Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

faru."

Jinjina kai Babban Yaya yayi, domin kuwa sai da yace K'anin Ciromane shi tukun yaga kamanninsu.
Kana ya bud'e baki cikin sakin fuska yana mia fad'in.

"Kace Asad ne ko, to ma sha Allah, ai komai ya huce, babu komai ka kwantar da hankalinka kaji ko."

Jinjina masa kai Yarima Asad kawai yayi.
Yayinda shi kuma Babban Yaya yace masa.

"To yasu Yayan naka da Mamy da Dady, fatan duk kuna lafiya.
Amma yanzu dai mushiga daga ciki kasha ko ruwane kafun katafi."

"Lafiya k'alau suke, amma ba saina shiga cikiba ma, kawai dai shi d'in nake son ka kira mun na basa hak'uri dan Allah."

Cewar Yarima Asad still asanyaye ba tare kuma da ya d'ago ido ya iya kallon Sheikh Ahmad ba har yanzu.

"A'a duk da haka mu shiga daga ciki sai nayi masa maganar ko."

Cewar Sheikh Ahmad yana mai kamo hannun Yarima Asad sukayi ciki, domin kuwa tun a lokacin da Babban Yaya ya basa labarin hallayarsa yaji yana tausayin yaron, sannan kuma a yanzu hakama a jiya da yaje masarautar kan batun tafiyarsu da'awa, sun sake tattaunawa da Babban Yaya akan batun yana son ya dinga koya musu karatun addini da shi da Al'amin.

Binsa Yarima Asad yayi jiki a matuk'ar sanyaye suka shiga ciki.

"Kai Abdulmajid zo nan kaji."

Babban Yaya ya kwad'awa Bir kira adai-dai lokacin da yake shirin shigewa cikin gida.
Juyowar kuwa yayi yana mai nufo wurin da suke, sai dai kuma idanuwansa na sauka akan Yarima Asad ya ganesa, hakanne ya sanyasa tsayawa cak a wurin da yake yana jifansa da wani irin matsiyacin kallo, domin kuwa shi duk a tinaninsa wani sabon iskancin yazo ya sakeyi masa.

Ganin da Sheikh Ahmad yayi ya tsayane ya sanyasa sakin hannun Yarima Asad, yana mai matsawa kusa da Bir d'in.
Tukun ya dafa kafad'arsa cikin taushin murya yana mai fad'in.

"Ya katsaya anan ne k'anina? Ka k'arasa mana ku gaisa ko."

"Ni bazani wurinsa ba, shine fa wanda yasa Gimbiyata takusa tafiya ta barni, wato yanzuma kenan ya dawone dan yasake sawa ta tafi."
Cewar Bir rai ab'ace yana mai wurgawa Yarima Asad da kansa ke durk'ushe a k'asa harara.

"Wayace maka yanzuma ya dawone saboda ta sake tafiya? Kuma ko abayama aiba shine ya sanyata ta tafi ba kaine dai ko, sannan ma kuma kar kamata kai musulmine a yanzu, addinin musulunci kuma yayi hani da gaba, hakan yasa Allah yake fushi da duk mai yinta, ta yadda harya tanadar masa da azaba mai rad'ad'i zarar ya mutu bai dena ba, to kai yanzu kana son kashiga wutane k'anina?"

Dasauri Bir ya girgiza masa kai hankalinsa a tashe.
Ganin hakan da Babban Yaya yayine ya sanyasa dafa kafad'arsa yana mai fad'in.

"To muddin bakason hakan da gaske sai kaje ku gaisa, kuma karka nuna masa wani abu akan abunda ya had'aku rannan kaji."

Ya k'arasa maganar yana mai yin gaba ya barsa a wurin.

Aikuwa cikin sanyin jiki ya fara d'aga k'afafuwansa yana mai tunkarar wurin da Asad yake.

Zama yayi akan kujera ba tare daya k'arasa har dab dashi ba, kana ya bud'e baki ba tare daya d'ago ya kallesa ba yana mai fad'in.

"Sannu ko."

Hakan da Yarima Asad yajine ya sanyasa d'ago k'afafuwansa da yake jin sun masa nauyi, yana mai k'arasowa wurin da Bir yake.
Kana ya zauna akan kujerar da take facing d'in wacce yake kai, yana mai mik'a masa hannu tare da fad'in.

"Assalamu alaikum."

Ba tare da Bir ya kallesa ba shima ya mik'o masa hannu yana mai fad'in.
"Wa'alaikumu Salam."
Kasancewar yanzu dagashi har Gimbiya Tasmir sun iya abubuwa da dama masu sauk'i da suka wajaba ga musulmi.

Shi kuwa Yarima Asad ganin yadda yak'i ya kallesa har yanzune yasa yaji jikinsa ya sake matuk'ar sanyi.
Tukun daga bisani kuma ya bud'e baki cikin k'asa da murya yana mai fad'in.

"Kayi hak'uri da abun da yafaru dan Allah, sai daga baya na gane rashin kyautawata akan abun da nayi maka."

Shiru Bir yayi tsananin mamaki na lullub'esa, saboda ko kad'an baiyi zaton jin hakan daga bakin guy d'inba, duba da yadda yay masa a ranar daya zo.
Kafin daga bisani kuma ya d'ago kansa akaron farko yana mai watsa idanuwansa akan fuskar Yarima Asad.
Kana ya janyesu yana mai fad'in.

"Nayi."
Tukun ya mik'e yana shirin tafiya.

Ganin hakan da Yarima Asad yayine ya sanyasa saurin sauka daga kan kujerar da yake, yana mai cake gwiwoyinsa a k'asa tare da rik'e k'aurin Bir da sauri.

Cak kuwa Bir ya tsaya a wurin da yake ba tare daya iya gaba ko kuma ya juyo ba, sai zallar mamaki kawai daya rufesa.
Yana cikin wannan yanayinne kuma ya jiyo sautin muryar Yarima Asad cikin rawar murya, yana mai fad'in.

"Ina rok'onka da sunayen Allah akan ka janye zuwa wurin gasar gobe, kayi mun rai badan halinaba, saboda idan na rasata zuciyata bugawa zatayi."

Ya k'arasa maganar muryarsa na rawa abun gwanin ban tausayi tamkar zai fashe da kuka.

Yayinda Bir kuma ya rumtse idanuwansa, yana mai jin wani irin abu na yawo a gangar jikinsa, hak'ik'a koda wasa bai tab'a tinanin zai iyayin hakan ba, duba da yadda ya dinga ihu akansa alokacin da yazo.

Bai futa daga cikin wannan mamakinba ya sake jiyosa ya d'ora da fad'in.

"Hak'ik'a ba komaine kud'i ke samar dasu ba, haka kuma ba komaine rashin mutunci da girman kai ke badasu ba, ina mata so irin son da bazai misaltuba, ina jin tamkar idan na rasata zan rasa rayuwatane nima, kayiwa Allah ka tausaya mun kabarmun ita badan halina b..."

Maganar tasa ta yanke, saboda yadda zuciyarsa tayi matuk'ar rauni.

Yayinda Bir kuma yaji jikinsa yayi tsananin sanyi, lokaci d'aya kuma tausayinsa ya mamaye gaba d'aya ilahirin jiki da zuciyarsa, saboda shi kansa ya san yadda mutum yake ji a soyayya ba sai ya fad'a masa ba, gaba d'aya sai yaji ya manta da duk abun da yayi masa, kana kuma zuciyarsa tayi sanyi.
Hakanne ya sanyasa juyowa jiki asanyaye yana mai zuba idanuwansa a cikin na Yarima Asad.

Da sauri ya k'ara zaro idanun nasa, sabo da ganin da yayi tamkar ruwan hawayene ke kwance akan fuskar tasa.
Hakanne ya sanyasa yin sauri ya dafo kafad'arsa yana mai d'agosa tsaye.
Kana kuma cikin tsananin tausayinsa ya d'ora yatsunsa akan fuskarsa, yana mai d'auke masa hawayen da suke zubowa, sannan ya bud'e baki atak'aice yana mai fad'in.

"Ka kwantar da hankalinka, ni na hak'ura har abada."

Da sauri kuwa, kana kuma cikin tsananin mamakin jin hakan da yayi daga bakinsa ya zaro idanuwansa yana mai kallonsa.

Ganin hakan da Bir yayine ya sanyasa lumshe idanunsa, tukun ya sake bud'esu akan fuskarsa yana mai fad'in.

"Tabbas dagaske nake, nima Gimbiyata kad'ai ta isheni komai."

Da sauri kuwa Yarima Asad ya rungumesa ba tare da yasan lokacin da yayi hakan bama, yana mai fad'in.

"Nagode! Nagode Aboki!! Allah ya saka da alkhairi."

Murmushi Bir ya saki yana mai jin gaba d'aya damuwarsa na yayewa, fargabar abunda zai faru idan Gimbiya tasan yaje masarautar fuld'e a gobe da yayi niyya gaba d'aya takau, sai wani irin farinciki ma da yaji yana lullub'esa, saboda a yanzu ya riga daya sani babu wata barazanar rabuwa tsakaminsa da masoyiyar tasa.
Tukun ya sanya hannuwansa yana mai b'amb'aro Asad daga jikinsa tare da fad'in.

"Banason godiyarka, kawai abunda nake buk'ata a wurinka shine, ka tayani addu'ar Allah ya karemun Iyata, yasa muna da rabon saduwa."

Ya k'arasa maganar asanyaye shima.

Ai kuwa cikin sauri Yarima Asad yace.

"Allah ya sadaka da Iyarka, ya kuma sa kuna da rabon sake rayuwa a wuri d'aya."

"Amin! Amin nagode sosai!!"

Ya fad'a a tak'aice yana mai zura hannunsa acikin aljihun rigar shaddar dake jikinsa da Sheikh Ahmad ya basa su, yana mai zaro takardar da Gimbiya Haddiyal ta basa da yaketa yawo da ita ya yagata, kana ya watsar da ita yana mai juyawa ya tafi ransa fes, ba tare daya tsaya sunyi ko sallama da Yarima Asad ba.

Shi kuwa Yarima Asad bashi ya janye idanuwansa daga kan Bir ba har sai da yaga ya shige cikin gida, tukun ya juya jiki asanyaye yana mai fatan Allah yasa dai da gaske yake, ba bari yayi sai yaje wurin ya gansa ba ya shiga motarsa ya tafi.

"Nagode Aboki, Allah ya bayyana maka Iyarka."

Yarima Asad ya fad'a acan k'asan mak'oshi, saboda yadda yake jin hatta da maganar tana yi masa wuya.
Tukun ya d'auki detol soap d'in da Ummi ta aijiye masa ya fara shafasa a jikinsa yana mai rumtse ido tare da sakin k'ara, saboda tsananin azabar da yake ji tana ratsasa.
Domin kuwa zuwa yanzu sosai ciwon kansa ya sake tsananta.


Acan gidan Gwamna b'angaren Billy kuwa, sosai da farko ta shiga cikin matsananciyar damuwa.
A ranar kuma da yamma saiga Sadik nan yazo tamkar yadda Dadynta ya fad'a mata zaizo.

Sosai yaci ado cikin k'ananan kaya, domin kuwa shi mahaifinsa na sanar dashi yaji hakan yayi masa, saboda dama yasanta, kuma tana matuk'ar birgesa tun ba yanzuba, sai dai kuma ko kad'an bai tab'a jin yana sontaba har sai yau da Mahaifinsa yayi masa maganarta.

Babu abunda bai saniba na daga cikin rashin mutuncin da Yarima Asad yayi mata, asalima yaga komai a socila media shima.
Sai dai kuma hakan baisa yaji bazai iya aurenta ba, asalima sai tsananin tausayi data basa, shiyasa kuwa ko da yazo d'in da tazo wurinsa sanye da hijabi ajikinta bayan sun gama gaisawa, sai ya fara kwantar mata da hankali tare da yi mata nasihohi akan abun da ya faru.

Ai kuwa tun alokacin taji ya birgeta sosai, saboda ganin da tayi shi ko haushi ma baijiba, wanda tasan da Yarim Asad ne da k'ilama daga ranar ko hanya bazai yadda ya k'ara had'awa da itaba.
Hakanne yasa koda ta koma d'akinta data kikkira numbobin Yarima Asad taji gaba d'aya yasata a black list ma.
Hakan yasa kawai ta k'udirtawa ranta cewar ta rabu da shi itama, ko da kuwa hakan zai zamto silar tsayawar bugun zuciyarta.

Wannan dalilin yasa ko da Sadik ya tashi dawowa har kwalliya tayi, duk da dai bawai taji tana sonsa bane ba, sai dai kuma sosai tagane abunda Zee takeson ta gane zai faru, idan har ta bari Asad ya rigata yin aure, domin kuwa har lokacin kasa hawa social media tayi, sai yau kawai tunda sanyin safiya ta hau tana mai watsa free wedding pics d'insu da sukayi a jiya ita da Sadik.
A faninsa kuma shima d'in yau ya watsasu haka su Zee ma.

Subahanallah, zo kuga yadda hotunan sukayi bala'in jan hankulan mutane kuwa.

Lokaci d'aya waccan maganar ta mutu, aka koma zancen free wedding pics d'in da sukayi posting, wanda duka ya rage saura sati biyu ma ayi bikin kawai yanzu.

Gaba d'aya dai mtaune suka rikice, suka fara tinanin dama k'ila ba wani sonsa take sosaiba, yayinda wasu kuma suka d'aro jirginta, suna fad'in dama dai ance da babu k'wara ba dad'i, wasu kuwa fad'i suke na wuce takaici kenan
Haka dai yau jama'a suka yini yin comments da sharhi a pages d'insu


*K'ASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAK'AR MASARAUTA.*

Gaba d'aya komai ya rikice ya hargirse a cikin Bak'a Masarauta.
Yayinda Dakaru kuma harma da sauran jama'ar cikin Bak'ar Masarauta suka kasance cikin shirin yak'i tun daga ranar dasu Bir suka gudu.

Sosai Sarki Barbaru ya futa daga hayyacinsa, ta yadda ko barcin arzik'i yanzu baya iyayi, saboda rashin sanin abunda zai faru dasu da baiyiba, domin kuwa dama Boka mai wutar kaskone yake musu duban abunda zai faru a gaba, yanzu kuma babushi kwata-kwata., Gashi shi kuma yana tsoron yasaki jiki kwatsam wani bala'in ya taso musu kamar yadda Boka ya fad'a a wancan shud'ad'd'en lokacin.

Hakan yasa ko zaman fada ma yanzu gaba d'aya aka dena yinsa.
Kana kuma sosai yayi nadamar kashe Boka mai wutar kasko da yayi, saboda ya sani ko banza da yana nan da yanzu ya binciko musu abunda zai faru a gaba, gashi kuma d'ansa daya bari bai kai ga koya masa yadda ake abubuwan ba bare shi yayi.

A b'angaren Gimbiya Salwa Mahaifiyar Gimbiya Tasmir kuwa, sosai ta rame ta kuma fige, a kullum cikin tinanin halin da 'yarta ta take aciki take.
Sai dai kuma duk da haka bata fatan ta dawo cikin gidan nasu kwata-kwata a yanzu, saboda a yadda taga Sarki Barbaru ya d'au zafi, tasan babu abunda zai hanasa kasheta har lahira idan ta dawo d'in, domin kuwa ya fad'a da bakinsa ma, kuma kullum cikin fad'a yakeyi.

Haka shima Yarima Sauman Babban d'ansa a kullum fad'i yake muddin ya ganta saiya kasheta.
Yayinda sauran ahalin gidan nasu kuma suke a cikin matsananciyar kewarta, tare da fatan su sake ganinta har Gimbiya Haiwa kuwa.


A b'angaren Iyar Bayi kuwa sosai jikinta yayi kyau, bayan doguwar jinyar datasha tamkar bazata tashiba ta silar azabar da aka gana mata.
Sai dai kuma zuwa yanzu Alhamdulillah, saboda jikinta yayi kyau, tana iyayin har 'yan k'ananan ayyuka da kanta, amma fa kullum da tinanin Jaruminta take yini ta kuma kwana.


*K'ASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.*.

Suna futowa daga cikin Fada Mai Martaba yacewa Waziri aje anemo bulalan shad'insu, da aka d'ebi sama da shekaru hamsin rabon da ayi amfani dasu a tsumasu.

Ai kuwa cikin sauri ya juya domin yaje ya aiwatar.

A b'angaren Jakadiya kuwa cikin matsanancin farinciki mara misaltuwa ta tafi amso maganin da aka sata ta karb'o, saboda tana ganin hakan wata babbar damace tazo musu ita da Gimbiya Huwaila, domin kuwa dama a yau sai da suka tattauna da ita akan yadda zasuyi su samu aiwatar da sabon aikin da boka yace suyi wanda sukai akan Asad.

Ita kuwa Gimbiya Amina lokacin da 'yar rahotonta tazo tana bata labarin halin da Yarima Asad yake ciki, tab'e baki tayi tana mai cigaba da girgiza k'afarta d'aya akan kujera.
Tukun daga bisani ta kalleta tana mai bud'e baki tace.

"Daga yau daga yanzu bana son na k'arajin kin kawo mun ko wane kalar labarinsu, domin kuwa nagaji da asarar dukiyata da nakeyi kullum babu abunda ke samunsu, dan haka na hak'ura, saboda ko ba haka bama nima bani da d'an da zai gaji Sarautar Wasai, tunda gashi har na gama haihuwa ban haifi d'a namiji ba, dan haka bazan cigaba da yiwa wasu aikiba."

Ta k'arasa maganar fuskarta a tsantsar d'aure, tana mai mayar da idanuwanta kan tamfatsetsiyar tv'n da take acikin d'akin.

Ita kuwa 'yar rahotonta jiki asab'ule ta mik'e tsaye tana mai fucewa daga cikin d'akin ranta duk ba dad'i, saboda sanin da tayi na shikenan tagama samu a wurinta.

Jakadiya kuwa da sassarfarta ta k'arasa wurin da mai had'a magani yake.
Itatuwa ne kala-kala yake dafasu a cikin tukunya sunata faman futar da tururi.
Kana bayan sun tafasa sosai ya d'aga tukunyar yana mai juye ruwan a cikin wata k'atuwar k'warya, sannan yacewa Jakadiya ta d'auka tayi maza ta kai.

Murmushi Jakadiya tayi tana mai fad'in.
"Angama bokan turai."
Tukun ta d'auki k'waryar tana mai kama hanyar futa daga cikin gidan.

Tana zuwa soro ta dire k'waryar a k'asa, tukun ta tawo da sauri tana mai lek'awa waje.

Ganin da tayi babu wanda ke tunkaro wurinne, ya sanyata zura hannunta a cikin riga tana mai zaro wani k'ullin k'aton tsumma aciki.
Tukun ta kwancesa tana mai sake duban hanya, kana ta k'arasa wurin da k'waryar take tana mai juyesa gaba d'aya cikin ruwan.
Sannan tayi sauri ta mayar da tsumman cikin jikinta, tukun ta d'auki k'waryar, kasancewar kuma itatuwan da aka dafa irin jajayen nan ne, shiyasa ko kad'an abun da ta zuba a cikin bai nunaba.

Da sauri ta fuce daga cikin wurin tana mai dosar part d'in Gimbiya Fulani, fuskarta d'auke da murumushi, saboda tabbacin da take dashi na burinsu yau zai cika cikin sauk'ak'k'iyar hanya, ba tare da kowa ya saniba.

Da sassarfa Hadima Larai data hango Jakadiya take tafiya har tana d'an had'awa da gudu-gudu.
Hakan yasa Jakadiya na shiga cikin compound d'in itama ta shigo.

Mai martaba daya sallami fadawansa shima yana hango Jakadiya yayi mata alamar da tayi sauri takai maganin da yake ta futar da turiri daga wurin da yake.
Wanda hakan kuma da Hadima Larai tagani ne ya sanyata yin sauri ta matsa kusa da Jakadiya, ya zamto sun jera kafad'u a saiti kenan.

Kafad'arta tasanya tana mai bangazar kafad'ar Jakadiya da ita.
Da sauri kuwa ta waigo b'arin da take cikin tsananin mamaki.
Take kuwa idanuwansu suka sark'e wuri d'aya.
Wani irin kallo sukayiwa junansu mai cike da ma'anoni daban-daban, kafin daga bisani kuma Hadima Larai ta shammaci Jakadiya tana mai sanya gwiwar hannunta ta bige k'waryar jikake fasssss!!!
K'arar fad'uwarta a k'asa tana mai darewa gida biyu, gaba d'aya ruwan maganin ya malale a k'asa.

Da sauri Mai Martaba kuma da yake shirin shiga ciki ya juyo, saboda k'arar da yaji, yana mai sauke idanuwansa akan fuskar Hadima Larai cikin wani irin yanayi, kafin daga bisani kuma ya janyesu yana mai mayar dasu kan ruwan maganin da yake malale a k'asa.........!!✍



_ABUN DA BAKU SANI BA SHINE, NI UMAR NA JIMA DA KAMMALA RUBUTUN BAK'AR MASARAUTA, HAKAN YASA BANK'I BA MU KAI WATA SHEKARAR BA TARE DA MUN GAMA DAN SAURAN DA YA RAGE BA MUDDIN BAZA KU DINGA COMMENT DA SHARHI BA. 😀😀_


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*28*



Da sauri Hadima Larai ta durk'usa k'asa tana mai d'aukar k'waryar, saboda wani irin kallo da taga Mai Martaba yayi mata, yayinda Jakadiya kuma takasa gaba ta kasa baya, tana mai jin wata irin muguwar tsanar Hadima Larai na lullub'eta, ta yadda har takejin tamkar ta shak'e mata wuya.
Hadima Larai kuwa tana d'ago fasassar k'waryar ta juyo b'arin da Jakadiya take a tsaye, hakan kuwa shine ya sanya idanuwansu suka k'ara sark'ewa cikin na juna.
Kallon da taga Jakadiya nayi matane ya sanyata wurga mata wani matsoyacin kallo itama, kana ta bud'e baki tana mai yin k'asa da muryarta wurin fad'in.

"Ko kina da abun fad'ene ankifar da mugun abun naku, kuma kisani ina gab da fallasa mugun abunku a cikin gidan nan, domin kuwa kome kukeyi a cikin tafin hannu kukeyinsa."

Ta k'arasa maganar tana mai hucewa da sauri ta tafi domin ta anso wani maganin.
Yayinda Jakadiya kuma taji wani irin masifaffen gumi ya yanko mata, lokaci d'aya kuma jikinta ya d'auki wata irin matsannaciyar karkarwa, sai dai kuma takasa ko da motsi daga wurin da take haryanzu.
Amma kallo d'aya mutum zai mata ya fahimci bata da gaskiya, saboda yadda tayi bala'in rud'ewa ta kuma firgice.

Mai Martaba da ransa yake ab'ace kuwa da ruwan maganin da suka b'arar, bayan sun san ana jira, sai yake ganin kamar Hadima Laraice ta kifar dashi tana sane, duk da dai ya juya baya abun ya faru k'ararce ta janyo hankalinsa, amma kuma yanayin yadda yaga jikin Jakadiya na rawa, ita kuma Hadima Larai ta d'au k'waryar ta huce ba tare data bita ba, yasanya yaji wani tinani ya d'arsu a zuciyarsa, hakanne ya sanyasa sake k'ure Jakadiya da ido, yana mai kallon yadda har lokacin take a matuk'ar firgice.

"Tabbas babu tantama da akwai abunda ke faruwa, wanda babu wanda yasansa sai ita da Hadima Larai."
Mai Martaba ya raya haka a cikin ransa yana mai janye idanuwansa daga kan Jakadiya, kana ya juya yana mai shigewa ciki.

Ita kuwa Jakadiya ganin da tayi Mai Martaba ya shige cikine ya sanyata juyawa da matuk'ar sauri, tana mai fucewa ta doshi b'angaren Gimbiya Huwaila kai tsaye.

Ganin da tayi bata falone ya sanyata hucewa zuwa bedroom d'inta da matuk'ar sauri.
Tana k'arasawa kuwa ba tare data tsaya wani neman iziniba ta hankad'a k'ofar, tana mai danna kanta ciki.

Da sauri Gimbiya Huwaila da take zaune a gefen gado ta mik'e tsaye cikin matsancin firgici, tana mai fad'in.
"Meke faruwane Jakadiya kika doko mun k'ofa bako sallama?"

"Da akwai matsala ranki ya dad'e ne, domin kuwa gaba d'aya wannan tsinanniyar Hadimar tata tasan abunda mukeyi, dan harma ta kifar da k'waryar maganin ya zube gaba ki d'ayansa a k'as...."

"Me kike nufi data kifar da k'waryar, idan na fahimta kinaso ki fad'amun cewar nayi asarar dubunna d'aru-ruwan kud'ina a wannan karanma, shin kinsan irin wahalar da aka sha kafun asamu had'uwar aikin nan."

Gimbiya Huwaila ta fad'a a wani irin hargitse tana sakin huci.

"To ai da iyakar asarar kud'inne ma da da sauk'i, saboda wasu zasu zo, amma fa yanzu ina miki maganar tasan abunda mukeyi, domin kuwa da bakinta ta furta mun kalmar tana gab da tona asirinmu."

Cewar Jakadiya har lokacin jikinta na rawa.
Wanda hakan kuma ya sanya Gimbiya Huwaila ta sake tsananin firgita, saboda abun da taji Jakadiya ta fad'a.
Kafin daga bisani kuma ta fara girgiza kanta, kana ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Inaaa wallahi tayi k'arya ta tona mun asiri, dan haka dolene ma nayi maganinta, shima kuma yaron zaici ubansa, domin kuwa bazan tab'a barin Fulani 'yar bayan-bayana ta zama uwar Sarkin gobe ba."

Ta fad'a a matuk'ar kausashe, tana mai fad'awa kan gado ta zauna tare da dafe goshinta da tafin hannu.

A b'angaren Hadima Larai kuwa cikin matsanancin sauri ta k'arasa gidan me magani.
Kasancewar kuma da ya juyewa Jakadiya wancan sabo ya mayar, a cewarsa ya huta da dafawa gobe da safe, sai dai kawai ya d'umamasa, shiyasa kuwa Jakadiya na zuwa ta sanar dashi wancan ya kife.

Tsayuwar 'yan mintina tayi a wurin kawai sabon ya tafaso, hakan yasa ya tafi ya d'auko wata sabuwar k'waryar ya juye mata a ciki.
Kana ita kuma ta d'auka cikin sauri tana mai nufar b'angaren Fulani.

Shi kuwa Mai Martaba lokacin da yazo yana shigowa yace.

"Ina Asad d'in yake ne?"

"Wanka yakeyi."
Gimbiya Fulani ta fad'a a tak'aice, tukun ta d'ora da fad'in.
"Barka da futowa."

Amsa mata yayi yana mai zama kusa da Babban Yaya, bayan sun gaishesa shi da Al'amin.
Tukun gaba d'ayansu sukayi shiru ba tare da ya basu labarin kifar da maganin da akayi ba.

Suna zaune anan sukaji k'arar k'wank'waso k'ofar.
Hakanne yasa Al'amin mik'ewa yana mai zuwa ya bud'eta.

Hadima Laraice rik'e da k'waryar maganin a hannunta.
Tana ganin Al'amin ta mik'o masa tana mai fad'in.

"Ya jikin d'an uwan naka ne?"

"Jiki da sauk'i ya shiga wanka ne ma."
Ya fad'a yana mai karb'ar k'waryar.

"Allah ya k'ara sauk'i, to ka kuma ce ina masa sannu."

Ta k'arasa maganar tana mai juyawa ta tafi.
Tukun shima Al'amin ya juya hannunsa rik'e da k'waryar yana mai komawa ciki.

Mai Martaba da kansa ya mik'e tsaye yana mai karb'ar k'waryar maganin a hannunsa, kana ya tafi zuwa bakin k'ofar bathroom d'in yana mai k'wank'wasata.

Yarima Asad kuma da yake lumshe da idanuwansa jikinsa na matsananciyar karkarwa kuwa, da k'yar ya iya mik'ewa tsaye.
Tukun ya juya bayansa yana mai mik'a hannu ya janyo towel d'in da Mamy ta ajiye masa.
Kana ya d'an d'aurasa a k'ugunsa cikin dabara, tukun yayi gyaran murya da muryarsa da bata futa kwata-kwata.

Shi kuwa Mai Martaba jin shirun da yayine ya sanyasa turo k'ofar ya shigo.

Da sauri ya k'araso wurin Yarima Asad, saboda ganin yadda jikinsa ke matananciyar karkarwa da yayi.

"Sannu kaji Babana."

Cewar Mai Martaba cikin tsananin tausayin d'an nasa, yana mai shafa sumar kansa.
Kana ya durk'usa k'asa yana mai zubar da wancan sauran ruwan na cikin bawon wankan, sannan ya juye na maganin aciki, tukun ya d'ebi ruwan sanyi ya d'an zuba a cikinsa saboda ya rage zafi.
Kana ya d'ago yana mai kallon Yarima Asad tare da fad'in.

"Yi maza kayi wanka dashi, ba saika sa sabuluba in sha Allah cikin kwanakin da basu zarce hud'u zuwa biyar ba zaka warke tas."

"S...sanyi...nakeji Da..dyyy!!"

Ya fad'a dak'yar leb'ensa na karkarwa tamkar zasu fuce daga jikin bakinsa.

"Sannu Babana, ka daure kayi zai taimaka maka har wurin dena jin sanyin."

Ya fad'a cikin matsanancin tausayinsa, tukun ya juya yana mai fucewa daga cikin d'akin.

Shi kuwa Yarima Asad cire towel d'in yayi yana mai komawa ya sake durk'usawa a gaban robar.
Kana ya fara d'ebo ruwan maganin da yake da matuk'ar zafi yana mai zubasa a jikinsa.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, saboda yadda yaji dad'in saukar ruwan tamkar yana sosa wuraren da ciwukan suke a jikinsa.
Hakan yasa ya cigaba da kwarasa a jikinsa har sai da ya tabbatar daya k'are tas duk yawansa, tukun ya mik'e tsaye yana mai sake d'aukar towel ya d'aura, sannan ya juyo yana mai yiwa bakin k'ofa cikin cije baki.

Yana futowa Al'amin da Babban Yaya sukayo wurinsa da sauri, suna masu fara jera masa sannu.

Jinjina musu kai kawai ya iya yi, saboda yadda jikinsa ke rawa, tukun ya samu gefen gado ya zauna akai.

Ita kuwa Gimbiya Fulani da sauri ta taso tana mai matsowa wurin da yake, hannunta rik'e da wani d'an k'aramin cup da yake cike da nono mai had'e da magani a cikinsa.

Zama tayi a gefensa tana mai d'ora masa cup d'in akan lips d'insa.
Amma sai ya janye baki yana mai

Please Login or Register in order to submit comment