Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

martaba dad'ima yaji abun yayi masa a zuciya, sabo da yasan hakan zai sanya Asad d'insa farinciki, sannan kuma ya tsira daga shiga fushin Allah, saboda dama baya tinanin d'an nasa zai iya adalci a tsakanin mata biyun da sukace sai yayi.

Acan b'angaren su mai girma Gwamna kuwa, cikin tafasar rai ya shiga cikin motar da escort suka bud'e masa ya zauna.
Tukun suka rufe murfin shima Alhaji Saleh ya shiga suka rufe kana sukayi gaba.

"Mai zai hana muhad'a Bilkisu da Sadik ayi auresu a cikin k'asa da wata d'aya kafun ayi na shi wannan yaron, saboda hakanne kawai zai sanya magan-ganun da mutane sukeyi akan abun daya faru su huce a lokaci d'aya, sannan kuma akashesu da mamaki, ta yadda zasuga wancan abun tamkar wani wasan kwai-kwayone aka shirya musu, kuma hakan shine zai kullewa 'yan adawarmu baki, sannan kuma shine zai sanya girman itama Bilkisu ya dawo a cikin idanuwan masoyanta, kana kuma hakan zai b'atawa shi Asad d'in rai muddin akace ita ta rigasa aure bashi ba, idan kuma har mukayi kuskuren barin ya rigata yin aure, to fa ita kanta ranar bikin nasa bazata iya bud'e wayarta ba ballantana har ta hau social medai, saboda tsokanar da zata sha, kana kuma 'yan jaridu zasu k'ara samu abun fad'e."

Alhaji Sale ya fad'i haka yana mai kallon mai girma Gwamna alokacin da motarsu ta fara tafiya.

Shi kuwa Sadik d'in da yake magana akansa Babban d'an sane daya kasance babban d'an kasuwa da sunansa ya zagaya gari, domin kuwa a yadda mutane suke zato ma shi d'in yafi mahaifinsa kud'i.
Yayinda Alhaji Saleh'n ma kuma ya kasance shahararren mai kud'i lamba d'aya, domin kuwa shi kansa mai Girma Gwamna sai dai yace zai nuna masa mulki amma ba dai nera ba.

Lumshe ido mai girma Gwamna yayi, yana mai jujjuya kalaman Aminin nasa acikin ransa, kafin daga bisani kuma ya bud'esu yana mai juyowa ya kalli Alhaji Saleh yace.

"Tabbas na aminta da duk bayananka hakane, amma sai dai kuma kafin nan shin shi Sadik d'in kana ganin zai yadda da abun da mukeso d'in?"

"Tabbacin hakan ya sanyani fad'a maka kai tsaye kuma lokaci guda, saboda tun usul Sadik baya iya ja da abun da nace masa yayi, bayan haka kuma ma Bilkisu Yarinyace wacce ta mallaki duk wani abu da Namiji yakeso a wurin Mace, dan haka ni nasan zasu dai-daita in sha Allah."

"Idan kuwa hakane na aminta ka turosa a yau da dare yazo su gana, idan yaso zuwa gobe sai a tsayar da maganar aurensu."

Cewar Mai Girma Gwamna, yana mai jin bak'in cikin zuciyarsa na yayewa.............✍


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*25*



Anan cikin Wasai GRA dai-dai k'ofar dank'araren gidan Alhaji Saleh suka saukesa.
Kana su kuma sukayi gaba zuwa Government House.
Kasancewar kuma basu da nisa a tsakani shiyasa cikin 'yan mintina kad'an suka k'arasa har bakin part d'insu mai girma Gwaman.

Ko kad'an har yanzu babu almaun walwala akan fuskarsa, duk da yadda sukayi da Alhaji Saleh kuwa, haka ya futo daga cikon motar yana mai shigewa cikin gidan.

A cikin dank'areren falonsu daya gaji da had'uwa ya tarar da Momyn Billy zaune akan kujera taci uban ado ta hakimce.
Hakanne yasa tun kafin ya zauna ya kalleta yana mai fad'in.

"Yi maza kije ki kiramun Bilkisu, kuma kutawo tare tabar kome take ku dawo yanzu ina jiranku."

"Meke faruwane Dady'n Billy, wani abunne ya faru acan d'in?"

"Kije ki kiramun ita nace zaki tsaya kina jan wani dogon zance."
Ya fad'a a zafafe, kana kuma cikin tsawa.
Hakanne ya sata tafiya da sauri tana mai hayewa up stairs.

Cikakken minti biyar batayi ba da hawan sai gasunan sun saukko, Billy da take sanye da k'ananan kaya na biye a bayanta.

Sosai ta rame tamkar wadda tayi ciwo, sai dai kuma a zahirin gaskiya ba wani ciwo da tayi zallar tinani da tashin hankalin abun da take ciki da Yarima Asad yayi matane ya sanyata komawa haka, domin kuwa har kawo yau kuka take akan cin mutuncin da yayi mata, sai dai kuma abun takaicin shine ama-makon taji ta tsanesa sai sonsa ma da takeji yana k'are mamaye zuciyarta, ta yadda har yau taita zumud'i da taji labarin su Dady'n nata sun tafi domin ayi maganar aure a wurin Momy'nta.

"Gani Dady."
Ta fad'a a sanyaye tana mai zama akan kujerar da take facing d'in wacce yake zaune akai, yayinda ita kuma Momynta ta zauna a kusa da Dady'n nata.

"Bilkisu!"

Dasauri Billy ta d'ago kanta, zuciyarta na harbawa da matuk'ar k'arfi, ta kalli Dadyn nata daya kira sunanta kai tsaye, abun da rabon da taji yayi hakan ita kanta ba zatace ga lokacinba, sai dai yace My Daughter ko kuma Baby.

Shi kuwa mai girma Gwamna cikin dakakkiyar muryarsa da take cike da fushi a cikinta ya d'ora da fad'in.

"Daga yau daga yanzu, har zuwa gaban abada bake ba d'an iskan yaroncan, ko wayarsa bance ki k'ara kiraba, ko kuma ki d'aga tashi idan shi ya kiraki, sabo da har abada bazan tab'a kaiki wurin da ba'a san darajarki ba."

Tamkar saukar tafasasshen ruwan zafi haka Billy taji dirar kalaminsa a cikin jikinta.
Wanda hakan kuma ya sanyata d'ago kai cikin matsanancin firgici, rud'u, had'i da azababben tashin hankali, tana mai watsa idanuwanta cikin nasa.
Lokaci d'aya jikinta ya d'auki wata irin matsananciyar karkarwa, kafin daga bisani kuma ta sakko daga kan kujerar da take tana mai cake gwiwoyinta a k'asa.
Yayinda Momynta ma tayi matuk'ar girgiza da jin abun da mijin nata ya fad'a.

Ita kuwa Billy cikin rawar murya da tsananin tashin hankali ya sanyata haka ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Karkayi mun haka Dady, wallahi tallahi ina tsananin son Prince, ina sonsa tamkar yadda nake son raina, kuma shima d'in ina da tabbacin yana sona kawai dai akasi aka samu..."

"Dallacan yimun shiru akasin banza akasin hofi shashasha wacce bata san ciwon kanta ba kawai. Wai har mutumin daya hulak'antaki yaci mutuncinki abainar jama'a akan wata zaki tsaya kina karesa, shin meye abunso ma ga mutumin da baya sonka?"

Dadyn nata ya daka mata wata azababbiyar tsawa data sanya jikinta k'ara d'aukar kyarma, kana kuma ta sake bala'in firgita.
Amma duk da haka bata hak'ura ba sai da ta sake bud'e baki tana mai fad'in.

"Wallahi dagaske nake maka Dady Prince yana sona, nima kuma shi d'in nake so."
Tayi maganar cikin matsanancin kuka.

Shi kuwa mai girma Gwamna cikin tsananin bak'in ciki da takaicinta ya bud'e baki yana mai fad'in.

"A yana sonki ne har sai Iyayensa sunyi masa dole akan ya aureki, duk da hakama kuma bai amintaba sai da yace sai dai ya had'aki da wata ya aura, wacce ta silarta kuma harya hulak'antaki acikin bainar jama'a, shin wannan d'in itace soyayya? To bari kiji, idan ma baki saniba na sanar dake, ba ke kad'ai Asad zai auraba a ranar ku biyune tare da ita wannan Yarinyar da yake kuka akanta, wanda zancen da nake miki a yanzu hakama suna can sun tafi nemo masa aurenta, kuma a hakan shine har zaki bud'e baki kina fad'amun yana sonki saboda baki da hankali ko. To kisani ko mutuwa zakiyi idan baki auresa ba wallahi tallahi sai dai ki mutu, amma har abada ni bazan tab'a had'a jini da shi ba, dan haka ki shirya yau da yamma Sadik na wurin Alhaji Saleh zaizo wurinki, kuma kimasa tarbar mutunci saboda shine zai kasance mijinki a cikin 'yan kwanakinnan ba nesa ba."

Ya k'arasa maganar yana mai mik'ewa ya doshi sama cikin sauri.

Ita kuwa Billy da Mahaifiyarta tunda ya fad'i kalmar su biyu zai had'a ya aure a rana d'aya gaba d'aya sukayi suman zaune, domin kuwa ita Billy k'wak'k'waran motsima kasayi tayi, sai idanu kawai data zuba masa har sai da ya gama fad'e yayi gaba, tukun ta rushe da wani irin gigitaccen kuka, tabbas har abada bazata tab'a iya had'a Asad da wata 'ya mace ba, balle kuma ma wannan yarinyar da yake kuka akanta, sannan kuma ya kirata da karuwa duk ta silarta.
Hak'ik'a Asad yaci mutuncinta ya cuceta, kuma ya yaudareta yaudara mafi muni daga cikin yaudara. Sai dai kuma a hakan bata jin zata iya rayuwa da wani bashiba duk da abunda taji mahaifinta ya fad'a.

Tana cikin wannan yanayin taji sautin muryar Momynta tana mai fad'in.

"Ki sani ko da shi Dadynki baice bazaki auresa ba, to nima bazan tab'a bari ki auresa ba har abada, saboda ba abola muka tsintoki ba ballantana har mu kaiki wurin da baki da daraja, dan haka ki tashi ki huce ki fara shirin zuwan Sadik nima na aminta da zancen Dadynki d'ari bisa d'ari."

Ta k'arasa maganar tana mai hayewa sama itama.

A guje itama Billy kana kuma cikin matsanancin kuka ta haye saman tana mai fad'awa d'akinta.

Cikin sauri ta d'auki wayarta tana mai nemo number Zee ta doka mata kira.

Zee na d'agawa tun kafin tayi magana ta fara zayyano mata duk abun da ke faruwa cikin matsanancin kuka.

Acan b'angren Zee kuma da take zaune akan kujerar alfarma cikin garden d'in gidansu, a wani irin zabure ta mik'e tsaye tana mai fad'in.

"Kan Ubancan kayyasa, to ke kuma saboda mahaukaciyace ke shine har zaki kama kuka akan mutumin daya gama hulak'antaki, kuma yake shirin sake yimiki wani sabon hulak'ancin mafi muni daga cikin hulak'anci. Shin uwarme Asad yake dashi da Sadik basa dashi da har zaki tayarwa kanki hankali? Shin waima kin san kuwa yadda darajarki zata k'arasa zubewa gaba d'aya a idanun k'awaye da jama'ar gari, idan har kika bari ya had'a ya aureki tare da yarinyar daya hulak'antaki akanta cikin bainar nasi? Hak'ik'a bantab'a sanin halin awaki gareki ba Billy sai yau, kuma wallahi tallahi ko Asad ne ya rage namiji d'aya aduniya bazaki auresa ba, nima sai na sake zuga Dady."

"Ke dallacan ya isa haka, akanme zaki kama yimun bala'i bayan kiranki nayi saboda ki bani shawara."

Billy ta fad'a da k'arfi, kana kuma cikin kuka tana mai jin haushin zagin da Zee tayi mata.

Ita kuwa Zee jin hakan da Billy ta fad'ane ya sanya taji gaba d'aya jikinta yayi sanyi, kana kuma taga rashin kyautawarta da tayi mata haka.
Hakanne ya sanyata bud'e baki cikin sanyi tana mai fad'in.

"Kiyi hak'uri k'awata, raina ne ya b'aci shiyasa na fad'i haka. Amma ina so ki bud'e kunnuwanki ki saurareni da kyau. Wato ko kad'an Asad baya k'aunarki, asalima baik'i yaji ance a kowane lokaci kin fad'i kin mutu ba, wanda irin hakan kuma na gudar miki tun farko, saboda sanin halinsa da nayi amma kika k'i ji, dan haka ni a shawarar da zan baki itace, ki hak'ura da Asad hak'ura ta har abada, kana kuma ki yadda ki auri Sadik, saboda Sadik ma namijine cikakke wanda ya mallaki duk abunda wata isasshiyar mace takeso a wurin Namiji. Shin dame ma Asad yafi Sadik ne? Asali, kud'i, ilimi wayewa ko kyawu, dan haka idan ma bacci kike ki farga yarinya a yanzu Sadik kawai shine gatanki, saboda hakan shi zai sanya bakin munafukai ya rufe b'am akan abunda ya faru, kana kuma masu yin taggin d'inki da videon abun daya faru tsakaninki da Asad suna sa emoji na dariya a IG su dena. Ko da yake nasan baki hau social media haryau bane, shiyasa baki san abun da ke faruwaba, dan haka a shawarar da zan baki shine, karki ta kuskura ki hau social media acikin kwanakinnan har sai ranar da aka fara bikinki da Sadik, kije musu kawai da new update na bikinki, hakan shine zai girgiza zukatan al'umma ya kuma sanya waccan maganar mutuwa gabaki d'ayanta, kana kuma masu tunanin mugun so kikewa Asad su dena, saboda shi kansa Sadik ai babu uban da bai san dashi ba."

"Ke k'awata wallahi Sadik bai kai Prince kyauba, dan haka sai da anjima nagode ni."

Cewar Billy tana mai yanke wayarta ta fad'a kan gado tare da sake fashewa da kuka.
Tabbas zataso yin abun da mahaifan nata suke son tayi na auren Sadik, saboda ita kanta tasan Sadik yakai asosa shima, sai dai kuma soyayyar Asad d'ince ba zata iya cireta a cikin rantaba yanzu, kana kuma duk da haka Asad yafi Sadik da abubuwa da dama, jama'a ne dai basu sani ba amma ita tasani.
Ta raya haka a cikin ranta tama mai cigaba da sakin kukanta.


*JAHAR KAGUL.*

Tarbar mutunci akayiwa su Babban Yaya a cikin masarautar Fuld'e sosai, tukun a k'arshe suka gabatar da abunda ya kawosu, wanda hakan kuma yayi matuk'ar yiwa Lamid'o dad'i, saboda dama so yake ya aurar da 'yarsa, to sun tsaya jiran shi Gid'ad'on da take fad'en zai bayyana ya bayyana ne sai ayi shad'i tsakaninsa da Yariman Yamma, sai kuma gashi a jiya suka tashi da jin labarin ya bayyana, sannan kuma yanzu ga wani nan ma ansamu, hakan yasa basu bar wurinba har sai da Lamid'o yasa aka tsaida ranar Shad'i, wato sati mai kamawa na gaba kenan, muddin yaga zai iya shi yaron sai yazo.
Cewar Wazirin Lamid'o.

Ai kuwa hakan ba k'aramun dad'i yayiwa Galadima da Wambai ba, yayinda Babban Yaya kuma yaji jikinsa yayi matuk'ar yin sanyi, saboda baya tunanin Asad d'insa zai yadda ya tsaya wani gardi ya dakesa ba tare dako riga a jikinsa ba, idan ma kuma ya tsaya d'in baya tinanin zai iya jurewa bulalan duka, saboda ko kad'an bai san wani abu duka ba tunda ya taso, ballantana kuma yayi tinanin zai iya daurewa.
Haka kuwa dai sukayi sallama a matsayin in sha Allah zasu zo ranar, kana suka tashi suka tafi gaba ki d'ayansu dai jikinsu yayi sanyi, saboda kowanne a cikinsu baya tinanin Asad zai iya jure bulalai.
Asalima kallon raggo shagwab'ab'b'en Mamy'nsa da kuma Mai Martaba suke masa.

Shi kuwa Lamid'on Fuld'e suna tafiya yaje ya samu Gimbiya Kab'el yana mai fad'a mata ta fad'awa Haddiyal ta sanar da shi Yaron da take so d'in, muddin da gaske ya shirya aurenta to yazo asati mai kamawa za'ayi bugun shad'i.
Tukun ya juya yana mai zuwa ya sanya aka rubuta wasik'a akan hakan aka aika da ita masarautar Yamma domin su kasance cikin shiri.

Ita kuwa Gimbiya Haddiyal da har yau take a cikin matsananciyar damuwa tun jiya data dawo daga Jahar Wasai, sabo da a jiya ma mafarkin Yarima Asad tayi yana mata kuka tare da magiya, ai kuwa tayi tsananin firgita alokacin da sak'on Lamid'o ya iso wurinta.
Duk da kasancewar tana kwancene a tsakiyar gado a lokacin da Dadenta tazo ta fad'a mata da kanta, batasan lokacin data fad'o k'asa ba tana mai d'ora hannu aka tare da sake fashewa da kuka, saboda bata sani ba ko Gid'ad'o zai yadda ya shiga gasar shad'in neman aurenta, wanda ak'arshe kuma ta yanke hukuncin komawa Jahar Wasai wurinsa gobe, domin ta sanar masa abun da ke faruwa, yau d'inma kawai dan yamma tayine shiyasa bazata tafi yanzuba, wanda hakan kuma ya sanya alokacin tasa aka nemo mata Buba ta sanar dashi ya sanar musu mota gobe zasu koma wurin Gid'ad'o am.

Misalin k'arfe biyar da rabi na yamma su Babban Yaya suka iso gida.
Kai tsaye yana futowa daga cikin mota part d'in Mamy yay.
Da sallama d'auke a bakinsa ya k'arasa ciki.

Da sauri Asad, Mamy tare da Al'amin suka zubo masa idanuwansu suna masu amsa masa sallamar, kasancewar gaba d'ayansu suna cikin falonne yanzu.

Shi kuwa Babban Yaya jiki asanyaye ya k'araso kan kujera ya zauna akusa da Al'amin.
Kana ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Barka da yamma Mamyna."

"Yawwa barkanku da dawowa ya kuma hanya?"
Cewar Mamy tana mai kallonsa tare da karantar yanayinsa.

"Alhamdulillah."
Ya fad'a, tukun Asad da Al'amin suma suka gaishesa suna masa barka da dawowa.
Da yawwa ya amsa musu, kana gaba d'aya sukayi shiru ba tare da wani ya sake cewa komai ba.
Ganin hakan da Al'amin yayine ya sanyasa bud'e baki cikin sanyi yana mai fad'in.

"Yayanmu wai ya kayi shirune bakace komai ba?"

"To me kakaso nace ne K'anina?"

Babban Yaya shima ya fad'a yana mai kallonsa, wanda hakan da Asad yajine kuma ya sanya jin k'irjinsa yayi tsanain bugawa


Shi kuwa Al'amin cikin sanyi murya yace.

"Ka fad'a mana yadda kukayi mana acan d'in."

Murmushi Babban Yaya yayi yana mai kallon yadda Asad ya durk'usar da kai.
Kana daga bisani ya bud'e baki cikin 'yar far'ah yana mai fad'in.

"To ai mun gama magana dasu, kuma sun aminta yanzu abu d'ayane kawai ya rage Haddiyal ta zamto ta Autan Mamynsa."

Da sauri gaba d'ayansu suka d'ago kai zuciyoyinsu cike da farinciki, ta yadda har suka gaza b'oyesa suna masu fad'in.

"Menene abun Yayanmu."

Ita kuwa Mamy data riga ta fahimci komenene d'in shiru kawai tayi, tana mai d'an sakin murmushin yak'e, domin kuwa bata tinanin Asad zai iya tsayawa wani ya dakesa.

Shi kuwa Babban Yaya zamansa ya gyara yana mai fuskantarsu, kana ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Shad'i, shine kawai ya rage, wanda shima d'in kuma a yau aka tsayar da ranar da za'ayi, wato rana ita yau kenan."

"Kana nufin wai sai wani k'aton ya daki Aboki tukun za'a basa ita."
Al'amin ya fad'a a firgice yana mai kallon Babban Yaya.
Shi kuwa Asad gaba d'aya kasa koda motsi yayi a wurin balle ya iya magana.
Yayinda Babban Yaya kuma ya saki murmushi yana mai fad'in.

"Bulalu d'ai-d'ai har guda talatinma kuwa, amma sai dai kuma ai bana jin k'anin nawa, nasan Jarumine zai iya shanye ko da d'arice bama talatinba, koko kamanta da sunansa ne Zaki."

Babban Yaya ya k'arasa maganar yana mai kallon Asad tare da d'an bugar kafa'arsa dan ya fahimci halin da yake ciki.
Shi kuwa Al'amin cikin tsantsar tashin hankali yadda kasan shi akace za'a daka, ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Amma dolene sai anyi dukan Yaya babu wata hanyar ta mallakarta bayan ita?"

"To tayaya za'a tabbatar da Jarumtarsa a gane zai iya rik'eta muddin ba'ayi hakan ba, al'adar fulanice a haka dan haka dolene za'ayi Shad'i.

Zumbur Yarima Asad ya mik'e daga kan kujerar da yake yana mai girgiza kai, kana ya juya da sauri ba tare daya iya ce musu komai ba, yana mai nufar hanyar d'akinsa.
Ganin hakan da Mamy tayine ya sanyata kiran sunansa da sauri.

"Mamy na hak'ura bazan iya tsayawa wani banza ya dakeni ba bayan ko ku baku dakeni ba."

Ya fad'a cikin wata irin murya ba tare daya iya juyowa ba, kana ya cigaba da tafiyarsa cikin sauri.
Ganin hakan da Al'amin yayine ya sanya sa tashi da sauri yana mai rufa masa baya, amma sai dai kuma yana k'arasawa jikin k'ofar d'akin nasa yaji ya murd'a mata mukulli.
Hakanne ya sanyasa juyawa jiki a matuk'ar sanyaye yana mai fucewa gaba d'aya daga cikin falon.
Yayinda Mamy da Babban Yaya kuma suka cigaba da tattaunawa akan batun.

Shi kuwa Yarima Asad bai tsaya ako ina ba sai da har ya isa cikin bedroom d'insa.
Da sauri ya zame rigar jikinsa tare da singilet d'insa gaba d'aya, yana mai tafiya gaban mirrow.

Kallon farar fatar jikinsa da take a wani irin kwance tana matuk'ar glowing tamkar wanda ke zuba mata madara ya dingayi, ga wasu irin kyawawan gargasa masu matuk'ar taushi da bak'i da sukayiwa fatar tasa k'awanya.

Cigaba da kallon jikinsa yayi a cikin mirrow d'in, yana mai k'iyasta yadda zai tsaya gaban wani gardi ya dinga zuba masa bulalai a haka tamkar wani jaki.
Hak'ik'a bazai iya jurewa ba, hakan ya sanyasa fara girgiza kansa yana mai taunar leb'ensa na k'asa da d'an k'arfi, yayinda idanuwansa kuma suka kad'a sukai jajajir tamkar gauta, kansa kuwa tini ya fara sara masa, zuciyarsa kuwa wani irin harbawa take da tsananin k'arfi tamkar zata hudo k'irjinsa ta futo waje.

A hankali ya fara ja da baya yana mai girgiza kansa, a haka harya k'arasa jikin gadonsa.
Kana ya fad'a kansa yaraf yana mai zama tare da rumtse idanuwansa da k'arfi.
Tukun ya d'aga lab'b'ansa cikin wani irin sauti daya samu ya janyosa da k'yar, yana mai fad'in.

"Na hak'ura Haddiyal, muddin har sai wani ya dake ni kafun na mallakeki a rayuwa."


Washegari.

Ko kad'an jiya Yarima Asad bai samu ya rintsaba, saboda tinanin-nikan da suka yiwa zuciyarsa k'awanya ta ko ina, ta yadda har a k'arshe ya gane cewar yaudarar kansa yayi da yay tinin zai hak'ura da ita.
Tabbas a jiyan da dare ya k'ara tabbatarwa kansa da ba k'aramun so yake yiwa Haddiyal ba, hakanne ya sanyasa aminta akan zaije zaiyi kuma komai muddin hakan zaisa sa ya mallaketa.
Tukun bayan ya samu ya dawo daga masallaci bacci b'arawo ya d'aukesa.


*JAHAR KAGUL.*

Tamkar yadda Gimbiya Haddiyal taga rana haka taga dare jiya ba tare data iya runtsawa ba.
Yau kuwa tun asubar fari ta shirya cikin wata bluen doguwar riga ba tare data shafa ko hoda akan fuskartaba, sai zallar mai kyau.
Amma duk da hakan ba k'aramun kyau tayi ba, domin kuwa sai ta futo tamkar balarabiya, tukun ta fuce cikin sauri ba tare data d'au komai ba sai wata 'yar takarda da tayi rubutu a cikinta kawai, alokacin k'arfe shida na safe.
Tana futa kuwa ta tarar da Buba da kuma direban mota suna jiranta, hakan yasa cikin sauri ta k'arasa tana mai shigewa ciki ba tare da ko amsa gaisuwar da Buba yake mata tayiba.
Tukun direban yaja motar suna masu d'aukar hanya.


*JAHAR WASAI, BABBAN ZAURE LOCUS.*

Sosai Gimbiya Tasmir taji ta samu nutsuwa da dangin Bir, saboda yadda suka dinga nan-nan da ita, yanzu fargabarta d'aya kawai itace Haddiyal, domin kuwa tun bayan tafiyarta har yau tinaninta yak'i ya bar zuciyarta, duk da dai ta fannin Jaruminta ma kwata-kwata ba taga alamun ya damu da ita 'yar Sarkin fulanin ba, yayinda su kuma suke cigaba da shan soyayyarsu hankali kwance, sai dai kuma a yanzu basa samun dogon lokaci kamar lokacin da suna Bak'ar Masarauta.
Sosai sukayi sabo da Alawaiyya mai aikin Ummi ad'an kwana biyun da sukayi tare, kana kuma Gimbiya Tasmir take sake lura da yadda suke ibadunsu da sauran mu'amalunsu abun na matuk'ar birgeta, a kowane lokaci cikin tinain mahaifanta take, sai dai kuma tana k'ok'ari wurin b'oyewa, saboda ganin da tayi Jaruminta baya jin dad'i.

A can b'angaren Bir ma kuwa sosai suka saba da Auta, a kullum kuma idan zaiga Auta yayi abu wanda ya danganci musulunci saiya tambayesa, yayinda shi kuma Auta yake zama yayta zayyanomasa abubuwa, ta yadda yake jin addinin na birgesa ako da yaushe.

Tun daga ranar da Gimbiya Haddiyal ta tafi har kawo yau kimanin kwana biyu kenan ya kasa cireta daga cikin zuciyarsa, ga tausayinta kuma daya samu wuri ya zauna, harma wanda shi kansa yarasa dalilin da yasa yake jin hakan dangane da ita, sai dai kuma yana k'ok'arin b'oye damuwarsa, muddin suna tare da Gimbiyarsa gudun karta zargi wani abu.

Kaka kuwa sosai take shakkar Gimbiya Tasmir yanzu, asalima ko kallon cikin idanuwanta bata iyayi, wanda hakan kuma yayiwa gaba d'aya jama'ar gidan dad'i.

Yanzu haka zaune Bir yake akan kujerun da suke a cikin compound d'in lumshe da idanuwansa.
Duk wanda zai gansa a yadda yake yanzu zaiyi tinanin ko mafarki yake yine, sai dai kuma a zahirin gaskiya babu mafarkin da yake sai zallar tinanin bafullatanar daya samu gurbi a zuciyarsa.


Misalin k'arfe goma na safe motarsu Gimbiya Haddiyal ta k'araso k'ofar gidansu Sheikh Ahmad.
A kuma dai-dai wannan lokacin Gimbiya Tasmir da take zaune akan kujera cikin falo suna 'yar hira ita da Ummi da kuma Alawiyya, tare da Matar Sheikh Ahmad taji gabanta yayi wata irin mummunar fad'uwa.
Da k'arfi kuwa ta rumtse idanuwanta tana mai d'an cizon leb'enta na k'asa.
Kafin daga bisani kuma ta mik'e tsaye zumbur, saboda wani tinani daya fad'o mata cikin rai.
Kana ta juya tana mai shirin fucewa daga cikin falon.
Hakan da Ummi ta ganine ya sanyata fad'in.

"Ina kuma zuwa d'iyata."

Cak ta tsaya a wurin da take, tana mai d'an juyowa ta kalli Ummi, tukun ta janye idanuwanta k'asa da sauri, tana mai fad'in.

"Dama..dam zan shiga garden ne."
Gimbiya Tasmir ta samu kanta da fad'in haka a sanyaye.
Yayinda Matar Sheikh Ahmad kuma ta bud'e baki cikin zolaya tana mai fad'in.
"Ko kuma wurin masoyi ba."

Da sauri kuwa ta juya tana mai tafiya kanta durk'ushe a k'asa, saboda kunyar da taji ta lullub'eta.
Ita kuwa Ummi cikin raha tace.
"Ke tafi abunki 'diyata rabu da ita, itama nan zaman jiran dawowar nata take."

Gaba d'ayansu dariya suka sa, yayinda ita kuma Gimbiya Tasmir ta fuce daga cikin d'akin.

Futarta daga cikin falon yayi dai-dai da lokacin da Gimbiya Haddiyal ta danno kanta zuwa cikin compound d'in gidan itama.
Take kuwa idanuwansu suka sark'e a cikin na juna, wanda hakan kuma ya sanya zuciyoyinsu sukayi wani tsananin harbawa, tamkar zasu

Please Login or Register in order to submit comment