Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hannun da matuk'ar k'arfi, wanda hakan kuma ya sanyata juyowa a matuk'ar firgice zuwa b'arin da yake.
Take kuwa jik'ak'k'un idanuwanta da kuka ya kod'ar dasu suka fad'a cikin nasa jajayen idanun masu d'auke da azababben tashin hankali a cikinsu.
A lokaci d'aya kuma zuciyoyinsu sukayi wani irin azababben bugu, tukun suka kafe junansu da idanu bako k'iftawa.
Yayinda jikinsu kuma ya d'auki wata irin kyarma.

Sun d'auki tsayin minti d'aya a haka suna kallon cikin idan juna, tukun Gimbiya Tasmir ta janye nata daga cikin nasa.
Kana ta juya tana mai shirin fuzge hannunta domin tayi gaba, amma sai taji ya sake damk'ar hannunta da wani irin azabar k'arfi, ta yadda har take jin tamkar zai tsinka mata jijiyoyin hannunta.
Hakanne yasata sake d'agowa da matuk'ar sauri tana mai kallonsa.
Wani irin masifaffen ja taga idanuwan nasa sun sake komawa, yayinda jikinsa kuma ya sake d'aukar bala'ya'y'yar karkarwa, ga wani irim huci da yake busarwa tamkar zaki.
Tukun daga bisani kuma yasa hannunsa d'aya yana mai funcike jakar, kana yayi wani irin funcikarta yana mai juyawa da matuk'ar sauri, ya doshi hanyar da zata mayar dasu gida ba tare da yace mata komai ba.

Sosai Gimbiya Tasmir take jin hannunta daya damk'a na mata bala'in zafi tamkar zai tsinke, tayadda har hawayen da suke futa daga cikin idanuwanta suka k'ara tsananta.

Shi kuwa Bir tsabar tashin hankalin da yake ciki ko cikakken gabansa baya iya gani, a haka har suka k'arasa k'ofar gidan nasu.

K'afarsa d'aya yasa yana mai hankad'a get d'in da ita.
Kana ya danna kansa ciki da bala'in sauri yana mai funciko Gimbiya Tasmir zuwa ciki itama.
Tukun ya doshi hanyar garden gaba d'ayansa a wani irin haukace.

Bai saketa ba har sai da sukaje k'arshen bango, tukun yayi wani irin hankad'ata ta fad'i a k'asa.
Yayinda shi kuma ya zube gwiwoyinsa a k'asa yana mai damk'ar kansa da matuk'ar k'arfi da hannunsa jikinsa na kyarma.
Tukun daga bisani ya fara jan gwiwoyinsa yana mai nufar wurin da take.
'Dago idanuwansa yayi da suke d'auke da azababben tashin hankali yana mai watsasu a cikin nata.
Kana ya bud'e baki cikin rawar murya tamkar zai fashe da kuka, yana mai fad'in.

"Me yasa zaki tafi ki barni Gimbiya? Me nayi miki da zaki zab'i kicutar da zuciyata?"

Ya k'arasa maganar muryarsa na rawa, zuciyarsa nayin matuk'ar rauni.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir da sauri ta mik'e tsaye tana mai d'anja baya, idanuwanta da har yanzu suke zubar da k'walla a cikin nasa.
Kana ta bud'e baki tana mai fadin.

"Saboda ka nuna baka buk'atata a cikin rayuwarka, shiyasa na zab'i na tafi na baka wuri, kuma ko a yanzu bawai zan zauna bane a tare da kai Bir."

Ta k'arasa maganar tana mai shirin juyawa.
Ganin hakan da Bir yayine kuma ya sanyasa mik'ewa tsaye a wani irin zabure, jikinsa na wata irin kyarma, wanda har hakan kuma ya tsorata Gimbiya Tasmir, tayi saurin ja da baya tana mai jingina da bango.

Shima d'in d'aga k'afafuwansa yayi yana mai matsowa kusa da ita dab, ta yadda har jikinsu ke gugar juna.
Tukun daga bisani ya durk'uso da kansa yana mai dawo da fuskarsa dai-dai saitin tata, kana ya had'e tsinin hancinsu wuri d'aya, tare da hulla k'wayoyin idanuwansa a cikin nata.

Cikin wata irin murya mai tafe da kuka tare da matuk'ar sanyi ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Ashe dama zaki iya tafiya ki barni Girmibiyata? Me yasa me yasa me yasa zakiyi mun haka, bayan kuma kin san dake kad'ai na sa...?"

Maganar tasa ta yanke, saboda yadda muryarsa ta tsananta da rawa, tukun sai ga ruwan hawaye nan, shar! Shar!! Shar!!! Suna b'allewa daga cikin jajayen idanuwansa tamkar anbud'e famfo.
Yayinda jikinsa kuma ya sake d'aukar matsananciyar karkarwa, saboda yadda wani irin azababben zazzab'in tashin hankali ya saukar masa alokaci guda.

Ganin hawayen nasa da tayi suna zubane ya sanya taji zuciyarta ta sake yin rauni, ta yadda har ta gaza tsaida nata itama sai k'aruwa da yawansu yayi.
Kafin daga bisani kuma ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Ba kai zaka cutuba a tafiyata nice da cutuwar, asalima kai idan kaji babu dad'i iyakar na 'yan kwanakine kamanta dani, saboda kai baka rasa kowa naka ba, kana da gata, bayan haka kuma kasamu wadda zata maye maka gurbina, wacce ta fini da komai, ta yadda harta sanyaka mantawa dani tun a yanzu, hak'ik'a da zamana anan d'in ina kallonka tare da wata, gwanda nayi nisa da kai ko da hakan yana dai-dai da tsayawar futar numfashinane."

Da k'arfi Bir ya rumtse idanuwansa jikinsa na d'aukar kyarma, sabo da jin kalaminta da tayi, yayinda zuciyarsa kuma ta sake tsananta da bugu. Hak'ik'a bazai tab'a iya jurar rasataba a cikin rayuwarsa, saboda yana mata sone irin son da bashi da iyaka, haka kuma baya tinanin zai iya hak'ura ya fasa zuwa wurin gasar shad'in, domin kuwa idan yayi hakan wancan mahaukacin gayen da yazo d'azu zai d'auka gargad'insa ne ya sanyasa k'in zuwan, tabbas cikinsu babu wacce zai iya hak'ura da ita.

Sosai jikinsa yake cigaba da kyarma, gaba d'aya ganin da yayi Gimbiya na shirin tafiya tabarsa ba k'aramun d'imautasa yayi ba, shi kansa bai gama sanin haka yayi zurfi a cikin soyayyartaba sai a yanzun da yaga tana shirin barinsa, bari kuma na har abada a cewarta.

Ya jima rumtse da idanuwansa, tukun ya sake bud'esu wasu irin sababbin hawayen na sake kwaranyowa da bala'in gudu, yayinda har yanzu kuma bugun zuciyarsa yak'i ya dawo dai-dai.
Kana ya bud'e baki cikin rawar murya yana mai fad'in.

"Ni bance bana buk'atarki ba a cikin rayuwata, asalima aduk duniya babu wata 'ya mace da nake buk'ata sama dake, kuma bazan tab'a yiwa wata 'ya mace ko da kwatankwacin son da nake miki ba, hak'ik'a idan kika barni zuciyata zata bugane Gimbiya, wallahi ina sonki kuma babu abunda ya canza ko zai canza a cikin soyayyar da nake miki ko a gaba.
Koko kin manta saboda kece na baro Iyata, duk da irin shak'uwar da mukayi da ita Gimbiya?"

Ya k'arasa maganar a sanyaye, har lokacin hawayen idanuwansa basu tsaya da zubaba.

"Gwanda kai iyakar Iya kawai kabaro acan, kuma a yanzu gashinan ka had'u da w'ayanda sukafi Iya, ni kuma fa, gaba d'aya dangina na baro, bari kuma na har abada, na yadda na kuma biyoka ba tare da fargaba ko tsoro ba."

Ta fad'a tana kallon cikin idanuwansa.

"Hakane tabbas kinyi mun abunda har abada bazan tab'a biyanki ba kome zan miki, dan haka kisani babu abunda zaisa na canza miki daga yadda nake, saboda Jarumi yasan hallaci, kuma in dai akan batun waccan yarinyarne ki kwantar da hankalinki ni kwata-kwata bana sonta, kuma bazan tab'a sontaba ko da babu ke ballantana kuma ina dake."

"Amma adress d'inta daka amsa kuma fa, sannan ka tabbatarwa da masoyinta cewar zakaje gasar kuma zaka yaddasa, ko kuwa kayi zaton duk banji lokacin da kake furta hakan bane Jarumi?"

"Na karb'ane domin ta tafi ta barni, shi kuma na fad'a masa hakane saboda karya rainani, amma kwatakwata ba haka abun yake acikin zuciyataba."

Ya samu kanta dayi mata k'arya, saboda karta tafi ta barsa, amma bawai dan yana jin zai hak'ura yabar Yarima Asad yaci banza ba.

Shiru tayi tana mai cigaba da kallon idanuwansa.
Ganin hakan da yayine ya sanyasa mik'ewa yana mai janyota cikin jikinsa.

Ba tare da tayi wata gardama ba kuwa ta rungumesa k'am-k'am, wanda hakan kuma ya sanyasu sauke wasu irin tagwayen ajiyar zuciya a tare.
Yayinda bugun zuciyarsu kuma ya dinga bugawa a lokaci guda.

Sun jima a haka rungume da junansu suna hawaye har lokacin.
Tukun daga bisani Bir ya sake durk'usowa ba tare daya janyeta daga cikin jikinsa ba yana mai fad'in.

"Ina sonki Gimbiyata, ina matuk'ar k'aunarki, na rok'eki karki k'ara cewa zaki tafi ki barni ko wane irin sab'ani zamu samu, saboda hakan tamkar dai-dai yake da tsayawar bugun zuciyata Gimbiya."

Ya k'arasa maganar yana mai sake fashewa da wani sabon kukan tare da k'ara rungumeta a jikinsa, saboda hakanan kawai yakeji tamkar idan ya saketan zata sake tafiya ta barsa ne.

Da k'arfi itama ta k'ara rumgumesa tana mai jin tausayinsa kuma na lullub'eta gaba d'aya, kana daga bisani ta d'ago kanta tare da tafin hannunta tana mai fara goge masa hawayen kan fuskarsa, tukun a k'arshe ta fara k'ok'arin raba jikinta da nashi. Amma sai taji ya sake rik'eta gam-gam yana mai girgiza mata kai, kana daga bisani ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Idan kika barni mutuwa zanyi Gimbiyata, idan kuma har na rayu to kisani bazan tab'a moruwaba a duniya."

"Hak'ik'a bazan barkaba Jarumina, yanzuma dana tafi nayi nadamar tafiya, na rok'eka da Ubangiji Gargabilu karka juya mun baya ko ba yanzu ba kaji ko?"
Ta k'arasa maganar cikin kuka.
Yayinda shi kuma Bir ya saki murmushi yana mai durk'usowa k'asa, tare da zaro harshensa ya fara d'auke mata hawayen fuskarta dashi.

Sun jima a haka suna rarrashin junansu har sai da suka tabbatar da kowannensu nutsuwarsa ta dawo masa, kana ya damk'i tafin hannunta a cikin nasa da k'arfi, suna masu fara d'aga k'afafuwansu a jere suka doshi hanyar futa daga cikin wurin.

"La Ummi kin gansu anan harda itama."

Cewar Matar Sheikh Ahmad da idanuwanta suka fara sauka akansu da suka futo, tukun ta ruga a guje tana mai yin wurin Gimbiya cikin tsantsar kuka.

Da sauri Itama Ummi tayi wurinsu tana kuka tare da dariya, haka itama Alawaiyya ta tafi a guje cikin matsanancin farinciki.

Yayinda Sheikh Ahmad kuma da suka shigo tare dashi a yanzu yake tsaye a wurin mai gadi yana sauraran yadda abun ya faru tun daga kan zuwan Haddiyal, har zuwan Yarima Asad da kuma futowar Gimbiya Tasmir da tsayawar da sukayi da Alawiyya, duk saida ya fad'a masa, kasancewar shi akan idonsa akayi abun, kana kuma yaji komai, saboda dukansu ba a hankali suka dinga magana ba.

"Amma shi yaron da yazo d'in baka san ko d'an inane shi ba?"

Cewar Sheikh Ahmad yana kallon mai fad'in ransa gaba d'aya ab'ace.

"Eh to, naji dai su yaran da yazo dasu suna kiransa fa Yarima Asad."
Mai gadi ya fad'a yana kallonsa shima.

"Yarima Asad! Yarima Asad!! Wato d'an sarkine kenan."

Ya fad'i haka a cikin ransa, kana daga bisani ya girgiza kansa yana mai yanke hukuncin samun Ciroman gida da maganar, tunda suna karatu tare, saboda ajawa yaron kunne karya cutar masa da k'ani, ya sake jefa Umminsa cikin wani sabon tashin hankalin bayan sun samu komai ya huce.
Tukun ya juya yana mai kai idanuwansa zuwa wurin dasu Bir suke.

Ita kuwa Matar Sheikh Ahmad da sauri ta janyo Gimbiya Tasmir jikinta tana mai rungumeta, tukun suka fashe da kuka a tare tana mai fad'in.

"Me yasa zaki tafi Gimbiya, idan kin tafi kije ina, dan Allah karki k'ara cewa zaki tafi."

Da sauri Ummi ta k'araso wurin da suke tana mai janyo Gimbiya Tasmir cikin jikinta.
Tukun ta rungumeta k'am-kam, kana ta bud'e baki cikin kuka tana mai fad'in.

"Me yasa zakiyi mun haka d'iyata? Akan me zaki yanke hukuncin tafiya ki barmu bayan kuma baki da wasu bayanmu?"

K'am-k'am Gimbiya Tasmir ta rungumeta itama hawaye na cigaba da zubo mata.
Yayinda Ummi kuma ta d'ora da fad'in.

"Daga yau daga yanzu karki k'ara cewa zaki tafi kibarmu, idan ma laifine yayi miki kizo ki fad'a mun, ni kuma na miki alk'awarin hukuntasa."

Ta k'arasa maganar tana mai shafa bayan Gimbiya Tasmir, kana ta juya b'angaren da Bir yake tana mai fad'in.

"Kabani mamaki, ban tab'a zatonka da aikata haka ba, wai ace harka fifita wata can da kaganta lokaci guda sama da wacce ta rasa komai nata dominka, sannan kuma tayi sanadin sadaka da naka komai d'in, to kasani ni ban amince maka da aurenta ba."

Duk'usar da kai kawai Bir yayi yana mai jin duk babu dad'i a ransa.
Yayinda shima Sheikh Ahmad ya k'araso wurin da suke, kana ya kalli Gimbiya yana mai fad'in.

"Daga yau karki k'ara cewa zaki tafi kinji k'anwata."

'Daga masa kai kawai tayi tana mai mamakin yadda mutanen suke da tsananin kirki, kana kuma lokaci d'aya taji tausayin Bir d'inta ya kamata, saboda yadda taga ya durk'usar da kai k'asa, su kuma sunata masa fad'a tamkar bashi bane suke na nan dashi a d'azu da safema.

Kama hannunta Ummi tayi suna masu dosar cikin gidan gaba d'ayansu.
Yayinda Sheikh Ahmad kuma ya dafa kafad'ar Bir, yana mai fad'in.
"Tawo muje mu zauna k'anina."

Binsa yayi suna masu nufar b'angarensu Sheikh Ahmad d'in.
A cikin falonsa kan kujera suka zauna.
Kana Sheikh Ahmad ya dafa kafad'ar Bir yana mai kallonsa cikin sanyi yace.

"Me yasa zakayi haka k'anina? Me yasa har zaka zab'i bare sama da wacce tayi maka komai a rayuwa? Hak'ik'a Gimbiya bata cancanci haka daga wurinka ba, dan haka ni ina mai baka shawara a matsayina na yayanka akan ka rabu da waccan yarinyar, karka kuskura kaje wurin gasar, idan ma baka da ra'ayin zama da mace d'aya ne, sai ka bari kamar bayan kunyi aure da shekara d'aya zuwa biyu saika bijiro da zancen wata, amma ba a yanzu ba da ko zafin rabuwa da iyayenta bai gama sakinta ba."

Shiru Bir yayi yana mai sauraron kalamansa kansa durk'ushe a k'asa. Ji yake inama ace zai iya hak'ura ya fasa zuwa wurin gasar, sai dai kuma bai san dalilin da yasa yake ganin tamkar idan bai jeba Yarima Asad zaiyi zaton saboda barazanarsa yak'i zuwa, kana kuma sai yake jin kamar bai kyautawa yarinyar data d'auki tsawon shekara da shekaru tana dakon soyayyarsaba ba tare data sansa ba.
Hakanne ya sanyasa yanke hukuncin barin mutanne gidan nasu a matsayin ya fasa zuwan, idan yaso a ranar da za'ayi abun sai kawai yayi tafiyarsa.
Tukun ya d'ago kansa yana mai kallon Sheikh Ahmad tare da fad'in.
"Ba zanje ba d'in Yayana."

"Yawwa k'anina ko kaifa."
Shiekh Ahmad ya fad'a cikin murmushi yana mai d'an bugun kafad'arsa.

Sosai Sheikh Ahmad ya basa shawarwari, tukun a k'arshe suka fuce daga cikin part d'in a tare, shi yayi cikin gida yayinda Sheikh Ahmad kuma ya shiga cikin motarsa yana mai kiran Babban Yaya yace masa idan ba damuwa yana son su had'u zasu d'an tattuna dashi.
Aikuwa cikin sauri Babban Yaya yace masa ko yanzu idan yana free shima free yake zasu iya had'uwa.
Hakan ko yasa daga nan k'ofar gidansu kai tsaye yayi gidan Sarkin Wasai.

Sosai Babban Yaya yayi masa tarbar mutunci, tare da sanyawa aka cika masa gabansa da abinci kala-kala a mtsayinsa na Malaminsa.
Tukun bayan sun gama gaisawa Sheikh Ahmad ya kora masa bayanin duk abunda ke faruwa, tun daga kan labarin haihuwar Bir har zuwa yau da Yarima Asad yazo gidansu cikin hikima irin tasu ta malamai.

Aikuwa idan ran Babban Yaya yayi dubu sai da ya b'aci da jin haukan da k'anin nasa yaje yayi, yayinda tausayin Bir kuma da Ummin su Shaikh Ahmad ya samu gurbi a zuciyarsa.

Hakan yasa ya dinga bawa Sheikh Ahamd hak'uri, yana mai basa tabbacin cewar zai yiwa Yarima Asad fad'a, in sha Allah hakan bazata sake faruwa ba.

Hakan da Sheikh Ahmad ya jine yasa yace masa karyayi masa komai, saboda shi bawai k'ararsa ya kawo bane, ya fad'ane kawai gudun kar asamu matsala, tukun a k'arshe kuma ya kora masa bayani akan da'awar da yake son suje masarautar fuld'e, tare kuma da k'asar malin cikin Bak'ar Masarauta, domin a tseratar da al'umma daga halaka a matsayinsu na Malamai.

Sosai kuwa Babban Yaya ya gamsu da bayanan Sheikh Ahmad, kana kuma ya tabbatar masa da cewar zai sanar da mai martaba in sha Allah kome ake ciki zai kira ya fad'a masa, tukun a k'arshe sukayi rabuwar mutunci Sheikh Ahmad ya haye motarsa yana mai d'aukar hanyar Jami'arsu.

Ko da dare yayi daga Gimbiya Tasmir har Bir gaba d'aya kasa rintsawa sukayi, sai faman juyi kawai da sukeyi akan gado, saboda yadda gabaki d'ayansu damuwa tayi musu yawa a yau d'in.
Haka dai suka d'auki dogon lokaci suna tinane-tinane, kafin daga bisani kuma bacci b'arawo yayi awan gaba da su.

Ko da asuba tayi kuwa Alawiyya na tashi domin tayi sallah itama Gimbiya Tasmir ta tashi, kasancewar damuwar da Ummi taga tana ciki a jiyane, shiyasa tacewa Alawiyya tazo ta tayata kwana hakan zai d'ebe mata kewa.

A b'angaren su Bir kuwa shima Abba na zuwa ya tashi Auta domin su tafi masallaci ya farka.
Sai dai kuma bai iya tashi daga kwancen da yake ba, asalima ko sanin ya tashi Auta baiyiba har yashiga bathroom ya d'aura alwala, kana yazo yayi raka'atanil fajir anan cikin d'akin, sannan ya fuce ya tafi massalaci Bir na kallonsa.

Sosai a yau ya k'ara jin addinin nasu yayi matuk'ar shiga ransa, domin kuwa dama ya dad'e yana kokonto akan nasu da suke bautar Gargabilu, tun daga lokacin da Iya ta basa labarinsa.

A b'angaren Gimbiya Tasmir itama kwance take akan gadon ta zubawa Alwaiyya ido, tana mai kallon yadda take sallah cikin nutuswa da kamala.
Kana bayan ta idar taga tayi addu'oi, tukun a k'arshe ta janyo al'qurani tana mai gyara zamanta ta bud'esa tare da fara karantasa.

Da sauri Gimbiya Tasmir ta lumshe idanuwanta, tana mai sauke wasu irin tagwayen ajiyar zuciya, saboda yadda take jin karatun na ratsa gaba d'aya ilahirin jiki da zuciyarta, lokaci guda kuma taji duk k'uncin data kwana ta tashi dashi ya yaye, sannan wata irin nutsuwa ta dinga saukar mata a gaba d'aya ilahirin jikinta.

A hankali ta d'an fara jijjiga kanta, tana mai jin inama ace kar Alwaiiya ta dena karatun nan, hak'ik'a tun Iman nayi taji yayi matuk'ar birgeta, domin kuwa su nasu addinin kwata-kwata babu wani abu mai suna karatu a cikinsa, asalima sai kad'a-kad'e da raya-raye tare kuma da d'aukar wuta kawai ake yi.

Ita kuwa Alawiyya ko kad'an batasan Gimbiya Tasmir na kallonta ba.
Misalin k'arfe bakwai na safe dai-dai kuma ta rufe k'ur'anin tana mai mayar dashi cikin bedside drower ta ajiye.
Tukun tana shirin mik'ewa daga kan sallahyar da take zaune akai taji sautin muryar Gimbiya Tasmir ta ratsa dodon kunnuwanta tana mai fad'in.

"Amma ya sunan wanan abun da kike karantawa ne."

Da sauri kuwa Alawiyya takai idanuwanta wurin da take, tana mai fad'in.

"Dama kin tashine Gimbiya?"

"Harma nayi brush baki sani ba kina karatu."
Cewar Gimbiya tana mai lumshe idanuwanta.

Ita kuwa Alawiyya zamanta ta gyara akan kujerar da take zaune akai, tana mai fad'in.

"Al'qurani kenan, littafin da bashi da tamka aduniya, littafin da ya zamto waraka ga duk wani ciwo, littafi mai yaye damuwa tare da sanya nishad'i, ga kuma roman lada ga duk mai karantasa, kana kuma zai zamto ceto ga duk ma'abocin karantasa a ranar gobe k'iyama wurin wuce sirad'i."

Cikin wani irin yanayi Gimbiya Tasmir ta mik'e zaune daga kwancen da take, tana mai zuba idanuwanta akan fuskar Alawiyya, tukun daga bisani ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Hak'ik'a na yadda da zancenki, domin kuwa nima ya yayemun damuwar da take dank'are a cikin zuciyata ta silar sauraransa da nayi daga bakinki, hakan yasa nake son nima ki koya mun shi, domin na dinga karantawa."

Jin hakan da Alawiyya tayine ya sanyata sakin murmushi, kana ta bud'e baki cikin tsananin jin dad'i, tana mai fad'in.

"Shi ba dai-dai yake ba da sauran littatafan da kika sani, wannan littafi ne wanda mutane masu tsarkine kawai suke karantasa, bawai kuma ina nufin tsarki na daud'a ba, duk da shima d'in dashi d'in, amma wanda nake nufi a yanzu shine mutanen da suka kasance Musulmai masu bautar Allah, wa'yanda basa had'a waninsa da shi, domin kuwa shi alqur'ani littafinsa ne.

"To ku a ina naku Allahn yake ne, naga tunda mukazo banga kunje wurinsa ba?"

Gimbiya Tasmir ta sake jefo mata wata tambayar.

"Allah'n mu yana sama, kuma a kullum muna zuwa garesa ta hanyar sallahr da mukeyi, sai dai kuma mu bama ganinsa shine yake da ikon ganin kowace halitta tasa da take a cikin duniya, tamkar yadda yake da ikon yimana ruwa da zafi, rana, harma da sanyi a cikin lokutansu. Shi kad'aine kuma Ubangijin gaskiya, yayinda Annabi Muhammad (S.A.W) kuma ya zamto shalele a wurinsa, kana kuma d'an aikensa zuwa garemu, hak'ik'a musulunci shine kawai addinin gaskiya Gimbiya, kuma duk mutumin da bai kasance cikinsa ba har ya koma ga Allah, to tabbas babushi babu d'an-d'anan rahamar Ubangji, wato dai Wutace makomarsa."

Ta futo mata kai tsaye, saboda yadda taga jikinta yayi matuk'ar sanyi, da alamun dai duka ta yadda da abubuwan data fad'a mata.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir cikin wani irin yanayi ta lumshe idanuwanta tare da bud'e su, kana daga bisani kuma ta bud'e baki ba tare data tsaya wani kokonto ba, tana mai fad'in.

"To a nawa ake shigarsa ne? Ko kuma wurinwa ake zuwa a shiga? Saboda ni dai na yadda dashi yanzu."

Cikin matsanancin farinciki Alawiyya ta mik'e tsaye, tana mai fad'in.

"Addinin Allah ba addini ne na kud'i ba, sauk'ak'an kalmomi tare da yadda dashi shine kawai zai sanyaki a cikinsa, sai kuma daga baya da mutum zaiyi wanka tare da fara koyon sallah da karatu."

"Tabbas na aminta dashi, kuma ina son yanzu ki sani a cikinsa nima."

Gimbiya Tasmir ta fad'i hakan tun daga k'asan zuciyarta
Wanda hakan kuma ya sanya Alawiyya cikin matsanancin farinciki mara misaltuwa, ta yadda har bata san lokacin data rungume Gimbiya Tasmir ba idanunta na zuba k'walla, kana daga bisani kuma ta kamo hannunta tana mai fad'in.

"Tawo muje, ba nice zan sakaki ba Yaya Sheikh shine da wannan aikin."

Ta k'arasa maganar tana mai jan hannunta zuwa cikin falo.

Wanda futowar tasu kuma tayi dai-dai da shigowar Sheikh Ahmad cikin falon domin yaje ya gaishe da Umminsa.
Yayinda itama Ummi kuma ta sauko k'asa alokacin.

"Yaya Sheikh ga Gimbiya nan tace na kawota wurinka musulunci take son kasanyata a ciki itama."
Tayi maganr da wani irin sauri, kana kuma cikin tsantsar zumud'i.
Yayinda Ummi, Shekh Ahmad harma da Abba da dawowarsa kenan daga masallaci ya shigo sukayi tsaye a wurin da suke cikin tsananin farinciki tare da mamaki.
A kuma dai-dai lokacin Auta ma ya futo rik'e da hannun Bir, yana mai fad'in.

"Yaya Sheikh dama wurinka zamu zo, Yayane yace mun yana son shiga musulunci!"

"Alhamdulillahi rabbil alamin."

Ummi ta fad'a daga wurin da take a tsaye hawayen farinciki na kwaranyowa daga cikin idanuwanta.
Yayinda Abba kuma ya k'araso wurin da su Bir suke da sauri, yana mai rungumesa a cikin jikinsa cikin matsanancin farinciki.

Kaka kuwa da tajiyo abunda ake fad'e daga cikin d'aki da sauri ta futo tana mai fad'in.

"Allahu akbar, ashe da wurima zata musulunta ban saniba naita jin haushinta da."
Ta k'arasa maganar tana mai rungumar Gimbiya Tasmir cikin farinciki.

Shi kuwa Sheikh Ahmad da yake jin wani irin matsanancin farinciki na lullub'esa. Gyaran murya yayi, tukun yace duka su zazzauna.

Zaman sukayi kuwa gaba d'aya harsu Ummi. Sannan ya kalli Gimbiya Tasmir yana mai tambayarta dalilin da yasa take son shiga musulunci.
Take kuwa a wurin ta shaidamasa da cewar, saboda ta gane shine addinin gaskiya, ta silar zaman da tayi dasu.
Sosai dai yayi mata tambayoyi akan dalilin da yasa take son shiga musulunci, gaba d'aya tana basa gamsasshiyar amsa, tukun bayan ya gama jin nata bayanin ya juya kan Bir shima yana mai tambayarsa tamkar yadda ya tambayeta.

Yadda kasan sun had'a baki da Gimbiya Tasmir haka shima ya zayyano makamancin yadda tace.
Tukun a k'arshe cikin tsananin farinciki Sheikh Ahmad ya fara takan Gimbiya Tasmir, yana mai fad'a mata kalmar shahada tana mai maitawa har kimanin sau ukku, kana kuma a k'arshe ya fassara mata me abunda ta fad'a d'in yake nufi, sannan ya juya wurin Bir shima yana mai fad'a ya fad'a har kimanin sau ukku.
Tukun yace su zab'i sunayen da suke so, domin kuwa komai nasu ya dawo sababbine su yanzu.

Bud'ar bakin Gimbiya Tasmir kuwa tace Halimatussadiya, wanda kuma taji sunan ne a wurin d'aya daga cikin jikokan gidan da sukazo a ranar da suka zo, tun daga ranar kuma taji sunan yayi matuk'ar birgeta.

Shi kuwa Bir yana tashi yace Umminsa ta zab'ar masa, shi bai san sunan da zaice ba.
Ai kuwa cikin matsanacin farinciki Ummi ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Abdulmajid!"

"Allahu akbar.! Allahu akabar!! Allahu akbar!!!"

Gaba d'aya d'aukacin jama'ar falon suka fad'a suna masu sakin kuka tare da dariya duk alokaci guda.
Tukun suka fara rungumarsu gaba d'ayansu, suna masu yi musu barka da shigowa musulunci cikin matsanancin farinciki mai tafe da kuka.

Suma gaba d'ayansu kukan sukeyi shab'e-shab'e da hawaye suna dariya, yayinda suke jin zuciyarsu kuma nayin haske, jikinsu kuwa na saki tamkar wa'yan da aka d'aukewa manyan duwatsu akansu.

Haka dai suka sha koke-koken su da dariya, kana a k'arshe, Sheikh Ahmad ya k'arasa sanar musu da abubuwan daya kamata su sani, sannan ya tsaida musu lokacin da zasu fara karatu, tukun yayi musu bayanin wankan tsarki take a wurin, kana ya umarcesu akan suje su aiwatar a lokacin.

A tak'aice dai fad'in irin faraincikin da gaba ki d'aya ahalinnan suka shiga a ranar yau b'ata bakine, domin kuwa haka sukaita kiran dangi suna sanar musu,

Please Login or Register in order to submit comment