Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma kuma bincike ya nuna musu hurin da muka gudu, to kasani ba zasu tab'a zargin Iyace ta baka labarinka ba, domin ko Baba da bakinsa ya bani labarin.
Dan haka ni d'in zasu d'orawa laifin ba iya ba.
Nice zasuce na sanar da kai har muka tafi."

Ta k'arasa maganar cikin sanyi, tana mai k'ara damk'ar tafin hannunta a cikin nasa.

Da sauri Bir ya lumshe idanuwansa, yana mai sauke k'ak'k'arfar ajiyar zuciya.
Sabo da nutsuwar da yaji ta d'an saukar masa ta sanadin bayanan ta.
Amma sai dai kuma yana jin ko a yanzu ba zai iya tafiya ya bar Iyaba ba tare da tasan da tafiyar tasa ba.
Sabo da ko da ace ba zasuyi mata komai d'in ba, to ba zai so ace hankalinta ya tashi ba.

A hankali ya bud'e idanuwan nasa akan fuskarta.
Kana ya fesar da iska daga cikin bakinsa, yana mai bud'e baki cikin sanyi yace.

"Tabbas na gamsu da duka bayananki, amma kafun nan kuma tambayar da zan miki itace.
Ta yaya kike ganin guduwar mu zata yiwu ba tare da wani ya ganmu ba, bayan kuma kin san irin tsaron da ake baki, da kuma yadda gaba d'aya Bak'ar Masarauta take a zagaye da dakaru?"
Ya fad'a yana mai kallonta.

Hakan da taji ne ya sanyata lumshe idanuwanta.
Kana ta sake bud'e su tana mai d'an girgiza kai.
Tukun daga bisani ta saki tafukan hannayensa da suke a cikin nata, sannan ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Bacci bai d'auke ni a daren jiya ba, har sai da na tabbatar da nagama shirya duk yadda zamuyi mu bar cikin Bak'ar Masarauta ba tare da wani ya ganmu ba."

Ta k'arasa furucin tana mai kallonsa.
Hakan da Bir yaji ne ya sanyasa saurin matsowa kusa da ita, yana mai fad'in.

"Ta wace hanya ce kenan?"

Bud'e d'an k'aramin bakinta tayi tana mai zuk'ar iska, tukun ta fesar da ita.
Kana ta daga lab'b'anta tana mai fad'in.

"Kamar yadda kasani, aduk shekara ana bikin samun yanci acikin Bak'ar Masarauta.
Shi kuma wannan bikin aduk lokacin da ake yinsa, kana zamtowa mutum na dabanne a cikin sauran mutanen.
Ana ware maka mazauni, sannan ayi maka kwalliya wacce ta bambanta data sauran jama'ar.
Kana kuma a k'arshe Boka mai wutar kasko ya zauna a gefen ka aci abinci ayi kid'a ayi rawa."

Tayi shiru tana mai sake fesar da numfashi.
Yayinda shi kuma Bir yake aikin jinjina mata kai, alamun tabbatarwar hakan.
Tukun daga bisani ta d'ora da fad'in.

"Shin kasan ko meye dalilin daya sanya ake wannan bikin aduk shekara?
Kana kuma ake bambanta ka da sauran Bayi?
To anayinsa ne aduk ranar haihuwarka idan ta zagayo, wato ranar da Bak'ar Masarauta tasamu yanci, ta tserata daga halaka, bayan anfutar da tsammanin hakan ta sanadinka.
Wanda hakan ya sanya ake wareka, sabo da kai d'in ne silar komai.
Sannan kuma aka yiwa bikin lak'abi da bikin samuwar yanci.
Shima kuma wannan tarihin duk Babana ne yasanar dani shi.
To zamuyi amfani da wannan ranar, da 'yan kwanaki k'alilan suka rage tazo wurin guduwarmu.
Ma'ana dai zamu gudu a daren ranar, kasancewar a ranar ne za'a bud'e kowace k'ofa da take acikin Bak'ar Masarauta.
Sabo da zuwan bak'i, sannan kuma ko wane Hadimi da Hadima tare da Dakaru da Bayi duk ayyuka zasuyi musu yawa.
Hankula zasu karkasu a wurare daban-daban duk ta silar shirin da kowa yakewa zuwan rana.
Kai kuma za'a wareka a haneka da duk wani aiki da Bayi sukeyi a daren ranar kamar yadda akace anayi.
To a wannan lokacinne ni kuma zan futo in sameka a wurin da zamu shirya had'uwar mu.
Tukun Shairama ta taimake mu ta hanyar sarar Dakarun da suke akan hanyar da zamu huce ta ita gudun tonuwar asiri, kafun kuma lokacin dama mun riga da mun gama shirya kayan mu.
Sannan kuma mun kaisu mun adana su.
Sannan kuma zakayi shigace irin shigar da Yaya ya keyi aranar.
Wato dai ba zaka tafi da wannan shigar ba.
Zan kawo maka kayan Yaya kasanya, ta yadda koda munje shiga jirgi baza'a taremu ba.
Kana abu na k'arshe kuma shine, zamuyi tafiyarne ta cikin ruwa.
Sabo da tinanin su bai zai fara zuwa nan ba, idan kuma yazo, to zai zamto lokacin da zasu farga mu kuma mun riga da muncimma gaci.
Sab'anin jirgin sama da idan mukace zamubi tashi asirin mu zai iya tonuwa, saboda yawan ma'aikatan da suke a filin jirgi, da kuma cike-ciken da za'ayi kafun a tafin."

Ta k'arasa maganar tana mai fesar da numfashi, tare da rumise idanuwanta, sabo da yadda har yanzu take jin wani b'angare na zuciyarta na gargad'inta da aikata hakan.
Shi kuwa Bir tunda ta fara bayanin baice komai ba, sai idanu kawai daya zuba mata yana mai jinjina girman basirarta a cikin ransa.
Hak'ik'a shi kansa ya san wannan hanyar ita d'ince kawai zasubi su gudu ba tare da an lura dasu ba.
Kuma shima ya aminta da bayananta d'ari bisa d'ari.
Sai dai kuma abun da bai saniba har yanzu shine, wurin da zasuje idan sun sauka a Ka'sar Hausa.

Hakanne ya sanyasa bud'e baki cikin sanyi yana mai fad'in.

"Amma kuma idan mun sauka daganan sai muyi ina kuma?
Domin ko sanin kanki ne iya sunan k'asar kawai muka sani.
Bamu san sunan jahar da suke acikin taba, ballantana har muce can mukayin.
Sannan kuma babu ko sunan mutum d'aya da muka sani acikin su, bare kuma muce zamuyi cigiya Gimbiya."

Ya k'arasa maganar da lumshe idanuwansa.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir hakan da tajine ya sanyata sake d'an ja da baya daga kusa da shi.
Tukun ta bud'e baki tana.mai fad'in.

"Zamu tafi da dukiya ba kad'an ba.
Zamu tafi da akwatin kud'i tare dana gwala-gwalai, dan haka karkatab'a tinanin idan munje zamu rasa wurin zama, ko kuma rayuwarmu zata shiga k'unci ko da bamu had'u da kowa ba kuwa.
Sannan kuma batun sanin sunan jaha tabbas hakane kayi gaskiya, bamu da wani abu da muka sani akansu bayan sunan k'asa.
Sai dai kuma jikina na bani cewar zama a k'asar ma kawai zai sanyaka cikin farinciki fiye da wanda kakeyi a wannan k'untataccen wurin.
Sannan kuma ko badad'e ko bajima wataran idan muka saba da jama'a, sai kaga mun had'u da wanda yasan su harma kun sadu.
Ni dai fatana kawai murayu a tare har abada ko a inane ma Jarumi."

"To Iyata fa, idan na tafi shikenan na gama ganinta har abada?"

Bir ya sake fad'e yana kallonta.
Yayinda ita kuma hakan da tajin ya sanyata d'an d'aure fuskarta.
Kana ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Idan da rabo wataran zamu waiwayosu, har mu zauna akan shimfid'a d'aya, alokacin kuma mun riga da muntara zuri'a tare, kaga babu yadda za'ayi damu.
Idan kuma har binciken Boka mai wutar kasko ya tabbata, shikenan mun rasa ahalinmu."

Ta k'arasa maganar cikin wani irin kuka mai ban tausayi daya kufce mata lokaci d'aya.
Wanda hakan da Bir ya ganine ya sanya nasa hawayen daya samu ya tsayar dasu suka sake b'allewa da tsananin gudu.
Sabo da yadda yake hango rayuwarsa a wani wurin daban ba tare da Iyar saba.
Kafin daga bisani kuma ya d'aga k'afafunsa yana mai matsawa kusa da ita.
Tukun a hankali ya d'ago tafukan hannayensa yana mai dafo k'eyarta dasu.
Kana shima ya durk'uso da kansa yana mai d'ora goshinsa akan goshinta.
Tukun suka cigaba da zubar da hawaye, idanuwansu sark'e acikin na juna.
Yayinda ko wanne a cikinsu yake sake jin tabbacin bazai iya rayuwa ba muddin babu d'aya.

Ahankali Bir ya bud'e bakinsa cikin muryar kuka, da sautinta ya futo acan k'asa yana mai fad'in.

"Ki dena kuka Gimbiyata, kukanki na k'ona mun rai kinji."

Girgiza masa kai itama tayi, tana mai sake dafa k'irjinsa da hannuwanta.
Kana itama ta bud'e baki tace.

"Kaima kadena kuka Jarumina, ganin hawayenka yana sani jin tamkar zuciyata zata tarwatse."

"Ni ba kuka nake ba Gimbiyata, kece dai kike kuka."

Ya fad'a wasu sabbabin hawayen na sake tsinkewa daga cikin idanuwansa, kuma ba komai bane yake sake sanyasa kukan, sai yadda yake hangen ranar da zai tafi yabar Iyarsa.

"Ka barni nayi kuka ko zuciyata tayi sanyi Jarumina, kaima nasan kana yinsa ne dan kaji dad'i a ranka."

Ta k'arasa maganar tana mai lumshe idanuwanta.
Hakan da Bir yaji ne, ya kuma ji gaba d'aya shima hawayensa sunk'i tsayawa ne, ya sanyasa had'e bakinsu wuri d'aya da sauri.
Kana ya fara aika mata sak'on sa cikin wani irin salo na daban, ba wanda taji ba a jiya.

Da sauri kuwa suka lumshe idanuwansu, suna masu sakin wasu irin k'arfafan ajiyar zuciya a tare.

Ya d'auki tsayin mintuna shida yana abu d'aya.
Bashi ya iya zame bakinsa daga cikin nata ba har sai da yaga ya samu nasarar tsayar da hawayensu su duka biyun.
Tukun ahankali ya d'ago tsaye, yana mai sakar mata kyakkyawan murmushinsa.
Kafin daga bisani kuma ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Ni yanzu zan wuce na koma b'angarenmu, kema ina son kitafi kiyi bacci.
Sannan kuma kici abinci, inyaso idan mun had'u da yamma sai na rakaki har can, alokacin babu masu wucewa gari yayi duhu, ballantana wani ya ganmu yakai rahoto."

Jinjina kai tayi tana mai sakar masa murmushin itama.
Kana ta juya ta tafi jiki asanyaye.

Hakan da Bir ya ganine ya sanyasa juyawa shima ya doshi hanyar da zata kaisu b'angarensu.

Gaba d'ayansu suna komawa kowanne ya kwanta, zuciyoyinsu cike da tinane-tinane.
Kafin daga bisani kuma bacci yayi awon gaba dasu, kasancewar jiya duk kusan basuyi bacci ba.


Misalin k'arfe tara da rabi na dare Iya ta shigo cikin d'akinsu Bir, da niyyar ta duba taga ko lafiya yake.
Sabo da rabonta data sasa acikin idanuwanta tun safe daya futa, bayan ya gama karyawa, dan kuwa ko abincin rana baizo ya tambayeta ba.

Zaune ta hangesa rakub'e a wuri d'aya ya had'a kai da gwiwa shi kad'ai acikin d'akin.

Hakanne ya sanyata k'arasawa wurin da yake hankalinta a tsantsar tashe, tana mai fad'in.

"Na shiga ukku na lace Jarumi!
Jarumina me yafarune?"

Ta k'arasa maganar tana mai fara k'ok'arin dago kansa daga jikin gwiwoyinsa hankalinta a bala'in tashe.
Jin hakan da Bir yayine ya sanya sa jin wani irin kuka ya kufcemasa da matuk'ar k'arfi.

"Nashiga ukku nalalce me ya sameka? Mai akayi maka Jarumina?"

Iya ta fad'a a tsantsar firgice, bayan ta zauna gefensa tare da janyosa cikin jikinta kuka na kufce mata.

Hakan da Bir yajine ya sanya jikinsa d'aukar kyarma, kafun daga bisani kuma ya d'ago kansa yana mai watsa rinannun idanuwansa a cikin nata.
Kana ya bud'e baki cikin matsanancin kuka yace.

"Kiyi hak'uri Iyata, kiyi hak'uri kiyafe mun Iyata, ina mugun sonki, itama kuma ina jin tamkar zuciyata zatayi bindiga idan na barta."

Yayi kalaman da suka sake hargitsa Iya gaba d'ayanta.
Kana kuma tagaza gane wurin da suka dosa gaba d'ayan su.

Jin da tayi ya ambaci itama bazai iya barinta bane, yasata fahimtar cewar damuwarsa ta danganci Gimbiya ne.
Hakan yasa ta mik'ewa tsaye cikin sauri.
Kana shima ta kamo hannunsa tana mai fad'in.

"Yi maza maza tashi mutafi d'akina muyi maganar acan Jarumi."

Ba tare daya musa matan ba ya tashi.
Tukun tayi gaba shima ya bita har lokacin tana rik'e da hannunsa suka fuce daga cikin d'akin.

Suna shiga cikin d'akin nata ta gark'ame k'ofar d'akin.
Tukun ta k'arasa gaban Bir cikin sauri, tana mai zama tamkar yadda shima d'in ya zauna.
Kana daga bisani ta dafosa tana mai fad'in.

"Kayi shiru ka natsu kayi mun duk bayanin abunda yake faruwa Jarumi."

"Tace mugudu mubar Bak'ar Masarauta Iyata.
Tace na tafi na barki, ni kuma na amsa mata da zanbita Iyata."

Ya sake fad'e a tsantsar rud'e yana mai damk'ar hannun Iya tare da girgiza mata kansa.
Yayin da idanuwansa kuma suke cigaba da ambaliyar ruwan hawaye.
Jin hakan da Iya tayine ya sanya hankalinta ya k'ara bala'in tashi.
Kafin daga bisani kuma itama ta bud'e bakinta ruwan hawaye na zuba daga cikin idanuwanta tace.

"Har yanzu bangane ba Bir, kayi shiru kanutsu kayi mun bayani yadda zan gane kaji Jarumina."

Hakan da Bir yaji ne ya sanya sa d'an tsagaitawa da kukan da yaje yi da k'yar.
Kana ya fara bawa Iya labarin duk yadda sukayi da Gimbiya tundaga farko har k'arshe, bai b'oye mata komai ba.
Cak ya tsaya baki sake tamkar wani dole yana mai kallon iya, sabo da yadda yaga ta saki wani irin mirmushin da har hak'waranta suka bayyana, tana mai kallonsa amai-makon yaga firgici da rud'u a tare da ita.

Lura da hakan da Iya tayine ya sanya ta bud'e bakinta tana mai fad'in.

"Ka zata zanyi kuka, ko kuma nace maka ba zaka bita bane ba ko, shiyasa har murmushina ya baka mamaki ko Jarumina?"

Ta fad'a tana mai k'ara sakin wani murmushin.
Yayinda shikuma Bir har yanzu ya kasa ce mata komai, sai kallonta kawai daya cigaba dayi cikin tsantsar mamaki.

Ita kuwa Iya cikin murmushin da takeyi ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Ta yaya zanyi kuka, bayan kuma rayuwarka ce zata inganta idan katafi Jarumina.
Taya kake tinanin Iya zata hanaka tafiya, bayan kuma 'yancin rayuwa zaka samu acan wurin da zakaje.
Hak'ik'a bana fargaba ko tsoron abun da ni zai sameni, muddin taka rayuwar zata inganta Jarumina.
Tun a waccan shud'ad'd'iyar ranar dana rungumeka a k'irjina, naji tausayin mahaifiyarka da kai kanka ya lullub'eni, ta yadda har naji inama ace akwai ranar da zaku sake gamuwa da juna.
To kaga kuwa akan me yanzu zan hanaka tafiya wurin da nake tsammanin zaku iya saduwa da juna.
Hak'ik'a koda baka had'u da ahalinka ba, zamanka acan d'in yafi anan.
Domin kuwa nan d'in babu wani cigaba da zaka samu a rayuwa, asalima sai dai ka k'are acikin bauta, tamkar yadda ka fara.
A dake ka ad'ora maka kaya tamkar jaki.
Aduk ranar da kayi aure ka tara 'ya'ya suma su taso cikin irin rayuwar daka taso.
Acan kuma zakayi rayuwa ce mai 'yanci, ka zauna cikin aminci da salama ba tare da bautar waniba.
Dan haka na amince maka katafi da yahuna Jarumi, kuma zan maka addu'a.
Ko da ni sun kasheni, babu wani abu tunda ai na mori duniyar dai.
Kasani kuma bazan tab'a dena alfahari dakaiba a rayuwa Jarumi."

Ta k'arasa maganar hawaye na b'alle mata alokacin da tsananin gudu.

Da matuk'ar sauri shima Bir ya rungumeta k'am-k'am ajikin sa yana mai k'ara fashewa da kuka.
Kana ya bud'e baki cikin tsananin kuk, yana mai fad'in.

"Bazaki mutuba Iyata, koda bana nan kona tafi babu abun da zasuyi miki, tunda har yayi gangancin bawa d'iyarsa labarin."

Rungumesa itama Iya tayi tana mai sakin kuka ba tare da tace komai ba.

Sun jima sosai a haka kafun daga bisani kuma Iya ta b'anb'are Bir a jikinta dak'yar.
Kana ta tashi taje ta bud'e k'ofar d'akin.
Tukun ta huce wurin da ta ajiye masa abincinsa a cikin wata silba ta d'auko ta ajiye sa a gabansa, tana mai fad'in.

"Gyara zamanka Jarumina, yau ni da kaina zan baka abinci."

Hakan kuwa akayi.
Ita tai-ta basa abincin yana karb'a zuciyarsu duk ba dad'i.

Sai dai kuma bai wani iya ci da yawa ba ya janye kansa gefe yana mai fad'a mata ya k'oshi.
Babu yadda ta iya haka ta hak'ura tabarsa, sabo da ya nuna ba zai ka'raba.
Tukun ta basa ruwa yasha, kana ta tashi ta rakasa har bakin k'ofar d'akin su alokacin tini dare ya farayi sosai.

*BAYAN WASU 'YAN KWANAKI.*

Gaba d'aya daga Bir har Gimbiya Tasmir duk sunyi sanyi, sakamakon yadda tafiyar su take k'ara kusantowa ako da yaushe.
Yayinda jama'ar bak'ar masarauta kuma suka fara shirye-shiryen bikin samuwar 'yanci tuni, domin kuwa ba k'aramun shagali suke sha a bikin ba.
Farincikin da suke a ranar ne ma ya sanya ko kad'an ba a dukan bayi a ranar, ba kamar sauran bukukuwan da sukeyi ba da Bayi ke shan bak'ar azaba a wurinsu.

Har yau babu ranar banza da Gimbiya da Bir basa had'uwa sau ukku a rana.
Wato safe, rana tare da kuma yamma.
Sai dai kuma har yau suna kaffa-kaffa, basu tab'a barin wani ya gansuba, balle har a zargi wani abun a b'ata musu bajat d'insu.
Yayinda shak'uwarsu kuma take tsananin k'aruwa a kowace rana.


*K'ASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.*

Yau take ranar idin sallah Babba.
Wanda hakan kuma ya sanya duk musulman duniya suke a cikin tsantsar farinciki, annashuwa tare da walwala da zuwan wannan tsadaddar ranar.

Duk inda ka gifta raguna da shanu tare da rak'uma harma da akuyoyine ake ta kayarwa ana yankawa, kasancewar an riga da andawo daga massallacin idi.
Yayinda yara kuma keta aikin hucewa da kulolon abinci kala-kala suna rabo.

Anan cikin Masarautar Wasai ma hakan take, kowa ka kalla fuskarsa d'auke take da annuri da annasuwa.
Yayinda acan kwatar da take acikin masarautar kuma Babban yaya yake ta aikin yanka duk shanun da aka kayar.
Gaba d'ayansa ya had'a uban gumi ta ko ina, domin ko ba k'aramar gajiya yayi ba, gashi kuma babu wanda zai yin sai shi d'in.

Acan b'angaren Yarima Asad kuwa, zaune yake ya buga uban tagumi da hannu bibbiyu akan kujera.
Yayinda Al'amin kuma yake zaune a kusa da shi, shima ya buga tagumin yana mai kallonsa tare da jin tausayinsa.
Domin kuwa har yau ya kasa hak'ura da Gimbiya Haddiyal.

Bayan wancan zuwan nasu da sukayi wanda har suka had'u da Jauron Yamma sun sake komawa kuma.
Sai dai kuma a shid'in kuma ko had'uwa ma basuyi ba, duk da yadda Habu yayta had'ata da Allah akan taje wurin nasu kuwa k'i tayi.
Hakanne yasa tunda suka dawo Yarima Asad ya k'ara canzawa. Gaba d'aya ya dena ko futa waje, sai yau daya shirya sukaje massalacin idi shima na nan cikin masarautar ne.

Sanye yake da suite a jikinsa blue color da tayi tsananin yimasa kyau.
Sosai yayi wata irin mahaukaciyar rama, yadda kasan wanda yayi jinyar shekara da shekaru.
Sai dai kuma ko kad'an ramar bata sanyasa yayi muni ba.
Saima kyawu daya k'ara, sabo da karan hancinsa daya k'ara futowa, da kuma yadda 'yan madai-daitan idanuwansa suka k'ara girma suma.

Yayinda Al'amin kuma yake sanye da wata dakakkiyar bluen shadda, tare da hula da sukayi matuk'ar yimasa kyau shima.

Gaba d'ayansa shima bashi da wata walwala, domin kuwa ya d'auki damuwar abokin nasa ya d'orata akansa.

Sosai Babban yaya yake k'ok'ari wurin ganin ya kwantarwa da k'anin nasa hankali, amma gaba d'aya abun abanza.
Babu wani abu da yake fata face Haddiyal taso sa a rayuwa.

A yau Mai Martaba da kuma Gimbiya Fulani zasu dawo, hakan yasa ake ta gyara musu b'angarensu ana jiran isowar su.

A b'angaren Billy kuwa, gaba d'aya ta dena kiran Yarima Asad, ta mayar da hankalinta duk akan shirye-shiryen birthday d'in sa.
Domin kuwa sosai ta aminta da shawarar da zuciyarta tabata.
Hakan yasanya gaba d'aya ita ko kad'an batayi wani abun sallah ba, domin kuwa ko k'unshi da kisto ma batayi ba, sabo da tace bazai futaba kafun zuwan ranar.
Sitirar da zata sanya a ranar kuwa tini ta kashe dukiya aka turo mata su masu tsananin kyau da tsada, kasancewar duka yau kwana shida ya rage ranar birthday d'in tazo.

*BABBAN ZAURE LOCUS.*

Gaba d'aya al'ummar gidansu Sheikh Ahmad yau cike suke da farinciki da annashuwa kasancewar ta sallah suma.

Gaba d'ayansu zaune suke a cikin falonsu suna cin tuwon shinkakafa miyar had'ad'd'iyar taushen da take d'auke da nama zuk'u-zuk'u a cikinta.

Baki d'auke da sallama Sheikh Ahmad ya shigo cikin falon hannuwan rigar shaddar jikinsa a nad'e, kasancewar gama yanka ragunan su kenan da yayi ya tawo nan d'in bayan ya wanke hannuwansa.

Yayinda babban d'ansa kuma yake biye dashi abaya, da irin shigarsa sak harma da babar riga ajikin sa.

"Kai amma Ummina da Abbana yau kun had'u kunsha kyau gaskiya, fatan kunyi sallah lafiya."

Ya fad'a cikin raha yana mai k'arasowa kusa da Ummi da take zaune akan kujera taci uban ado, cikin shigar doguwar rigar shaddar da tayi tsananin yimata kyau.

Sosai ta kwantar da hankalinta a 'yan kwanakin nan, gaba d'aya ta dena yawan damuwar da takeyi, domin kuwa ita da kantama tayi miyar sallahr tasu, tuwone kawai 'yan aikin su sukayi.
A yanzu ta dena ganin saurayin da take mafarkinsa aduk daren duniya a cikin damuwa.
Wanda hakan shine ya sanya hankalinta kuma ya kwanta sosai.

Cikin masifa Kaka ta bud'e baki, saboda jin abun da Sheikh Ahmad ya fad'a, tana mai fad'in.

"To seme dan bakace nayi kyau ba, aikin banza aikin hofi sai kace shi kyawun garesa."

Ta k'arasa maganar tana mai buga masa harara.

"Allah ya baki hak'uri, ni yau ba ranar fad'a bace a wurina, dan haka bama zan kulaki ba."

Cewar Sheikh Ahmad yana mai d'an tabe baki.
Ita kuwa Kaka k'wafa ta buga tana mai cigaba da cin tuwonta.


*BAYAN KWANA BIYAR.*

Sosai hankalin Fulani ya sake tashi da ganin yadda Yarima Asad ya mayar da kansa.
Hakan ya sanya akullum take zama a kusa dashi tai ta kwantar masa da hankali, tana basa k'arfin gwiwa akan zataso sa.
Yayinda shikuma Mal Martaba ya fara k'ok'arin ganin ya tura masarautar fuld'e domin a tambayo musu auren yarinyar.

Gobe ce ta kasance ranar birthday d'in Yarima Asad.
Hakanne yasa gaba d'aya jama'ar gidan suketa shiryawa ranar, domin kuwa har anko sai da 'yammata suka futar, wanda zasu sanya, kasancewar sun riga da sun saba da yin shagali aduk zagayowar ranar irin haka dama.

Ita kuwa Fa'iza tini itama ta tanadi abun da zatayi wanda zai janyo hankalin Yarima Asad gareta a gobe.
Kai bama ita kad'ai ba, harma da sauran 'yammatan da suke sansa na cikin masarauta, sabo da batun ya futar da mata da akayi masa da yaje kunnensu, shi ya sanya gaba d'aya suka d'aura d'amarar janyo hankalinsa garesu.

Yayinda shi kuma ubangayyar da ake abun dan shi, gaba d'aya ya manta da zuwan ranar, domin kuwa ba itace a gabansa ba yanzu.

Shi kuwa Al'amin yana sane da goben, shiyasa ma tun safe yau ya fuce ya tafi Asadullah Palace domin a fara shirya wuri.
Yayinda kuma yana zuwa ya tadda Billy itama a wurin tsaye cikin masu docoration, taci uban kitso da k'unshi tana nuna yadda za'ayi.
Gaisawa kawai sukayi da ita, tukun suka cigaba da kula da yadda ake aikin, ba tare da yayi mata maganar Asad ba, itama kuma batayi masan ba.


*K'ASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAK'AR MASARAUTA.*

Sosai shirye-shiryen bikin zagayowar ranar samuwar 'yanci ya kankama a cikin Bak'ar Masarauta, kasancewar kuma gobene ranar, shiyasa ko ina ka gifta kake ganin Bayi d'auke da abubuwa iri-iri ahannunsu suna shirye shirye.

Yayinda wasu kuma suke acan filin biki suna ta faman sharesa tare da jera kujeru.

A b'angaren Bir kuwa, kwance yake akan shimfid'arsa lumshe da idanuwansa.
Duk wanda zai gansa ahaka zaiyi tinanin bacci yake yi, amma kuma a zahiri idanunsa biyu, kawai ya rufesu ne yana tinanin yadda daren yau zai kasance musu ne.
Daren da zai rabu da iyarsa rabuwar da ba lalaine su sake saduwa da itaba har abada.

Wasu irin zafafan hawayene yaji sin silalo masa daga cikin idanuwansa suna bin gefen kunnensa.
Kafin daga bisani kuma ya kai tafukan hannayensa zuwa kan fuskar tasa yana mai share hawayen, tare da mik'ewa zaune da matuk'ar sauri, yana mai juya bayansa, sabo da m...............✍



*Tabbas a kwai alamun zamu kai har bayan sallah bamu kammalasa ba saboda k'arancin comment da sharhinku. 😠😠😠*


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*17*



Motsin tawowar mutum da yaji zuwa cikin d'akin.
Ita kuwa Iya da tashigo danta dubasa a hankali ta mayar da k'ofar ta rufe.
Kana ta fara takowa tana mai yowa inda yake jikinta a tsantsar sanyaye.
Zube gwiwoyinta tayi a k'asa daga bayan Bir, tukun ta d'ago tafukan hannayenta tana mai dafa kafad'unsa dasu.
Kana ta bud'e baki cikin sanyi tana mai fad'in.

"Jarumina ba dai kuka kakeba ko?"

Tayi maganar itama cikin wata irin murya, wadda duk wanda yajita zai fahimci itama tana kusa da sakin kukan daurewa ne kawai takeyi.
Kana ba tare data tsaya jin abunda zaice ba ta d'ora da fad'in.

"To me zai saka ma kayi kuka in banda abuna, bayan na nariga dana sani wata sabuwar duniya zaka tafi, wacce take cike da 'yanci, abubuwan nishad'i, walwala tare da ban sha'awa.
Tabbas na sani ko da Jarumina yana kuka ba zai yisa a irin wannan ranar ba."

Da matuk'ar sauri Bir da idanuwansa suke zubar hawaye ya juyo gareta, sabo da jin abun da take fad'e da yayi yana mai rungumeta a jikinsa.

A hankali Iya ta d'ago tafin hannunta tana mai kifesa akan lallausar sumar kansa.
Kana ta bud'e baki cikin rawar murya, hawaye na b'allewa daga cikin idanuwanta tace.

"Banaso kayi kuka a wannan ranar Jarumina, domin ko ranar farincikice a wurinka bata kuka ba."

"Ba ina kuka bane dan zanbar Bak'ar masarauta Iyata, ina kukane sabo da tinawar da nake na yau d'in zan tafi na barki, yau d'in zanyi nisa dake, nisa mai mugun zurfi, kinga kuwa dolene nayi kuka iyata.
Hak'ik'a ina jin tamkar na fasa tafiyar nan Iya, sabo da bana tinanin rayuwa zata yuwu a wurin da babu ke akusa...

"Ya isa haka Jarumi, banason na k'arajin kayi furucin fasa tafiyar nan, domin kuwa tafiyarka tafiye mun zamanka anan d'in

Please Login or Register in order to submit comment