Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai janyo mana k'aninsa zuwa cikin shago kawai suzo su buga mana wasan kwikwayo aciki, wai suna son gida, shi kuma ya dawo ya tafi da su."

Yake ta sak'a haka a ransa, sabo da shi ko kad'an bai yadda cewar basu san junaba.

A b'angaren su Sheikh Ahmad kuwa, suna futa suka doshi gaban motarsa da take fake a wuri d'aya, alokacin tinima har an loda masa kayan anbincin daya siya, hakanne ya sanya sa karasawa wurin but d'in ya rufesa.
Sannan ya dawo yana mai bud'e murfin motar baya.
Kana ya nunawa Gimbiya Tamsir ciki yana mai fad'in.

"Bismillah shiga daga ciki ko k'anwata "

Shiga cikin tayi ta zauna.
Tukun yaron dake rik'e da jakarsu ya zuro mata ita.

Tana shirin zare kud'i ta basa Sheikh Ahmad ya zaro d'ari biyu acikin aljihunsa yana mai mik'a masa ita.
Kana ya rufe mata murfin yana mai komawa ya bud'e gidan gaba daga wurin mai zaman banza.
Tukun ya kauce Bir ya ma shiga ciki, sannan shima ya shiga yana mai rufota tare dayi mata key.

A hankali ya juyo da kansa yana mai kallon Bir daya lumshe idanuwansa, alokacin da suka hau saman titi.
Kana daga bisani ya janye idanuwansa nasa yana mai mayar dasu kan tuk'in da yake.
Tukun daga bisani ya bud'e baki cikin kamilalliyar muryarsa, yana mai fad'in.

"Amma dai ba 'yan k'asar nan bane ba ku ko?"

Bir yaji sautin muryarsa ta daki kunnensa.
Hakanne ya sanyasa bud'e idanuwan nasa daya lumshe su.
Kana kuma ahankali ya juyar da idanunsa zuwa kan fuskar Sheikh Ahmad da yake tuk'insa.
Tukun yace.

"Eh gaba d'aya jiya ma muka tab'a zuwa k'asar nan."

"Allah sarki, daga wata k'asar kuke kuma?"
Sheikh Ahmad ya k'ara watso masa tambayar, duk da kasancewarsa ba ma'abocin shiga abunda babu ruwnasa bane shi, sabo da yasani ko a addinance hakan ba abu bane mai kyau, amma sai dai kuma bai san dalilin daya sa yaji yana son jin daga wurin da suka futo ba.

"K,asar Malin, a yankin Jahar Karfu...."

K'iiiiiiiiii!!!

Kakejin k'arar take birki atsakiyar titin da matuk'ar k'arfi da Sheikh Ahmad yayi, sabo da jin furucin yaron da yayi ya daki kunnensa.
Kafin daga bisani kuma ya bud'e baki hawaye na tsinkewa daga cikin idanuwansa da tsananin gudu, yana mai fad'in.

"Alhamdulillah! Alhadulillahi!! Alhamdulillah!!! Hak'ik'a yau kukanki ya k'are Ummina, Ubangiji mai ruwa da wut, rana da wata ya yaye miki damuwarki, lokacin murmushinki yazo, Allah yayi kina da rabon sake sanya gudan jininki acikin idanuwanki. Alhamdulillahi rabbil alamin!"

Yayi maganar da harshen larabci, wanda hakan kuma ya sanya kwatakwata daga Bir har Gimbiya babu wanda ya fahimci komai a cikinsu, hawaye na tsinkewa daga cikin idanuwansa.
Kana kuma yana mai sakin murmushi afili, tare da cigaba da mai-maita kalmar "Alhamdulillah."

K'rarar horn d'in da yaji ta cika masa kunnuwansa ne ta sanyasa tina a wurin daya take birkin, wato a tsakiyar titi, wanda kuma shi kwata-kwata bai san lokacin daya takasan bama.
Hakanne ya sanya sa janye k'afarsa akan birkin, yana mai cigaba da tafiya ba tare daya tsaya bi takan jama'ar da yaji sun fara masifa ba, sabo da har ga Allah farincikin da yake ciki a yanzu bama zai barsa ba ya iya bada hak'uri.
Yayinda Bir da Gimbiya Tasmir kuwa sukayi matuk'at firgita alokacin daya take birkin.
Kana kuma kalaman da sukaji yanayi wa'yan da basu iya gane ko abu d'aya daga cikin abubuwan da yake fad'a ba, tare da ruwan hawayen da sukaga yana zuba a idanunsa, sukayi matuk'ar tada hankalinsu.

Sai dai kuma ko kad'an basu iya tambayarsa dalilin daya sanyasa kukan ba, sabo da ganin da sukayi har yanzu yana aikin sharar k'wallah tare da cigaba da mai-maita kalmar Alhamdulillah, wacce basu san kome take nufiba.

A haka har suka k'arasa Babban Zaure Locus.

Tunda suka shiga unguwar Bir da Gimbiya suke aikin kalle-kalle.
Sosai tsarinta yayi matuk'ar birgesu, sabo da ganinta da sukayi shiru babu wata hayaniya, wanda hakan ya basu tabbacin zasuyi rayuwa mai da'di a cikinta, sabo da su duk atinaninsu gidan da zai siyar musun ne ya kawosu, kamar yadda ya fad'a musu.

Da matuk'ar k'arfi ya fara danna horn tundaga nesa da get d'in su.
Wanda hakan kuma ya k'ara sanya Bir da Gimbiya cikin tsananin mamakin mutumin.
Kafin daga bisani kuma sukaga an bud'e get d'in d'an madai-daicin gidan da suke tunkararsa mai tsananin kyau.

A guje Sheikh Ahmad ya shige da motar, tukun ya bud'e murfinta bayan ya kasheta ba tare da ko parkin d'in arzik'i ya gyaraba, yana mai bud'e muryarsa da tsananin k'arfi ya fara fad'in.

"Ummina! Ummina!! Ummina!!!
Ki futo ki gani futo da sauri yau ga gudan jininki yazo gareki, Allah ya kawo miki shi addu'ar mu ta karb'u, Ummina dan Allah futo da sauri yau ranar takice, Ubangiji ya kawo k'arshen kukanki, d'anki yazo har inda kike komai daya faru a shekaru talatin har da d'aya da kwana d'aya a yau ya huce ya zama tarihi Ummina."

Yayi maganar ajere a kuma wani irin haukace da tsananin k'arfi, tamkar ba shine babban malamin da duniyar musulunci ke alfahari dashi ba a cikin Jahar wasai, kana kuma har yanzu bai fasa kukan da yake yi ba.
Wanda hakan kuma ya sanya Bir da Gimbiya Tasmir shiga cikin matsanancin rud'u, kasancewar yanzu da harshen hausa yayi maganar, suma d'in kuma hausarce yarensu dama, shiyasa har suka fahimci komai daya fad'a.

Hakan yasa Bir yaji kansa ya k'ara mahukaciyar sarawa.
Yayinda jikinsa kuma ya d'auki kyarma, zuciyarsa kuwa wani irin harbawa take da azabar k'arfi, tamkar zata yaga fatar k'irjinsa ta futo waje.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir banda zubar hawaye tamkar anbud'e famfo babu abun da idanuwanta sukeyi.
Shi kuwa mai gadi cikin tsananin aljabi tare da ta'ajjudin da kalaman Sheikh Ahamd suka saukar masa ya fara zare idanuwa, yana mai kallon Bir da Gimbiya da suka riga suka futo daga cikin motar suma.

A cikin gida kuwa tamkar a mafarki Aishatu da Ishak' da suke zaune akan kujera suka jiyo sauti Sheikh Ahmad yana furucin daya kusan zautasu.
Kafin daga bisani kuma suka d'iba aguje har suna rige-rigen futa daga cikin d'akin.

Kakama kuwa da take a cikin d'akinta da sauri ta futo tana mai gyara d'aurin zaninta tare da fad'in.

"Yau kuma mahaukatane suka b'ullo masu ihu, su Sheikh an fara zarewa."

Ta k'arasa maganar tana mai kwashewa da dariya, tare da yin hanyar wajen da sauri itama.

A lokacin da Iyayen Sheikh Ahmad suka futa tini gaba d'aya sauran jama'ar da suke acikin gidan hatta da 'yan aikinsu sun futo compound d'in suma.

Cikin wani irin yanayi na tsantsar d'imuwa Aishatu ta tsaya cak, tana mai kallon photocopy d'inta, kana kuma yaron cikin mafarkinta a zahiri tsaye a gabanta, tana mai nunasa da yatsa.
Yayinda karankaf ilahirin jikinta kuma ya d'auki wata irin kyarma, tamkar wacce ake girgizawa.

Cigaba da kallon Bir tayi tana mai nunasa da yatsarta da take rawa, wasu irin hawaye na ambaliya daga cikin idanuwanta.
So take ta bud'e tai masa magana, amma gaba d'aya taji ta kasa, saboda yadda lab'b'an nata su kansu suke rawa, ga kuma wani irin nauyi da taji kanta yayi mata.

Shima Bir sosai ya d'imauce da ganin matar, yana mai kafe idanuwansa akanta.
Yayinda kowace tsoka ta ilagirin jikinsa take kyarma kuma.

Shi kuwa Ishak' cikin tsantsar firgici ya k'ame a wurin da yake yana mai bin matsashin saurayin da idanuwansa.
Shima d'in kuma banda karkarwa babu abun da ilahirin jikinsa keyi, yayinda idanuwansa kuma suke futar da ruwan hawaye da tsananin gudu, bakinsa kuwa hangame yake yana sakin wani irin murmushi, da yake tasowa tundaga k'asan zuciyarsa.
Ita kuwa Kaka da iyalin Sheikh Ahamd tare da sauran ma'aikatan gidan, gaba d'ayansu suman tsaye sukayi a wurin da suke, suna masu kallon Bir da kuma kyakkyawar budurwar da take a gefensa mai mayawaicin gashi.

Da k'arfi Aishatu da take jin k'afarta ta mak'ale ta funciketa, tana mai fara d'agata ta doshi wurin da Bir yake
Har lokacin kuma jikinta bai barmar kyarmar da yake yiba, kana kuma bata fasa nunasa da son bud'e bakin da take so tayi tai masa magana ba.

Tana gab da zuwa garesa kawai sukaga ta tafi luuuu! Tana mai zubewa a k'asa gaba d'aya numfashinta na d'aukewa!


*K'ASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAK'AR MASARAUTA.*

Gimbiya Tasmir da Bir idanuwansa suka gane masa alokacin da suka k'araso bakin k'ofa a cikin wutar.
Ga kuma lokacin da Shairma ta sari gaba d'aya dakarun k'ofa, sai dai kuma daga lokacin da suka fuce bai k'ara ganin komai ba, wato dai baiga hanyar da suka biba wutar ta komo jarta.

Cikin tsantsar firgici da kad'uwa ya d'ago jikinsa na rawa, yana mai watsa idanuwansa acikin na Sarki Barbaru.
Kafin daga bisani kuma ya bud'e baki cikin rawar murya, yana mai fad'in.

"Sun...gudune, sun bar BAK'AR MASARAUTA su biyun."

"Dakata Boka mai wutar kasko!!!
Kamarya sun gudu? Su waye ne suka gudu daga cikin Bak'ar Masarautar? Ina Gimbiyata ta tafine nace maka ne!?"

Sarki Barbaru yayi furucin a wani irin haukace, da kuma tsananin k'arfi.
Yayinda ita kuma Gimbiya Salwa ta d'ora hannu aka, tana mai sakin wata irin gigitacciyar k'ara.
Shi kuwa Boka mai hutar kasko, cikin tsantsar firgicin sanin da yay na yau alkadarinsa ya karye, ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Ita dashi, wannan yaron daya zamto mana Garkuwar Bak'ar Masarauta gaba d'aya, wato dai Bir da aka samesa shekaru talatin baya a cikin jirgin ruwa, tare da shi suka gudu har da kayansu."

Ya k'arasa maganar jikinsa na karkarwa.
Yayinda shi kuma Sarki Barbaru ya tsaya cak yana mai yin shiru, jikinsa na d'aukar kyarma, sabo da tsananin firgitar da yayi da kalaman Boka, wai 'yarsa Gimbiyarsa ce yake nufin ta gudu, tare da yaron da shi da kansa ya sanar musu da cewar har dai ya bar cikin Bak'ar Masarauta to k'arshensu yazo.

"Kai taya ma hakan zata faru, inaa da sake."
Ya raya haka acikin ransa yana mai bud'e baki tare da matsawa gaban Boka mai wutar kasoko cikin sauri, yana mai fad'in.

"K'arya kake Boka mai wutar kasko! Yau baka binciko gaskiya ba, k'aryane tarihina bazai tab'a shafewaba, labarina bazai b'acewa ba, duniyar Bak'ar Masarauta zata cigaba da hab'b'aka har k'arshen duniya. 'Yata kuma bazata tab'a guduwa ta barni ba, dan haka ka gaggauta sake sabon bincike akan idanuwana na gani nima."

Yayi furucin a wani irin haukace, yana mai tsayawa a gaban wutar kasko kusa da Boka.
Shi kuwa Boka mai wutar kasko, cikin rawar jiki tare da tsantsar firgici ya sake d'ibar k'ullikan abubuwansa yana mai fara zubasu a cikin wutar, tare da cigaba da surutansa.
A haka har wutar ta sake komawa koriya shar.
Tukun ya bud'e idanuwan nasa yana mai d'orasu a cikin tsakiyar wutar, tamkar yadda Sarki Barbaru ma yayi.

Ko kad'an sakamakon bai bam-banta dana farko ba, wanda kuma Sarki Barbaru yaga komai fes.
Hakanne ya sanya sa d'ago kansa cikin wani irin firgici da tsantsar tashin hankali, tare da tafasar zuciya, yana mai sa k'afarsa yayi ball da wutar kasko da matuk'ar k'arfi.
Take kuwa ta tafi tana mai dukan bango, tukun ta tarwatse wani irin hayak'i na futa daga cikinta bayan ta mutu.
Kana ya juyo b'arin da Boka mai wutar kasko yake a wani irin haukace, yana mai fad'in.

"Inaaa k'aryane wallahi, babina bazai tab'a shafewa ba adoron duniya.
Dan haka kayi maza-maza ka dubo mun hanyar da sukabi Boka."

Cikin tsantsar firgici da tashin hankalin ganin yadda Sarki Barabaru ya fasa wutar kasko, Boka ya bud'e bakinsa da yake rawa yana mai fad'in.

"Babu wata hanyar yakai Shugaba, wannan dama ita kad'aice hanyar da tayi saura, kuma gashi ba muga k'arshenta...."

"Yimun shiru Boka. Kasan da haka me yasa tun farko ka kasa sanar dani cewar suna shirin guduwa? Me yasa tun farko ka kasa fahimtar shi yaron zai tafi, bayan kai da kanka ka shaidamana cewar shine duniyarmu hatta da kai kanka a shekaru talatin har da d'aya da suka shud'e a baya?
Me yasa a yanzu kuma zakace mun babu wata hanya? Shin kana nufin kace mun shikenan na rasa 'yata? Sannan kuma duniyarmu tazo k'arshe, kafaffen tarihin BAK'AR MASARAUTA zai goge, zamanin mu zai shafe adoron duniya.
Inaaaa hakan bazai tab'a yuwuwa ba, k'arya kake Boka, kasan da haka zata faru amma ka hana na kashesa tun a wancan lokacin, kasa na rayu wuri d'aya da mak'iyina ina kaffa-kaffa da rayuwarsa, gashi kuma yanzu yayi mun babbar illah ya tafar mun da 'Yata.
Dan haka kasani tamkar yadda na rasa 'yata, kaima sai karasa numfashinka a yau, a kuma wurinnan Boka mai wutar kasko."

Ya k'arasa maganar a wani irin haukace, yana mai funciko wata irin takobi, tare da kibiya mai tsini a cikin jikinsa
Da matuk'ar sauri Iyalansa suka d'ora hannuwa aka, suna masu zaro idanuwa tare da sakin ihu.

Yayinda shi kuma Boka mai wutar kasko ya fara ja da baya, jikinsa na d'aukar wata irin kyarma.

Shi kuwa Sarki Barbaru taku biyu kawai yayi ya cimmasa.
Hakan yasa ba tare daya tsaya wata-wataba ya d'aga kibiyar yana mai sauketa asaitin k'awon zuciyarsa.

Wata irin gigitacciyar kuma razananniyar k'ara mai matuk'ar figitarwa Boka mai wutar kasko ya saki, kafin daga bisani kuma gaba d'aya d'akin ya d'auki wata irin k'ara.

Luuuuu yayi baya yana shirin b'ingirewa, hakan da Sarki Barbaru ya ganine kuma yasa cikin zafin rai ya k'ara d'ago takobin da take rik'e a hannunsa yana mai fille wuyansa da ita.

Fiiiit!
Kuwa kakejin k'arar yanke kansa gaba d'aya daga jikin wuyansa, tukun ya fad'i a k'asa bayan ya saki wata irin doguwar k'ara, alamun ran ya gama fucewa kenan, wato shima dai yau k'arshensa yazo, yayi mutuwar hulak'anci da k'ask'anci tamkar yadda ya dinga sawa ana kashe mutane.

Ganin hakan da Iyalan Sarki Barbaru sukayine, ya sanyasu fucewa waje a guje suna masu sakin ihu.

Shi kuwa Babban d'ansa ko kad'an baiji wani abu ba dan gane da mutuwar Boka, asalima sai ganin kyautawar Mahaifinsa yayi daya kashesan, domin kuwa bada ban shiba da tini yanzu suna tare da 'yar uwarsu, saboda da tun a wancan lokacin za'a kashe Jaririn tamkar yadda akayiwa sauran.

Da matuk'ar sauri Sarki Barbaru ya juya ransa a wani irin mugun b'ace, yana mai yin wajen shima.

Cikin tsakiyar mutanen nan ya tsaya yana mai fad'in.

"Maza-maza a d'ebi kayan yak'i a hau jirage abi kowace hanya, duk jirgin da aka samu a caje mutanen cikinsa, ina son kafin nan da fad'uwar rana ku tabbatar kun kawo mun su gabana."

Ya fad'a yana mai nuna wasu dakaru da suke tsaye a wuri d'aya, suma gaba d'ayansu a matuk'ar rud'e.
Kana ya nuna wasu dakaru biyu yana mai fad'in.

"Ku kuma yanzu nake so ku huce b'angaren Bayi, ku d'auko mun Iyar Bayi dana bawa rik'onsa ku kai mun ita d'akin azaba!"


*K'ASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR FUL'DE.*

K'arfe shabiyu na rana dai dai tayi musu abakin part d'in su.

Da sauri Gimbiya Haddiyal ta bud'e murfin motar tana mai fucewa, sabo da gaba d'aya hankalinta yana wurin mafarkin da tayi jiya.
Hakan yasa take so taje tayi bincike dan taga abunda ke faruwa.

Da 'yar sassarfarta ta shiga cikin falon nasu.
Tana shirin hucewa cikin d'akinta ne kuma taji sautin muryar Daddenta tana mai fad'in.

"Ke kuma lafiyarki k'alau kuwa?"

Turus! Taja ta tsaya a wurin da take.
Kafin daga bisani kuma ta juyo da fuskarta a hankali, tana mai kallon mahaifiyarta, kana ta durk'usar da kanta k'asa tana mai juyawa ta dawo wurin mahaifiyarta.

"Ina kwana Daddena.!"
Ta fad'a asanyaye tana mai durk'usar da kanta k'asa.

"Lafiya k'alau har kun dawo ne?"
"Eh Daddena."
Ta fad'a a hankali tana mai k'ara mik'ewa ta juya ta tafi.
A kuma lokacin Habu shima ya shigo cik, yana mai yowa wurin Mahaifitar tasu.

Ita kuwa Gimbiya Haddiyal da matuk'ar sauri ta k'arasa cikin d'akinta.
Da sauri ta cire kayan jikinta tana mai sanya nasu na fulani, kasancewar tafi jin dad'insu sama da kowane kaya.
Kana ta juya tana mai tafiya ta bud'e wannan 'yar k'ofar da take a cikin d'akin nata.

Sandar tsafinta ta gado ta d'auko, tukun ta futo tana mai bi ta k'ofar baya ta fuce.

Cikin sauri take tafiya tamkar zata tashi sama.
A haka har ta isa gaban dank'areriyar bishiyar nan mai kogo.
Kana ta jingine sandar tsafinta ajikin bishiyar, sannan ta durk'usa k'asa tana mai sa hannu ta d'auko kaskon nan, tare da k'ullikan tsummokaranta.
Tukun ta tsiyaya wani ruwa a cikin kaskowan, kana ta zuba wasu iccina aciki, sannan ta bud'e garin wani icce tana mai bad'asa a ciki shima.
Tukun ta mik'e tsaye bayan ta dunk'ule wasu layoyi acikin tafin hannunta, tana mai fad'in.
"Zaiba! Zaiba!! Zaiba!!!"

Haka tai ta mai-maitawa da sauri tana mai zagaye kaskon.
Tukun daga bisani ta bud'e idanuwanta akansa.

Cikin wani irin yanayi ta durk'uso k'asa da matuk'ar sauri, tana mai sake bud'e k'wayoyin idanuwanta akan ruwan.
Yayinda jikinta kuma ya d'auki kyarma.
Sabo da ganin ruwan da tayi ya koma fari daga yalon da yake, kana kuma sai wata hanya ta bud'u a cikinsa.
Daga nan kuma sai taga Jihar Wasai acikin ruwan cikin tsakiyar garin ma kuwa.
Sai dai kuma bayan nan ba ta sake ganin wani abunba.

'Dan rumtse idanuwanta tayi, tana mai farayin nazarin abunda ta gani.
Kafin daga bisani kuma ta d'ago da matuk'ar sauri tana mai fad'in.

"Wayyo dad'i Gid'ad'o am na cikin Jahar Wasai. Hak'ik'a ba da ban kona tafi yanzu ba bazan isaba sai dare, da babu abun da zai hanani komawa, amma gobe asuba zamuyi, kuma na sani ruwan randa zai kain har mazauninka."

Ta k'arasa maganar cikin wani irin matsanancin farinciki, irin wanda tunda tazo duniya bata tab'a tsintar kanta a cikin makamancinsa ba.

Take kuwa duk wata damuwar da take k'unshe a cikin ranta data dawo da ita taji ta yaye tas.

Tukun ta fara mayar da kayan nata wuri d'aya.
Kana a k'arshe ta d'auki randar tana mai rungumeta a hannunta, saboda da ita zata tafi gobe, itace zata kaita har wurin da yake.

Tana shirin juyawa ta tafi taji motsin gudu a bayanta.
Hakanne ya sata juyawa da sauri dan taga abun da ke faruwa.

Buba amintaccenta ne ta gansa ya tawo fuskarsa d'auke da annuri.
Da sauri itama kuwa ta juya b'arin da yake tana mai sakar masa murmushi.

"Allah ya k'ara lafiya uwar d'akina, hak'ik'a yau nazo miki da daddad'an labarin da nake da tabbacin zai sanyaki murmushi."
Buba ya fad'a da sauri cikin harshen filatanci, yana mai durk'usar da kansa a k'asa.

"Ina maraba da jin labarin Gid'ad'o am daga bakin Buba am a kowane lokaci."

Itama ta fad'a murmushin kan fuskarta na k'ara bayyana.

"Yau na gano wurin da Gid'od'anki yake Gimbiya, wato dai yana cikin garin Jahar Wasai, sai dai kuma wurin da yake a zaune ne kawai ban ganiba."

"Bincikenmu ya bada amsa d'aya kenan."

Ta fad'a cikin tsantsar farinciki.
Kana ta d'ora da fad'in.
"Karka damu da wurin da yake, tabbas gobe idan mun tafi ruwan randa zai kaimu har wurin da yake da zarar mun isa Jahar Wasai, dan haka abun da zakayi kai kawai a yanzu shine. Kaje kasamar mana motar da zata kaimu har can, gobe da asuba zamu tafi."

"An gama Uwar d'akina."
Ya fad'a yana mai juyawa ya tafi.
Kana itama ta juya ta tafi, tana mai jin farinciki tako ina tattare da ita.
Hak'ik'a lokaci yayi da zata tabbatarwa da duniyar masarautar fuld'e Gid'ad'onta mutum ne ba aljanba, tamkar yadda suke tsamanni.


*JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI."

Tunda Babban Yaya ya tafi ya barsa yake zaune a wurin, yana mai sak'a yadda za'ayi ya sanya manyan kaya a jikinsa gobe, domin kuwa a goben zai koma wurinta ko Allah zai sa ya dace.
Hakan yasa bayan ya gama tinane tinaninsa ya tashi yana mai zuwa ya bud'e wani b'angare na cikin kayansa. Wanda kuma ya kasance manyan kayane a cikinsa gaba d'aya.

Kallon kayan ya farayi, yana mai jin tsigar jikinsa na wani irin tashi, kana gefen kansa na d'an sara masa.
Hak'ik'a ko son ganinsu bayayi kwata-kata a rayuwa, shiyasa ako da yaushe ma da zarar Mai Martaba ya aiko masa dasu yake sanyasu anan ya ajiye, sabo da har yau idan zaiyi d'inki tare yake musu, a cewarsa wataran zai sanyasu, yanzun harda yarinyata tasa yake abun da yakeyi.

Ya jima yana kallon kayan jikinsa a sanyaye, kafin daga bisani kuma ya rufeta yana mai rumtse idanuwansa, tare da komawa ya zauna akan gado yaraf.

A b'angaren Gimbiya Fulani kuwa, sosai tayi matuk'ar farinciki da jin labarin gobe Zakinta zai sanya manyan kaya a bakin Babban Yaya.
Hakan yasa har tayi tinanin Allah ne ya amshi addu'ar da take aikinyi ako da yaushe, shiyasa har ya d'ora masa soyayyar Gimbiya Haddiyal a zuciyarsa domin ta zamto sanadin shiryuwarsa.

Ita kuwa Fa'iza tun jiya bayan dawowarta daga wurin party azababben zazzab'i ya rufeta, sabo da tabbatarwa kanta da tayi na tarasa Yarima har abada, d'iyar sarkin fulanin da taji ana fad'i ta kuma ganta ta k'wace zuciyarsa.

A b'angaren Babban Yaya da mai martaba kuwa, basu rabu ba har sai da suka tsayar da magana akan jibi za'aje Masarautar Fuld'e a nemarwa Asad auren Haddiyal.


*BABAN ZAURE LOCUS.*

Cikin tsantsar firgici, rud'u, had'i da tashin hankali gaba d'ayansu sukayi kan Ummi, har suna rige-rigen isa gareta.

Da sauri Sheikh Ahmad ya rigasu k'arasawa wurin tare da durk'usawa k'asa yana mai ciccibarta a hannunsa.
Kana yayi cikin gidan da ita a guje, yana mai kuka tare da fad'in.

"A'a Ummina, a'a Ummina karkiyi mun haka, karki tafi ki barmu, ki tashi lokacin farincikine yazo bana kukaba, ki tashi ga d'anki nan ya dawo, Allah yau ya cika miki burinki, ki tashi Ummina, ki tashi muna buk'atarki d'anki da bai tab'a jin d'umin jikinki ba yana buk'atarki rungumesa a yanzu."

A wani irin haukace yake fad'in haka cikin kuka, yana mai girgizata a haka harya k'arasa zuwa cikin falonsu.

Akan kujera ya direta, yana mai juyawa da niyyar ya d'auko ruwa, sai kuma yaga har matarsa ta mik'o masa ma, hakanne ya sanyasa fara k'ok'arin bud'e murfin jarkar da tsananin sauri, hannunsa na rawa.

Shi kuwa Abba ganin da yayi kowa ya dawo cikin falon banda bak'in nasu ne, ya sanyasa komawa da sauri compound d'in.

Da sauri ya k'arasa wurin da Bir yake yana mai bud'a masa hannuwansa biyu, tare da fad'in.

"Tawo tawo gareni d'ana, tawo jikin Abbanka ashe da rabon zamu saka a cikin idanuwanmu."

Ya fad'a cikin kuka jikinsa na rawa.
Da sauri shima Bir da yake kukan sosai, gaba d'aya ya jik'e sharkaf da gumi yayi wurinsa.

Yana k'arasa kusa dashi ya shige cikin k'irjinsa da wani irin sauri, tukun shi kuma Abba ya lumshe idanuwansa, yana mai sake rungumarsa da wani irin k'arfi, tamkar zai maidasa cikin jikinsa.
Kafin daga bisani kuma ya fara sakar masa wasu irin sumba a tsakiyar kansa, yana mai cigaba da kuka jikinsa na karkarwa.

Shima Bir d'in kuka yake, yana mai k'ara ruk'un-k'ume dattijon da yajisa ajikinsa, jiki mai tsanain dad'i da wani irin d'umi, irin wanda bai tab'a jin makamncinsaba a jikin wani a duniya.
Ta yadda har hakan ya sanya ko wace jijiya ta jikinsa ta fara d'an harbawa, yayinda tsokokin jikinsa kuma suke karkarwa, yana mai k'ara ruk'unk'ume mutumin, tare da sauke wasu irin tagwayen ajiyar zuciya..............✍




_Umar Dayyan_


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*21*



Wata irin nutsuwa sukaji tana saukar musu a cikin jikinsu gaba d'ayansu su biyun.
Yayinda had'uwar jikinsu wuri d'aya kuma ta sanya jinjin jikinsu k'ara gudu fiye da yadda yake ada.

Sun d'auki tsayin mintina har kusan shida ahaka suna rungume da juna.
Yayinda Gimbiya Tasmir kuma take tsaye a wurin da take tana mai kallonsu, tare da jin tausayinsu na matuk'ar lullub'eta.
Kafin daga bisani kuma Ishak' yasa Hannuwansa biyu, yana mai b'anb'aro Bir daga cikin jikinsa.
Tukun ya shafa sumar kansa yana mai fad'in.

"Alhamdulillahi ya Allah."
Kana ya rik'e hannunsa yana mai d'aga ido ya kalli Gimbiya Tasmir, tare da fad'in.
"Mushiga ciki d'iyata."

Ya fad'a fuskarsa d'auke da murmushi, har lokacin kuma hawayensa basu tsaya ba.
Tukun yayi gaba rik'e da hannun Bir, itama Gimbiya Tasmir ta take musu baya jikinta a tsantsar sanyaye.

Shi kuwa Sheikh Ahmad cikin sauri ya tsiyaya ruwan a tafin hannunsa.
Kana ya yarfawa Ummi a fuskarta da k'arfi.
Hakan yayi har kimnin sau ukku, tukun daga bisani taja wata doguwar ajiyar zuciya da k'arfi, tana mai bud'e idanuwa.
Hakan daya ganine yasa ya durk'usa k'asa yana mai damk'ar tafin hannunta.

Yayinda ita kuma ta juyo da kanta b'arin da yake, tana mai bud'e baki cikin sanyi tace.

"Ina yake? Ina Jaririna? Dan Allah karkuce mun mafarkine nayi ba azahiri na gansa ba. Tabbas shine na gani, ashe da gaske ne basu kashe mun shi ba.
Yana ina ku kawo mun shi na gansa."

Ta fad'a hawaye na cigaba da tsiyaya daga cikin idanuwanta.

A kuma lokacin Abba da yake rik'e da hannun Bir Gimbiya Tasmir na biye dasu abaya suka k'araso wurin.
Hakanne ya sata mik'ewa zaune zumbur akan

Please Login or Register in order to submit comment