Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yarima Asad ya d'ora da fad'in.

"Ina mai gargad'inki da babbar murya, akan koda wasa, karki k'ara kuskuren gigin barin hannunki ya kusanci jikin matata.
Idan kuma har ki kai kuskuren mai-maita hakan, to ki sani tabbas zan karyasa, domin kuwa ta fiye mun ke a komai, asalima itace duniyata ahalin yanzu."

Ya sake fad'e cikin amo yana mi cigaba da sakin huci.

Ita kuwa Gimbiya Haddiyal cikin wani irin sauti ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Me yasa ka dakatar da ita? Da kabarta! Da kabarta ta mareni. Hak'ik'a da kin bambance tsakanin aya da tsakuwa a yau a wurin nan.
Kuma da nace miki karuwa kice k'aryane ba k'aruwar bace ke?
Ki dubi jikinki fa ki gani ina marabar taki take da karuwa, wata macen arzik'ince zata futo ta tsaya gaban maza da irin shigar jikinki bayan karuwa.
Sa'arki d'aya, itace banayinsa, kuma ba zanyisa ba, Gid'ado shine kai d'ai mutumin da nake so, kuma zan cigaba da sonsa har k'arshen rayuwata, amma ki sani bada ban hakaba, da daga yau kin gama ganin murmushi akan fuskarsa."

Ta k'arasa maganar tana mai janye idanuwanta daga cikin na Billi da tini hawayen bak'incikin abun da Yarima Asad yayi mata sun jik'a fuskarta, tana mai shirin juyawa ta tafi.
Ganin hakan da Yarima Asad yayi da kuma jin abun da tace ne, ya sanya sa mik'a hannunsa da sauri yana mai cafko yatsun hannun Haddiyal dasu.
Yayinda jikinsa kuma ya d'auki wata irin karkarwa, gaba d'ayansa ya rud'e hankalinsa ya tashi.

Jin hakan da Gimbiya Haddiyal tayine ya sanyata sake tsayawa, tukun ta juyo cikin tsantsar b'acin rai tana mai kallon yatsun hannuwansu da suke sark'e wuri daya, kana ta janye idanuwan nata daga kan yatsun tana mai mayar dasu cikin na Asad.

Ganin hakan da yayine ya sanyasa bud'e baki cikin rawar murya, yana mai fad'in.

"Kiyi hak'uri dan Allah, bansan zatayi miki hakaba."

Ya k'arasa maganar muryarsa na rawa.
"Sakar mun hannu."
Itama ta fad'a atak'aice still tana kallonsa.

Hakan da Yarima Asad yajine ya sanya sa girgiza mata kansa.
Kana ba zato ba tsammani sai kawai gani jama'ar wurin sukayi ya zube gwiwoyinsa a k'asa yana mai had'e tafukan hannayensa wuri d'aya.
Kana ya sake bud'e baki cikin rawar murya, yana mai fad'in.

"Na rasa walwalata, na dena duk wani nisahad'i, akullum zuciya cikin bugu take da tsananin k'arfi dominki, gangar jiki da ruhina na matuk'ar wahala ta sanadin sonki.
Ina miki so irin wanda baki bazai iya misaltasa ba.
Kiyiwa Girman Allah, kiyiwa darajar mahaifanka, ki soni ko da kwatankwancin irin son da nake miki ne."

Yarima Asad ya fad'a a fili, What kana kuma cikin rauni tamkar zai fashe da kuka.

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'u!!!"
Kusan gaba d'aya jama'ar da suke a cikin wurin suka fad'a, suna masu d'ora hannuwansu a tsakiyar ka, domin kuwa ba k'aramun gigitasu kalaman Asad sukayi ba, kasancewar kuma gaba d'aya wa'yanda suke a wurin sun san halinsa.

Su kuwa abokansa na Dubai suman tsaye sukayi, gaba d'ayan su suka kasa koda k'wak'k'waran motsi, sai idanuwa kawai da suka zuba masa suna kallonsa cikin tsantsar firgici.

Yayinda 'yan cikin masarautarsu kuma suka zazzaro idanuwa waje suna kallonsa tare da kallon Haddiyal.
Atak'aice dai duka wurin babu wanda bai girgizaba da abunda Asad ya aikata.
Domin kuwa ko a mafarki basu tab'a tinanin zasuga Asad ahaka ba.

Wai yau Asad ne da mata sukebi ko kallo basu ishesaba yana hulak'antasu, shine a durk'ushe a gaban mace yana rok'onta tasosa.
Tabbas inda ranka kasha kallo.
Kusan kowane mutum dake cikin wurin ya raya haka acikin ransa.

Su kuwa k'awayen Billy gaba d'aya daskarewa sukai a wurin da suke, suna masu kallonta tare da kallon su Asad, domin kuwa ba k'aramun girgiza sukayi ba da abun da ke faruwa.
Yayinda Zee kuma ta tab'e baki tana mai fad'in.
"Ke kika jawa kanki."

Ita kuwa Billy cikin tsantsar kad'uwa, firgici, had'i da tashin hankalin da kalaman Yarima Asad da kuma durk'ushen da taga yayi a k'asa suka sanyata, ta d'ora hannuwa biyu aka tana mai fashewa da wani irin gigitaccen kuka.

Sosai jikinta yake kyarma tamkar wacce aka sanya a cikin ruwan sanyi, yayinda idanuwanta kuma sukayi wani irin kad'awa sukai jajajir tamkar gauta.
Wai yau itace haka Asad ya hulak'anta abainar jama'a, yaci mutuncinta, ya zageta ya aibata ta, duk da haka bai tsaya anan ba sai da har ya nunawa duniya cewar baya sonta ga wacce yake so.
Sosai take wani irin kuka tana mai kallon Asad da Gimbiya Haddiyal.

Itama Gimbiya Haddiyal sosai durk'ushen da taga yayi a gabanta ya firgita ta, sai dai kuma hakan ba shine zai sanya taji sonsa ba a zuciyarta, sabo da Gid'ad'onta ya riga daya cike ko ina.
Wannan dalilin yasa ta bud'e baki cikin sanyi, tana mai fad'in.

"Ba zan iyaba, bana sonka, kuma ba zan tab'a soka ba."

Ta fad'a tana mai girgiza masa kai itama.
Yayinda shi kuma ya rumtse idanuwansa da matuk'ar k'arfi, jikinsa na d'aukar kyarma, kana daga bisani ya sake bud'esu acikin nata.
Tukun ya sake d'aga lab'b'ansa cikin rawar murya, yana mai fad'in.

"Idan kika barni mutuwa zanyi, zuciyata zata buga, dan Allah ki soni ko yayane n..."

"Nima idan na soka mutuwa zanyi, zuciyata bugawa zatayi."

Ta katse sa da fad'in haka wasu irin hawaye masu tsananin gudu na b'allewa daga cikin idanuwanta.

Sharr sharr sharrr.
Haka shima Yarima Asad idanuwansa suka fara tsiyayar da ruwan hawaye da matuk'ar gudu.
Tukun ya sake bud'e baki cikin rawar murya, yana mai cewa.

"Ki fad'i kome kikeso a duniya, nayi alk'awarin yi miki shi duk tsananin wahalarsa muddin zaki soni.
Hak'ik'a zuciyata na wahala, gangar jikina na jigata, idan kika tafi kika barni rayuwata zata lalace"

Da sauri itama ta katsesa da fad'in.

"Shine kad'ai mutumin da nake so, na fara sonsa tun ban san meye so ba, na fara sonsa tun ina da k'arancin shekaru.
Shin tayaya kake tinanin zan iya jure rasasa, idan har kai da ka ganni a kwanan nan ka kasa.
Ka sani nima ina jin duk yadda kakeji, inajin rad'ad'i da k'unar da kakeji a zuciyata akan Gid'ad'o am.
Itama kuma waccan tanaji irin haka akanka.
To tunda hakane mai zai hana ba zaka rabu dani ba kaso mai sonka, nima ka barni da wanda nakeso ko zuciyoyinmu sa samu salama. Sabo da nima idan ban samu Gid'ad'o ba zuciyata bugawa zatayi!"

Ta k'arasa maganar tana mai juyawa ta tafi da sauri, wasu irin hawaye na cigaba da ambaliya daga cikin idanuwanta.

Da sauri Habu da yake tsaye a gefe yana sharar k'walla yabi bayanta, gudun kartayi wani wurin daban idan ta futa, saboda ya lura gaba d'aya bata cikin hayyacinta.
Hak'ik'a daya san irin abunda zai faru kenan da bai janyota sunzo ba.

Shi kuwa Yarima Asad da k'arfi ya dunk'ule hannunsa yana mai kaiwa iska naushi.
Kafin daga bisani kuma ya bud'e baki cikin wata irin murya mai tafe da kuka yana cewa.

"Wallahi ina sonki, kuma kowane shi dole ya barmun ke, sabo da bazan iya rayuwa ba idan babu ke."

Ya k'arasa maganar yana mai kifewa a k'asa tare da dirza kansa akan grass capet d'in da yake a cikin wurin.

Da gudu Al'amin dake kukan tausayin Asad yayi kansa yana mai k'ok'arin d'agosa.

Yayinda jama'ar wurin kuma masu d'aukar video a wayoyinsu tun lokacin daya durk'usa a gaban Gimbiya Haddiyal, suka fara mayar da wayoyinsu aljihu.

Ita kuwa Baby sosai take kuka, sabo da ganin yadda yayan nata da bata tab'a ganin ko k'walla acikin idanuwansa ba tunda ta taso yake kuka.
Yayinda Fa'iza kuma tayi cilli da gift d'in da tayi niyyar bawa Asad, wanda yake k'unshe da letter a cikins, tana mai fucewa a guje daga cikin wurin cikin tsantsar kuka mai cin rai.

Haka dai gaba d'aya masoyansa suka dinga fucewa zuciyarsu a matuk'ar dagule.
Yayinda wasu kuma daga cikin jama'ar wurin da sukayi video suka fara watsasa a social media.

Ita kuwa Billy cikin tsantsar bak'inciki da k'unar zuci ta zube gwiwoyinta a k'asa, tana mai sake rushewa da wani irin gigitaccen kuka mai cin rai da sosa zuciya.
Yayinda take ji aranta kuma shikenan yanzu Asad ya gama zubar mata da mutunci, babu ita babu wani sauran kuri akansa wurin k'awaye.
Tabbas da ace zataga Haddiyal, da babu abunda zai hanata ta shak'e mata wuya har sai taga ta dena numfashi sannan ta barta.

Shi kuwa Al'amin dak'yar ya samu ya iya d'ago Yarima Asad idanuwansa na zubar k'walla.
Tukun ya dafasa suna masu yin wurin motarsu hannunsa dafe da k'irjinsa.
Sabo da yadda yake jin zuciyarsa na masa wata irin suya, ga kuma wutar sonta da take k'ara ruruwa a zuciyarsa amai makon ta ragu.

Hak'ik'a so bala'i ne, kuma masifane idan baka samu yadda kakeso ba a cikinsa.
Ji yake inama ace mutuwa yayi da zuwan wannan ranar.

Ba tare da Al'amin ya tsaya bi takan bak'insu ba ya bud'e murfin mota yana mai sanya Asad a ciki, kana shima ya shiga yana mai rufeta ya fafareta a guje, domin kuwa gaba d'aya ji yay haushin bak'in nasu ya turnuk'esa, sabo da yadda yaga da yawa daga cikinsu suna d'aukar videon abun daya faru, wato dai dan suji dad'in nunawa duniya, su abun ma dad'i yayi musu Asad ya durk'usawa mace kuma yay mata kuka.

Ganin da jama'a sukayi kowa ya watse ne, ya sanya duk suka fara fucewa daga cikin wurin.
Haka suma masu kayan kid'a suka fara kwashe kayansu.
Gaba d'aya dai taro baiyi armashi ba ko kad'an tamkar yadda aka zata zaiyi.

Ita kuwa Billy har lokacin duk'ushe take a k'asa tana mai cigaba da gurshek'en kuka tamkar ranta zai futa.

Sai da duk aka gama watsewa, tukun k'awayen Billy da jikinsu yake a matuk'ar sanyaye suka k'arasa wurin da take suna masu d'agota, tukun suka doshi wurin motarsu Zee na cewa.

"To ai ga irinta nan, yau kin tabbatar da abun da na dad'e ina fad'a miki.
yanzu kinga ai ko shine kad'ai ya rage namiji aduniga kya rabu dashi.
Ace kamarki, da girman ki, a matsayinki na 'yar gwamna namiji yaci mutuncinki abainar jama'a har mutane nayin video. Ai wallahi wannan cin mutuncin ba iya ke kad'ai yayiwa shiba, hatta da su Dady ya hulak'anta, kuma ba kowa yaja musu hakan ba face ke."

Ta k'arasa maganar cikin masifa tana mai zama a cikin motar itama.
Tukun suma suka fafareta suna masu fucewa daga cikin wurin aguje.


*K'ASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAK'AR MASARAUTA.*

Babu wanda Allah ya kawo bakin k'ofar masarautar ballantana har yaga mutanen da suka zamto gawa har sai da asuba tayi.
Shima kuma an gansu ne ta sanadin bak'in da suka k'araso alokacin.

Ai kuwa cikin tsantsar firgici da rud'u mutanen da suka riskesu a sheme a k'asa sukayi ciki aguje suna sakin ihu.

Kafin kace wani abu kuwa tuni wurin ya cika mak'il da jama'a harda su Sarki Barbaru.

Cikin matuk'ar firgici Sarki Barbaru ya fara bin dakarun da kallo hankalinsa a bala'in tashe, sabo da shi duk a zatonsa ko harine aka kawo musu.
Hakan yasa cikin rud'u ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Ayi maza maza a futo da kayan yak'i, sannan kuma wani ya huce ya kiramun Boka mai wutar kasko."

Ko rufe bakinsa bai gama yiba suka hango tawowa Boka mai wutar kasko a durk'ushensa, shima d'in gaba d'aya hankalinsa a tashe.
Yayinda su kuma sauran dakarun suka tafi da gudu domin su aiwatar da abun da Sarkin nasu ya sasu.

Shi kuwa Boka mai wutar kasko yana k'arasowa wurin ya durk'ushe a gaban na farko.
Kana ya fara duban wuyansu da d'ai-d'ai da d'ai-d'ai.
Tukun bayan d'an wani lokaci ya d'ago a firgice yana mai watsa idanuwansa akan fuskar Sarki Barbaru.
Sannan ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Dafin Shairama ne ya kashe su!"

"Shairama kuma? Me yasa 'Ya zata turo Shairama ta kashe mun dakaru? Kaiii ka sake dubawa dai Boka."

Sarki Barbaru ya fad'a yana mai girgiza kai, domin kuwa shi ko kad'an bai yadda ba Shairama ce tai musu haka, sabo da yasani Shairama tana amfani da fad'ar Gimbiya Tasmir ne, kuma babu abun da zaisa Gimbiya Tasmir ta kashe masa dakaru.

"Na gama dubana tabbas Shairama ce, sai dai kuma aje aji dalilin daya sa hakan ta faru daga bakin Gimbiya."

Cewar Boka mai wutar kasko yana kallon Sarki Barbaru.

Ai kuwa da sauri Sarki Barbaru ya juya yana mai dosar hanyar da zata mai da sa b'angarensu tamkar zai kifa a k'asa tsabar sauri.
Yayinda suma sauran jama'ar ciki kuwa har da Boka mai wutar kasko suka rufa masa baya, kowa burinsa bai huce yaji dalilin dayasa Shairama ta saresu ba.


*JIRGIN RUWA.*

Tunda jirgin ya baro Jarhar Markuz sau d'aya kawai suka tsaya a wata jaha, alokacin ma sun futa daga cikin K'asar Malin duka sukai siyayya.
Tukun kowa ya dawo aka cigaba da tafiya.

Misalin k'arfe tara na dare jirginsu ya tsaya a tashar jirgin ruwa ta K'asar Hausa.
Hakan yasa gaba d'aya jama'ar cikin jirgin suka fara furfutowa cikin farinciki.

Gaba d'ayansu daga masu sakin hamma sai masu mik'a, domin kuwa ba k'aramun gajiya sukai ba.

A b'angaren su Bir kuwa, kasancewar tun misalin k'arfe hud'u na yamma wani irin azababben zazzab'i ya rufesa.
Shiyasa ko a yanzu da ake futa su gaba d'aya suka kasa ko motsawa daga wurin da suke.

Sosai jikinsa ke wata irin karkarwa, hak'waransa na had'uwa da juna.
Yayinda fuskarsa kuma tayi wani irin jajajir. Banda mak'alk'alewa a jikin Gimbiya Tasmir babu abun da yake iyayi.
Ita kuwa hawaye kawai ke zuba daga cikin idanuwanta, tana mai shafa lallausar sumar kansa tare da k'ara ruk'un-k'umesa.

"Ya ku futo mana ku kad'ai ne kukai saura, ko kuwa bakusan an iso bane?"

Muryar d'aya daga cikin matuk'an jirgin ta daki dodon kunnen Gimbiya Tasmir.

Da wani irin sauri Bir ya k'ara shigewa cikin jikinta yana mai rungumeta, sabo da jin da yake tamkar idan ta mik'e tsayen sanyi zai lahantasa.
Yayinda ita kuma ta d'ago kai hawaye na zuba daga cikin idanuwanta, tana mai kallon mutumin.
Kana ta bud'e baki cikin kuka tana mai fad'in.

"Kamana hak'uri mu kwana anan, in yaso da safe sai mu tafi kaga mijina ne bashi da lafiya."

"Dan kuma kawai mijinki bashi da lafiya shine zai zamto a barku ku kwanar mana a jirgi.
Kinga Baiwar Allah kawai kiyi maza ki futo tun kafin Oga ma ya k'araso."

Mutumin ya fad'a da k'arfi yana mai nuna mata hanya.

Jinjina masa kai kawai ta iyayi ba tare da tace komai ba.
Tukun ta fara k'ok'arin mik'ewa tsaye, amma sai taji Bir ya k'ara kanan-nad'eta jikinsa na cigaba da karkarwa.
Hakan yasata durk'uso da kanta a hankali, tana mai kawosa kan fuskarsa.
Kana ta fara murza gashin kansa da tafin hannunta, tana mai bud'e baki hawayen idanuwanta na d'iga akan fuskarsa tace.

"Tashi Jarumina, ka tashi mutafi waje kaji, Ubangiji Gargabilu zau baka lafiya."

"Iyata!"
Ya fad'a a hankali, hawaye na tsiyayowa daga cikin idanuwansa shima.

"Kayi hak'uri muje waje mu samu wuri, Iya batanan, ka manta mun bar gida ne."
Ta fad'a tana mai d'ago kansa.

Hakan daya jine ya sanye sa fara k'ok'arin mik'ewar jikinsa na karkarwa.

Cikin zubar k'wallar ta da fasa jikinsa na wata irin rawa, suna masu kama hanyar waje.

Sosai duhu ya bayyana a wurin, wanda hakan kuma ya sanya taji wani irin tsoro ya dirar mata a zuciya, sabo da ita dai bata saba da wannan k'asarba, asalima yauce ranarta ta farko da tazo cikinta.

A hankali suke tafiya Bir na ruk'un-k'ume da ita, har suka k'arasa wurin rumfar wani mai shayi da sukaga ba kowa anan.
Tukun Gimbiya Tasmir ta zaunar da Bir tana mai shirin mik'ewa tayi gaba, amma sai taji ya rik'o hannunta gam.

Hakan yasata bud'e baki cikin kuka tana mai fad'in.
"Kayi hak'uri kaji Jarumina, jakun-kunan mu zanje na d'auko mana sai na dawo yanzu."

Ta k'arasa maganar tana mai fucewa, saboda hannun nata daya saki.

Jan jakun-kunan ta farayi dak'yar tana mai yowa waje dasu.
Yayinda takobinta kuma da take a cikin d'an gidanta ta mak'aleta a hammatarta.
A haka har ta futo dasu duka daga cikin jirgin.
Tukun ta cigaba da jansu tana nishi.
So take ta tsaya ta huta, amma idan ta tuna ta barosa shi kad'ai sai taji ba zata iyaba.

A haka dai taita ja har ta k'arasa cikin rumfar da k'yar.

"Sannu kaji Jarumina, kaga har na dawo ko."
Ta fad'a tana mai durk'usawa akusa da shi.
Tukun ta mik'e tana mai bud'e jakar kayansu ta futo da wata k'atuwar rigar sanyi ta yayanta daga ciki ta sanya masa ita a jiki.
Kana ta shimfid'a wasu rigunan ak'asa, sannan ta kama Bir tana mai kwantar dashi akan shimfid'ar.

Gaba d'ayansa yayi matuk'ar laushi, kasancewar kuma ya saba iya na shagwab'asa idan yana ciwo, shiyasa yaketa aikin nanik'ewa Gimbiya.

Tana shirin mik'ewa taji ya kamo hannunta.

"Abun rufa zan samo ma kaji."
Ta sake rad'a masa tana mai janye hannunta daga cikin nasa.

Wasu rigunan ta k'ara cirowa masu kauri har guda biyu, tukun ta lullub'a masa d'aya a jikinsa.
Kana ta kwanta a gefensa tana mai yafa d'ayar ajikinta itama.
Yayinda hawaye kuma suka b'alle daga cikin idanuwanta, sabo da tino ko wacece itan da tayi.
Ko amafarki bata tab'a tinanin kwanan titiba, sai gashi yau soyayya ta sanyata yin hakan, fatan ta d'aya kawai shine Ubangiji yasa kar Bir ya juya mata baya.

Kamar Bir yasan kuka take ya d'ora hannunsa akan jikinta yana mai shafa bayanta.
Jin hakan da tayine ya sanyata sanya tafin hannunta ta goge hawayenta, kana ta juyo b'angaren da yake, kasancewar da baya ta juya masa tana mai kallonsa.

Shi kuwa ahankali ya matso kusa da ita, yana mai had'e jikinsu huri d'aya, sabo da sanyin da yake ji sosai.
Kafin daga bisani kuma ya bud'e baki cikin rawar murya da sanyi irin ta mai ciwo.
Yana mai fad'in.

"Kuka kike ko?"

Kasa amsa masa tayi, sai girgiza masa kai kad'ai da tayi, yayinda su kuma hawayen suka sake tsinkewa.

"Ki dena kuka kinji Gimbiyata, gobe bazamu kwana anan ba kinji."
Ya k'ara fad'e a sanyaye hakwaransa na futar da sauti.

Da k'arfi tak'ara rungumesa acikin jikinta hawayen na cigaba da zubo mata.

Shima d'in kanan-nad'eta ya k'arayi, yana mai jin dad'in d'umin jikinta dake ratsa nasa jikin.
Ahaka har bacci b'arawo ya sacesu ba tare da sun shirya ba.


Hayaniyar jama'a ce ta tashesu daga baccin da suke suna masu bud'e idanuwa a tare.

Ido hu'du sukai da junansu, sabo da yadda Gimbiya Tasmir ta koma saman Bir gaba d'aya tamkar ta samu katifa, da alamun dai duka batasan tayi hakan bama.

"Aucccch wayyo Gimbiya zata k'arasa miki Jaruminki Iyata."

Bir da gaba d'aya ya tashi babu zazzab'in a jikinsa ko kad'an, ya fad'a acan k'asan mak'oshinsa yana mai tab'e baki tamkar zai fashe da kuka.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir, da sauri ta sanya tafukan hannayenta ta rufe fuskarta tana mai sakin murmushi.
Kana daga bisani ta sauka akansa tana mai jin duk kunya ta lullub'eta.

"Ke kuma naki salon kenan, daga kuma jinya sai kinemi k'arasa mara lafiya da nauyin ki."
Bir ya fad'a yana mai mik'ewa zaune.

"Ina kwana ya jiki."
Gimbiya ta fad'a ahankali tana mai jin dad'in yadda ya farka garau.

"Lafiya k'alau na samu sauk'i ya naki jikin kema."
Ya fad'a yana mai mik'ewa tsaye.
"Ni lafiyata k'alau."
Itama Gimbiya ta fad'a tana kallonsa.

To taso mu tafi ko, kin san dai bazamu bari dare ya k'arayi mana abakin ruwan nan ba."

Bir ya fad'a yana mai shirin d'aukar jakarsu.

"Tom shikenan, amma mu fara wanke baki mu siya abinci sai mutafi."

Cewar Gimbiya tana mai bud'e jakarta ta zaro brush har guda biyu sababbi da suka siye su agarin da suka tsaya jiya, tare da maclean ta tatsa a jikinsu.
Kana ta basa d'aya tana mai cewa.
"Muje mu samu ruwa a waje sai muyi ko."

Amsa yayi suna masu fucewa a tare.
Anan bakin wurin suka samu ruwa suka siya da sauran kud'in data canza, a wurin wani da yake akusa dasu acikin jirgi jiya dana su kud'in.
Tukun sukayi brush d'in gaba d'ayan su, tare da wanke fuskokinsu.
Kana ya huce wurin da yaga ana siyar da abinci ya fara duban abun da yake tinanin Gimbiya zata iyaci, domin kuwa shi baya jin kansa, yasan babu kalar da bazai iya ciba.

Bredi da lemon jarka daya gani a wurin wani mai shago kuma yake tinanin sune kad'ai abun da zata iya ci a wurin ya siyo musu.
Tukun ya juyo ya dawo wurin da take yana mai zama a gabanta.

Bud'e bredin yayi suka cisa sosai kuma ba laifi, sabo da ba k'aramar yunwa suke jiba, sunayi suna korawa da lemo.
Kana ak'arshe bayan sun k'oshi suka sake mik'ewa tsaye.

"To ina zamu tafi kuma yanzu."

Gimbiya ta fad'a asanyaye tana kallonsa.
Hakan daya jine ya sanya fad'in.

"Duk inda ya samu Gimbiyata, kawai dai zamu bar wurin nan mutafi wani garin, inyaso idan munje sai mu nemi wurin zama ko."

Ya fad'a yana mai d'aukar jakun-kunan ya farayin gaba.
Ba tare da tace komai ba tabi bayansa suna masu yin wurin da sukaga motoci a jere.

Tun kafin su k'arasa wurin suka jiyo sautin muryar masu lodi, suna masu nuna motocin gabansu tare da fad'in.

"Jahar Wasai! Jahar Kagul! Jahar Kwaski! Jahar B'ab'ur! Ku tawo nan ku shiga."

Kai tsaye kuwa Bir ya doshi motar daya ga ana nunawa ana fad'in Jahar Kagul, Gimbiya Tasmir na biye da shi abaya..............✍




COMMENT! COMMENT!! COMMENTS!!!


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*19*



Isarsu wurin yayi dai-dai da lokacin da wani mutumi ya shiga cikin motar, wanda shigar tasa kuma tasa ta cika taf.
Hakan yasa me lodin ya kallesu yana mai fad'in.

"Wannan ta cika, sai dai kuje kushiga waccan ku zauna."

Jinjina masa kai Bir yayi ba tare da yace komai ba, sai juyawa da yayi yana mai nufar wurin wacce ya nuna masan.
Har sun kusa k'arasawa kusa da ita kawai kuma sai ya juya yana mai yin wurin motar da yaga tafi kusanci dasu, wacce aketa fad'in.
"Wasai! Wasai!!"

"Ya malam ina zakuje ne?"
Drivern motar ya fad'a yana kallonsu.
'Dan lumshe idanuwa Bir yayi, sabo da shi baima rik'e sunan wurin da yaji drivern yana fad'e ba, hakanne yasa ko da ya bud'esu sai kawai yace masa.

"Inda zakuje muma zamu je."

"To ga wurinan kushiga ku zauna daga ciki, kafin mu samu cikon mutum na k'arshe sai mu huce."

Ya fad'a yana mai nuna masu cikin motar da suka hangi wata mace zaune acikinta, yayinda daga gaban kuma maza biyune a kujerar gaban, kasancewar goalf ce motar.

"Muje kawai me mota, zamu baka kud'in duka."

Cewar Gimbiya Tasmir tana mai fara shigewa ciki, sabo da ita dai ba k'aramun gajiya tayiba, gashi kuma ganin da tayi duk wurin da suka gifta ana binsu da ido, shiyasa taji gaba d'aya ta gaji da wurin.

"To amma Hajiya bazan muku ragiba fa dubu d'ai-d:ai d'innan zaku bani."
Direban ya fad'a yana mai kallonta, bayan ya gama sanya musu kayansu acikin boot.

Hakan da Gimbiya Tasmir tajine, ya sanyata zaro kud'i masu yawa 'yan dubu-dubu, tukun ta mik'a masa su tana mai fad'in.

"Gashi ka d'auki kud'inka ka bani canji idan da akwai."

"Amma dai bak'ine ku kowa Hajiya?"

Direban ya fad'a yana mai d'an zaro idanuwa, sabo da kud'in da yaga ta mik:o masa wai ya d'auki nasa.
Banza gaba d'ayansu sukayi masa ba tare da sun amsa masaba.
Wanda hakan daya jine kuma ya sanyasa zarar dubu ukkunsa, sabo da yadda yaga gaba d'aya mutanne cikin motar suna kallonsa, yana mai mik'a mata sauran.
Tukun ya bud'e mazauninsa bayan ya gama duk abubuwan da ya kamata yayi na tasha, yana mai yiwa motar key, kana ya cilka hancinta zuwa kan kwalta.
Sai dai kuma ba k'aramun zafi Gimbiya Tasmir har Bir sukaji sunaji ba, sabo da sabo da sukayi da k'asarsu wacce take da yawan duwatsu tare da ruwaye, hakan yasa akoda yaushe suke cikin sanyi.


Ab'angaren Gimbiya Haddiyal kuwa koda ta futa daga cikin Asadullah Palace, tafiya kawai ta farayi, tana mai jefa k'afafuwanta aduk wurin daya samu, ba tare da tasan inda ta nufaba.
Yayinda takejin zuciyarta na k'ara zafi, wata irin muguwar tsanar Billy da dacan batajita ba alokacin da take a gabanta ta taso mata yanzu, tana mai tokare mata k'awon zuciya.

Kalaman Asad kuwa da hawayen da taga suna futa daga cikin idanuwansa sosai suka tsaya mata arai, tayadda har itama ta gaza tsaida nata hawayen.
Hak'ik'a yau taji wani abu mai kama da tausayi akan mutumin, sai dai kuma har abada batajin ko zai fad'i ya mutu zara iya yimasa abun da yake so
Sabo da Gid'ad'o shi kad'aine, kuma da shi take so ta k'are, fatanta dai kawai Allah ya bayyana mata shi tun kafin komai ya dagule mata.

"Hadiyyal! Haddiyal!! Dan Allah ki tsaya saurareni mana."

Habu daya k'araso wurin da take da sauri ya fad'a, yana mai rik'o tsintsiyar hannunta.
Rumtse idanuwanta tayi, tana mai taune leb'enta na k'asa da k'arfi, sabo da shi kansa ji tayi gaba d'aya tana jin haushinsa, tabbas da ace shi d'in ba yayanta bane ba, da babu abun da zai hana ta masa hulak'ancin

Please Login or Register in order to submit comment