Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fad'a.

Yayinda Al'amin da Bir kuma da suke zaune akan kujera suka kalli junansu suna masu sakin murmushi, saboda su da duk sunyi tinanin za'ace za'a fasa kai musu Amaren yau.

Kama hannun Gimbiya Haddiyal da Gimbiya Tasmir Fulani tayi tana mai nufar bedroom d'inta dasu, domin kuwa ta tanadar musu kayan da zasu sanya su tafi gidan mijin nasu dasu dama.

Hakan da suka ganine yasanya Babban Yaya ya taimakawa Yarima Asad ya mik'e tsaye.
Tukun suka doshi d'akin Yarima Asad suma d'in domin su shirya.
Shima Sheikh Ahmad kuwa yana gama yin addu'a acikin ruwan ya barwa Umminsa shi, yana mai fad'in gashi nan akai musu shi gidan nasu, daga shi har ita suna shansa, sannan shima ya huce d'akin Yarima Asad d'in, saboda dama sunce su zasuyiwa k'annen nasu rakiya.

Misalin k'arfe tara na dare aka gama shirya gaba ki d'aya Amaren cikin wani azababben yellon less, tukun aka fara kaisu wurin Mai Martaba yayi musu nasihohi sosai, sannan aka kaisu wurinsu Ummi, Iyayen Gimbiya Tasmir, harma da Iyayen Gimbiya Haddiyal, dukansu sukayi musu nasihohi, sannan aka fuce dasu ana masu sasu acikin mota duk da kasancewar gidanjen anan cikin Masarautar suke kuwa.
Gaba d'ayansu shararar k'walla suke, musamman ma Gimbiya Haddiyal da bata tab'a tinanin zuwan wannan ranar ba.

Sosai gidajen nasu suka tsaru suka kuma yi bala'in kyau, cikin azababbun kayan funitres d'in da aka k'awata su dasu.

Plat buildings ne masu d'auke da babban falo tare da 5 bedroom a cikinsu, sai k'aton compound da yake d'auke da parkin space a cikinsa, tare da wasu irin shukokin furanni masu tsananin kyau da sukayi bala'in k'awata gidajen.
Motocine har guda ukku acikin gidansu Bir, yayin da guda biyu kuma suka kasance nasa, sai guda d'aya kuma ta Gimbiya Tasmir, kuma hakan duk aikin Mai Martaba ne.

2 bedrooms ko wacce gareta da yaji had'ad'un kayan funitures, sai kuma guda d'aya na mazajensu da suma suka gaji da had'uwa.
Haka dai Iyaye suka kaisu suka tawo sunata yabon gidajen aka barsu da 'yammata kawai.

Misalin k'arfe tara da rabi dai-dai suma su Bir suka gama shiryawa cikin wasu had'ad'un bluen shadda getzner da Babban yaya yayi musu ita su duka ukkun.
Sai dai kuma har lokacin Babban Yaya rik'e yake da hannun Yarima Asad acikin nasa, saboda kwata-kwata babu k'wari a jikinsa sai azababben ciwon kan da har yanzu yak'i sakinsa.
A haka suka k'arasa b'angaren Fulani tayi musu nasihohi sosai, kana kuma da suka futa daga nan suka huce b'angaren Mai Martaba, Sosai shima yayi musu nasihohi masu ratsa jiki, tukun suka futo daga nan ciki.
Haka duk suka zaga wurin Iyayen nasu tamkar yadda Matan sukayi kowa yasa musu albarka, tukun suka shiga motar Babban Yaya, Angwayen daga gidan baya, yayinda Babban Yaya da Sheikh Ahmad kuma suke zaune a gaba, Baban Yaya na driving a haka har suka k'arasa wurin gidajen.
Kasancewar kuma gidan Yarima Asad ne a farko shiyasa suka fara futowa gaba d'ayansn har su Bir, tukun Babban Yaya ya sake dafa kafad'arsa sukayi cikin gidan.

Anan cikin had'ad'd'en falon da za'a iya kiransa da aljannar duniya suka tsaya suna masu zama akan kujeru.
Tukun Sheikh Ahmad yacewa wata budurwa data futo ta gaishesu su cewa Amaryar ta futo nan.
Hakan kuwa akayi cikin k'ank'anin lokaci sai gasunan sun dawo, d'aya daga cikinsu na rik'e da hannun Gimbiya Haddiyal da fuskarta take lullub'e acikin mayafi.
Tukun gaba d'ayansu suka zauna akan kujerun da suke facing d'in wacce su Sheikh Ahmad suke akai.
Sai dai kuma ko gama dai-daita zaman nasu basuyi ba suka ji muryar Babban Yaya yana mai fad'in.

"To sai da safenku, kowacce taje ta kwanta ko."
Saboda fahimtar da yayi na yaran ba kunya garesu ba so suke suce sai sun basu na siyan baki, duk da sanin da sukayi na su d'in ba abokan ango bane."

Cikin sanyin jiki kuwa gaba d'ayansu suka mik'e suna masu cewa Haddiyal sai da safe tare da fucewa.
Wanda hakan kuma shine ya sanya Sheikh Ahmad yayi gyaran murya, yana mai fara yi musu nasihohi masu ratsa jiki da jini akan zaman aure da sauke hak'kok'in junansu da suka rataya akansu.
Sosai kuwa nasihohin sukayi tasiri a cikin zuciyar Haddiyal, tukun bayan ya gama shima Baban Yaya ya d'ora daga inda ya tsaya.
Sannan a k'arshe suka tashi, Babban Yaya yana mai cewa Haddiyal ta taimaka masa ya shiga daga ciki kansa na ciwo ne sosai.
Da "tom." Ta amsa tana mai murza 'yan yatsun hannunta da suke sark'e a wuri d'aya.

Yayinda shi kuma Bir ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Dan Allah idan anje gidan Al'amin ayi shaf-shaf, danni dai gaskiya na gaji, yanzu nasan Gimbiya tana can tanata jirana."

Da sauri daga Babban Yaya har Sheikh Ahmad suka zaro ido suna kallonsa.
Kafin daga bisani kuma Sheikh Ahmad ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Wai kai wane irin angone da basa da kunya ko kad'an."

Turo baki Bir yayi tamkar k'aramin Yaro, kana yana 'yan gunguni ya futa.
Haka suma d'in suka bi bayansa suna kallonsa tare da mamakinsa.
Suna futa daga nan d'in kuma gidan Al'amin suka shiga da yake a tsakiya.
Suma d'in dai nasihohi da jan hankali sukayi musu kamar yadda sukayi a gidan Asad.
Tukun suka tashi suna masu fucewa suka doshi gidan rasa kunya Bir, da yaketa faman sakin murmushi, wanda hakan kuma dasu Sheikh Ahmad suka ganine ya sanyasu girgiza kai kawai suna masu murmushin suma.

Zaune suka samu Gimbiya Tasmir akan kujera ita kad'ai, domin kuwa 'Yammatan dasu Sheikh Ahmad suka kora daga gidan Haddiyal suna futowa nan d'in suka shigo suna masu cewa 'Yammatan da suke tare da Gimbiya Tasmir.

"To iyayen sambanza idanma zaku futo ku futo, saboda wallahi ba Abokan Angwaye bane Yayyinsu ne kuma korar hulak'anci zasuyi muku."

Hakan da sukaji ne kuwa ya sanyasu mimmik'ewa suna masu cewa Gimbiya sai da safe.
Wanda hakan kuma ya sanya ta dawo falo ta zauna ita kad'ai kanta lullub'e a cikin mayafinta, saboda jin da tayi sunce falo zasu kirata inma sun shigo.

Ba tare da wata kunya ko karaba Bir ya huce jikin Gimbiya Tasmir yana mai zama ya manne mata, fuskarsa d'auke da murmushi.
Hakan dasu Sheikh Ahmad suka ganine ya sanyasu girgiza kansu, suna masu zama akan kujera suma.
Tukun suka fara yi musu nasiha mai ratsa jiki da jini, data sanya gaba ki d'aya jikinsu yin sanyi.

Tukun a k'arshe bayan sun gama suka mik'e suna shirin tafiya, a lokacinne kuma Bir shima ya mik'e, saboda ya rakasu daga nan kuma ya rufo gidan.

"Kai kai Masha Allah, irin wa'yannan motoci haka, amma gaskiya Mai Martaba yanaji da wa'yannan Yaran nasa."

Cewar Sheikh Ahmad suna masu yin wurin motocin da shi da Babban Yaya.
Take kuwa Bir ya tsuke fuska, saboda shi dai ya k'agara suyi suyi su tafi, amma yaga sai wani dak'ilewa suke yi.

Ganin da yayi sun tsaya ajikin motar suna magana ne, ya sanyasa matsowa wurin da suke, yana mai turo baki tare da fad'in.

"Matanku suna can suna jiranku har shad'ayan dare yayi, amma kunk'i ku koma sai kunja sunji tsoro. To ni dai dan Allah ina son tafiya wurin Gimbiya, nasan yanzu ma ta fara jin tsoron gidan."

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un korarmu ma kake kenan Abdulmajid dan munzo gidanka, to kwantar da hankalinka ko minti d'aya bazamu k'arayi acikinsa ba."

Da sauri kuwa ya juya baya yana mai sakin murmushi, saboda abunda yaji yayan nasa yace.
Kana ya bud'e baki cikin shagwab'b'ab'iyar muryarsa yana mai fad'in.

"Ni fa ba korarku nake ba."

"Kai rabu dashi k'anina da gaskiyarka ai."
Cewar Babban Yaya yana mai sakin murmushi, tukun su kuma sukayi hanyar wajen yana biye dasu a baya.
Suna shirin futane kuma Sheikh Ahmad ya juyo yana kallonsa, tare da fad'in.

"Allah dai yasama baka manta da duka addu'oin dana koya mukuba garin wannan zumud'in."

"Allah ban manta komai ba Yaya Sheikh, banda ma dai dare yayi da yanzu na karanto maka su kaji."

Bir ya fad'a cikin sauri fuskarsa d'auke da murmushi.

"Tom shikenan sai da safenku."

Suka fad'a a tare suna masu fucewa daga cikin gidan.
Garam, kuwa sukaji ya bugo murfin get d'in ba tare da ko amsa musu yayiba, yana mai juyawa ya doshi cikin gidan.

Ko da ya shiga cikin falon bai tadda Gimbiya aciki ba, hakanne ya sanyasa zaro idanuwansa waje yana mai waige-waige, tukun daga bisani kuma ya d'aga k'afafuwansa yana mai dosar d'aya daga cikin bedroom d'inta, wanda yake tsammanin tana cikinsa, saboda hasken futulun daya hango.

Da sallama d'auke a bakinsa ya turo kansa zuwa cikin d'akin.
Cak ya tsaya daga bakin k'ofa yana mai zuba k'wayoyin idanuwansa akanta, saboda hangota da yayi zaune a tsakiyar gado, fuskarta rufe da gyalenta.

Hakan kuwa shine ya sanyasa jin wani irin farin ciki, tare da mugun shauk'i suna lullub'esa.
Cikin sanyin ya fara d'aga k'afafuwansa yana mai nufar gadon, har yanzu idanuwansa akanta.
A hankali kuma ya haye saman gadon, yana mai matsawa daf da ita daga gabanta, tukun ya tank'washe k'afafunwansa.
Kana ya bud'e baki cikin wata irin murya ta mussaman da bata sansa da itaba sai yau, yana mai fad'in.

"To me ye kuma abun wani rufemun fuskar, salon kawai ki wahalar dani ko Ammatana."

Rumtse idanuwanta tayi, saboda yadda sautin muryar tasa ta daki har mad'igarta, sannan kuma ta saukar mata da 'yar guntuwar kasala, amma sai dai bata bud'e fuskar ba, asalima bata da niyya sai durk'usar da kanta k'asa data k'arayima.
Hakan da Bir ya ganine kuma ya sanyasa sake bud'e baki, yana mai fad'in.

"Wai me kike nufi da wannan k'udun-dunar jikin da kikeyi? To bari kijima yarinya, wallahi baza'a aikata sab'o a gidana ba, dan haka bud'e mun fuskata na gani, babu ruwan mu da wata kunya mu dama kowa ya sani."

Ya k'arasa maganar yana mai mik'a hannunsa ya janye gyalen data rufe fuskarta dashi.
Hakanne yasa tayi saurin kai tafukan hannayenta kan fuskar ta tana mai rufeta tare da turo baki.

"Ai kuwa wallahi baki isaba sai kin bud'e mun naga kayata."

Bir ya fad'a cikin wata irin murya mai tafe da shagwab'a, yana mai janye hannuwanta daga kan fuskarta ta.

"Ni dai a'a."

Ta fad'a a wani irin sakalce tana mai rumtse idanuwanta.
Hakanne kuma ya sanya Bir ya kafe fuskarta ta da idanuwa, yana mai yaba asalin kyawun hallitar da Allah yayi matan.

Jin da tayi yayi shiru ne kuma ya sanyata bud'e idanuwan nata.

Take kuwa suka fad'a cikin nasa, kana kuma ta janye nata idanun da sauri, saboda hakanan kawai yau take jin yay mata wani irin mugun kwarjini shi d'in.

"Godiya ta tabbata ga Allah daya mallakamun wannan kyakkyawar hallitar tasa a matsayin Mata, hak'ik'a ni d'in d'an sa'a ne zan fad'a da kaina basai wani ya fad'a ba, tun da har na mallaki Gimbiyar Gimbiyoyi."

Ya k'arasa maganar yana mai janyota cikin jikinsa cikin wani irin yanayi na tsantsar shauk'in da yake jin kansa a ciki.

"Ni dai ka sakeni dan Allah."

Ta fad'a tana mai turo lips d'inta gaba.
Hakanne kuma ya sanyasa kafe jajayen kyawawan lips d'in nata da suke ta futar da k'yallin man leb'e da ido, yana mai jin wani irin abu na fuzgarsa zuwa garesu.
Tukun daga bisani kuma ya janye idanuwan nasa akansu, yana mai fesar da sassanyan numfashi, kana ya bud'e baki, yana mai fad'in.

"To taso muje muyo alwala, sai muyi sallah mu godewa Ubangiji daya mallakamana junan mu ko."

"Nayi alwala ni."
Ta fad'a a tak'aice tana mai zuro k'afafuwanta k'asa.
Hakanne kuma yasa ya mik'e shima, yana mai kama hanyar bathroom d'in da yake acikin d'akin.
Bai wani jimaba ya futo yana d'igar ruwa.
Tukun ya shimfid'a musu prayer mat tare da mik'o mata sabon hijab.

Raka'a biyu sukayi tamkar yadda addini ya koyar, kana bayan sun idar ya dafa goshinta yana mai yimata addu'ar da Sheikh Ahmad ya koyar dasu.
Kana bayan sun gama ya mik'e tsaye yana mai fad'in.

"Jirani naje na dawo Gimbiyata."
Tukun ya fuce daga cikin d'akin.

Bai wani d'au dogon lokaci ba kuma sai gashinan ya dawo hannunsa rik'e da plate, da kuma kofi tare da ledar da suka shigo da ita.
Wurin daya tashi ya koma ya zauna.
Kana kuma cikin nutsuwa ya bud'e ledar yana mai juye farfesun naman kajin da yake futar da tururi tare da asalin k'amshi acikin plate d'in.
Tukun ya gyara zamansa, kana kuma ba zato ba tsammani Gimbiya Tasmir taji ya d'agota yana mai d'orata akan cinyarsa.

Da k'arfi ta rumtse idanuwanta, saboda yadda taji gabaki d'aya tsigar jiki ta sun mik'e yarrr.
Afannin nasa shima hakan yaji, sai dai kuma hakan baisa ya fasa abun da yayi niyyaba.

Hannunsa ya zura cikin plate d'in yana mai yago lallausar tsokar kazar dashi.
Sannan ya d'ora lallausan gemunsa akan kafad'arta, yana mai fara jujjuya kansa yana goga mata shi har zuwa wuyanta.
Kana ya d'ago hannunsa da yake rik'e da naman, yana mai kawosa saitin bakinta tare da fad'in.
"Haaaa!!"

Da sauri kuwa ta bud'e bakinta domin ta futar da numfashi ta nan, saboda yadda yake mata da yasa ta jin tamkar numfashin zai d'auke, wanda hakan kuma ya bashi damar tura mata tsokar acikin bakinta haryana had'awa da yantsunsa.

Lumshe idanuwanta tayi kuwa, tana mai taunarta ahankali.

A haka dai yayta ciyar da ita shima yana ci, kana kuma yanayi yana yawo da fuskarsa tare da d'ayan hannunsa a sassan jikinta, ahaka harta ture masa hannu gefe, kasancewar kuma shima ya k'oshi a lokacin, shiyasa ya bud'e murfin k'atuwar jarkar yoghurt d'in, yana mai tsiyayasa aciki.
Sannan ya d'agosa yana mai kaisa saitin bakinta.

"Na k'oshi."
Ta fad'a asanyaye, kana kuma cikin shagwab'a.
"Dan kadan to kinji."
Ya fad'a yana mai sake d'ora mata cup d'in akan lips d'inta.
Hakanne ya sanyata bud'e bakin tasha, tukun bayan ta gama sha shima ya d'an sha kad'an.
Kana ya sauketa daga kan cinyarsa, yana mai mik'ewa a matuk'ar kasalance, ya d'abe kwanikan yana mai fucewa dasu.

Hakan data ganine ya sanyata mik'ewa itama tana mai fara cire kayan jikinta.
Tukun ta sanya wata lallausar sleeping dress a jikinta.
Kana ta huce cikin bathroom kai tsaye.
Bata wani d'au dogon lokaci a cikiba kuma ta futo da alamun dai brush tayo.
Tukun tazo ta haye saman gadonta, tana mai jan lallausan bargon da yake akansa ta rufe jikinta da shi.

Shi kuwa Bir d'akinsa ya huce bayan ya ajiye kwanikan, yana mai hucewa cikin d'akinsa yaje yayi brush tare da d'auro alwala, kana ya sanya brown d'in jallabiya a jikinsa yana mai fucewa daga cikin nan ya doshi d'akin Gimbiyarsa.
Yana shigowa ciki ya kashe k'wan d'akin, yana mai barin na kwanciya bacci, tukun ya huce kan gadon kai tsaye yana mai kwanciya akai, tare da bud'e eskimon da take a cikinsa ya shige yana mai matsawa kusa da ita.


Acan b'angarensu Yarima Asad kuwa, su Babban Yaya na futa Gimbiya Haddiyal ta taso jikinta a bala'in sanyeye tana mai yowa wurin da yake zaune lumshe da idanuwansa yana faman cizon leb'e.

"Sannu kaji."

Ta samu kanta da fad'in haka ba tare data shirya ba.

Jinjina mata kai kawai yayi, yana mai d'an bud'e idanuwansa da suka k'ank'ance ya kalleta.

"Katashi ka tafi d'akinka to ni zan tafi nawa."
Ta fad'a a sanyaye tana mai kallonsa daga tsayen da take.

"Bazan iya baaah!!!"

Ya fad'a cikin wata irin sassanyar murya, yana mai jan wani irin numfashi a k'arshen furucin nasa.
Da sauri kuwa ta lumshe idanuwanta, saboda yadda taji sautin muryar tasa ta ratsa har cikin kwanyarta, ga kuma tsigar jikinta da taji duk sun bada yarrr!

Tukun cikin kasalalliyar muryarta ta sake bud'e baki, tana mai fad'in.

"To tashi in temake ka."
Ta k'arasa maganar tana mai lumshe idanuwanta, yayinda nasihohin Sheikh Ahmad kuma suka farayi mata amsa kuwwa a cikin k'wak'walwa.
Shi kuwa hakan da yaji ta fad'ane ya sanya sa mik'ewa da k'yar, yana mai cizon leb'ensa. Sai dai kuma yana gama tsayawa yayi baya-baya yana shirin kifawa k'asa tamkar d'an maye.
Da sauri kuwa ta matso wurinsa tana mai fad'in.
"Ayyah sannu kaji."
Tukun ta kama hannunsa d'aya suka fara d'aga k'afafuwansu, suna masu dosar d'aya daga cikin bedroom d'in.

Har bakin gado ta kaisa, kana ta fara shirin sakinsa, tana mai fad'in.

"To zauna gashi na kawoka."

Hakan da yaji ta fad'ane kuma ya sanyasa bud'e shanyayyun idanuwansa yana mai kallonta.
Wai gashi ta kawosa tamkar wacce ta wani d'aukosa, daga d'an dafa masa hannun da tayi.
Ya fad'a a cikin ransa yana mai shirin zama.
Ita kuwa Gimbiya Haddiyal, tana shirin juyawa ta tafine ta taka ledar biscuite d'in da d'aya daga cikin 'Yammatan da suka rakota ta yar a wurin.
Ai ko take ta tafi baya luuu, tana mai shirin kifawa kan gadon.
Wanda hakan kuma da Yarima Asad ya ganine yasa sa yin kanta da sauri da niyyar ya tarota, saboda shi duk a tinanisa k'asa zata fad'a, kasancewar kuma jikinsa babu k'warine kwata-kwata, shiyasa tana fad'awa kan gadon shima ya biyota yana mai kifowa kanta, yayinda kansa kuma da yake tsananin ciwo ya gwaru da nata kan, tausasan red lips d'insa kuma suka sauka akan nata pink lips d'in, tamkar wanda aka hankad'o.......✍


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*






*33*

*END*



*GAISUWA TA MUSAMMAN TARE DA JINJINAR BAN GIRMA ZUWA GAREKU MUTANEN K'WARAI.* πŸ‘πŸ‘

_MUHAMMAD KARIM MK_
_HASSAN ATK_
_HUSSAINI ATK_
_IT'S ABBAS_
_NAZIFI YARIMA_
_AK SARAKI_
_MU'AZ_
_MUHSHANIQ_
_DR MUHAMMAD MK_
_ALL THE MEMBERS OF MK PALACE ADMINS._
_AND ALL THE MEMBERS OF ATK PALACE ADMINS._

*ALKHAIRIN ALLAH YA ISAR MUKU HAR GADON BACCINKU* 😍😍


_KUMA BAN MANTA DA KU BA MASU COMMENTS DA SHARHI, INA MUKU FATAN ALKHAIRI ADUK INDA KUKE GABA DAYANKU, KUNYI YAWAN DA BAZAKU LISSAFU BA ALOKACI GUDA, AMMA KUSANI INA SANE DA KOWANNE DAGA CIKINKU, KUMA INA MATUKAR JIN DA'DIN ADDU'OIN KU GARENI MY FANS.* 😍😍_



"Washhhhh Allah na Mamyna Abbana wayyo kaina ciwo zai cireeehhh!!!"
Ya fad'a cikin wata irin murya mai matuk'ar rauni, idanuwansa na tara ruwan hawaye, saboda jin da yayi kan nasa tamkar zai dare gida biyu ta sanadin buguwar da yayi da nata.
Yayinda lips d'insa kuma suke karkarwa akan nata lips d'in, yana mai busa mata zazzafar iskar bakinsa.
Ita kuwa Haddiyal da k'arfi ta rumtse idanuwanta, tsigar jikinta na cigaba da mimmik'ewa, yayinda zazzafan numafshinsa kuma daya gaurayu da nata ya sake jefata cikin wani irin yanayi na tsantsar kasala.
Sosai take jin nauyinsa tamkar gini, sai dai kuma abun haushi amai-makon ita tayi raki sai taji shine yake yi harda wani Mamy da Abba yake kira.
So take kawai taji ya d'agata, amma gaba d'aya taji babu alama, hakanne kuma ya sanyata bud'e lumsassun idanuwanta domin taga a yadda yake.
Take kuwa idanuwan nata suka fad'a cikin nasa da suke cike da ruwan hawaye, banda aikin turo baki babu abunda yakeyi tamkar wani d'an k'aramin Yaro.

"Washhh Allah k'irjina."
Ta fad'a da k'yar, tana mai fara d'an jujjuya jikinta ko zai d'agata, amma gaba d'aya taji ta kasa motsawarma duka.
Shi kuwa Yarima Asad tsanin azabar zafin ciwon kan dake damunsa ne ya sanyasa kasa ko da k'wak'waran motsi daga yadda yake, saboda ko yaya ya motsa d'in ji yake kan nasa tamkar zai rabe gida biyu.

"Wayyo ni dan Allah ka d'agani!"
Ta fad'a acan k'asan mak'oshi, cikin tsananin gajiya, tana mai jin bayanta tamkar zai rabe gida biyu, saboda tsabar nauyinsa, amma still dai ba taga ya motsa daga yada yake ba.
Hakan kuwa shine ya sanyata fashewa da kuka tana mai dunk'ule tafin hannunta ta d'agosa tare da sakar masa dundu a gadon baya, wai ko zai d'agata.
Sautin shashshekar kukanta da yajine ya kuma ga hawayen ya sanyasa mirginawa gefanta a hankali, yana mai rumtse idanuwansa tare da damk'e tafin hannunta a cikin nasa gam, yana mai faman fad'in.

"Wayyo Mamyna Dadyna kaina zai cire."
Ya k'arasa maganar cikin wata irin murya mai kama data kuka, data sanya Gimbiya Haddilyal da take aikin sauke numfashin wahala juyowa ta kallesa da sauri
Ganin da tayi da gaske dai sosai kansa ciwon yake masa, saboda yadda taga yana d'an shura k'afafuwa tare da k'ara damk'ar hannunta, ya sanyata taji wani irin matsanancin tausayinsa ya lullub'eta.
A hankali kuma ta d'ago d'ayan lallausan tafin hannunta tana mai janye nasa da yake akan goshinsa ta kife nata a wurin, tare da d'an danne masa wata jijiya da take a gefen kunnensa da taga yanata faman danneta tun d'azu.

Da k'arfi kuwa ya saki ajiyar zuciya yana mai lumshe ido, saboda yadda yaji tamkar ta d'ebe wani kaso mai yawa daga cikin ciwon kan nasa ta sanadin jijiyar data danne masa.
Suna a hakanne kuma ba tare da sun shiryaba bacci b'arawo ya d'aukesu su duka biyun, ba tare da ko kayan jikinsu sun cireba kuma.

***
Kiran sallahr da akeyi a masallacin masarautar shine ya farkar da Yarima Asad daga nannauyan baccin nasa na yau.
Cikin wani ikon Allah kuma sai ya tashi babu ko alamun ciwon kan.
A hankali ya sake mayar da idanuwansa yana mai lumshesu, kana daga bisani ya k'ara bud'esu akan kyakkyawar fuskarta da take kife akan k'ijinsa.
Yayinda k'afarta d'aya kuma take akan nasa k'afafun, gaba d'aya dai ta kanannad'esa ta yadda har rabin jikinta ke kan nasa ba tare data sani ba.
A hankali ya d'an d'aga lab'b'ansa yana mai fesar da wata sassanyar iska daga cikin bakinsa, tare da cigaba da kallon fuskarta.
Yayinda yake jin wani irin farinciki mara misaltuwa tare da annashuwa suna lullub'esa, saboda ganin da yayi wai yau shine suka kwana wuri d'aya da Haddiyal d'insa rabin jikinta akan nasa jikin, shi da ta tsana ta tsani ko ganin fuskarsa.
Lokaci d'aya kuma wani sassanyar murmushi ya kufce masa, saboda tino moments d'insu na jiya da dare kafun suyi bacci da yayi, wanda hakan kuma ya sanyasa jin wani irin abu na taso masa tundaga ka tsakar kansa, yayinda tsigar jikinsa kuma take bada wani irin yarrr.
Kana daga bisani kuma ya bud'e baki yana mai fad'in.
"Alhamdulillah!"

Jin da yayi har an tada sallah ne, ya sanyasa fara k'ok'arin zame jikinsa daga nata a hankali, amma sai yaji ta k'ara kannand'esa sosai.
Hakanne kuma ya sanyasa d'an zaro idanuwansa waje, kana daga bisani kuma ya k'ara kamo hannunta yana mai b'anb'aresa daga jikinsa data rik'e, tukun yayi sauri ya janyo fulo yana mai d'ora matashi a wurin .
Sannan ya sauke k'afafuwanta daga kan nasa suma.
Sassanyar iska ya sake fesarwa, saboda ganin da yayi ta rik'e fulon ba tare data farka ba tamkar yadda yaso d'in.
Tukun a hankali kuma ya janye idanuwansa daga kan nata, yana mai mik'ewa ya sauka daga kan bed d'in, sannan ya kama hanyar bathroom.

Almost 30 minutes ya d'auka a cikin bathroom d'in, tukun sai gasa nan ya futo sanye da bathrobe a jikinsa, yayinda hannunsa kuma yake rik'e da wani d'an k'aramin lallausan towel, yana mai tsane sumar kansa da shi.

Kai tsaye yayi gaban dressing mirrow, yana mai zuwa ya d'au mai ya shafe jikin nasa da shi.
Kana ya huce gaban wadrobe yana mai bud'eta ya d'auko wata had'ad'd'iyar jallabiya blue colour ya sanyata a jikinsa.
Kana ya saka farin boxer kar, tukun ya juya wurin da prayer mat take yana mai shimfid'ata ya tada sallah.

Ko da ya idar da sallahr kuwa addu'a ya zauna yayi sosai, tare da azkarul sabah na cikin hisnul muslim, tukun ya huce zuwa wurin da ruwan addu'ar su yake ya d'ibi kad'an yasha, sannan kuma a hankali ya koma ya kwanta akan bed d'in ba tare daya matsa kusa da itaba, yana mai lumshe idanuwansa, saboda bacci yake son komawa shi dai.

Rufe idanuwansa ke da wuya ita kuma ta bud'e nata, wato dai ta tashi daga baccin.
Da sauri ta k'arasa wara idanuwanta tana mai bin cikin d'akin da kallo.
Lokaci d'aya kuma ta tuno da yadda ta kasance a tsakaninsu jiya kafun suyi bacci, hakanne ya sanyata juyawa bayanta.
Take kuwa idanuwanta suka sauka akan kyakkyawar tsararrar fuskarsa da take futar da wani irin annuri akanta.
Tashi zaune tayi daga kwancen da take tana mai sake zuba masa idanuwanta, kafin daga bisani kuma ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Tunda dama na gama wahalar jinyarka jiya da dare ai dole yau katashi kai sallah ni kak'i tashina."

Ta k'arasa maganar tana mai hararar fukarsa, domin kuwa ita duk a tinaninta bacci yake yi, sai dai kuma abunda batasani ba shine sarai yana jinta kuma yana ganinta, saboda ba rufe idanuwan nasa yayi ba tas.
Tukun ta d'ora da fad'in.

"Dubeshi dan Allah, ahaka kamar Jarumi ashe girmanne kawai, daga d'an ciwon kai ya ishi mutane da raki tare da kuka. Washhhh Allah na Mamyna Abban na wayyo kaina ciwo zai cireeehhh!!!"

Tayi maganar cikin kwaikwayar yadda yayi tana mai sake sakar masa harara.
Shi kuwa Asad da k'yar ya samu ya iya rik'e dariyarsa ba tare da ta k'wace ba, saboda sanin da yayi a tinaninta bacci yake yi.
Yayinda ita kuma ta d'ora da fad'in.

"Da wani nauyinsa kamar na buhun sumunti hamsin, amma yana jin zafin dunduna ya d'agani. Ai wallahi ka k'arane dan

Please Login or Register in order to submit comment