Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rayuwa ita da kanta tasani tayi dacen had'ad'd'en miji.
Yana da wani irin salo wanda yake saurin dilmiyar da zuciya zuwa ga sonsa, tabbas komai nasa na dabanne, tun daga kan salon kallonsa, tafiyarsa, maganarsa, harma da murmushinsa.

Ba ita ta iya janye idanuwanta ba daga hanyar da yabi, sai da har ta dena hangensa gaba d'aya.
Tukun ta sauke kanta k'asa tana mai lumshe idanuwanta ahankali, kana ta bud'e su tana mai fad'in.

"Hakika kai d'in na daban ne a cikin maza.
Tabbas baka cancanci zamtowa Bawa ba, kai d'in da Sarki kafu kama ba 'Dan Sarki bama.
Ina sonka, zan kuma cigaba da sonka har zuwa lokacin da numfashi zai rabu da gangar jikina.
Rabuwa da kai kuwa tamkar zare rai da ruhi daga cikin jikina ne, dan haka dolene ma murayu tare, a daren yau ba gobe ba zan samar mana da mafuta."

Ta k'arasa maganar asanyaye a kuma fili, tana mai juyawa ta doshi k'ofar da zata kaita cikin d'akin ta.

Tana shiga cikin d'akin nata ta wuce wurin waccan k'ofar ta rufeta gam, domin kuwa bata son kowa yazo wurin da take a yaud'in, gudun kar a fahimci halin da take ciki, ko kuma a yanke mata tunanin da zata fara a yanzu.
Tana rufe k'ofar kuwa ba tare da ta tsaya komai ba ta fara zagaye d'akin, kanta d'age asama tana kallon rufinsa.

Ko kad'an bata iya rumtsawa ba, duk da yadda dare ya tsala sosai kuwa, iyakar ta kawai zama da tashi, tare da zagaye a cikin d'akin take ta aikin yi, tana mai neman mafuta.
Sosai zuciyarta take raya mata abubuwa da yawa, amma gaba d'aya bata samu wanda yayi mata ba har yanzu.

Yayinda acan b'angaren Bir shima kuma yake zaune akan shimfid'arsa ya zuba uban tagumi, idanuwansa akan su Mauzum da suke shararar baccinsu hankali kwance.
Idan kaga yadda yake kalon su sai kayi tinanin wani abun yake nema ajikin su, amma kuma a zahiri kwakwata hankalinsa ma baya kansu, idanun nasa ne kawai akan jikin su, domin kuwa ba k'aramun nisa yayi ba acikin duniyar tinanin irin mafutar da zata samar musu, ta yadda har yake jin tamkar ya janyo safiya dan yaji abun da zata fad'a.

Bashi ya samu bacci ya suresa ba har sai da iskar gabannin asuba mai matuk'ar sanyi ta fara busowa, tukun ya b'ingre a gefe, yana mai fara bacci ba tare daya san lokacin daya sace sa ba.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir har sai misalin k'arfe hud'u na dare, tukun zuciyarta ta bata wata mafuta, wadda kuma taji tayi mata fiye da duk sauran na baya.
Sai dai kuma har lokacin ta kasa yin bacci, sai kwanciya da tayi rigingine akan gadonta.
Yayinda k'afafuwanta kuma suke dire a k'asa, tana mai kallon rufin d'akin tare da nazari akan abun da ta yanke musun.
Yayinda a wani b'angare na zuciyarta kuma take cike da tsoro da fargaba, ta yadda har take jin anya ko zata iya aiwatar da abun da zuciyarta ta kud'irta mata ta aiwatar, shin idan tayin bazata zo tayi nadama ak'arshe ba kuwa.
Da sauri kuma ta girgiza kanta tana mai fad'in.

"Hak'ik'a bazan tab'a nadama ba akan sonka Jarumi.
Sabo da kaima d'in kana sona irin son da nake maka, tunda har ka iya jure irin azabtarwar da nai maka abaya, ka kuma manta da ita yanzu."

Haka dai tai ta sak'e-sak'e har zuwa lokacin da bacci b'arawo ya saceta, ta sanadin sanyin iskar asubar daya fara kad'awa a gari.

*WASHEGARI*

Tamkar an mata duka da mugayen iccina haka taji jikinta na ciwo a lokacin da ta farka daga bacci.
Ba kuma komai ne ya kawo mata hakan ba sai rashin isashen baccin da batayi ba.
A hankali ta fara motsa idanuwan nata tana mai d'an yamutsa fuska.
Kana daga bisani kuma ta bud'esu dak'yar, sabo da yadda take jin tamkar an d'ibi tsakuwa an watsa mata acikin su, sabo da ko kad'an baccin bai isheta ba.

Zumbur ta mik'e zaune daga kwancen da take, sabo da yadda ta idanuwanta suka sauka akan hasken ranar daya dallo cikin d'akin ta windownta na baya.

Da k'arfi ta rumtse idanuwanta tana mai jin babu dad'i a ranta, saboda tasan yanzu k'ila yana can yana jiranta, tunda sunyi da ita akan cewar da wuri zasu had'un.
Kafin daga bisani kuma ta mik'e tsaye tana mai fara cire kayan jikinta anan, tukun bayan ta gama ta doshi bathroom jiki a tsantsar sanyaye.
So take tayi sauri ko tayi tagama abun da take taje ta same sa, amma gaba d'aya taji ta kasa, asalima jin zuciyarta take tai mata wani irin mugun nauyi tamkar an d'ora dutse a kanta.

Bata wani d'au dogon lokaci ba ta futo daga cikin bathroom d'in d'aure da towel a k'ugunta.
Kai tsaye ta doshi gaban madubi, tana mai zuwa ta zauna ta fara shafa mai ajikin ta.

A sanyaye take komai tamaka wacce k'wai ya fashewa aciki.
Ba kuma komai bane ya saukar mata da sanyin jikin sai fargabar abun da take shirin aikatawa.
Ta rasa dalilin daya sanya har yanzu ta kasa samun nutsuwa da shawarar data yanke d'in, sai dai kuma ya zatayi.
Babu wata bayan ita da zata sanyasu su rayu wuri d'aya da masoyin nata rayuwa ta har abada.

Cikin sanyi ta mik'e daga kan kujerar, tana mai nufar gaban wardrobe d'in ta.
Under wears ta fara sanyawa ajikin ta.
Tukun ta ware milk colour d'in doguwar rigar data d'auko tana mai sanyata a jikinta.

Sosai dirinta yayi matuk'ar bayyana a cikin rigar tai mata d'as ajiki, kasancewarta ta roba.

Sosai tayi matuk'ar kyau a cikin rigar, duk da yadda ta d'an fada kuwa, sabo da tinanin da take tayi da kuma rashin samun wadataccen baci.
Amma sai dai kuma ko kad'an ramar bata sanyata muni ba, saima wani irin kyawunta ne ya k'ara bayyana.
Turaren data tawo dashi daga kan mirrow ta feshe ilahirin jikinta dashi.
Kwata-kwata batayi kwalliya akan fuskarta ta ba, sai hoda kawai da ta d'an murza.
Yayinda tausasan jajayen siraran lab'b'anta kuma suka kasance suna futar da shek'i, tamkar ta shafa musu wani abun.

Ko kad'an bata tsaya neman abun da zataci ba, duk da kuwa ko ajiya da dare bataci komai ba, tasa kai tana mai fucewa daga cikin d'akin.

Kasancewar ranar da ake bame zafi bace yau, asalima futowa take tana lumshewa tamkar yadda aka sabayi musu ita a k'asar tasu, shiyasa wata irin sassanyar iska ke kad'awa tana dukan jikin ta.
Da hakanan ne tasan da ba k'aramun dad'in yanayin zataji ba, amma da yake yau d'in gaba d'aya bata cikin farinciki, shiyasa ko kad'an bata wani lura da ita bama.

Tunkarar wurin take tana mai cigaba da juya girman abun da take shirin aikatawa a cikin ranta.
Yayinda wata zuciyar kuma ke nusar da ita akan karta ce zatayi hakan, domin kuwa idan tayi hakan ko kad'an batayiwa ahalinta adalci ba a rayuwa.
Wanda hakan kuma shine ke sanyawa jikin ta na k'arayin sanyi tun jiya.
Sai dai kuma ko kad'an batajin zata iya bin shawarar wannan zuciyar.
Sabo da bin natan tamkar dai-dai yake data bud'e baki tace ta hak'ura da Bir ne har abada.
Sabo da muddin bata waccan hanyar data gama aminta da ita ba, babu wata hanya da take ganin zatabi su cimma gaci.

Tsaye ta hangesa daga can jikin wannan bishiyar data gansa jiya, sai dai kuma yau d'in banan yake kallo ba bayansa ya juya.
Hakanne yasa tun daga nan wurin da take ta kafe faffad'an farin bayansa da k'wayoyin idanuwanta, tana mai jin wani irin abu na sake fuzgar zuciyarta zuwa garesa.

Shi ko sanye yake da sitirarsa ta yau da kullum, sai dai kuma fes-fes tasan take tamkar koda yaushe.
Domin kuwa kwata-kwata Bir bai yadda da zama da daud'a ba ko acan baya.
Shiyasa ma a kullum yake cikin wanke 'yan kyallayen kayansa.

Tsaye tayi a dab da shi daga bayansa ba tare da tace komai ba.
Sai idanuwanta data cigaba da binsa da su, tana mai kallon yadda gaba d'aya ilahirin jikinsa yake d'auke da wata irin kwantacciyar lallausar gargasa, da tayi matuk'ar hawa da fatar jikin sa.
Sosai take mamakin yadda taga babu alamun tabo ko kad'an a bayan nasa, duk da irin wahalar da suke sha amatsayinsu na Bayi, da kuma irin wahalar da itama ta basa, asalima sai wani irin shek'i da taga fatar jikin nasa tanayi, ta yadda ko tata da take murjeta da tsadaddun lafiyayyun mayuka bazata fita k'yalli ba sai dai su kara.

Shi ko Bir tunda sanyin safiya su Mauzum na tashi shima ya tashi suka fara ayyukan da suka saba na kullum.
Tukun bayan sun gama ya wuce band'akin su yayi wanka.
Kana bayan ya futo ya shirya cikin 'yan kayansa daya wanke su jiya, yana mai tawowa nan duk da uban baccin da yake cike a idanuwansa kuwa.
Kasancewar rashin wadataccen bacin da bai samu yayi ba jiya.

A hankali ya fara juyowa har ya juyo da jikinsa duka b'angaren da take, yana mai sauke dara-daran idanuwansa a cikin nata, sabo da alamun tsayuwarta da yaji a wurin.

A tare gaba d'ayan su suka sauke numfashi suna masu kallon juna.
Kafin daga bisani kuma Bir ya bud'e baki cikin sanyin murya, bayan ya langwab'ar da kansa gefe, yana mai cewa.

"Me ya hanaki kiyi bacci jiya, bayan kuma nace miki ba tinani?"

'Dan lumshe idanuwa tayi, tana mai jin wani irin abu na tsarga mata tun daga kan 'yantsunta har zuwa kwanyarta, sabo da jin salon yadda yayi furucin nasa.
Kana daga bisani ta bud'e idanuwan nata tana mai fad'in.

"To ai kaima bakayi baccin ba, ni kuma nayi banyi da yawa bane ba kawai."

Itama tayi maganar asanyaye tana kallonsa.
Yayinda shi kuma Bir ya fesar da iska, yana mai lumshe idanuwansa ya bud'e su.
Kana ya d'an d'aga lab'b'ansa cikin muryarsa mai shige data yara a wasu lokutan idan yana yiwa Iya shagwab'a, yace.

"To tayaya kuwa kike tinanin zumud'in son jin mafutar da zaki samar mana zai barni na iya bacci, da alamun dai naga har yanzu baki gama gane irin son da nake miki ba ko?"

'Dan gajeran numfashi ta fesar tana mai durk'usar da kanta k'asa.
Yayinda jikinta kuma ke sakeyin matuk'ar sanyi, zuciyarta kuwa sosai take dukan tara-tara, sabo da fargabar abun da take shirin aiwatarwa.

Cikin sanyi, kana kuma a hankali tace.
"Ina kwana."

Lumshe idanuwa Bir yayi, yana mai jin wani irin farinciki na lullub'e zuciyarsa, wai yau shine Gimbiya ta gaisar da kanta.

Hakanne ya sanya sa bud'e baki cikin 'yar shagwab'a, yana mai fad'in.

"Ni fa mafutar mu nake son ji tun d'azu ba gaisuwa ba, amma ke naga sai jamun aji kikeyi."

"A'a nifa ba ajin dana jamaka, daga gaisuwa kuma."
Ta fad'a itama tana d'an sakin murmushin yak'e.
Kana ta d'an juyar da kanta gefe, tana mai fesar da wata zazzafar iska daga cikin bakinta.
Tukun ta sake dawo da kanta b'angaren da yake tana mai sanya k'wayoyin idanuwanta a cikin nasa.
Kana ta bud'e baki cikin sanyin murya mai had'e da tsoro acikin ta, bayan ta rumtse idanuwanta, tana mai fad'in.

"Hanya d'aya ce kad'ai zamubi muyi rayuwa ta har abada a tare.
Nayi duk wani tinanin da zanyi domin naga na samo wata bayan ita, amma gaba d'aya abun yacitura, ita kad'aice wacce zata kaimu ga cimma gaci Jarumi na."

"Ina jinki Gimbiyata, yi sauri ki fad'a muni wata kalar hanyace."
Bir ya fad'a cikin zak'uwa, yana mai k'ara bud'e kunnuwansa.
Hakanne ya sanya itama Gimbiya Tamsir ta bud'e idanuwanta.
Tukun ta sake fesar da zazzafar iskar daga cikin bakin ta tana mai fad'in.

"Ta hanyar barin gari, ina nufin mu gudu mubar k'asar nan mutafi wata k'asar, wannan ita kad'aice hanyar da zamubi muyi rayuwa ta har abada, ba tare da giftawar wata matsala ba."

Tayi maganar cikin wata irin murya, idanuwanta a cikin na Bir.

Yayinda shi kuma Bir kalamanta sukayi matuk'ar gigitasa, tare da d'imautasa.
Ta yadda har baisan lokacin daya fara ja da baya ba, yana mai girgiza mata ka, idanuwansa a waje.

Ba shi ya iya tsatawa ba har sai da yaji sa ya had'e da jikin bishiyar nan.
Tukun ya cigaba da girgiza mata kansa, yana mai faman zare idanuwansa.
Kafin daga bisani kuma ya fara fad'in.

"Ina! Ina!! Inaaa!!!
Shin babu wata hanyar ne bayan wannan Gimbiya?
Wannan hanyar ba mai yuwuwa bace ba tayi tsauri da yawa."

Ya fad'a a wani irin rud'e yana mai kallonta.

Ganin yadda yake yi da tayi ne da kuma jin abun da ya fad'a, ya sanya itama tayi matuk'ar rud'ewa, tana mai fara girgiza masa kai itama.
Kafin daga bisani kuma hawayen da take aikin danne su tun data tashi daga bacci suka samu damar b'allewa daga cikin idanuwanta.
Tukun ta d'aga baki cikin rawar murya, tana mai fad'in.

"Me yuwuwace Jarumi, dole ka hak'ura da rayuwar Bak'ar Masarauta ka tawo mu gudu mu bar k'asar gaba d'aya muddin kana mun irin son da nake maka."

"A'a Gimbiyata, ina miki fiye da irin son da kike mun, amma ki sake sabon tinani, mu zauna tare mu binciko wata hanyar, sabo da wannan kwata-kwata bamai yuwuwa bace ba."

Ya fad'a da wani irin sauti, muryarsa na rawa, yayinda hankalinsa kuma yakai k'ololuwa wurin tashi.
Sabo da jin furucin da yaji tayi, ga kuma hawayen da yaga suna zuba daga cikin idanunta tana mai girgiza masa kai itama.

"Kar kace haka Jarumi, domin ko jiya kusan kwana nayi ina tinani amma banga wata hanyar da takai wannan ba.
Dan haka dolene ka hak'ura mu gudu mubar BAK'AR MASARAUTA mudin da gaske kake kana son mu rayu tare."

Itama Gimbiya Tasmir ta fad'a a wani irin hargitse hankalinta a bala'in tashe, tana mai cigaba da girgiza masa kai, tare da kafesa da idanuwa.
Yayinda fuskarta kuma gaba d'aya ta jik'e da ruwan hawaye tare da majina.

Jin abun da Bir yayi ta fad'a ne, ya sanya sa jin wasu irin zafafan hawaye na b'allewa daga cikin idanuwansa.
Tukun ya cigaba da girgiza mta kai, yana mai bud'e baki yace.

"Ina sonki Gimbiya, ina miki son dani kaina ban san adadin saba, amma ki sani bazan iya tafiya na bar Iyata ba, bazan iya guduwa na bar Iyata ba, idan aka wayi gari Iya bata ganni ba tayi yaya kenan?"

Cak Gimbiya Tasmir ta tsaya a wurin da take, tare da dena girgiza kanta da take aikin yi, ta kuma tsayar da kukan ta, sabo da jin kalamin da suke futowa daga bakinsa.
Cigaba da binsa tayi da idanuwanta, tana mai jin kalamansa na ratsa cikin k'wak'walwarta.
Yayinda shima har lokacin yake kallonta, yana mai-maita kalmar. "Iya." Tare da cigaba da girgiza kai, hawaye na kwaranya daga cikin idanuwansa tamkar an bud'e famfo.

Da k'arfi ta rumtse idanuwanta, kana daga bisani ta juyar da kanta gefe tana mai bud'e su.
Tukun ta bud'e baki cikin tafasar zuciyar da b'acin ran da kalamansa suka saukar mata, tana mai fad'in.

"Ashe ni bani da iyaye ban saniba, ashe ni idan aka wayi gari basu ganni ba zasuji dad'i, ashe ni ban san dad'in su ba shiyasa har na zab'i na tafi na barsu."

Ta k'arasa yin furucin tana mai rumtse idanuwanta da k'arfi.
Kana ta bud'e su tana mai juyo da kanta b'arin da yake, wasu irin hawaye masu tsananin gudu na b'allewa daga cikin su, ta watsasu a tsakiyar nasa.
Shima d'in hawayen yake sosai, zuciyarsa na wani irin suya.
Tukun ta bud'e bak, tana mai d'orawa da fad'in.

"Na sadaukar da farincikina domin ka! Na sadaukar da matsayina domin ka! Na sadaukar da dukiyata domin ka! Na sadaukar da soyayyar da nake yiwa Iyayena Yayyane. Na yadda na gudu na barsu guduwa ta har abada dominka.
Amma kai shine bazaka iya sadaukar da abu d'aya ba a rayuwarka dominni, bazaka iya tafiya kabar Iyarka ba sabo da kar ranta yay zafi.
Ashe dama ba sona kake ba Jarumi! Ashe dama ka shigo cikin rayuwata domin ka cutar da zuciyata ne, Ashe bazaka iya sadaukar da farincikinka ba domin nawa.
Hak'ik'a nayi ganganci tare da kuskuren barin zuciyata ta kamu da son wanda bai damu da ita ba.
Ban san meye so ba sai da ka koya mun, ban san ya duniyarsa take ba sai da kashigo rayuwata, bansan zafinsa ba da dad'in sa sai ta sanadinka.
Naso ka tamkar yadda nake son rayuwata, na soka irin son dani kaina bana yiwa kaina shi, na soka ta yadda har soyayyarka ta sanya na zab'i na bika na bar Ahalina.
Amma kai da abun da zaka sakamun kenan.
Tom shikenan, nima daga yau zanyi k'ok'arin fara koyawa zuciyata rashinka."

Ta k'arasa maganar cikin wani irin kuka, ta yadda har muryarta ke sark'ewa, tukun ta fara shirin juyawa ta tafi.

Ganin hakan da Bir yayi ne, ya sanya hankalinsa ya sake bala'in tashi.
Lokaci d'aya ruwan hawaye suka sake tsinkewa daga cikin idanuwansa tamkar an bud'e famfo.
Tukun ya bud'e baki cikin rawar murya da tsananin kuka tamkar k'aramin yaro, yana mai fad'in.

"Iya tayi mun komai a rayuwa, iya ta soni fiye da yadda take son ranta.
Ba ita ta haifeni ba, amma tana mun so irin san da uwa takewa d'anta ne.
Ta rungumeni tunda jinin haihuwa d'auke a jikina, tayi mun wanka, tabani madara, ta wanke mun kashi, ta goyani a gadon bayanta.
Ta koya mun zama, ta koya mun tafiya, sannan kuma ta koya mun cin abinci.
Idan nayi kuka hankalinta na tashi, idan nayi dariya itama tayi dariya, idan ko banda lafiya tana jin tamkar ta d'auki ciwon ta mayar dashi cikin jikinta sabo da in bar wahala.
Iya ta sadaukar da komai nata ciki kuwa har da rayuwarta domin farincikina, duk da kasancewar bata haifeni ba kuwa.
To idan namata haka kina ganin nai mata adalci kuwa? Idan aka wayi gari bata ganni ba kina ganin ba zatai da tasanin rainon da tayi mun ba da wahalar da taci akaina?
Ko kad'an iya bata cancanci wannan sakayyar daga wurina ba Gimbiya."

Ya k'arasa furucin dak'yar, kuka nacin k'arfinsa.
Yayinda ita kuma Gimbiya Tamsir lokaci d'aya taji zuciyarta tayi wani irin dakewa, gaba d'aya dana sanin afkawa cikin soyayyarsa yayi mata k'awanya.
Kafin daga bisani kuma ta sake watsa jik'ak'k'un idanuwanta zuwa cikin nasa, tana mai bud'e baki cikin wata irin murya tace.

"Ashe ni tawa Uwar bata shayar dani ba, ashe ni tawa Uwar bata goyani ta wanke mun kashi ta koyan tafiya da cin abinci ba, ashe duk irin soyayyar da Iyayena da Dangina suke nunamun ba soyayya bace da har na zab'i na bika ma barsu.
Ashe ni idan na tafi suka wayi gari basu ganni ba zasuyi farinci kuma suyi alfahiri dani.
Tabbas idan katafi kabar Iya bakayi mata hallaciba.
Nima kuma nagode da tinatarwar da kayi mun akan irin wahalhalun da nawa Iyayen sukayi dani.
Zan tafi yanzu daga gabanka sabo da ka nuna baka buk'ata ta acikin rayuwarka, amma kafun na tafi ina son kasani.
Kaine mutum na farko da Tasmir ta fara so.
Kuma na soka fiye da yadda nake son raina, ina sanka so irin wanda bazai tab'a misaltuwa ba, wanda har hakan ya sanya na sadaukar da komai da kowa nawa na yadda na bika muyi rayuwa, bayan kuma baka cancanci hakan ba kwatakwata.
Amma ina son kasani, daga yau daga yanzu zanfara koyawa zuciyata rashinka, na koyawa kunnuwana rashin jin sautinka, haka kuma zan shafe hotunan fuskarka daga cikin idanuwana, sannan kuma idan na tafi na barka har abada.
Ba zaka k'ara sanya k'wayar idanuwanka ba akaina, koda kuwa rashin ganinka zai zamto silar tsayawar bugun zuciyata kuwa!"

Ta k'arasa maganar tana mai janye jik'ak'k'un idanuwanta da suke ambaliyar ruwan hawaye tamkar yadda nasa sukeyi daga cikin nasan.
Kana ta juya tana mai fara d'aga k'afafuwanta tayi gaba.
Hakan da Bir ya ganine, ya kuma ji furucin da tayi suka k'ara matuk'ar gigitasa.
Ta yadda take a wurin jikinsa ya d'auki kyarma, yayinda idanuwansa kuma suka k'ara b'allewa da wasu sababbin hawayen.
Zuciyarsa kuwa jinta yake tamkar zata hudo k'irjinsa ta futo waje, sabo da tsananin bugun da take da k'arfi.
Kansa kuwa jinsa yake tamkar zai dare gida biyu tsabar ciwon da yake yi.
Tukun ya bud'e baki cikin rawar murya tare da tsananin kuka, yana mai yin sauri ya damk'o yatsun Gimbiya Tasmir data fara tafiya, yace.

"Idan kika tafi kika barni zuciyata zata buga Gimbiyata, idan kika tafi na sani mutuwa zanyi.
Hak'ik'a ina sonki fiye da irin son da kike mun, dan haka na aminta juyo ki fad'amun wace k'asa kike son mutafi.
Na aminta na yadda mu gudu mubar BAK'AR MASARAUTA."

Ya k'arasa maganar cikin matsanancin kuka, jikinsa na cigaba da kyarma.
Ita kuwa Gimbiya Tasmir tana jin ya rik'o yatsun hannunta ta tsaya cak, ba tare data juyo ba, tana mai sauraran furucinsa.
A lokacin kuwa da taji k'arshen maganar tasa, ji tayi wani irin farinciki ya lullub'e zuciyarta.
Hakanne ya sanya ta juyowa garesa, har lokacin idanuwanta na zubar ruwan hawaye.
Ta jefa k'wayoyin idanuwanta a cikin nasa.
Tukun ta bud'e baki cikin wani irin sauti, bayan tayi k'ok'arin tsayar da kukanta, tana mai fad'in.
"K'asar Hausa..............✍




_GASKIYA NA YAU NAYISA YAYI OVER, DAN HAKA NA TAFI HUTU SAI WATARAN KUMA 😊😊_


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*16*



Cikin tsantsar firgici, rud'u gami da tashin hankali Bir ya k'ame k'am a wurin da yake, yana mai cigaba da binta da idanuwa.
Yayinda sunan K'asar Hausa kuma ya farayi masa amsa kuwwa a cikin kunnuwasa yana yawo a k'wak'walwarsa.
Gaba d'aya labaran da Iya ta basa suka fara dawo masa.
So yake ya bud'e baki ya tambayeta yadda akai tasan k'asar.
Amma gaba d'aya yaji ya kasa, sabo da yadda yaji lab'b'an nasa sun masa wani irin nauyi.

Lura da hakan da Gimbiya Tasmir tayi ne, ya sanya ta juyowa gaba d'ayanta.
Tukun ta fara takowa idanunta a cikin nasa, tana mai dawowa gabansa ta tsaya.
A kuma hankali ta lumshe idanuwanta, tana mai fesar da iskar bakinta.
Kana daga bisani ta sake bud'esu a cikin tsakiyar nasa, tana mai bud'e baki tace.

"Tabbas zamu gudu, kuma daga nan babu inda zamutafi face k'asar hausa.
Domin ko lokaci yayi da kaima zaka zamto mutum mai 'yanci, lokaci yayi da zaka sadu da iyayenka na asali, lokaci yayi da bak'incikin mahaifanka da yake dashe a cikin zuciyarsu tsawon shekaru talatin da d'aya zai yaye."

Ta k'arasa maganar tana mai jinjna masa kai.

Shi kuwa Bir gaba d'aya kasa motsi yayi a wurin, balle kuma har ya iya bud'e baki yay magana, sabo da yadda magan-ganunta sukayi matuk'ar d'aure masa kai.
Babu abun da yake aikin tinanin, sai yadda akai tasan da tarihinsa.

Ita ko Gimbiya Tasmir ba tare data tsaya jiran abun da zaice ba, ta d'ora da fad'in.

"Nasan kana mamakin yadda akai nasan tarihinka, bayan kuma ko kai kanka ba lallaine kasan da shiba.
To idan baka manta ba kai da kanka katab'a bani sak'on tayaka neman ko suwaye.
Wannan dalilin shine harya sanya na fara bincike, har mahaifina ya bud'e baki da kansa ya bani labarin, wanda hakan kuma shine yayi sanadin daya sanya na fara jin tausayinka a zuciyata, ta yadda har ya hanani sukuni, kana kuma na zubar da duka mugayen k'udirirrikana akan ka.
Dan haka idan ka shirya sauraran tarihinka, ni kuma zan karanto maka shi tun daga farko har k'arshensa, tamkar yadda aka fad'amun.

Ta k'arasa maganar tana mai kafesa da idanuwanta.
Shi kuwa Bir da k'arfi ya rumtse idanuwansa, yana mai sakin ajiyar zuciya.
Kana daga bisani ya bud'esu akan fuskarta.
Tukun kuma a hankali ya d'aga lab'b'ansa cikin rawar murya, yana mai fad'in.

"Iya ta sanar dani komai, tun a washegarin ranar bikin godiya, wanda hakan kuma shine ya sanya na fad'a miki cewar Iya ta sadaukar da har rayuwarta domin farincikina.
Sabo da ta fad'amun futar labarin da dai-dai yake da rasa rayuwarta ne, a lokacin da aka mata gargad'in akace.
Sai dai kuma a yanzu bansan yadda zanyi ba Gimbiya.
Hak'ik'a ina matuk'ar sonki, kuma ina mugun tsoron kar Iyata ta rasa rayuwarta ta sanadin tafiyar da zamuyi."

Ya k'arasa furucin hawaye na sake kwaranyo masa.

Jin hakan da kuma ganin yadda yake kuka da Gimbuya Tasmir tayi ne, ya sanya ta fara d'aga k'afafuwanta tana mai k'ara matsawa kusa da shi dab, ta yadda har jikin su ya fara gugar na juna.
Yayinda har lokacin itama hawayen ke tsiyaya daga cikin idanuwanta.
A hankali ta d'aga tafukan hannayenta, tana mai damk'o nasa dasu.
Tukun ta rumtsesu da k'arfi acikin nata.
Kana ta bud'e baki cikin rawar murya, bayan ta watsa idanuwanta a cikin nasa, tana mai fad'in.

"Iya bazata mutuba Jarumi, babu abun da zai sameta dan muntafi, wannan tabbacine nake baka.
Domin kuwa babu wanda yasan lokacin data baka labarin, sannan kuma bakai kad'ai bane zaka gudu mu biyu zamu tafi, kaga idan hakane, kenan ko kad'an ba zasuyi tinanin can wurinsu zamu tafi ba.
Sai dai su kawo wani wurin daban.
Idan

Please Login or Register in order to submit comment