Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma har wani ya k'ara bud'e baki yayi magana acikin ku da zummar ya hanani, to kai Ishak'u kasani ayau a kuma yanzu a wurinnan zan tsine maka, sanann kuma ni in futa na barmaka gidan d'anka, tunda ka nuna mun ban isaba."

Ta fad'a a wani irin zafafe babu alamun wasa ko barazana acikin maganarta, wanda hakan kuma yayi bala'in tayarwa da duk wani mutumi da yake acikin falon hankali.
Domin kuwa hatta su Sheikh Ahmad da suke iya fad'a mata magana yanzu shiru sukayi, sabo da bazasu so ganin Mahaifinsu acikin wani hali ba.
Yayinda ita kuma Gimbiya Tasmir jikinta ya d'auki wata irin kyarma.
Hankalinta idan yayi dubu gaba d'aya sai da ya tashi, nadamar biyo Bir da tayi suka tawo ta fara lullub'eta, tinanin wurin da zata tafi tayi rayuwa ba tare da Bir da kuma ahalinta ba yay mata saukar ungulu a zuciya, wanda hakan ya sanya ta saki wani irin gigitaccen kuka, tana mai durk'ushewa a k'asa tare da fara girgizawa Kaka kai cikin tsantsar firgici.
So take ta bud'e baki ta bata hak'uri, amma gaba d'aya taji ta kasa yin hakan.

Take kuwa tausayinta ya sanya gaba d'aya jama'ar da suke acikin falon hatta da Sheikh Ahmad da kuma Ishak' zubar da k'walla.

Shi kuwa Bir da k'arfi ya rumtse idanuwansa, sabo da bazai iya jurar ganin masoyiyar tasa ba acikin yanayin da take a ciki.

Yayinda ita kuma Kaka tayi wurin da Gimbiya take tana mai gyara d'aurin zaninta, tare da fad'in.

"Wallahi tallahi kisani ko kukan jini zakiyi mayun idanuwanki su zubo k'asa saboda kallona bazan tab'a jin tausayinki ba, sabo da ni nan da kika ganni bana jin tausayin mara tausayi, bani da imani akan wa'yan da basu da imani, bazan tab'a bari na had'a jini da mugun iri ba zuri'ata ta gurb'ta.
Dan haka mik'e koda idan kika futa daga gidan nan 'yan mafiya zasu kamaki ko namun daji su cinyeki sai kin futa ba zaki kwanar mun ba."

Ta k'arsa maganar tana mai sakar mata dundu agadon baya, wanda hakan ya sanya Gimbiya ta rumtse idanuwanta.
Tukun ta damk'i hannunta tana mai fad'in.

"Tashi kafura d'iyar kafurai wa'yan da basu san mece sallah ba a ahalinsu, gashinan har warin kafurci kike, bak'ar arniya mik'e na rakaki har k'ofar gida, sannan na rufo k'ofata, dan wallahi bazaki rayu acikin muba, dan koda na barki ma zan iya zaune ki wataran ki mutu kijaza mun bala'i, gidan bimasin na talabijin d'in nan (BBC) da suke yamad'id'i da mutane su dingayi dani suna nayi kisan rai, dan kuwa aduk duniya banga munafukai ba irin wa'yan nan mutanen, a kullum sai naji sun jawo gulmar wani."

Ta k'arasa maganar tana mai funcikar hannun Gimbiya Tasmir.

Da sauri gimbiya ta mik'e jikinta na tsantsar rawa, tukun Kaka ta fara janta tana gyara d'aurin zaninta da hannu d'aya.

Zumbur Bir ya mik'e tsaye yana mai funcike hannunsa daga cikin na Iyayensa jikinsa na tsantsar rawa, yayinda idanuwansa kuma suka kad'a sukai jajajir, sabo da yadda yaga tsohuwar na cin mutuncin Gimbiya an kuma rasa wanda zai hanata cikin duk mutanen wurin.

Da sauri yayi wurin da suke tamkar zai kifa a k'asa.
Yana k'arasawa wurin ya damk'i hannun Gimbiya d'aya yana mai janyota cikin jikinsa.

K'am-k'am kuwa ta rungumesa tana mai fashewa da wani irin gigitaccen kuka mai sosai zuciya.
Shi d'in ma kukan ya fashe da shi yana mai bud'e baki cikin matsanancin kuka yace.

"Tabbas bakuyi maraba da zuwan muba, sannan kuma bakuyi farinciki da dawowata gareku ba, dan haka zamu koma wurin da muka futo, domin kuwa bazan tab'a rayuwaba ba tare da itaba. Domin ta na baro wurin dana saba da shi, na baro Iyata da abokanai na. Saboda ni ta bar kowa da komai nata, ta yaddda matsayinta ta biyoni, sannan kuma ta dawo muku dani cikin rayuwarku, ta yadda ta rasa kowa nata ita, amma da irin wannan hallacin zaku saka mata.
To shikenan ku sani zamu tafi tare da ita kamar yadda mukazo a tare, kuma idan na tafi bazan sake wai-wayar kuba har abadan abada, sabo da bakuyi farinciki da zuwana ba..........." ✍






_Da damuwa Yau, nayi 2 pageS amma Page 22 ya goge, gashi ni kuma bazan iya sake wani ba gaskiya dan haka kuyi hakuri sai dai mu had'e a page 23 duk zaku gane ai._ 😩😩😩


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*22*



_*BARKA DA SALLAH GA DAUKACIN MUSULMIN DUNIYA, ALLAH UBANGIJI YASA MUNYI IBADA KARB'AB'B'A, YA KUMA NUNA MANA NA BA'DIN BA'DIN BA'DA'DA. πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€*_



Cikin tsananin firigici, rud'u, had'i da matsanancin tashin hankali Ummi ta mik'e tsaye tana mai girgizawa Bir kai, kafin daga bisani kuma tayi wurin da suke a tsaye da matuk'ar sauri, tana mai zuwa ta damk'i tsintsiyar hannunsa, bakinta na fad'in.

"A'a 'Dana karkace haka, ni nayi farinciki da zuwanka, kuma har abada bazan k'ara kuskuren barin na rasaka ba a karo na biyu, dan haka zan bika mutafi tare nima bazan zauna ba, saboda ina sonka kuma ina son Gimbiyarka."

Tayi maganar a wani irin rud'e, hawaye na b'allewa daga cikin idanuwanta itama, yayinda jikinta kuma yake wata irin rawa.

Shi kuwa Bir har lokacin rungume yake da Gimbiya Tasmir da tayi lamo a jikinsa tana mai sakin wani irin sassanyan kuka, yayinda shima idanuwansa ke zubar k'walla har lokacin.

Da sauri Kaka ma ta mik'e tsaye saboda jin abun da Bir yace, tana mai fad'in.

"A'a jikana, babu inda zaka k'ara tafiya kabarmu, wallahi ina sonka, kuma na amince ta zauna ita d'in ma har dai hakan zai sa ka zauna.
To ya zanyi tunda anfi k'arfina, dole ne na zauna da kafura a gida d'aya."

Ta k'arasa maganar tana mai matsar k'walla tare da face majina da gefen zaninta.

"To Alhamdulillah sai ku tawo ku zauna ko."
Cewar Abba cikin tsananin farinciki, yana mai d'auke tasa k'wallar da yatsu.

Da sauri Aunty Bilkisu mai bin Sheikh Ahmad ta taso tana mai yowa zuwa wurin da su Ummi suke a tsaye.

"To saketa ko d'an K'anina."
Ta fada a lokacin data k'arasa wurin da su Bir suke tana mai rik'o hannun Gimbiya Tasmir.

Jin hakan da Bir yayine ya sanyasa lumshe jik'ak'k'un idanuwansa, kana daga bisani kuma ya bud'e su akan fuskar Gimbiya, tukun ya janye hannunsa daga rik'on da yayi mata a hankali.
Hakan yasa Aunty bilkisu ta kamota suna masu tafiya zuwa wurin da sauran 'yan uwansu suke a zaune, tukun itama Ummi ta rik'o hannun Bir suna masu komawa kan kujerar da suka taso, wato dai ya zamto sunsa Bir a tsakiya ita da Abba.

Take kuwa falon ya sake kaurewa da hira cikin matsanancin farinciki, kowa bakinsa a washe ban da Kaka kad'ai da tacika tayi bam.

"Yawwa K'anwata taso muje na rakaki d'akinki ko."
Cewar Aunty Bilkisu tana mai mik'ewa tare da rik'o hannun Gimbiya Tasmir.
Yayinda Aunty Amina kuma mai bin Aunty Bilkisu ta tashi ta tafi kiching domin ta d'ora musu a abinci.

'Dakin da yake a jikin na Kaka wanda ya kasance nasu Iman, babbar 'yar Aunty Bilki idan sunzo kwana gidan shi suka shiga.
Madai-daicin d'aki ne da yake d'auke da had'ad'd'un kayan furnitures tare da komai na buk'ata a cikinsa.

Ba ita ta saki hannun Gimbiya ba har sai da ta zaunar da ita akan bed d'in da yake a cikin d'akin, tukun ta dafa kafad'ar ta tana mai fad'in.

"Wannan shine d'akinki halak malak, dan haka daga yanzu ina son kisa a ranki cewar baki da gida sama da wannan, mu kuma ki d'auke mu a matsayin 'yan uwanki na jini, Abba da Ummi kuma ki rik'e su a matsayin mahaifa. Idan har kina da wata damuwa ko neman shawara ki sameni ki sanar dani a ko yaushe, ni kuma na miki alk'awarin share miki kukanki muddin abun baifi k'arfina ba.
Kaka kuma kiyi hak'uri da abun da tayi miki, ina mai tabbatar miki da wataran zata soki, yanzu ma hada rikicin tsufa ya sanyata yin abun da tayi, kuma bama ke kad'ai ba hatta da mu kanmu bata barmu ba kullum cikin fad'a muke, dan haka ki manta da abun da tayi karki kuskura ki barsa a cikin ranki harya hanaki sukuni."

"Tom Momy nagode sosai."
Cewar Gimbiya tasmir tamkar yadda taji su Iman na kiranta da Momy a falo kanta durk'ushe a k'asa.

"Ba Momy zaki na ce mun ba, wannan sunan nasu Iman ne, dan haka ke ki kirani da Aunty saboda ya nake a wurinki."

"Tom Aunty nagode."

"Babu godiya a tsakanin mu k'anwata."
Cewar Aunty Bilkisu fuskarta d'auke da murmushi, tana mai sakin kafad'arta tayi hanyar bathroom d'in da yake a cikin d'akin.

Sosai Gimbiya Tasmir taji matar tayi matuk'ar birgeta tare da shiga ranta, ta yadda har taji kaso saba'in cikin d'ari na damuwarta ya yaye.

Baifi minti goma Aunty Bilkisu ta d'auka a cikin bayin ba sai gatanan ta futo tana yarfe hannuwanta da suke jik'e da ruwa, tukun ta bud'e baki a lokacin data k'araso wurin da Gimbiya take tana mai fad'in.

"Ga ruwa can na had'a miki ki tashi yanzu kije kiyi wanka, akwai komai na buk'ata a ciki, yanzu kuma ni zan futa idan naje falo zan turo miki Iman tazo ta shirya miki kaya."

"Tom." Gimbiya tace tana mai mik'ewa tsaye, yayinda ita kuma Aunty Bilki ta juya tana mai fucewa daga cikin d'akin.

Zaune ta samu su Iman a cikin falon suna kwasar hira, yayinda Ummi da Bir kuma suka tafi d'akin Auta dan ta had'a masa ruwan wanka, hakan yasa tace mata.

"Yawwa Iman tashi ki d'auki jakarnan ki kai mata, sannan kuma ki tayata shirya kayan."

Da tom Iman ta amsa mata tana mai mik'ewa taje ta d'auki jakar tare da kama hanyar d'akin.

Zaune tayi a bakin gado bayan ta a jiye jakar a k'asa tana jiran futowa Gimbiya.

Zamanta baifi da minti goma ba ta d'ago kanta daga kan wayar hannunta da take dannawa, tana mai juyawa zuwa b'arin bayi saboda motsin mutum da ta jiyo.

Gimbiya Tasmir ce ta futo d'aure da farin towel a k'ugunta, sai kuma wani d'an k'arami yafe a kanta tana mai tsane ruwan fuskarta da shi.
Hakanne ya sanya Iman ta sakar mata murmushi tana mai fad'in.
"Barka da futowa Aunty na."

"Yawwa barkanki."
Ta fada tana mai sakar mata murmushin itama.
Tukun Iman ta mik'e tsaye tana mai fad'in.

"Ga mirrow can akwai komai na buk'ata akai, ni kuma bara na shirya kayan nan a cikin wadrobe d'in."

Ta k'arasa maganar tana mai d'aukar jakar tayi wurin wadrobe d'in da ita.
Yayinda ita kuma Gimbiya Tasmir ta tafi zuwa gaban dressing mirrow d'in da yake d'auke da da mayuka tare da duk wani abun buk'ata a kansa.

Cikin k'ank'anin lokaci gaba d'aya Iman ta gama shiryawa Gimbiya kayan a ciki, tukun ta d'auko mata wata bluen doguwar riga mai adon duwatsu data gani a cikin kayan nata, tana mai yowa bakin gadon da ita.

K'arasowar ta yayi dai-dai da lokacin da Gimbiya Tasmir ma ta tawo wurin da niyyar amsar kayan da zata sanya.
Hakanne yasa ta mik'a mata na hannunta tana mai fad'in.

"Ga wayanda na zab'a miki Aunty nasan ba k'aramun kyau zasu miki ba."

Ta k'arasa maganar da sakin murmushi tana Mai mik'a mata kayan.
Itama Gimbiya Tasmir murmushi ta sakar mata tana mai sa hannu ta karb'a.

"Wow Masha Allah Aunty na kinga yadda kikai kyau kuwa, a gaskiya ke me kyauce."

Cewar Iman a lokacin da Gimbiya ta gama sanya kayan a jikinta.
Lokaci d'aya kuwa murmushi ya kwacewa Gimbiya Tasmir tana Mai fad'in.

"Ke ko, wallahi kin fiye zolaya da yawa."

"Yawwa Auntyna dama ina son na fad'a miki dan Allah kiyi hak'uri da abun da kaka tai miki, saboda dama ba mutunci tsohuwar nan ta cika ba, kuma babu wanda ta bari wallahi har nima kullum nazo Sai munyi, Amma mu muna sonki tamkar yadda muke son Auncle."
Cewar Iman tana Mai dafa kafad'ar Gimbiya.

"Bakomai wallahi 'yar uwa na fahimceta ai itama."

Gimbiya ta fad'a cikin far'a tana mai jin wata irin soyayyar Iman na lullub'eta tamkar dama sun saba.
Tukun Iman ta rik'e hannunta suna masu juyawa suka doshi hanyar waje a tare.

Zaune suka tarar da gaba d'aya mutanen gidan a tsakiyar falon kan capet. Yayinda manya manyan trayn abinci kuma suke a tsakiyarsu.

"Masha Allah k'anwar tamu ba dai kyauba, Allah ya nuna mana lokacin."
Cewar Aunty Maimunatu mai bin Aunty Bilkisu cikin far'a tana kallon Gimbiya tamkar yadda duka sauran jama'ar ma suke kallonta.

"Yawwa Gimbiyata tawo nan ki zauna a kusa da ni kinji ko."
Cewar Bir da yake sanye da wata 'yar ubansun bluen shadda sabuwa da sheikh Ahmad ya d'auko masa a jikinsa,yana zaune a gefen Ummi ya d'ora kansa a kafad'arta.

Da sauri duka jama'ar cikin falon suka kallesa suna masu sakar masa dariya, yayinda Ummi kuma ta lakaci hancinsa tana mai fad'in.
"To me budurwa a kusa da ni zata zauna ba kusa da kai ba."
Ta k'arasa maganar da ya futo Gimbiya zuwa gefenta.

"Mtswwwww!!!"

Kaka ta buga wani uban tsaki da ya janyo gaba d:aya hankalin mutanen wurin zuwa kanta, tana mai yatsina fuska.

"Kanki a keji wai mahaukaci ya fad'a rijiya."
Aunty Ruk'ayya ta fad'a tana mai watsawa Kaka harara.

"To futsararra, wallahi kika kuskura kikai mun rashin kunya yanzu sai nasa ubanki ya koraki gidan mijinki."
Kaka ta fad'a a masifance tana mai jifanta da harara itama.

Banza gaba d'aya kowa yayi mata suka fara cin abincinsu cikin farinciki da annashuwa, irin wanda suka manta rabon su da suyi kamarsa.

A haka gaba d'aya suka k'are wunin yau suna nunawa Bir kulawa da tarairaya tamkar zasu goyasa, sallah ce kawai ke tayar da su daga mazan har matan, yayinda Gimbiya da Bir kuma suke aikin binsu da ido a duk lokacin da suka tashi yin sallah.
Sosai Gimbiya Tasmir taji ta samu nutsuwa da ahalin gidan, musamman ma kuma Iman da ta zamto mata babbar k:awa a iyakar yinin yau kawai da suka had'u.
Wanda hakan kuma yasa ko da suka tashi tafiya sai Aunty Bilkisu tace Iman ta zauna a wurin Gimbiya su kwana a tare, saboda ta d'ebe mata kewa.
Hakan kuwa ba k'aramun dad'i yayiwa Gimbiya Tasmir ba.

Haka gaba d'aya k'annen Sheikh Ahmad mata suka watse kowacce taja zugar 'ya'yanta zuwa gidajensu cikin matsanancin farinciki.

Anan b'angaren Ummi kuwa wata irin soyayyar take nunawa Bir da Gimbiya Tamkar ta mayar da su cikin cikinta, musamman ma Bir da ko ina tayi yana tare da ita a mak'ale tamkar wani k'aramin yaro, domin kuwa ko da dare yayi ma itace ta kaisa har cikin d'akin Auta ta had'a masa ruwa yayi wanka tamkar yadda tayi masa da rana, tukun bayan ya futo ta basa kayan bacci yasa, sannan tasasa ya kwanta tayi masa addu'a tare da jamasa bargo ta rufesa, kana ta juya zuwa nata d'akin.



*JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FUL'DE.*

K'arfe hud'u da minti goma dai-dai Gimbiya Haddiyal ta farka daga daddad'an baccin da take mai cike da mafarkin Gid'ad'on ta.
Cikin matuk'ar sauri ta ture bargon jikinta tana mai saukowa daga kan gado.
Kai tsaye ta doshi hanyar bathroom tamkar wacce zata tashi sama saboda sauri.

Ta d'auki tsayin mintina talatin aciki, tukun sai gata nan ta futo d'aure da pink din towel a k'irjinta. Yayinda hannunta kuma yake rik'e da d'an k'arami tane tsane ruwan da yake kwance akan wuyanta zuwa fuskarta.

Direct ta doshi gaban dressing mirrow, tana mai janyo kujera ta zauna akai.

Cikin matuk'ar nutsuwa ta fara tsarawa kanta kwalliya, tanayi tana sakin murmushi tare da lumshe kyawawan idanuwanta.

Bata wani cika fuskarta ta da kwaliyya ba, asalima gira kawai taja sai hoda data shafa, tukun a k'arshe tabi pink lips d'inta da wani had'ad'd'en man leb'e a samansa.
Kana ta ware mayawaiciyar sumar kanta tana mai tajeta ahankali, sannan a k'arshe ta koma ta tufketa a wuri guda.
Sosai tayi bala'in kyau tamkar ita ta tsara kanta, Wanda hakan da ta ganine kuma ya sanyata sakin murmushi ita da kanta.
Tukun ta mik'e daga kan kujerar tana mai tafiya zuwa gaban had'ad'd'iyar wadrobe d'inta ta bud'eta.
Tsayawa tayi tana mai kallon kayan da suke shirye a cikinta, tukun a k'arshe ta sauke 'yantsun hannuwanta akan wasu kayan Fulani farare irin wa'yanda ko wane bafullatani yake sawa sababbi fidigil da su.

Cikin k'ank'anin lokaci ta gama sanya kayan da sukayi bala'in amsar jikinta, riga da zani.
Tukun ta koma gaban mirrow tana mai zuwa ta d'auki wasu sarak'una masu tsananin kyau irin nasu na Fulani ta mak'ala a wuyanta, kana ta kawo wata ta goshi ta d'aurota tunda k'eyarta. Tukun ta juya gefenta wuraren da hulunan kabarta tare da jakun-kuna suke a sak'ale tana mai ciro wata guda d'aya mai adon ja a k'arshenta tamkar yadda kayan jikinta ma suke da ratsin adon ja ajikinsu ta d'orata a tsakiyar kan nata.
Wani irin kyakkyawan murmushi ne ya kufce mata a lokacin da taga kanta a cikin madubi, saboda ita da kanta ta gane yau d'in ba k'aramun bala'in kyau tayi ba a cikin shigar da tayi.
Tukun ta sanya wasu tausasan fararen takalma marasa tudu a k'afarta tare da d'aukar jakar kaba ta rik'eta a hannunta.
Kana ta sake yiwa kanta wankan turarruka masu sanyin k'amshi da dad'i, tukun ta juya tana mai nufar d'akin da sandar tsafinta take taje ta d'aukota, kana ta kama hanyar waje cikin sauri tamkar yadda take komai da sauri.

A lokacin kuma k'arfe biyar har ta gota.
Kai tsaye ta doshi wurin da sukayi zasu had'u da Buba.
Tun daga nesa kuwa ta hangosu shida drivern taxi d'in da ya d'auko musu tsaye a jikin motar.
Yayinda daga gabansa kuma randar tsafinta tare da sauran kayan suke a jiye, da alamun dai shine ya tawo da su.

"Barka da futowa kyakkyawar Gimbiya sauraniya ga tsuntsayen masarautar fuld'e."

Buba ya fad'a cikin tsananin ladabi a lokacin da Gimbiya Haddiyal ta k'arasa wurin, yana mai durk'usar da kansa k'asa.

"Yawwa barkanka dai amintacce na."

Ta fad'a fuskarta d'auke da tsantsar murmushi, tukun ta juya b'arin da drivern yake tana mai amsa gaisuwarsa da taji Yana yi gareta.
Kana ta d'ora da fad'in.
"Ya kamata mu huce yanzu, saboda lokaci na sake tafiya."

Da sauri kuwa Buba ya bud'e mata mufrfin motar ta shiga, kana ya mik'a mata randar nan da sauran kayan karikitan zuwa ciki, tukun ya rufe k'ofar yana mai komawa ya shiga gefen da drivern yake, tukun drivern yayiwa motar key yana mai take ta suka kama hanyar titi ba tare da wani yasan da tafiyarsu ba a cikin gida.



*JAHAR WASAI, CIKIN MASARAUTAR WASAI.*

A b'angaren Asad kuwa ko da dare yayi gaba d'aya kasa bacci yayi, babu abun da yake tinani face yadda za'ayi ya iya sanya manyan kaya a jikinsa a gobe, domin kuwa ko kusa ko kad'an baya jin sonsu a ransa, hakan yasa bashi yayi bacci ba har sai da dare ya tsala sosai, shiyasa yau ko da asuba tayi bai iya tashi ba har sai misalin k'arfe bakwai na safe, tukun ya tashi yay sallah.

Misalin k'arfe takwas na safe ya shiga wanka.
Bai wani d'au dogon lokaci ba a cikin bathroom d'in ba ya futo d'aure da towel a k'ugunsa, yayinda hannunsa kuma yake rik'e da wani d'an k'aramin towel d'in yana tsane sumar kansa da shi.

Kai tsaye ya doshi gaban dressing mirrow, gaba d'aya yana yin komai ne a matuk'ar sanyaye hatta da tafiyarsa kuwa.
A haka ya k'arasa gaban mirrow d'in, yana mai d'aukar mai ya fara shafe jikinsa da shi.
Sosai yake jin wata irin fargaba na dirar masa ta dalilin kayan da yake shirin sanyawa a yau d'in, ko kad'an ko kusa bai tab'a tinanin zuwan wannan ranar ba, amma ya zaiyi haka Allah ya tsara masa.

Sosai ya shafe sumarsa da mayika tare da taje ta, da kuma sajensa har zuwa kan tattasaun gemunsa da yake matuk'ar zautar da 'yan mata, ta yadda suke ta futar da wani irin shek'i da k'yalli.
Tukun ya juya yana mai nufar gaban wadrobe d'insa.

B'arin da manyan kayansa suke da Mai Martaba ke yi masa su yana sawa a jere masa a ciki ba tare da ko takansu yana bi ba ya bud'e.

Da k'arfi ya rumtse idanuwansa, yana mai had'awa da cije lower lips d'insa, saboda yadda idanuwansa sukayi tozali da sababbin manyan kayan da suke a jere a ciki.
Kana daga bisani ya bud'e idanuwan nasa yana mai fara binsu da idanuwa, tukun a k'arshe ya dire 'yan yatsunsa akan wata dark brown d'in getzner shadda mai bala'in kyau da tsada.

Lokaci d'aya yaji kansa yayi wata irin bala'in sarawa, kana kuma gaba d'aya tsigar jikinsa suka mik'e suna masu bada yass!
Amma kuma kasancewar gaba d'aya tinaninsa a yanzu yana ga Haddiyal ne, babu abun da idanuwansa suke hasko masa face fuskarta, shiyasa ya k'arasa d'auko kayan ba tare da yabi takan sabon yanayin da yaji ya dirar masa ba, yana mai diresu akan gado.
Tukun ya cigaba da binsu da kallo yana mai jin wata irin muguwar tsanar shigar na lullub'esa, ta yadda har jikinsa yake 'yar rawa.

"Assalamu alaikum, wai har yanzu baka gama shiryawa ba Asad dan Allah."
Muryar Al'amin ta daki dodon kunnuwansa yana mai fadin.
Hakanne ya sanyasa juyawa zuwa b'arin da ya juyo sautin da sauri, yana mai dire idanuwansa akansa ba tare da ya iya ce masa komai ba.

Sanye yake data sa shigar manyan kanyan da tayi matuk'ar amsar jikinsa tare da bala'in yi masa kyau.
Kana daga bisani ya janye idanuwansa daga kan Al'amin yana mai mayar dasu zuwa kan agogon bangon da yake manne a jikin bangon d'akin.

Da k'arfi ya rumtse idanuwansa, yana mai d'an cizon leb'ensa na k'asa a hankali, saboda yadda yaga lokaci yaja da yawa, tukun a k'arshe kuma ya sake warasu akan kayan tare da sauke yantsunsa akan inner wears d'in da ya d'auko.
Su ya far'a sanyawa a jikinsa, kafin daga bisani kuma ya ware dogon wandon kayan yana mai zura k'afufuwansa a ciki.

Ya subahanallah, da k'arfi ya rumtse idanuwansa tare da cizon leb'ensa adai dai lokacin da fatar jikinsa ta had'u da kayan, domin kuwa tamkar wacce take manne da garwashi a kanta haka yaji tsantsar a zaba na gogarsa.
Sai dai kuma hakan baisa ya fasa sanyasu ba, asalima sai rigar da ya d'auko itama ya bud'e ya zura.

Lokaci d'aya kuwa jikinsa ya d'auki wata irin kyarma.
Yayinda idanuwansa kuma suka kad'a sukai jajajir tamkar gauta, gumi kawai ke aikin tsattsafo masa a duk ilahirin jikinsa.

"Wash Allah na Umminahhh!!!"

Ya fad'a cikin wata irin murya alokacin daya d'ora hula a kansa, saboda yadda yaji kan nasa yayi wani irin bala'in nauyi tamkar wanda ya d'ora dutse, ga kuma wani irin azababben zafi da yake futowa daga cikin hular tamkar zai k'onasa.
Wanda hakan kuma ya sanya Al'amin da hankalinsa ke kan wayarsa ya d'ago kai da sauri yana mai sauke idanuwansa a cikin na Asad.

Da matuk'ar sauri ya mik'e tsaye yana mai fad'in.

"Ya dai Asad? Me yeka damunka ne? Me yasa idanuwanka yin ja hakane?"
Ya jero masa tambayoyin alokaci guda, yana nai kafesa da idanu.

Amma amai makon Asad ya basa amsa, sai gani kawai yayi ya sake taune leb'ensa da matuk'ar k'arfi, yana mai d'ora yatsunsa akan hular da niyyar ya cireta, saboda yadda yake jin tamkar ana saukar masa da ruwan wuta daga cikinta.
Ta yadda har zuwa yanzu ya zamto numfashima sai da k'yar yake iya jansa tare da fesarwa, Amma kuma tunowa da yayi da fuskar Haddiyal tare da kalaman Babban Yaya, sai yayi saurin girgiza kansa, yana mai yarfar da hannun nasa a k'asa.
Tukun ya juya zuwa b'arin da Al'amin yake, yana mai bud'e baki cikin wani irin sauti yace.
"Muje ko."
Kana yayi gaba ba tare daya tsaya jiran cewarsa ba.
Iyakar kyau yau Asad yayi kyau a cikin shigar manyan kayan, irin wanda rabonsa da yayi makamancinsa shi kansa ba zaice ga lokacin ba, sai dai kuma yanayin azabar da yakeji tattare da kayance ta sanya ko lura da hakan shi baimayi ba, domin kuwa lokaci d'aya gumi ya fara b'atasu.

K'arasowarsu cikin fallon yayi dai dai da lokacin da Mamy ke d'auko ruwa a cikin fridge zata sha.
Jin sautin motsinsu da tayine ya sanyata juyawa da sauri zuwa b'arin da suke.

"Kai Masha Allah, Ashe haka yaran nawa suke da tsananin kyau ban sani ba sai yau, ko kufa, yanzu dan Allah bakufi jin dad'in jikinku ba cikin shigar mutunci haka."

"Mamy zafi nakeji, wayyo Allah jikina zai k'one Mamyyyy!!!"
Cewar Asad cikin wata irin murya da take rawa, yana mai sake rumtse idanuwansa da k'arfi.

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, me yake damunka ne Zaki, me yasa idanuwanka yin ja haka?"

Ta jero

Please Login or Register in order to submit comment