Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baya zamu shiga kenan?"

Suka doko masa tambaya suna masu kallonsa cike da mamaki.

Shi kuwa Sheikh Ahmad da yaji labarin komai na yadda sukeyi a wurin Bir, baiji wani mamakiba kwata-kwata.
Yayinda shi kuma mutumin ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Hakan shine d'a'a, kuma ko d'an Sarkine a haka ake zuwa gabansa ballantana kuma ku da kukazo wurin Sarkin gaba d'aya."

Ya k'arasa maganar yana mai juyawa ya fara tafiya, domin kuwa shi duk a tinaninsa zasuyi yadda ya fad'a musun, amma sai kuma yaga sunk'i suyi yadda yayin suna masu biyosa a baya, gaba d'aya cikinsu babu wanda ya juya bayansa, wato ya zamto dai suna facing d'in kujerar Sarki Barbaru da take kallon k'ofar Fada.

Hakan kuwa shi yasanya wani badakare da yake tsaye a gefen Sarki barbaru ya daka musu wata irin azababbiyar tsawa, yana mai fad'in.

"Su waye ku da zaku tunkaro gaban Shugaba a haka?"

Yayinda idanuwan Sarki Barbaru kuma suka kad'a suka jajajir saboda b'acin rai.

Hakan da suka jine ya sanyasu juya bayan suma, saboda su dai maslaha sukeso a yi ba fitina ba.

Suna k'arasawa gab dasu sukaga mutumin nan ya juya gaba, hakan yasa suma d'in suka juya, amma kuma sai sukaga ya zube a k'asa wanwar a gaban Sarki Barbaru.
To anan ne fa su kuma sukai k'edagege sai bin mutane da suke da ido cikin matsanancin mamaki.
Wanda hakan ne kuma ya k'ara harzuk'a zuciyoyin Dakarun wurin, harna da shi kansa Sarki Barbaru.

Cikin tsananin zafin nama tare da azababben b'acin rai wani badakare yayo kansu bayan ya zate tatobinsa yana mai fad'in.

"Hak'ik'a mutuwa ta cancanta ga duk wani mara d'a'a ga Shugaba!"

"Dakata!!!"

Sarki Barbaru ya fad'a yana mai d'aga masa hannu.
Hakanne ya sanyasa komawa gefe gaba d'ayansu suna masu sakin huci.
Yayinda su kuma su Sheikh Ahmad sukayi shiru suna kallonsu, kwata-kwata babu alamun tsoro a tattare dasu.

Hakan kuwa da Sarki Barbaru ya ganine ya sanya yaji ransa ya k'ara kai k'ololuwa wurin b'aci, gaba d'aya idanuwansa suka rikid'e sukai jajajir.
Amma a hakan ya bud'e baki cikin muryarsa mai futar da amon sauti yana mai fad'in.

"Su waye ku? Daga ina kuke? Kuma me kukazo yi wurinmu?"

Ya k'arasa maganar yana mai binsu da jajayen idanuwansa, tare da kallon suturar dake sanye a jikinsu.

Cikin nutsuwa da dakiya, mana kuma babu alamun tsoro kwata-kwata a tare da Sheikh Ahamd ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Mu bak'inku ne, da muka tawo muki da guzurin alkhairi wanda zai zamto tsira gareku ya Shugaba."

"Ku zauna."

Sarki Barbaru ya fad'a a tak'aice, yana mai kafe Sheikh Ahmad da idanuwansa, domin kuwa idan ba gizo idanunsa suke masa ba shi dai kamannin Bir sak yake gani a tare da shi.

Zama gaba d'ayansu sukayin tamkar yadda yace suyi.
Tukun ya sake bud'e baki har lokacin idanuwansa suna akan Sheikh Ahmad, yana mai fad'in.

"Meke tafe daku ne muna sauraronku?"

Hakan da sukaji ne yasa sukayi gyaran murya, kana Sheikh Aliyu ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Kamar yadda d'an uwanmu ya fad'a muku tun farko, munzo muku da alkhairine mai girma, wanda bakomai bane shi d'in kuma face Addinin Allah, bima'ana Addinin gaskiy...."

"Kai yimana shiru! Dama har akwai wani Addinin gaskiyane aduniya bayan namu addinin da muka taso cikinsa?"

Sarki Barbaru ya katsesa da fad'in haka a wani irin zafafe, kana kuma cikin bala'ya'y'yar tsawar data firgita duk wani mutumin cikin wurin.

Amma amai-makon su tsorata sunemi hanyar guduwa, sai d'aya daga cikinsu ma da aka k'ara samu yace.

"Babu wani Addinin da yake gaba da musulunci aduniya, addinin Allah shi kad'aine addinin tsira, kuma muna neman alfarma a wurinku ta 'yan awanni domin mufahimtar daku ta yadda zaku gane, idan kuma har baku gane ba mun yadda kuyi man..."

"Har abada bazan tab'a cin amanar addinin Iyaye da Kakanni na ba, bazan tab'a barin Ubangiji Gargabilu ba na kama wani Ubangiji."

Cewar Sarki Barbaru a wani irin zafafe yana mai mik'ewa tsaye.
Kana ya d'aga k'afarsa cikin zafin rai yana mai hanb'are Sheikh Aliyu da yake a saitinsa da ita.
Tukun ya sake bud'e baki cikin muguwar tsawar data firgita har dakarun wurin yana mai fad'in.

"Ku ji wani zancen banza zancen hofi a wurin mutanan nan, dama har akwai wani addine ne bayan namu, to kusani ni ba zantab'a cin amanar Ubangiji Gargabilu ba, bazan tab'a barinsa ba na kama wani, dan haka hukuncin kisa a gaban jama'ane ya tabbata akan ku marasa kunya! Ku kama mun su ku huce dasu wurin fille kai, duk wanda yayi gardama kuma a kashe sa tun a hanya, sannan kuma ku taro mun gaba d'aya jama'ar gari, hak'ik'a yau zakusan ko wane wuri kuka shigo, zan tabbatar muku da BAK'AR MASARAUTA ba dai dai take da sauran ba ko daga sunan ma!!"

Ya fad'a a wani irin zafafe kana da tsananin k'arfi, ransa a bala'in b'ace.

Su kuwa su Sheikh Ahmad jin abunda ya fad'ane ya sanyasu mik'ewa da tsananin sauri.
Amma sai dai tun kafin suyi wani motsin kirki Dakarun nan suka funcikesu suna masu fara jansu.

"Addinin Allah d'ayane aduniya, wato musulunci, kuma duk wanda baya acikinsa harya koma ga mahallici, hak'ik'a tab'ewa da hasara sun tabbata a garesa, sannan kuma wuta itace madawwamarsa, dan haka baku isa ku mana komai ba da izinin Allah."

Cewar Sheikh Ahmad yana mai kallon idanun Sarki Barbaru.
Wanda hakan kuma ya sanyasa ganin tamkar yaron da yake nema ne ya dawo.

Yayinda su kuma Dakarun nan suke aikin funcikarsu da tsananin zafi, ransu a tsanain b'ace.
Shi kuwa Sarki Barbaru da zuciyarsa ta raya masa cewar Bir ne ya dawo, cikin tsananin zafin rai ya biyo bayansu, yana mai fad'in.

"Ni da hannuna zan maka kisan gilla kisan hullak'anci kafin ka rusa mun rayuwata, ka shafar mun da kafaffen tarihina."

Haka sukaita jansu jama'a duk wanda ya gani sai ya biyo baya cikin tasnanin firgici.
Su kuwa sun k'i zaro makamansu ne saboda sanin da sukayi idan har banisa sukayi sosai ba 'yan uwansu bazasu jiyo abunda ke faruwa da wuri ba.
Hakanne ya sanya sai da suka bari an kusa zuwa wurin kisan, wanda kuma yake da kusanci sosai da wurin da su Bir suka b'uya, tukun cikin dabara ba tare da sun bari dakarun nan sun lura da abunda suke ba kowanne su ya d'ora hannunsa akan cikinsa.
Kafin daga bisani kuma suka saki wata irin gigitacciyar k'ara suna masu fad'in.
"Allahu akbar!!!"

Tukun suka funciko takubban jikinsu suna masu cakawa gaba d'aya dakarun da suke rik'e dasu tare da funcikesu ba tare da sun bari sun luraba.

Wasu irin gigitattun k'ara suka saki kuwa suna amsi zubewa a k'asa wanwar ransu na fucewa.
Hakan da Sarki Barbaru ya ganine kuwa ya sanya hankalinsa yayi bala'in tashi.

Wata irin gigitaccuyar k'ara ya buga data sanya gaba d'aya cikin Masarautar gabanta da bayanta amsawa.
Wanda hakan kuma ya sanya gaba ki d'aya dakarunsa suka fara b'ullowa cikin wurin da tsananin gudu.
Haka suma a fannin su Mai Martaba a guje suka b'ullo wurin.
Wanda b'ullowar tasu kuma tayi dai-dai da d'ago kan da Sarki Barbaru, take kuwa k'wayoyin idanuwansu suka sark'e cikin na juna.

Cikin tsantsar kid'ima, firgici, rud'u tare da tashin hankali Sarki Barbaru yake kallon Bir daya zare kibiya tare da kwari da gwafa a jikinsa.

Wato kenan dai maganar Boka mai wutar kasko ta tabbata yau.
Ya raya haka acikin ransa hankalin sa a bala'in tashe.
Kafin daga bisani kuma yayi wani irin kukan kura yana mai yin cikinsu da yaga azababen fad'a ya kaure atsakanin Jama'ar Masarautar Wasai tare da Dakarunsa.

Fad'a suke mai tsananin figitarwa da tashin hankali, ta yadda har duk al'ummar da suke acikin Masarautar suka farga da abunda yaje faruwa yanzu.
Tuni Bayi mata harma da maza matsorata suka nemi wuri suka b'uya cikin matsanancin tashin hankali.

A b'angaren Iya itama d'akinta ta shige tana mai rufosa jikinta na wata irin bala'ya'y'yar kyarma.

Yayinda acan cikin gidan Sarki Barbaru wurin iyalansa kuma Gimbiya Salwa da Haiwa suka hana gaba d'aya yaran futa, suka kulle gidan suna masu sakin azababben kuka cikin marsanancin firgici da tashin hankali, tare da curewa wuri d'aya.
Kafin daga bisani kuma Yarima Sauman ya tashi a wani irin figice yana mai zare mugayen makamansa.

Hakan da Iyayensa suka ganine ya sanyasu rik'esa suna masu hanasa futa, amma ko saurarensu baiyi ba ya funcike jikinsa yana mai fucewa ba tare daya tsaya ko sauraransu ba ya doshi filin da ake zabga azababben yak'in.

Yak'i suke cikin bajinta k'warewa tare da taimakon Allah, domin kuwa duk da kasancewar dakarun cikin Bak'ar Masarauta sun nininkasu a yawa, amma sune akafi zubarwa a k'asa.

Ganin hakan da Sarki Barbaru yayine kuma ya sanya hankalinsa ya sake bala'in tashi.
Ai kuwa cikin wani irin zafin nama ya dunk'ule tafin hannunsa yana mai yin wasu irin surutai da azabar k'arfi.
Kana daga bisani ya hud'e ido yana mai watsa wasu abubuwa da suka bayyana a hannunsa zuwa cikin mutanen masarautar wasai.

Wata irin jar wutace mai matuk'ar ci ta bayyana tana mai yin kan iya jama'ar cikin masarautar wasai a guje, amma sai dai kuma cikin ikon Allah tana dosarsu sai ta koma ta daki jikin dakarun BAK'AR MASARAUTA.
Hakan kuwa shine ya sanya cikin k'ank'anin lokaci kusa rabinsu da kwatansu suka zube a wurin wanwar babu alamun rai tattare dasu.
Dalilin kuwa da ya k'ara d'imauta Sarki Barbaru kenan.

Ai kuwa cikin zafin naman da yafi duk na farko yayi kan Mai Martaba Sarkin Abdallah da yaga tamkar yafi duk sauran k'warewa a wurin yak'in.
Yayinda a wannan lokacinne kuma shima Yarima Sauman yayi kan Sheikh Ahmad.

Hakan yasa azababben fad'a ya kaceme a tsakaninsu, sai dai kuma Bir na lura da hakan yaja kibiyarsa yana mai saita bayan Yarima Sauman ya sakar masa ita.
Take kuwa ya zube a wurin wanwar ba tare da ya k'ara ko shurawaba, wanda hakan kuma ya faru akan idanun Sarki Barbaru.
Wata irin gigitaccuayr k'ara kuwa ya saki cikin masifar tashin hankali, yana mai hankad'e Sarki Abdallah da azabar k'arfi.

Take kuwa yayi baya taga-taga, tukun ya kifa rigin-gine a k'asa.
Hakan da Sarki Barbaru ya ganine ya sanyasa d'ago takobinsa yana mai saita k'awon zuciyar Sarki Abdallah ya..............✍



*ZAKUJI HAR YANZU INA FAD'IN SUNAN BIR DA GIMBIYA TASMIR A HAKA BADA SABON SUNAYENSU NA MUSULUNCIBA, SO NAYI HAKANNE SABO DA KAR WASU SU DINGA RIKICEWA SHIYASA, BUT YANZU BA HAKANE SUNAYENSU BA KOWA YA SANI.*


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*30*



Yayi k'asa da ita yana shirin caka masa ita. Bir daya lura da abunda yake faruwa yayi wani irin juyi yana mai sakin k'ara tare da sakarwa Sarki Barbaru kibiya a gadon baya.
Luuuuu yayi baya kuwa yana mai kifawa a k'asa cikin tsananin azaba da futar hayyaci.
Yayinda Bir kuma ya k'araso zuwa kansa, ya zamto suna kallon junansu.

Wani irin kallo Sarki Barbaru yake bin Bir dashi cikin tsananin azaba da futar hayyaci.
Kafin daga bisani kuma ya fara bud'e baki yana son yayi magana, amma gaba d'aya ya kasa.
Wanda hakan da Bir ya ganine kuma ya sanyasa d'ago takobinsa yana mai buga masa ita a saitin k'awon zuciyarsa!
Wani irin dogon numashi yaja kuwa, daga nan kuma shikenan rai yayi halinsa, idanuwansa duka suka kakkafe.

Ganin hakan da sauran Dakarun sukayine, ya sanyasu zubar da makamansu cikin tsananin tashin hankaki da rud'u, suna masu neman wurin guduwa, wanda hakan kuma da Jama'ar Masarautar Wasai suka ganine ya sanyasu suma dakatawa suna masu fara bincikar junansu, domin suga ko akwai wanda suka rasa.


***
A k'asar hausa kuwa cikin Masarautar Fuld'e, cike filin shad'in yake dank'am da al'umma, kasancewar yaune ranar da Yarima Asad zai daki Jauron Yamma.

Sanye yake da riga da wando na wani tattausan yadi a jikinsa.
Yayinda Al'amin dasu Babban Yaya kuma suke sanye da manyan kaya harda rawani akawunansu.

A b'angarensu Lamid'on yamma suma duk zaune suke da tawagarsu, kallo d'aya mutum zai musu ya gane babu nutsuwa kwata-kwata a tattare dasu, domin kuwa zuciyoyinsu cike suke da fargaba, sab'anin wancan lokacin da sukazo cikin matsanancin farinciki.

A haka har lokacin da za'a fara yayi alk'alin gasa ya nemi su futo.

Rai a tsananin b'ace babu alamun annuri ko kusa a fuskarsa ya futo, daga shi sai gajeran wando a jikinsa.
Sosai shima fatarsa take a kwance, duk da kasancewarta mai duhu, saboda shima d'in dai bai sanwata wahalaba, sai dai kuma ko kad'an baisa a ransa bulalun Asad zasu sanyasa kuka ba.

Yayinda shi kuma Yarima Asad ya taso ya futo hannuwansa rik'e da wasu irin zura-zuran bulalai da suke d'igar ruwa, kai kana ganinsu basai an fad'a maka ba zaka san ba k'aramun tsimi suka sha ba.

Tafe yake yana motsa bakinsa da alamun adduo'i dai yakeyi harya k'arasa kan dakalin.

Kafe junansu sukayi da idanuwa, kowa yana mai jin haushin d'an uwansa a cikin ransa, tare da fatan ya zamto shine mai nasara.
A haka har alk'alin gasa ya busa.
Hakan yasa Jauron Yamma ya d'age kansa sama yana mai kallon giza-gizai, irin ya daka d'innan ya gama.
Shi kuwa Yarima Asad gyara rik'on bulalunsa yayi.
Kana ya d'agasu da matuk'ar k'arfi yana mai fad'in.
"Bismillah."
Tukun ya saukewa Jauron Yamma ita a gadon baya.
Amma sai dai kuma ko motsi baiyiba daga yadda yake ballantana kuma suyi tinanin bulalar ta shigesa.
Hakan yasa Yarima Asad ya k'ara zage k'arfinsa, yana mai sake shimfid'a masa wata a tsakiyar bayansa.
Kana kuma ba tare daya bari ya huta ba ya k'ara kai masa ta hud'u.
A kuma lokacinne Jauron Yamma ya rumtse idanuwansa yana mai bud'esu, kana jikinsa ya fara 'yar karkarwa, gumi na tsatstsafo masa, alamun dai na bulalun sun fara shigarsa sosai kenan.

Shi kuwa Yarima Asad cikin tsananin dagiya ya sake d'aga bulalar yana mai shimfid'a masa ta takwas a tsakiyar bayansa ta zagayo har kan cikinsa.

Cikin tsananin gigita tare da azabar da yaji ta ratsasa ya sauke kansa da yake d'age asama k'asa, yana mai zuba firgitattun idanuwansa da suka kad'a sukai jajajir akan fuskar Yarima Asad.

Shi kuwa Yarima Asad tina irin muguntar da yayi masa a ranar da yake dukansa da yayine, ya sanyasa yaji wani irin mugun k'arfi ya k'ara zuwar masa, hakanne yasa sa yin matuk'ar dagewa yana mai sauke masa ta goma sha ukku a kafad'arsa ta b'ullo har kan cikinsa.

"Yihhhhhhhhshhhh!!!"

Jauron Yamma ya saki wani irin sauti mai matuk'ar k'ara, jikinsa na d'aukar azababbiyar karkarwa, wanda hakan kuma da Jama'arsu suka ganine ya sanya hankalinsu yayi bala'in tashi.

Yayinda Yarima Asad kuma da ya tashi yi masa ta goma shabiyar ya daka tsalle, saboda tino yadda yayi shima tsalle alokacin da yake yi masa yana mai shimfid'a masa ita a tsakiya baya.

Wata irin b'ankarawa kuwa Jauron Yamma yayi yana mai d'agowa cikin tsananin gigita, kafin daga bisani kuma ruwan hawaye suka b'alle daga cikin idanuwansa da bala'in gudu tamkar anbud'e famfo, saboda ta sha shidan daya k'ara sauke masa ita cikin zafi.

Wata irin karkarwa jikin Jauron Yamma ya d'auka, hawayen da kowa ya gansu tsabar yawansu na cigaba da zubowa.
Amma a haka Yarima Asad ya k'ara d'aga bulalar yana mai shirin sauke masa ita Alk'alin gasa ya rik'e hannunsa da sauri, yana mai busa husur d'insa tare da d'aga hannun nasa sama.

Take kuwa wurin ya d'auki sowa da ihu na wa'yanda suke sonsa.
Yayinda Al'amin da Habu kuma suka futo aguje zuwa tsakiyar filin suna masu fara d'irkar rawa cikun matsanancin farinciki mara misaltuwa.

Shi kuwa Jauron Yamma cikin tsananin kunya, b'acin rai tare da azababben bak'in ciki ya fara sauka daga kan dakalin ko cikakken gabansa baya iya gani

Da sauri Lamid'on Yamma ya tawo yana mai rik'osa ransa a matuk'ar b'ace.
Tukun ya jasa ba tare da yayiwa ko Lamid'o Sulaiman sallama ba suka doshi wurin da dawakansu suke, hakama jama'arsu duka sukaita binsu zuciya duk ba dad'i.

Shi kuwa Yarima Asad take a wurin ya zube k'asa yana main sujudu shukur ga rabbil izzati daya k'addaro masa rabon mallakar Gimbiya Haddiyal, bayan futar da tsammani da yayi.
Hakan kuwa da Babban Yaya ya ganine yayi matuk'ar k'arasa sanyasa farin ciki, ta yadda harya zaro wayarsa yayi masa video, domin ya kaiwa Mamy ta gani d'an nata ya koma mutumin k'warai fa sosai yanzu.

Tukun bayan ya gama ya d'ago yana mai rungume Habu da Al'amin da suka k'araso wurin da yake, tare da fashewa da wani irin kukan farinciki mai had'e da dariya yana mai fad'in.

"Shikenan ta zama tawa, Haddiyal ta zama tawa, Allah Ubangiji ka nuna mun kuma ranar da zata soni tamkar yadda ka nuna mun wannan lokacin."

"Amin Amin." Suka fad'a harda Babban Yaya daya k'araso wurin da suke."
Kana suka had'u su duka akayi fadar Lamid'o domin suje su tattauna yadda abun zai kasance, a kuma tsayar da ranar da za'ayi auren.


Bak'ar Masarauta.

Cikin tsananin farinciki mara misaltuwa sukayi kabbara, wasun su har suna sujjada, saboda ganin da sukayi ko mutum d'aya basu rasaba a cikin nasu, sai dai raunika da wasu suka samu.

Yayinda gawarwakin azzaluman cikin BAK'AR MASARAUTA kuma da suka dad'e suna kisan ran mutane tamkar yadda ake kashe na kiyashi suke warwas a k'asa ta koina.

A guje Bir shi kuma ya zura da kayan yak'insa yana mai nufar hanyar b'angaren Bayi.

Yana k'arasawa wurin ya gansa fayau babu ko alamun mutum a ciki, da alamun dai duk sun b'uyane a cikin d'akunansu.
Hakanne ya sanyasa yin d'akin iya daya hango k'ofar itacensa a rufe, yana mai zuwa ya fara bubbuga ta tare da fad'in.

"Iyata! Iyata!! Iyata!!! Ki bud'e yau gani Jaruminki na dawo zan tafi dake kema."
Ya k'arasa maganar cikin kuka da dariya tamkar wani zararre.

Ita kuwa Iya da take a cikin d'aki sosai tayi matuk'ar firgita, ta kuma gigice da jin yadda ake bugo k'ofarta, domin kuwa kwata-kwata tashin hankalin da take ciki baisa ta fahimci abunda me bugowar yake fad'e ba, asalima ita duk a zatonta mutanan ne suka k'araso wurinsu su kashe su.
Hakanne ya sanyata ta k'ara curewa wuri guda jikinta na matuk'ar karkarwa.

Shi kuwa Bir jin da yayi shiru bata bud'e bane, gashi kuma ya matsu ya ganta, ya kuma jisa a jikinta, ya sanyasa sa k'arfinsa yana mai jijjige k'ofar.
Kana yayi cilli da ita yana mai yin wurin daya hangi Iya a guje.

Durk'ushewa yayi a gabanta yana mai sakin dariya tare da kuka yace.

"Iyata Jaruminki ne ya dawo, d'ago kanki ki kalleni kinji."

Cikin tsananin d'imuwa da firgicin da sautin muryarsa ya sata ta bud'e ido, tana mai d'orasu akan fuskarsa.
A matuk'ar gigice kuwa ta fara dukansa tana mai sakin kuka tare da fad'in.

"Me yasa kadawo? Me yasa zaka dawo bayan kasan kashemun kai zasuyi? Me yasa zakayi mun haka Jarumi? Shin kasan irin neman da ake yimaka kuwa? Me yasa kadawo nace maka?!!!"

Ta k'arasa maganar a matuk'ar gigice tana mai fara marinsa a fuska.
Hakan da Bir ya ganine ya sanyasa rungumeta da sauri a cikin jikinsa yana mai fad'in.

"Kiyi shiru ki nutsu Iyata, babu abunda zai faru dani, domin kuwa azzaluman cikin Bak'ar Masarauta sun riga da sun mace, k'arshen zalinci yazo, a yau huk'uba da azabar da suke ganawa mutane ta k'are, domin kuwa ni da hannuna na kashe shugaban azzalumai bak'in kafuri mara imani da tausayi Sarki Barbaru, dan haka yanzu sunan Bak'ar Masarauta zai canzane, zata koma farar masarauta, domin kuwa haske ya shigo cikinta yana kuma shirin haska kowa ne lungu da sak'o na cikinta."

Suman tsaye Iya tayi tana mai kallon Bir, saboda jin furucin da yake yi, kafin daga bisani kuma ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Shin kasan abunda kake fad'e kuwa Bir?"
Ba sunana Bir ba yanzu Iyata, sunana Abdulmajid, wato bawan Almajid kenan, shikuma Almajid Allah ne."

Ya k'arasa maganar yana mai nuni da sama.
Amma sai dai kuma ko kad'an Iya bata fahimci abunda yake nufi ba, hakanne ya sanyata bud'e baki tana mai fad'in.

"To ina kuma ka baro Gimbiyar ne yanzu?"

"Gimbiya tana wurinsu Ummina da Abbana, addu'ar ki ta karb'u Iyata, kwanan mu d'aya da zuwa K'asar Hausa muka had'u da Iyayena na asali, kuma yanzu hakama tare da Yayana muke harma da Sarkin mu da sauran jama'ar Masarautar mu."

Da matuk'ar k'arfi Iya ta rungumesa tana mai sakin dariya tare da fad'in.

"Burina ya cika a yau, godiya a gareka Ubangiji Gargabilu."

Girgiza kai Bir yayi, saboda jin abun da take fad'e.
Kana ya rik'o hannunta yana mai fad'in.

"Tawo muje Iyata, ga 'yan Uwana can suna waje."

Binsa kuwa tayi suna masu fucewa daga cikin d'akin, sai dai kuma yanzu da suka futo gaba d'aya sun tadda sauran d'akunan Bayin a bud'e basa ciki, hakan yasa Bir ya gane cewar jama'ar sune suka tattaresu kenan.

Hakan yasa kai tsaye ya doshi b'angarensu Sarki Barbaru hannunsa rik'e dana Iya.
Suna kuma b'ullawa suka hangi dan dazon Jama'ar cikin Bak'ar Masarauta marasa galihu zazzaune a k'asa.
Yayinda daga can gaba kuma ahalin Sarki Barbarune, tun daga kan matansa har zuwa 'Ya'yan, sai shine da kuma Babban d'ansa da aka kashe kawai babu su suna durk'ushe a k'asa, suna aikin rusar kuka mai cin rai suma.
Kai tsaye Bir ya doshi wurin dasu Sheikh Ahmad suke a tsaye suna yiwa jama'ar bayanin abun da ya kawosu ta cikin sigar da suka san zasu fahimcesu.

Bir na tsayuwa a wurin gaba d'aya jama'ar suka bisa da idanu cikin tsananin mamaki.
Yayinda Gimbiya Salwa kuma ta mik'e a zabure, kana kuma cikin kuka tana mai fad'in.

"Dama ka dawo ina ka kaimun 'Yata ne?"

Murmushi yayi idanunsa na zubar da k'walla, kana ya bud'e baki cikin sanyi yana mai fad'in.

"Gimbiya tana nan cikin aminci da wadatar lafiya a wurin Mahaifana, kuma a yanzuma zamu tafi tare da ku har wurin da take."

Hakan yasa lokaci d'aya kuwa ta saki murmushi, tana mai komawa ta zauna, yayinda su kuma sukaji kaso hamsin na damuwarsu ya ragu, saboda jin abun da ya fad'a da sukayi.

Su kuwa su Sheikh Ahmad cigaba da wa'azin da suke mai ratsa jijiya da jini sukayi, yayinda gaba d'aya al'ummar wurin kuma sukayi shiru jikinsu nayin bala'in sanyi, hatta da iyalan Sarki Barbaru kuwa. Saboda lokaci guda sukai amanna da tabbas addininsu na k'aryane, wannan da akazo musu da shi yau shine na gaskiya, duba da hujjojin da aka fad'a musu.

Ai kuwa a wurin jama'a da dama suka fara cewa sun yadda da addinin sun aminta dashi, kuma suna son su zamto d'aya daga cikinsu.

Cikin matsanancin farinciki mara misaltuwa kuwa aka fara basu kalmar shahada.
Yayinda wasunsu kuma sukayi shiru basuce komai ba, ciki kuwa harda ahalin Sarki Barbaru, amma sai dai suma kallo d'aya zakayi musu ka fahimci jikinsu yayi sanyi.
A k'arshe dai basu watse daga wurin ba har sai da akayi musu bayanin wankan tsarki, sannan kuma aka basu sunaye suka zab'a.
Kana Sarki Abdallah yasa aka nemo masa wani Malami musulmi da yake a jahar da take mak'otaka da tasu, tukun suka sasa ya dinga bawa jama'ar karatu, yana kuma koya musu sallah.
Yayinda ahalin Sarki Barbaru kuma gabaki d'ayansu harma da Iya suka tattarasu suna masu tafiya dasu, saboda suna son suje da sune k'asarsu, domin suga yadda ake shugabanci sannan kuma a karantar dasu shi kafun su dawo.

Hakan yasa tun a wurin Wazirin Sarki Barbaru da shima ya gudu ya b'uya, kuma ya musulunta yanzu ya zama shugaba, saboda shi sugabanci dolene a addinance, bazai tab'a yuwuwa a bar mutane sakakaba, yayinda wannan Malamin da aka samo kuma aka bashi wuri anan cikin gidan.

Tukun su kuma suka tattara yanasu yanasu tare da ahalin Sarki Barbaru gaba d'ayansu suka shiga cikin jirgi a yammacin, ba tare da sun tsaya jiran sai gobe ba suka d'auki hanyar K'asar Hausa.


A K'asar Hausa cikin gidansu Sheikh Ahmad kuwa, tun daga ranar da suka tafi har kawo yau babu wanda hankalinsa yake kwance a cikinsu, domin kuwa ko da wayoyi basu tafiba, hakan yasa gaba d'aya hankalinsu yake a bala'in tashe, banda aikin addu'oi ako da yaushe babu abunda suke iyayi.
Domin kuwa ita Gimbiya Tasmir ma kusan ko da yaushe cikin kuka take, sai Ummice ma mai rarrashinta.

A can b'angarensu Yarima Asad kuwa cikin matsanancin farinciki suka baro cikin Masarautar Fuld'e bayan an yanke ranar da za'ayi d'aurin auren, wato dai nan da sati ukku masu zuwa kenan, yayinda zasu fara al'adunsu na biki kuma daga satin da zai kama na gaba.
Wanda kuma dole sai Yarima Asad yazo tare dashi za'ayi, kuma shima sai ya sanya kayan Fulani, sai dai kuma ko kad'an hakan bai damesa ba, saima k'aguwa da yayi ranar tazo.
Basu je wurin Gimbiya Haddiyal ba ya bari sai jibi idan ya dawo suka tawo gida.

Yayinda a b'angarensu Billy kuma yau d'in suka fara bukukuwansu, tayadda hotuna da videos ya cike ko ina a social medai.
Biki ne aka farasa da

Please Login or Register in order to submit comment