Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsula uban gudu akan titi tanmkar zai tashi sama.


*ASADULLAH PALACE.*

Akan had'ad'd'iyar kujerar na da take a gaban swimming pool d'in nan Billy ta zauna tana mai zuba tagumi da hannu bibbiyu.
Yayinda idanuwanta kuma suka kasance k'ur akan hanyar shigowa wurin, zuciyarta kuwa sosai take jin ta mata wani irin nauyi, fargaba da tsoron abun da fushin Yarima Asad yake nufi akanta gaba d'aya suka cika ta, saboda yadda tun da tazo wurin take kiran sa a waya amma yak'i d'agawa, gashi kuma har yanzu da yamma ta fara dosowa ba taga alamun zai zo ba.
Hakan yasa gaba d'aya hankalinta yayi bala'in tashi, domin kuwa ko abinci sai da taji yunwa na shirin illata ta tukun tasa aka kawo mata, shima kuma kad'an ta iya ci ta kora da lemo ta ture sa gefe.
Ta d'auki alwashi ba zata tab'a barin wurin nan ba muddin ba magariba taga tayi ba, kuma idan magaribar tayi ma bata tinanin zara iya komawa gida ba tare da ta had'u da Yarima Asad ba, domin kuwa tana jin har gidansu zata iya zuwa yau muddin baizo ba, sai dai kome za'a fad'a akan ta a fad'a, saboda tana masa wani irin makawon so ne wanda take jin muddin babu shi to itama babu ita, wato dai ba zata iya rayuwaba ba tare da shi ba, wannan dalilin shine ya sanya har ta aikata abun da ta aikata.


Acan cikin Masarautar Wasai b'angaren Al'amin kuwa, sosai mamakin Yarima Asad ya cika zuciyarsa.
Ta yadda har yayi ta faman surutai shi kad'ai a cikin d'akin sa tamkar mara hankali.
Tukun a k'arshe da yaga abun bazai masa ba ya mik'e daga kan kujerar da yake a zaune, yana mai rufe d'akin sa ya kama hanyar part d'in su Asad.

Ko da ya k'arasa Part d'in nasu bai tadda kowa a fallon ba, hakanne yasa sa yin lungun da d'akin Asad yake anan ba tare da ya tsaya neman Mamy'n tasu ba balle ya gaishe ta.

Yana k'arasawa bakin k'ofar yasa key yana mai bud'e ta, kasancewar ko wanne a cikinsu yana da mukullin d'akin d'an uwansa saboda shak'uwar su.
Kana ya danna kansa zuwa ciki yana mai turo k'ofar tare da neman wuri ya zauna yana jiran dawowar Yarima Asad, yayi masa bayanin abun da ya mayar da shi Masarautar Fuld'e.


*K'ASAR MALIN, YANKIN JAHAR KARFUZ CIKIN BAK'AR MASARAUTA.*

Daga Iyar Bayi har Bir kuka suke sosai-sosai a lokacin da takai k'arshen labarin da take basa.
Da sauri ya matsa zuwa kusa da ita, yana mai sanya hannuwansa duka biyu ya rungumeta k'am-k'am.
Kana suka k'ara fashewa da wani irin kuka mai matuk'ar ban tausayi a tare.
Ita Iyar Bayi tana na tausayin kanta ne, saboda abun da ta aikata.
Yayinda shi kuma Bir yake na tausayin kansa tare da Iyayensa da aka basa labarin su a yanzu, ga wata irin azababbiyar soyayyarsu da mararin ganin su da yaji sun lullub'e zuciyarsa a lokaci guda.

Hawaye ke shatata daga cikin idanuwansa da matuk'ar gudu, yayinda zuciyar sa kuma ke hasasho masa yadda abun ya faru, ta yadda har yake kamanta kamannin Mahaifiyar sa a cikin idanuwansa tamkar a gaban sa abun ya faru.

Wata irin matsananciyar tsanar Sarki Barbaru yaji tana lullub'e gaba d'aya ilahiri jiki da zuciyar sa.

Ji yake a duk duniya bashi da wani mak'iyi wanda ya huce shi a yanzu, ji yake zai iya yi masa komai da zai sa yaga hawaye a cikin idanuwansa, ciki kuwa harda rabasa da rayuwarsa daga gidan duniya.

A yau a kuma yanzu yaji gaba d'aya Masarautar ta ishe sa, kana kuma kokonton addinin da suke bi ya d'arsu a ransa, domin kuwa taya za'ace abun da suke yiwa bauta suke kiransa da mahallicin su ace ya kasa nemar musu da mafuta a duniya, ta yadda har jariri zai iya fin k'arfin sa, ace har akwai wani fad'an da bazai iya warwaresa ba, hak'ik'a k'arya ne wallahi.
Ya raya hakan a cikin ransa yana mai cigaba da sakin kukan sa.

Ita kuwa Iyar Bayi cikin zubar k'walla da sanyin jiki ta zame jikinta daga cikin nasa.
Kana ta d'ago tafin hannunta tana mai kife sa akan lallausar sumar kansa, tare da d'an fara shafata a hankali a hankali.

Take kuwa Bir ya fara sauke wasu irin tagwayen a jiyar zuciya, tare da lumshe idanuwansa.
Kafin daga bisani kuma ya warasu da sauri akan fuskar Iyar Bayi, saboda abun da yaji tana fad'i.

Cikin sanyi ta cigaba da shafa lallausar sumar kan sa tana mai fad'in.

"A yau na maka abun da kake so Jarumi na, na cika maka alk'awarin da na d'aukar maka, wato na shaida maka yadda akai aka same ka a cikin Bakar Masarauta, duk da sanin da nayi na hakan tamkar dai-dai yake da na d'au takobi na caka ta a k'awon zuciya ta ne.
Hak'ik'a na riga dana sani rayuwata tazo k'arshe a gidan duniya, k'arshe na yazo, k'ura ta na gab da b'acewa a cikin BAK'AR MASARAUTA, kafin daga baya kuma tarihina yazo ya shafe daga cikin kundin BAK'AR MASARAUTA shima, domin kuwa tun daga yanzu, yau, gobe, ko jibi, duk ina iya zamtowa gawa!
Wato dai zan mutu, kashe ni za suyi, saboda amanarsu da naci.
Dan haka Al'farma d'aya nake nema a wurin ka Jarumi na."

Ta fad'a tana mai sa hannunta ta goge hawayen da suke kwance akan fuskarta, duk da wasu sababbin da suke sake tuttud'owa kuwa.

Shi kuwa Bir kasa ce mata komai yayi, sai aikin kukan da yake tamkar ransa zai futa, gaba d'aya idanuwansa sun kod'e, yayinda fuskar sa kuma tayi wani irin jajahur abun ka da farar fata.

Ita kuwa Iyar Bayi ba tare da ta tsaya lallashinsa ba ta d'ora da fad'in.

"Ko bayan raina, ma'ana bayan shafewar zamani na a duniya.
Ina son ka k'auracewa shiga harkar Gimbiya, ka guji duk wani abu da zai had'aka da ita wanda har zai sanya ta nemi halaka ka.
Ina nufin karka k'ara gigin bin hanyar da take kanta, karka kuskura wata magana ta had'aka da ita muddin ba ita d'in ce ta buk'aci jin hakan daga gare ka ba, kar kuma kayi mata gardama a duk abun da zata saka gudun shigar ka matsala, wato kafuta harkarta gaba d'aya, hakan shi zai sanya ruhi na ya samu salama ko bayan bana numfashi a doron duniya, domin ko ina maka so ne irin wanda Uwa take yiwa 'Danta, ina jin duk wata damuwar kace a cikin jinin jikina, tamkar yadda nake mararin ganin murmushi akan fuskar ka ako da yaushe.
Wannan ita ce kad'ai Alfarmar da zakayi mun, ruhina ya samu salama aduk inda nake Jarumi na.............✍


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*07*



Da matuk'ar sauri Bir ya sake matsawa jikin Iyar Bayi, yana mai girgiza mata kansa, hawaye na cigaba da tsiyaya daga cikin idanuwansa.
Kafin daga bisani kuma ya d'aga hannuwansa yana mai kife tafukansu akan kafad'unta, tukun ya bud'e baki cikin rawar murya, yana mai fad'in.

"A'a Iyata, a'a ba zaki mutu ba, ba zaki tafi ki barni ba, ba zaki mutu ba babu abun da zai faru dake, domin kuwa a duk fad'in duniya babu wanda ya san kin bani wannan labarin ballantana har ya kai rahato, mu biyu ne kawai a cikin wurin nan, dan haka babu wanda zai san abun da muka tattauna akai.
Ki dena kuka kinji Iyata."

Ya k'arasa maganar cikin rud'u, kana ahankali, yana mai janye tafin hannunsa d'aya da yake akan kafad'ar ta ya mayar da shi kan fuskarta, yana mai goge mata hawayen da suke sauka akanta.

Yayinda ita kuma Iya ta saki wani irin murmushi mai ciwo, tana mai girgizawa Bir kai, domin ko tariga da tagama saddak'ar da cewar ita tata rayuwar duniyar tazo k'arshe.
Kafin daga bisani kuma ta d'aga lab'b'anta cikin sanyi, tana mai fad'in.

"Ba zaka gane bane Jarumi, ni nasan kalar mutanen da muke zaune a k'ark'ashin mulkinsu tun ina 'yar k'ank'anuwata, wanda har hak..."

"A'a Iya ta, na rok'ek'i akan kar ki k'ara cewa komai, ni na san zamu rayu a tare."
Bir ya katseta da fad'in haka ba tare da ya tsaya yaji k'arshen bayanin ta ba, yana mai cigaba da girgiza mata kai.
Hakan da Iyar Bayi ta gani ne ya sanya ta yin shiru ba tare da tak'ara cewa komai ba, sai tafin hannunta da ta janye daga kan sumar Bir, tana mai mayar da shi zuwa kan fuskarsa ta fara share masa hawayen da suke kwance akanta.
Tukun a k'arshe ta mik'e tsaye tana mai fad'in.

"Tashi maza mu koma gida, kaga har yamma tariga tayi tun kafin wani yazo ya ganmu anan wuri tare a kai harato."

Ta k'arasa maganar tana mai mik'a hannunta ta kamo hannun Bir da shi.

Ba tare da yace komai ba ya mik'e d'in shima, tukun suka fara d'aga k'afafuwansu suna masu dosar hanyar da zata mayar da su sashin su.

Ko da dare yayi gaba d'aya Bir kasa yin bacci yayi, saboda yadda labarin da Iya ta basa ya tsaya masa a rai.
Babu abun da yake muradin gani a halin yanzu face Iyayensa na asali.
Sai dai kuma ta ina zai fara neman su, a wane gari suka kasance zaune a yanzu ne? Mene ne sunan mahaifinsa da mahaifiyarsa? Taya ya zai gane su d'in ne idan sun had'u bayan su kansu ba zasu iya cewa gashi ba? Shin har yanzu suna nan da ransu ko kuwa? Shin suna tinaninsa ko kuwa sun manta da shi? Shin suma bautar Ubangiji Gargabilu sukeyi ko kuwa suna da nasu addinin?
Shin yana da Yayye, K'anne ko kuwa iya shi kad'ai ne suka haifa?

Babu wani abu da ya sani dan gane da su wanda har zai bi ya sadasa da wurin da suke ban da sunan k'asarsu kawai da yaji daga bakin Iyar Bayi.
Wato K'asar Hausa, domin kuwa iya ta shaida masa cewar k'asar Hausa jirgin ya nufa daga nan cikin bak'ar masarauta.
Hakan yasa sunan k'asar ya zauna masa daram a cikin zuciya, kana kuma yaji babu inda yake burin zuwa face can a halin yanzu.

Sosai yake juyi akan shimfid'arsa ta tsummokarai, gaba d'aya bacci ya k'auracewa idanuwansa.


A b'angaren Gimbiya Tasmir kuwa, itama gaba d'aya ta nemi nutsuwarta ta rasa tun bayan gama saurarar labarin Bir da tayi a bakin mahaifinta.
Tuni ta kwanta akan tamfatsetsen gadon ta tana mai san bacci ya d'auke ta, amma gaba d'aya yak'i zuwa, asalima ko alamun zai zo d'in bata ji ba, saboda yadda abubuwa da dama suka taru suka cunkushe mata a zuciya, tinaninnika sukabi suka mata yawa a cikin ranta.
Ga wani irin matsanancin tausayin Bir da take ji ya samu gurbi a zuciyarta.
Ga kuma tinanin abun da ya sanya take jin fad'uwar gaba a duk had'uwarta da shi da ya tsaya mata a rai, ta yadda har take mararin sake ganinsa, domin ta tambayesa cikin lalama a wannan karan kota samu ya bata amsar ta.

"K'asar Hausa."

Ta fad'a a k'asan mak'oshinta tana mai lumshe idanuwanta, tare da sake yin juyi.
Tukun ta cigaba da tinanin kenan shi ba d'an asalin K'asar Malin bane, yanzu shikenan ana nufin ba zai tab'a had'uwa da iyayensa ba.

Ta raya haka a cikin zuciyarta, tana mai sake yin wani juyin, tare da kamanta kanta a matsayinsa, tana mai tinanin yadda zatayi idan akace bata gaban iyayenta.
Da sauri kuma ta girgiza kanta tana mai fad'in.

"Hakan ma bazai tab'a faruwa ba."
Ta fad'a a fili tana mai lumshe idanuwanta.

Haka dai tai ta juyi akan gadon gaba d'aya bacci ya k'auracewa idanuwanta a wannan daren, saboda tinanin k'ask'antaccen Bawanta da ya cunkushe mata a zuciya.


*K'ASAR HAUSA, JAHAR WASAI.*

_ASADULLAH PALACE._
i
Sosai damuwa ta k'ara yiwa Billy yawa, saboda ganin da tayi har magariba ta doso babu alamun ko inuwar Yarima Asad.
Ga kuma yadda har yanzu take aikin kiran wayar sa bai d'auka ba.

Tini ta fara nadamar abun da ta aikata masa, sai dai kuma bakin alk'alami ya riga da ya bushe tunda har abun yaje kunnensa.

"Akan me zaka mun haka Prince, dan Allah dan annabi na rok'ek karka bani kunya, kai da kanka kasan ina sonka, ina sonka tamkar yadda nake son rayuwaota.
Shin me yasa nima ba zaka so ni ba ko da bakai irin wanda nake maka ba? Shin me ne bani da shi wanda har ban cancanci ka soni ba.
Wallahi tallahi sai ka so ni tamkar yadda nake son ka Prince, sai ka aure ni, domin ko babu wata mace da ta dace da kai bayan ni."

Ta fad'i maganar a lokacin da ta mik'e ta doshi wurin da motar ta take,idanuwanta na zubar da k'walla.
Tun bayan sallah'r la'asar mahaifiyarta ke kiranta amma gaba d'aya ta kasa d'aga wayar, saboda damuwar da take a ciki.

Ji take muddin bata samu ganinsa a yau ba to ba zata iya rintsawa ba.
Sosai take jin zuciyarta nayi mata wani irin rad'ad'i da suya.

Hakan yasa ko da ta fuce daga cikin wurin a mai-makon ta kama hanyar gidansu sai ta kama hanyar da zata kaita gidan Sarkin Wasai, domin ko tana jn muddin ba taji daga Yarima Asad ba to ba zata iya kai kanta gidansu ba.

Acan cikin Masarautar Wasai b'angaren Al'amin kuwa, har yanzu zaune yake a cikin falon Yarima Asad yana mai kallo a cikin tafkekiyar tv'n bangon da take manne a jikin bangon d'akin, saboda yace ba zai tab'a futa daga ciki ba muddin ba Asad ne ya dawo ba, domin kuwa yana son ya fara riskarsa a cikin d'akin, saboda yaga da wane ido zai kallesa, kana kuma yaji abun da zai ce masa akan komawarsa Masarautar Fuld'e yau.
Hak'ik'a Allah abun tsoro ne, wato Asad da ya raina mata yake fad'in ba ayi wacce takai matsayin ya so ta ba a duniya, kuma baza a tab'a yinta ba shi ne yau Allah ya damk'a da matsananciyar soyayyar wata, watan ma kuma wadda bai tab'a tinanin zai so irin ta ba, soyayyar ma kuma mai k'arfi ba k'arama ba, domin kuwa ban da haka da yasan babu abun da zaisa sa ya koma wurinta a yau.

Al'amin ya raya a cikin ransa yana mai girgiza kansa.
A kuma dai-dai lokacin wayarsa ta d'auki ruri alamun shigowar kira.
Hakanne yasa ya kai idanuwansa zuwa kan screen d'in wayar.

Lambar Billy mai had'e da sunanta da ya gani akan screen d'in wayar ne ya sanya sa kai hannunsa wurin da take, yana mai d'aukota yayi picking d'in kiran tare da karata a kunnensa.

"Kana ina ne d'an uwa?"

Yaji muryar Billy ta daki dodon kunnensa tana mai fad'in haka ba tare da ko sallama tayi ba.

'Dan tab'e baki Al'amin yayi, yana mai fad'in.

"Ina gida mana."

Sabo da sanin da ya riga yayi na ba zai huce sun samu sab'ani bane da mutuminta take son ya taya ta basa hak'uri.
Kasancewar ba kiran sa take ba sai idan hakan ta faru tsakaninsu, tukun take nemansa wani lokacin har kuka take masa akan ya tayata bawa Asad hak'uri.

"To Dan Allah kayi maza ka futo ganin nan a k'ofar gida."
Muryar Billy ta katse masa tunanin da yake da fad'in haka.

Hakan da yaji ne ya sanya sa mik'ewa tsaye da sauri, kana cikin tsantsar mamakin abun da ya kawo ta har k'ofar gidan nasu yau, ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Kamar ya kina k'ofar gidan mu kuma, ke d'in ce kikazo har gidan mu, shin me yake faruwa ne?"

Ya watso mata tambayoyin duka a jere gaba d'aya mamakin abun da ya kawo ta gidan nasu ya gama rufe sa.

"Dan Allah kawai kayi maza ka futo, idan kum ba haka ba ni zan shigo yanzu, saboda akwai matsala ce babba."

Yaji muryar Billy tana mai fad'in haka muryarta na rawa, alamun tana gab da fashewa da kuka.

Hakanne yasa sa fad'in.
"Tom shikenan gani nan."

Kana ya yanke kiran ba tare da ya tsaya jin mai zatace ba, yana mai kama hanyar waje cikin sauri.

Acan b'angaren Billy kuwa da niyyar shiga har cikin gidan nasu ta tawo, saboda ita da farko ma gaba d'aya ta manta da wani Al'amin, saboda rud'un da take ciki, har sai da tazo kusa da get d'in masarautar tukun ta tuno da shi.
Hakanne yasa tayi ribors da sauri, tana mai komawa can baya jikin katanga k'ark'ashin wata bishiya ta faka motarta a wurin, domin kuwa dama can ta riga da tasan bai kamata ace ta shiga ciki ba a matsayin ta na wacce za'a aure akawo ta gidan.
Tukun ta zaro wayarta cikin sauri, tana mai nemo number Al'amin ta doka masa kira.

Shi kuwa Al'amin da matuk'ar sauri tamkar zai tashi sama ya k'araso bakin masarautar.

Tun daga ciki yake ta faman wurga idanuwansa waje, yana mai son ganin ta inda zai hango motar Billy.
Amma bai hangota ba har sai da ya futo duka waje, kana ya hango wata had'ad'd'iyar bak'ar mota fake acan nesa da get d'in gidan nasu.
Hakanne yasa sa tun karar inda take ba dan yana da tabbacin ita d'in ce a ciki ba, kasancewar ba mota d'aya ta saba hawa ba, sannan kuma shi sai su shafe sama da wata basu had'u ba har dai ba sun samu sab'ani da Asad bane, shima kuma yawanci ta waya take kiran sa tana masa magiya.

Tun kafin ya k'araso bakin motar Billy ta bud'e masa murfin da yake a gefen ta, saboda hango sa da tayi ta cikin glass yana tawowa.

Al'amin kuwa yana k'arasowa bakin motar ya tsaya daga gefe yana mai kai idanuwansa cikinta, domin ya tabbatar da in ita d'in ce.
Sai dai kuma tun kafin idanuwan nasa su sauka a cikin motar ma ya jiyo sautin muryar ta tana mai fad'in.

"Dan Allah yi maza ka shigo mana d'an uwa."

Kana ta k'ara hangame masa murfin motar.
Jin hakan da Al'amin yayi ne ya sanya sa k'arasawa jikin murfin, yana mai rank'wafowa ya shigo daga cikin motar.
Tukun ya mayar da murfin ya rufe.
Kana ya juya b'arin da Billy take yana mai zuba mata idanuwansa tare da fad'in.

"Ya dai meke faruwa ne yau kuma?"

"Ai babu ma abun da ma bai faru ba d'an uwa, domin kuwa ina cikin muguwar matsala, ina cikin matsananciyar damuwa.
Zuciyata na zafi da k'una tamkar zata babbake d'an uwa, saboda Prince ya canza mun, tun daren jiya nake kiransa har kawo yanzu amma yak'i yak'i dagawa, kana kuma baizo Palace ba ma.
Ban san ya zanyi ba idan har Prince Asad ya dena kulani na shiga ukku na lalace, ka temake ni d'an uwa."

Ta fad'i haka a tsantsar haukace, hawaye na b'allewa daga cikin idanuwanta.

Jin hakan da Al'amin yayi ne, ya sanya sa gyara zaman sa a wurin da yake zaune tare da k'ara zuba k'wayoyin idanuwansa akan fuskarta.
Kana ya sake cewa.

"Amma me ne ya had'aku kafun ki kira san yak'i d'agawa?"

Jin tambayar da yayi mata ne ya sanya Billy yin shiru, tana mai d'an fara yin muzurai ba tare da tace masa komai ba.

"Ke nake sauraro fa."

Al'amin ya fad'a yana mai kafeta da idanuwansa.
Hakan da taji ne ya sanyata janye idanuwanta daga kan fuskarsa.
Kana ta bud'e baki cikin sanyin murya, tana mai fara zayyano masa duk abun da tasan ya faru wanda itace musabbabin faruwarsa.

Shiru Al'amin yayi ba tare da ya iya cewa komai ba, sai kawai jinjina kai da yake ta aikin yi.
Domin kuwa gaba d'aya rasa abun fad'e ma yayi, saboda shi kansa ya sani Asad bai tab'a son Billy ba ko da na dak'ik'a d'aya ne kuwa, tamkar yadda yasan itan ma tasan da hakan, saboda yasha fad'a mata cewar shi ba sonta yake ba har a gabanta, kasancewar shi Asad babu ruwansa muddin zakice kina son sa to a gaban idanuwanki zai ce baya son ki, ko kad'an babu ruwansa da yadda zakiji.

"Cab', babbar magana kenan, to da farko ma ke me yasa ki yin hakan, bayan kuma kin riga da kin san halinsa."

Al'amin ya fad'a yana mai kallon Billy.

"Saboda ina son sa ne, kuma ako da yaushe zuciyata na fad'amin babu wanda ya dace dani bayan shi, yayinda shi kuma ako da yaushe yake nuna bai san ina yi ba, duk da ko muna tare da shi yana morata."

Ta fad'i haka cikin sanyi tamkar zata sake fashewa da kuka.

Jin da Al'amin yayi tace yana morarta ne ya sanya sa d'an sakin murmushi, kana ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Batun yana morarki ma a yanzu duk bai taso ba Billy, domin kuwa kin sani muddin kika fad'i haka a gaban Asad to daga lokacin kin gama ganin murmushi a fuskar sa har abada, saboda zai ce ne ai ba shi yake gayyato ki ba ke kike zuwa da kanki, kana kuma ya tambayeki abun da ya tab'a yi miki tun da dai ke kanki kin san shi ba zurfi yayi ba, dan haka ina ganin ma kawai ki bar wannan batun anan wurin kar ki k'ara cewa zaki mai-maita sa gudun kar ya koma kunnensa."

"To yanzu mece mafuta? Me kake tinanin zai faru?"

Billy ta fad'a tana mai aminta da zancen Al'amin na cewa karta kuskura ta fad'i haka a gaban Asad muddin tana son alak'arsu ta cigaba.

"To wannan ne kuma banace ba, saboda ni kai na kin ganni rabon dana sa Asad a gaba na tun jiya da yamma da muka dawo daga tafiya, domin ko yau tun da safe na hangesa ya fuce kuma har yanzu bai ma dawo ba, wanda kema kuma ina tinanin hakanne ya sanya har bai d'aga wayarki ba.
Amma dai yanzu ina son ki kwantar da hankalinki ki tafi gida, ni kuma na miki alk'awarin da zarar ya dawo zan same sa da maganar, kana kuma zan rarrasarmiki shi, in sha Allahu babu abun da zai faru."

Al'amin ya fad'a mata haka saboda hankalinta ya kwanta ta tafi, amma shi da kansa ya san wajibine gagarumin abu ya faru a tsakaninsu tun da har ta aikata hakan bayan tasan ba sonta yake ba.

"Wato Asad auren dole ya zama wajibi kenan, maga kuma k'arshen cika baki."

Ya fad'i haka a cikin zuciyarsa yana mai fucewa daga cikin motar, bayan sunyi sallama da Billy.

Ba shi ya bar wurin ba har sai da yaga ta hau kan titi, tukun ya juya yana mai komawa cikin gida.

Kai tsaye ya sake dosar d'akin Yarima Asad, domin ko yayi rantsuwa da Allah akan cewar sai ya ritsa Asad yau.
Yayinda yake tinanin irin gwaramar da za'asha tsakaninsa da Billy da kuma iyayensu akan batun auren nan nasu.

Acan b'angaren Yarima Asad kuwa sosai yake kawarara uban gudu a tsakiyar titi har ya shigo cikin garin Wasai bai dakata ba.
Duk inda ya huce sai kaga anbi motar da kallo, kowa da abun da yake fad'e akan matuk'in cikinta.

Yayinda shi kuma da yake tuk'in gaba d'aya yake a matuk'ar hargitse.
Sosai yake jin kansa na masa wani irin mugun ciwo.
Ga kuma yadda har yanzu muryar Gimbiya Haddiyal take cigaba da yi masa amsa kuwwa a cikin kunnuwansa lokacin da take fad'in.
Ta tsanesa tamkar yadda ta tsani mutuwarta.

Da k'arfi ya daki sitiyarin motarsa yana mai take wani irin mahaukacin birki a tsakiyar kwalta, jikake k'iiiiiii!!! Sautin futar k'arar birkin.

Yayinda gaba d'aya jama'ar da suke a kusa da wurin tun daga na kan titi har zuwa wa'yan da suke acan k'asa suka kawo idanuwansu zuwa wurin motar cikin tsantsar firgici, tare da mamakin abun da ya sanya driver'n cikinta yin hakan.
Kasancewar babu wani abu da yake a gabansa ballantana ace ya tsaya ne saboda yana shirin bigesa.

Shi kuwa Yarima Asad kwata-kwata baima san lokacin da ya take birkin ba har sai da yaji tsayuwar motar, tukun ya lura, saboda yadda gaba d'aya kansa ya d'au zafi.
Tukun daga baya ya janye k'afarsa daga kan birkin, yana mai cigaba da tsala uban gudu.
Yayinda yake jin zuciyar sa na masa wata irin tafarfasa, su kuwa idanuwansa har yanzu basu dena hasko masa hoton kyakkyawa fuskarta ba.

Ikon Allah ne kawai ya kaisa gida lafiya yau.
Dominko ko da ya shiga cikin Masarautar tasu ma bai dakata da mahaukacin gudun da yake ba har sai da ya isa part d'in su.
Kana ya bud'e murfin motar yana mai d'aukar wayarsa ba tare da ya tsaya ko cire key d'in ta balle ya dai-dai ta parking d'in ta, ya doshi cikin gidan su.

Gaba d'ayansa a hargitse yake, domin ko hatta da sumar kansa duk ta mimmik'e tsaye tare da wargajewa, saboda yadda ya ringa yamutsata.
Ga kuma idanuwansa da suka rikid'e su kai jajajir tamkar gauta.
Kana kuma har yanzu bai fasa sakin huci

Please Login or Register in order to submit comment