskiya ne abun da ya fad'a mata, na cewar itama tana son sa, wanda hakan kuma shine ya k'ara sanyawa hankalinta ya sake bala'in tashi, domin kuwa ko kusa ko kad'an bata fatan magan-ganunsa su tabbata, saboda hakan ba k'aramun k'ask'anci zai janyo mata ba.

To tayaya ma hakan zata faru, bayan babu a inda ta tab'a jin labarin cewar an tab'a samun d'iyar Sarkin da taso Bawa, kana kuma idan ya zamto gaskiyarne ma, ita ta sani ko da zata mutu babu ta yadda za'ayi iyayen ta su aminta da wannan banzan al'amarin ba, domin ko ba k'aramun buri iyayen nata suke da shi akan ta ba.

Jin da tayi zuciyarta tak'i tabar tinanin kalamansa ne, ya sanya ta yanke hukuncin yin tambaya akan alamun soyayya tamkar yadda ya shawarceta tayi, domin kuwa ba k'aramun damunta abun yayi ba.
Hakan ya sanya yau tun da ta tashi da safe tana yin wanka ko karyawa bata iya tsayawa tayi ba ta aika a kira mata amintacciyar Hadimarta, wacce a shekaru ta girme ma ta har da kusan shekaru biyar.
Wato Hadima Fulaika, ita kad'aice Hadimar da take iya tsayawa a gaban Gimbiya Tasmir ba tare da taji fargaba ko tsoronta ba, ballantana kuma har jikin ta yay ta karkarwa, domin kuwa tun Gimbiya na 'yar k'aramarta suke tare tana yi mata wasu 'yan ayyukan, duk da dai itama a lokacin ba wani girman can gareta ba, wannan dalilin ne ya sanya har Gimbiya Tasmir take sakewa da ita har su d'anyi hira wani lokacin.

Sosai Hadima Fulaika take da hankali da nutsuwa, ko kad'an bata da rawar kai irin na sauran 'yan Uwanta Hadimai da Bayi, wannan dalilin ne ma har ya sanya jinin su yazo d'aya da Gimbiya Tasmir, ta yadda har wasu lokutan idan taga abun da bata sani ba take tambayarta kuma ta bata amsa.


Zaune take a gefen gadonta ta buga uban tagumi da hannu bibbiyu, tana mai jiran isowar Hadima Fulaika da ta aika a kira mata ita.

Sanye take da bak'ar doguwar riga da tayi matuk'ar yi mata kyau.
Yayinda fuskarta kuma ta kasance shafe da mai kad'ai babu wata kwalliya akan ta, domin kuwa tun daga ranar da abun nan ya faru har kawo yau bata k'ara samun nutsuwar da zata iya tsayawa ayi mata kwalliya ba, asalima ko kwalli bata iya sawa idanuwanta, da zarar tayi wanka kawai mai take murzawa akan fatarta ta koma ta kwanta akan gado tana tinaninsa.

Kallo d'aya mutum zai mata muddin ya santa a baya ya gane ramar da tayi, domin kuwa ko kad'an bata b'uya ba.
Gaba d'aya jin duniyar take tai mata wani irin k'unci.
Ko a mafarki bata tab'a tinanin irin wannan lokacin zai tab'a riskarta ba, wato lokacin da damuwa zata kutso cikin rayuwarta, sai gashi kuma tazo ta risketa a lokacin da bata shiryawa zuwanta ba.

Sautin k'arar k'wank'waso k'ofar daya daki dodon kunnuwanta ne ya sanya ta dawowa daga duniyar tinanin data tafi, tana mai janye hannuwanta daga kan kuncinta tare da d'ago kanta takai idanunya zuwa kan k'ofar.

"Shigo."
Ta fad'a da d'an sauti, kana kuma a tak'aice tana mai janye idanuwanta daga kan k'ofar.
Tukun tamayar da su ta lumshe.

Ita kuwa Hadima Fulaika jin da tayi ta bata izinin shigowar ne ya sanya ta d'ora hannunta akan k'ofar, tana mai tura ta tare da danna kanta cikin d'akin.
Tukun ta mayar da k'ofar a hankali tana mai rufe ta.
Kana ta juyo tana mai nufo wurin da Gimbiya Tasmir take, wato bakin gadon ta.

Matashiyar budurwace mai kimanin shekaru ashirin da bakwai a duniya.
Sanye take da d'an guntun bak'in kyalle d'aure a k'ugunta, tare da farar wargajejiyar rigarta.

Daga d'an nesa da Gimbiya Tasmir ta tsaya tana mai sunkuyar da kanta k'asa, tare da fad'in.

"Barka da safiya kyakkyawar Gimbiya, hak'ik'a gani gabanki na amsa kira."
Ta fad'a cikin nutsuwa kanta durk'ushe a k'asa har lokacin.

A hankali Gimbiya Tasmir ta d'ago kanta tana mai bud'e idanuwanta akan fuskar Hadima Fulaika.
Kana ta janye su tana mai mata alama data zauna da tafin hannunta.
Hakan da Hadima Fulaika ta gani ne ya sanya ta zube gwiwoyinta da sauri a gaban Gimbiya Tasmir, tana mai sake durk'usar da kanta k'asa.

Shiru ne ya biyo baya har kusan bayan giftawar dak'ik'u biyar a gaba, kana Gimbiya Tasmir ta sake d'ago kanta tana mai fesar da wata irin zazzafar iska daga cikin bakinta, tare da lumshe idanuwanta.
Tukun daga bisani ta bud'e su akan Hadima Fulaika.
Kana a hankali kuma cikin sanyin murya ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Tambayar ki zanyi, ina son ki fad'amun gaskiyar abun da kika sani, karki k'ara da ko kalama d'aya, kar kuma ki rage ko kalma d'aya daga abun da kika sani, ma'ana dai ki fad'amun zallar gaskiya."

Cikin tsantsar ladabi Hadima Fulaika ta k'ara durk'usar da kai k'asa tana mai fad'in.
"Ubangiji ya taimaki Gimbiyar Bak'ar Masarauta, hakika bakin Fulaika yayi kad'an dayi miki k'arya, hakan yasa nake fatan tambayar ta zamto wacce nasan amsarta."

Fesar da iska Gimbiya Tasmir tayi daga cikin bakinta, kana ta sake d'ora idanuwanta akan gashin kan Hadima Fulaika, kasancewar ta durk'usar k'asa.
Kana ta rumtse idanuwan nata da k'arfi, tana mai jin nauyin abun da take shirin fad'e a zuciyarta.
Kafin daga bisani kuma ta bud'e su, tana mai d'aga lab'b'an ta cikin wani irin sauti tace.

"A duk lokacin da na gansa, ina mai jin yanayi na na sauyawa, bugun zuciyata na canzawa, ta yadda har nake jin tamkar zata hudo k'irjina ta futo, su kuwa k'wayoyin idanuwansa, sun zamto tamkar mayen k'arfe ne, ta yadda har idan nawa da nasa suka had'u nake kasa janye su daga cikin nasa kwata-kwata.
Shin me yake kawo hakanne? Me hakan ke nufi? Wannan itace amsar tambayar da nake buk'atar ji daga gareki."

Ta k'arasa maganar da lumshe idanuwanta, tana mai jin yadda zancensa kawai ya sanya bugun zuciyar ta sauyawa.
Yayinda take fatan kar ta sake jin irin abun da ya fad'a mata daga bakin Hadimar a zuciyarta.

Yayinda idanuwanta kuma suka kasance k'ur akan gashin Hadima Fulaika tana mai jiran jin abun da zai futo daga bakinta.

Ita kuwa Hadima Fulaika wani irin gajeran numfashi taja, tana mai fesar da shi, a lokacin da tagama jin tambayar Uwar d'akin nata.
Kana tayi shiru tana mai nazari akan abubuwan da tafad'a cikin k'wak'walwarta.
Tukun daga bisani ta sake fesar da iska a karo na barkatai, sannan ta daga lab'b'an ta har lokacin kanta na durk'ushe a k'asa tana mai fad'in.

"Ya Shugabata, na zata al'amarin da yake zuwa da firgici yana zuwane tattare da abinda yake d'arsuwa a zuciyar mutum na tsoro ko mamaki, a yayinda tsoro ya zowa mutum, sai jininsa ya kad'u, bugun zuciyarsa ya k'aru, yanayin jikin sa ya canza.
Shin ba haka kika ji ba a lokacin da kika had'a ido da shi?"

Sautin muryar Hadima Fulaika ya daki kunnuwan Gimbiya Tasmir tana mai fad'in haka.
Wanda hakan da ta fad'a d'in kuma ya sanya Gimbiya Tasmir tinanin anya ko mutum ce Hadimar tata, domin kuwa babu wani abu da bai faruba aduk lokacin da suke had'uwa dashi da bata fad'e sa yanzu ba.
Hakan ko shi ya sanya ta cikin matsanancin mamaki, tare da fargabar abun da taji yana shirin tabbata, ta yadda har ta kasa bud'e baki ta bawa Hadima Fulaika amsar tambayar da tayo mata.

Ita kuwa Hadima Fulaika ba tare da ta damu da rashin amsawar da Gimbiya tayi ba ta d'ora da fad'in.

"Wannan shine alamun so.
Shin waye shi? 'Dan wane Sarki ne? Daga cikin wace babbar Masarautar ya futo?
Hak'ik'a ko d'an Sarkin inane ma, shi d'in ya zamto mai sa'ar rayuwa, tunda har Gimbiyar Bak'ar Masarauta ta kamu da soyayyarsa, so mai tsanani ma kuwa, ba tare da kinsan da hakan ba."

Ta dakata a haka, tana mai jan numfashi tare da fesar da shi.
Yayinda zuciyar ta kuma take cike da son jin ko wanene Gimbiyar tasu ta kamu da son sa.
Ita kuwa Gimbiya Tasmir sosai ta rud'e da jin kalaman da suka futo daga bakin Hadimar tata, wato ya tabbata dai son nasa take tamkar yadda ya fad'a.

Tana cikin wannan rud'un ta sake jiyo muryar Hadima Fulaika na cigaba da fad'in.

"Shawara ce zan baki yake Uwargijiyata.
Hak'ik'a alamarin so ba a sanya acikin sa, ke d'in kin kasance irin macen da kowane namiji zaiyi fatan mallakarta a duniya, duk girman mulkin sa da yawan dukiyar sa kuwa.
Kin had'a komai da komai da ake buk'ata a wurin mace, wato dai kyawun jiki dana sura, gata, mulki tare da narkon dukiya.
Hakan yasa nake shawartarki da ki cire tsoro, fargaba, kunya, ki k'arfafa zuciyarki ki farauci soyayyarki a wurin sa tun kafin lokaci ya k'ure miki, wato dai ki fuskance sa ki sanar masa da abun da ke cikin zuciyarki game da shi, domin kuwa ba'a sanya kwata-kwata alamarin soyayya, tamkar yadda na fad'a miki da farko, saboda gudun cutar da zuciya ya Shugaba, dan haka ki samesa ki fad'a masa cewar kina son s...."

"Ya isa haka Fulaika!!!"

Gimbiya Tasmir ta katseta da fad'in haka da wani irin k'araji, jikin ta na d'aukar rawa tamkar mazari, kafin daga bisani kuma ta mik'e tsaye zumbur daga kan gadon da take a zaune, tana mai fara zagaye d'akin gumi na yanko mata akan goshi.

Yayinda ita kuma Hadima Fulaika tayi matuk'ar firgita da jin irin tsawar da uwar d'akin nata ta daka mata, abun da tunda suke da ita bata tab'a yi mata ba.
Ko kadan batayi tinanin hakan zai b'ata mata rai ba idan ta fad'a, saboda jin da tayi ita ta buk'aci sanin hakan shi yasa ta fad'a mata.
Tsoron ta d'aya a yanzu shine kar tace zata sa a hukunta ta akan abun da ta fad'a d'in.

"Tashi ki fucemin daga d'aki, yau kalaman ki basu farantamun ba Hadima."

Muryar Gimbiya Tasmir ta daki kunnuwanta ta cikin wani irin sauti mai amo.
Hakanne yasata k'ara durk'usar da kanta k'asa jikinta na karkarwa, tukun ta bud'i baki tana mai fad'in.

"Tuba nake ranki ya dad'e, yau d'in ma akasi ne aka samu."
Tukun ta mik'e tsaye da sauri tana mai sake fad'in.
"Ubangiji ya huci zuciyarki, na barki lafiya Shugabata."
Kana ta juya tana mai kama hanyar futa daga cikin d'akin cikin sauri.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir cikin sauri ta doshi wurin da takobinta take tana mai d'auko ta.
Kana ta zareta daga cikin d'an gidan ta tana mai damk'arta a cikin tafin hannunta tare da nuna saman gadon ta da ita, tace.

"Shairamaaa!!!"

Take kuwa wannan dank'areriyar macijiyar tata ta bayyana a tsakiyar gadon nata.

Cikin wani irin yanayi na tsantsar rud'un da take a ciki tayi kan gadon gadan-gadan.

Tana k'arasawa gaban sa taja ta tsaya tana mai watsa idanuwanta akan macijiyar nan da take aikin kallon ta tana kad'a harshenta.
Tukun daga bisani ta bud'e baki cikin wata irin murya mai matuk'ar rauni, tana mai fad'in.

"Shairama kiji yadda zuciya tai dani, kiji yadda rayuwa take shirin canzamun, kiji yadda k'arfin ikona, izzata suke shirin zubewa wanwar a k'asa.
Hak'ik'a na yadda da zancen Hadima Fulaika, ni Gimbiya Tasmir d'iyar Sarki Barbaru na kamu da soyayyar Bawan gidan mu.
Shin wane taimako ne zaki munne akan hakan Shairama? Domin ko ina jin zuciyata tamkar zata fashe a koda yaushe, ina buk'atar mantasa a rayuwata, ina buk'atar cire soyayyar sa a zuciyata, amma taya ya? Me zanyi ya zanyi Shairama?
Ni d'iyar Sarki ce, shi kuma Bawa ne, dan haka babu batun so a tsakanin mu har abada.."

Wani irin lank'washewa macijiyar nan tayi, kafin daga bisani kuma ta fara zagaye akan gadon tana mai cigaba da karkad'a harshe.

Cikin tsantsar firgici Gimbiya Tasmir ta zaro idanuwanta, saboda fahimtar abun da macijiyar ke nufi da hakan da tayi, tana mai fad'in.

"Ke kin aminta da naje na same sa na sanar mishi? Shin me yasa bakin ku zai zo d'aya dana Hada Fulaika ne? Me yasa ba zaku iya taimakona ba ta wata hanyar sai wannan, akan me zan kai kaina wurin da bai kamace ni ba? Shin idan naje ma nace masa me ma?"

Ta sake fad'a a wani irin hargitse, idanuwanta na zubar da wata irin k'walla, yayinda take jin zuciyarta na cigaba da harbawa, wani b'angaren daga jikin ta na shawartarta akan tayi amfanin da shawarar amintattun nata, yayinda wani b'angaren kuma take gargad'in ta da aikata yin hakan, tare da nusar da ita irin danasanin da zatayi a gaba.
Kafun daga bisani kuma ta fara shirin hawa kan gadon, sai dai kuma tana d'ora hannunta akai Shairama ta b'ace b'at, tamkar ba atab'a yin taba a wurin.
Wanda hakan kuma ya sanya Gimbiya Tasmir ta k'ara fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi, saboda fahimtar da tayi na Shairama bazata iyayi mata komai ba akan lamarin, bayan shawarar data bata.
Hak'ik'a so bai mata adalici ba, amma ya zatayi, dole ne ta zauna tayi tinanin abun yi, domin kuwa a halin yanzu babu wanda take muradin gani a gaban ta face shi.


Acan b'angaren Bir kuwa hankalinsa kwance yake harkokinsa yanzu.
Tun daga ranar daya fad'awa Gimbiya abun da ke cikin ransa yaji gaba d'aya duk wata damuwarsa ta yaye, yawan fargabar da yake akan al'amarin gaba d'aya ta gudu, domin ko ya tabbatar da Gimbiya ma na masa irin son da yake mata, kuma jikin sa na basa cewar ko ba dad'e ko bajima zatazo da kanta ta nemesa, domin ta shaida masa cewar baiyi k'arya ba, duba da yadda yaga an kwashe kawanaki da fad'a mata maganar da yayi amma batasa an yi masa komai ba har kawo yau, hakan yasa jikin sa ke basa cewar Gimbiya na gab da zamtowa tasa, sai dai kuma a kullum idan ya tuna matsayinsa da nata, sai yaji wata irin fargaba na lullub'e sa, domin kuwa shi kansa yasan abu ne wanda yuwuwarsa ke da matuk'ar wahala.


*K'ASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.*

Tini shirye-shiryen bikin babbar sallah ya kankama ako wane b'angare na k'asar da ya kasance d'auke da musulmai.
Ko ina ka gifta raguna da shanune har ma da rak'uma kake ganin ana hucewa da su.
Yayinda kasuwanni kuma suka cika suka tumbatsa da al'umma masu siyan kayan sallah.
Domin kuwa duka-duka yau sati d'aya ne ya rage sallah, yayinda arfa kuma ta rage saura kwana shida.

Anan cikin Masarautar Wasai ma hakan take, sosai ake shirye-shiryen sallah, yayinda Mai Martaba Sarki Abdallah da Gimbiya Fulani tare kuma da wasu daga cikin 'yan masarautar suka tafi k'asa mai tsariki sauke farali.

Kowa ka gani acikin masarautar zaka same sa da irin shirin da yake yiwa zuwan sallah'r, idan aka cire mutum biyu kawai dake cikin ta.
Wato Yarima Asad da kuma Al'amin, wanda ya ari damuwar abokin nasa ya yafa a jikin sa ta zamto tasu su biyu.
Gaba d'aya Yarima Asad ya susuce tun bayan dawowarsa daga Masarautar Fuld'e.
Ta yadda duk wanda ya gansa har dai yasan yadda yake ada sai ya tambaya abun da ke damun sa, domin kuwa ba k'aramar rama yayi ba, kasancewar har zazzab'in kwana biyar sai da yayi, saboda kalamin da Gimbiya Haddiyal ta fad'a masa.
A duk rintsawar duniyar da zaiyi sai tazo masa acikin mafarkinsa.
Yayinda a zahiri kuma idan ya tashi yake jin sautin muryar Baby tamkar tata idan tayi magana, wanda har ta sanadin hakan ya sanya sa dena zama a kusa da Baby gaba d'aya.
Babu yadda baiyi ba domin ya manta da ita, amma gaba d'aya abun ya citura, asalima yadda adadin futar numfashin yake haka yake jin soyayyar ta nak'ara damk'ar zuciyarsa, ta yadda har ya tabbatarwa kansa da cewar bazai tab'a iya rayuwa ba idan babu ita a kusa da shi.
Babu juyin duniyar da Mahaifansa basuyi ba kafun su tafi Saudiyya akan ya fad'a musu abun da yake damun sa amma gaba d'aya yak'i.
Ganin hakan da sukayine ya sanya su suka kira Al'amin suka zaunar da shi tare da tambayarsa, aiko ba tare da b'ata lokaci ba ya kwashe komai da ya sani ya fad'a musu.
Sosai suma kuwa suka girgiza da jin lamarin, wanda hakan kuma shiya k'ara sanya Gimbiya Fulani taji ta k'agara su tafi k'asa mai tsarki, domin tayiwa d'an nata addu'ar cikar burinsa, tare kuma da fatan shiriya.
Yayinda shi kuma Mai Martaba ya k'uduri aniyar turawa zuwa Masarautar Fuld'e a tambayarwa d'an sa auren Yarinyar idan sun dawo, muddin hakan zai dawo masa da walwalarsa, tamkar yadda yake ada, in yaso sai a had'a da Billy ya auresu su duka biyun a rana d'aya, domin kuwa bazai tab'a iya jurar ganin d'an nasa a cikin irin halin da yake ciki ba yanzu.

A lokacin da suka tashi tafiya kuwa, Asad da kansa yaje ya durk'usa gaban fulani cikin sanyin murya mai tafe da rauni, yana mai rok'on ta akan idan taje tayi masa addu'ar samun nasarar rayuwa, da mallakar muradin zuciyarsa.
Sosai kuwa hakan ya sake girgiza Fulani, domin kuwa tun da take da d'an nata bata tab'a jin muryarsa na rawa ba idan yana magana sai a ranar, ga kuma wata irin nutsuwa da taga ta saukar masa.
Aiko take a wurin taji tausayinsa yayi matuk'ar mugun lullub'e ta, ta yadda har batasan lokacin data d'ago sa tsaye ba tana mai rungumesa a jikin ta, tare da fad'a masa cewar ya kwantar da hankalin sa zatayi masa addu'a, kuma in sha Allahu zai samu abun da yake nema.
Tukun sukayi sallama anan cikin gida ba tare daya iya rakasu ko airport ba, sai Babban Yaya ne kawai suka tafi a tare.

Ganin da Al'amin yayi abun Yarima Asad na k'aruwa ne, ya sanya sa ce masa ya shirya yau tun adaren jiya su koma Masarautar Fuld'e a tare ya kara shaida mata abun da ke cikin ransa, ko Allah zai sa adace a wannan karan.

Ba tare ko da yayi masa musu ba ya amince, domin kuwa ko banza dama idanuwansa suna mugun mararin sake ganinta, yayinda kunnuwansa kuma suke buk'atar jin sautin zazzak'ar muryarta.

Zuwa yanzu ya yadda da cewar soyayya babu ruwanta da kud'i, mulki, gata ko kyawu, duk wanda ta riske sa bata yi masa da sauk'i muddin bata samu yadda take so ba.

Hak'ik'a ya d'auki darasin rayuwa a 'yan kwanakin nan da suka huce, ta yadda har yake jin da ace baya zata dawo, da babu abun da zai sanya sa yayi kuskuren furta cewar yafi k'arfin yaso sai dai asosa, da babu abun da zai sanya sa fad'in ba a haifi 'ya macen da zai so ta ba, kuma za'a tab'a haifar taba har abada, tamkar yadda yasha fad'i kowa kuma yasan da hakan.

Tini Ya gama shiryawa cikin black jieans tare da white t shirt, da sukayi bala'in yi masa kyau ajiki, yana zaune akan kujera cikin d'akin Al'amin yana jiran sa.
Sosai mamaki ya rufe Al'amin a lokacin da Yarima Asad ya shigo d'akin sa yana ce masa ya taso su tafi, saboda tunda suke a rayuwa Yarima Asad bai tab'a jiran sa ba in zasuyi tafiya sai dai shi ya jirasa, ta yadda har ak'arshe ma sai ya b'ata masa rai, amma wai sai gashi nan yau ya iso alokacin da ko wanka ma shi bai shigaba.
Hakanne yasa sa fad'awa bathroom da sauri ya bar Yarima Asad anan kan kujera, yana ta faman mita tare da sakin tsakin rashin shiryawar tasa da wuri.
Domin ko ji yaje tamkar ya zama tsuntsu ya gansa a cikin masarautar fuld'e.

Misalin k'arfe tara da rabi dai-dai Al'amin ya gama shiryawa cikin irin shigar da yarima Asad yayi, tukun suka had'u suka fuce daga cikin d'akin.

Yau acikinn motar Al'amin suka tafi, sai dai kuma Yarima Asad ne yake tuk'in, saboda a ganinsa idan ya barwa Al'amin yayi to baza su isa da wuri ba, wato ba sauri zaiyi ba tamkar yadda yake so.


A b'angaren Billy kuwa, sosai ta kwantar da hankalinta ta dena har kiran wayar Yarima Asad, ba dan komai ba kuma tayi hakan sai dan birthday d'in sa da taga ya kusa zagayowa, hakan yasa ta k'udirtwa ranta cewar a ranar zata masa abun da zai janyo hankalinsa gareta acikin bainar jama'a.
Shi yasa ma gaba d'aya ta hak'ura da kiran wayar sa, kana kuma ta dena zuwa Asadullah Palace, tayi zamanta a gida kullum tana cikin shiri tare da lissafin kwanakin da suka rage ranar tazo, wato bayan sallah da sati biyu ranar zata kama.


K'arfe d'aya dai-dai tayiwa su Yarima Asad a bakin get d'in Masarautar Fuld'e.
Ba tare da b'ata lokaci ba Al'amin ya janyo wayar sa ya kira Habu, yana mai sanar masa da isowar tasu, kasancewar tun jiya dama ya riga da ya sanar da shi zuwan nasu.
Yayinda Yarima Asad kuma yaji gaba d'aya yanayin sa ya sauya, zumud'in isowarsu da yakeyi duk ya gudu, sai wata irin fargaba da tarin tsoron rashin sanin kalar tarbar da zata yi masa yau ne, sukayiwa zuciyarsa dirar mikiya, ta yadda har ya fara daya sanin zuwan nasa.
A lokacin daya hango tawowar Habu kuwa da

Please Login or Register in order to submit comment