Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

basu samu ba.

Mamakin kalaman ta na farko basu gama sakin sa ba ya sake tsinkayo sautin muryar ta cikin amo, tana mai cigaba da fad'in.

"To bari kaji, daga yau daga yanzu ina mai gargad'in ka da babbar murya, akan ko da wasa karka k'ara barin k'wayoyin idanuwanka su had'u da nawa, saboda na tsani mugun kallon da kake bina da shi, ballanta na kuma har kayi gigin sake rik'e wani sassa na jiki na.
Idan kuma har kabari hakan ta sake faruwa, to hak'ik'a hukuncin da zai biyo baya gare ka bamai dad'i bane ba, dan ko tsaf zansa allura na caccake k'wayoyin idanuwan, tamkar yadda zan iya gille tsintsiyar hannun da takobi, saboda jikin tsaftatacce ne, tamkar yadda kaga mai shi sanye da tsaftattaciyar tufa.
Hakan yasa mammallakin sa ma ya zamto tsaftatacce ba irin ka ba!
Dan ko jikin ya kasance na mutum d'aya ne, wato dai mutun d'aya ne ya dace ya rik'e sa.
Sannan kuma mutum d'aya ne ya dace ya kalle sa, saboda shine kad'ai zuciya ta aminta da shi, wato Gid'ad'o am!

Tamkar saukar ruwan dalma haka Yarima Asad yake jin dirar kalaman ta a cikin dodunan kunnuwansa.
Babu abun da yafi b'ata masa rai da soya masa zuciya face wani da yaji ta had'a sa da shi, wanin da ya riga yasan bai fisa da komai ba a duniya.

Take kuwa a wurin gaba d'aya yanayin sa ya sauya.
Idanuwansa suka kad'a sukayi wani irin jajahur.
Yayinda jijiyoyin kansa kuma suka futo sukai rad'a-rad'a akan goshin sa.
Gumi kawai ke yanko masa ta kowace kafar gashi dake jikinsa, yayinda gaba d'aya ilahirin naman jikin sa kuma ya d'auki tsuma, domin ko tunda yake a rayuwa ba a tab'a fad'a masa irin kalaman da ta jefe sa da su.
Bai tab'a jin ransa ya b'aci ba irin yau.

Kallo d'aya mutum zai yi masa ya fahimci halin da yake ciki, saboda yadda gaba d'aya kammanin sa suka sauya lokaci guda, ga wani irin zazzafan numfashi da yake fesarwa idanuwansa akan fuskar ta, saboda yadda yake jin k'wak'walwarsa na masa wata irin tafarfasa.

Da k'arfi ya rumtse idanuwansa a lokacin da yaji ta danganta wanda take cewa ya fishi da kalmar Gid'ad'on ta, kasancewar ya riga da yasan abun da kalmar ke nufi da shi tun yana k'arami.

Hakan yasa ko rufe bakin ta bai bari ta k'arasa yi ba ya fara d'aga k'afafuwansa yana mai tunkarar ta cikin matsanancin fushi.

Ganin hakan da Gimbiya Haddiyal tayi ne, ya sanya ta d'an fara d'aga k'afafuwanta, tana mai ja da baya daga wurin da take, tare da girgiza masa kai, tana mai masa alamar da kar ya k'araso wurin da take da idanuwanta da kuma kanta, amma sai dai kuma ko fahimtar abun da take nufi Yarima Asad baiyi ba, saboda yadda yake jin zuciyarsa na wani irin tafarfasa.

Cigaba da ja baya tayi yana mai binta harta had'e bayanta da k'atuwar bishiyar da take daga bayanta.
A kuma dai-dai lokacin shima Yarima Asad ya k'araso zuwa wurin, ta yadda har ya zamto ba wata tazara da tayi saura a tsakaninsu.

Da sauri Gimbiya Haddiyal ta d'aga idanuwanta tana mai sanya su a cikin nasa cikin tsantsar firgici, saboda yadda taga yana shirin had'e jikinta da nasa.
Kafin daga bisani kuma tayi wani irin juyar da kanta gefe, tana mai shirin zame jikinta ta gefe ta huce.

Lura da hakan da Yarima Asad yayi ne, ya sanya sa k'arasa manne jikinsa da nata gaba d'aya.
Kana ya d'aga hannunsa d'aya sama, yana mai kife tafin sa akan bishiyar, tukun ya d'an rank'wafo da kansa zuwa saitin fuskarta, ta yadda har zazzafan hucin da yake futarwa daga cikin bakinsa yake dukan fuskarta.

Da k'arfi Gimbiya Haddiyal ta rumtse idanuwanta, tana mai d'auke numfashinta, saboda yadda taji gaba d'aya ya sanya jikinsa ya matse ta da bishiyar nan, ga kuma idanuwansa da gaba d'aya taga sun rikid'e sun koma jajahur.
Kana kuma yana buso mata wani irin huci mai matuk'ar zafi akan fuska.

Wata irin muguwar tsanarsa taji na k'ara lullub'e zuciya da ruhinta.
Lokaci d'aya jikinta ya d'auki wata irin kyarma, yayinda take ganin fuskar Gid'ad'on ta a cikin mafarkinta, ta yadda har take jin tamkar ba tayi masa adalci ba da har ta bari waninsa ya had'a jikin sa da nata.

Shi kuwa Yarima Asad cikin tsantsar b'acin ran da ya turnuk'e zuciyarsa, ya kafe jajayen idanuwansa akan fuskarta.
Ji yake tamkar ya shak'e mata wuya ta mace gaba d'aya ko yaji sanyi a ransa.
Kafin daga bisani kuma ya d'aga lab'b'ansa cikin kakkausar muryarsa, yana mai fad'in.

"Da alamun baki san koni waye ba, shi yasa har kika iya bud'ar baki kika fad'amun k'azaman kalamanki, dan kawai kin samu na rik'e hannunki.
Shin kin san adadin yawan matan da suka dad'e suna muradin wa'yan nan idanuwan da kika samu suka kalleki su kallesu amma basu samu hakan ba?
Shin kin sa irin yawan matan da suke son ko farcen su ya gogi wani sashi na jiki na amma hakan bai samu ba.
Mata masu ji da kyawu, ilimi, kud'i, gayu!
Mata wa'yan da suka taso cikin gata, mata wa'yan da suka zaga duniya-duniya ta gansu suka ganta, mata tun daga kan larabawa, turawa har zuwa hausawa da gidadawa fulani irinki, amma hakan bata samu ba gare su.
Sai ke da kika samu har hannuwana suka rik'e naki, kana idanuwana suka shiga cikin naki, shine har zaki iya d'aga k'azamin bakin ki kina had'ani da wani can sha-sha-shan mutum.
Hak'ik'a da kin san koni d'in wane ne, da ko kallo na baki iya tsayawa kinyi ba, ballantana har ki bud'i baki ki fad'amun magan-ganun banza, saboda raina kanki da zakiyi tun a karon farko."

Ya k'arasa maganar yana mai cigaba da busa mata zazzafan hucin sa.

Da sauri itama ta bud'e jajayen idanuwanta akan fuskar sa, saboda yadda taji ya kira Gid'ad'onta da sha-sha-sha.
Wanda hakan kuma ya sanya ta sake jin tsanar sa sama da ta kowa da komai da yake a cikin duniya.

"Waye kai d'in? Waye kai bayan d'an iskan kan hanya!
Su kuma matan da kake fad'i, ina so ka sani gaba d'ayan su Jakai ne! Babu d'aya daga cikin su data mallaki koda rabin abubuwan daka dangantasu da su da gaske, domin kuwa duk wata mace da ta cika mace, kana kuma ta amsa sunanta na 'ya mace ba zata tab'a mararin samun namiji irin ka ba."

Ta fad'a cikin zafi itama idanuwanta a cikin nasa.
Yayinda shi kuma Yarima Asad ya rumtse idanuwansa da matuk'ar k'arfi, jikin sa na cigaba da karkarwa.
Tukun ta janye idanuwanta daga kan fuskarsa, tana mai mayar da su k'asan sa saitin wuraren k'afafuwansa, wato kan wandon jikin sa.
Kana ta sake d'ago kan nata tana mai mayar da idanuwanta har zuwa kan sumar kansa, wato dai tayi masa kallon sama da k'asa.
Sannan ta sake d'aga lab'b'anta tana mai fad'in.

"Ka dubi kanka fa ka gani, har ina wani abun burgewa yake a tattare da kai.
Ko-ko ba irin wannan suturar bace 'yan iskan 'ya'yan turawa suke sanyawa a jikin su?"

Jin hakan da Yarima Asad yayi ne, ya sanya sa d'an ja baya da sauri, yana mai bud'e idanuwansa yabi jikinsa da kallo tun daga sama har k'asa, tamkar yadda tace masan yayi cikin tsantsar mamaki, domin kuwa tun da yake a rayuwa bai tab'a had'uwa da macen data kushe suturarsa ba sai wannan 'yar k'auyen.
Yayinda Ita kuma Gimbiya Haddiyal ta d'an kauce daga jikin bishiyar, tana mai sakin numfarfashi tamkar wata zakanya, saboda matsawar da yayi daga jikinta.
Kana ta d'ora da fad'in.

"Shi kuma wanda kake kira da sha-sha-sha, ina son kasani yafi mun kai sau dubun-dubbai, domin kuwa shi d'in ya kasance mutum na k'warai ne, kana kuma kamilalle kyakkyawa mai daraja.
Shine mutumin da ya zamto komai nawa a halin yanzu, idan kuma nace komai ina nufin komai d'in, wato tun daga kan farinciki na, murmushi na, dariya ta, har zuwa kuka na, atak'ai ce dai shine duniya ta gaba d'aya, tamkar yadda ya zamto zuciya ta.
Ina son sa, ina son sa fiye da yadda nake son rayuwata, haka kuma ina tsanar duk wanda ya nuna baya son sa, ko kuma ya nemi ya kusanto ni a matsayi na na mallakin sa, saboda kishin da nake taya sa da shi.
Dan haka ina son kasani kai d'in ba kowa bane a wuri na.
Baka birgeni ba, kuma ba zaka tab'a birgeni ba har abadan-abada.
Kana kuma na tsane ka tamkar yadda na tsani mutuwata, dan haka kaje kaji da sha-sha-shan 'Yammatan ka, daga yau karka k'ara gigin kallon ko k'ura ta, ballantana har ka kusanto kanka da ni!"

Ta k'arasa maganar da sakin huci, tana mai juyawa ta tafi ta barsa a tsaye tamkar dutse, ba tare da ta tsaya jin abun da zai k'ara cewa ba, domin ko a halin yanzu babu sautin da taji ta tsani saurara a duniya sama da sautin muryarsa.

Shi ko Yarima Asad tun lokacin data sake kiran sunan Gid'ad'on ta yaji gaba d'aya komai na sa ya tsaya da aiki, sai zuciyarsa kawai da take wani irin bugu tana tafarfasa tamkar zata hudu k'irjin sa ta futo waje.

Da k'arfi yake jan numfashi, yana mai jin wani irin abu mai nauyi tamkar dutse ya tsaya masa akan k'irji.
Yayi nadamar dawowarsa cikin Masarautar nan yafi sau dubu daga lokacin data fara fad'a masa mugayen kalamai har kawo yanzu a zuciyar sa.

Ba shi ya iya motsawa daga wurin da yake a tsaye ba har sai da ya dena hangen Gimbiya Haddiyal gaba d'aya.
Tukun ya rumtse idanuwansa da matuk'ar k'arfi, jikinsa na wata irin tsuma.
Kafin daga bisani kuma ya kaiwa iska naushi, yana mai sakin huci, tamkar kumurcin zakin da yaga abun farauta a gaban sa.

Ko a mafarki bai tab'a tsammanin zuwan wannan ranar gare sa ba, ranar da zai kai kansa gaban wata 'ya mace har ta tsaya ta jefe sa da munanan kalamai, ranar da zai zubar da mutuncinsa da k'imarsa, ranar da kwarjin sa da haibar sa zasu zube a k'asa wanwar, ranar da shi da kansa zaiji kunyar kansa, sai gashi yau ta riske sa.
Hak'ik'a yau d'in ta zamto rana mafi muni daga cikin ranakun da yayi a rayuwarsa, ranar da bazata tab'a shafewa ba daga cikin zuciyarsa.

Tabbas da ciwo mutimin da ka raina, kake ganin bai kai ba ya tsaya a gaban ka yana fad'a maka mugayen kalamai.
Wai yau shi Asad ne aka samu 'ya macen data bud'e baki ta zage sa tace masa baiyi ba, kana ta yabi wani Banza Wawa Jaki akan sa.
Shi Asad da mata ke rububin ya kalle su ya rab'e su, yau aka samu wata d'iya macen da tace karya k'ara kuskuren tab'a ta da k'azamin hannunsa, shi Asad da dubban 'Yammata suke rububin yace yana son su basu samu ba, yau aka samu wacce ta bud'i baki tace ta tsane sa sama da kowa da komai a duniya.

"Shin me nayiwa rayuwa ne da take shirin juyamun baya?
Me nayiwa duniya da take shirin kifar da ni? Me yasa zuciya zakiyi mun haka? Me yasa zaki kawo ni wurin da bai kai nazo saba, har kuma aka samu wacce ta zage ni a cikinsa.
Tace wani Jaki can Dak'ik'in mutum ya fini, kana ta danganta ni da k'azanta.
Wai nine mai k'azamin hannu ni ni Prince Asad."

Ya k'arashe maganar da d'an sauti, kana cikin wani irin b'acin rai, yana mai bin hannun nasa da kallo tare da neman abun k'azanta akan sa.
Amma sai dai ko kad'an bai gani ba.

Be san mene so ba, sannan kuma bai san ya masu yin sa suke ji ba, saboda bai tab'a yi ba, sai dai ayi akansa, amma a yau a kuma yanzu ya tabbatar da shima zuciyarsa ta kamu da soyayyar wata.
Watan ma kuma bagidajiya 'yar k'auye mara ilimin addini dana zamani, watan ma kuma wacce batasan darajarsa ba, kana kuma babu alamun zata daraja sa ko anan gaba.
Ya gane ya kamu da son ta ne saboda yadda yaji har yanzu zuciyarsa ta kasa ganin bak'in ta tamkar yadda yake so ta gani.
Sai dai kuma ya k'udiri aniyar daga yau daga yanzu bazai k'ara doso ko hanyar wannan bak'in garin ba, ballantana kuma har ya kawo kansa cikin Masarautar nan, ko da kuwa rashin zuwan nasa zai zamto ajalinsa ne.
Domin kuwa bazai tab'a iya jurar d'aukar hulak'anci ba daga wurin wacce yake ganin bata kai tako tsaya a gaban sa ba.

Tabbas idan ya futa daga cikin Masarautar nan ya mata futa ta k'arshe har abadan-abada, domin kuwa bazai tab'a iya jurar sake had'a idanuwansa dana waccan fitsararriyar Yarinyar ba.

Ya raya hakan a cikin ransa, yana mai jin yadda zuciyarsa ke cigaba da tsalle.
Yayinda idanuwansa kuma suke a rikid'e babu kyan gani kwata-kwata, goshinsa kuwa d'auke yake da rad'a-rad'an jijiyoyi akan sa tamkar zasu hudo fatar wurin su bayyana a fili.

A hankali, kana kuma cikin sanyin jiki ya fara d'aga k'afafuwansa yana mai dosar wurin da ya baro ya tawo nan d'in, wato ya koma baya kenan.

So yake ya saita kansa gudun kar Habu ya gane yanayin da yake ciki, amma yaji gaba d'aya ya kasa, domin kuwa har yanzu bai fasa sakin hucin da yake saki ba.

Babu abun da ke sake hautsina masa rai sai kalaman ta da tace Gid'ad'on ta shine komai nata, kana kuma ya fiye mata shi sau dubun-dubbai.
Wa'yan nan kalaman sune suka zauna daram a cikin k'wak'walwarsa, domin ko har yanzu amsa kuwwa kawai suke masa a cikin kunnuwansa.

Wai kamar shi Asad ne har zatace wani ya fisa, tabbas yarinyar nan ta gama da shi a rayuwa, amma bakomai, sai idan ta k'ara ganinsa ma ballantana har ta sake fad'in wani ya fisa, kana kuma ta tsane sa.

Ya raya haka a cikin ransa yana mai k'arasawa bakin kujerar nan daya tashi daga kanta.

Sosai yaji dad'in rashin ganin Habu da baiyi ba a wurin, domin kuwa ya san da ace ya dawo wajibi ne ya tambayesa abun da ke damun sa, saboda ko da yanzu mutum ya fara ganin sa dole ne ya fahimci yana cikin b'acin rai.
Sosai yake jin kansa na sara masa tamkar ya rabe gida biyu.

Zama yayi akan kujerar yana mai sa tafin hannunsa ya dafe goshinsa da shi, tare da lumshe idanuwansa yana sakin numfarfashi.
Sosai yake son yaga ya kawar da damuwar fuskarsa gudun kar Habu ya gane, amma abun ya citura, sai dai kuma duk da haka ya d'an rage jin zafin da yake ji a zuciyar sa.

Zaman sa baifi da minti biyar ba a wurin ya fara jiyo motsin tawowar mutum zuwa wurin da yake.
Sanin da yayi babu wani da yake tsammanin zuwan sa wurin a yanzu face Habu ne, ya sanyasa fara dai-dai ta nutsuwarsa, ba tare da ya d'ago kansa ba.

"Sorry fa Bro kaga na jima ban dawo ba ko?"

Yaji muryar Habu na fad'in haka adai-dai saitin kansa.

Hakanne yasa ya d'an janye tafin hannunsa daga kan goshinsa a hankali, sannan ya d'ago kansa yana mai k'ak'alo murmushin yak'e ya yafa akan fuskarsa tare da fad'in.
"A'a ai babu komai 'Dan uwa."

Ya k'arasa maganar da sake lumshe idanuwansa, gudun kar Habu ya gano halin da yake ciki.
Yayinda shi kuma Habu yayi shiru ba tare da ya k'ara cewa komai ba, sai idanuwansa da ya zuba akan fuskar Yarima Asad, yana mai nazartar yanayinsa, domin ko muryar sa kawai yaji ya fahimci kamar yana da damuwa, ga kuma launin idanuwansa da yaga tamkar sun canza ba kamar lokacin da suka rabu ba.

Jin alamun idanun da Yarima Asad yayi akan fuskar sane ya sanya sa bud'e idanuwansa akan fuskar Habu, yana mai k'irk'iro murmushin yak'e wanda masu iya magana ke cewa yafi kuka ciwo, tare da fad'in.

"Ya dai da kallo haka Aboki."

Gwauron numfashi Habu ya sauke, yana mai janye idanuwansa daga kan fuskar Yarima Asad.
Kana daga bisani ya bud'e baki, yana mai fad'in.

"Amma sai naga kamar kana cikin damuwa ko, saboda gaskiya ba haka na tafi na barka ba?"

Ya k'arasa maganar yana mai zama a gefen Yarima Asad.

Shiko Yarima Asad sake lumshe idanuwansa yayi, yana mai jin yadda har lokacin zuciyarsa ke masa ciwo, kana daga bisani ya bud'e su yana mai cewa.

"Wallahi kaina ne ke d'an yi mun ciwo shi yasa, amma karka damu nasan da zarar na sha magani zai sauka."

"Subahanallahi, to gaskiya tashi muje kasha maganin tun kafin abun yayi nisa."

Cewar Habu yana mai mik'ewa tsaye daga kan kujerar da yake.

"A'a ka barshi kawai akwai magani a cikin mota, idan na shiga na sha."

Cewar Yarima Asad ba tare da ya motsa ba daga wurin da yake a zaune.

"To Allah ya kawo sauk'i, amma kaga abun da kake neman kuwa?"
Habu ya fad'a yana mai kai idanuwansa k'asa.

"Ai ina ganin ba anan d'in na barsa ba gaskiya."
Cewar Yarima Asad acan k'asan mak'oshi.

Habu na shirin sake yin magana wayar sa ta d'auki ruri.
Hakanne yasa sa yin shiru, yana mai kai idanuwansa kan screen d'in wayar.

Number Al'amin da ya gani tana yawo akan screen d'in wayar ne ya sanya sa d'an zaro idanuwansa, yana mai komawa ya zauna a wurin da ya tashi, wato kusa da Yarima Asad.
Tukun ya juya b'arin da Yarima Asad yake baki a washe yana mai fad'in.

"Kaga d'an rainin hankalin shine ke kira yanzu, bara na d'aga naji abun da zaice bayan yak'i biyo ka kuzo tare."

Ya k'arasa maganar da yin pickin d'in kiran, yana mai kai wayar kan kunne sa ba tare da ya jira jin abun da Yarima Asad zai ce ba.
Yayinda shi kuma Yarima Asad ya d'ago kansa da sauri, yana mai watsa idanuwansa akan fuskar Habu, gaban sa na wata irin mahaukaciyar fad'uwa, saboda jin furucinsa da yayi, wanda yasa ya fahimci kowane ne ya kira san, wato Al'amin d'in da ya gama cewa yak'i biyo sa, saboda ya riga da ya sani shikenan asirin sa ya tonu yanzu kuwa.

Shi kuwa Habu cikin d'an d'aure fuskar yace.

"Assalamu alaikum shugaban marasa kirki na Africa."

Acan b'angaren Al'amin kuwa da sauri yace.

"Please kayi hak'uri Abokina tuba nake, dan ko kai kanka kasan bazank'i d'aga wayar kaba haka kawai, lokacin da ka kira jiyanne nayi bacci, saboda gajiyar da muka kwaso, sai yau da safe bayan na gama break fast da na d'auki wayar nake ganin misscall d'inka."

Ya fad'i haka cikin sauri, kasancewar jiya da Habu ya kirasu yayi musu ya suka sauka gaba d'ayan su basu samu damar d'aukar wayar tasa ba, shi yasa yanzu yay zaton abun da yake nufi kenan.

Shi ko Habu cikin sauri yace.

"Eh na yadda da wannan, kuma nima dama na kawo hakan tun jiyan, amma itama yau d'in duk gajiyar jiyan ce tasa kace ba zaka zo ba ko?"

"Kamar ya yau kuma nace bazan zoba Habu?"

Al'amin ya fad'i haka da sauri cikin rashin fahimtar inda batunsa ya dosa.

"Kaji d'an rainin hankali, to wallahi ka sani babu abun da zakace na aminta, dan haka kama dena shirin wani waskewa, domin kuwa Prince ya sanar mun da duk yadda kukayi da shi."
Cewar Habu yana mai jiran yaji abun da Al'amin zai sake fad'e.
Yayinda shi kuma Yarima Asad ya kasa koda k'wak'waran motsi daga yadda yake, saboda jin abun da Habu ke fad'e.

A b'angaren Al'amin kuwa da sauri ya sake fad'in.

"Asad kuma, a yaushe Asad d'in yace maka haka, kai nifa har yanzu ban gama fahimtar inda zancen ka ya dosa ba wallahi?"

"To dama taya zaka fahimta tunda kana son ka kare kanka, dan haka bara na yi maka dalla-dalla yadda zaka fahimta, sai kuma naji abun da zakce a gaba.
To kasani da kace ba zaka rakosa ba gashi nan ya iso lafiya, kuma yanzu haka ma gani gashi zaune muke a wuri d'aya yana mai jin abun da kake fad'e.
Dan haka ina son kasani nima duk randa nazo to karkayi zaton wurinka nazo, domin kuwa hurin Asad kawai nima zanzo, dan haka karma kace zaka kulani."

Da k'arfi Yarima Asad ya rumtse idanuwansa, saboda fahimtar da yayi na asirin sa ya riga da ya gama tonuwa a wurinsu su duka biyun.

Shi kuwa Al'amin cikin tsantsar mamaki da aljabin da ya kamasa ta sanadin kalaman da yaji sun futo daga bakin Habu yayi shiru, yana mai zaro idanuwansa waje ba tare da ya iya cewa komai ba, saboda zuwa yanzu ya riga da ya gama fahimtar inda zancen Habu ya dosa, wato dai wurin da Yarima Asad ya tafi d'azu kenan, shiyasa ma har yak'i kulasa yana kallonsa, saboda kar yasan inda zashi, shine kuma da yaje ya shirgawa Habu k'aryar cewar shi yace bazai biyo sa ba.
"To uban me ya mayar da Asad Masarautar Fuld'e a yau kuma, bayan kuma babu kalar kushewar da bai yiwa garin ba a jiya?"

Ya fad'i haka a cikin ransa, har lokacin wayar tana mak'ale a kunnen sa ba tare da ya katse ta ba.
Tuno abun da ya faru a jiya tsakanin 'yar fulanin da sukaji an kira da Haddiyal da Yarima Asad a jiyan da yayi ne, ya sanya sa jinjina kansa, yana mai tabbatar da zargin da yake yi.

"Malam ya kayi shiru, wato ka rasa abun fad'e tunda kaji na k'uro ka kenan ko?"

Yaji muryar Habu ta daki dodon kunnensa yana mai fad'in haka.

Hakan yasa ya dawo daga duniyar tinanin da ya tafi, yana mai cewa.

"A..a.. aboki... Ba haka nace....masa ba, kawai dai ya fad'a ma hakane, saboda ya had'ani da kai, amma ai kai da kanka yaci ace ka gane k'arya ya tsula maka bazan iya fad'in haka ba."
Al'amin ya samu kansa da fad'in haka a d'an daburce.

"To ka fad'i gaskiyar mana idan har ba hakan bane ba."
Habu shima ya fad'a cikin dariya yana mai ganin ai yariga da ya gama k'uro Al'amin.

Shi kuwa Al'amin haka nan kawai yaji gwanda ya rufawa Abokinsa kuma d'an uwansa asiri, tunda har ya riga da ya tsula k'aryarsa da farko, sai dai kuma yana nan yana jiran dawowarsa yasin saiya yi masa bayanin abun da ya mayar da shi wurin, domin kuwa Allah ya riga da ya toni asirin sa duk da yadda bayason ya sani d'in.
Hakan yasa sa fad'in.

"Kawai fa haka nace masa ya bari sai gobe mazo kar aga daga zuwan mu jiya mun dawo, shine kawai yayi shigewar sa mota ya rufe, ina masa magana yamun banza tare da take mota yayi gaba, kasan sa da bak'ar zuciyar tsiya, amma fa dan Allah kayi hak'uri kar kayi fushi dani ina nan zanzo nima."

Al'amin ya samu kansa da fad'in haka ba dan kuma hakan ta kasance ba, sai dan kawai ya rufawa Abokin nasa asiri.

"Tom shikenan sai anjima, mutumin harya mik'e na san tafiya zaice zaiyi."

Habu ya fad'a saboda ganin da yayi Yarima Asad ya mik'e har ya fara tafiya yana mai mik'ewa tsaye shima.

"To sai an jima, kace masa ina gaishe da shi, kuma ya tanadi amsar da zai bani kafun ya dawo, dan wallahi yau sai yayi bayani."

Al'amin ya fad'a yana mai kashe wayar sa ba tare da ya jira jin abun da Habu zai fad'a ba.

Shiko Habu murmushi yayi yana mai bin bayan Yarima Asad, tare da fad'a masa sak'on Al'amin da yace ya fad'a masan.

'Dan tab'e baki Yarima Asad yayi ba tare da yace komai ba, yana mai cigaba da tafiyar sa, saboda shi a yanzu gaba d'aya bata su yake ba, bak'in cikin abun da waccan yarinyar tayi masa ne kawai ke cigaba da tafasa mata rai.

Direct suka doshi wurin da motar Yarima Asad take daga nan wurin.

Har bakin motar Habu ya raka Asad yana mai fad'a masa cewar sai yazo shima, tukun sukayi sallama a daddafe bayan yacewa Yarima Asad d'in yasha maganinsa.
Kana Yarima Asad d'in ya fafari motar tasa da wani irin mahaukacin gudu, yana mai dosar hanyar get.
Yayinda Habu kuma ya zaro idanuwansa daga nan wurin da yake a tsaye, saboda irin gudun da yaga Yarima Asad ya tafi da shi.
Kana daga bisani ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Allah ubangiji ya tsare to."

Tukun ya juya jiki a sanyaye yana mai kama hanyar d'akin sa, saboda ba k'aramun firgita yayi ba da kalar tuk'in da yaga Yarima Asad ya tafi da shi.

A b'angaren Yarima Asad kuwa ji yake tamkar baya gudun a haka, duk da dai tini ya haye kwalta, saboda matsanancin gudun da yake
Ba shi da wani buri wanda ya huce ya gansa a cikin d'akin sa ko ya samu yaji sauk'in rad'ad'in da zuciyar sa take masa, gaba d'aya ji yake ya tsani, tsana irin mai tsananin nan, baya fatan abun da zai sake ko biyo da shi ta hanyar garin gaba d'ayan ta balle har ya k'arasa cikinsa.

Hak'ik'a ranar yau ta zama mummunar rana kuma Bak'ar rana a gare sa.
Haka ya cigaba da

Please Login or Register in order to submit comment