Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baka san halina bane shiyasa, jibi d'an mitsitsin baki kamar na Shalle, dogon hanci uwa karas, ga saurin kuka kamar Innahuro, ai wallahi kai dai 'ya'yanka sun bani wurin kuka saboda gado da zasuyi."

Ta k'arasa maganar tana mai sake harararsa, tukun daga bisani kuma ta sauka daga kan gadon taba mai fad'in.

"Ya sani kawai na kwana a d'akin Namiji duk ya ishi mutane da kuka."

Ta k'arasa maganar a fili, tana mai juyawa ta fuce daga cikin d'akin.
Hakan kuwa shine ya sanya Yarima Asad ya bud'e idanuwansa yana mai kwashewa da wata irin shegiyar dariya.
Tukun daga bisani ya cije leb'ensa yana mai fad'in.

"Tsabar sharrima wai zafin dundunta ne ya sa na d'agata, da wani d'an hannunta da ko katifa ta fisa tauri, zakiyi bayanine yarinya zakisan nine raggo mai nauyin buhun simunti hamsin."

Ya k'arasa maganar yana mai yin juyi tare da rungumar fulo ya k'ara lumshe idanuwansa.

Misalin k'arfe takwas na safe Baby ta kawo musu abinci da suka had'asa ita da Mamy da hannunsu gaba ki d'aya gidajen ukku.
Sannan ta tambayi Gimbiya Haddiyal da har tariga tayi wanka ta shirya ya mai jiki.

"Jiki da sauk'i ya warke."

Ta fad'a badan tana da tabbacin hakan ba, saboda tunda ta baro cikin d'akin bata koma ba shima kuma bai futo ba.
Tukun Baby ta mik'e ta futa.

A b'angaren su Bir kuwa daren jiya ya zame musu dare na mussamman a cikin dararen rayuwarsu wa'yanda suka shud'e da kuma masu zuwa anan gaba. Ya zama daren da yayi rantsats-tsen gini a cikin zuciyar ko wanne daga cikinsu.

Wani irin tattali Bir yake nunawa Gimbiya Tasmir, irin wanda ko k'wai bai fiye samun kamarsa ba, domin kuwa motsi tayi saiya tambayeta me nene, wanda hakan kuma shine ya sanya take ta faman zuba masa shagab'a, irin wadda ita kanta bata san ta iyata ba sai a yau d'in.
Yayinda soyayyar junansu kuma ta sake samun muhalli na mussamman a cikin zukatansu.

A b'angarensu Al'amin suma tamkar yadda su Bir suke a cikin farinciki da annashuwa haka suke shi da Amaryarsa.

****
Sosai Gimbiya Huwaila take hauka tuburan tana neman hanyar guduwa, wanda hakan da 'Ya'yata suka ganine kuma ya sanya suka kulleta a cikin wani d'aki, ya zamto sai dai a zira mata abinci ciki.

Gaba d'ayanta cikin kwana d'ayan da tayi tayi wani irin firgicewa, gashin kanta duk ya warwatse, ta yaga kayanta yadda kasan wacce ta d'au shekara da shekaru tana hauka, kana kuma har yau bata fasa lissafo irin mugayen abubuwan da tayi ba.

A b'angaren Jakadiya kuwa azaba bata wasa ba ake gana mata, tayi nadamar abunda ta aikata daga daren jiya zuwa yau tafi a k'irga, domin kuwa garin neman duniya gashinan ta hulla kanta cikin masifa, saboda ko da an saketa tasan babu mai sake barinta ta zauna acikin gidan.

Shi Kuwa Mai Martaba haka yace har abada ya gama yin wata Jakadiya, daga yanzu babu wata da zata na shiga tsakanin sa da Iyalansa.

Haka dai rayuwa ta fara lulawa, Bir da Gimbiya Tasmir suna zuba wata irin tsaftattaciyar mayyar soyayya a cikin gidansu.
Yayinda a b'angaren su Yarima Asad kuma har yau babu wani abu daya tab'a shiga tsakaninsa da Haddiyal, domin kuwa ko d'aki ma kowa anasa yake kwana tun daga waccan ranar.
Amma fa iya kulawa tare da jin kalamin soyayya tana jinsu a bakin Yarima Asad bila adadin a kowace rana, wanda hakan kuma shine ya sanya itama har ta fara yi masa mazauni a cikin zuciyarta, ta yadda har idan ya futa zuwa wurin Mamy take jin ta k'agara ya shigo, kuma a yanzu tana zama suyi hira da shi kawai dai tace masa tana sonsa ne har yau batayi ba, yayinda shi kuma Yarima Asad ya k'udurtawa ransa cewar bazai tab'a takura mata ba.
Wanda hakan kuma data fahimtane yasa a kullum take jin tausayinsa na lullub'eta.
Iyayenta na komawa gida kuma aka turo mata hadimarta ta dawo nan aka bata d'aki ta cigaba da kula da ita dayi mata hidindumu.
Ab'angaren Gimbiya Tasmir itama Fulanice ta had'ata da d'aya daga cikin hadimanta kafun nata Iyayen su koma gida a turo mata Hadima Fulaika da tace ita take son tazo su zauna tare.


BAYAN SATI BIYU.

Yau itace ranar da Ahalin Gimbiya Tasmir zasu koma garinsu cikin Masarautarsu.

A yanzu Yarima Sairan ne zai koma Sarki duk da dai da ya nunawa su Sheikh Ahmad cewar ba zaiyi ba ya tsorata da mulki sosai yanzu.
Amma nagartaccen wa'azin daya samu daga bakin Sheikh Ahmad akan Shugabanci daya zamto dole, yasa sa hak'ura, sai dai kuma ya k'udirtawa ransa zama adalin shugaba mai tsoron Allah tare da tausayin talakawansa, da kuma aiki da fad'an Annabi Muhammad (SAW).

Har airport suka rakasu gaba d'aya harda su Ummi, Gimbiya Fulani, Kaka, Iyar Bayi data dawo nan gaba d'aya ita, da kuma su Sheikh Ahmad, Babban Yaya, Abba da Mai Martaba.
Sai kuma Amare da Angwayensu gaba ki d'aya harda Al'amin ma.

Sosai Gimbiya Tasmir tayi kuka da zasu rabu.
Tukun bayan sunga tashin jirginsu da suke sa ran zai isa cikin awa hud'u kacal, suka juyo zuwa gida kowa a cikin motocinsu.

A yanzu haka Babyce ke zuwa tana yiwa Gimbiya Tasmir da Gimbiya Haddiyal k'arin karatu, kuma Alhamdulillah sosai kansu yake bala'in ja su duka biyun, domin kuwa zuwa yanzu babu bak'in da basu saniba na k'urani, kuma suna iya karantasa.
Yayinda Yarima Asad, Bir da kuma Al'amin suke zuwa wurin Sheikh Ahmad tun bayan sati d'aya da bikinsu duk bayan magaribar duniya.
Wanda hakan kuma shine ya sanya Yarima Asad ya dena yiwa kaya sawa d'aya da duk wasu abubuwan amfani ma, saboda yadda Sheikh Ahmad ya fad'a masa hakan almubazzarancine da kuma izgilanci, kana ya karanto masa hukuncin almubazzari, hakan kuwa shi ya sanyasa cikin matsanancin tsoro da firgici, domin kuwa a ranar ko bacci sai dai k'yar ya samu yayisa, tundaga kuma wannan ranar ko brush ya dena yaddasa dan yayi amfani d'aya da shi.

A cikin mota kuwa sosai Bir yake aikin lallashin Gimbiyarsa cikin salonsa daya san zata lallasu tini.
Kuma hakance ta kasance, domin kuwa tini tayi luf a jikinsa tana mai sauke ajiyar zuciya. Hak'ik'a duk wanda zai gansu sai sunyi bala'in birgesa, saboda tsananin dacewar da sukayi da junansu, sosai kuma Gimbiya Tasmir take masa biyayya, gaba d'aya tama manta da ya tab'a zamtowa Bawanta.

A cikin motarsu Yarima Asad ma rik'e yake da tafin hannun Gimbiya Haddiyal cikin nasa, yana mai faman murzasa a hankali, kana kuma cikin wani irin salo na mussamman, sannan kuma yana furta mata dadad'an kalamansa da a kullum take jin wasu sababbin daga bakinsa.
Hakan kuwa shine ya sanyata jin wata irin matsananciyar kasala ta saukar mata, ga tsigar jikinta kuma da taketa bada yarrr! Wani irin abu na taso mata tun daga tsakarka har zuwa tafukan k'afafuwanta.
Hak'ik'a zuwa yanzu ta aminta da salonsa, kana kuma tana jin wani irin abu dangane da shi itama, yayinda zuciyarta kuma ta manta da wani Gid'ad'o tunda ta fahimci shi kwata-kwata bama ta ita yake ba.

A hankali Yarima Asad ya zagayo b'angaren da take yana mai bud'e murfin motar.
Tukun ya mik'a mata tafin hannunsa yana mai jifanta da wani irin mayen kallo da shanyayyun idanuwansa.
Nannauyan numfashi ta fesar tana mai lumshe idanuwanta, saboda yadda take jin idanuwansa da suke yawo a jikinta suna sake canza yanayinta.
Kana daga bisani kuma ta bud'esu, tana mai d'ago nata lallausan tafin hannun ta d'ora akan nasan.
Rumtsesa yayi a cikin nasan kuwa, yana mai d'an janyonta daga cikin motar ta futo waje.
Tukun kuma ya saki tafin hannun nata yana mai matsowa bayanta ya had'e jikinsa da nata bayan k'am.
Wanda hakan kuma ya sanyasu sakin wasu irin tagwayen ajiyar zuciya a jere, tare da rumtse idanuwansu alokaci guda, saboda wani irin abu da suke ji yana bin gaba d'aya ilahirin jikinsu.
Da k'arfi Yarima Asad ya janyo numafshi yana mai fesar da shi, lokaci d'aya kuma launin idanuwansa suka fara sauyawa.
Tukun daga bisani kuma ya bud'e baki cikin wata irin sassanyar murya ta mussaman, bayan ya d'ora hab'arsa akan huyanta yana mai jujjuya lallusan gemunsa mai matuk'ar yawa, yace.

"Ki rufe idanunki gam-gam, kar ki bud'esu har sai nace miki ki bud'e kinjihhhh!!!"

Da k'arfi kuwa ta rumtse idanuwan nata, saboda yadda take jin dirar zazzafan numfashinsa akan wuyanta, wanda hakan kuma ya sanya k'afafuwanta suka fara 'yar rawa kad'an.
Shi kuwa Yarima Asad murmushi ya saki, yana mai janye kansa daga wuyanta.
Tukun ya sake mannota jikinsa ta silar ziro hannuwansa da yayi duka biyun ta kan cikinta ya kullesu.
Kana kuma yace mata su tafi to a haka.
A hakan kuwa suka fara tafiya tana rufe da idanuwanta, yayinda jikinsu kuma yake sark'e a wuri d'aya, wanda hakanne ya sanya kuma suke jin tamkar zasu fad'i a k'asa.

Shi yake juyata suna tafiyar a haka har suka shiga cikin d'an madai-daicin had'ad'd'en garden d'in gidan.
Bai tsaya ba har sai da suka isa gaban wani d'an k'aramin gini da yake d'auke da k'ofa.
Kasancewar kuma k'ofar a bud'e take shiyasa kawai yasa k'afarsa yana mai haurinta ta bud'e, tukun suka cigaba da tafiya zuwa ciki.

Kukan tsuntsayen da taji suna dukan kunnentane ya sanyata ta fara sakin wani lafiyayyen murmushi daga tsayen da take.
Shi kuwa Yarima Asad kallonta kawai ya tsaya yi, yana mai jin wani irin mugun nishad'i na lullub'esa.
Kana daga bisani kuma ya bud'e baki cikin sassanyar muryarsa, yana mai fad'in.

"Bud'e to."

Bud'e idanuwan nata keda wuya kuwa suka sauka akan wasu irin had'ad'ud'un tsuntsaye da suke cike a cikin wani tafekken keji da kusan ya cinye wurin gaba d'aya.

"Wayyo Allah naaah!!!"

Ta fad'a cikin wata irin murya mai tafe da dariya, tana mai zaro idanuwanta tare da bin had'ad'd'un tsuntsayen da idanuwan nata.
Tukun daga bisani kuma ta fara zagaye tana mai neman k'ofar shiga.
Hakan da Yarima Asad ya ganine ya sanyasa matsawa wurin da k'ofar take, yana mai bud'e mata ita.
Da sauri kuwa ta shige ciki tana mai kwashewa da wata irin sassanyar dariya, sai dai kuma ganin da tayi duk sun gudune suna neman tsira, ya sanyata shash-shake fuskarta, tana mai fad'in.

"Zamu sabane nan gaba, ku da kanku zakuzo wurina nima na gudar muku Yara."

Hakan da Yarima Asad yajine kuma ya sanyasa kwashewa da dariya yana kallonta.

Ai kuwa da sauri ta futo daga ciki tana mai turo baki tare da fad'awa jikinsa ta fara kai masa dukan wasa a k'irji, tana mai fad'in.
"Mugunta! Mugunta ko!!"

Da sauri ya rik'e hannun nata yana mai fad'in.

"Ni d'inne mugu, bayan kuma kece kullum kike k'warata."

"Ni kuma, to me nayi makane ni?"
Ta fad'a da sauri, kana kuma ashagawab'e tana mai k'ara kwanciya a jikinsa da take tsananin jin dad'insa.

Au bama kisan abunda kike mun ba ko, to kawo kunnenki kiji in fad'a miki yanzu kuwa."

Ya fad'a yana mai matso da bakinsa zuwa kan kunnenta.

Sake b'oye fuskarta tayi a jikinsa tana mai dirza k'afafunta a k'asa, saboda jin abunda yace, kana kuma cikin shagwab'ab'b'ar muryarta tace.

"To..to.ba kai bane kake tafiya d'akin..ka!"

Jin abunda tacene kuma ya sanyasa yin sauri ya d'ago kanta, yana mai sanya idanuwansa a cikin nata.
Kana ya bud'e baki cikin wata raunananniyar murya tamkar zai saki kuka, yana mai fad'in.

"To bake bace bakya sona."

"Injiwa ya fad'a maka bana sonka. Ni ina son Mijina, I love you forever and ever my Prince!!!"

Ta k'arasa maganar tana mai b'oye fuskarta a cikin k'irjinsa.
Shi kuwa Yarima Asad jin abun yayi kawai asama ba tare da yayi tsammani ba, hakan kuma shine ya sanyasa suman tsaye a wurin, yana mai kallonta cikin wani irin yana yi.
Kafin daga bisani kuma ya dawo dai-dai, yana mai d'agata sama sunkutu-kum ya fara zagaye da ita a cikin wurin, cikin matsanancin farinciki mara misaltuwa idanunsa na zubar da k'wallar dad'i.
Domin kuwa ko kusa bai tab'a tsammanin jin wannan kalmar daga bakinta ba.
Hakan kuma shine ya sanyasa fucewa da ita rungume a hannunsa tamkar 'yar jaririya suka doshi cikin gidan, banda aikin sakin murmushi tana mai jin wani irin nishad'i a cikin ranta babu abun da take iyayi itama
A haka har sai da ya kaita kan bed d'inta, tukun ya kwantar da ita yana mai durk'usowa cikin sassanyar muryarsa da take ratsa k'wak'walwarta yace.

"Ki kwanta ki huta yanzu, karki kuskura ki k'ara tashi, ni yanzu zanje na dawo Amaryar prince d'in Mamaynsa shagwab'b'eb'e raggo kuma me nauyin buhun siminti hamsin."

Da sauri ta kife kanta akan gado tana mai sakin murmushi, saboda jin da tayi ashe ranar da taci masa mutunci idansa biyu ba bacci yake ba yay mata banza.
Shi kuwa juyawa yayi yana mai fucewa daga cikin gidan gaba d'aya cikin matsanancin farinciki mara misaltuwa.

Washe gari.
A yau d'in sun tashi da wata irin matsananciyar k'aunar junansu mara misaltuwa gaba ki d'ayansu.
Yayinda Yarima Asad kuma yake jinsa tamkar a cikin aljanna, banda aikin shimata albarka tare da riritata ba abun da yake iyayi, motsin kirki kuwa idan yaga tayi to ya fara jero mata tambayoyi kenan.
Hakan kuma shine ya sanyata take ta cigaba da langwab'e masa, tana mai sakin kukan shagwab'a irin wanda ita kanta take mamkin kanta a yau d'in.
Yayinda tun safe kuma take godiya ga Allah daya sota da rahama ya bata wanda ya dace da ita duk da k'insan da tayi a farko, domin kuwa yanzu ne ta gane dama can shine masoyinta, kuma shine takeso tamkar yadda ta fara sonsa a cikin mafarki da farko, shi Gid'ad'o kawai kutse yayo musu ne.


*BAYAN SHEKARA HUD'U*

Abubuwa da yawa sun faru na dad'i dana kishiyarsa a cikin shekarun da suka gabata.
Ciki kuwa sun had'a harda haihuwar da gaba ki d'aya Amaren ukku sukayi.
Matar Al'amin itace ta fara haihuwar d'a Namiji, duka watansu tara alokacin da aure.
Kana suna a cikin wata na goma ne kuma Gimbiya Haddiyal ta haifo kyawawan 'ya'yanta masu kama da ubansu sak 'yan biyu maza.
A daren ranar data haihunne kuma kasancewar ita haihuwar safe tayi, Gimbiya Tasmir ma ta sullub'o 'yan ukunta masu azabar kyau a cikin d'akinta kuma, domin kuwa ko kad'an bata wani jigata sosai ba, dan Gimbiya Haddiyal ta fita jigata, saboda ita Yarima Asad ma har kuka yasha tamkar k'aramin yaro kafin ta haihu a asibiti.
Maza biyu ta haifo masu kama da Bir sak tamkar yayi kaki ya tofar, sai kuma macen data kansance Babbarsu da take kama da mahaifiyarta basu da bambanci kwata-kwata.

Fad'ar irin farincikin da akayi a cikin wannan Ahalin gaba d'aya a ranar b'ata bakine.
Haka da ranar suna ta zagayo 'yan Kasar Malin Jahar Karfuz cikin BAK'AR MASARAUTA, da yanzu suka mayar da sunanta FARAR MASARAUTA, Saboda alkhairan da suke cikinta tare da addinin Musulunci daya bunk'asa suma duk sukazo.
Irin dai shagalin da akayi a wannan ranar bazai tab'a fad'uwa ba.
Yaran Yarima Asad sukaci sunan. Mai Martaba da kuma Lamid'o Sulaiman.
Amma ana kiransu da Dady da Abba.
Yayinda Yaran Gimbiya Tasmir kuma macen taci sunan Ummi wato Aishatu, mazan kuma sukaci sunan Abba da kuma Sheikh Ahmad.
Amma ana kiransu da, AMIR, MU'ALLIM, MAMY.
Shi kuwa D'an Al'amin daya fisu wayo Kabir sunansa, wato sunan Babansa shima yasa masa, amma suna kiransa da Hisham.

Sosai Yaran suka taso cikin gata mara misaltuwa, wanda hakan kuma ya sanya kwata-kwata basa zama a wuri d'aya, wato dai ko kasamesu a b'angaren Gimbiya Fulani ko kuma gidansu Ummi da suka koma cikin Wasai GRA yanzu, sai dai kuma har kawo yau suna tare da Sheikh Ahmad b'angarensa daban.
Yayinda Auta ma kuma aka sanya ranar bikinsa.
Iya da Kaka kuwa d'akinsu d'aya, idan mutum ya gansu zaiyi tinanin 'yan biyune su muddin ba sani yayiba, saboda yadda suke sanya har kaya iri d'aya.
A tak'aice dai yanzu gaba d'aya farinciki ya lullub'e ahalin nan tun daga 'yan FARAR MASARAUTA, MASARAUTAR WASAI, DA KUMA MASARAUATR FULD'E.
Kana kuma addinin Allah ya yad'u a cikinsu sosai.

Gimbiya Tasmir da Bir suna zuwa K'asa Malin lokaci bayan lokaci, domin kuwa b'angare guda garesu acan ma, wanda suke zama a cikinsa idan sunje har su dawo.
Yayinda Abokantarsu kuma su ukkun nan tayi bala'in k'arfi, domin kuwa yanzu aduk duniya basu da Abokai sama dasu d'in nan.
Hakama a fannin Matansu suma sun had'a kai sun zamewa junansu 'yan uwa bama k'awaye ba.
Yayinda b'angaren Ilimin addinin da suke nema kuma suka samesa sosai, domin kuwa zuwa yanzu gaba ki d'ayansu sun sauke alk'urani da biye, yayinda a yanzu kuma suka juya sukeyin hadda, wadda aduk magaribar duniya suke tafiya wurin Sheikh Ahmad a cikin motocinsu, kowa da matarsa hatta Al'amin kuwa.

Sosai Allah yasanyawa kasuwancin Bir albarka, ta yadda a yanzu yake da plazozi har kusan guda takwas a cikin kasuwanni manya-manya.
Itama Gimbiya Tasmir super marke d'inta har biyu yanzu da aka bud'e matasu da kud'inta na wurin Sheikh Ahmad da suka gudo dasu.
Yanzu haka gaba ki d'ayansu suna d'auke da k'ananan cikine masu kimanin watanni hud'u, sai dai kuma tun yanzu har anfara shiryawa zuwansu duniya.


Zaune Gimbiya Tasmir take a gaban dressin mirrow taci uban ado, cikin wata doguwar rigar less mai azabar kyau, tana k'ara gyara fuskarta.
Yayinda Bir kuma yake zaune a gefen gado sanye da Shadda getzner mai azabar kyau kalar less d'in nata tare da hula akansa.
Babu wanda zai ganta yace ita take da 'ya'ya har ukku, domin kuwa babu abunda ya canza na jikinta, sai wata irin muguwar murjewa tare da kyawu da kuma 'yar k'iba dai-dai misali da tayi.

Kallon agogon fatar da yake d'aure a tsintsiyar hannunsa yayi, yana mai fad'in.

"Please sweet heart kiyi sauri mana, kinsan dai Asad bala'ine har dai ya riga mutum shiryawa."

"Yay ta bala'insa mana Baby, suma ai haka sukeyi mana, kuma wallahi yanzuma k'ila basu shiryaba, amma bani mayafina na gama mu futa."
Ta fad'a tana mai matsowa kusa da shi.
Yafa mata mayafin nata da yake rik'e a hannunsa yayi, tukun ya rik'o hannun nata cikin nasa suna masu kama hanyar waje gwanin ban sha'awa dasu.

Acan b'angaren su Yarima Asad kuwa zaune suke akan doguwar kujera sunci uban ado da shida Gimbiya Haddiyal.
Yayinda kanta yake akan cinyarsa yana mai aikin shafa lallausar sumar kanta suna kallon juna.

Lumshe idanuwanta tayi tana mai bud'esu, kana ta bud'e baki cikin wani irin yanayi dake nuni da zallar shauk'i tare da farincikin da take ciki, tana mai fad'in.

"Sautari idanuwanmu na rufewa, kunnuwanmu kuma su ddod'e mu rasa gane dai-dai da akasinsa, idan har zuciyoyinmu suka afka cikin kogin soyayya. Hak'ik'a da ace ban sameka ba a matsayin miji bansan ya zanyi ba Ruhi, domin kuwa sai daga baya na gane ashe yaudarar kaina da cutar da kaina naso nayi, naje can ina hauka akan wani bayan bashine cikon farin cikina ba. Hakan yasa a kullum a kuma ko da yaushe nake cikin godiyar Allah daya mallakamun kai bai barni da halina ba. Hak'ik'a ina tsananin k'aunarka Ruhi, k'auna irin wadda baki ba zai iya misaltata ba, zuciya bazata iya hasashota ba. I love you Mijina!!"

Ta fad'a cikin wani irin yanayi, tana mai sakar masa sumba akan ciki.

Shi kuwa Yarima Asad da ako da yaushe idan yana gabanta yake tashi daga miskili ya koma gara, kuma mara aji, ya saki wani irin ihun farinciki da tsanain k'arinsa yana mai buga k'afa a k'asa tare da fad'in.

"Wayyo Allah na wayyo Dady na Wayyo Mamy na Dadyna Matata zata zautar dani da kalamanta na yauuu hhhhh!!"

Ya k'arasa maganar yana mai sake sakin ihu adai-dai lokacin dasu Bir suka danno kansu cikin falon nasu suma.

"Amma gaskiya manyan 'yan iska ne ku, kawai kun kora Yara daga gida kunyi zaune ku biyu kuna ta zuba iskanci harda ihu ko tsoron Allah bakwa ji."

Cewar Bir yana mai harararsu gaba ki d'aya su biyun.
Yayinda Gimbiya Haddiyal kuma ke manne a jikinsa yana ta faman yawo da da hannunsa akanta.

"Ku dama har akwai 'yan iskane sama da ku. Jifa My Mata a cikin gidan mutane suke ta faman shafa juna tsabar jaraba wai a haka kuma suke da bakin cewa wasu sunyi."

"Barsu Ruhi ai ni na dad'e da gane mugayen 'yan sa'ido ne gayun nan, dan yanzu harma sunfi wa'yancan mayun. (Al'amin da Matarsa) kuma wallahi sai dai suyi su gama amma iskanci ma yanzu muka farasa mu."
Cewar Gimbiya Haddiyal tana mai sake shigewa cikin jikin Yarima Asad.

"Wayyo Mata kina son kisa nace na fasa tafiyar nan fa wallahi idan baki dena ba."

"Ai kuwa wallahi k'ila da har dukanka yau sai Al'amin yayi, duk da dai naga suma basu futoba har yanzu."
Cewar Bir yana mai harararsa.

"To ta ina zasu futo munafikin bayan sun kora Yara daga gida."

Yarima Asad ya fad'a cikin dariya yana mai janye Gimbiya Haddiyal daga jikinsa, tare da d'aukar mayafinta da yake a jiye a gefe ya yafa mata akai.

"Wai tsabar rainin hankali ma har yanzu baku shirya ba wai, kai dan Allah Asad sai yaushe zaka canza ne wai?"

Suka jiyo muryar Al'amin daga waje yana mai fad'in haka cikin masifa, kana kuma yana doso cikin gidan.

"Kunji ko, dama na fad'a muku Al'amin d'an sharrine kunk'i ku yadda, wai Yaron da muketa jiransu tun d'azu shine dan ya futo yaga bamu futoba har yake fad'in haka."
Yarima Asad ya fad'a adai-dai lokacin da ya kama hannun Gimbiya Haddiyal, da itama d'in bata canza ba kamar Gimbiya Tasmir sukayi waje.

"Kai wallahi Al'amin kashiga ukku, tun d'azu muke jiranku amma kun rufe kanku a cikin gida Allah kad'ai yasan iyakar abun da kukeyi, shine yanzu har kake da bakin yin zancen banza."

Yarima Asad ya fad'a yana mai kai masa duka a kafad'a adai-dai lokacin da suka futo waje.

"To kace laifi mukayi mana dan mun rufe kanmu a gida mu biyu, banza d'an sa'ido kawai, kuma ai halinkane b'atawa mutane lokaci shiyasa na fad'i haka."

Al'amin da yake rik'e da hannun matarsa ya fad'a yana mai hararar Asad shima.

Shi kuwa Bir banda dariya babu abun da yake yi, a haka har suka k'arasa gaban had'ad'd'un motocinsu da suke d'auke da numbobi masu sunan Triple a jikinsu, domin kuwa komai nasu yanzu haka suka mayar dashi triple, saboda 'yan ukkun da suka mayar da kansu, domin kuwa yanzu ma gidan Ummi zasuje gaisheta shiyasa sukai wannan shirin, haka kuma sukeyi ako da yaushe idan zasu futa.

Cikin matsanancin farinciki tare da matsananciyar soyayyar junansu ko wanne ya bud'ewa Matarsa murfin mota ta shiga ta zauna, tukun ya rufe, kana suka juya suna masu shiga suka zauna a driver sit, kana sukayi musu key suna masu takesu suka fuce a jera da kuma matuk'ar gudu.✍



ALHAMDULILLAH!
ALHAMDULILLH!!
ALHAMDULILLAH!!!

*ANAN NA KAWO K'ARSHEN WANNAN LITTAFIN NAWA MAI SUNA BAK'AR MASARAUTA. ABUN DA NAYI DAI-DAI A CIKINSA INA ROK'ON ALLAH KA BANI LADANSA, WANDA YA KASANCE NA BADAI-DAI BA KUMA UBANGIJI KA YAFE MANA DANI DANA RUBUTA DAKU DA KUKA KARANTA ALBARKACIN ANNABI DA ALK'UR'ANI.*


*SAI MUYI SALATI DA SALLAMA GA AHMAD MAI SHIRYARWA, MAI CETON MUTANE GABA D'AYA.*
*YA ALLAH KAYI SALATI DA SALLAMA GA BAWANKA KUMA MANZONKA ANNABI MUHAMMAD (SAW).*
*KUMA YA ALLAH KA YARDA DA DUKKAN IYALAN GIDANSA DA SAHHABANSA, KA HAD'A HARDAMU YA MAI KARAMCI DA YAWAN BAIWA.*



_Umar Dayyan Abubakar_

*A.K.A*

UMAR FARUQ*D*

08038135929 ✍

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an

Please Login or Register in order to submit comment