Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nuni da tray ɗin da yake ajiye a ƙasa kan capet.

Ba tare da tayi musu ba ta zauna akan lallausan capet ɗin daga gaban tray ɗin, domin ko ba ƙaramar yunwa take ji ba dama, saboda rabon ta da abinci tun jiya da safe.
Hakan yasa takai hannunta kan akushin da yake ajiye akan tray ɗin, tana mai janye murfin sa.
Yayinda ita kuma Gimbiya Salwa ta sauko ƙasa tana mai sa hannu ta buɗe flas ɗin ruwan shayin da yake ajiye.
Kana ta tsiyaya ruwan bunun shayin da yaji uban kayan ƙamshi yana faman tashin turiri a cikin wani ɗan ƙaramin kofi mai azabar kyau.
Tukun ta ajiye sa a gaban Gimbiya Tasmir tana mai mayar da murfin flas ɗin ta rufe sa.

A cikin akushin da Gimbiya Tasmir ta buɗe kuwa, farfesun kayan cikin rago ne da roman sa, da sukayi matuƙar jin kayan haɗi suna ta faman tashin ƙamshi da turiri.

Kofin shayin ta fara ɗauka tana mai kai sa kan jajayen laɓɓanta ta ɗan zuƙe sa.
Kana ta ajiye sa a gefe, tare da sanya hannunta a cikin akushin ta fara cin naman.

Ba laifi ta ɗan ci naman da yawa kafun ta ture sa gefe, shi kuwa shayin sai da ta shanye duka na cikin kofin ma.
Sannan ta miƙe tana mai kama hanyar bayin ta kai tsaye.

Ko minti ɗaya ba tayi a ciki ba sai gata nan ta dawo.
Direct ta doshi kan gadonta tana mai hayewa saman sa.
Kana ta tanƙwashe ƙafafuwanta a gaban mahaifin nata, tana mai miƙa hankali da nutsuwar ta gaba ɗaya zuwa gare shi, domin kuwa bata son tayi missing ɗin ko kalma ɗaya daga cikin kalmomin da suke a cikin labarin da zai bata.

Shi kuwa Sarki Barbaru a hankali ya lumshe idanuwansa, kana daga bisani ya buɗe su akan fuskar Ƴar tasa yana mai yin gyaran murya.
Tukun ya buɗe baki yana mai cewa.

"Tashin hankalin ya farane a safiyar wata laraba, shekaru talatin baya da suka shuɗe kenan."
Ya ƙarasa maganar da sake lumshe idanuwansa.
Yayinda ita kuma Gimbiya Tasmir ta sake mayar da hankalinta gaba ɗaya gare sa, tana mai jin wani irin yanayi na tsarga mata.

Shi kuwa Sarki Barbaru tirya-tiryan ya cigaba da bata tarihin abun da ya faru tun daga ranar farko, da Ƴammatan Bayin nan suka shigo fada a guje.

Sosai ta nutsu tana sauraron mahaifin nata.
Da farko ta firgita da jin farkon labarin, amma kuma da aka nutsa cikin sa sai ta fara jin yanayin ta na sauyawa, gaba ɗaya zuciyar ta na tsinkewa.

Yau rana ɗaya da ta taɓa jin wani abu mai kama da tausayi na lulluɓe ilahirin jiki da zuciyar ta.
Lokaci guda gaba ɗaya jikin ta yayi sanyi, yayinda idanuwanta da zuciyar ta kuma suka dinga hasasho mata fuskokin iyayen da aka ƙwacewa jarirai tamkar a gaban ta abun ya faru.

Da ƙarfi ta rumtse idanuwanta a lokacin da Sarki Barbaru yazo wurin haihuwar Bir a labarin sa.

Babu abun da take hangowa a cikin idanuwanta sai matar da ta haifi jinjiri a cikin jirgi aka kuma ƙwace mata shi ba tare da ta yanke masa ko cibi ba, domin kuwa babu abun da Sarki Barbaru ya ɓoye mata na daga cikin labarin.

Wani irin tausayin Bir taji ya lulluɓe gaba ɗaya rai da zuciyar ta.
Haƙiƙa shi ɗin abun tausayi ne, kenan kwata-kwata bai san mahaifiyar sa ba, asalima ko ɗumin jikin ta bai taɓa ji ba, kana kuma bazai taɓa sanin ta ba a rayuwarsa.
Ashe wannan dalilin ne ya sanya yace mata shima bai san ko suwaye iyayen sa ba, amma ya barta da aikin binciken su.

"Kai! Wannan wane irin rashin tausayi ne hakan."

Ta faɗi haka a cikin ranta, tana mai buɗe idanuwanta akan fuskar mahaifinta Sarki Barbaru da har yanzu yake cigaba da bata labarin.

Kallo ɗaya mutum zai mata ya fahimci ba ƙaramun sanyi jikin ta yayi ba, domin ko hatta da launin idanuwanta sai da suka sauya.
Babu abun da take faman gani face fuskar Bir alokacin da yake ƙoƙarin haɗa jikin sa da nata.

Lokaci ɗaya taji gaba ɗaya bugun zuciyar ta na sauyawa, yana mai komawa irin yadda yake a duk lokacin da suka kasance a wuri ɗaya da Bir.

Cigaba da kallon mahaifin nata tayi, tana mai jinjina girman rashin tausayin sa a zuciyar ta.

Haƙiƙa bata taɓa zaton rashin imanin mahaifin nata yakai har ya iya kashe jariri, bata taɓa tinanin zai iya raba uwa da ɗan taba a lokacin da ta haife sa sai yau.
Yau rana ɗaya itama data fara jin tausayin wani a ranta, ranar farko kenan da imani ya ɗarsu a zuciyar ta, domin kuwa bata taso taga ana tausayin ba a cikin ahalin ta ballantana har itama tayi.

"Jarumi! Jarumi!! Jarumi!!"

Ta mai-maita sunan har sau ukku a cikin ranta, saboda tino lokacin da ya faɗa mata sunan da tayi.
Ko kaɗan bata so ta fara da jin tausayin sa ba a cikin ranta.
Haƙiƙa Bawan ya kafa babban tarihi a duniyar Baƙar Masarauta, wanda bazai taɓa shafuwa ba har abadan abada.
Kana kuma ya shiga cikin tarihin rayuwarta.

Shi ne ya zamto mutum na farko da ya taɓa ɓata mata rai aduk faɗin duniya, shine ya zamto mutum na farko da ya fara sanya ƙwayoyin idanuwansa a cikin nata, har ya faɗa mata maganar da ransa ke so a duniya, kana kuma ya zamto mutum na farko da yasan ya ta zubar da ƙwalla aduniya, sannan kuma ya zamto mutum na farko da ta tsane sa sama da kowa da komai a duniya, gashi kuma yanzu ya zamto mutum na farko da ta fara jin tausayin sa a duniya.

Haƙiƙa yau ɗin ta yadda da cewar shi ɗin Jarumi ne tamkar yadda ya faɗa mata, kana kuma ta zubar da makaman yaƙin ta akan sa, domin ko tausayin sa da ya samu gurbi a cikin zuciyarta yanzu, bazai taɓa barin ta tayi masa irin abun da tayi masa ba abaya, sai dai kuma hakan bashi ne zai sa ta juri ko wane kalar raini daga wurin sa ba.
Haƙiƙa muddin ya cigaba da yimata abun da ya fara yanzu, to zatayi watsi da duk wani tausayinsa da ya samu gurbi acikin zuciyarta tayi masa hukunci dai-dai da laifin sa.
Kana kuma ko a yanzun tana jin bazata iya haƙura duka ba muddin bata samu amsar tambayar ta ba a wurin sa, wato dalilin da ya sanya take jin faɗuwar gaba a duk lokacin da sukayi kusanci da shi, domin kuwa abun ba ƙaramun damun ta yake yi ba, sai dai kuma a yanzu ta ƙudiri aniyar canza salon tambayar tasa, wato dai zata yi masa ta sanyi ne ba kamar da ba da take masa ta zafi.

"Ina fatan zuwa yanzu kin fahimci dalilin da ya sanya na hanaki hukuntasa ko, kana kuma zaki taimake ni wurin ririta rayuwar mu gaba ɗaya?"

Cewar Sarki Barbaru a lokacin da yakai ƙarshen labarin da yake bata, yana mai zuba idanuwansa akan fuskar ta.
Yayinda a zuciyar sa kuma yake fatan ta fahimci abun da yake nufi.

Ahankali Gimbiya Tasmir ta janye idanuwanta daga kan fuskar sa, tana mai ɗan juyar da kanta gefe.
Kana ta fesar da wata zazzafar iska daga cikin bakinta tana mai lumshe idanuwanta.

Yayinda har lokacin kuma take jin zuciyar ta na wani irin bugu da ƙarfi da ƙarfi.
Tukun daga busani ta buɗe idanuwan nata tana mai juyowa ɓarin da mahaifin nata yake.

Jinjina masa kai tayi idanuwanta akan sa.
Kana daga bisani ta buɗe baki cikin sanyin murya, tana mai cewa.

"Haƙiƙa na fahimci dalilinka Baba na, kuma na tabbatar da ba sone ya sanya ka hanani hukunta sa ba, asalima zan iya cewa babu wani mahaluƙi da kake ƙi aduk faɗin duniyar nan face shi, domin kuwa shine mutum na farko da ya fara sanya ka cikin ruɗu da firgici tin kan yazo duniya, shine mutumin da yake barazana da duniyar ka.
Kana kuma ya zamto mutumin da ya zame maka ƙarfen ƙafa, ta yadda har yafi ƙarfin ka ya kuma fi ƙarfin ikon Ubangiji Gargabilu.
Tabbas a yau na shaida baka da wani maƙiyi bayan shi a duniya, sannan kuma na gane babu wanda ka tsana sama da shi aduk duniya, saboda da kana son sa da tun farko ma bazaka taɓa kwatanta cewa zaka rabasa da mahaifiyar sa ba a lokacin da ta haife sa, domin kuwa gashi nan ni da kake so tun da nazo duniya baka taɓa barin nayi nisa da ku ba.
Dan haka na fahimce ka fiye da yadda kake tinani Baba na, kana kuma nayi maka alƙawarin tayaka ririta rayuwarsa daga rana irin ta yau, domin ko yanzu na fahimci rayuwar sa itace tawa rayuwar nima, wato gaba ɗayan sa dai shine duniya ta!"

Ta ƙarasa maganar a hankali, tana mai jin wani irin abu na cigaba da tsarga ilahirin ƙashi da tsokar ta yana kwanciya a cikin jinin ta.

Shi kuwa Sarki Barbaru wata irin ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ya sauke, saboda jin da yayi ƴar tasa ta fahimce sa, domin kuwa a cikin duka magan-ganun data faɗa babu ɗaya da yake ba dai-dai ba, wato dai bashi da wani maƙiyi sama da Bir aduk faɗin duniya, saboda shi kaɗai ne ya gagare sa a duniya.

Cikin tsantsar farin cikin da ya shiga na ganin ƴar tasa ta fahince sa ya miƙa hannuwansa duka biyu, yana mai janyo ta cikin jikin sa, kana ya rungume ta tsam, yana mai shafa lallausar sumar kanta.
Yayinda ita kuma ta lumshe idanuwanta, tana mai sauke wasu irin tagwayen ajiyar zuciya.


*ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI GIDAN GWAMNA.*

Sosai farinciki ya lulluɓe Billy mara misaltuwa a lokacin da Dad ɗin ta yayi mata bayanin yadda sukayi da su mai martaba.
Hakanne yasa tana komawa ɗakinta ta janyo wayarta tana mai fara dokawa Yarima Asad kira, sai dai kuma har tayi ringing ta gama bai ɗauka ba.
Ko kaɗan bata damu da rashin ɗaga wayarta ta da baiyi ba, domin kuwa tuni ta saba da hakan, wato sai tayi masa kira har kusan sau ukku tukun yake ɗagawa ako da yaushe dama.

Hakanne yasa ta sake doka masa wani kiran, amma still har ta gama ringing bai ɗauka ba.

Bata haƙura ba ta ƙarayi masa wani kiran, wato har sau ukku alokaci guda duk baya ɗagawa, hakanne yasa ta barinsa, tana mai komawa ta kira Zee, domin ko a tinanin ta ko baya kusa da wayar ne shiyasa.

Zee na ɗaukar wayar ta fara karanto mata abun da ke faruwa.
Sosai kuwa ta taya ta murna har tana cewa zata zo har gidan tayi mata barka a fili.

Haka dai tai-ta kiran ƙawayenta da suka san Yarima Asad tana basu labari.
Tukun a ƙarshe bayan ta gama waya da ƙawayen nata ta sake dokawa Yarima Asad kira, amma still bai ɗauka ba, bata haƙura ba ta sake yi masa wani kiran.
Har ta fara shiga sai kuma kawai taji ta yanke.
Hakan ne ya sanyata ɗago wayar, tana mai kawo ta saitin idanuwanta cike da mamaki.

Cikn sanyi ta sake doka masa wani kiran, amma sai taji matar nan ta mtn tana shaida mata cewar layin a rufe yake.

Wanda hakan kuma yayi bala'in gigita ta lokaci guda.
Domin kuwa sai yanzu ta fahimci dama can yaga kiran nata ƙin ɗagawa yayi.

"Na shiga ukku ni Billy, Allah dai yasa ba haushi Prince yaji ba."

Ta faɗi haka a fili, tana mai nemo ɗayar number tasa ta doka masa kira da ita.
Still switch off itama aka ce mata.
Aiko take ta duro daga kan gadon da take, tana mai ɗora hannuwanta duka biyu aka, tukun ta fara zarya acikin ɗakin hankalinta a tsantsar tashe.

Haka tai ta gwada kiran wayar sa amma tana jin ta akashe har dare ya tsala sosai, tukun ta haƙura tana mai komawa ta kwanta akan gadon ta ba tare da ta iya ko cire kayan jikinta ta sanya na bacci ba, tsabar tashin hankalin da take a ciki.

Tsoron ta ɗaya kar ace Yarima Asad yayi fushi da ita ne saboda zuwan iyayenta gidan su.
Haka tai ta juyi akan gadon har zuwa lokacin da bacci ɓarawo yayi awon gaba da ita ba tare da ta sani ba.

Yau kuwa tunda safe tana tashi ta fara shiryawa da niyyar taje har wurin Asad ta same sa ayita ta ƙare.
Ko break fast bata tsaya yiba ta fara shiryawa.

Sosai tayi mugun kyau cikin azababbiyar kwalliyar da tayi da wasu irin arnan English waer.
Dole ne duk wanda ya kalle ta ya sake kallon ta, saboda yadda kayan sukayi matuƙar bayyana surar jikin ta.
Tukun ta ɗauki ɗaya daga cikin key ɗin motar ta tana mai haɗawa da hand bag ɗin ta, wacce ta kasance mahaɗin hill shoe ɗin da yake sanye a ƙafar ta.

Sosai taji daɗin rashin ganin iyayen nata da batayi ba a fallo, domin kuwa ta sani muddin suka ganta sai Dady'n ta ya tambaye ta inda zataje, kana kuma a ƙarshe yace dole sai ta tafi da masu tsaron ta, wanda ita kuma ko kaɗan bazata so faruwar hakan ba, saboda yadda Yarima Asad ya tsani ganin ta da mutanen, domin kuwa yace babu abun da suke yi sai ƙarin hayani da aikin sanyawa mutane ido, wannan dalilinne ya sanya aduk lokacin da zataje wurin sa take tafiyar ta ita kaɗai ba tare da ta gayyace su ba.

Da uwar wuta ta fafari motarta ta tana mai ɗaukar hanyar da zata kaita Asadullah Palace direct, domin kuwa acan ne take tsammanin zata haɗu da Yarima Asad cikin sauƙi, duk da dai ta sani ba lallai bane ace ya shigo yanzu da safe, sai dai kuma a yadda take jin kanta bazata taɓa iya haƙura ta zauna a cikin gida ba har zuwa yamma, gwanda kawai taje tai ta zaman jiran sa har zuwa lokacin da zai zo.


A ɓangaren Yarima Asad kuwa bai tsaya ako ina ba tunda ya hau kan kwalta yana zuba uban gudu, har sai da ya isa cikin Jahar Kagul gaban ƙatoton get ɗin Masarautar Fulɗe.
Tukun ya taka birki da ƙarfi daga nesa da get ɗin, yana mai rumtse idanuwansa, sabo da yadda yaji gaban sa yayi wata irin mahaukaciyar faɗuwa, kana kuma sai alokacin ya farga da wurin da ya kawo kansa, wanda ko a mafarki bai taɓa tinanin zai sake zuwan sa ba a jiya da suka shigo sa, impact mai bai zata zai iya gane hanyar ba, sai kuma gashi harya iso ma.

Lokaci ɗaya kuma ya fara girgiza kansa, yana mai ɗaukar hannunsa ya dafe saitin zuciyar sa da yaji tana wani irin mahaukacin bugu da shi.

Cigaba da girgiza kansa yayi, kana ya buɗe idanuwansa yana mai kallon get ɗin masarautar da su.

"Shin me nake shirin aikatawa ne haka ni Asad?
Me yake damuna ne? Ina hankali na ya tafi dana kwaso jiki na tawo wannan ƙauyen, to yanzu idan na shiga ciki nace musu nazo wurin wa ma?"

Ya faɗa a bayyane, yana mai cigaba da girgiza kansa, yayinda har lokacin kuma zuciyar sa ke cigaba da bugu da ƙarfi, tamkar zata hudo ƙirjinsa ta futo waje, su kuwa idanuwansa babu ahun da suke hango masa face kyakkyawar fuskar Gimbiya Haddiyal.

"Kace kazo wurin Yarinyar jiya ne mana, ko kuwa da akwai wani abun da ya kawo ka ne bayan hakan."

Zuciyar sa ta basa amsar tambayar sa.

Da sauri ya girgiza kansa, yana mai faɗin.

"Inaa! Kamar ni Asad nace nazo wurin wata yarinya, yarinyar ma ƴar ƙauye bagidajiya, to nazo wurin ta nayi mata me ma tukun?"

Ya sake faɗe da ƙarfi, yana mai jujjuya kansa, gaba ɗayan sa ya rasa sukuni, yayinda har lokacin kuma idanuwansa suke cigaba da mararin sake ganin ta a zahiri.

"Ka faɗa mata tinanin ta yaƙi yabar zuciyar ka ta samu salama, tun bayan haɗuwar ku ta jiya mana."

Zuciyar sa ta sake basa amsa.

"Allah ya kiyaye, kamar ni Asad nace ina tinanin wata.
Subahanallah, Insha Allahu hakan bazata taba faruwa ba, wannan baƙar ranar bazata taɓa zuwa ba, domin ko ni Asad nafi ƙarfin na buɗe baki na sanarwa wata ƴa mace cewar ina tinanin ta.
Kai ba ayita bama wallahi."

Ya faɗi haka da ƙarfi, yana mai dukan sitiyarin motar, tare da jin haushin kansa da kansa.
Tukun daga bisani yayi saurin lailaya kan motar, yana mai shirin juyawa, domin ya koma inda ya futo.
Yayinda har lokacin kuma zuciyar sa bata fasa bugun da take da tsantsar ƙarfi ba.

"Why? Why zuciya zakiyi mun haka?
Me yasa? Me yasa ni Asad zan damu da wata ƴa mace? Me yasa me yasa hakan zata faru dani?
Shin anya ma mutum ce ko ita?"

Ya faɗa da ƙarfi, yana mai ƙarasa yin kwana a wurin, kana ya rumtse idanuwansa da ƙarfi, yana mai ganin yadda fasalin kyakkyawar fuskarta take a cikin su, ga kuma mafarkan da yayi jiya akan ta da suke ta dawo masa cikin ƙwaƙwalwarsa.
Hakan yasa ya buɗe idanuwan nasa da sauri yana mai fara tafiya.
Sai dai kuma ko nisa baiyi ba ya take birki da matuƙar ƙarfi, ta yadda har sai da ya futar da wani irin sauti jikake ƙiii!
Yayinda zuciyar sa kuma ta cigaba da bugu da ƙarfi, kana ya sake mayar da idanuwansa yana mai rumtse su da ƙarfi, saboda tozalin da ƙwayoyin idanuwan nasa sukayi masa da ɗirkeken jan dokin daya ƙaraso gaban sa.
Yayinda saman dokin kuma yaga H................✍



_WALLAHI RASHIN COMMENTS DA SHARHI ZAI IYA SAWA NA JINGINE LABARIN NAN, KO KUMA YA KOMA NA KUDI, DAN HAKA ZABI YA RAGE GAREKU_ 😠


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*05*



Habu zaune akansa, yana mai jifan sa da murmushin farin cikin sake ganin sa da yayi.
Sanye yake da kayan sport a jikin sa, yayinda hannun sa ɗaya yake riƙe da sanda, ɗayan kuma riƙe da linzamin dokin sa.

Dawowar sa kenan daga wurin wasan polo'n da yake zuwa, tun daga nesa da ya hango motar a lokacin da take kallon get d'in gidan nasu, ya gane ko waye mammalakin ta, saboda number dake d'auke jikin ta da ya gani, sai dai kuma bai tabbatar da shi d'in bane ba har sai lokacin da ya kusa k'arawo wurin da yake, a lokacin shima kuma Yarima Asad ya juyo da motar sa domin ya tafi, kasancewar glass d'in gaban motar mai haske ne ba kamar sauran na bayan ba da suke d'auke da bak'in tintek a jikin su.

Durowa yayi daga kan dokin nasa yana mai nufo bakin motar Yarima Asad, fuskarsa d'auke da tsantsar murmushi.

Shi kuwa Yarima Asad tun da ya rumtse idanuwansa bai iya bud'e su ba har yanzu, ko kad'an ko kusa baiyi farin ciki da ganin Habu ba a halin yanzu, domin kuwa kwata-kwata bai tanadi kalaman da zai fad'a masa ba idan ya tambayesa dalilin dawowar tasa, wanda kuma yasan dole ne hakan ta kasance.
Hakan yasa ya sake rumtse idanuwansa, yana mai tinanin abun da zai ce masa idan ya tambaye sa dalilin dawowar tasa.

Bai iya bud'e idanuwan nasa ba har sai da yaji muryar Habu ta daki dodon kunnensa, yana mai fad'in.

"'Dan uwa ashe kai d'in ne da gaske."

Ya fad'a cikin tsantsar farin ciki, yana mai jingina da jikin k'ofar motar.

Ahankali Yarima Asad ya fara bud'e idanuwansa da yake jinsu sun masa jingim, ji yake inama ace idan ya bud'e idanuwan zai gansa kwance akan gadon sa, wato ace duk a mafarki ne wannan abun yake faruwa ba a zahiri ba, sai dai kuma yana gama bud'e idanuwan nasa ya sake yin arba da fuskar Habu tsaye a gaban sa, gaba d'aya bakin sa ya gaza rufuwa.

K'ak'alo murmushin yak'e shima yayi, yana mai jin-jinawa Habu kai, ba tare da ya iya cewa komai ba.

"To amma mai ya tsayar da kai anan ne, naga alamun ma kamar shirin juyawa kake yi, alhalin kuma banga alamun ka shiga ciki ba."
Cewar Habu yana mai bud'e murfin motar ya d'ora hab'ar sa da hannuwansa a saman sa.

Shi kuwa Yarima Asad hannunsa na hagu ya d'aga sama yana mai dafe k'eyar sa da shi.
Kana ya bud'e baki yana mai cewa.

"Eh da yake ma har zan huce ne, dama..dama."

Ya fad'i maganar acan k'asan mak'oshi, ta yadda Habun ma sai da k'yar ya jiyo ta, yana mai tsayawa ba tare da yakai k'arshen ta ba, saboda rasa abun cewa da yayi.

"Kamar ya hucewa zakayi, sannan kuma dama me?
Kaga kawai malam karya kan mota mu shiga daga ciki, ma k'arasa zance mu acan."

Habu ya fad'a yana mai shigewa cikin motar yayi zaman sa a gefen Yarima Asad, kana ya rufo murfin motar ba tare da ya tsaya bi takan dokin sa da yake a tsaye ba har yanzu.
Sai a yanzu ne ya tuna da magan-ganun Al'amin na jiya, da yake fad'in sunga iri ai su ba abun mamaki bane gobe ma yaga sun dawo.

Lokaci d'aya ya saki murmushi, yana mai jinjina kansa, duk da dai bai tabbatar da abun da yake tinani ba akan zuwan Yarima Asad d'in.

Shi kuwa Yarima Asad gaba d'aya suman zaune yayi a wurin, ta yadda har ya kasa yin gaba ko baya da motar, ji yake tamkar Habu ya sanya igiyoyi ya d'aure gaba d'aya ilahirin jikinsa da su.

Sosai zuciyar sa take cigaba da bugun tara-tara, yayinda har yanzu k'wak'walwarsa ta gaza basa amsar tambayar da zai bawa Habu idan ya tambaye sa dalilin zuwan nasa.

"Muje ko Aboki."

Yaji muryar Habu ta sake dukan dodon kunnen sa.

Hakan yasa ya d'an cije leb'en sa na k'asa a hankali, kana ya fara juya motar, domin suyi cikin tamkar yadda Habu ya buk'ata ba tare da yace komai ba.

Suna shiga ciki Habu yacewa Yarima Asad ya d'an dakata anan, kana ya bud'e glass d'in motar yana mai kiran d'aya daga cikin hadiman da ya hanga tsaye abakin get d'in.
Sannan ya umarce sa da yaje ya shigo masa da dokin sa a waje, kana suka cigaba da tafiya suna masu nufar part d'in su Habu kai tsaye.

Acikin d'an madai-daicin falon Habu da ya gaji da had'uwa suka sauka.

"Bismillah ga wuri ka zauna mana ko."
Habu ya fad'a yana mai yiwa Yarima Asad nuni da had'ad'd'iyar kujerar k'arfen da take a bayan sa.

Ba tare da yace komai ba, sai d'an murmushin yak'e da ya sakarwa Habu ya zauna akan kujerar.

Shi kuwa Habu juyawa yayi zuwa wurin da d'an k'aramin fridge d'in sa yake, yana mai bud'e sa ya zaro ruwan jarka a cikin sa, tare da d'an k'aramin kofi na glass
Kana ya dawo gaban Asad, yana mai bud'e murfin jarkar ya tsiyaya masa ruwan a cikin cup d'in.
Tukun ya d'ago yana mai mik'a masa shi, tare da fad'in.

"Bismillah Aboki ga ruwa kafara sha ko."

Still dai murmushin yak'e ya k'ara jifan Habu da shi, yana mai mik'a hannu ya karb'i ruwan ba tare da yace komai ba, domin kuwa bai san abun da zaice d'in ba.

Shi kuwa Habu mik'ewa yayi yana mai tafiya ya zauna akan kujerar da take facing d'in wacce Yarima Aaad yake zaune akai.
Har lokacin ya gaza rufe bakinsa, saboda murnar sake ganin Yarima Asad da yayi a cikin gidan nasu.

Shiko Yarima Asad kafa kofin ruwan nan yayi akan lab'b'an sa yana mai fara shan sa.

Bashi ya iya janye kofin daga kan lips d'in nasa ba har sai da ya tabbatar da ya shanye sa tas.
Tukun ya janye sa yana mai d'an lumshe idanuwansa, tare da sakin wasu irin tagwayen ajiyar zuciya, tamkar wanda yaci kuka ya more.

"Ina ka baro mun Abokina ne da baku tawo tare ba.?"

Muryar Habu ta daki dodon kunnuwansa yana mai fad'in haka, ba tare da yayi zaton jin hakan daga bakin sa ba.
Hakanne yasa sa bud'e idanuwansa da suke a lumshe, yana mai zubasu akan fuskar Habu.
Kana ya d'an fesar da wata sassanyar iska daga cikin bakinsa, tukun daga bisani ya d'an d'aga lab'b'ansa bayan ya sake lumshe idanuwansa, yana mai fad'in.

"Haka yace bazai zo ba ne, da yake kasan wani lokacin shi d'in ba wani kirki ya cika ba."

Ya samu kansa da fad'in haka, yana mai d'an juyar da kai gefe.

"Kuma yasan nan d'in zaka tawo ne?"
Cewar Habu yana kallon Yarima Asad.

"Tabbas ko."

Ya fad'i haka a tak'aice, yana mai fatan kar Allah yasa ya k'ara yo masa wata tambayar.

"Lallai ne, aikuwa idan ka koma ka fad'a masa cewar nima duk randa nazo karya yi zaton wurin sa nazo, dan haka karma ya fara cewa zai kulani."

Cewar Habu yana mai mik'ewa daga kan kujerar da yake zaune akai.
Yayinda shi kuma Yarima Asad ya saki murmushi, ba tare da yace kamai

Please Login or Register in order to submit comment