Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sanya tuni su Baby Al'amin da kuma camera man d'in da suka d'auko suka fara aikin yi musu hotuna.

Iyakar shagali dai yau sunsha shi, yayinda su Al'amin kuma sukaci rawa irin rawar fulani daya koya a zuwansa wurin yau, domin kuwa shi dama mayen rawane, Yarima Asad ne wannan bata damesa ba, asalima shi ko kad'e-kad'e baya sonsu, yanzu zaice hayaniya ne zasu sanya masa ciwon kai, sai kuma gashi yau amai-makon yaji ciwon kan sai farincikin da yake ji yana lullub'esa ma.
Haka dai akasha shagali iyakar shagali, Amarya da Ango suka sha lik'i.
Tukun da dare yayi taro ya watse, su Yarima Asad suka huce b'angarensu Habu.
Yayinda su Baby kuma suka tafi d'akin Gimbiya Haddiyal.

****
Yau itace ranar da za'a kai lefe a cikin masarautar wasai.
Hakanne yasa Ummi ta janye Gimbiya suka tafi gida, saboda Mai Martaba yace nan d'in za'a kawo lefe.
Kwata-kwata kuma babu abunda aka bambanta a tsakanin kayan da aka zubawa Gimbiya Haddiyal, da kuma Gimbiya Tasmir, tare da budurwar Al'amin.

Sosai aka kaske kud'i bana wasaba a wurin had'a lefen, domin kuwa iyakar jakun-kunan da aka zuba kayayyakin ma abun kallone.
Saboda komai daga Dubai aka kawosu.
Haka aka tafi kai kayan duka a lokaci guda, ko wacce akwatuna goma shabiyu dai-dai.

Haka dai shagalin biki yayta tafiya cikin tsananin farinciki da jin dad'i har aka gama na Masarauatr Fuld'e tas.
Tukun suka had'o suka dawo cikin masarautar wasai gaba d'aya har da jama'ar masarautar fuld'e, saboda anan za'a cigaba da gudanar da shagalin.

Ko da Gimbiya Tasmir suka had'u da Gimbiya Haddiyal, cikin farinciki suka tarbi juna ba tare da wata ta nunawa d'aya a cikin su wani sab'ani ya tab'a shiga tsakaninsu ba, asalima sai had'uwa da suka farayi tare ana koya musu karatun al'qurani, tare da hadisai da kuma tauhidi aduk asubar duniya da kuma bayan sallahr magariba.

Yau ta kama ranar Alhamis, wato dai jajibirin d'aurin auren da za'ayin.
Kuma a yauce ranar da zasu futa lunching misalin k'arfe hud'u na yamma, wanda ya had'a gaba d'aya angwayen ukku tare da amarensu.

Misalin k'arfe ukku da rabi na yamma aka gama shirya amaren cikin wasu irin dogayen riguna masu sharar k'asa, maroon colour da sukayi musu wani irin azababben kyau.
Yayinda su kuma Angwayen ukku sukayi shigar suite marron colour mai tsananin tsada da kyawu iri d'aya.

Ya subahanalla, iyakar kyawu sunyisa, kana kuma ko wanne yayi matuk'ar yin maching da Amaryarsa.

Hannuwansu sark'e a cikin na juna gaba ki d'ayansu suka tawo a jere, suna masu shiga cikin fararen sababbin motocin da aka jere.
Ko da Gimbiya Haddiyal suka had'u da Bir bayan gaisuwa babu abunda ya sake had'asu.
Sai dai kuma ko wurin da yake bata d'aga kai ta kallaba, saboda haka kawai taji idan tayi hakan tamkar Asad zaiji ba dad'ine, domin kuwa a hakanma ba k'aramun mamaki ya bata ba, saboda ita dai da itace a matsayinsa na yadda yasan irin bala'ya'y'yen son da tayi masa da bama zata bari su had'u da juna ba.
Amma sai dai kuma shi taga kwata-kwata ko a fuska ma bai nuna ba, sai wani irin tattalinta da yake duk da har yanzu ba wata doguwar magana ke had'asu ba, bayan basa amsa idan ya tambayeta.

Su kuwa 'yammatan Masarautar tare da dangin amaren harma da iyaye ankon wani material sukai mai azabar kyau da tsada.
Gaba d'aya 'yammata sukayi d'inkin doguwar riga, yayinda iyaye kuma sukayi riga da zani, cikinsu kuwa harda Iyayen Gimbiya Tamsir da suka koma tamkar 'yan nan d'in suma.
Su kuwa maza ankon shadda sukayi mai ruwan material d'in da matan sukayi, wato dai milk color.

Fad'in irin shagalin da akayi a wurin lunching d'in nan ma b'ata bakine, amma kowa ya hasasho a cikin zuciyarsa.
Hotuna dai da videos an shasu a wurin.
Yayinda social media kuma ta cika da zancen manya-manyan bukukunan 'ya'yan sarakan da akeyi da kuma 'yar attajirin mai kud'i, wato budurwar Al'amin.

Haka dai taro ya watse misalin k'arfe bakwai na dare aka fara shiga motoci ana komawa, yayinda a gobe kuma za'a d'aura aure, da dare kuma za'ayi mother's night d'in da Mamy ta shirya, tukun kuma a gobe akai Amare gidajen mazajensu da suke anan cikin masarautar ajere wuri d'aya, kana kuma iri d'aya sak babu ta inda aka bambantasu.
Wanda hakan kuma duk ya kasance aikin mai Martaba.


*WASHEGARI, JUMA'ATU BABBAR RANA.*

Yauce ta kasance ranar d'aurin aure, wanda za'ayi sa kuma da zarar an idar da sallahr juma'a anan cikin masallacin Sarki.
Hakanne kuma ya sanya gaba ki d'aya masarautar ta d'inke da al'umma ta ko ina, domin kuwa tun jiya bak'i suketa zuwa, saboda ba k'aramar gagarumar gyayya Mai Martaba yayi ba, haka kuma su Babban yaya ma.
Dalilin da yasa wasu irin azababbun motoci suketa danno hancinsu cikin Masarautar.
Duk wanda zaiso wurin ba sai an fad'a masa ba zai tabbatar da yau d'in ana bikin 'yan gatane na gaban goshi, domin kuwa iya shanu ma ba'asan adadin da aka kayarba tun a wancan satin har zuwa jiya.
Abinci kuwa an yisa fiye da k'ima.
Gaba d'aya Ummi itama nan ta dawo aka ware musu part d'aya ita da danginsu gaba ki d'aya.
Su kuwa dama dangin Gimbiya Tasmir suna cikin part d'insu, to hakama jama'ar masarautar fuld'e suma aka basu nasu part d'in.

Wuri d'aya Gimbiya Tasmir da Gimbiya Haddiyal duk suke zaune.
Sunci wani irin ado mai masifar d'aukar hankali, cikin wata azababbiyar shadda green color da tayi azabar yi musu kyau.
Yayinda tun jiya kuma jama'a suke son bambance wacce tafi kyawu a cikinsu, amma har kawo yau sun gaza, sai dai kawai ace wannan tana da nan ita kuma na wannan ga yadda yake.
Kai idan kaga yadda suke hira tare bazaka tab'a tinanin sun tab'a samun sab'ani a tsakanin suba.
Yanzu haka rik'e suke da sababbin wayoyinsu k'irar iphine 13pro max da aka sanya musu acikin kayan lefensu, ko wacce tana danna tata.
.
Acan kuwa b'angaren Angwaye shiryawa suke cikin wata 'yar ubansun getzner shadda fara kar, d'inkin riga da wando tare da Babbar riga data sha wani uban dakakken aiki da ash d'in zare.
Kawunan su kuwa sanye suke da ash color d'in hulunan da sukaji had'ad'd'iyar sak'a, gaba ki d'ayansu iri d'aya.
Yayinda k'afafuwansu kuma suke sanye da ash d'in cover shoe da yakai mak'ura wurin had'uwa.
A lokaci d'aya su duka ukkun suke d'aure had'ad'd'e ash d'in agogon fatar a hannunsu, suna masu futowa daga cikin d'aki.
Yayinda Habu dasu Huzaifa da kuma Yarima Sairan suke biye dasu abaya, suma d'in sanye da fararen kaya a jikinsu.
Iyakar kyawu dai Angwayen sunyi mak'urar yinsa.
Hakanne kuma ya sanya suna b'ullowa cikin falon Gimbiya Fulani d'aukacin matan da suke aciki suka rangad'a wata uwar bud'a mai tsananin k'arfi.
Tukun suka fara tsokanarsu da Angwaye, a haka dai har suka fuce daga cikin gaba d'aya bakinsu ya kasa rufuwa.

Yanayin cikowar da take a cikin gidanne kuma ya sanyasu suka hau motoci zuwa masallaci, duk da ba wata tazarace da shi ba.

A lokacin da suka shiga Masallacin sun taddasa d'inke da Al'umma, tun daga kan Sarakai na garuruwa da dama, tare kuma da manya-manyan attajiran k'asa, domin kuwa hatta da mai girma Gwamnan wasai ya amsa gyayyata, duk da sab'anin daya shiga tsakaninsu, saboda ganin da yayi tasa 'yar ma ta ruga nasu yin aure.

Zamansu Yarima Asad baifi da minti d'aya ba Sheikh Ahmad ya shigo cikin masallacin, yana mai yin kan mambarin hud'uba kai tsaye.
Sanye yake da farar shaddar da take matuk'ar k'yalli da d'aukar ido.
Sai bak'ar hular daya d'ora akansa da tayi bala'in k'ara futo da hasken fatarsa.
Yayinda ya d'ora wani d'an farin glass akan k'wayoyin idanuwansa, kyakkyawan sajensa kuwa banda aikin k'yalli da d'aukar ido babu abunda yake yi.
Iyakar kyawu dai yayisa a yau d'in tamkar shine Angon.

Tsit kakejin masallacin ya sakeyi, saboda yadda ya busa lasifikar daya mak'aleta ajikin rigarsa.
Tukun daga bisani ya d'ago idanuwansa, yana mai d'orasu akan d'aruruwan jama'ar da sukayi dacen samun mazauni acikin masallacin, wanda kusan rabi da kwatarsu kuma da suke a gaba manyan attajirai ne tare da masu muk'amai.
Kana ya bud'e baki cikin daddad'ar muryarsa da take matuk'ar ratsa zuciyar bayin Allah idan yana tafsir ko lecture, yana mai farawa da fad'in.

"Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafarrasa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawunanmu, da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai b'atar dashi, wanda kuma ya b'ata to babu mai shiryar dashi. Kuma ina shaidawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah. Shi kad'aine bashi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa ne. Allah ya turoshi dan ya kasance rahama ga hallitu da addini mik'ak'k'e, da kuma wata shari'a wacce ta bada kulawa ga mukallafai, wato masu hankali daga Mutane da Aljanu. Sai Manzo ya tafiyar da rayuwarsa cikin kira da ita, kuma zuwa gareta yana d'aukar hujjojinta, na yankan shakku yana bada kariya da su. Salatin Allah da sallamarsa suk'ara tabbata ga Iyalan gidansa da Sahabbansa.
Bayan haka Assalamu alaikum warahamatullahi wabarakatu."

Amsawa gaba d'aya d'aukacin jama'ar cikin massalacin harma dana waje sukayi, suna masu komawa suka sake nutsuwa.
Yayinda shi kuma Sheikh Ahmad ya gyara zaman glass d'in dake kan idanuwansa, tukun ya d'ora da fad'in.

"Manufofin hud'uba.
Bayyana cewa shari'ar musulunci cikakkace acikin tsarinta.
Bayyana cewa shari'ar musulunci ta wajabta samun Shugaba acikin Al'umma.
Sanar da Shugaba hak'k'ok'in talakawa da suke kansu. A kuma sanar da talakawa hak'k'ok'in shuwagabanni akansu.
Hak'ika addinin musulunci addinine ingantacce, dan haka ya tanadi duk wani abu da mutane ke buk'ata, a rayuwarsu, daga ciki akwai Shugabanci, dan hakane ma ya shimfid'a yadda mu'amala ya kamata ta kasance tsakanin Shuwagabanni da talakawansu, da hak'k'ok'in da suka rataya akan kowacce daga cikinsu.
Yaku wa'yanda kukai imani, kuji tsoron Allah yadda ya cancanci aji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi.
Yaku Mutane, kuji tsoron Ubangiji wanda ya halliceku daga rai guda d'aya, kuma ya hallicci Matarsa daga gareshi, kuma ya yad'a Maza da Mata daga garesu su biyu. Kuji tsoron Allah wanda kuke magiya dashi, kuma ku kiyaye Zuminci. Lallai Allah mai kulane daku.
Yaku wa'yanda kukai imani, kuji tsoron Allah kuma ku fad'i magana ta dai-dai, sai Allah ya gyara muku ayyukanku kuma ya gafarta muku zunubanku. Wanda yabi Allah da manzonsa hak'ik'a ya rabauta rabauta mai girma. Bayan haka lallai mafi gaskiyar magana maganar Allah. Kuma mafi kyawun shiriya shiriyar annabi Muhammad (S.A.W). Kuma mafi sharrin al'amura a addini k'agaggunsu. Kuma duk wani k'agaggen abu a addini bid'a ce, duk wata bidi'a b'atace, duk wani b'ata kuma yana wuta.
'Yan Uwa Musulamai Allah mad'aukakin Sarki yana cewa acikin littafinsa mai tsarki.
*AL'YAUMA ALKMALTU LAKUM DIYNAKUM WA'ATMAMTU ALAIKUM NI'IMATIY WARADITU LAKUMUL ISLAMA DIYNAA. (Al'ma'ida 3)*
Ma'ana a yau na cika muku addininku, kuma na cika muku ni'imata gareku.
Hak'ik'a addinin musulunci cikakkene ta kowane b'angare, dan haka musulmi basa buk'atar wani addini wanda bashi ba, basu buk'atar wata shari'a wadda ba itaba, saboda cikar shari'ar musulunci ta k'unshi dukkan abunda yake maslaha ne a al'umma, tabawa dukkan mutane hak'k'ok'insu, talakawa, da masu arzik'i, masu mulki da wa'yanda ake mulka, Namiji da Mace, kai harma da dabbobi. Allah mad'aukakin sarki yaba duk wani mai hak'k'insa, to daga cikin abunda musulunci ya bashi kulawa, al'amarin Shugabanci da kuma jagoranci. Musulunci bai bar mutane su zauna kara zubeba, a'a yayi umarmi da nad'a Shugaba ko da ahalin tafiyane, saboda amfanin samun Shugaba acikin al'umma amfanine bayyananne baya buk'atar wani dogon bayani, don rayuwar mutane bazata tsayuba ta gyaru sai idan akwai Shugabanci a tsakaninsu, dan haka Allah mad'aukakin Sarki da Manzonsa suka nuna muhimmancin bin shugaba da samun Shugabanci a cikin mutane.
Allah mad'aukakin Sarki yace.
*YA'AYYAHALLAZINA AMANU A'DIULLAHA WA'A'DI'U RASULAH WA'ULIL AMRU MINKUM. (Nisa'i 59).*
Yaku wa'yanda kukai imani kubi Allah kubi manzonsa, sannan kuma kubi ma'abota al'amari daga cikinku. Kuma Manzon Allah (S.A.W) yace duk wanda yayimin d'a'a to yayiwa Allah, haka duk wanda yabi Shugaba to ya bini, wanda kuma ya sab'awa Shugaba to ya sab'amin.
Shugaba garkuwace da ake yaƙi abayan ta, ake kariya da ita, dan haka idan shugaba yayi umarni da tsoron Allah yayi adailci to yana da lada, in kuwa ya ai'kata saɓanin haka to wannan laifi yana kansa. Bukharine ya rawaito.
Ankarb'o daga Ummasala matar Annabi (SAW) daga Annabi (SAW) yace. Hak'ik'a za'anad'a muku Shuwagabbani abayan wa'yanda zakuga abu mai kyau a tare dasu kuma kuga marasa kyau. Wanda yak'i mara kyau d'in ya kub'uta, hakama wanda yayi ink'ari, sai dai wanda ya yarda yabi, to wannan mai laifine, sai sahabbai sukace bazamu yak'esu ba ya manzon Allah? Sai yace a'a matuk'ar dai sunyi sallah. (Muslim ne ya rawaito).
'Yan uwa wa'y'yanna kenan daga cikin dalilan da suke nuna muhammancin samar da shugabanci acikin musulunci, saboda hakama musulunci ya tsara hak'ok'in shugaba akan talakawansa, ya kuma tsara hak'ok'ik'in talakawa akan shugabasu. Yana daga cikin hak'k'in talakawa akan shugaba ya samar musu da kotunan da zasu rink'a yanke hukunci tsakanin mutane da sasantasu, yasamar da kwamitocin da zasu dinga sasanta mutane suna umarni da kyakkyawan aiki suna hana mummuna. Kamar yadda yake wajibine akan Shugaba ya tsaida hak'k'i akan duk wanda ya k'etare iyaka ya zalunci Bayin Allah, ya tab'a rayukansu ko jininsu ko dukiyoyinsu. Manzon Allah (SAW) yana cewa, haddi d'aya da za'ayi aiki dashi abayan k'asa ya fiyewa mutane ruwa na kwana arba'in. Ibn majah ne ya rawaito."

'Dan tsakaitawa yayi yana mai jan numfashi a karo na barkatai, yayinda gaba d'aya al'ummar da suke sauraransa kuma sukayi shiru, mussaman ma shuwagabbin da suke a wurin da jikinsu yayi matuk'ar sanyi, dan kuwa shi Yarima Sairan ma hawaye kawai yake tayi, saboda tino yadda suka dinga gudanar da nasu shugabancin da yayi.

Shi kuwa Sheikh Ahmad zamansa ya gyara, kana ya d'an sa yatsunsa bayan ya janye glass d'insa yana mai goge k'wallar data tawo masa, kasancewarsa mutum mai raunin zuciya, shiyasa kusan koda yaushe idan yana hud'uba ko wani wa'azin sai yayi kuka, musamman ma kuma idan yazo wurin azaba.
Kana ya gyara zaman glass d'in nasa, yana mai d'orawa da fad'in.

"Hakanan kuma wajibi ne Shugaba ya zama mai adalci tsakaninsa da talakawansa, saboda adalci shine tushen rayuwa, kuma sai da adalci ne al'amura ke dai-daita duniya da lahira.
Sannan kuma Sheikhul Islam Ibni taimiyya yana cewa. Al'amuran mutane na duniya suna dai-daita ne da adalci da yake haɗe da nau'ika na zalunci, fiye da yadda al'amura zasu miƙe da zalunci acikin haƙƙoƙi, ko da kuwa basuyi tarayya azunubi ba, dan haka akace Allah yana tsayar da daular mai adalci ko da kuwa musulma ce, hakanan akace duniya tana dawwama da adalci da kafirci, amma bata dawwama da zalunci da musulunci.
Manzon Allah Sallalahu Alaihi Wassallam yana cewa. Babu wani zunubi daya fi sanya azaba da wuri fiye da zalunci da yanke zumunci. Azzalumi ana bugeshi aduniya koda kuwa an masa gafara da rahama alahira, saboda adalci tsarine acikin komai da komai, idan aka tsayar da al'amarin duniya akan adalci sai komai ya tsaya, koda kuwa ma'abocin duniyar nan bashi da rabo alahira, idan kuwa ba atsayar da al'amuran duniya akan adalci ba, to lamarin bazai tsaya ba, ko da kuwa ma'abocinsa yana da imani da zai ishesa alahira. (Duba maj'mu'ul fatawa 28/146).
Hakanan Shugaba ya zama ƙarfi wajen zartar da abun da yake gaskiya ne acikin talakawansa, ya nisanci zalunci, da ƙarya, da cin amana, da ha'inci da sauran munanan halaye. Wannan sune kaɗan daga cikin haƙƙoƙin talakawa akan Shuwagabanninsu, dan haka wajibi ne akan Shuwagabanni su kiyaye waƴan nan haƙƙoƙin, saboda al'amuran talakawansu amana ce a wuyan su, kuma Allah zai tambaye su abun da ya basu kiwo daga bayinsa.
Kuji tsoron Allah yaku Shuwagabanni, ku kamanta ku nemi taimakon Allah ta hanyar sallah da hak'uri, Allah yana tare da mai hak'uri. Kyakkywan k'arshe yana ga masu tsoron Allah da hak'uri.
Allah mad'aukakin Sarki yayi mana albarka cikin abinda mukaji na al'qurani da hadisai.
*HU'DUBA TA BIYU."
Hak'kin Shuwagabanni a wurin talakawa.
"Yaku 'yan uwa musulumi, babu ko shakka Shuwagabanni suna da hak'k'i mai girma akanmu, wanda da samuwarsu ne al'amura zasu mik'e su dai-daita, komai ya tafi yadda akeso, daga cikin wa'yannan hak'k'ok'in akwai ji da biyayya akan abunda ba sab'on Allah da manzonsa bane.
Ji da biyayya ga Shuwagabanni ya 'Yan uwa wajibi ne ko da kuwa Shuwagabannin suna zalunci da son kai, yin tawaye da fito na fito dasu bai hallata ba, saboda Manzon Allah (SAW) ya hana.
Manzon Allah (SAW) yana cewa, zaku samu son kai da wasu abubuwan da kuke k'i, to ku sauke nauyinkan da suke kanku sai ku rok'i Allah hak'k'in ku,
Sannan kuma wajibine ji da biyayya ga Shugaba, ko da kuwa wanda yake kai azzalumi ne mai shirme. Sai abashi hak'k'insa na biyayya, ba za'ayi masa tawaye a cire shiba, za'a koma a k'ask'antar da kai ga Allah akan ya yaye cutarsa da sharrinsa ya gyarasa. Duba (littafin sharhin sahihi muslim)
Haka kuma hak'k'ine da yake kan wuyan Malamai da masu da'awa, sannan ya dace adingawa Shuwagabanni nasiha, alura da sukela dace da maganganun da suka dace, a tunatar dasu kyawawan aiki a hanasu mummunan aiki cikin ilimi, tare da sauk'ak'awa da ragwantawa. A kiyaye da matsayinsu da darajarsu, hakan zai sa su karb'a a kuma samu abunda ake nema.
Ibnul Jauziy. Allah yayi masa rahama yana cewa. Abinda yake halak wajen umarni da kyakkyawan aiki da kuma hani da mummuna gama su mulki shine, wa'azi da tausasawa, amma kausasa magana kamar cewa yakai azzalumi wanda baya tsoron Allah. Idan irin wannan zai kawo fitina da sharrinta zuwa ga wani to baya hallata, in kuwa abin bazai shafi wani ba to shi k wa'azin to ya hallata a wurin jumhurun malamai.
Dan haka yaku 'yan uwa, abunda wasu matasa sukeyi na fito na fito da shuwagabanni da yak'arsu abune da yaci karo da dalilai na shari'a.
Wa'yanda kuma sukayi umarni da rashin yin haka, da hak'uri da kawar da kai da abun da irin wad'annan Shuwagabbanin sukeyi, matuk'ar dai suna sallah.
Yana daga cikin hakkin Shugaba akan Takakawansa suyi masa addu'a"

Sosai akayi hud'ubar data ratsa jiki da jinin Talakawa da masu muliki a yau d'in, tukun a k'arshe saboda k'aratowar lokaci badan abun fad'e sun k'are ba ya rufe da fad'in.

"To sai kuyi salati ga Ahmad mai shiryawa mai ceton mutane gaba d'aya. Saboda idan mutum yayi masa salati d'aya, to Allah ta'alah zaiyi masa guda goma.
Ya Allah kayi salati da sallama ga bawanka kuma Manzonka Muhammad.
Kuma ya Allah ka yadda da dukkan Iyalan Annabi da Sahabbai ka had'a harda mu ya mai karamci ya mai yawan baiwa.
Ya Allah ka d'aukaka musulunci da musulmai, kuma ka k'ask'antar da shirka da mushirikai, kuma ka halaka mak'iya wannan addinin, ka sanya wannan k'asa ta zama cikin aminci da zaman lafiya da sauran k'ashashen musulmai.
Ya Allah ka datar da Shugabanmu kuma jagoranmu ga zuwa ga abinda kake so, kuma ka yarda.
Ka kama k'eyarsa izuwa aikin biyayyarka da aikin tak'awa.
Ya Allah ka tseratar da wa'yanda ake raunanasu daga cikin musulmai, a kowane guri ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka kawo aminci a iyakokinmu ka kare rindinoninmu.
Ka taimakesu akan mak'iyanmu kuma mak'iyansu.
Ya Allah ka karb'i matattu cikin shahidai, ka warkar da wad'an da akayi musu rauni daga cikinsu ya mai amsa addu'a.
Ya Allah kasa addu'oinmu su zama karb'ab'b'u.
Sautinmu kuma abun zagawa ya mai karamci, ya mai girma da jin k'ai.

Ya k'arasa addu'ar yana mai sakin shashshekar kuka, tamkar yadda jama'a da dama daga cikin wa'yanda suka saurari hud'ubar suka sha kuka cikinsu kuwa harda iyayensu Gimbiya Tasmir da suke a cikin gida.
Yayyinta kuwa na cikin masallaci ba k'aramun kuka sukai ba, haka suma masu mulki duk jikinsu yayi sanyi, tsoron Allah ya k'ara d'arsuwa a zuciyarsu.

Tukun Sheikh Ahmad ya mik'e yana mai fad'in.

"Wak'umu ila salatikum wayarhamkumullah."

Gaba d'aya jama'a suka mimmik'e, yayinda ladan kuma ya fara tayar da sallah.
Kana bayan ya gama Sheikh Ahmad ya kabbara.

Kasancewar kuma sallahr juma'a raka'a biyuce, sannan kuma ba afiya tsawaitasu ba, shiyasa cikin d'an k'ank'anin lokaci aka idar.
Tukun baya d'an wani lokaci Sheikh Ahmad yayi sanarwar d'aurin auren da za'ayi, yana mai fad'in.

"Idan walliyan suna kusa sai su matso."
Tamkar anyiwa Bir, Asad, tare da Al'amin bushara da gidan aljanna haka sukaji, ta yadda kwata-kwata bakinsu ya gaza rufuwa tun kafin a d'aura d'in.
Yayinda su kuma su Mai Martaba, Abba, da duk sauran wa'yanda zasuyi waliccin suka taso suka dawo gaban, gaba ki d'ayasu kuma suna sanye da manyan fararen kayane.
Kasancewar kuma Abba shine walliyin Gimbiya Tasmir, Mai Martaba kuma na Bir, shiyasa bayan sun zauna sun nutsu Mai Martaba ya zura hannu a cikin aljihunsa yana mai zaro rapa 'yan dubu d'aya har guda biyar.
Kana ya mik'awa Ishak' ita yana mai fad'in.

"Ni Abdallah Ahmad Abdallah, ina nemarwa Yarona Abdulmajid Ishak' auren 'yar wurinka Gimbiya Halimatussadiya, akan sadaki nera dubu d'ari biyar lakadan ba ajalanba."

Cikin tsananin farinciki mara misaltuwa Abba ya mik'a hannunsa yana mai karb'ar kud'in, tare da fad'in.

"An baku Allah yasanya alkhairi."
Ya k'arasa maganar yana mai karb'ar kud'in a hannunsa akan idanun jama'a.
Kana Mahaifin budurwar Al'amin ya matso shima dai kamar yadda akayi na Bir haka akai nasa, mai martaba ne waliyyinsa kuma akan sadaki dubu d'ari biyar.
Sanan Lamid'o Sulaiman ya matso.
Cikin tsananjn farinciki mara misaltuwa kuwa Mai Martba ya zaro dubu d'ari biyar yana mai mik'a masa tare da fad'in.

"Ina nemarwa Yarona Ahmad Abdallah Ahmad auren 'yarka Haddiyal Sulaiman akan sadaki dubu d'ari biyar lakadan ba ajalanba!"

Cikin matsanancin farinciki mara misaltuwa shima Lamid'o sulaiman ya karb'a, yana mai fad'in.
"Am basa."
Wanda hakan kuma yasa Sheikh Ahmad da duk mutanen da suke a wurin shiga cikin matsanancin farinciki.
Tukun ya busa iska ajikin sifika, kana ya fara kwararo addu'oi tare da neman albarkar Allah.
Yayinda Yarima Asad, Bir da kuma Al'amin suna jin an d'aura auren a take a wurin da suke suka kai goshikansu k'asa, suna masu yin sujudu shukur d'in da Sheikh Ahmad ya koyar dasu.
Tukun daga baya suka d'ago sai ga hawaye nan shar! Sharr!! Shar!!! Suna dira akan kuncin Asad da Bir, tare da dariya a kuma lokaci d'aya.
Yayinda marok'a kuma suka fara shelanta d'auruwar auren.
Babban Yaya kuwa cikin tsananin farin ciki mara misaltuwa yake raba dabino da alawoyi tare da goro.

Acan b'angaren Amare kuwa suna zaune a cikin d'aki suka jiyo ihun marok'an suna masu shelanta d'aurin auren nasu.
Zumbur kuwa Gimbiya Tasmir ta mik'e tsaye tana mai zaro idanuwa, kafin daga bisani kuma ta fashe da kuka tare da murmushi alokaci guda, saboda jin da tayi yau Jaruminta ya zama nata.
Ita kuwa Gimbiya Haddiyal suman zaune tayi a wurin da take tana mai raba idanu.
Wani irin yanayi take jin kanta a cikinsa, wanda tarasa gane ko wane kalane, sai dai kawai abunda ta sani shine, bana bak'inciki bane ba, haka kuma bana farinciki bane.
Kana daga bisani itama d'in sai ga hawaye nan suna kwaranyo mata.
Hakan kuwa shine ya sanya su Baby suka fara yi musu dariya tare da tsokanarsu.

A b'angaren Iyayen Angwaye da Amare kuwa fad'in irin farincikin da suka shiga a yanzuma b'ata bakine, domin kuwa ita Fulani har kukan farinciki sai da tayi, saboda yadda take jin abun tamkar al'mara, ko tace *MU'UJIZA*, wai Zakinta yau shine Allah ya shirya mata shi har aka d'aura aurensa.

Acan b'angaren Angwaye kuwa cikin matsanancin farinciki suka k'arasa wurin iyayen nasu suna masu gaishe da su.
Haka sukai ta shafa kansu suna samusu albarka tare da fatan zaman lafiya.
Tukun suka tashi suna masu futowa daga cikin masallaci.

Tamkar dama jiransu ake suna futowa tun daga kan abokai har zuwa marok'a sukayo musu caaa.
Yayinda bakunansu kuma suka gaza rufuwa gaba d'ayansu.
A haka suka fara tafiya tare da zugar Abokansu zuwa b'angaren da Iyaye mata suke.
Amma duk da haka marok'a basu fasa biyosu ba suna sakin kid'a tare da kirari, amai-makon kuma Yarima Asad yaji haushinsu tamkar yadda ya saba, sai yau yake jin kid'an nasu nayi masa tsananin dad'i, hakanne ya sanya ya dinga zura hannu a cikin aljihu yana d'ebo kud'in da baisan adadinsu ba yana damk'a musu.

Bayan an gama d'aurin aure anyi komaine kuma aka nad'a Sheikh Ahmad Garkuwar Malaman Wasai, inda mai martaba ya d'ora masa rawani akansa da kansa.

Haka dai yau gidan aka yini ana shagali, duk inda ka gifta banda bushabushe da kad'e-kad'e babu abunda akeji yana tashi.
Yayinda hotuna kuma akayisu bila adadin.
Kuma Gimbiya Haddiyal sosai ta bawa Yarima Asad had'in kai a wurin yin pics d'in, domin kuwa harda wanda suka yisa suna kallon cikin idanuwan juna tare da murmushi, saboda hakanan kawai take jin zuciyarta tayi matuk'ar sanyi yau d'in, yayinda asalin madarar kyawunsa kuma da duk bata ganinsa yau ta gansa.
Haka aka sha shagali iya shagali har magariba tayi.
Tukun aka fara shirin tafiya wurin mother's night, duk da dai shi a

Please Login or Register in order to submit comment