Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kafin daga bisani kuma ya lailaya kanta yana mai take ta a guje, ya doshi get ɗin da zai futar da shi daga cikin part ɗin su.

A kuma lokacin shima Al'amin ya danno kansa cikin part ɗin domin yazo wurin sa, kasancewar rabon su da juna tun jiya da suka dawo babu wanda ya sake neman wani, saboda gajiyar da suka kwaso.

Cikin tsantsar mamakin ganin motar Yarima Asad da yayi tana nufo get ɗin yaja ya tsaya a wuri ɗaya, domin kuwa bai taɓa tinanin idan ya ƙarasa cikin bama zai samu Asad ɗin ya tashi daga bacci, sai kuma gashi ya gansa yana shirin futa.

"Yess! Yess!! Asad! Asad!! Asad!!!"

Al'amin ya faɗa da ƙarfi bayan ya matso saitin wurin motar Asad, yana mai ɗaga masa hannu, saboda ganin sa da yayi ya fafaro motar a guje yana shirin fucewa daga cikin part ɗin.
Amma kuma sai dai ko alamun tsayawa baiga Asad yayi ba, duk da yana da tabbacin ya gansa, saima sake fafarar motar sa da yayi yana mai fucewa daga cikin part ɗin gaba ɗaya.

Hakan yasa ko Al'amin suman tsaye yana mai bin bayan motar da idanuwansa.
Yayinda zuciyar sa kuma take cike da tarin tinanin wurin da Asad ɗin zaije da har baya son su tafi a tare.
Domin ko a yadda yasan Yarima Asad ko kaɗan bai kawo zai tashi daga bacci da wuri ba yau, duba da irin tafiyar da sukayi jiya, amma sai gashi nan yaga alamun bama a yanzu ya tashin ba, tunda gashi nan har ya shirya ya tafi wani wurin.

"Tabbas akwai abun da ke faruwa, domin kuwa nasan haka nan banza kawai Asad ba zaka tashi a irin wannan lokacin ba.
Kana kuma kayi tafiyarka ba tare daka nemi rakiyata ba.
Haƙiƙa da akwai abun da ke damun ka, amma koma menene ina nan ina jiranka ka dawo kabani labari, dan kuwa nasan yanzu ba lokacin zuwanka palace bane balle nace can ka tafi."

Al'amin ya faɗa har lokacin idanuwan sa akan hanyar da yaga Yarima Asad yabi.
Tukun daga bisani kuma ya juya yana mai komawa wurin da ya fito jiki a sanyaye.

A ɓangaren Asad kuwa sarai yaga Al'amin tun lokacin da ya shigo part ɗin, amma yayi hucewar sa ba tare da ya tsaya bi takan sa ba, duk da kuwa yasan wurin nasa yazo.
Sai dai kuma a yanzu ko kaɗan baya buƙatar ganin sa, domin kuwa yasan babu abaun da zai fara tarbar sa da shi sai tambayar wurin da zashi, gashi shi kuma bai tanadi amsar da zai basa ba idan hakan ta kasance.
Kana kuma zaice zai rakasa, wanda shi kuma ko kaɗan bai shiryawa yin hakan ba, asalima bazai taɓa bari Al'amin ɗin yasan abun da ke damun saba gudun rainin hankali.
Wannan dalilinne ya sanya sa nuna tamkar bai gansa ba yayi hucewar sa.

A guje ya fuce daga cikin get ɗin masarautar tasu, yana mai jin zuciyar sa na wani irin biting.

Cak motar ta tsaya abakin titi, ta sanadin take birkin da yayi, kana ya ɗan jujjuyar da kansa gefe da gefe, yana mai kallon hanyar, tukun ya ɗaga birkin yana mai shilla hancin ta zuwa kan shimfiɗeɗiyar kwaltar da take kwance a ƙasa a guje, tamkar wanda zai tashi sama.


*ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.*

Ko kaɗan jiya Bir baiyi bacci daɗi ba, saboda yadda gaba ɗaya jikin sa yayi mugun tsami.
Domin ko da farko ma gaba ɗaya baccin ƙauracewa idanuwansa yayi, babu abun da yake faman aikin yi sai tinanin-nika biyu, wato tinanin rayuwar sa da yake muradin son jin tarihin sa, da kuma tinanin yadda zai iya haƙura da Gimbiya Tasmir ya cireta aransa, domin kuwa hakan ba ƙaramun cutarwa zai zamto a gare sa ba, sai dai kuma yayi alƙawarin cire tan daga cikin ransa a hakan, ba dan komai ba kuwa sai dan farin cikin Iyar Bayi.
Kana kuma ya ƙudiri aniyar sake tambayar Iya labarin sa a gobe ko Allah zai sa ta faɗa masa, kamar yadda tai masa alƙawari.

Haka yay ta tinanin-nika ba tare da yana iya ko juyi ba daga kwanciyar da yake, saboda ciwukan da suka yiwa jikinsa ƙawanya, a haka har ya samu bacci ɓarawo ya sace sa bayan dare ya riga da ya fara yin nisa.

Yau kuwa tunda sauran sanyin safiya ya tashi.

Sosai yaji jikin sa ya saki, kana kuma duk raɗaɗin ya kauce sai ɗan abun da ba arasa ba, wato dai maganin Iya yayi aiki kenan.

A hankali yake buɗe idanuwansa har ya buɗe su duka akan fuskar Iyar Bayi da take zaune a gaban sa cikin ɗan ƙaramin ɗakin su.
Kasancewar da tinanin sa jiya ta kwana a ranta, domin kuwa har ƙaguwa tayi safiya tayi domin tazo taga halin da yake ciki, shiyasa ma tana tashi daga baccin wanke jikin ta kawai tayi ko karyawa bata tsaya tayi ba ta tawo ɗakin nasa, tana mai zama a gaban sa tare da zuba masa idanuwan ta cike da tsantsar tausayin sa a ranta.

"Sannu Jarumi na, Barkan ka da tashi."
Iyar Bayi ta faɗa a hankali, tana mai kife tafin hannun ta akan lallausar sumar kansa ta fara ɗan shafata.
Yayinda shi kuma Bir ya ɗan sake mayar da idanuwansa yana mai lumshe su.
Kana daga bisani ya sake buɗesu, tukun ya ɗan yunƙura bayan ya ɗan taune leɓen sa na ƙasa, tare da yamutsa fuskar sa yana shirin miƙewa zaune.

"Bi ahankali dai Jarumi na, karkayi fami kaji."

Cewar Iya cikin sanyi, tana mai ɗan tallabo bayan sa, yayinda idanuwanta kuma suka tara ƙwallar tausayin sa a cikin su.

"Barka da safiya Iya ta."

Cewar Bir bayan ya jingina da iccinan da suka zamto katangar ɗakin, yana mai ɗan sake lumshe idanuwansa.

"Yawwa Jarumi na yaka kwana da jikin naka kuma?"

Iyar Bayi ta faɗa idanuwanta akan sa.

Shi kuwa Bir a hankali ya buɗe idanuwansa da ya lumshe su, kana yaɗan juyar da kansa gefe, yana mai fesar da iskar bakin sa, tare da ɗan sauke numfashi.
Tukun ya sake juyowa ɓarin da Iya take, yana mai faɗin.

"Ina son na ɗan watsa ruwa, tare da wanke baki Iyata."

Yayi maganar a can ƙasan maƙoshi, ta yadda Iyar ce kawai zata iya jin abun da yace, itama ɗin kuma dan ta bada gaba ɗaya hankali da nustuwar ta zuwa gare sa ne shiyasa.

"Tom shikenan Jarumi na yanzu kuwa."
Iya ta faɗa tana mai miƙewa tsaye tare da juyawa ta fuce daga cikin ɗakin da sauri.

Ruwan zafi ta haɗa masa irin mai ɗan ƙona jikin nan, bayan ta zuba magun-gunan kashe raɗaɗin ciwukan jikinsa tare da warkar dasu a cikin sa.
Kana ta ɗauke sa da kanta tana mai kai masa shi har wurin da suke wanka.
Tukun ta juyo tana mai dawowa cikin ɗakin.

Tsaye ta samu Bir akan ƙafafuwansa yana mai shirin futowa shima.

"Yawwa Ashe ma har ka tashi Jarumi."
Iya ta faɗa fuskar ta ɗauke da murmushin farin ciki.

Jinjina mata kai kawai Bir yayi ba tare da yace komai ba, sai ɗan ɗingisawa da ya farayi yana mai ɗan cizon leɓen sa, alamun dai har yanzu da sauran ciwuka a jikin sa, yana mai kama hanyar waje.
Yayinda ita kuma Iya ta juya da sauri tana mai tafiya dan taje ta amsowa Bir abincin sa.

Ya ɗauki kusan mintina talatin a wurin wankan, kasancewar har bakin sa sai da ya wanke da hodar da suke wankewa, tukun ya juyo yana mai nufo ɗakin.

Sosai yayi matuƙar jin daɗin zafin ruwan wankan, domin kuwa ba ƙaramun ƙwari yaji jikin sa ya ƙarayi masa ba.

A hankali yake takowa, gaba ɗaya fuskar nan tasa a kumbure, ruwa na ɗiga daga cikin sumar kansa yana sauka akan fatar sa.
A haka har ya ƙaraso zuwa cikin ɗakin nasu.

Zaune ya tadda Iyar Bayi a wuri ɗaya ta tasa ƙwaryar tuwo mai zafi a gaban ta.

"Yawwa an dawo kenan Jarumi na, to maza ka shirya ka matso nan yanzu na baka tuwon nan da kaina yau."
Iya ta faɗa idanuwanta akan sa, fuskar ta ɗauke da murmushi.

Shima Murmushi Bir ɗin yayi ba tare da yace komai ba, kana ya huce zuwa wurin da wani ɗan ƙullin zani yake yana mai kwance sa.

Ƙaton ƙyallen yadi ya zaro a cikin sa yana mai goge ruwan jikin sa, sannan ya ɗauko wani wankakken ƙaton farin gajeran wandon yadi, wato dai irin na jikin sa.
Cikin ƙanƙanin lokaci ya gama shirya kansa iya na zaune a wurin da take tana kallon sa.
Kana ya juyo zuwa wurin da take yana mai samun wuri ya zauna daga gaban ta tare da tanƙwashe ƙafafuwansa.

"Yawwa Jarumi na, yanzu kaga sai na fara baka abincin tunda ka shirya ko, bayan an gama kuma sai ka sake shan maganinka gasa nan shima."

Ta ƙarasa maganar da yi masa nuni da kofin da yake ajiye a gaban ta.
Kana ta fara ƙoƙarin sanya hannun ta acikin ƙwaryar tuwon, bayan ta janye murfin fefen kanta.
Amma sai taji Bir yayi ram ya riƙe hannun nata da sauri kafin ya kai ga isa cikin ƙwaryar tuwon.
Hakanne yasa ta ɗago kanta da sauri itama, tana mai watsa idanuwanta akan fuskar sa.

Ido huɗu sukayi da shi, shima yana mai jifan ta da wani irin kallon tausayi, gaba ɗaya idanuwansa sunyi wani irin rau-rau, tamkar zai fashe da kuka.

A hankali ya janye idanuwan nasa daga kan fuskar ta, yana mai mayar da su kan hannuwansu da suke haɗe a wuri ɗaya, kana ya sake ɗago ɗayan hannun nasa a hankali, yana mai kamo ɗayan hannun Iya dashi ya haɗa ya damƙe su a cikin tafukan hannayensa da ɗan ƙarfi.
Tukun ya ɗago kansa yana mai jefa dara-daran idanuwansa da suke cike da ƙwalla a cikin na Iyar bayi, da itama take kallon nasa.
Kana ya ɗan langwaɓar da kansa gefe, sannan ya buɗe baki cikin yin ƙasa da murya, bayan ya ɗan lumshe idanuwansa tare da buɗe su, yana mai cewa.

"Kimun afuwa Iya ta, haƙiƙa banso irin wannan ranar ta sake mai maituwa ba.
Wato ranar da zan sake tambayar Iya ta akan tarihin samuwa ta.
Naso na haƙura da son jin labarin tun a waccan ranar, dana lura da yadda hankalin Iyata ke kai ƙololuwa wurin tashi a duk lokacin da zan tambaye ta, naso ace nabar zancen tun a ranar dana ga firgici da tashin hankali acikin ƙwayoyin idanuwan Iyata, naso ace tambayar itama ta zama tarihi ba tare da na samu amsar taba, tamkar yadda labarin ya kasance tarihi.
Sai dai kuma Kash, gaba ɗaya hakan yaƙi yuwuwa, domin kuwa zuciya taƙi aminta da haƙurin da nake bata, taƙi ta yadda da tausasawar da nake mata, taƙi ta yadda da lallashin da nake mata akan ta rabu da son jin koni ɗin wane ne."

Ya ƙarashe maganar cikin sanyin murya, yana mai rumtse idanuwansa da matuƙar ƙarfi.
Kana yana jin wani irin yanayi na tsarga jiki da jijiyoin jikin sa, yanayi wanda bai taɓa jin makamancin sa ba a rayuwa, yanayi mai kama dana maraici.
Yana mai jinsa tamkar yaron da ya rasa Uwa da Ubansa bayan yayi muguwa shaƙuwa da su a lokaci guda.
Gaba ɗaya jikin sa yayi sanyi, irin sanyin da bai taɓa yi ba, yayinda zuciyar sa kuma ta cika da zumuɗin son jin tarihin sa.

Ita kuwa Iyar Bayi da matuƙar ƙarfi ta sake damƙe tafukan hannyen su da suke haɗe wuri ɗaya, tana mai dunƙule su.
Yayinda jikin ta kuma yake wata irin karkarwa, fargaba da tashin hankali gaba ɗaya sukai mata saukar ungulu a jiki da zuciyar ta.

Wani irin duka zuciyar ta take yi da matuƙar ƙarfi tamkar zata hudo ƙirjinta ta futo waje, ga kuma gumi da ya fara yanko mata a lokaci guda, duk da sassanyar iskar da aka tashi da ita a yau ɗin kuwa.

Da ƙarfi itama ta rumtse idanuwan, tana mai jin yadda kalaman Bir ke ratsa ko wane lungu da saƙo na ilahirin jini da tsokar ta.
Ta yadda har wani irin mugun tausayinsa ya sake lulluɓe ta.

A lokaci ɗaya suka buɗe jajayen idanuwansu da gaba ɗaya suka canza launi a cikin na junan su.
Kana Bir ya sake buɗe baki cikin yin ƙasa da murya, yana mai ɗorawa da cewa.

"Wato tarihin rayuwa ta. Zuciyata ta kasa yin haƙuri, na rasa dalilin da ya sanya ako da yaushe nake son sanin ko wane ne ni ɗin na ƙara ƙaruwa acikin zuciya ta, na rasa dalilin da ya sanya na kasa yiwa Iyata abun da take so bayan ita kuma tayi mun komai a rayuwa."

Ya ƙarasa maganar hawaye na ɓallewa daga cikin idanuwansa, saboda yadda yaga na Iyar Bayi ma na tsiyaya.
Kana kuma ba tare da ya tsaya jin abun da Iya zata faɗa ba ya cigaba da cewa.

"Yauce rana ta ƙarshe, wacce zan ƙara tambayar Iya ta waye ne ni.
Muddin kuma yau ɗin ma ta zamto tamkar waƴan can ranakun, wato ban samu amsar tambaya ta ba daga bakin Iya ta, to nayi alƙawarin kulle bakina daga rana irin ta yau akan batunnan, nayi alƙawarin sanyawa zuciya ta haƙuri da dangana koda hakan kuwa zai zamto cutarwa gare ta.
Wato ina nufin daga yau bazan sake yin makamanacin irin wannan kalamin ga kowa ba bama Iya ta kaɗai ba, domin kuwa na sani muddin ban samu amsa ta ba ayau, to babu amfanin da samun nata zaiyi mun a rayuwa, shiyasa Iya ta taƙi faɗa mun, kana kuma na tabbatar da babu alkhairi acikin labarin."

Ya ƙarasa maganar yana mai sake gyara zaman sa a wurin da yake, wato dai ya ƙara fuskantar Iya, yayinda ruwan hawaye kuma keta aikin shatata daga cikin idanuwansu tamkar an buɗe famfo.

A hankali, kana kuma cikin sanyin murya ya ɗan sake ɗaga jajayen laɓɓansa, yana mai faɗin.
"Shin wanene Jarumi? Su waye ne iyayen sa?
Shin da gaske ba iya bace ta haifi Jarumi Iyata?"

Ya ƙarasa maganar da lumshe idanuwansa.
Yayinda Iyar Bayi kuma ta miƙe tsaye zumbur daga zaunen da take tamkar wadda aka tsikara da allura.
Lokaci guda gaba ɗaya ta sake ruɗewa da kiɗimewa, babu abun da take aikin yi sai faman zaro idanuwanta da suka koma jajaye tare da girgiza kai.
Kafin daga bisani kuma ta juya bayan ta tana mai kai duban ta zuwa bakin ƙofar ɗakin, domin taga ko akwai wanda yaji furucin da Bir ɗin yayi.
Kana kuma ta sake juyowa gare sa tana mai sake watsa idanuwanta akan fuskar sa.

Shi kuwa Bir cikin sanyi ya buɗe idanuwansa da ya lumshe su akan fuskar Iya.
Ganin da yayi jikin ta na wata irin tsuma da karkarwa ne, ya sanya hankalin sa sake bala'in tashi shima.
Lokaci ɗaya ya fara girgiza kansa, yana mai jin inama bai tambaye tan ba, domin kuwa ba ƙaramar firgita yayi ba da ganin yadda ruwan hawaye ke kwaranya daga cikin idanuwanta.

Ita kuwa Iyar Bayi cikin karkarwar da jikin ta keyi tamkar mazari, ta sake ɗan durƙusowa kan Bir.
Kana ta miƙa hannuwanta biyu tana mai kamo na Bir da su, tare da yi masa alamar ya tashi tsaye shima.
Ganin hakan da yayi ne ya sanya sa miƙewa tsaye da sauri shima, yana mai zuba firgitattun idanuwansa akan fuskar Iyar tasa shima.
Yayinda ita kuma Iya ta saki hannun sa ɗaya, tana mai sake damƙar tsintsiyar hannun sa ɗaya da ƙarfi.
Kana ta juya tana mai fara ɗaga ƙafafuwanta ta doshi hanyar futa daga cikin ɗakin.
Ganin hakan da Bir yayi ne ya sanya sa ɗaga ƙafafuwansa da yake jin sun masa wani irin mugun nauyi, yana mai bin bayan ta.

Cikin sauri Iyar Bayi take tafiya hannun ta riƙe dana Bir tana jansa.
Kallo ɗaya mutum zaiyi musu ya gane cewar kwata-kwata basa cikin nitsuwa, musamman ma Iya kuwa da take wata irin tafiya tamkar zata kifa ƙasa.

A haka har suka ɓulla zuwa wani tafkeken wuri mai cike da dogayen bishiyu tare da duwar-watsu tako ina.
Amma duk da haka Iya bata tsaya ba har sai da ta dangana da gaban wata shirgegiyar bishiya.
Kana ta jingina Bir a jikin ta tana mai sakin hannun sa da ta riƙe.
Tukun ta juya tana mai yin taku ɗaya biyu zuwa biyar daga wurin da take zuwa gaba, kana ta kama hancinta tana mai face wata uwar majinar data taru a cikin sa.
Sannan ta sake juyowa cikin sauri tana mai dawowa wurin da Bir yake a tsaye.
Shi kuwa Bir idanu kawai yake bin Iya dasu, domin kuwa gaba ɗayan sa shima ɗin a ruɗe yake, wanda kuma ba komai bane ya ruɗar da shi ɗin sai irin halin da yaga Iyar ta shiga ta sanadin tambayar da yayi mata.

Sake kamo hannuwansa Iya tayi, kana ta zaunar da shi a ƙasa.
Sannan itama ta zauna a gaban sa, tana mai tanƙwashe ƙafafuwanta.
Tukun suka haɗe idanuwansu wuri ɗaya suna masu kallon-kallo ya junnan su.
Kafin daga bisani kuma Iya ta ɗaga laɓɓanta cikin dashash-shiyar muryarta da kuka ya dusashe ta, tana mai faɗin.

"Haƙiƙa yau zan sanar da kai labarin samuwa ka a cikin BAƘAR MASARAUTA Bir, zan baka tarihin da aka gargaɗe ni akan kar in taɓa barinka kasan da shi, gargaɗi mai tsauri ma kuwa.
Amm yau zan faɗa maka ko waye ne kai ɗin, duk da sanin da nayi hakan tamkar dai-dai yake da na ɗau huƙa na burma wa ƙawon zuciyata ne!
Zanyi hakanne kuma ba dan komai ba sai dan soyayyar da nake yi maka, zan haƙura da rayuwata domin ta Yaro na ta in ganta.
Zanyi sadaukarwa irin sadaukarwar da Uwace kawai take iyayin ta a duniya, wato zan sadaukar da rayuwata domin kasan labarinka.
Tabbas daga yau tambayar ka ta kai ɗin wanene zata ƙare a wurin ka Jarumi na, sai dai kuma ina so ka sani, ako wane lokaci ni kuma zaka iya rasani tun daga yanzu kuwa, dan haka kasa a ranka cewar Iyarka ta zama gawa, amma kuma bana son kayi kuka ko bayan raina, abu ɗaya kawai da zan so kayi shine.
Muddin ya zamto babu ni a cikin BAƘAR MASARAUTA, to ina son ka fara tinanin hanyar da zakabi ta sadaka da iyayen ka na asali."

Ta ƙarasa maganar tana mai ɗaukar tafin hannunta ta ɗora sa akan fuskar Bir, tana mai goge masa hawayen da suke kwaranya daga cikin idanuwansa, domin kuwa sosai take jin zafin kukan nasa acikin ranta.

Shi kuwa Bir lokaci ɗaya yaji gaba ɗaya baya son jin labarin nasa da yake muradin ji da, asalima sai wata irin fargaba da tsoro ne yaji sun lulluɓe sa, saboda furucin iya, domin kuwa shi kansa ya sani bazai taɓa iya jurar rashin ta ba a duniyar BAƘAR MASARUTA.
Tabbas ya sani muddin akace babu Iya a cikin BAƘAR MASARAUTA, to shima babu shi ko, domin kuwa itace komai nasa, kana kuma ita kaɗaice wacce ya shaƙu da ita a cikin Baƙar Masarauta.

Hakanne yasa ya fara girgiza kansa, yana mai buɗe baki cikin kuka yace.

"A'a, a'a Iyata, indai nine na haƙura ki dena wannan furucin, domin ko bazan taɓa iya jurar rashin ki ba, bazan iya ju...."

"Zaka iya Bir, zaka iya ɗin, ko ka kamanta kai ɗin wnane ne.
Jarumi fa, Jarumi sunanka, shi kuma Jarumi kasan daban yake a cikin mutane, kana kuma babu abun da yake gagarar Jarumi."

Cewar Iyar Bayi bayan tasa tafin hannunta ta toshe bakin Bir da shi, tana mai girgiza masa kai itama.
Kana ta rumtse idanuwanta da ƙarfi, tana mai jin yadda zuciyarta ke wani irin tsinkewa.
Tukun daga bisani ta buɗe idanuwan nata akan fuskar Bir, sannan ta buɗe baki tana mai faɗin.
"Shekaru talatin baya da suka shuɗe, a safiyar wata laraba tashin hankalin ya fara."

A kuma dai-dai wannan lokacin Sarki Barbaru y................✍


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*04*



Ya miƙe daga zaunen da yake akan kujera, yana mai yin bakin gadon Gimbiya Tasmir da matuƙar sauri, saboda idanuwanta da yaga tana motsa su, alamun ta farka kenan.

A hankali take buɗe idanuwan nata har ta buɗe su duka akan fuskar mahaifin nata.
Kana ta mayar da su ta lumshe tana mai ɗan fesar da numfashi.
Yayinda shi kuma Sarki Barbaru ya nemi wuri ya zauna a bakin gadon cikin tsantsar farin ciki, yana mai faɗin.

"Marhabun da farkwa Ƴata."

Ya faɗa cikin farin ciki, yana mai miƙa hannunsa ya kamo tafin hannunta da shi yana mai riƙe sa a cikin nasa.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir a hankali ta sake buɗe idabuwanta akan fuskar sa.
Kana ta fara yunƙurin tashi zaune daga kwancen da take.

Ganin hakan da Sarki Barbaru yayi ne, ya sanya sa sakin hannunta da ya riƙe, yana mai miƙewa ya ɗago ta zaune tare da jingina ta da allon gadon ɗakin.
Tukun ya koma ya zauna a kusa da ita.

A kuma lokacin itama Gimbiya Salwa ta shigo cikin ɗakin.
Tun daga bakin ƙofa ta fara washe baki, tana mai ƙaro saurin ta, sabo da hango ƴarta ta da tayi ta tashi.

Yayinda ita kuma Gimbiya Tasmir ta sake ɗan lumshe idanuwanta.
Kana ta buɗe su tana mai ɗan matsowa daga jikin allon gadon da take jingine zuwa gaban mahaifinta.

Cikin sanyi ta dago tafukan hannayenta biyu tana mai kamo tafukan hannayen mahaifin ta da su.
Kana ta ɗan ɗago kanta tana.mai juyar da shi gefe ta fesar da numfashi, sannan ta sake juyowa ɓarin da Sarki Barbaru yake tana mai watsa idanuwanta a cikin nasa.
Yayin da hannuwan su kuma suka kasance haɗe huri ɗaya.

A hankali, kana kuma cikin sanyi ta buɗe baki tana mai cewa.

"Haƙiƙa babu abun da kunnuwana suka tashi da muradin ji face labarin sa.
Ina son sanin ko shi waye, ina son jin yadda murɗaɗɗen tarihin da ako da yaushe Babana ke faɗen sa yake, ina son sanin dalilin da ya sanya ya futa daban da sauran Bayi."

Ta dakata haka tana mai ɗan sauke numfarfashi.
Yayinda idanuwanta kuma har lokacin suke akan fuskar mahafinta, tamkar yadda shima ɗin yake kallon ta.
Kana ta ɗora da faɗin.

"Shin wane shi Baba?"

"Amma ai kya bari kiyi wanka ki wanke baki, kana kuma ki karya kafun a baki labarin ko, ko ko kin manta yanzu kika tashi daga bacci ne?"
Cewar mahaifiyar ta tana mai dafa kafaɗar ta.
Yayinda ita kuma Gimbiya Tasmir ta rumtse idanuwanta da matuƙar ƙarfi, tana mai ɗan taune leɓen ta na ƙasa, domin ko ba ƙaramin ƙagara tayi ba taji labarin wancan ƙasƙantaccen Bawan, da ta tsanesa sama da komai da kowa dake a cikin duniya yanzu.

"Tabbas hakane Ƴata, kije ki fara yin wankan ina nan ina jiran ki, da zarar kin gama ni kuma zan fara baki labarin."

Sarki Barbaru ya faɗa shima yana mai zame hannuwansa da suke a cikin nata.

Jin hakan da tayi ne, ya sanya ta buɗe idanuwanta tana mai ɗan fesar da iskar bakin ta a gefe.
Kana ta fara ƙoƙarin sauka daga kan gadon ba tare da tace komai ba.

Hakan da Gimbiya Salwa ta gani ne ya sanya ta ƙarasowa zuwa wurin da take, tana mai sa hannu ta kamo ta, sannan ta riƙe ta suka doshi hanyar bayin da yake a nan cikin ɗakin nata.

Sai da Gimbiya Salwa ta gama haɗa mata komai, tukun ta juyo ta futo daga ciki.
Yayinda ita kuma ta fara wankan cikin sauri.
Gaba ɗaya hankalinta na can cikin ɗakinne, babu abun da take muradin ji face labarin sa, shiyasa ma ko kaɗan bataso ta tashi daga wurinba ba tare da an gama bata labarin ba, saboda da abun takwana a ranta kuma da shi ta tashi.

Duka-duka baifi minti goma shabiyar ta ɗauka a ciki ba sai gata nan ta futo ɗaure da tawul a ƙirjinta.
Yayinda hannunta ɗaya kuma yake riƙe da wani ɗan ƙarami tana tsane jikin ta da shi.

Kai tsaye ta huce gaban tamfatse-tsen haɗaɗɗen mudubinta da yake cike da kayan kwalliya akan sa.

Tana zuwa taja kujera ta zauna tana mai janyo mayukanta ta fara murje fatar jikin ta da su.

Cikin sauri take yin komai tamkar wadda zata tashi sama.

Body spray ta ɗauka tana mai feshe jikinta da shi.
Kana ta juya tana mai nufar gaban wardrob ɗin ta ba tare da ta shafa ko hoda akan fuskarta ba sai mai kawai.

Doguwar riga mara nauyi ta sanya a jikin ta.
Kana ta mayar da murfin wardrobe ɗin ta rufe.

Sosai tayi matuƙar rama yadda kasan wacce tayi ciwon sati a kwance, kana fuskar kumata ta ƙarayin haske da ita, yayinda har lokacin kuma idanuwanta suke aɗan kumbure, saboda kukan da tayi jiya.
Sosai tayi matuƙar kyau cikin shigarta, yadda kasan a saceta.

Ahankali ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai nufar wurin da mahaifan nata suke a zaune, wato bakin gadon ta.

"To saura abinci kuma ya rage yanzu ko."
Cewar Gimbiya Salwa tana mai yiwa Gimbiya Tasmir

Please Login or Register in order to submit comment