Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masu ɗaukar hanyar da zata mayar da su cikin gari, tamkar yadda suka tawo da shi da farko.

Basu suka barsa ba har sai da suka kaisa ɓangaren bayi, tukun suka yada shi a wurin suna masu juyawa suka koma filin biki.

Acan ɓangaren Gimbiya Tasmir kuwa tana shiga ɗakinta ta sake durƙushewa a ƙasa tana mai cigaba da rusar wani irin kuka mai cin rai da taɓa zuciya.
Idan kaga yadda take kuka sai ka rantse kace tarasa wani muhimmin abu ne a rayuwar ta wanda bazai taɓa dawowa gare ta ba, sabo da yadda gaba ɗayanta ta firgice, ga hawaye da ruwan majina da suka ɓata mata fuskarta gaba ɗaya.
Babu abun da yake sake dagula mata lissafi, sai irin yadda idanuwanta suka ƙi su dena hasko mata abun da ya faru, ga kuma yadda har yanzu zuciyarta take cigaba da yin irin bugun da take yi a duk lokacin da suka kasance a wuri ɗaya, ta yadda har take jin tamkar tana gaban sa har yanzu.
So take ta cire tinaninsa a cikin ranta, amma gaba ɗaya abun ya citura, hakan yasa take ta cigaba da rusar kukanta tana mai jin inama ace bata iske wannan ranar ba.
Ko a mafarki bata taɓa zaton za'a samu bawan da zai iya tsayawa a gabanta ba tare da ya tsorata ba, amma sai gashi a zahiri aka samu, kuma abun yazo mata a yadda bata taɓa zato ko tsammani bama.

Bata ita ta iya miƙewa daga durƙushen da take a wurin ba, har sai da taji wani irin sanyi ya lullube gaba ɗaya ilahirin jikinta, ta yadda har take karkarwa, haƙwaranta na gwaruwa da juna, wato dai matsanancin zazzaɓi ya rufe ta ruf a lokaci guda.
Hakan yasa ta fara rarrafawa daga wurin da take a hankali, tana mai nufar haɗaɗɗen gadon ta da yake ɗauke da wani irin bedsheet mai matuƙar ado da taushi.

Daƙyar ta iya hawa kan gadon, sabo da yadda take jin wani irin duhu na mamaye cikin idanuwanta, ta yadda har sai da ƙyar take iya ganin abun da ke a gaban ta.

Jan luntsumemen eskimon da yake akan gadon tayi tana mai lulluɓe jikinta da shi, har kuma lokacin idanuwanta basu bar zubar da hawayen baƙin ciki ba.
Ji tayi ko kaɗan bata fatan abun da zai sake sanyawa su sake cin karo da Bir, ballantana har ya ƙara kwatanta yin abun da yayi a yau, wato dai ba ƙaramun tsorata tayi da lamarin sa ba, kana kuma ta yadda zai iya yi mata komai, tunda har ya gwada haɗa jikin sa da nata, gashi kuma bata da ikon yi masa hukunci da take tunanin zai rabasu da shi har abada, sabo da yadda Baban ta ya taka mata birki a kansa, sai dai kuma duk da hakan tayi alƙawarin bincikar labarin sa domin ta wargaza farin cikin sa, tamkar yadda ya wargaza nata farin cikin itama.


*ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.*

Tunda suka tawo kan hanya har suka iso cikin Masarautar wasai Yarima Asad bai buɗe idanuwansa ba, kana kuma shi baiyi bacci ba, asalima ko gane sunzo baiyi ba sai da har Al'amin ya daki kafaɗar sa yana faɗin ya taso ya futo.
Sabo da yadda yayi nisa a tinanin Gimbiya Haddiyal.

Sosai ta tsaya masa a rai, kana komai nata ya zauna acikin ƙwaƙwalwarsa, babu abun da yake gani sai zubin hallitarta tare da kyawun fuskarta da surar ta a cikin idanuwan nasa har suka ƙaraso masarautar ta su.

Jiki a matuƙar sanyaye ya ƙarasa zuwa part ɗin su.
Ko da Gimbiya Fulani ta gansa a haka sai da ta tambaye sa abun da yake damun sa, amma sai yace mata ba komai kawai gajiyar hanyace ya kwaso.
Hakan yasa ta rabu da shi ba tare da ta ƙara ce masa komai ba.
Yayinda shi kuma ya huce zuwa cikin ɗakin sa.

Yana ƙarasawa cikin bedroom ɗin nasa ya cire rigar dake sanye a jikin sa yana mai yin cilli da ita, kana ya faɗa kan gadon sa yana mai kwanciya rigin-gine, idanuwansa akan rufin ɗakin.
Yayinda zuciyar sa kuma take acan cikin masarauatr fulɗe.
So yake ya tashi yaje ya watsa ruwa a jikin sa ko zaiji daɗi, amma gaba ɗaya ya kasa yin hakan, asalima bashi ya iya motsawa daga wurin da yake ba har sai da ya jiyo kiran sallahr magariba da yake futowa daga cikin masallacin masarautar tasu, kasancewar dawowar yamma sukayi liƙis dama, a hakan ma kuma dan ba ƙaramun uban gudu suka kwarara ba a hanya, domin kuwa saurin da sukayi a dawowar har yafi wanda sukayi a tafiya.

Daƙyar ya iya miƙewa zaune daga kwancen da yake yana mai rumtse idanuwansa da ƙarfi.
Kana daga bisani ya ɗan juyar da kai gefe, yana mai buɗe idanuwansa tare da buɗe bakin sa ya fesar da wata zazzafar iska daga cikin sa.
Tukun daga bisani ya miƙe tsaye yana mai zuwa wurin da rigar sa daya yar a ƙasa take, ya ɗauke ta ya mayar da ita jikin sa, abun da tun da yake zai iya cewa bai taɓa yi ba, wato bayan ya cire kaya ya kuma sake mayar da su jikin sa, amma yau da yake jin duk jikin sa ba daɗi gaba ɗaya yama manta da ƙa'idar tasa.

Cikin sanyin jiki ya fara ɗaga ƙafafuwansa yana mai dosar hanyar da zata sadasa da waje.

Ba tare da ya kula jama'ar da ya samu a cikin falon nasu ba ya hucewar sa gaba kansa sun sunkuye a ƙasa.

Ko da aka tayar da sallama fuskar Gimbiya Haddiyal ya cigaba da gani a cikin idanuwansa.
A haka har aka idar da ita gaba ɗayan sa dai babu wata cikakkiyar nutsuwa tattare da shi tamkar ko da yaushe.

Ko da ya futo daga cikin masallacin yana shirin juyawa ya koma part ɗin sa, yaji sautin muryar mai martaba a cikin kunnuwansa yana mai faɗin.

"Baba na!"

Hakan ne yasa sa juyowa da fuskar sa gare sa, tukun ya tawo wurin da yake yana mai ƙaƙalo murmushi ya yafa akan fuskar tasa.

"Good evening Dady!"
Ya faɗa yana mai ɗan sunkuyar da kansa ƙasa.

"Lafiyar ka kuwa Babana naga gaba ɗayanka ka sauya yau? Shin me yake damun kane, ina ne yake maka ciwo?"
Mai Martaba ya faɗa a ruɗe yana mai kai hannun sa kan lallausar sumar kan ɗan nasa ya fara shafata.
Shi kuwa Yarima Asad lumshe idanuwansa yayi yana mai jin duk wani iri a cikin ransa, kana daga bisani ya warasu yana mai buɗe baki yace.
"Babu komai Dady na, kawai dai gajiyar hanyace da muka kwaso har yanzu bata sake ni ba."

"Amma ka watsa ruwa bayan kun dawo ɗin."
Mai Martaba ya faɗa yana kallon sa.

"A'a."
Yarima Asad yace a ɗan gajar ce.

"To kagani ai dole kaji jikin ka babu daɗi ko, amma abun da za'ayi yanzu shine, dama ina neman ka zamu ɗanyi wata magana da kai, to yanzu tawowa kawai zakayi mutafi part ɗina, idan yaso bayan mun gama sai kayi wankan naka acan ko."

Cewar Mai Martaba yana mai kamo hannu Asad cikin nasa suka fara tafiya a tare.
Duk wanda ya gansu a hakan dole ne suyi matuƙar birge sa, wanda sanadin irin wannan soyayyar da mai martaba yake nunawa Asad ita ta sanya gaba ɗaya magautansu suke sake jin tsanar sa ako da yaushe, domin kuwa sun so ne mai martaba yaƙi sa saboda hallayar sa, amma sai suka ga babu abun da ya canza akan soyayyar da yake masa ta baya, saima kamar ninkuwa da take sake yi a kullum.

Ta gaban Jakadiya sukazo suka huce, amma ko darajar kallo bata samu a wurin Asad ba ballantana har ya gaishe ta, duk da yadda yaji sun gaisa da mai martaba a gaban sa kuwa.
Yayinda ita kuma Jakadiya tabi bayan sa da harara tana mai sakin ƙwafa a hankali.

"Yawwa zauna nan ko?"

Mai Martaba ya faɗa yana mai zaunar da Asad akan kujerar da suke a gaban ta tamkar wani ɗan ƙaramin yaro.
Kana shi kuma ya koma kan wacce take facing ɗin wadda Asad ɗin yake akai yana mai zama, tare da kafe sa da idanuwansa.
Kafin daga bisani kuma ya ɗanyi gyaran murya yana mai sake gyara zaman sa akan kujerar.

Hakan da Yarima Asad yaji ne ya sanya sa ɗago kansa, yana mai ɗora idanuwansa akan fuskar mai martaba.

Shi kuwa Mai Marataba cikin sakin fuskar ya buɗe baki yana mai cewa.

"Ashe yaron nawa ya girma, amma kwata-kwata na kasa ganewa, sannan kuma shima ya kasa sanarwa Dady'n sa."
Mai Martaba ya faɗa fuskar sa ɗauke da murmushi.
Yayinda shi kuma Yarima Asad ya sake zubawa mahaifin nasa ido, yana mai son gano abun da zancen nasa yake nufi, tukun daga bisani da yaga ya kasa fahimta ya buɗe baki yana mai faɗin.
"Kamar ya Dady na, ni fa ban gane abun da keke nufi ba."

"Hmmmmm!"
Mai Martaba ya saki murmushi, yana mai ƙara fuskantarsa, kana daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin.

"To abun da ke faruwa dai shine, ɗazu mai Girma Gwamna yazo wurin mu akan batunku, wato cikin Masarautar nan mun tattauna da shi akan maganar auren ka da ƴar wajen sa Bilkisu, sabo da ya faɗa mana cewar kun daɗe kuna tare kai ɗin ne dai ka ɓoye mana baka sanar damu ba.
Amma Alhamdullila dai munyi duk abun da ya kamata yanzu ranar biki kawai ya rage a tsayar, ina fatan zakayi farin ciki da jin hakan."

Ya ƙarasa maganar yana sakin murmushi, gaba ɗaya ko kaɗan bai lura da yadda yanayin Yarima Asad ya canza ba, domin kuwa sosai yayi matuƙar girgiza da jin kalamin da suke futowa daga bakin mahaifin nasa.
Hakan ne yasa sa haɗiyar wani irin ƙaton yahu, saboda yadda idanuwan
sa suka sake hasko masa fuskar Gimbiya Haddiyal tsaye a gaban sa,
Tukun daga bisani kuma ya ɗago kansa cikin tsantsar firgici da ruɗu, yana mai watsa idanuwansa akan fuskar Mai Martaba.
Yayinda bakin sa kuma ke faɗin...............




UMARFARUQ✍


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*02*



"Da..d.dy..! Shin mene kake faɗe? Mene ne mai girma Gwamna yazo yi nan gidan, ban gane mai kake nufi ba fa?"

Ya faɗa cikin wani irin yanayi da yake nuni da tsantsar tashin hankalin da ya shiga, bakin sa na wata irin karkarwa, yayinda zuciyar sa kuma take wani irin bugu tamkar zata hudo ƙirjin sa ta futo waje.
Lokaci ɗaya yaji kansa yayi wata irin muguwar sarawa, kana idanuwansa suka yi wani irin rikiɗewa, suna masu komawa jajaye, ko kaɗan ko kusa bai taɓa tinanin hakan zata taɓa faruwa ba, hakan yasa yaji saukar bayanin a cikin kunnuwansa tamkar Al'mara.

Da ƙarfi ya rumtse idanuwansa yana mai girgiza kai, domin kuwa babu abun da yake gani a cikin su sai Gimbiya Haddiyal tsaye a gaban sa a halin yanzu.
Kana daga bisani ya buɗe su akan fuskar Mai Martaba da shima ya zubo masa nasa idanuwan yana kallon sa, ba tare da ya iya ce masa komai ba.
Tukun ya sake ɗaga laɓɓan sa da suke wata irin karkarwa, yana mai ɗorawa da faɗin.

"Ƙarya take Dady, ni ban taɓa ce mata ina sonta ba, asalima ko gidan su ban taɓa zuwa ba Dady, wallahi ƙarya ta faɗawa baban ta ba gaskiya ba."
Ya ƙarashe maganar yana mai sauka daga kan kujerar da yake zaune akai, tare da yin nildown a gaban Mai Martaba.

Shi kuwa Mai Martaba sosai yanayin Asad yayi matuƙar ruɗasa, barin ma da yaga yadda hankalin sa yayi matuƙar tashi daga jin labarin.
Dama shi can ya kawo hakan zata faru a ransa, sai dai kuma bakin Alƙalima ya riga da ya bushe, domin kuwa bazai taɓa yuwuwa su buɗe baki su cewa mai girma Gwamna ba haka ba.
To taya ma za'a fara yin hakan a matsayin su na manyan mutane.
Ya raya haka a cikin ransa idanuwansa akan fuskar ɗan nasa.
Kana daga bisani ya buɗe baki cikin sanyi yana mai faɗin.
"Amma ai gaskiya ne kuna tare da ita yarinyar ko?"

Ya watsowa Yarima Asad tambayar a lokacin da bai azon jinta ba daga gare sa.
Hakan ne yasa sa ɗago kansa cikin sauri yana mai sake ɗora ƙwayoyin idanuwan sa akan fuskar mai martaba, kana ya komar dasu ƙasa da sauri yana mai ɗan rumtse idanuwan sa, yayinda zuciyar sa kuma ke wani irin bugu da matuƙar ƙarfi, su kuwa idanuwan sa har yanzu kyakkyawar hallitar da yayi gamo da ita yau suke sake hasko masa.


Cikin rawar murya kansa durƙushe a ƙasa yace.

"Ban taɓa cewa ina sonta ba Dady."

"Amma ai kuna tare ko?"

Mai Martaba ya sake jofe masa tambayar sa ta farko tun kafin ya kaiga ida rufe bakin sa.

Hakan da Yarima Asad yaji ne ya sanya sa fahimtar amsar kawai Mai Martaba yake son ji.
Sake rumste idanuwansa yayi da ƙarfi, kana ya buɗe baki yana mai faɗin.
"Eh Dady."
Yayi furucin acan ƙasan maƙoshi, domin kuwa koshi Mai Martaba banda gaba ɗaya hankalin sa na kansa da bazai fahimci abun da yake nufi ba.
Kana ya sake ɗorawa da faɗin.
"Amma ban taɓa zuwa inda take ba, asalima ko gidan su ni ban taɓa shiga ba, kana ban taɓa buɗar baki nace mata ina sonta ba, ita ɗin ce dai ke kulani, kuma take ɗauko ƙafafuwanta tazo har wurin da nak..."

"Tsawon shekaru nawa kuka ɗauka kuna a tare yanzu?"
Mai Martaba ya sake doko masa wata tambayar tun kafin ya kai karshen bayanin sa.

Sake rumtse ido Yarima Asad yayi, yana mai yin shiru ba tare da yace komai ba.
Hakan da Mai Martaba yaji ne ya sanya sa sake buɗe baki yana mai faɗin.

"Kai nake sauraro fa Baba na."

"Ɗaya da rabi zuwa biyu, amma ko farkon haɗuwar mu ma itace tazo har wurin da nake."

Yarima Asad ya faɗa yana mai fatan Dady'n nasa ya rusa abun gaba ɗayan sa, yayinda yake jin wata irin tsanar Billy na taso masa tun daga ƙasan zuciyar sa, ko kaɗan bai san haka yarinyar take ba, domin kuwa da yasan zata aikata hakan da tini ya daɗe da rabuwa da ita, kai da tun farko ma baiyi accepting ɗin ta cikin rayuwar sa ba.

"Amma ai ina tinanin kai namiji ne ko, me yasa tun farko ka kasa dakatar da ita zuwa wurin naka har kuka ɗauki tsawon lokaci a tare?"
Tambayar mai martaba ta sake dukan kunnuwan sa.

Shiru yayi ba tare da ya iya cewa komai ba, sai kansa ma da ya durƙusar ƙasa, yana mai jin yadda zuciyar sa ke cigaba da harbawa, gaba ɗaya fargaba da tashin hankali sunyi masa rubdugu.

Shi kuwa Mai Martaba jin da yayi Yarima Asad yayi shiru ne, ya sanya sa yin gyaran murya yana mai k'ara gyara zaman sa akan kujerar da yake zaune a kai.
Tukun ya buɗe baki cikin muryar rarrashi, yana mai faɗin.

"Tabbas kayi wauta Baba na, ai da tun farko da kasan ba sonta kake ba sai ka kore ta daga wurin ka, bawai kabar ta tai ta ƙara shaƙuwa da kai ba a kullum, domin kuwa ko wacece abun da zatayi kenan.
Sannan kuma kasan ko suwaye mu ba sai na faɗa maka ba, kasan irin gidan da muke ciki, ka riga daka sani babu ta yadda za'ayi mu zamto ƙananan mutane. Wato abun da nake nufi shine, bazai taɓa yuwuwa muce ba haka bane ba dole ne sai anyi abun nan, domin kuwa bama ƙaramar magana mu."
Mai Martaba ya faɗa idanuwansa akan fuskar Asad.

Shi kuwa Yarima Asad cikin tsantsar firgici,ruɗu, had'i da tashin hankali ya ɗago idanuwansa yana mai watsa su akan fuskar Dady'n nasa.
Babu abun da ƙwaƙwalwar sa take tariyo masa a halin yanzu face fasalin fuskar Gimbiya Haddiyal.

Hakan yasa ya fara jan guiwoyin sa daga wurin da yake yana mai nufar gaban mai marataba cikin tsantsar ruɗu.
Da sauri ya miƙa hannuwan sa duka biyu yana mai kamo tafukan hannayen mai martaba cikin nasa, sannan ya buɗe baki cikin rawar murya yana mai faɗin.

"Wallahi tallahi Dady na bana sonta, kuma itama da kanta ta sani, saboda nasha faɗa mata cewar bana sonta, dan girman Allah Dady na roƙeka ku janye wannan batun."

Ya ƙarasa maganar cikin wata irin murya, yana mai jin yadda kansa ke sake hautsinewa da bala'in ciwo, ta yadda har idanuwan sa suka ƙanƙance.

Da ƙarfi Mai Martaba ya sake damƙar tafin hannun Yarima Asad a cikin nasa, yana mai jin wani iri a cikin zuciyar sa, domin ko tunda yake da ɗan nasa bai taɓa ganin sa a cikin tashin hakali irin na yau ba, hakanne yasa shima gaba ɗayan sa yaji yayi matuƙar ruɗewa, sai dai kuma ko kaɗan bai bari Asad ya fahimci halin da yake ciki ba.

"To wacece kake so, tunda ita kace baka sonta, domin kuwa ka sani dama lokaci ne aka baka ka futar da matar aure."
Mai Martaba ya faɗa yana kallon sa.

Rumtse ido Yarima Asad ya sakeyi ba tare da ya iya cewa komai ba, domin kuwa shi dai bai san abun da zaice ba yanzu, sabo da ya sani babu wata ɗiya mace daya taɓa jin sonta a cikin ransa.

"Kai nake sauraro Baba na."

Mai martaba ya sake faɗe yana mai ɗan sake damƙar tafin hannun Asad cikin nasa.

"Babu."

Yarima Asad ya faɗa cikin sanyi, ba tare da ya iya ɗago kansa ya kalli mahaifin nasa ba.

"To alfarma ɗaya zan iya yi maka Asad a matsayina na mahaifin ka, domin kuwa bazan taɓa jin daɗin ganinka a rashin walwala ba, dan haka na baka nan da wata ukku ka nemo yarinyar da kaga tayi maka, wato wacce kake so, inyaso sai a haɗa ayi bikin a tare.
Ma'ana dai ka auresu su duka biyun a lokaci gud..."

Miƙewar da Asad yayi tsaye zumbur yana mai zaro idanuwansa akan fuskar Mai Martaba ne ya sanya maganar mai martaba katsewa, yana mai binsa da kallo shima.

Sosai tashin hanakali mara misaltuwa ya sake bayyana a tare da shi.

"Mata biyu lokaci guda, ina Dady bazan iya ba, kuma ma wata ukku ya mun kaɗan Dady."
Yarima Asad ya faɗa cikin wata irin murya, wacce zata bawa duk wanda ya saure sa tausayi, yana mai girgiza kansa.

"Zaka iya mana Baba na, koko ka manta da kai ɗin gwarzo ne, sannan kuma ka manta da sunan da momy'n ka da jama'ar gari suke kiran ka da shi, wato Asad, wanda a hausance kuma kalmar take nufin Zaki.
To mene ma acikin mata biyun?
Wata ukku kuma da kace yayi kaɗan babu kaɗan ɗin da yayi, asalima yawa yayi, domin kuwa ga mata nan birjik a gari kala-kala, a iya gobe ma idan ka futa zaka iya haɗuwa da wacce tayi maka, dan haka kaje nima na gama magana ta, domin ko iyakar wannan alfarmar kawai zan iya yi maka a mtsayina na mahaifin ka, idan kuma har baka aminta da hakan ba sai ka haƙura ka auri ita Bilkisun kaɗai."

Mai Martaba ya ƙarasa maganar yana mai miƙewa tsaye.

Shima Asad juyawa yayi cikin tsantsar firgici, yana mai kama hanyar da zata sadasa da part ɗin mamy'n su ta cikin ɓangaren mai mataba.
Gaba ɗayan sa a matuƙar ruɗe yake, domin kuwa idan hankalin sa yakai dubu sai da duka ya tashi.

"Asad!"

Muryar Mai Martaba ta sake dukan kunnen sa adai-dai lokacin da yake shirin fucewa daga falon nasa.
Hakan ne yasa sa tsayawa cak a wurin da yake ba tare da ya iya juyowa ba.

"Ina son daga yau, daga kuma yanzu, kasa a ranka cewar kai ɗin mijin mace biyu ne."

Mai Martaba ya faɗa cikin muryar gaskiya da gaskiya, domin kuwa iyakar abun da zai iyayiwa ɗan nasa kenan, kuma a hakan ma yasan sai jama'ar su sunga sankan sa, sai dai kuma dole ne yayi hakan, domin kuwa bazai taɓa jurar ganin ɗan nasa a cikin damuwa ba, sabo da ya sani shima mai Girma Gwamnan gudun ganin damuwar ƴar tasa ne ya sanya sa yin hakan, wato zuwa da kansu zancen aure a matsayin sa na bahaushe, dan haka babu abun da zaisa yana ji yana gani dan sa ya cutu shima, sai dai kuma ya ƙudiri aniyar sanya Yarima Asad yayi adalci atsakanin matan nasa muddin ya samo wacce yake son.

Ba tare da Yarima Asad ya iya juyowa ba ya ɗagawa mahaifin nasa kai daga wurin da yake, domin kuwa sosai ya ƙarajin abun babu daɗi ko kaɗan a cikin kunnuwan sa.
Kana ya cigaba da ɗaga ƙafafuwansa yana mai fucewa daga cikin falon gaba ɗaya.

Koda ya ɓulla falon mamyn tasu bai tadda kowa a cikin sa ba, da alamun dai tunda sukayi sallahr magariba basu sake futowa ba, hakan ne yasa sa wucea nasa falon direct yana mai jin yadda kansa ke wani irin sara masa.

Kai tsaye ya doshi bedroom ɗin sa yana mai zuwa ya kife akan gado.
Kana ya ɗago tafin hannuwan sa duka biyu yana mai kifesu akan goshin sa ya damƙe sa da matuƙar ƙarfi, wai ko zai samu yaji sauƙin azababben ciwon kan da ya turnuƙe sa.
Yau ɗin tazo masa da abubuwa daban-daban, gaba ɗayan su kuma babu wani mai daɗi ɗaya da zaice gasa.
Na farko shine takurawar da Babban Yaya yayi masa ya sanya sa dole binsa wancan ƙaddararren garin, abu na biyu kuma shine haɗuwar sa da waccan fitsararriyar yarinyar mai zubin aljanu, gashi nan ta barsa da bala'in tinanin ta a cikin ransa, abun da bai sansa ba kwata-kwata a rayuwar sa, wato tinanin ƴa mace, abu na ukku kuwa shine sauraron wannan baƙin labarin daya futo daga bakin Dadyn sa, ga kuma na ƙarshe da yafi ɗimauta sa na matar da yake so da mai martaba yace ya samo.

Wai shine za'ace ya auri mata biyu, shi da ya tsara yin kalar rayuwar turawa a cikin gidan sa, ya tsara yadda komai nasa zai tafi, amma ake danganta sa da auren mata biyu a lokaci guda, kuma da gaske bada wasa ba.
Tabbas ya tsani Bilksu a yau, tsana irin wadda bai taɓa yiwa wata ɗiya mace ita ba a duniya, yayi nadamar sanin ta da yayi a rayuwar sa, bai taɓa sanin daƙiƙiya bace ita ɗin ma sai a yau data turo Dady'n ta yayi aikin daƙiƙanta a cikin gidan su, amma shima kuma ya ɗauki alƙawarin sanya ta cikin damuwa muddin ta bari aka sanya sa dole ya aure ta.

Ya raya haka a cikin ransa, yana mai sake rumtse idanuwansa, yayin da har lokacin kuma Gimbiya Haddiyal bata bar yi masa gizo a cikin idanuwan sa ba.

Yana ji ana kiran sallah isha'i a cikin massalacin masarautar tasu amma gaba ɗaya ya kasa tashi, ballantana har ya tafi, sabo da azabar ciwon kan da yake jin yana damun sa.

Misalin ƙarfe takwas da rabi yaga kiran Babban Yaya na shigowa wayar sa, amma gaba ɗaya ya kasa ɗagawa kwata-kwata.
Jin da yay ta yanke ya sake kirawowa ne ya sanya sa janyo wayar yana mai yin picking ɗin ta tare da sanya ta a handsfree.

"My ƙani ya ka shanya ni tun ɗazu ina zaman jiranka ka futo muci abinci, kana ina ne?"
Yaji muryar Babban Yaya na faɗin haka.

Lumshe idanuwansa yayi, kana daga bisani ya buɗe su yana mai ɗan fesar da iska daga cikin bakin sa, tukun ya ɗan saita muryar sa gudun kar Babban Yaya yaji sa ba adai-dai ba yanzu ya tawo ya ƙara isarsa da tambayoyi, yana mai faɗin.

"Ina ɗaki yaya na, kawai kaci abincin ni na riga da nasha fura harma na kwanta."

"Lafiyar ka kuwa Asad, shin me yake damunka ne naji gaba ɗaya yanayin ka ya sauya?"
Babban Yaya ya watso masa tambaya da sauri.

Fesar da iska Yarima Asad ya sake yi, kana yace.
"Ka kwantar da hankalinka lafiya ta ƙalau Yaya na, kawai dai dama gajiyar da muka kwaso ce har yanzu bata sake ni ba, saboda kasan ba saba yin irin tafiyar nan nayi ba."
Ya karasa maganar murya can k'asa sosai, domin kuwa jin kansa yake tamkar zai rabe gida biyu.

"Kai ashe ƙanin nawa raggo ne dama ban sani ba sai yau, tom shikenan sai da safe, amma ka tabbatar kayi addu'ar kwanciya bacci kaji ko."
Babban Yaya faɗa muryar sa ɗauke da murmushi.

"Tom shikenan thank you Yaya na."
Yarima Asad ya faɗa yana mai yanke kiran nasa.
Kana ya yunƙura da ƙyar yana mai tashi zaune, tukun ya sauko daga kan gadon hannun sa dafe da kansa yana mai nufar hanyar bathroom.

Ya ɗauki tsawon mintina ashirin a

Please Login or Register in order to submit comment