Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta yadda har k'warya-k'waryar walima sai da su Hajiya Bilkisu suka had'a da yamma a cikin gidan.


*BAYAN KWANA BIYAR.*

Sosai farinciki ya baibaye zukatan a halin Gidansu Sheikh Ahmad, yayinda a kullum kuma Ummi, Auta, Sheikh Ahmad harma da Alawiyya suke koyawa su Bir da ya koma Abdulmajid a yanzu karatu da addu'oi kad'an-kad'an.

A fannin Sheikh Ahmad kuwa sosai ya mayar da hankali wurin tafitar da suke shiryawa zasuyi ta da'awa, domin kuwa Sarkin Wasai ya goyi baya kuma ya bada guddumawa d'ari bisa d'ari, yayinda tini kuma yaje masarautar fuld'e sukayi magana da lamid'o akan Haddiyal, kana kuma ya fara nuna masu munin abunda suke aikatawa.

Sosai Bir yake cikin damuwa tun adaren jiya, saboda sanin da yayi na gobene ranar da za'ayi shad'i, sai dai kuma tuni ya riga ya yanke hukuncin tafiya masaratar fuld'e a gobe, ta yadda harya tanadi kud'in mota ba tare da kowa ya sani ba.

A cikin Masarautar Wasai b'angaren Yarima Asad kuwa, sosai yake cikin matsananciyar damuwa, saboda fargabar da yake na karyaje goben ya fad'i.

Acan jahar kagul cikin masarautar fuld'e kuwa, sosai Gimbiya Haddiyal take cikin matsanancin tashin hankali tare da fargaba, saboda bata sani ba ko Gid'ad'o am d'inta zai zo d'in ko kuwa zaik'i zuwa, hakanne ya sanya gaba d'ayanta ta rame ta fige sosai, kana kuma jikinta yayi bala'in sanyi, saboda nasihohin da Sheikh Ahmad yayi mata a lokacin da sukazo da suka tsaya a cikin zuciyarta.

Da dare kuwa yayi gaba d'aya kasa rintsawa tayi kwata-kwata.


Washegari.

Sosai mutane na garuruwa da dama da suke a k'ark'ashin Masarautar Fuld'e harma da mak'otansu tare da jama'ar Masarautar Yamma suka cika filin shad'i.
Yayinda a gefe-da gefen filin kuma aka a jiye kujeru wa'yanda Lamid'on Yamma tare da Lamid'on Fuld'e suke zaune akai.

Misalin k'arfe goma na safe motar jama'ar masarautar wasai ta k'araso cikin masarautar Fuld'e.


Motoci ukku sukayo, wa'yanda mutanen cikinsu kuma suka had'a da Babban Yaya, Galadima, Wambai, tare da Waziri, sai kuma d'ayar motar Yarima Asad ne da kuma Al'amin d'in sa.
Yayinda ta k'arshen kuma take cike da Dogarai.

Tarbar mutunci sosai suka samu, tukun akayi musu jagora zuwa filin Shad'in da yake cike dank'am da mutane.

Cikin tsantsar sanyin jiki da matsananciyar fad'uwar gaba Yarima Asad yake tafiya, yayinda Al'amin shima kuma jikinsa yayi bala'in sanyi.
Bai san dalilin daya sanya kwata-kwata yaji baya jin tsoron Jauron Yamma ba sai na Bir.
Wanda hakan kuma shine ya sanya k'irjinsa yake ta dukan tara-tara.

Suna b'ullawa cikin filin yaji jikinsa ya d'auki 'yar rawa, saboda hango dan-dazon mutane da yayi a wurin.
Su kuwa su Babban Yaya akan kujerun da aka tanadar musu gaba d'ayan su suka zauna.

Alk'alin wasane yayi sanarwar za'a fara, dan haka ana buk'atar da su futo fili.

Lumshe idanuwa Yarima Asad yayi, yana mai tashi jiki a matuk'ar sanyaye ya hau kan k'aton dakalin da aka nuna masa, tukun ya fara baza idanuwansa dan yaga ta wurin da Bir zai b'ullo, amma sai kuma yaga Jauron Yamma ne kawai ya fito sanye da wasu kaya marasa nauyi a jikinsa.

A hankali ya sauke ajiyar zuciya, yana mai lumshe idanuwansa tare da fatan Allah yasa tinaninsa ya zamto gaskiya a cikin zuciyarsa.

Yana cikin wannan yanayinne kuma ya jiyo sautin muryar Alk'alin gasar yana mai fad'in.

"Zaki shire kayanki ne duka."

Da matuk'ar sauri kuwa ya bud'e idanuwansa yana mai watsa su akan fuskar mutumin da yaji yana fad'in ya cire kayansa.
Tukun daga bisani kuma ya janye idanuwan nasa daga kansa yana mai mayar dasu kan dandazon jamar da suke cike a filin.
Sannan ya taune lower lip d'insa da k'arfi, yana mai girgiza kansa, saboda haka nan kawai yaji bazai iya cire kayansa ba a cikin dandazon mutanen.

Yayinda Jauron Yamma kuma da yake rik'e da wasu irin sharb'a-sharb'an bak'ak'en bulalai da suke matuk'ar maik'o, suna wani irin motsi ya k'araso wurin yana mai cije leb'ensa na k'asa, tare da kafe Yarima Asad da idanuwansa.

Ganin da Al'k'alin gasar yayi Yarima Asad bashi da niyyar cire kayansa ne, ya sanya sa fad'in.

"Ko baki shirya bane ba ana ki shire kayanki kinyi shiru kina kallon mutane?"

Amma still dai baiko motsa daga yadda yake ba.
Hakan da Babban Yaya ya ganine ya sanyasa mik'ewa da sauri, yana mai tawowa ya hayo kan dakalin.
Kana ya matsa kusa da Bir yana mai rad'a masa cewar.

"Kacire mana k'anina, ko kuwa ka hak'ura ka barmasa itane kawai mu tafi?"

Rumtse idanuwansa yayi da azabar k'arfi, kana ya fara b'alle mab'allin doguwar rigar shaddar da take sanye a jikinsa, tukun ya mik'awa Baban Yaya ita, sannan kuma a hankali, kana kuma cikin rawar hannu da bugun zuciya ya zame farar singilet d'in da take sanye a jikinsa ya bawa Babban Yaya itama.
Tukun yayi tsaye ba tare daya cire wando ba.
Hakan da Babban Yaya ya ganine ya sanyasa sake fad'in.

"Saura dogon wandon Asad, dan haka kayi maza tun kafin suce an fasa da kai."

Aikuwa da k'arfi ya sake rumtse idanuwansa.
Kana ya d'ora hannunsa akan zariyar wandonsa yana mai zageta, tukun ya durk'usa yana mai cire dogon wnadon yayi saura daga shi sai farin boxer'n da ya d'an kama jikinsa kawai.
Wanda hakan kuma ya sanyasa jin wata irin matsananciyar kunya, wacce ko kad'an bai sansa da itaba ta lullub'esa, saboda duk iskancinsa ko mata baya bari suga jikinsa kome zaiyi da kaya a jikinsa yake yi shi.

'Dauke wandon ma Babban Yaya yayi yana mai juyawa jiki asanyaye ya sauka daga kan floor d'in.
Yayinda gaba d'aya ilahirin jama'ar da suke a wurin kuma suka sauke k'wayoyin idanuwansu akan jikin Yarima Asad.

Kusan gaba d'aya rabi da kwatan mutanen wurin tun kafin a fara suka tabbatar daya fad'i, saboda farar fatarsa da suka gani tana futar da wani irin k'yalli, ga wata irin lallausar bak'ar gargasa da tayiwa ilahirin jikinsa k'awanya, mussamanma kuma k'irjinsa da tafi yawa duka anan d'in, kana kuma ta gangara har zuwa k'asan cikinsa, babu alamun tabo ko d'aya a gaba d'aya ilahirin jikin nasa.

Shi kuwa Jauron Yamma wani irin murmushin gefen baki yake saki yana mai sake cizon leb'ensa na k'asa, domin kuwa iyakar raini ya raina wannan farar halittar da yake tsaye a gabansa.
Yayinda shi kuma Yarima Asad ya bud'e idanuwansa yana mai kallon k'asa, saboda hakanan kawai yaji bazai iya kallon jama'ar da suke tsaye a wurin ba a cikin yanayin da yake.

Ko kad'an baiji lokacin da alk'alin gasar ya busa farawa ba, sai kawai sautin tashin kayan kid'a da yaji sun cika kunnuwansa, kafin daga bisani kuma yaji wata irin matsananciyar azaba ta tsarga gaba d'aya ilahirin jikinsa.
Amma sai dai ko gezau baiyi ba daga yadda yake.

Shi kuwa Jauron Yamma cikin tsannin mugunta da jin tsanarsa ya sake d'aga mahaukatan bulalansa da suke wani irin motsi, yana mai mai sauke su akan gadon bayan Asad.

Da k'arfi ya taune leb'ensa na k'asa jikinsa na d'aukar wata irin kyarma, yayinda wani irin jini kuma yayi tsartuwa daga jikinsa.
Bai gama futa daga cikin yanayin wannan azabarba ya sake jin saukar wata da tafi ta baya rad'ad'i a jikinsa.
Wanda hakan kuma ya sanyasa rumtse tafin hannunsa da k'arfi, yayinda farin wandon jikinsa kuma tuni ya koma jajahur da jini.

Shi kuwa Jauron Yamma ganin da yayi har yayi masa biyar ba tare daya gudu ba ko kuma yayi kuka, yasa daya tashi yi masa ta shida yayi wata irin dagewa har yana daka tsalle, tukun ya sauke masa ita a tsakiyar gadon bayansa ta zagoya har zuwa kan cikinsa.

Ohhhhh!!!
Yarima Asad ya futar da wani irin sauti, saboda matsananciyar azabar da yaji ta ratsasa, yayinda gaba d'aya ilahirin naman jikinsa kuma yake karkarwa, su kuwa yatsun k'afafuwansa wani irin motsi sukeyi tamkar zasu cizge su fuce.
Wata irin azaba yake ji tana ratsa ilahirin jiki da b'argonsa aduk lokacin da bulalar ta sauka a jikinsa.

A lokacin kuwa daya sauke masa ta goma shabiyar a gadon baya, wata irin k'ara ya saki jikinsa na sake d'aukar kyarma.
Yayinda wani irin jini kuma ya sake yin tsartuwa tare da feshi a jikinsa.

Da k'afi Babban Yaya ya rumtse idanuwansa jikinsa na d'aukar kyarma, saboda wata irin tsartuwar jini da yaga jikin k'anin nasa na futarwa.
Yayinda Al'amin kuma ya saki wani irin gigitaccen kuka yana mai mik'ewa tsaye a zabure.

Ganin hakan da Babban Yaya yayine ya sanya damk'ar tafin hannunsa yana mai girgiza masa kai, tukun saiga hawaye nan shima sun tsinke daga idanuwansa.
Yayinda Al'amin kuma yake kuka tun k'arfinsa yana mai kallon yadda jikin Abokinsa ke zubar da jini.

"Dan Allah ka barni naje kashe mana shi yake son yayi Yayanmu."

Al'amin ya fad'a cikin kuka yana mai shirin k'wace hannunsa.

"A'a K'anina bazai kasheshiba ka zauna kaji."
Babban Yaya shima ya fad'a yana mai sake damk'ar hannunsa.

Su kuwa su Galadima shiru sukayi kawai suna masu kallon Yadda ake jibgar d'ansu tamkar jaki.

Acan kuwa kan dakali sosai tsoro ya fara kama Jauron Yamma, saboda ganin da yayi har yanzu da yayi masa ta ashirin baiyi k'walla ba, shida mahaifinsa ya basa tabbacin cewar yayi dauriyar dunjya ya jure biyu a ta ukku dole ya gudu, hakan kuwa shine ya k'ara harzuk'asa, ta yadda daya tashi yi masa ta ashirin da d'aya ya zage gaba d'aya ilahirin k'arfinsa, tukun ya sauke masa ita.

Baya kuwa Yarima Asad yayi taga-taga tamkar zai kifa k'asa, sabo da tsananin azabar da yaji ta sake ratsasa, sai dai kuma ta ashirin da biyun da ya sake sauke masa ce ta sanyasa dawowa yadda yake cikin tsananin jigata.

Da sauri shi kuwa Al'k'alin gasa da yake tinanin k'walla ta ciko a cikin idanun Yarima Asad yace a tsaya.
Tukun ya matsa kusa da Yarima Asad yana mai kallon cikin jajayen idanuwansa da suka koma tamkar jini tsabar azaba.

"Aradun Allah iddonta baiyi ruwaba."

Ya fad'a yana mai ja baya, wanda hakan kuma ya sanya duk wani da yake tare da Jauron Yamma firgita hatta da Lamid'onsu kuwa.

Shi kuwa Jauron Yamma da yake jin tsanar Asad na sake turnuk'e zuciyarsa, cikin tsantsar mugunta ya sake d'aga bulalar yana mai sauke masa ta ashirin da shida akan k'eyarsa ta zagayo ta sauka har gadon bayansa, tukun ta b'ullo kan cikinsa.

"Wayo Abbannnnhhh wuhhhhh!!!"

Yarima Asad ya fad'a cikin tsanin gigitar da bulalar ta saukar masa da d'an k'arfi leb'ensa na rawa tamakar zasu cizge.
Sai dai kuma kafun ta gama sakinsa yaji wacce ta zarce gaba d'aya sauran bala'i da masifar zafi, domin kuwa ita ba iya kar fatarsa ta sauka ba, hatta da zuciya da k'wak'walwarsa sai da ta tab'asu.
Kasancewar daya tashi yi masa ita k'arshen k'arfinsa ya saki yana mai zuba masa ita a gadon baya, take kuwa ta zagayo tana mai sauka akan al'aurar gabansa.
Wanda hakan kuma ya sanya sa jin numfashinsa na shirin d'aukewa gaba d'aya, kana komai nasa ya tsaya cak hatta da rawar da jikinsa yake yi, sai wani irin gumi da yay bala'in yanko masa ta ko ina, yayinda idanuwansa kuma suka tsattsafo da r...............!!!✍



*NA KWANA BIYU NE.*


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*27*



Saman fatar idanuwansa kuma suka tsattsafo da ruwan gumi sosai, yayinda cikin idanuwan nasa kuma suka sake yin matuk'a ja tamkar jini.
Banda aikin muzurai babu abun da yake iyayi.

Sosai Jauron Yamma da duk wani makusancinsa suke sakin murmushi, domin kuwa su duk a tananinsu k'walla ta sanyasa komawa haka, wanda hakanne kuma ya sanya Alk'alain gasa ya matso kusa da Yarima Asad yana mai hulla nasa k'wayoyin idanuwan cikin jajayen nasa.
Kafin daga bisani kuma ya d'ago yana mai fad'in.

"Aradun Allah wanga ta shanye duka tsumagiyan shad'i daga wurin Jauron Yamma ba tare da ko d'igon kwalla sun futa ba."

Heyyyyyyyyyyyy!!! Kake jin wani irin ihun masoyansa da yayisu a wurin da tsananin k'arfi, yayinda makad'a kuma suka canza salon kid'ansu.

Shi kuwa Jauron Yamma cikin tsanin firgici da tashin hankali yayi watsi da bulalan hannunsa, yana mai girgiza kansa.

Lokaci d'aya gaba d'aya idanuwansa suka rikid'e sukai jajajir.
Ji yayi kwata-kwata bai yadda da abunda Alk'alin gasar ya fad'a ba, hakanne ya sanya tafiya a wani irin haukace zuwa wurin da Yarima Asad yake tsaye har lokacin tamkar dutse, domin kuwa kwata-kwata ma shi bai san an gama bulalunba, kana kuma baiji maganar Alk'alin gasar ba, saboda yadda gaba d'aya komai nasa ya tsaya cak ta silar bulalar k'arshen da yayi masa.

Banda aikin k'ok'arin janyo numfashi babu abunda yake iyayi, ga kuma b'arin cikinsa da yaji yayi masa wata irin bala'in k'ullewa har zuwa gefe d'aya na mararsa.

Shi kuwa Jauron Yamma da sauri ya k'arasa wurin, yana mai watsa k'wayoyin idanuwansa a cikin na Yarima Asad, sai dai kuma tabbatarwa kansa da babu hawaye a cikin idanunsa da yayine, ya sanyasa ja baya cikin matsanancin fushi yana mai kaiwa iska naushi.
A kuma lokacin Babban Yaya da Al'amin suka hayo kan dakalin domin su janye Asad ganin da sukayi har yanzu yak'i ya motsa.

Shi kuwa Lamid'on Yamma a matuk'ar firgice ya mik'e tsaya, domin kuwa koda wasa bai tab'a tinanin akwai wani mahaluk'i da zai iya shanye bulalun shad'insu ba, sai gashi kuma yau ansamu, abun takaicin ma kuma Jauronsa shalelensa ne yayi amma ba ayi hawaye ba.
Yayinda Lamid'o Sulaiman kuma yake zaune a wurin da yake, gaba d'aya babu mai fahimtar yanayinsa, wato dai farinciki yake ko bak'in ciki, saboda Lamid'on Yamma dai amininsa ne, gashi shi kuma Sarkin Wasai abokin kasuwancinsu, wato dai akwai alak'a mai k'arfi a tsakaninsu.

Su kuwa Jama'ar Masarautar Wasai murmushi kawai suketa faman saki cikin matsanancin farinciki, yayinda jure bulalun da yayi kuma yasa su cikin matuk'ar mamaki.

A b'angarensu Babban Yaya kuwa, cikin tsananin tausayin k'anin nasa ya d'ora hannunsa akan kafad'arsa da take b'ace da jini yana mai d'an girgizasa.

Shi kuwa Al'amin ba tare daya damu da yadda jikinsa yake kaca-kaca da jini ba ya rungumesa da k'arfi yana mai sakin kuka.
Hakanne kuma ya sanya Yarima Asad ya dawo cikin hayyacinsa, saboda azabar da yaji ta ratsasa ta dalilin rungumar da Al'amin yayi masa, ta yadda har ya kasa jurewa yana mai sakin wani irin sauti, kyarmar da jikinsa yake yi na dawowa.

Dasauri kuwa Al'amin ya sakesa yana mai fad'in.

"Na famaka ko Aboki, sannu kaji."
Ya k'arasa maganar cikin kuka.

Shi kuwa Yarima Asad rumtse idanuwansa yayi da azabar k'arfi, domin kuwa kwata-kwata bai fahimci abun da Al'amin yace ba ma, saboda yadda yake jin wani irin azababben zazzab'i na lullub'esa, ga kuma ko wane wurin na jikinsa daya d'inke da azabar rad'ad'i.

Ganin da Babban Yaya yayi jikinsa na kyarma ne sosai, ya sanyasa kamo hannunsa yana mai jansa suka fara sauka daga kan dakalin, a kuma lokacinne alk'alin gasa yake sanar da ranar da zaiyi ramuwa shima.

Da sauri direbobinsu suka matso da motocin har kusa da wurin da jama'a suke, sannan Babban Yaya ya fara shiga ciki, tukun Al'amin ya temakawa Asad da yake ta faman taunar jan leb'ensa da k'arfi, kana shima ya shiga ya zamto sunsa sa a tsakiya, sai dai kuma duk da haka jikinsa bai fasa karkarwar da yakeyi ba, hakanne kuma ya sanya Babban Yaya d'aukar kayansa yana mai yafa masa su ajiki.

Dole duk wani mai imanin da zai gansa ya tausaya masa, domin ko hatta da zaman sai da dabara yayi.
A haka duk suka shish-shiga cikin motocinsu bayan sunyi sallama a mutunce da jama'ar masarautar fuld'e, suna masu d'aukar hanya.

Acan b'angaren Gimbiya Haddiyal kuwa sosai take cikin matsanancin tashin hankali da fargaba, ta yadda har ta kasa tsaye ta kasa zaune, sai faman kai kawo da take tayi a cikin d'akinta tana mai jin tamkar ta futa taje ta dubo taga ko Gid'ad'onta yazo.
Hak'ik'a taso komawa gidan a jiya, sai dai kuma nasihohin da Sheikh Ahmad yayi mata alokacin daya zone suke sanyaya mata gwiwa aduk lokacin data raya hakan a ranta, domin kuwa sosai ya mata bayani akan k'addara da kuma yadda ko wane al'amari yake zuwa a rubuce, kuma sosai ta tsorata alokacin da yake nuna mata abubuwan da takeyi tsaf idan ta mutu a haka wuta zata tafi, wanda hakan yasa tun a ranar yana tafiya taje ta k'one gaba d'aya kayan tsafinta cikin matsanancin firgici, ita kuwa sandar gado dama tana wurinsa tun waccan ranar.
Haka a b'angaren su Lamid'o suma bai tafiba sai da ya tabbatar da sun k'ok'k'one abubuwan tsafinsu, sannan kuma a k'arshe yayi musu alk'awarin dawowa dashi da tawagarsu ta Malamai.

To hakan shine yasa gaba d'aya takasa yin komai, sai dai kuma tun daga ranar take fatan Allah yasa Gid'ad'o ne mijinta ba wani ba a cikinsu.

Da sauri tayi bakin k'ofa harta na d'an had'awa da gudu-gudu, saboda jiyo motsin tawowa da tayi, sai dai kuma tun kafin ta k'araso Habu ya danno kansa cikin d'akin bakinsa d'auke da Sallama.
Hakan yasa cikin matsanancin sauri mai had'e da firgici tace masa.

"Ya zone Hamma Habu, ? Nasani Gid'ad'om am ya shanye bulalun ko?"

Cikin matsanancin tausayinta ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Kiyi hak'uri k'anwata, amma babu wani daya zo bayan Yarima Asad da kuma Jauron Yamma, kuma Yarima Asad ya shanye duka bulalun Jauron Yamma ba tare daya zub da k'wallaba."

Da sauri ta fara ja da baya tana mai girgiza kanta, a haka har ta koma bakin kujera.
Tukun ta fad'a kanta tana mai sakin wani irin gigitaccen kuka mai sosa zuciya da ruhi.
Shin me yasa zai mata haka? Me yasa ya zab'i ta rasa rayuwarta da a dakesa duk da irin wahalar da tayi a soyayyarsa?
Ta raya haka acikin ranta cikin wani irin matsanancin kuka na futar hayyaci.
Tukun daga bisani kuma ta cije leb'enta na k'asa da k'arfi, saboda tino wani b'angare na nasihar Shekih Ahmad data sakeyi, tana mai jin haushin kanta da kanta a yau, saboda haukar son wanda bata saniba da tayi.
Hak'ik'a bai mata adalciba, kuma daga yau zata fara k'ok'ari wurin ganin ta mantasa, duk da dai tasan hakan tamkar dai-dai yake da tsayawar bugun numfashinta.

Lokaci d'aya kuma idanuwanta suka fara hasko mata fuskar Yarima Asad, alokacin da yake kuka durk'ushe a gabanta cikin bainar jama'a, da kuma lokutan da yake mata magiya akan tasosa.
Tukun daga bisani kuma k'wak'walwarta ta fara tariyo mata yadda Jauron Yamma yake nuna mata gadara, tare da bata tabbacin ita d'in mallakinsace, asalima shi ko lallab'ata bai tab'ayi ba, sai dai ya nuna mata b'acin rai yayi tafiyarsa idan tayi masa maganar Gid'ad'o'n ta.
Wannan tinanin da tayine kuma ya sanyata jin ai gwanda Yarima Asad akan Jauron Yamma sau dubu a yau kenan.
Sai dai kuma ko kusa bata da alamun zata bar kukan da take, wanda hakan kuma da Habu ya ganine ya sanyasa fucewa daga cikin d'akin jiki asanyaye, saboda yasani bazata tab'a jin rarrashiba a halin yanzu.

Ita kuwa sosai tayi kukan har ya saukar mata da zazzafan zazzab'i, tukun ta k'udun-dune a cikin bargo idanunta na cigaba da zubar k'walla.


Misalin k'arfe hud'u na rana suka isa cikin Masarautar Wasai, zuwa lokacin kuma sosai jikin Yarima Asad yayi matuk'ar tsananta, yayinda ciwukan kuma sukayi tsami, ta yadda har sai da k'yar yake iya d'aga idanuwansa tare da jan numfashi.
Ai kuwa hakan ba karamin sake tayarwa dasu Babban Yaya hankali yayiba.

Kai tsaye Babban Yaya ya umarci direbansu daya huce dasu part d'in Mamy'nsu, yayinda su kuma su Galadima suka huce Fada.

Ana sanarwa Mai Martaba halin da ake ciki ya mik'e tsaye, kana ya bada umarnin aje a had'o magun-gunan ciwo, idan an gama a bawa Jakadiya ta kawo masa can b'angaren.

Da sauri kuwa wanda ya umarta da yin hakan ya tafi, yayinda shi kuma ya kama hanyar da zata sadasa da b'angaren Fulani, Fadawansa na biye dashi abaya suna masa kirarinsu na sabo.

Acan kuwa b'angaren su Babban Yaya kai tsaye suka huce da Yarima Asad d'akinsa, Mamy na biye dasu abaya gaba d'aya hankalinta atashe, saboda ganin yadda d'an nata ya koma.

Suna shiga ciki ta huce bathroom tana mai zuwa ta had'a masa ruwan zafi, kana tacewa Babban Yaya ya shiga dashi ciki yayi wankan kafun akawo ruwan magani sai ya sakeyi dashi.

Hucewa kuwa yayi dashi d'in zuwa ciki yana dafe da kafad'arsa, yayinda Al'amin kuma ya zauna anan kusa da Mamy yay shiru yana mai jin tausayin Abokinsa.

A cikin bathroom d'in kuwa suna shiga ciki Babban Yaya yacewa Yarima Asad.

"To nayi maka wankan ko kuma zaka iyayi da kanka ne?"

Turo masa baki Yarima Asad yayi tare da yamutsa fuska.
Hakan da Babban Yaya ya ganine ya sanyasa sakin dariya yana mai d'an dukan kafad'arsa, tare da fad'in.

"Wato mai hali dai baya fasa halinsa ko, to ni dama tausayinka nakeji amma tunda bakaso ni na futa waje sai ka futo to."

Ya k'arasa maganar yana mai fucewa daga ciki.
Tukun shi kuma Yarima Asad ya zame farin gajeran wandon da yayi kaca-kaca da jini daga jikinsa.
Kana kuma ahankali yakai dubansa zuwa wurin da bulalar nan ta sauka, saboda har yanzu jin b'angaren yake a wani irin d'aure.

Ganin da yayi babu alamun ciwo akai ne ya sanyasa fesar da iska, yana mai lumshe idanuwansa.
Kana ya durk'usa k'asa cikin cije baki tare da sakin k'ara da k'yar.
Kofin da yaga Mamynsa ta sanya masa a cikin bathoob d'in ya d'auka yana mai d'ebo ruwan mai zafi ya zubasa a jikinsa.

"Ohchhhh!!!"
Ya futar da wani irin sauti da d'an k'arfi, saboda azabar da yaji ta ratsa duk wuraren da yake a farfashen.
Kafin daga bisani kuma ya rumtse idanuwansa yana mai k'ara ciko kofin ya juyesa a jikinsa.

Shash-shake fuska yayi yana mai turo baki tamkar zai fashe da kuka, saboda ba k'aramun zafin ruwan yakeji a jikinsa ba, sai dai kuma hakan ya taimaka masa wurin raguwar rawar da jikinsa yake yi.

Lokaci d'aya kuma ya sake lumshe idanuwansa yana mai tuno had'uwarsu da Bir ta k'arshe, hak'ik'a bai tab'a tinanin da gaske yake ba abunda yace sai da yaga har sun baro wurin baije ba tukun ya yadda, hakan kuwa ya sanya lokaci d'aya yaji danasani da kuma nadamar gabaki d'aya rashin mutuncin da yayi masa da farko sun lullub'esa, saboda bai tab'a tinanin yana da kirki haka ba.

Abunda ya faru da har yasa Bir baije wurin gasarba kuwa shine.

A ranar da Sheikh Ahmad yazo ya sanarwa Babban Yaya abun da Yarima Asad yayi, sosai ya samesa yay masa kaca-kaca, kana kuma a k'arshe ya basa labarin ko wayene Bir d'in, sannan kuma ya shawarcesa da yaje ya basa hak'uri akan abunda yayi masa, k'ila hakanma ya sanya ya janye zuwa wurin gasar da yace zaije.

Sai dai kuma take a wurin yace Allah ya kiyaye kamarsa yaje yana bawa wani hak'uri, ina shi ba zaiyi hakan ba, ya dai ji kuma bazai sake zuwa gidansu yayi wani abunba.

Tashi kuwa Babban Yaya yayi ya bar wurin ba tare daya sake ce masa komai ba.
Yayinda shi kuma tun daga wannan ranar tsoron Bir d'in ya sake lullub'esa, haka kawai sai yaji zuciyarsa ta karye, ya dinga ganin tamkar idan yaje wurin shi zai cinye gasar, amma sai dai kuma duk da haka bai aminta da shawarar Babban Yaya ba har sai ana gobe za'ayi gasar, wato jiya da dare.

Tunda rana a jiyan kuwa yaji gabansa ya tsananta da fad'uwa, tsoron Bir ya sake turnuk'e zuciyarsa, ta yadda tun yana daurewa har hakan ya gagara, gaba d'aya jikinsa yay sanyi, tukun a k'arshe bayan an idar da sallar magariba ma kawai ya yanke hukuncin zuwa ya basa hak'uri ko Allah zaisa ya dace tamkar yadda Babban Yaya yace yayi, domin kuwa daya rasa Haddiyal gwanda uban kowa ya dena ganin girmansa da ajinsa har abada.

Cikin sauri-sauri harda d'an gudu-gudu ya k'arasa bakin motarsa yana mai bud'eta ya shiga.
Kana yayi mata key yana mai taketa a guje ya fuce daga cikin masarautar.

Cikin k'ank'anin lokaci ya iso unguwar Babban Zaure dai-dai gidansu Sheikh Ahmad.
Wanda hakan kuma yayi dai-dai da lokacin da Babban Yaya, Bir tare da Auta suka dawo daga masallaci.

Da sauri kuwa Asad ya bud'e murfin motarsa ya futo, wanda hakan kuma da Sheikh Ahmad ya ganine ya sanyasa tsayawa ba tare daya shiga ciki ba.

Shi kuwa Yarima Asad jiki a matuk'ar sanyaye ya k'araso wurin da Sheikh Ahmad yake kansa duk'ushe a k'asa.
Kana ya bud'e baki cikin sanyi, yana mai fad'in.

"Ina yini Malam."

"Lafiya k'alau, amma sai dai kuma ban shaida fuskarba."
Sheikh Ahmad ya fad'a yana kallonsa.

Hakan da Yarima Asad yajine ya sanyasa sake durk'usar da kansa k'asa, kana kuma cikin sanyi yace.

"K'anin Ciromane, dama nazone na baku hak'uri akan abunda ya

Please Login or Register in order to submit comment