Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yariman Yamma.

Shiru yayi yana mai tinanin wanene shi kuma wannan d'in aransa.
Tukun daga bisani ya janye idanuwansa daga kan Jauron Yamma, yana mai juyawa ya koma wurin da Asad yake.

"Mu k'arasa ciki mana ko."

Al'amin ya fad'a yana mai tab'o Yarima Asad.
Hakan da Yarima Asad yaji ne, ya sanya sa janye idanuwansa daga kan Jauron Yamma, yana mai fesar da wata zazzafar iska daga cikin bakin sa.
Kana ya fara d'aga k'afafuwansa yana mai bin Al'amin, suka kutsa kansu zuwa ciki, yayinda kowanne kuma a k'asan zuciyarsa yake tinanin waye ne wanda ya ganin.

Jikin wata bishiya da take a saitin wurin da Jauron Yamma yake amma daga d'an nesa, Yarima Asad yaja ya tsaya yana mai jingina da ita, domin kuwa haka nan kawai tsanar gayen daya gani sanye da kayan gidadawa a jikin sa ta lullub'e zuciyarsa.
Ganin da Al'amin yayi ya tsaya anan ne ya sanya fad'in.

"Mu k'arasa kan kujerar mana ko."

"Kana iya k'arasawa kai, amma ni ina nan wurin."

Yarima Asad ya fad'a ba tare daya kallesa ba.
Hakan da Al'amin ya gani ne ya sanya sa tafiya zuwa kan kujrar ba tare daya kara cewa Yarima Asad komai ba, domin kuwa shi dai bazai iya wannan tsayuwar ba.

Al'amin na barin wurin kuwa suka hango tawowar Gimbiya Haddiyal zuwa wurin da suke.
Hakanne kuwa ya sanya Yarima Asad yaji zuciyarsa tayi wani irin harbawa da matuk'ar k'arfi.
Tukun ya juya b'angaren da Jauron Yamma yake a firgice, yana mai watsa idanuwansa akan sa, domin kuwa take a wurin zuciyarsa ta basa cewar shi ne Gid'ad'on ta da take cewa yafisa.
Wanda kuma hakan yayi dai-dai da lokacin da shima Jauron Yamma ya juyo b'arin da Yarima Asad yake a matuk'ar firgice, yana mai watsa idanuwansa akansa, domin kuwa shima take a wurin zuciyarsa ta shaida masa da cewar shine Gaid'ad'on tan da take fad'in ya fisa komai ita tasace.
Kallon kallo suka fara jifan junan su da shi, ko wanne na jin tsanar d'an uwansa na cakar zuciyarsa.

A b'angaren Gimbiya Haddiyal kuwa, kallo d'aya mutum zai mata ya fahimci ranta a tsantsar b'ace yake, domin kuwa dole Daddenta tayi mata akan sai tazo wurin Jauron Yamma da Lamid'o yasa ta turata.
Wanda hakan kuma shine ya sanya taji gaba d'aya wani irin mugun bak'in ciki ya turnuk'eta, ta yadda har ya gaza b'oyuwa akan fuskarta, sosai ta k'udiri aniyar yiwa Jauron Yamma rashin mutunci, ta yadda shi da kansa zai je ya samu iyayensa da batun ya janye.

Sanye take da kayan fulani a jikin ta.
Ko kad'an babu wata kwalliya akan fuskarta, yayinda kanta kuma ya kasance d'auke da wasu irin manya-manyan kitso irin na fulani, da jelolinsa suka zubo har ta kan fuskarta suka sauka zuwa gadon bayanta.

Ko kad'an bata kula da kowanne a cikin su ba, saboda kanta da yake sunkuye a k'asa har sai da ta kusa zuwa dab da su.
Tukun ta d'ago kanta, kuma Allah yasa alokaci guda gaba d'aya ta hangi kowanne daga cikin su.

Take kuwa ta tsaya cak a wurin da take, ba tare da ta iya ko sake k'wak'k'waran motsi ba a wurin.
Kafin daga bisani kuma ta kai idanuwanta kan fuskar Jauron Yamma da shima yake kallonta, tukun ta janyesu daga kan fuskarsa tana mai mayar da su kan fuskar Yarima Asad da yake tsaye shima yana kallon nata.
Lokaci d'aya kuwa idanuwan nasu suka sark'e wuri d'aya.
Kafin daga bisani kuma ta sake d'auke su daga kansa tana mai mayar da su kan fuskar Jauron yamma.
Haka tai tayi har kimanin sau ukku, tukun ta durk'usar da kan nata k'asa tana mai taune lowar lips d'in ta da tsananin k'arfi.
Yayinda zuciyarta kuma ta d'auki wani irin turirin bak'in cikin ganin mutanen da tafi tsana sama da kowa da komai da tayi a lokaci d'aya, kana kuma duk a wuri d'aya da zummar sun zo wurinta.

Take kuwa ta fara kissima irin abun da ya kamata tayi musu a cikin ranta, wanda zai k'ona musu rai tamkar yadda suka k'ona mata nata ran.

Su kuwa ganin da sukayi ta d'auke idanuwansu daga kanta ne, ya sanya su juyawa a lokaci d'aya, suna masu kafe junansu da ido.
Ko wanne najin tamkar yaje ya shak'e d'an uwansa har sai yaga ya dena numfashi, tukun ya barsa, domin kuwa gaba d'ayan su kowa a zatonsa wanda yake gani shine Gid'ad'on ta.

Ita kuwa Gimibiya Haddiyal sai da ta d'auki kimanin mintina biyar a wurin da take daga tsaye, kafin daga bisani kuma ta sake d'ago kanta tana mai kallonsu.
Kana ta fara d'aga kafafuwanta cikin tsantsar zafin rai, tana mai t...........✍


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*14*



Tunkarar wurin da Jauron Yamma yake, idanuwanta k'ur akan fuskarsa.
Hakan da Yarima Asad ya ganine ya sanya sa binsa da idanuwansa, zuciyarsa na wani irin bugu da tsantsar k'arfi tare da tafarfasa.
Yayinda tsanar Jauron Yamma kuma take k'ara lullub'e ilahirin jiki da zuciyarsa, domin kuwa yanzu ya tabbatar da shine wanda take kira da Gid'ad'onta.

Sai da taje har dab da wurin da yake a tsaye, tukun taja ta tsaya.
Kana ta d'an duk'usar da kanta k'asa tana mai lumshe idanuwanta, kafin daga bisani kuma ta d'ago su tana mai fesar da iska.
Yayinda shima Jauron Yamma ya kafeta da nasa idanuwan, yana mai jin wata irin muguwar soyayyarta na fuzgarsa, sannan kuma zuciyar sa na yin sanyi, sabo da ganin da yayi ta tawo wurin sa ba wurin wancan banzan na gefen sa ba, wanda hakan kuma yasa sa fahimtar ba shine Gid'ad'on ba, domin kuwa ya sani da shi d'inne a yadda ta karanto masa matsayinsa a wurinta, babu abun da zai sa tak'i kulasa ta tawo wurinsa.
Kafe junan su sukayi da idanuwa ba tare da wani yace komai ba.

Acan wurin Yarima Asad kuwa sosai yake jin zuciyarsa na wata irin tafarfasa, wani irin kishi wanda bai san yana da shi ba ko kad'an yaji yana taso masa, ta yadda har yake jin tamkar yaje ya shak'e wuyan Jauron Yamma har sai yaga ya dena numfashi tukun ya sake sa.

Lokaci d'aya idanuwansa suka kad'a sukai jajajir tamkar gauta.
So yake ya janye idanuwan nasa daga kasu ko yasamu sauk'in rad'ad'in da yake jin zuciyarsa nayi masa, amma gaba d'aya yaji ya gagara yin hakan.

Yayinda Al'amin kuma yake zaune akan kujerar nan, yana mai kallon ikon Allah shima.
Hak'ik'a yau ya fahimci dalilin daya sanya Asad matowa akan yarinyar, wato azababben kyawun da Allah yayi mata, domin kuwa shi kansa ba k'aramun jan hankalinsa kyawun nata yayi ba.

Cigaba da kallon juna sukayi, ko wannen da yadda yake ji a cikin ransa akan d'an uwansa.
Kafin daga bisani kuma Gimbiya Haddiyal ta juyar da kanta gefe.
Kana ta bud'e baki cikin wata irin murya tana mai fad'in.

"Da alamu kunnuwanka sun samu matsalane a waccan ranar da kayi zuwan farko, shi ya sa har ka sake kwaso tsummokaran k'afafuwanka ka dawo yau ma ko?
To bara kaji in fad'a maka, ba kadawo yau ba kayi tinanin ko zaka samu d'igon murmushi akan fuskata, to idan duka nan zaka dawo ka tare da zama, ina mai tabbatar maka da har abada bazaka tab'a ganinsa ba.
Shin wai in tambayeka ma mana.
Dama acikin hallitu mutane, akwai wa'yan da ake yin su ba tare da an dasa musu zuciya a k'irjinsu ba ne?"

Ta k'arasa maganar tana mai juyowa tare da d'ago kanta ta watsa dara-daran idanuwanta a cikin nasa jajayen.
Tukun ta k'ara gyara tsayuwarta tana mai sake fuskantarsa, tare da d'orawa da fad'in.

"Kasani rashin zuciyarka ba zai tab'a damuna ba, domin kuwa abun da na sani shine, har abada bazan tab'a k'aunarka ba, sabo da zuciyar haddiyal ta dad'e da zamtowa mallakin wani, mutum mai daraja da k'ima a idanuwanta.
Hakan yasa zan sake shawartarka a karo na biyu, akan ka koma ka shaidawa mutanen da suke aiko ka zuwa wuri na, cewar Haddiyal ba kalar matarka bace ba har abada."

Ta k'arasa maganar tana mai janye idanuwanta daga cikin nasa, tare da juyawa ta doshi wurin da Yarima Asad yake ranta a tsantsar b'ace, ba tare data tsaya jin abun da Jauron Yamma zai ce ba.

Shi kuwa Jauron Yamma sosai kalamanta suka sake tafasa zuciyarsa.
Da karfi ya rumtse idanuwansa yana mai jin yadda ransa ke k'ara kai k'ololuwa wurin b'aci.
Hak'ik'a Yarinyar nan ta hulak'antasa, taci mutuncinsa k'arshen cin mutunci akan wani can banza, dan haka shi kuwa ya k'udiri aniyar sai ta zamto tasa muddin bugun shad'i shi zai bam-bance tsakaninsa da wancan sha-sha-shan farin yaron, domin kuwa kallo d'aya yayi masa ya fahimci cewar ba zai tab'a yin dauriya ba ko kusa ko kad'an.

Hakanne ya sanya sa bud'e idanuwan nasa yana mai juyawa yabi bayanta da kallo, zuciyarsa na sake tafar-fasa, sabo da duk atinaninsa shima Yarima Asad shine Gid'ad'on nata.

Shi kuwa Yarima Asad ba shi ya iya janye idanuwansa daga kansu ba, har sai da yaga tawowar Gimbiya Haddiyal zuwa wurin da yake, tukun ya kaudar da kansa gefe yana mai rumtse idanuwansa.
Yayinda a k'asan zuciyarsa kuma yake tinanin abun da zata zo tayi masa da tayo wurinsa, bayan ta gama soyayyarta kuma, domin ko shi duk a tinaninsa kalman soyayya take fad'awa Jauron Yamma a tsayuwar da tayi a gaban sa bakinta na motsawa.

Ba shi ya iya bud'e idanuwan nasa ba har sai da yaji alamun tsayuwarta a gaban sa.
Tukun a hankali ya juyo b'arin da yake jin motsinta, yana mai bud'e jajayen idanuwansa akan fuskarta.

Kallonta ya farayi yana mai jin yadda wani irin tuk'ik'in bak'in ciki ke taso masa, saboda tinowar da yayi na daga wurin wanda ta dawo.

Ita kuwa Gimbiya Haddiyal a hankali ta juyar da kanta gefe, tana mai fesar da wata irin zazzafar iska daga cikin bakinta.
Tukun ta d'ago kanta tana mai watsa idanuwanta a cikin nasa.
Kana ta d'ago yatsarta tana mai bud'e baki, tare da juyawa ta kalli wurin da Jauron Yamma yake a tsaye, tana mai nunasa da yatsa tace.

"Ka ganshi can, duk da irin shigar mutuncin da yake zuwa da ita sanye a jikin sa, hakan baisa na tab'a jin ko d'igon sonsa ba a zuciyata, ballantana kuma kai da kake kwaikwayon 'ya'yan arna."

Ta fad'a tana mai janye yatsarta daga nuna Jauron Yamma da take yi, ta juyo gaba d'ayanta b'arin da Yarima Asad yake tana mai zube idanuwanta akan fuskarsa.
Shi kuwa Yarima Asad lumshe idanuwansa yayi, yana mai jin wani irin abu mai kama da farinciki na lullub'esa, tukun ya fesar da numfashi bayan ya bud'e idanuwansa, saboda jin da yayi zaton sa bai zamto gaskiya ba, wato dai shima wancan d'in ba yinsa take ba, asalima mutuncinsa taci tamkar yadda yasan tazo taci masa mutuncinne shima.
Tabbas ko banza jin hakan ya sanyaya masa rai, kuma ya sa zai k'ara d'aura d'amara wurin ganin ya bigesu su duka.
Yana cikin wannan yanayin ya jita ta cigaba da fad'in.

"Ba zan gaji da fad'a maka ba, muddin ba zaka gaji da zuwa wurin da nake ba!
Hak'ik'a bakayin munba, zubinka baya birge ni, gaba d'aya Gid'ad'o ya cike ko ina,e baka da wuri a zuciyata.
Shi kad'ai nake so, haka kuma shi kad'ai nake gani da mutunci, dan haka ka tafi ka koma inda ka futo, har abada ko zaka dawwama anan ba zaka tab'a samun abun da kake so ba a wurina, domin ko bana sanka ko kusa ko kad'an."

Ta k'arasa maganar tana mai juyawa ta fara shirin tafiya.
Ganin hakan da Yarima Asad yayi ne, ya sanya bud'e baki da sauri, duk da yadda yake jin zuciyarsa na rad'ad'i, yana mai fad'in.

"Ban tab'a sanin haka al'amarin soyayya yake da zafi ba, ban tab'a sanin haka zuciya take ciwo da rad'ad'i ba idan wacce kake so bata sonka.
Na mallaki komai da komai na jin d'ad'in duniya, na tara dukiya wacce ni kaina bansan adadinta ba.
Na miki alk'awarin jiyar dake dad'i, irin wanda baki tab'a mafarkinsa ba, na miki alk'awarin nuna miki tattali fiye da irin tattalin da ake yiwa k'wai.
Na rok'eki ki k'aunace ni ko da kwatankwacin irin wadda nake miki ne, idan kuma har kika k'ini yauma ban san yadda zanyi ba, ba mamaki kiji labarin mutuwata ma, sabo da ina miki so na hak'ik'an ne.
Dan Allah ki juyo ki kalleni ki furta mun ko da kwatankwacin irin wannan kalaminne, ko hakan zai sanya zuciyata tayi sanyi, yau nayi bacci cikin salama."

Ya k'arasa maganar muryarsa nayin rauni, tamkar zai fashe da kuka.

Ita kuwa Gimbiya Haddiyal tunda ya fara zancen taja ta tsaya a wurin da take ba tare da ta juyo ba.
Hak'ik'a taji duk kalamin da ya fad'a gaba d'aya, sai dai kuma babu wanda aka samu yayi tasiri ko kad'an a zuciyarta.
Hakanne ya sanya ta juyo da kanta tana mai sake zuba k'wayoyin idanuwanta a cikin nasa.
Tukun ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Ba yau bama, har gaban abada ba zaka tab'a jin makamanciyar irin wannan kalamin daga bakin Haddiyal ba, domin ko Haddiyal mutum d'aya kawai take so, kuma shine kad'ai zata iya fad'awa haka.
Dan haka ba zaka tab'a ganin ko murmushi na ba, ballantana kuma kaji irin wannan furucin, koda kuwa za'ace da zarar na bar wurin nan zaka fad'i ka mace ta sanadin k'in fad'ar tawa.

Ta k'arasa maganar tana mai janye idanuwanta daga cikin nasa, tare da juyawa tayi tafiyarta.

Da k'arfi Yarima Asad ya rumtse idanuwansa, jikin sa na d'aukar rawa.
Shin me yasa zuciya zatayi masa haka? Me yasa ya kasa hak'ura da wannan yarinyar koya samu salama a cikin ruhinsa? Shin anya kuwa akwai ranar da zata so sa?

"Ina babu, sabo da banga alama ba."

Ya fad'a afili yana mai girgiza kansa, yayinda har lokacin kuma yake jin zuciyarsa na rad'ad'i tamkar zata k'one.

Jin saukar hannun da yayi akan kafad'arsa ne, ya sanya sa bud'e idanuwan nasa yana mai watsa su a cikin na Al'amin da yake tsaye a gaban sa.
Kana kuma a hankali cikin sanyi ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Al'amin ba zata soni ba, yanzu ma ta shaida mun cewar ko da da zarar tabar wurin nan za'a kira ta a shaida mata da mutuwata bata da damuwa.
Shin ya zanyi ne Al'amin?
Nayi mata da zafi naga hakan baiyi ba, na nuna mata matsayina da yadda mata suke sona, duk hakan baiyi ba, yanzu kuma na durk'usar da kaina gareta na bita ta lalama, shima duk a banza.
Shin me kuma zanyi? Ya zanyi ne Al'amin?"

Ya fad'a cikin wani irin yanayi, muryar sa na rawa yana mai girgiza kansa.
Wanda hakan kuma ya sanya Al'amin jin wani irin mugun tausayinsa ya lullub'esa, ta yadda har yake jin inama ace yana da ikon sanyata taso sa, tabbas da babu abun da zai hanasa yin hakan, amma sai dai ina, ko d'an uwanta ma bashi da wannan ikon ballantana kuma shi.
Hakanne yasa ya sake dafa kafad'ar Yarima Asad, yana mai fad'in.

"Zata soka Aboki, jikina na bani cewar watarana zata zamto mallakinka, zata soka irin son da kake mata koma fiye da shi, domin ko shi al'amarin soyayya ya gaji haka.
Bama iya soyayya ba, komai na rayuwa yana tafe da k'alubale ne a cikin sa, idan kuma mutum yayi hak'uri ya daure ya cije sai kaga a k'arshe ya dace.
Hakan yasa nake baka tabbacin kaima zaka dace a gaba muddin kayi hak'uri in sha Allah."

Al'amin ya fad'a yana mai d'an girgizasa.

Lumshe idanuwa Yarima Asad yayi, yana mai jin zuciyarsa na cigaba da suya, ji yake inama ace zai samu damar zubar da hawaye, ko Allah zai sa rad'ad'i da nauyin da suka danne zuciyarsa su ragu.

Ya d'an jima lumshe da idanuwan nasa, tukun daga bisani ya bud'e su yana mai fad'in.

"Allah ya tabbatar da hakan to d'an uwa, hak'ik'a nima d'in zan jure, muddin zan samu dacewa a gaba, sai dai kuma ina tsoron kar kafun zuwan lokacin ya zamto zuciyata ta tarwatse, sabo da ba k'aramun k'una nake jin tana yi mun ba aduk lokacin dana tina matsayina da kuma irin yadda nake abaya, da yadda na koma a yanzu."

"Ina so ka manta da duk wani matsayinka na baya Asad, ka fuskanci sabuwar rayuwar daka samu kanka a cikinta yanzu, hakan shine zai sanya kaccima gaci, dan haka in sha Allah babu abun da zai faru, Haddiyal takace d'an uwana.

Jin-jina kai Yarima Asad kawai yayi ba tare da yace komai ba, domin kuwa shi yanzu babu abun da yake tinanin za'ace yayi sa ya kasa yinsa, muddin ance masa tanan ne kawai zai samu damar mallakarta.

Acan wurin Jauron Yamma kuwa, bashi ya iya janye idanuwansa daga kan Yarima Asad ba har sai a lokacin da yaga tafiyar Gimbiya Haddiyal, tukun ya rumtse idanuwansa yana mai jin tsanar Asad na kewaye ilahirin jiki da zuciyarsa, domin kuwa shi har yanzu a tinaninsa shine Gid'ad'on ta, ga kuma abun da ya k'ara k'ona masa rai, ganin yadda ta juyo ta nuna sa, kana kuma shima ya kallesa, tukun suka janye kansu a tare, wanda hakan kuma da tayinne ya sanya sa yayi zargin zaginsa take yi, tana cigaba da kushe sa a wurin sa.

Cikin tsantsar k'unar rai ya sake bud'e idanuwansa yana mai juyawa b'arin da Yarima Asad yake ya kallesa.
Take kuwa idanuwansu suka sark'e a wuri d'aya, saboda yadda shima Yarima Asad ya juyo b'angaren da yake adai-dai lokacin.

Kallon-kallo suka fara jifan junan su da shi, ko wanne da abun da yake sak'awa acikin zuciyarsa game da d'aya.
Tukun a k'arshe suka janye jajayen idanuwansu daga cikin na juna, shi Jauron Yamma ya sanya takalmansa da suke a jiye a gefen shimfid'ar nan, yana mai sauka daga kanta yayi gaba.

Ita kuwa Gimbiya Haddiyal tana shirin futa daga cikin wurin, shima Habu na sanyo kansa ciki.
Yayinda daga bayansa kuma wata matashiyar budurwa take biye da shi hannunta rik'e da tray.

Cak ya tsaya a wurin da yake yana mai bin fuskar Gimbiya Haddiyal da idanu.
Da niyyar yaje ya lallab'ota ya samu tazo wurin Asad ya tafi d'akinta, sai dai kuma yana zuwa yaga bai ganta ba, da kuma ya tambayi mahaifiyarsu sai take fad'a masa cewar ai tana waje, Jauron Yamma ne yazo yau.

To shine fa yasa aka dama masa fura ya tawo da ita, da niyyar da anjima ya dawo idan ta sallami Jauron Yamma, ya rok'e ta taje wurin su Asad, sabo da shi kwata-kwata bai san anan suke had'uwa da shi ba.

A hankali ya janye idanuwansa daga cikin nata, yana mai kai su can cikin wurin.
Take kuwa suka gano masa Jauron Yamma dake tawowa wurin, fuskarsa a tsantsar d'aure shima, tamkar yadda ta tan take.

Yayinda acan gefe kuma ya hangi Al'amin da Asad zaune akan kujera, Asad ya lumshe idanuwansa tamkar mai yin bacci.
Hakanne ya sanya sa dawo da duban sa kan Gimbiya Haddiyal, amma sai kuma yaga ta janye nata idanuwan, tana mai cigaba da tafiyarta tazo zata huce ta kusa da shi ba tare da tace masa komai ba, domin kuwa shi kansa haushinsa taji tana ji yanzu, sabo da tasan yasan da zuwan wancan mutumin da bata son ganinsa.

"Ina fatan dai kin k'arasa wurinsa kun gaisa ko?"

Habu ya fad'a k'asa-k'asa, kana kuma cikin sanyi adai-dai lokacin da tazo saitin sa tana shirin shigewa.

Jin-jina masa kai kawai tayi ba tare da tace komai ba, sai cigaba da tafiyar tama da tayi itama.
A kuma lokacin shima Jauron Yamma ya k'araso wurin.
Hakan da Habu ya ganine ya sanya sa mik'a masa hannunsa yana mai fad'in.

"Ah kace yau babban bak'o mukayi."

Jinjina masa kai kawai jauron yamma ya iyayi, yana mai k'ak'alo murmushin daya tsaya a iyakar kan lab'b'ansa tare da mik'a masa hannu.
Tukun ya yi gaba abun sa yana mai jin zuciyarsa na cigaba da tafar-fasa.

Ganin hakan da Habu yayi ne ya sanya ya jinjina kansa.
Kana yayi gaba abinsa yana mai nufar wurin da su Al'amin suke.

"A'a wai anan kuka zauna, amaimakon ku k'arasa kan shimfid'ar kenan."

Habu ya fad'a adai-dai lokacin daya k'araso wurin da suke, bayan yayiwa Hadimar da take d'auke da tray'n nan alamar ta sauke sa a k'asa.

"Hmmm! Ina mu da k'arasawa kan shimfid'a bayan mun samu ribol d'in mu a wurin."

Al'amin ya fad'a yana mai d'an yamutsa fuska.
Shi kuwa Asad k'ala baice ba, sai ma k'ara gyara zamansa da yayi akan kujerar, alamun bazai tab'a tashi ya koma kan shimfid'ar ba kenan.
Jin hakan da Habu yayi ne ya sanya sa sakin murmushi, tukun daga bisani yace.

"To amma aikwa sakko a muku wata shimfid'ar, tun da ba kwasha furar a haka ba ko?"

"Malam ni bani ma furar nasha, ko ta rage mun rad'ad'in da nake ji a zuciya."

Al'amin ya fad'a yana mai durk'usawa ya d'auko furar tare da tsoma ludayi acikin ta ya fara shanta.
Jin hakan da Habu yayi ne ya sanya sa sakin dariya, tukun ya fara yiwa Yarima Asad magiyar yasha furar shima, har ya samu yad'an sha ludayi ukku tukun ya ture ta gefe.
Kana suka mik'e duka tsaye da niyyar tafiya.
Hakan da Habu ya ganine ya sanya sa fad'in.

"Wai kuna nufin tun yanzu har zaku koma, ko cikakken minti talatin ba tare da kunyi ba?"

"To mene amfanin zaman, tunda mun riga munyi abun da ya kawo mu Habu, ai sai dai mu d'aukarwa kan mu dare ma fa."

Al'amin ya fad'a alokacin da yabi bayan Yarima Asad, kasancewar shi har ma yayi gaba.

"Amma dai ai yau kwazo muje ku gaida su Baffa ko."
Habu ya fad'a yana mai kallon su.

"A'a abok, gaskiya ina ganin zuwa gaisuwar nan ba zai yiwu ba a yanzu, sai dai azuwa na gaba, a lokacin duka mun sanyo manyan kaya ma."

Al'amin ya fad'a duk da sanin da yayi na Yarima Asad bazai tab'a sanya manyan kaya ba kuwa.
Hakan da Habu yaji ne ya sanya yin shiru yana mai binsa suka doshi hanyar futa daga wurin gaba d'aya.


*K'ASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAK'AR MASARAUTA.*

Cikin tsantsar farinciki da annashuwa irin wadda Bir bai tab'a tsintar kansa ba a ciki ya koma b'angarensu.

Kai tsaye ya doshi d'akin Iyar Bayi, sabo da ganin da yayi bai ganta ba a waje, domin yaje ya labarta mata yadda sukayi da Gimbiyarsa yau, kana kuma ya bata abun da ya farauto musu.

Zaune ya sameta a cikin d'akin ta jingina da bango.
Yayinda hasken fitilar wutar data kunna kuma ta haske cikin d'an d'akin.

K'arasowa yayi har gaban ta yana mai zama ya tank'washe k'afafuwansa shima.
Ganin hakan da iya tayi ne ya sanya ta gyara zamanta itama, tana mai fuskantarsa.
Kana daga bisani ta bud'e bakinta tana mai fad'in.

"Shin wane abun farincikin Jarumi na yayi gamo da shi ne a hanyarsa, domin ko hak'ik'a naga farinciki muraran akan fuskar Yarona."

Ta k'arasa maganar fuskarta d'auke da murmushi.
Yayinda shi kuma Bir ya lumshe idanuwansa, yana mai jin wani irin farinciki na k'ara lullub'e sa.
Kafin daga bisani kuma ya bud'e su, yana mai fesar da iska daga cikin bakinsa.
Kana ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Hak'ik'a nayi gamo da babban farinciki kuwa Iyata, domin kuwa burina ya cika, mafarkina ya tabbata.
Gimbiya tazo har wurin da nake ta furta mun kalmar so da bakinta yau."

Da sauri Iya ta zaro idanuwanta, tana mai d'ora tafin hannunta akan k'irjinta ta dafe sa da shi, kana ta bud'e baki cikin wata irin murya mai tattare da fairgici a cikin ta, tana mai fad'in.

"Shin kasan abun da kake fad'e kuwa Jarumi?"

"Tabbas kuwa Iya ni nasan abun da nake fad'e, kuma yanzu zan baki labarin yadda duk abun ya faru kiji kema."

Ya fad'a fuskarsa d'auke da tsantsar annuri.
Tukun ya k'ara gyara zamansa yana mai fara bata labarin duk abun da ya faru, har zuwa rakiyar da yayi mata sannan ya tawo nan.

Shiru Iya tayi ba tare da ta iya cewa komai ba, sai aikin jinjina kai kawai da take yi, domin kuwa ita zancen gaskiya ba wani sosai tayi farinciki da faruwar hakan ba, sabo da tasan babu tayyada za'ayi wannan abun ya tab'a yuwuwa a tsakanin su.
Hakanne ya sata bud'e baki cikin sanyi, tana mai fad'in.

"Amma me yasa bakayi tinanin abun da zai faru ba aduk lokacin da wannan abun ya bayyana?"

"Mene zai faru kuma a gaba Iyata, bayan ita da kanta ta furta kalmar.
Shin me yasa naga kamar ma bakiyi farinciki da jin labarin ba Iyata?"

Bir ya fad'a a sanyaye shima yana mai kallon Iyar Bayi.
Jin hakan da Iyar Bayi tayi ne ya sanyata gyara zamanta a wurin, kana ta bud'e baki cikin sany, tana mai fad'in.

"Ta yaya zanyi wani farinciki Jarumi, bayan kuma nasan hakan matsala ce a gare

Please Login or Register in order to submit comment