Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bayan ta janye yantsun hannuwanta daga cikin kunnuwanta.
Kana ta kalli cikin k'wayar idanuwan Yarima Asad, tana mai bud'e baki cikin kakkausar murya tace.

"Hak'ik'a kalaman ka suna gab da tarwatsa mun k'wak'walwata!
Domin ko ruhina na mutum d'aya ne, gangar jikana ta mutum d'aya ce, haka kuma zuciyata ma tasa ce.
A duk duniya babu wanda na tsana, sama da wanda naga yana shirin gina mun katanga tsakanina da Gid'ad'o am.
Na fara sonsa tun kafin in san meye so, na fara sonsa tun a lokacin dana fara sanin kaina, haka kuma zan cigaba da sonsa har k'arshen rayuwata."

Ta k'arasa maganar tana mai juyawa da matuk'ar sauri, ruwan hawaye na b'allewa daga cikin idanuwanta ta doshi bakin k'ofar futa.
Ganin hakan da Yarima Asad yayi ne, ya sanya jikinsa d'aukar wata irin karkarwa, da matuk'ar sauri ya sake bud'e baki, ba tare da yasan lokacin da yayi hakan ba adai-dai lokacin da yaga tana shirin futa, yana mai fad'in.

"Karki mun haka, idan kika tafi zuciyata zatayi zafi, wallahi ina sonki da gaskiya."

Cak ko ta tsaya adai-dai bakin k'ofar ba tare da ta futan ba.
Kafin daga bisani kuma ta juyo kanta, ba tare da ta juyo da gangar jikinta ba, tana mai watsa jik'ak'k'un idanuwanta a cikin tsakiyar nasa da suka rine da ja shi kuma.
Kana ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Ba a yanzu bama, har gaban abada kar katab'a sanya rai da jin wannan kalamin daga bakina, domin kuwa ni bana sonka, bana k'aunar ka, asalima na tsaneka.
Dan haka ina mai shawartarka daka koma wurin 'Yammatan Turawa! Larabawa! Indiyawa! Masu kud'i, aji, gata, tare da kyawu da suke rububin ka ka futar da d'aya a cikin su, domin ko gaba d'aya a cikin su babu wacce na kama ko da yatsar k'afarta, saboda kai da kanka ka sani kuma ka fad'a ni d'in bagidajiyace 'yar k'auye!
Ka sani ko da babu Gid'ad'o am, kai d'in baka yimun ba, zubinka bai birgeni ba, baka cikin tsarin wa'yan da Haddiyal zata iya k'auna ko kusa ko kad'an!"

Ta k'arasa maganar tana mai janye idanuwanta daga cikin nasa, kana ta juyawarta tana mai fucewa daga cikin falon duka.

Shi kuwa Yarima Asad wata irin karkarwa jikin sa ya d'auka tamkar mazari.
Iyakar tashin hankali yau dai ya shigesa yanzu.
Gaba d'ayan sa ya rud'e ya kid'ime, babu abun da yake sai aikin zare jajayen idanuwansa.
Yayinda yake jin kansa kuma na masa wata irin matsananciyar sarawa.
Da sauri shima ya kama hanyar wajen a tsantsar firgice.

Kai tsaye ya doshi gaban motarsa yana mai bud'e ta ya shige tare da yi mata key.
Tukun ya fafareta a wani irin haukace yana mai kama hanyar get, gaba d'aya ma ya manta da batun wani Habu a duniya, ballantana har ya tsaya jiran sa suyi sallama.

Tun kafin ya k'araso bakin get dakarun da suke tsaye a wurin suka bud'e masa k'ofar da matuk'ar sauri, suna masu kauce gefe.

Fiiit! Kakejin sautin futar iska a duk wurin da ya huce, a haka har ya haye kan shimfid'ed'iyar kwaltar nan.

Sosai hankalinsa yayi bala'in tashi, gaba d'ayan sa ya fuce daga hayyacinsa.
Ko kad'an baya lura da kalar tuk'in da yake, saboda yadda ya kai k'arshe wurin kid'imewa
Ji yake ina ma ace mutuwa yayi da zuwan wannan mummunar rana gareshi.
Wai ace shi Asad shine yau ya bud'i baki a karo na farko ya furtawa wata d'iya mace kalmar so a duniya, amma ta k'isa, asalima sai cewa tayi ta tsane sa, ba kuma ta tsaya a iya haka ba sai da har ta had'a da yabon wani a gaban sa, sannan kuma tace masa baya d'aya daga cikin fasalin mutanen da zata iya so a rayuwarta har gaban abada.

Sosai kalaminta suke masa amsa kuwwa a cikin kunnuwansa, yadda kasan yanzu take kan fad'ar su.

_"Ka sani ko da babu Gid'ad'o am, kai d'in baka yimun ba, zubin ka bai birgeni ba, baka cikin tsarin wa'yan da Haddiyal zata iya k'auna ko kusa ko kad'an!"_

Muryarta ta sake yi masa amsa kuwwa a cikin kunnuwansa tana mai fad'in hakan.
Hakan ko ya sanyasa dukan sitiyarin motar yana mai sakinsa, tare da rumtse idanuwansa da matuk'ar k'arfi.

Aiko take a wurin motar ta canza hanya, tana mai gangarawa k'asan kwalta ta doshi wurin wata bishiya gadan-gadan.
A kuma dai-dai lokacin shima Yarima Asad ya bud'e idanuwansa yana mai ganin abun da yake shirin faruwa.
Ai kuwa cikin tsantsar rud'u, firgici, gami da tashin hankalin ganin mutuwar da yayi k'arara ya kai hannuwansa yana mai k'ok'arin rik'e sitiyarin, tare da taka birki, amma ina ya riga da ya makaro, domin kuwa duka-duka 'yar k'aramar tazarace ta rage a tsakanin motar da jibgegiyar bishiyar, da bayan ta kuma ya kasance k'aton rami!


*K'ASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAK'AR MASARAUTA.*

B'angarensu na Bayi Bir ya juya yana mai tafiya ba tare da ya samo musu naman ba.

Sosai yake jin wani irin nishad'i mara misaltuwa na mamaye zuciya da ruhinsa.
Hak'ik'a a yau d'in ya k'ara ganin tsantsar soyayarsa a cikin idanuwan Gimbiya Tasmir, kana kuma ga sheda nan ya gani, tunda har ya iya yimata kwarjini ta kasa sauke hannunta akan fuskarsa, wanda yasan da wanine ba shi d'in ba ya aikata mata hakan, to da tabbas sai dai uwarsa ta haifi wani idan tana raye kuma bata tsufa ba, amma ba dai shi ba.
Sai dai kuma a k'asan zuciyarsa yana jin tamkar yaci amanar iyane, tun da dai yayi mata alk'awari akan ba zai k'ara fad'awa Gimbiya maganar da bata kamata ba, amma sai gashi yayi d'in, duk da dai ita d'in ce ta buk'ata.

Yana b'ulla b'angaren nasu ya hango Iya durk'ushe a gaban murhu, tana shirin had'a huta.
Hakanne ya sanyasa hucewa zuwa wurin da take kai tsaye.

Da sauri Iya ta d'ago kai tana mai watsa idanuwanta akan fuskar Bir, adai-dai lokacin da ya k'araso wurin da take tana mai fad'in.

"Lafiya dai Jarumi, na ganka har kadawo daga futarka?"

"Yafiyar ki na dawo nema ne Iya ta."

Ya fad'a a sanyaye yana mai kallon ta.
Jin hakan da Iya tayi ne ya sanya ta kama hannunsa cikin sauri, tana mai fad'in.

"Tawo! Tawo mu je gindin bishiya, kalamanka na shirin rud'ani Jarumi."

Bin ta yayin tana rik'e da hannunsa, a haka har suka k'arasa k'ark'ashin inuwar bishiyar da suka tashi d'azu a cikinta.
Sakin hannun Bir tayi tana mai zama a k'asa.
Kana ta masa alamar da ya zauna shima d'in.

A hankali kuwa ya durk'usa k'asa yana mai zube gwiwoyinsa a gabanta.
Tukun ya d'an lumshe idanuwansa yana mai bud'e su, kana ya d'an sunkuyar da kansa k'asa yana mai fesar da iska.
Sannan ya bud'e baki cikin sanyin murya yana mai fad'in.

"Kiyi hak'uri na karya alk'awarin da na d'aukar miki Iya ta, wato dai na yiwa Gimbiya magana yau ma."

Da matuk'ar sauri Iya ta d'ago idanuwanta tana mai watsa su akan sa.
Ganin da tayi kansa durk'ushe a k'asa ne, ya sanyata kai hannuwanta zuwa kannasa tana mai d'ago da shi, ya zamto yana kallonta.
Tukun ta bud'e baki cikin rawar murya tana mai fad'in.

"Akan me zakayi hakan Jarumi?
Shin me yasa kake son fara b'ata mun rai ne? Me yasa zakaje wurin da take? Me ma kuma ya faru a tsakaninka da ita?"

Ta watso masa tambayoyin duka a jere, kana kuma a lokaci guda, cikin tsantsar firgici, duk da dai ba taga alamun wuya a tattare da shi bama.

"Ba ni naje wurinta ba ita tazo har inda nake Iya ta, nayi k'ok'arin in gudar mata tamkar yadda kikace na dinga yi idan mun had'u, amma ta dakatar da ni.
Kana kuma ta mun tambayar da ta saba yi mun ako da yaushe, ni kuma shine na bata amsar ta a yau ba tare da nai mata gardama ba, tamkar yadda kikace na dinga yi matan.
Wato dai nayi mata bayanin abun da ke cikin zuciyarta akai na, tare kuma da wanda ke cikin zuciyata akan ta."

Ya k'arasa maganar yana mai lumshe idanuwansa.

Yayinda ita kuma Iya ta bud'e baki cikin sauri tana mai fad'in.

"Kayi mata bayanin abun da kuke ji a zuk'atanku game da junan ku kuma, wane kalar bayanine wannan?"

Ta sake watso masa tambaya, har yanzu dai hankalinta bai kwanta ba.
Hakan da Bir yaji ne ya sanya gyara zaman sa a gabanta.
Tukun ya fara karanto mata abun da ya faru tun daga ranar da suka fara had'uwa da Gimbiya Tasmir, har zuwa kan abun da ya shaida mata a yau, da kuma yadda tayi a lokacin da ya fad'a matan.

Cikin tsantsar firgici Iya ta d'ago kanta tana mai watsa idanuwanta a cikin na Bir.
Kana ta bud'e bakinta da lab'b'an ta suke karkarwa tana mai fad'in.

"Me yasa zaka yi haka, me yasa zaka yi mata k'aryar kana sonta? Me yasa zaka ce itama tana sanka, bayan kuma kasan hakan na iya haifar da komai Jarumi.
Shin kasan irin matsalar da kake shirin jefa kan ka a cikinta kuwa?
Shin me yasa zaka mun haka Jarumi"

"Zuciya duk bata san wannan ba Iya ta.
Hak'ik'a da gaske nake ba k'arya ba ina son Gimbiya, so ba k'arami ba, so irin wanda nake fatan ya dunk'ule rayuwarmu wuri d'aya, ma'ana dai ta zamto mallakina ta har abada.
Kallo d'aya nai mata komai nawa ya rikice, lissafina ya koma kanta, haka ma tinanina ya zamto nata.
Hak'ik'a zuciya bata shawara a harkar so, ban da haka da ko kusa ba zan tab'a bari na kai kaina wurin da na riga na san bani da abinci a cikinsa ba.
Wato dai da gaske nake ina sonta ba k'arya ba Iya ta."

Ya fad'a kai tsaye yana mai kallon Iya.

"Shin a ina ka tab'a jin tarihin da ya nuna an tab'a auren d'iyar sarki da bawa ne?
Shin me yasa zaka kai kanka da kanka wurin da kasan mutuwar kace anan?"

Iya ta fad'a tana kallonsa.

Jin-jina kai Bir shima yayi idanuwansa akan fuskar Iya.
Kana daga bisani ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Ban tab'a ji ba ko a labaran masu tsara labari, amma abu d'aya kawai da na sani, kuma yake sanyani nishad'i shi ne, ba ni kad'ai nake aikin sonta ba, itama tana mun kalar son da nake mata, wanda har sanadin hakan ya sanya ta kasa d'ora tafukanta akan fuskata."

Shiru Iyar Bayi tayi ba tare da ta k'ara cewa komai ba, sai kallon Bir d'in kawai da take tamkar ta samu tv, domin ko ita kanta a labarin da ya batan ta yadda da Gimbiya ta kamu da son sa.
To amma tayaya wannan gingimemen al'amarin zai yuwu?
Hak'ik'a ta sani ko da Gimbiya na son Bir, ba zasu tab'a zamtowa a inuwa d'aya ba, saboda bambancin da yake a tsakaninsu, ita 'yar Sarki ce 'yantacciya mai gata da galihu, yayinda shi kuma ya kasance Bawa k'ask'antacce mara gata da galihu.
Amma ba komai zata bar Ubangiji Gargabilu yayi ikon sa akan lamarin, fatanta dai kawai shi ne, kar Ubangiji yasa hakan ya zamto matsala a rayuwar Bir.

Abu d'aya kawai take tinawa ako da yaushe taji dama idan Bir yayi wani abun, wato ba za'a tab'a kashesa ba kome zai aikata a cikin masarautar.
Hakanne ya sanya Iya ta sake bud'e baki tana mai fad'in.

"Tabbas na yadda, kuma na aminta da abun da ka fad'a mun.
Zuciya bata da k'ashi, dukanku kun kamu da soyayyar da bata dace da ku ba.
Dan haka kawai mubarwa Ubangiji Gargabilu yayi ikon sa akan lamarin."

Ta k'arasa maganar tana mai mik'ewa tsaye.
Yayinda a k'asan zuciyarta kuma take tsananin tausayin halin da Bir zai shiga.

Hakan da Bir yaji ne ya sanya gane cewar ta goya masa baya kenan.
Wanda hakan kuma ba k'aramun farinciki ya sanya sa ba.
Shi ya sa ma ya mik'e tsaye shima da sauri, hannunsa rik'e da kwari da gwafarsa yana mai kama hanyar daji, domin yaje ya samo musu abun da ya tafi samo musu tun farko.

Acan b'angaren Gimbiya Tasmir kuwa, cikin tsantsar tashin hankali, firgici had'i da rud'u ta fad'a cikin d'akin ta.
Sosai idanuwanta suke zubar da k'walla tamkar an bud'e famfo.
Gaba d'aya ruwan hawayen sun dame kwaliyyar fuskarta.

Sosai kalaman Bir suke cigaba da yi mata amsa kuwwa a cikin kunnuwanta tamkar yanzu yake kan fad'ar su.
Yayinda hoton kyakkyawar fuskarsa kuma da tun da suke had'uwa da shi bata tab'a lura da irin kyan nasa ba sai yau, ta zauna damar a cikin idanuwanta.

Kai tsaye ta doshi gaban madubi a wani irin haukace.
Tana k'arasawa wurin ta d'auki kwalbar turaren huta tana mai doka ta a jikin bango, gaba d'aya ta tarwatse.
Tukun ta cigaba da yin watsi da komai da yake akan madubin, cikin tsantsar tashin hankali.

Lokaci d'aya ta rikid'e ta koma tamkar wata mahaukaciya sabon kamu, wanda hakan kuma duk ya farune ta sanadin kalaman Bir da suke cigaba da dukan k'wak'walwarta.
Wai kamar ita Gimbiya Tasmir ce Bawa zai bud'i baki ya kalli k'wayoyin idanuwanta yace mata yana sonta, abun takaicin ma kuma shi ne, bai tsaya a iyakar kansa ba har sai da ya furta cewar itama tana sonsa, kamar ta, kamar ta diyar Sarki ta kamu da soyayyar Bawa.

"Inaaaa hakan ba zai yuwu ba wallahi.
Shin me ma ya hanani na hukunta sa? Me yasa na barsa ya tafi ba tare da na masa komai ba.
Hak'ik'a bazan tab'a yafe maka wannan laifin daka aikata mun ba, bazan tab'a barinka kaci banza ba, dole ne ka girbi hukunci dai-dai da abun da kayi.
Zan illataka, sannan kuma in tagayyara rayuwarka, tun kafin ni ka illatani ka tagayyara tawa rayuwar."

Ta fad'a da wani irin k'araji, jikinta na tsantsar karkarwa.
Kana ta fara d'aga k'afafuwanta tana mai ratsawa ta cikin kwalaban da suke watse a k'asa ta doshi kan gadon ta.

Ko kad'an bata damu da yadda jini ke d'an futa a tafin k'afafuwan nata ba ta sanadin kwalaban da suka caketa, ta cigaba da tafiyarta har ta k'arasa bakin gadon, asalima ko sanin da su d'in ba tayi ba kwata-kwata.

Da matuk'ar sauri ta fad'a rubda ciki a kan gadon tana mai murza kanta akan katifa, tare da cigaba da sakin kukanta mai matuk'ar sosa zuciya.


*K'ASAR HAUSA, JAHAR KAGUL.*

A dai-dai lokacin da ya gama futar da tsammanin sake rayuwa a gidan duniya, yaji motar tasa tayi wani irin cijewa bayan gabanta ya d'an daki jikin bishiyar kad'an, tana mai futar da wata irin k'ara.

Wasu irin tagwayen ajiyar zuciya ya fara saukewa, yana mai muzurai tare da zare idanuwa.

Gaba d'ayan sa ya jik'e sharkaf da gumi, tamkar wanda aka tsamo daga cikin ruwa, gashi kuma har kawo yanzu kalaman Gimbiya Haddiyal basu dena masa amsa kuwwa a cikin kunnuwa ba.

Cikin wani irin yanayi na firgici ya kai idanuwansa k'asansa dai-dai saitin k'afarsa.
Sai alokacin ya gane wai ashe k'afar tasa take ta ke da Birki, wato dai hakan shine yayi sanadiyyar tsayawarta ba tare da ta k'arasa ba.

Aiko take a wurin ya lumshe idanuwansa yana mai fesar da numfashi.
Kana daga bisani ya bud'e su yana mai fara k'ok'arin yin ribors a hankali.

Cikin ikon Allah kuwa ya bar gaba d'aya kusa da bishiyar, tukun ya lailaiya kan motar tasa yana mai k'ara d'ibarta a guje ya haye kan kwalta, tare da cigaba da tsala uban gudun sa, domin kuwa a halin yanzu ba shi da wani buri wanda ya huce ya gansa a cikin gidan su.

K'arfe biyar da rabi dai-dai ta kawosa cikin masarautarsu ta wasai, saboda irin mahaukacin gudun da yayi.
Kai tsaye ya doshi part d'in su Al'amin amai-makon ya huce na su part d'in.
Yayinda karankaf ilahirin jama'ar da suke a area'r kuma sukabi bayan motar da kallo baki a sake, saboda irin gudun da sukaga yana yi, duk da dai ba yau ne karonsu na farko da suka tab'a ganinsa yana mahaukacin tuk'i ba, sai dai kuma na yau d'in sosai yasha bamban da sauran, domin kuwa ko da ba'a fad'a musu ba sun san a haka ya tawo tun daga wurin da yaje ma.

A wurin da Al'amin yake paking d'in motocinsa shima ya parka tasa, sai dai kuma shi ko kad'an ba parkin d'in nutsuwa yayi ba, asalima ko gama dai-daita ta baiyi ba ya bud'e murfinta yana mai futowa a wani irin haukace, ya doshi d'akin Al'amin.

Acan b'angaren Al'amin kuwa kishingid'e yake akan kujera a cikin falon sa yana mai kallo a tv.
Idan kaga yadda ya idanuwansa suke akan tv'n zaka rantse kace da gaske kallon yake, kana kuma yana fahimtar abun da ake yi a tv'n.
Sai dai kuma a zahirin gaskiya gaba d'aya hankalinsa baya hurin ma, yana can wurin tinanin Abokinsa.
Shin ya dace yau d'in ko kuwa, yayi abun da yakamata yayi ko kuwa yayi halinsa na girman kai.

Yana cikin wannan yanayin ba zato ba tsammani yaji an banko k'ofar d'akin nasa da matuk'ar k'arfi, kafin daga baya kuma yaga Asad ya biyo k'ofar cikin wani irin yanayi, tamkar wanda baya cikin hayyacinsa gaba d'aya ma.

Hakanne ya sanya Al'amin mik'ewa tsaye a wani irin firgice yana mai bin Asad da idanuwa.

Shi kuwa Yarima Asad kai tsaye ya doshi wurin da Al'amin yake a tsaye.
Yana k'arasowa wurin yayi saurin mik'a hannuwansa yana mai damk'ar tafukan hannayen Al'amin a cikin nasa da matuk'ar k'arfi.
Yayinda jajayen idanuwansa kuma suka kasance k'ur a cikin na Al'amin.

Shi kuwa Al'amin cikin tsantsar rud'u da fargici yake kallon Asad, gaba d'ayan sa shima ya rud'e ya rasa mai ya kamata yayi, domin kuwa tun da yake a rayuwarsa bai tab'a ganin Abokin nasa a cikin irin wannan yanayin na yau ba.

Cikin wata irin murya wacce Al'amin bai sansa da ita ba ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Shin me yasa zatayi mun haka? Me yasa ta kasa fahimtar irin son da nake mata? Me yasa ta kasa gane ko ni d'in wane ne duk da irin bayanin da nayi mata?
Shin me na rasa ne a rayuwa wanda mace take buk'ata a wurin namiji Al'amin?"

Ya k'arasa furucin a wani irin rikice jikin sa na cigaba da karkarwa, yayinda jijiyoyin kansa kuma suke sake bayyana akan goshinsa rad'a-rad'a da su.

Da sauri Al'amin ya zare tafukan hannayensa da suke a cikin na Yarima Asad.
Kana ya mayar da su kan kafad'ar sa yana mai dafasa tare da yimasa alamun ya zauna akan kujera.

Ba tare da yayi musu ba ya zauna d'in, yana mai binsa da idanuwa tare da son jin amsar da zai basa.
Yayinda shi kuma Al'amin ya juya da sauri yana mai tafiya gaban frig d'in da yake a cikin d'akin.
Sassanyan ruwan jarka d'aya ya d'auko a ciki yana mai juyowa ya dawo wurin da Asad yake, tukun ya bud'e murfin cikin sauri yana mai mik'awa Asad jarkar.

Ba tare da yayi musu ba ya amshe ta yana mai kafa bakinta akan nasa bakin.

Ba shi ya janye jarkar daga kan lab'b'an sa ba har sai da ya dena jin wucewar ruwan a mak'oshinsa, wato dai sai da ya k'are.
Kana ya saketa a k'asa yana mai lumshe idanuwansa tare da fara sauke wasu irin tagwayen ajiyar zuciya, ajere-ajere.
Ganin hakan da Al'amin yayi ne ya sanyasa zube gwiwoyinsa a k'asa daga gaban k'afafuwan Yarima Asad.
Kana a hankali cikin taushin murya ya bud'e baki yana mai fad'in.

"To kai d'in me kace mata ne Asad, da har tace bata sonka?"

A hankali Yarima Asad ya sake wara jajayen idanuwansa akan fuskar Al'amin.
Kana kuma cikin sanyi ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Na fad'a mata cewar ina sonta, na aikata abun da tun da nake a rayuwa ban tab'a aikatawa ba, na fad'a mata kalmar da d'aruruwan mata suke san jinta daga wuri na a garesu, amma ko kad'an ita ba tayi tasiri akanta ba, asalima amai-maikon ta sanyata nishad'i sai b'ata mata rai da tayima.
Shin me ka sani wanda ake sha ya b'atar da soyayya a zuciya, ko kuma ya mantar da mutum komai na rayuwa, nima na sha ko naji sauk'in rad'ad'i da k'unar da nake ji a cikin raina akanta."

Ya k'arasa maganar da girgiza kansa da yake jin tamkar zai cire, saboda tsananin ciwon da yake.

Shi kuwa Al'amin cikin sanyin jiki tare da mamakin yadda Yarima Asad ya canza lokaci guda, ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Ka kwantar da hankalin ka d'an uwa, ita dama soyayya ta gaji haka da farko, sautari mutum zaije wa yarinya da soyayyarsa, amma ko kallon arzik'i bai isheta ba, idan kuma yayi hak'uri ya cigaba da zuwa wataran sai kaji ita da kanta take fad'in tana sonsa, ba zata iya rayuwa ba muddin babu shi.
Dan haka kaima ina mai tabbatar maka da zata soka wataran, domin kuwa babu wani abu da Allah bai mallaka maka shi ba a cikin wa'yan da mata suke buk'ata a wurin nam..."

"Ta yaya? Ta yaya zata soni? Shin ka san kuwa mai ta fad'a mun a yau ma.
Ta ce ta tsaneni, kana kuma tana da wanda take so ita, sannan kuma ko da ace babu shi d'in, to na sani bana d'aya daga cikin mazan da take da muradin mallaka, tsari na bai mata ba, tamkar yadda nima d'in ban mata."

Ya k'arasa maganar acan k'asan mak'oshi, yana mai rumtse idanuwansa da matuk'ar k'arfi, domin kuwa ba k'aramun ciwo tina kalaman nata suke sake saukar masa ba a zuciya.

Shi kuwa Al'amin cikin ganin ya k'ara k'arfafa masa gwiwa yace.

"Zata soka mana, zata soka ta hanyar taimakon yayanta Habu bi'izinillah."

Jin hakan da Yarima Asad yayi ne, ya sanyasa bud'e idanuwansa da sauri, yana mai fad'in.

"Kamar ya ta hanyar Habu, shin me Habu ya sani dangane da abun da yake a tsakanina da ita da har zai taimake ni?"

"Habu yasan komai kuwa Asad, domin kuwa shine ya turo ta wurinka, domin kasamu damar had'uwa da ita yau ma."

Al'amin ya fad'a yana mai kallon Yarima Asad, tukun ya d'ora da basa labarin duk abun da ya faru, saboda ganin da yayi ya zuba masa idanuwansa da alamun yana son sanin ta yadda a kayi Habu'n ya san da batunne.

Lumshe idanuwa Yarima Asad yayi a lokacin da Al'amin ya gama fad'a masa yadda sukayi da Habu.
Hak'ik'a Al'amin d'an uwan arzik'i ne, ako da yaushe ba shi da wani buri wanda ya huce ya gansa yana murmushi, duk wata damuwarsa yana mayar da ita tasa, tabbas shi da kansa ya sani ba shi da wani abu wanda zai iya biyan Al'amin da shi a duniya.


*JAHAR KAGUL, CIKIN MASARAUTAR FUL'DE.*

Tana k'arasawa cikin d'akin nata ta huce kan gadonta tana mai zubewa akansa tare da lumshe idanuwanta.
Sosai take jin zuciyarta na mata wani irin rad'ad'i da k'una.
Yayinda hawaye kuma har lokacin suke cigaba da tsiyaya daga cikin idanuwanta.
Tabbas ko ganinsa bata son ta sakeyi a rayuwarta, ballantana kuma har taji sautin muryarsa.
Hak'ik'a babu wani mutum da take buk'atar ya furta mata kalmar so duk kud'in sa, kyawunsa da mulkinsa bayan Gid'ad'o d'in ta.
Shi ta fara so, shi kad'ai ta sani a duniyar so, kana kuma da shi take buk'atar ta k'ark'are rayuwarta ta duniya.
Tabbas ita d'in ta Gid'ad'o ce haka Gid'ad'o ma nata ne.
Ta raya haka a cikin ranta tana mai cigaba da kukanta.

Acan b'angaren Habu kuwa ba shi ya koma d'akin nasa ba har sai bayan barinsa da kusan minti arba'in, tukun ya doso wurin, saboda yana tinanin a wannan lokacin sun riga da sun gama duk wata tattaunawar da zasu yi.
Amma sai dai kuma tun daga nesa mamaki ya lullub'esa, tare da tinanin wurin da motar Asad ta koma.
Saboda ganin da yayi bai hangota ba a wurin da ya tafi ya barta, asalima babu ko kalar tayoyinta a cikin duka wurin.
Hakanne yasa sa k'arasawa zuwa cikin d'akin nasa da matuk'ar sauri.
Sai dai kuma tun kafin ya kai ga gama shiga ya hango kujerar da ya tafi ya bar Yarima Asad akanta wayam babu shi babu alamunsa.

Cikin tsantsar mamaki had'i da d'an rud'u ya juya baya da sauri, yana mai fucewa daga cikin d'akin.

Direct ya huce wurin mutanen da suke gadin get d'in gidan nasu, yana mai tambayarsu shin wanda suka shigo tare da shi yazo ya tafi ne.
Ai ko take a wurin suka amsa masa da ai ya dad'e da tafiya ma.
Hakanne ya sanya Habu juyowa jiki asanyaye yana mai nufar hanyar da zata kaisa wurin Haddiyal, domin yaji daga gareta.

Da sallama d'auke a bakinsa ya tura kansa zuwa cikin d'akin.
Hangota da yayi kwance akan gado ta kife kanta a cikin fulo da alamun kuka ma take ne ya sanyasa k'arasawa zuwa wurin da take a matuk'ar firgice.

"Haddiyal! Haddiyal!!
Me ya sameki ne? Me ya faru da kika kwanta kina kuka?"

Ya watso mata tambayoyin a jera, kana kuma cikin sauri bayan ya zauna a gefen gadon.

Mirginowa Gimbiya Haddiyal tayi daga kwancen da take, tana mai mik'ewa zaune tare da zuba k'wayoyin idanuwanta akan fuskar Habu.
Kana daga bisani ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Shin me yasa kasan shine zakace mun naje da kaina Hamma?"

Ta fad'a tana mai zuba

Please Login or Register in order to submit comment